Turken Gida – Chapter Forty-seven
by Janafty*MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE*
Shuru na yi da bakina kamar yadda Yallaɓai ya yi shuru bai faɗa mini ko ya nuna mini sun samu matsala da matarsa saboda ya siya mini mota. Nima sai na yi kamar ban ji wata magana ba na cigaba da sabgogin gabana. Addu’a kawai nake yi ma Jidda akan Allah ya ba ta sa’a ta samu gurɓin karatu a jami’ar bayero saboda ta ƙwallafa rai sosai akan makarantar.
Cikin ikon Allah satin ta ɗaya a Zaria Khaleesat ta kira ni tana faɗa mini Jidda ta ci Jarabawar da ta yi, na yi ta murna da farinciki Yallaɓai na dawowa na faɗa masa sai ya ce mini Jiddan ta kira shi ta faɗa masa, har yana cika baki da cewa shi da man ya san abin da ya haifa he is sure za ta tsallake, baki na saki ina kallon Yallaɓai yana yaɓon ƴar sa, har yana kallona yana ce mini ƙwakwalwarsa ta biyo shi ya sa take da hazaƙa.
“Me kake nufi Yallaɓai?
“Ni ai ban ce komai ba na dai ce Jidda ƙoƙarina ta ɗauko. Shi ya sa duk abin da ta yi ma himma take samun nasara da taimakon Ubangiji.”
Ya faɗa yana ƴ’ar dariya.
“Allah Ya ba mu sa’a.”
Na faɗa kawai saboda ba na so maganar ta yi tsayi amma Yallaɓai bai so haka ba kawai sai ya kalleni yana sake faɗin” Amma kin ga Baby ina jin kanki ta ɗauko sam ba ta kai Jidda ƙoƙari”
“Au ni daƙikiya ce kake so ka ce ko Yallaɓai?
Na faɗa ina masa wani kallo sai ya fara dariya yana faɗin” Ni yaushe na ce miki daƙiƙiya?
Ban bari ya cigaba da magana ba na yi wucewata ina faɗin” Sai kuma ka yi. Na gode da cin mutumci Yallaɓai. Ka ji na ce Na gode.”
Jin yadda na yi maganar ya san na yi fushi sai ya biyo ni ciki yana rage mini murya, da ƙyar na haƙura sai da ya yi mini rantsuwa da cewa da wasa yake yi sannan na aminta da shi har na saki fuska muka cigaba da hira. Daman da daddare ne ya zo yi mana sallama tun da gidan Gimbiya zai kwana yau da gobe.
Ranar jumma’a Jidda ta dawo, gidan Khaleesat na saka aka aika mini da saƙon hijabai ta taho mini da shi, ta dawo a jigace ta sha wuya motarsu ta yi ta lalacewa a hanya sai mangariba ta iso. Yallaɓai ya kirani ya fi sau biyar yana yi mini masifan ya zan haɗa yarinya da kaya na san ba ta taɓa tafiya waje mai nisa ba, ko da za ta tafin ma da kyar ya bari da ace baya da wani abin da zai yi shi zai kaita. Amma sai da ya kaita tasha yana jadadda mata ta kula da kanta, kafin ta kai ko ban san sau nawa ya kira ta a waya ba, to yau ma za ta dawo ya yi ta kiranta daga baya sai ya daina samun ta a waya shi ne zai sauke faɗan shi a kaina, tun ballatana da Jiddan ba ta taso da wuri ba saboda jiran sakona. Ai ni sai shuru da ba da haƙuri tun da dai ba ni da gaskiya. Sai da ta shigo gidan nan na samu sauke numfashin salama na kira Yallaɓai na faɗa masa duk da haka bai fasa faɗin abin da ke ran shi ba.
“Sai yanzu ta iso? Sadiya ba ki kyauta mini ba, kawai ki haɗa yarinya da kaya ki wahalar da ita fisabillahi kin kyauta kenan?
