Turken Gida – Chapter Forty-six
by Janafty*MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE*
Washe-gari haka Yallaɓai ya tashi yana mini cin magani ina masa magana da ƙyar yake amsa ni, sai ya koma ma ya na ba ni dariya. Sai da na sallami yara zuwa makaranta sannan na yi ma Yumna wanka na shiryata na bashi ita ya riƙe ta na koma kitchen ina duba dankalin turawan da na saka amai kar ya ƙone.
Har Jidda yau suna da paper ta tafi daga ni sai Yallaɓai a gida sai Yumna ina daga Kitchen ina jiyo dariyan ta yana yi mata wasa. Mirmishi kawai na yi, in dai Yumna ne yanzu har ta waye da wasannin Yallaɓai ƙiyuwa ta fara yi ma Jidda saboda ita ba ta yi mata wasa amma da Baby ne ko su Khalipa da ba ma ganin su take yi koda yaushe ba har tana zillo in ta gan su. Yallaɓai ko ta riƙa harba ƙafafuwa kenan in ta gan shi in ko tana zaune ne sai ta tsintsira tun ina mamaki har na daina.
Yallaɓai da wuri ya ce mini zai fita, zai fara biyawa ta Gwammaja ya duba Nene kafin ya wuce office. Shi ya sa da wuri ya yi wanka ya shirya nima wankan na yi sannan muka zauna a kan dining muna karyawa sai kiran shi ake yi a waya harkokinsa can dai.
“Yallaɓai ka ce harkokin sun buɗe?
“Alhamdulillah.”
Ya faɗa fuskarsa ba walwala lokaci ɗaya yana tusa dankalin a bakin shi sannan ya bi da ruwan tea ɗin dake cikin ƙaramin mug a gaban shi.
“To duk fushin na mene ne mijin Sadiya?
Kallona ya yi sai kawai ya ɗauke kan shi ya cigaba da cin dankalin shi da tea.
“Mene ne uhm? Ni ce? To yi hakuri ka ji Yallaɓai na. Ba na son ina ganin ɓacin ranka”
“A baya ne ba ki san ganin ɓacin raina amma ban da yanzu.”
Ya faɗa ba tare da ya kalleni ba, sai na yi mirmishi kafin na ce” To na ji yi haƙuri ka ji?
“Uhn”
Ya faɗa kawai yana cigaba da tura dankali bakin sa.
“To ka ce ka haƙura mana?
“Me kika yi mini? Ba ki yi mini laifin komai ba so ki daina ba ni haƙuri”
“Na yi mana. Maganar jiya ko?
Na faɗa ina kallon sa, ni dai na san ran shi ya ɓaci kuma ya na jin haushina ko don ganin yadda yake magana yana cin magani.
“Ka yi haƙuri ni ba da kai nake ba”
“To da wa kike?
Ya faɗa yana kallona sai na kasa magana saboda ya zura mini idanuwansa cikin wani yanayi yana kallona.
Kai kawai ya girgiza sannan ya mai da kansa ƙasa ya cigaba da shan tea ɗin sa ba tare da ya ƙara wata magana ba ni kuma sai jikina ya yi sanyi sosai nima sai na debo dankali ina mai turawa a bakina cikin sanyin jiki da na zuciya.
Bai wani ci da yawa ba ya share bakin sa da tissue ɗin da ke saman dining sannan ya ɗago yana kallona nima shi na ke kallo.
“Har ka ƙoshi?
“Alhamdulillah”
Ya faɗa yana mai miƙewa sai kuma na ga ya koma ya zauna yana mai duba agogon fatan da ke tsitsiyan hannun shi na hagu, sannan ya sake ɗagowa yana kallona kafin ya kira sunana a kausashe.
“Sadiya”
“Na’am”
Na amsa ina kallonsa cikin natsuwa ganin kamar magana zai yi ganin yadda ya kira sunana.
“Kin yi mini laifi jiya kuma har na ji haushin ki. Amma sai na yafe miki kafin na kwanta saboda ba na so ki kwana da fushin Mala’iku a kan ki.”
Sai na kasa mgana na yi jagale ina kallon shi.
“Ba zan hana yin magana ba saboda bakin ki ne. Amma ina so ki sani ni mijin ki ne, ki san irin kalaman da za ki riƙa amfani da su wajen mgana da ni, mijin ki ne ni ba kanin ki ko ɗan ki ba, bai kamata ina fara magana ki rufe ni da faɗa ba kina ta faɗin mganganu son ranki, daga karshe ma har zagina kika yi.”
“Zagi kuma? Ni?
Na faɗa ina nuna kaina cikin zaro ido.
“E zagi ko ƙarya zan yi miki? > Janaftybaby: Ya faɗa yana kallona, sai na kasa magana na dukar da kaina ina fadin” Ni fa ba da kai na ke yi ba. Kawai na”
“Kawai me! Ai ni ne na ke yi miki maganana. Ya kamata ina magana ki ce mini jar uba!?
Ya faɗa yana mai kafe ni da ido sai ya karya lagona. Saboda na san ban kyauta ba amma na kasa magana ba.
“Kar ki sake, ba na so in kuma kina so ki ƙure hakurina ne to shike nan ki ciga ba. “
Ɗagowa na yi ina kallonsa ganin ya mike tsaye alamun zai fita.
“Ka yi haƙuri.”
“Na haƙura na faɗa miki ne saboda ki kiyaye.”
“In sha Allahu.”
Na faɗa cikin sanyin murya kamar ba shi ba sai na ga ya yi mirmishi ya matso ya ɗan ramkwafa ya sumbaci goshinaa.
“Sai na dawo.”
Na miƙe ina shirin masa rakiya da sauri ya saka hannuwan shi ya ma yar da ni zaune ya na faɗin” Ki gama ba sai kin yi mini rakiya ba.”
“To sai ka dawo. Allah Ya ba da sa’a.”
“Amin ki kular mini da kanki. Ke da Yumna.”
Sai na gyaɗa masa kai, ina kallonsa har ya fice daga falo ya bar mini ƙamshin turaren shi, ina zaune a wajen na ji tashin motarsa da fitarsa sannan na ji karan jan get an ma yar an rufe, ajiyar zuciya na sauke sannan na cigaba da tura dankalin gabana nima sai na ji cikina ya tushe sai kawai na tattara na rufe ma su Baby in sun dawo makaranta su ci, da yake da safen ma ba su tsaya ci ba amma sun tafi da shi. Khalipa da Anwar amma Jidda tuni ta daina ɗaukan abinci ta ce na yara ne. Baby ce ba ta girma ita wannan uwar acicin ma ranar da ba ta je da abinci makaranta haka za ta dawo kamar ta ci babu.
Bedroom na koma saboda na baro Yumna tana barci, wayata na ɗauka ina latsawa bayan na zauna a gefen gado Data na buɗe na shiga yanar gizo-gizo ina ganin abin da ke faruwa, waɗanda suka yi mini magana duk na amsa su yawancin duk masu oder hijabai ne da yake na kwana biyu ban kawo su amma ina haɗa kan kudaɗen hannuna ne, ko na salla babba ban saro hijabai ba, na dai saro su inners ɗin saboda ba ishashun kudaɗe a hannuna. Daga nan I. G na shiga ina ta kalle-kalle na sai da na gaji jin na fara jin barci sannan na ijiye wayar na kwanta ban tashi ba sai bayan azahar Allah ya taimake ni yau Yunma barci take sha ko tashi ba ta yi ba amma na san za ta taɓa kukan dare tun da ta yi barcin rana sosai haka.
Barcin da na yi duk sai ya sakar mini kasala shi ya sa ko girki ban yi ba. Gidan ma ko sharan shi ban yi ba, yini na yi kwanciya sai danna waya sai da Yumna ta tashi ne na haƙura ma da kwanciyar da suka dawo daga makaranta sauran dankali suka sha tare da Tea, Jidda kuma na ce ta ɗora mana girki har da ni da Babansu tun da yau ba zan iya yin wani girki ba. Shinkafa da miya ta yi sai na kira Musbabu na ce in ba damuwa ina son kayan lambu, sai ya ce mini ba sa nan sun fita shi da Yallaɓai sai na ce to ya bar shi kawai daga karshe Adnan na kira shi ya siyo mana su kabeji da cocumber sai da ya kawo na bashi kudin nan ma ya yi isha’i ya ci abincin yana ta santin har yana ba ma Jidda Tuƙwaicin dubu biyar na girkin da ta yi. Bai jira dawowar Yallaɓai ba ya ta fi saboda Yallabai sai after 10 ya dawo a gajiye ya ce mini na haɗa masa kayan tafiya kala uku Jigawa zai je gobe kuma akwai yuyuwar ya yi kwana uku a can.
Tafiyar Yallaɓai ya sa su Khalipa ba su koma gidan su ba, ni kuma ban ji na duba ta ba na dai kira ta a waya na yi mata sannu ta ce mini ai ta ma samu lafiya, har tana ce mini ya su Khalipa an kawo mini hayaniya na ce ai ba komai. Yallaɓai sai da ya yi kwana shidda sannan ya dawo. Washe gari kuma ko hutawa bai yi ba ya wuce Kaduna daga can ya je Abuja kwangiloli ne yake samu ga su nan akai akai shi ya sa yanzu ba ya samun zama dalilin haka ne ya sa su Khalipa suka share wajen sati uku a gidana ba su koma ba sai a satin da suke da uku ne Yallaɓai ya samu zama a weekend ranar kuma sai ya faɗo yana gidana ne.
Safiyar lahadi, ranar Yallabai zai koma gidan Gimbiya kuma ya ce a shirya kayan su Khalipa za su koma gida tun da Gimbiyar ta samu lafiya. > Janaftybaby: Wankin kayan su daman mai wanki na haɗa mawa sai na kira shi na ce ya kawo sauran kananun kuma tare da Uniform na saka Jidda ta ɗan wanke musu, ni da Baby kuma muka gyara gidan bayan mun gama na ce ta gyara Kitchen ta yi mini wanke-wanke sai Baby ta fara tura baki tana cewa ita kanta ke ciwo.
“Ai ko kan naki zai cire ne sai kin gyara mini Kitchen kin kuma yi mini wanke-wanke yarinya.”
Na faɗa ina zare mata ido. Ta san halina tana yi mini wata magana za ta ji dundu shi ya sa bakin ta alaikun ta wuce, Jidda ke yi to yau tana wanki in ta gama ma za ta yi mu su Khalipa wanka. Yumna na goye a baya tun da na yi mata wanka take barci. Yallaɓai na ciki yana ta barci tun bayan da ya dawo sallar asuba ya koma bai tashi ba har muka karya sai ban tashe su ba sanin ya fi sati biyu bai samu lokaci ya huta ba bawan Allah ya na ta fadi tashi duk an kan mu, jiya ma Gwammaja muka yini ni da yara sai dare muka dawo da yake Nene ta ɗan yi zazzabi kwana biyu.
Baby na tura baki da komai ta gama aikin da na saka ta ban bari ta zauna ba na ce ta ɗora musu abinci Jidda tana gama ayyukata ta saka hijabi ƙawayenta sun biyo mata sun tafi tahfez suna ta mura’ju’a domin an kusa yin musu walimar saukar su, jarabawa kuma sauran ta paper ɗaya su gama shi ya sa nake ta tunanin tun da abin ya zo a tare zan ɗan jinkirta na haɗe graduation ɗin ta tare da Walimar saukar su gabaɗaya.
Yallaɓai sai biyu saura ya tashi, ya yi salla sannan ya sha tea ya hau kuma aiki a cikin laptop ɗin sa na wani lokaci ni kuma a lokacin na gaji sai kawai na kwanta Yunma ma a wajensa na bar ta, na daɗe ina barci sai bayan la’sar na tashi shima ɗin hayaniyan yaran ne ya tashe ni, na duba agogon wayata hudu da rabi har ta gota sai ban fita ba, na shiga Tiolet na ɗauro alwala na zo na yi salla sannan na fita falo. Abin da na gani ne ya sa ban san na riƙe kugu daga korido na ƙame ina kallon ikon Allah ba.