“Na ce ka yi haƙuri Yallaɓai ganin za ta dawo ne ya sa na ce ta karɓa ta taho mini da shi.”
“Ni dai ba na so. Kar ƙi kara yin haka. Ba ta fa taɓa tafiya ta yi ita kaɗai ba”
Mamakinsa ya kama ni, Jidda kamar wata ƙaramar yarinya ni dai shuru na yi har ya gama bambamin sa ya kashe wayar ban ƙara ce masa komai ba, tun da tun ɗazu nake ba shi haƙuri amma kamar ya haƙura sai kuma da ya ji ba ta dawo ba sai ya fara mini masifan wai ni na ja. Ni fa daman na sani Jidda a wajen Yallaɓai ta musamman ce, in dai lamarin da ya shafe ta ba ya zaune ba ya tsaye, ya yi ta wani kafa kafa da ita kamar wata ƙaramar yarinya. Ai ban ma ga kafa kafa ba sai da ya dawo gidan haka ya zaunar da ita yana tambayanta ta sha wahala? Ta gaji ne ba dai ta samu wata matsala ba ko? > Janaftybaby: Tana dariya tana faɗa masa ita lafiyanta ƙalau, ba ta samu wata matsala ba kawai lalacewar motar ne, har yana tattaɓa wuyanta, ya ji ko tana da zazzaɓi, ni dai ina gefe ina kallon ikon Allah na kasa mgana. Na ɗauka Yallaɓai ya gama faɗan shi amma ina yana ganin hilimin saƙon da Jidda ta taho da shi faɗan shi ya dawo farko wai da gangan na yi kamar Jidda ne zan saka ta ɗauko uban kaya haka? Wai har Yallaɓai na faɗin an ya ina da tausayi kuwa?
Baki na saki kafin na rufe ina faɗin” To wai duk wannan faɗan na mene kuma Yallaɓai? Ina ce ba ga Jiddan ta dawo ba? Kuma ita Jiddan yarinya ce kar ka manta she is 19yrs kuma jami’a za ta shiga so Jidda ba yarinya ba ce, ka ma daina jijiyan wuya ko Baby ta wuce yarinya ballantana Jidda.”
Na faɗa cikin jin haushin sa, to ya dame ni magana ta ƙi ta ƙare kamar cin kwan makauniya, maimakon ya yi shuru sai ya ma ya harzuƙa ya fara faɗin duk haƙurin da na ba shi na ƙarya ne tun da ban yi nadaman abin da na yi ba ina cewa wai Jidda ba yarinya ba ce.
“Za ki haɗa da kanki ne? Kin ga ko har yanzu yarinya ce.”
“Jaririya ce Nono take sha Yallaɓai”
Sai ya yi shuru bai ƙara mgana ba ni kuma a lokacin na hau sama na miƙe ina faɗin” Kayan fa ba akanta ta ɗauko su ba. Yadda kake wanman faɗan ko dakon su ta yi daga Zaria zuwa nan sai haka”
Ina gama faɗin haka na ɗauki Yunma muka bar musu falon haba ba ta yuyuwa kamar wata Jiddan gwal ne, ai ganin yadda na yi cuɗuncuɗun da fuska na haɗe rai ya san halina shi ya sa sai ya bar maganar amma da ban yi masa haka ba abin mamaki ba har ya gama kwana biyun shi kullum sai ya ta da maganar ina dalili.