An yi mini kaca kaca da falo ba ma wannan ne abin mamakin ba. Illa Yallaɓai da na gani daga shi sai bakin wando sai singlet haka su Khalipa ba riguna sai kananun wanduna har da Baby itama ta ci zanzaro da kayan tekwando ɗin su na makaranta suna wasan doke ni in doke ka su da Yallaɓai gabaɗaya sun haɗa zufa. Jidda ce kaɗai ba ta shiga ba tana zauna ɗauke da Yumna da ke zillo kamar ta je a yi da ita.
Baki na saki da hanci ina kallon ikon Allah. Yallabai na ware hannu yana faɗin su zo su zo, suna zuwa suna kai masa duka yana tarewa suma yana kai musu suna tarewa, Baby ce ta ba ni mamaki yadda na ga ta ware ƙafa ta na kai ma Yallaɓai bugu yana ƙarewa itama yana kai mata tana karewa da sunan wasa. Na ma kasa magana saboda haushi da mamaki Jidda ce ta fara ganina tana dariya ta ce.
” Umma ko zaki shiga a yi chinese din da ke ne?
Hararan da na wurga mata ne ya sa ta rufe bakinta tana dariya ƙarisowa na yi falon ina fadin” Na shige su ni Halima. Yallaɓai me zan gani haka?
Sai a lokacin ya lura da ni ya na wani tsalle na ga kamar zai yo kaina na kwace ina faɗin” Yallaɓai.'”
Na ma kasa magana saboda mamaki Baby ta kalleni tana faɗin” Umma akwai dadi ki shigo mu yi da ke’
“E Umma ki shigo”
In ji Khalipa.
Hararansu na yi kafin na ce” Ni? Ai ba ni da irin ƙarfin ku Allah ya ba da sa’a.”
Buɗe bakin Yallaɓai sai cewa ya yi wai na zo ko na rage kitse na ce na ji, amma ni ba zan shiga ba na tuna lokacin ina amarya Yallaɓai ya yi ta ja na da irin wannan wasan tuni na nuna masa bana so saboda shi ya iya kai duka ni kuma ban iya ba daga wasa sai a cuceka.
“Ke me ya sa ba ki shiga ba?
Na faɗa ina zama gefen Jidda. Yumna na ganina ta fara zillo tana miƙo mini hannu sai na karbeta.
“Ban iya ba Umma.”
Ta faɗa a hankali ni da man na san ba za ta shiga ba. Ina son Jidda saboda kamewarta da Ajin ta.
“Kin taimaki kanki. Ita wancan da ba ta san ciwon kanta ba ai ga ta can ta na ware kafa kamar wata namiji.”
Jidda ta fara dariya ni kuma haushi ya kume ni ganin yaran sun danne Yallaɓai suna kai masa naushin wasa gabaɗaya sun cika mana kunnuwana da iface ifacen su hauahi ya kama ni na yi ma Baby tsawa na ce ta baro wajen nan.
“Me ya sa? Ki ƙyale ta mana.” > Janaftybaby: In ji Yallaɓai ganin ta yi mini wani nakwa nakwa da fuska kamar za ta yi kuka.
“Haba Yallaɓai ita fa mace ce. Ka dai yi can da su Khalipa su da suke maza amma ita bai da ce ba.”
“A wajen ba shi ne bai dace ba,
amma ni a wajena Normal ne. Domin ta na mace shikenan ba za ta yi wasa da babanta ba? Ko su mata ba ƴaƴa ba ne?
Sai na yi shuru saboda Yallabai tun da ya tare maganar ba zam iya ja da shi ba, ita ko jin ban yi magana ba sai ta koma cikin murna shi kuma sai ya zo ya ja hannun Jidda yana faɗin” Come on Daughter mana.”
Sai ta maƙe kafaɗa tana faɗin” Abba karatu zan yi”
“Ba za ki yi wasa da Abba ba?
Sai ta noke kanta ba ta yi magana sai kawai ya ƙyaleta yana fadin” Kar ki zama raguwa irin mamanki mana Jidda.”
Hararan shi na yi kafin na yi magana ya tare ni da fadin” Ƙarya na yi ai ragganta ke hana ki yi, wannan fa koya ma yarana nake yi faɗan kare kai domin wata rana.”
Ni da Jidda muka kalli juna na tsintsire da dariya itama tana ta ya ni, ganin muna yi masa dariya ya sa ya ce” Au dariya ma kuke yi mini ko? Shi ke nan.”
“Yallaɓai baka da aikin yi ne yau?
“Kin san dai ba zaman banza na ke yi ba ko?
“To na ga ne yau kana ji da karfi.”
Yana ɗaga power ɗin hannun shi kafin ya ce” Sosai. Amma yau din rana ce ta musamman domin iyalaina da yarana.”
Ina dariya na ce” Ka ce yau Happy Family day ce Yallaɓai”
Banza ya yi dani ya koma ya zauna yana sauke ajiyar zuciya. Jidda ya ce ta ɗauko masa ruwa mai sanyi a fridge su Baby na kalla har suna kusa ɓaro mini da Tv ƙasa cikin ɗaga murya na ce” Duk barnan da aka yi mini baby ke ce za ki ɗauki asara domin bugun tsiya zan yi miki. Kuma ki sani ku gama ke za ki gyara mini falo na ma faɗa miki.”
“Ubanta dai kike so ki ce ya gyara ba ita ba.”
Ina dariya na kalli Yallaɓai kafin na ce” Ni dai ban ce ba”
“In ma kika ce ai kin san ba zai gagare ni ba malama.”
“Na sani.”
Na amsa ina masa dariya Jidda ta kawo masa ruwan gora da kofi bai ma zuba a kofin ba ya buɗe ya kafa kai kaɗan ya rage ina kallon shi na ce.
“Lalle Yallaɓai ka gajiyar da kanka.”
“Ni ai ba malalacin namiji ba ne. Lebura ne ni mai aikin ƙarfi.”
“Allah ya taimaki Md Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana.”
Na faɗa ina masa dariya har ina aika masa da jinjina. Miƙewa ya yi bayan Jidda ta koma kitchen mai da kofin da ruwan, Yunma ke zillo za ta wajen shi sai ya ƙarbeta yana faɗin” Ke kuma za ki shiga wasan ne?
Ina jin haka da sauri na ce” Yallaɓai don Allah kar ku wahalar mini da ƴa'”
Amma ki saurarena bai yi ba sai ma ya juya yana ce ma su Baby” Mun samu ƙarin patner.’
Suka fara ihi kafin in ce me ina zaune an dadumar mini yarinya na miƙe ina kiran sunan Yallaɓai amma ya yi biris da ni shilla sama yake yi yana caɓewa maimakon ta yi kuka sai dariya kwantar da ita ya yi a ƙasan cafet yaran suka rufu kanta suma mata wasa suna kai mata hannu itama jaira tana kamawa.
Ihu na yi musu ina faɗin” Wallahi Yallabai kada kai da yaranka kun halaka mini yarinya to.”
Ko sauarara na ma ba su yi ba da na ga za su ma yar da ni mahaukaciya sai na bar musu falon amma ina cike da fargaba kar su naushe mini yarinya. Kitchen na shiga na ɗibo abinci na koma ɗakina na ci na koshi, har lokacin ba su bar wasan ba har daga ɗaki ina jin iface ifacen su Yunma ina jiyo dariyanta na ɗauka za ta ga ji ta fara kuka sai ta ba ni kunya ko kukanta ban ji ba. Sai da aka kira mangariba Yallaɓai ya hakura da wasan nan ya zo ya yi wanka ya tara su Khalipa zuwa masallaci Yunma kuma an kawo mini ita ina ba ta nono na cire mata pampers na sake yi mata wanka da ruwan zafi sai barci ina ta masifa ni kaɗai.
“Ai dole ki yi barci kin sha wuya.”
Falo ma da na fita bayan na yi salla kaca kaca Baby ba ta gyara ba ai da muryan ɓacin rai na fara kiran sunanta sai ga shi ta fito da hijabi alamun salla ta idar.
“Ke ubanki kika bar ma falon ya gyara ko ni?
Sai ta fara sosa kai kafin ta ce” Umma na gaji ki bari da safe sai na gyara.”
“Ko mutuwa za ki yi yau sai kin gyara mini falo na aike ki ki yi mugun wasa har ki gaji? > Janaftybaby: Sai ta girgiza mini kai shammatanta na yi na ƙarisa gabanta tana shirin guduwa na damki kunnenta ɗaya na matse ina faɗin” ba ki da hankali ashe ban sani ba Maimuna?
Sai ta fara kukan shagwaɓa tana faɗin” Umma zafi kunnena.”
“Ke namiji ce da za ki je kina wasan maza?
“Umma Abba ne ya ce na shiga.”
“Abban ne ya ce ki shiga ko? Ya ce ki shiga dole ne? Ba ga ƴar uwan ki nan ba kin ga ita ta shiga ne?
“A’a”
Ta faɗa cikin kuka har ta fara hawaye, ƙara jan kunnen na yi ina faɗin” Wallahi in na sake ganin kin shiga irin wannan wasan sai na yi fata fata da ke a cikin gidan nan”
“Kin ji ko ba ki ji ba?
Na faɗa cikin tsawa da sauri ta ce” Allah ba zan ƙara shiga ba Umma.”
Dundu mai lafiya na yi mata a baya sannan na sake ta ina faɗin” Ki ma ƙara ki gani ɗin. Maza ki gyara mini falo wawiya kawai kin girma amma kina cin ƙasa.”
Sai ta yi gefe tana sosa kunnenta lokaci ɗaya tana faman hawaye daidai shigowar su Yallaɓai ganin tana kuka ya sa ya kalleni yana faɗin” Me ta yi miki kika da ke ta?
Na yi masa banza na wuce, ina jin sa yana faɗin” Sadiya ki daina duka mini yarinya fa. Na faɗa miki ba na so amma kin ƙi jin magana ta.”
Na yi shigewata Bedroom ina masifa ni kaɗai yarinya na mace amma tana yin abubuwa irin na maza shi kuma Yallaɓai ba zai fahimci illa abun ba sai nan gaba ni ko ina uwa ba zan zauna in yi shuru ba.
Daga yaran har Yallaɓan ban ƙara ganin su ba sai bayan sallar isha’i da ya zo ya shirya ya ce mini za su ta fi saboda su Khalipa na fito ina da jakar lilipop na ɗauko na ba su shi da Anwar na Yumna ne da Suwaiba ta kawo mata tun da ta shan zaƙi, abinci ma na fara ba ta mai ruwa ruwa kamar tea kwai da sauran su ruwa daman tun haihuwanta na ce zan yi exclusive Yallaɓai ya ce ya bi Exclusive da gudu ba takalmi in har na yi ma yarinyar sa mugunta na hana ta ruwa bai yafe mini ba, shi ya sa ba mu yi ba sannan ga shi ta sha madaran yara sosai shi ya sa kullum ƙara ƙiba kawai Yumna ke yi tana ba ma masu ɗaukanta wahala ni kaina sai ina nishi in zan ɗaga ta.
Saboda Baby ba ta da hankali ta yi ɗamara za ta bi su, kallo ɗata kawai na yi mata ta shiga taitayin ta Yallaɓai na cewa ta ɗauko kayan makarantar ta, ta je can ta kwana cikin masifa na ce” Ba za ta je ba.
“Saboda mene?
“To me za ta je ta yi? Su Khalipa ne kuma ba ga su nan sati uku tare damu yau ne za su koma ba?
“To ina ruwanki tana son ta je. Ba ta gaji da ganin su ba.”
“Sai dai ko ta mutu amma ba yau ba. Ba za ta je ba.”
Yallaɓai zai yi magana na tare shi da faɗin” Wallahi ba za ta je ba, ka ji ma na rantse.”
Yallabai ya kasa mgana ya kira sunana na yi kamar ban ji ba, na shafa kan Anwar ina faɗin su gaida mamannsu.
“Bye Umma.”
“Bye Khalipa.”