Waɗanan Hijabai ai ban siyar da su cikin daɗin rai ba domin na tuna da bambamin faɗan da Yallaɓai ya yi ta mini raina sai ya sosu, in ta yi ƙyafci ni kaɗai saboda takaici. Zan ga yadda zai yi in ta samu admission za ta tafi makaranta sai na ga ƙarewar so da ƙauna. Kuma ba daɗewa suka ba ta Admission, da kuma Course ɗin da ta zaba wato Phamarcy, nan da Yallaɓai ya fara yi mata shirin makaranta privision kamar za a buɗe shago komai Jidda ta ce tana so ya siya mata har da ma wanda ba ta ce ba, tare suka je kasuwan shi da Jiddan da Baby ni ina gida ko gayyata ta bai yi ba kuma na so ya ba ni ragama ni na samu riba a ciki amma Yallaɓai ya yi fuska ni kuma ban yi masa mgana ba saboda kar ya ranfo ni, na zura masa ido kawai ina ganin ikon Allah wajen uban da yar gabaɗaya.
Da yake sai January sabuwar shekara za ta yi rigistration ta koma sannan su fara karatu. Shi ya sa shekaran na kamawa na 2022 ana buɗe portal ɗin biyan kuɗin makaranta ya ɗauke ta suka tafi. Ranar cikin ikon Allah zai je Kaduna sai ya biya ya sauke ta a cikin makaranta da in ta gama abin da za ta yi ta wuce gidan Uncle Hamza. To kwanan ta biyu tun da har hostel sai da ta tsaya ta yi clicking ta samu Queen Amina Room of 12 ta ce su huɗu ne a ɗakin ta samu loka da gadon ƙasa, a gida daman Babanta ya siya mata katifa mai kyau, ranar da Yallaɓai zai dawo ya biya ya ɗauko ta suka dawo tare bakin shi ya huta nima kunnuwana suka huta.
Washegari kuma ya saka Adnan ya rakata firstbank ta buɗe, banki saboda makaranta.
Jidda duk ta zagaya gidajen yan’uwan Babanta ta yi musu sallama. Mimisco ta ce na ba ta hijabai guda biyar za ta biya kuɗin. Su Anty Bahijja kuɗi duk suka ba ta, har Gwammaja ta je da Ɗorayi ta yi musu sallama su Ya Aina a waya na faɗa musu suka yi fatan Allah ya sa a fara cikin nasara. Ta je har gidan Gimbiya ta yi mata sallama sai ta ba ta takalmi cover shoe guda biyu sai abaya guda ɗaya da kayan kwalliya. Kawu kuma ya aiko mata da dankalin turawa da kwai da yawa, dankalin ma kaɗan na ɗibar mata kwan kuma Yallaɓai ya ce sai ta je can ta siya saboda zai jigata a hanya kafin su kai. Ranar lahadi 28january Jidda za ta tafi makaranta za ta bar mu da kewa.
Duk da Yallaɓai bai ce da ni za a je ba amma na yi shiri ni da Baby da Yumna na ce zamu raka Jidda har makaranta itama na ta murna ashe Yallabai ya shirya da wacce zai je, sai ana gobe tafiya ranar asabar kenan ya ga ina ta shiri, na yi mata dambun nama ita kuma ta yi ma kanta su Snacks cokes, donut, cincin cake kaɗan ta yi saboda lalacewa > Janaftybaby: sai miya da ta yi mai naman rago, sai ƙuli da na siya mata mai yawa yaji kuma Munnira ta dako mata mai daɗi ya ji tafarnuwa, Hauwa ta aiko mata da garin rogo mai kyau, da kansu suka zo suka kawo mata tare da yi mata yan nasihohin ta yi abin da ya kaita ba ruwanta da rayuwar makaranta ta tuna da tarbiyan da iyayenta suka ba ta.
Sai bayan tafiyar su na zaunar da ita na yi mata nawa. Karatun Qur’ani salla da azkar kar ta yi wasa da su ta dake da karatu ban da shagala da ƙawayen banza duk abin da ya shige miki duhu ga gidan Uncle ɗin ki ne, in kina jin kewan gida ki je ki yi musu Weekend na yi mata fada sosai tana kuka ta ce in sha Allahu ba za ta saɓa magana ta ba. Ni daman ba na jin ta Jidda ba ta da rawan kai, da man dai Baby ce uwar rawan kai. Ina cikin yi mata nasihan sai ga Yallaɓai ya shigo jiya da yau duk a gidan Gimbiya yake. Ganin mu zaune a falo ga su Jidda duk a ƙasan cafet sun natsu ya sa ya ƙariso yana faɗin.