Na faɗa ina ɗaga musu hannu, na yi shigewata ɗaki ina jin idanuwan Yallaɓai a kaina na ki yarda ma mu haɗa ido. Ai suna fita na sake fita falo suna ɗakin su Jidda na ninke ƙananun kayanta da ta wanke Baby na kan gado tana kuka saboda na hana ta zuwa. Ban yi wata ba ta ɗaka mata duka a baya sai ta banƙare tana ganina ta yi tsalle ta yi ƙarshen gado tana matse kukanta.
“Kuka kike yi mini saboda wannan mganar?
Sai ta fara girgiza kai cikin kuka kafin ta yi magana na tare ta da cewa” To kukan me kika hau gado kina yi mana a cikin gida?
“Ba komai.”
Ta faɗa tana hadiye kukan ta.
Kallonta na yi kafin na wata dariya ina nuna ta da yatsa kafin na ce” Kin ga Jidda na yin haka? Ke ce mara jin magana ko? ke Yarinya ce?
Nan ma ta girgiza mini kai zare mata ido na yi kafin na ce’ Wallahi ya zama na ƙarshe in sake yi magana a gaban babanki ki ce za ki yi mini gaddama kika ga yadda zan yi ƙulin kubura dake a cikin gidan nan.”
“Ki yi hakuri Umma”
Ta faɗa cikin kuka sai ta ba ni tausayi amma ban nuna mata ba.
“Ki yi haƙuri Umma ba za ta ƙara ba.”
Jidda ta faɗa cikin sanyin ta sai na yi ƙyafci na fita daga ɗakin fuu har ina bango musu ƙofar na koma ɗaki ina masifa ni kaɗai daga baya sai na koma ina dariyan kaina. Na rasa haushin wa na ke ji? Yallaɓai ko yayan shi? Tun daga cikin Yumna na samu wannan ɗabi’ar abu kaɗan yake harzuƙa ni in ta faɗa kan abin da bai kai ya kawo ba. > Janaftybaby: **
Jidda ta gama jarabawarta gabaɗaya sannan Walimar saukar su kuma za a yi a farkon watan August ne, sai kawai na ce za mu haɗe shi da waliman gradution ɗinta da birthday ɗin ta na cika shekara sha tara a duniya duk da ta ɗan gota amma zan haɗa mata kayattaciyar Walima. Yallaɓai ne wani lokacin ko na ce za mu yi sai ya ce a’a na dai yi musu tun suna yara amma suna kawo girma sai ya riƙa hanawa iya fa mu kaɗai a gida amma sai Yallaɓai ya ce wai birthday haramun ne.
Wannan karon dai na ci karfin sa ya amince. Tun da har da Waliman saukar su sannan Amarya ta saka baki Gimbiya ba. Shi ya sa ya bari sannan ya saki kuɗi aka yi ta shirye-Shirye kuma dai daman Jidda is his fav Daugther. Ba wani gayya muka yi ba iya yan makarantan su na boko sai ƙawayenta na Tahfez su goma ne mata za su yi sauka sai maza huɗu. Sun yi ankon Hijabai masu ruwan ƙasa da dogayen baƙaƙen riguna sannan sun haɗa kudi kowa 20k amma Yallaɓai 50k ya ba ma makarantar suna ta godiya.
Ni dai daga gida na yi mata memo da yar jaka ƙarama, ita kuma Gimbiya ta yi mata kayan su Snacks, Mimisco ta yi mata sabbin kaya kala huɗu har da jallabiyoyi da takalma sannan ta yi mata jaka na takarda babba a ka saka hoton ta. Ai na ci dariya domin ni da na ce zan yi na hoto Yallaɓai ya tuma ya ce bai amince ba sai ga shi Mimisco ta yi da ya gani sai ya kasa magana. Anty Maimuna ta siya maltina katan goma da ruwan gora. Anty Bahijja ta yo abinci mai rai da lafiya, Suwaiba ta kawo mata sabon alqur’ani da casbaha. Naja ta kawo mata darduma na Makka da hijabi, sauka ne Jidda za ta yi da walimar Graduation amma ta samu kyatttuka sai da na yi mamaki kaf dangin Babanta sun nuna mata bajinta. Hatta Babanta Usman ya aiko mata da 50k. Ya Auwal Laptop sabuwa ya aiko mata da shi Ya Hamza kuma ya gwangwaje da kayan su chaculte kala kala sama da guda biyar. Musbahu kuma ya gwangwaje ta da sabuwar waya. Jidda sai da ta yi kuka da ta ga irin kayan da a ka haɗa mata Baby na ta tura bakin ba a kawo mata ba ta ce sai ta yi ƙoƙari itama ta sauke Qur’ani sai a yi mata abin da ma ya fi haka.
Kaf yan gidanmu suma sun yi bajinta matan da Mazan. Alhajimmu ya saka aka yanka mata tinkiya cikin dabobbinsa na ƙauye Baba Aminu ya taho da ita tare da kaji da zabbi shi ya sa Yallaɓai bai siya komai ba yana gefe iyayenta sun gama mata komai. Ranar saukar lahadi ce tun tara muna haraban tahfezz ɗin su Jidda. Kaf ɗin su Ya Aina sun taho Rahila ce kaɗai ba ta zo ba laulayi, Kawu Abba shi da Marwa da tsohon ciki Gimbiya tare da su Khalipa da Naja, su Maman farko da Hajiya Iya. Su Munnira da Hauwa hatta Mimisco ta zo ita da Anty Bahijja da Anty Maimuna. Kaf din su Musbahu da Adnan Muttaƙa da su Suwaiba suna wajen taro sosai Jidda ta gani sai hamdala. Yallabai na da ganawa da wasu mutanen sai daga baya yazo lokacin ma Jidda aka kira tana karatu.
Sai da na yi ƙwalla da Jidda ke karatu, y’an uwanta na ta ɗaukan ta Video cikin burgewa. Bayan sun gama karatu aka kaddamar da su sha huɗu masu sauka aka ba su allon sauka. Mun yi hotuna tun da Adnan ya kira mai hoto, ta samu kyattuka, wajen malamai Kawu a envilop ya saka mata sabbin yan 1k A wajen a matsayin shi na Uba ta rumgume shi tana masa godiya. Duk mun zo da abinci da lemuka da ruwa da abun rabo. Tantin da muka zauna ba fariya ba sai muka zama abun kallo Jidda haka ta yi ta rabon jaka da Memo da abinci ruwa da maltina haka suke rabo. Baby kaf yan ajinsu ta gayyato suka ci suka sha, daga makaranta muka dawo gida muka ya da zango muka cigaba da walimar a gida. Mazan daman daga makarantan muka rabu da su.
Mimisco har gida ta biyo ni ta ci abinci sannan ta tafi. Su Anty Bahijja sai la’asar suka tafi har Gimbiya ranar sai dare. Na aika da abincin walimar da naman da kayan Snacks da abin rabo na aika da shi Gwammaja da Ɗorayi suma su shaida. Sauran kuma duk wanda zai fita jakan sa cike da kayan walima. Rahila ma na ba da saƙo akai mata Halima ce ba ta zo ba a cewar Gimbiya ba ta da lafiya ne, amma ni ban damu ba ta kanta na ke yi ba. > Janaftybaby: Ranar gidana cike da jama’a har dare ranar ba gidana Yallaɓai yake yi ba sai washegari ya dawo gidan, sannan ya ga kayattukan da Jidda ta samu sai da ya shafa kanta kafin ya ce.
“Good girl. Am so proud of you Daughter.”
Ga waya ga laptop, shi Yallaɓai Tab ya siya mata sabuwa, tsohuwar ya ce ta bar ma Baby, da take ta tura baki ita ba a siya mata komai ba ya ce ta ƙara ƙoƙari itama za a siya mata. Hotuna sun yi kyau na yi ta carbi a status mutane nata saka albarka bayan kwana biyu na saka ta , ta shirya ta je Gwammaja ta kai ma Nene allon saukar ta, daga can ta wuce Ɗorayi ta kai ma su Alhajinmu suka gani suka saka albarka.
Kuɗin da Jidda ta samu na tattara su na siya mata ɗan kunnen gold na ba ta ta maƙala a kunnen ta. Sai da na yi shawara da Yallaɓai shi kuma ya ce kudi na Jidda ne in ta amince sai na siya mata. Da na tambayeta tace mini tana so shi ne muka je tare kasuwa na siya mata. Amma na cire 30k a ciki na ƙara jarin hijabai da na ce ma na ara sai ta ce ba aro ba na baki Umma, na yi ta saka mata albarka. Adanan ya kai ta ta yi register ɗin layi tun da ta yi waya. Ta sha dokoki wajen Yallaɓai ban da shige shige WhatsApp kawai ta buɗe lambobi daga na mu sai na kawunta sai na yan ajinsu sai na y’anuwanta su kenan a cikin wayar. Ganin za ta fara zaman gidan kafin cuku cukun makaranta sai ta ce mini tana son ta koyi kayan su Snack haka sannan tana son koyon kwalliya na aminta da shawaranta sai na yi ma Yallaɓai magana shima sai ya yi na’am da mganar ya ce ta nemi in da ake yi sai ya ba ta kudi ta shiga..
Gimbiya na yi ma mgana saboda na ga ita duk ta iya su, ni kuma ba su dame ni ba, ita ta yi ma wata da ta sani mai yin snack sosai ta buɗe online class aka saka Jidda sannan ta na yin na gida sau biyu a sati alhamis da jummaa wata uku 20k Yallaɓai ya biya mata ta fara zuwa. Sannan na kwalliya ni kuma da na ke yi followimg ɗin su a I.G na yi ma wata Zahrajj magana da bayanin kuma ita a sharaɗa take amma tana da shago a nan zoo road wajen kamfanin Yallaɓai. Da na yi ma Jidda rigister ita sau uku ne a sati jumma da asabar da lahadi da safe. Shi kuma na Snack daman da yamma ne.
Jidda tana da naciya da dakiya in dai ta sa kanta za ta yi abu. Ko sati biyu ba ta yi da fara zuwa ba ta fara iyawa. In ta dawo gida sai ta gwada Yallaɓai kuma ya ɗaure mata kugu ya sa aka kawo mata fulawa da siga sauran kayan kuma ya ba ta kuɗi ta siya kwalliya kuma Tariq ya aiko mata da babban kit na ƙwalliya, Baby ta yi jin haushi ta ce an fi son Jidda a kanta in ta yi mata dariya. Maganar gaskiya Jidda na da farinjinin jama’a sosai saboda yanayinta na sanyi da rashin hayaniya.
A tsukin Marwa ta haihu an samu mace ta ci sunan Innayi ana kiran ta Afiya muka tafi Rano suna har Gimbiya ta je, itama cikinta har ya turo gaba. Kwana uku muka yi a gidan Marwa ni da Munnira da Hauwa da su Ma’u da Rahila sai Ya Balki. Su Anty Bahijja sun zo suna amma ba su ko kwana ba, dangin Baban Marwa ma sun zo amma washe-gari suka koma mu kaɗai aka bari muka yi soye muka natsa. Ana gobe za mu koma gida ne muka yawata garin mun je gidan su Kawu gidan su Nene kenan daga nan muka je gidan su Hauwa. Na karshe shi ne gidan su Gimbiya. Hajiyar Tafida na nan da ƙannen Gimbiya da suka zo gida.
Ƙiri-ƙiri suka yi mana wulaƙanci ita dai Hajiyar ta karbe mu faram faram amma ƙannen Gimbiya saboda ni a wulakance suka amsa gaisuwar mu. Shashen Mamansu Sameena me kawai aka karrama mu. Bayan mun fito daga gidan Munnira na ta kumduma zagi ni da Hauwa muna yi mata dariya. Na ɗan ji haushi amma ban damu ba daga baya na watsar da abin. Washegari muka koma gida Kano kuma ko a labari ban taba faɗa ma Yallaɓai ba.