“Me ake tattaunawa na ga har Yumna ta yi ladabi”
Sai da ya faɗa na kalleta can gefen Baby ta yi zuru tana kallona kamar tana jin abin da na ke faɗi, sai na hau dariya ita kuma ganin babanta yasa ta mike da gudu tana faɗin” Aba Aba.”
Da yake ta fara mgana tana kiran Aba Uma, Ya Jido da Baby ita dai na yi na yi amma Yumna bakin ta ya saba da Baby ba ta kiran ta Yaya.
Ɗagata sama ya yi yana faɗin” My chubby Daugther.”
Saboda har yanzu Yumna da kibanta.
Tana ganin ta a hannun babanta sai ta fara zillo tana kamo habarsa, ita a dole sai ya yi mata wasan da ya saba mata. Ɗaga ta sama ya yi ya dawo da ita haka ya riƙa yi mata sai ka ji ta fara bangala dariya. Yumna daman ai yar son mugun wasa ne ko jiya sai da na cauleta da bulala Baby kuma ta ci dundu saboda sun ɓata mini falo, wai da sunan wasa, bai zauna ba sai da ya ga ta kusa siƙewa saboda dariya sannan ya zauna ya zaro chaculate a aljihun wandon jikinsa ya ba ta ɗaya, ɗaya ya ba ma Baby ɗayan kuma ya ba ma Jidda amma ni ina zaune bai ba ni ba.
“Ina nawa abin daɗin Yallaɓai?
“Kin yi girma da yawa abin yara ne.”
“Lalle na ga son kai.”
Na faɗa ina girgiza kaina kai tsaye ya ce mini nima na so kaina bai hana ni ba. Na ce ya ci bashi ne wallahi zan rama ya ce sai dai na rame.
Kiran sunan Jidda ya yi ganin ta yi shuru tana ɗagowa ya gane ta yi kuka.
“Jidda me ya faru? Kukan kewan gida kike yi?
Sai ta gyaɗa kanta da hannuna ya nuna mata kusa dashi yana faɗin” Taho nan Mamana.”
Sumu sumu ta tashi ta ƙarisa kusa da shi ta zauna Yumna na kan jikinsa ya buɗe mata chaculte ɗin ta fara sha duk ta yi dama dama da shi a bakinta.
“Kar ki damu kin ji ko? Zariya ai gida ce ba wata matsala ki dai ki ma yar da hankalinki a wajen karatu. Make us proud Jiddan Abban ta.”
Sai ta gyaɗa mai kafin ta ce” In Allahu Abba.”
Kanta ya shafa kafin ya ce” Allah ya yi miki albarka. Allah ya ba ki sa’a a dukkan karatun ki.”
Ni da shi da ita muka amsa da Amin sai ya cigaba da ce mata in ta ji ganin gida kawai ta hayo mota ta taho, in kuma ba dama ta kira shi a waya shi sai ya je ya ganta. Sannan ga Uncle ɗin ta Hamza ga Abban ta Tariq. Duk wandr ta ke son gani ko take bukatar wani in ta yi musu mgana za su yi mata ta ce to Abba.
Ina daga gefe na ce” Tariq ai ya yi nisa Ya Hamza dai da suke kusa. Da na kira shi ina fada masa ga Jiddan nan za ta zo makaramta a kular mana da ita. Kañiyarki Dubu ya ce mini wai ni ce na ke masa kashedin ya kula da Jidda?
Na ƙarishe faɗa ina dariya. Yallabai ya ce shima sun yi waya kusan abin da ya ce mishi shima haka ya ce masa amma shi bai zage shi ba, amma dai ya ce masa daga shi har ni kar mu ƙara kiran shi a kan Jidda tun da mu ba mu da kara.