*
Yallaɓai tuni ya zagaye filin shi an saka get har an fara gini gadan-gadan domin yanzu Yallaɓai kuɗi yake samu mahaukata. Kwangiloli sama da biyar yake yi a lokaci ɗaya. > Janaftybaby: Ba zato ba tsammani ban ma saka rai ba Yallaɓai ya siya mini mota a watan November ranar goma ga wata ranar da Yunma ta cika shekara ɗaya. Har na shirya mata party a gida Jidda ta yi mata cake tun da yanzu ta ƙware, sai ga Yallabai da maƙullin mota ya siya mini vibe fara, amma ba sabuwa ba ce sai dai ba ta sha miya ba. Na daka tsalle na ruƙumƙume Yallaɓai ina faman ihu da murna ni da yara shima farinciki yake yi ganin yadda gabaɗaya na rikice saboda murna.
“Mota ka siya mini Yallaɓai? Innalillahi.”
Na ke faɗa na ma kasa mgana saboda murna da farimciki.
“Mu je ki ganta tana haraba. Ita na tuƙo, tawa na ce Musbahu ya taho mini da ita daga baya.”
Ai sai gani ni da yara muna rige-rigen fita har da Yumna dake tafiya itama har ana neman ture ta Yallaɓai ya sunkuto ta ya biyo bayana.
Da na ga motata sai na dafa ta kawai na fashe da kuka.
“Yallaɓai wannan mota ta ce?
Shi da yara suna ta mini dariya ganin ina kuka sai ya ƙariso ya rumgumeni shi da Yumna yana bubbuga bayana lokaci ɗaya yana faɗin” Kin yi mota saura ki je ki sauke farali My Sady.”
“Yallaɓai har saudiya za ka biya mini?
“In sha Allahu Sadiya ta.”
Ai sai na ƙara fashewa da kuka na rumgume Yallaɓai na ƙamƙame shi ina ɗaga murya cikin kuka amma na kasa magana.
“Shii. Bar kuka yau ranar farimciki ne ok?
Ya faɗa yana ɗago fuskata ya fara share mini hawaye. Yumna na ta ya shi.
“Kin ga har Yumna ma ba ta son ganin Umman ta na kuka.”
“Yallaɓai kukan farinciki ne”
Na faɗa wasu hawaye, na gangaro mini na farinciki.
“To za ki karar da hawayen na ki ne a yau? Ki adana su saboda ba ki ga komai ba. Tun da Ubangiji ya wadata ni ni kuma zan yi ta saka ki farinciki har ƙarshen rayuwar mu Sadiya ta.”
A gaban yara na yi ɗage na sumbaci bakin Yallaɓai sannan na sake shi ina kallon shi kafin na ce.
“Na gode Yallaɓai. Ubangiji ya yi ma dukiyarka albarka. Na gode.”
Na faɗa ina ƙara gocewa da kuka Yunma ma sai ta fara. Baby da Jidda na can suna santin mota, ko ta kan mu ba su bi ba,
“Bar kuka nan kin ga Yunma ta fara.”
Ya faɗa yana bubbuga bayana. Amma na kasa tsaida hawayena. Sai da ya share mini sannan ya saka ni na shiga motar na yi bismilla da addu’a..
“Allah ya tsare Hanya Madam me”
Yallabai ya faɗa yana lekowa ta window
Yunma ta ya fito ni, na karɓeta ina fadin” Amin Sadaukina “
Babby har ta kame a gaba Jidda dai baya ta buɗe ta shiga tana faɗin.
“Umma tubuli Allah ya sa ki kashe ta lafiya.”
“Amin Amin Jidda. Yallaɓai saura Jidda ka siya mata ta ta motar”
“Da a ce nan garin za ta yi makaranta da na siya mata amma tun da zariya ne sai dai in ta gama in sha Allahu.”
“Allah ya amimce Yallaɓai na.”
Jidda ta kalli Babanta kafin ta ce” Mun gode Yallabai Allah ya karo buɗi.”
Baby ta ƙyalƙyace da dariya kafin ta ce” Abba Yallaɓai “
Ni da shi muka yi dariya gabaɗaya.
Daran nan da kyar na iya barci gani na ke yi kamar mafarki waahegari ni na kai Baby makaranta a mota ta, daga can ɗorayi na dira Yallaɓai na bari a gida shi da Jidda daman na ce sai in da mai ya ƙare.
Sai da su Gwaggo su ka ganni da mota na ce su fita ita da Alhajinmu suna ta murna da saka albarka. Daga nan sai gidan Ya Abubakar shima na kai masa ya gani. Na je har gidan Ya Aina na nuna mata sannan na koma gida na ɗauki hoton motar na yi status da ita sannan na yi caption a kasa da cewa.
“Alhamdulillah. Yallaɓaina ya gwangwaje ni da mota jiya. Matar Yallaɓai ta yi mota jama’a ku ta ya ni murna.”
Nan da nan aka yi mini caa Sadiya kin yi mota! Congratulaton Mimiaco ta ce kin chanchanta ta Yallabai. Ita ce kaɗai ta yi mini murna sai su suwaiba da Nasara da Jamila. Gimbiya ta gani amma ko Allah ya tsare ba ta ce ba, Ya Hamza ya turo mini rawa kafin ya ce” Lalle Yallaɓai ya iya gwangwaja danƙari. Allah ya tsare “
Adanan kuwa faɗi yake yi” Ya Sadiya kin rigani yin mota? Na ce to ka zauna ni ai na yi gaba.
Su Maijidda da Samira suna ta mini fatan alheri. > Janaftybaby: Munnira da Hauwa gida suka zo yi mini murna, da za su tafi na tuka su na kai kowacce gidan ta. Ni fa tun da na yi mota na dai na zaman gidan ni ce can ni ce nan, har Jidda ni ke kai ta wajen koyon kwalliyarta tun da sun gama na snacks, sati mai zuwa ma zata je zariya yin POS UME. Ni ce har Gwammaja na kai ma su Nene mota suka saka albarka. Lokacin Jawahir da Umma Salma sun zo ganin gida suma sun saka albarka suka ce ai na caancanci mota na kuma chanchanci na shiga na fita. Yallaɓai ai nawa ne an sha gwagwamarya.
Wajen sati biyu ban zauna a gida ba, Yallaɓai ya gaji ya ce na zauna na huta har abada fa motar nan tawa ce sannan na hakura gani nake yi kamar zai ce na kawo key ɗin an fasa za a mayar ma da masu shi. Faridan Tariq ta ce itama a satin Tariq ya siya mata na ce mun yi amarya a tare. Anty Zabba da muka yi waya ta ce ta yi mini murna yayan shi da ya ji sai ya ce ya kyauta muka yi ɗan tsegumi har tana ce mini yanzu sai Gimbiya ta daina yi mini gani gani anan ne ma na ke faɗa mata ita da su Anty Bahijja ba su yi mini murna ba.
Ta ce na raba su hassada ne da bakin ciki na ce sai dai ya koma musu kuwa. Ba sa gabana ta ce ya fi haka.
Ni ina gida ban san wainar da ake toyawa ba. A satin da Jidda ta tafi Zariya gidan Ya Hamza ta sauka bayan ta gama jarabawar ba ta dawo Ya Hamza ya ce sai sakamako ya fito za ta dawo. A Safiyar litin Ni kaɗai a gida Baby na makaranta daga ni sai Yumna da ta koyi shegen ɓarna tana tafiya turba turɓa da ƙyar, Yallaɓai ba gidana ya kwana ba bai kuma shigo da safe ba sai na yi tunanin fitan gaggawa ce ta kama shi, da man wani lokacin in bai samu dama ba sai dai mu yi gaisuwar ta waya.
Wajen sha ɗaya na safe Sameena ta kira waya muka gaisa tana yi mini murna. Har ina mata tsiyan ta makara ta ce mini wallahi ba ta ji labari ba sai satin nan da ta je gida ta ji ana ta rigima kan motar. Ashe har yaji Gimbiya ta yi akan Yallaɓai ya siya mini mota. Saboda ta yi masa maganar siyayyan kayan haihuwa ya ce ta jira sai ya siya mini mota sannan zai dawo kanta shi ne ta suka yi tsiya fata fata har ta yi yaji. Kwananta hudu a gida amma ta dawo shekaranjiya yara ma can Gwamnaja aka kai su wajen Nene.
Na yi ta mamaki domin Yallaɓai bai ba ni wata alama ba, tun da ni dai bai zo gidana ya kwana ba ashe shi kaɗai ya riƙa kwana don kar na fahimci wani abu. Sameena ta ce tana gidan shekaranjiya asabar Yallabai ya je can Rano tare da Kawu aka zauna ana ma yar da magana Gimbiya tana ta kuka tana faɗin ba ya yi mata adalci komai ni komai kamar na shanye sa shi ne ya ce e na shanye sa ne, itama za ta iya shanye sai bai hana ta ba mota ne ya siya mini haihuwa kuma tun da ba gobe ba ne ta jira ta gani in bai ba ta kudin siyayyan ba sai ta yi magana. Sai da Tafidan Rano ya shiga maganar sannan ta biyo sa suka dawo gida tare.
Na jinjina lamarin Gimbiya a raina sosai. Hasashena ya kasa hasaso mini tsanar da matar nan ta yi mini ta zo ta same ni da mijina amma tana neman ta hana ni zaman lafiya! Kwana na yi ina auna abin a kasan raina wai ta yi ya ji saboda an siya mini mota. A bakin Sameena na ke ji tana cewa itama ai ta yi ta yi ya sauya mata mota ya ƙi. Amma ni ya siya mini shi kuma ya ce ita tana da shi, ni kuma ban da shi shi ya sa ya fara siya mini tun da ni ce uwargida. Ta jira in ya samu kuɗi sai ya sauya mana gabaɗaya ta ce Hajiyarsu na ta yi mata faɗan ita ba ta ga ƙoƙarin da ya ke yi ba miye don ya siya ma matarsa mota shekara nawa suna tare bai siya mata ba sai yanzu? Ita na za ta gode ma Allah da ni’imar da ya yi mata sai ta bari sheɗan na yi mata susa a kunne. Ta bakin Sameena ta ce bakin ciki ƙiri kiri Gimbiya ta nuna akan an siya mini mota. Ni ko da gayya na ce ta ko fara gani in sha Allahu sai dai ta mutu in ba za ta iya ba ta fi ta bar ni gidana da mijina daman a ciki ta zo ta ganni na matsa mata amma shi ne za ta yi mini butulci. > Janaftybaby: Kamar in yi ma Yallaɓai magana sai na fasa ganin shi bai faɗa mini amma na riƙe ta a raina, a satin da na ji maganar muka haɗu a Gwamnaja Maman farko ce ta zame daga bene ta samu gocewa shi ne na je dubata kuma da motar na je a ɗakin Nene a gaban Anty Bahijja da ita kanta Nenen na kalli Gimbiya na ce mata.
“Gimbiya Yallaɓai ya siya mini mota kowa ya yi mini murna ban da ke ko ba ki sani ba ne?
Da gayya na faɗi haka, ai sai ta ji kunya ta fara kame kamen wai kwana biyun nan ba ta ji daɗi ba ne ta so ma ta zo har gida ne ta yi mini murna. Kallonta kawai na ke yi ni sai na raina wayan ta. Matar da ke da shago guda amma ɗan abin da Yallaɓai yake yi mini ya hana ta sukuni.
“Allah Ya sanya alheri.”
Na amsa da Amin ina kaɗa key ɗin hannuna.
“Kema Anty Bahijja ba ki yi mini murna ba.”
Duk na kunyata su, ita da yake akwai isa kai tsaye ta ce” Kin kawo mini ita har gida ne kika ga ban yi miki murna ba?
Sai na nuna mata na fita iya bariki kai tsaye na ce” Ban kai miki gida ba amma yau ga ta can a haraba na zo da ita. In za ki fita ki duba ta, ki saka albarka Anty Bahijja.”
Sai ta kasa magana Nene na wajen ta saka baki ta ce ba su kyauta. Abin alheri ne ya same ni yana da kyau su yi mini murna sai ga shi jiki an sanyaye da zan tafi suka fita ganin motar suna saka albarka na ciki na ciki. Halima ina haraba ta shigo yadda ba ta gaisheni ba, nima ban nuna na ganta ba, na shige mota ta ni da Yumna na yi tafiyata suka bini da kallo har na fice a raina na ce ku yi ku gama. Babu yadda kuka iya da ni nan gani nan bari ɗumammen Manya.
*Janafty*