“Kai Ya Hamza ba dama.”
Na faɗa ina dariya. Yallabai na taya ni dariyan
Ina maaganar ko Weekend bayan sati ta ji kewan mutane sai ta je ta yi musu acan.
“Bai yi nisa ba?
“Ba wani nisa. Ina samaru ina pizzet?
Sai ya jinjina kai kafin ya ce” Ya yi nisa mana. Karatu Jidda za ta yi so in dai ba hutu suka samu ba ba zan so ta rika barin cikim makaranta ba.”
Sai na yi shuru kawai ina kallon Yallaɓai da mamaki ba ya so ta je gidan Yayan nawa ne me ya ke nufi da maganarsa? > Janaftybaby: “Akwai wata ƙawar Daughter da suka yi karatu tare a BUK. Tana auren wani H.O.D na department ɗin Computer Science kuma acikin Abu samaru suke zaune. So Daughter ta ce ta yi mata mgana nake ga zai fi in ta ji kewan gida ta je wajenta tun da duk cikin makarantar ne.”
“Ba shakka.”
Na faɗa ina kallon Yallaɓai yadda ya dage yana bayani.
“Ai kin ga ba za ki haɗa cikin makaranta da wajen makaranta ba ko?
“Ba zan haɗa ba. Amma ai ba garin za ta bari ba, duka duka mintina nawa ne tsakanin makarantar da Gidan Ya Hamza? Kenan kana so ka ce ƴa ta tana karatu a garin da Yayana ke zaune kenan ba za ta je ba ko? Sai gidan wata bare ka amince ta je kenan?
Na faɗa ina yi masa wani kallo, kallona ya yi kamar zai yi magana kawai sai ya ja tsaki ya kauda kai yana gyara ma Yumna bakin ta. Na ji zafin tsakin da ya yi mini, amma ban nuna ba sai na yi shuru ban ƙara mgana ba a ƙasan zuciyata na ce na ga mai hana ta zuwa gidan Yayana. Ko shi Yallaban bai isa ba ballanta wata matarsa.
Gajiya na yi da zaman na ga sai magana yake yi da yayan sa. Sai kawai na mike na miƙa hannu na ƙarɓi Yumna ina kallon Jidda da Baby kafin na ce” Ku kwanta da wuri kun san muna da tafiya gobe”
“Ina za ku je?
Yallaɓai ya tare ni lokaci ɗaya yana mai kallona.
“Za mu yi ma Ya Jidda Rakiya makaranta ne Abba.”.
Baby ta famshe ni, ga mamakina kawai sai na ji Yallaɓai na faɗin” Ke da wa kenan?
“Ni da Umma da Yumna”
Na juya zan bar falon saboda nu na gaji da wannan shan ƙamshin na Yallaɓai kawai sai na ji yana faɗin” Ke dai da su Khalipa. Ni Umman ki ba ta faɗa mini za ta je ba. Tare da Daughter na shirya ita da ta ce mini za ta je.”
Kan uba.!
Na faɗa a fatar bakina, na juyo ina son kallon fuskar Yallaɓai amma ya ƙi bari mu haɗa ido.
“To Umma fa Abba?
Jidda ta tambaya cikin ƴar damuwa.
“Ba ta ce za ta je ba an riga ta.”
Haka ya faɗa ko a jikin shi, saboda bakin ciki ya sa na juya kawai na shige ta kitchen zuwa ɗakin barcin mu. Ni Yallaɓai ke nuna ma iyakata akan y’ar da na haifa, wai ni ina uwar Jidda yana faɗa ma yayan shi cewa ban tambaya da wuri ba an rigani. To in sai na tambaya sai dai kar na je in har ya ga bam chanchanta ba, to ya je da wacce ya ke ganin ta cancanta. Na kasa sukuni maganar Yallaɓai ya tafasa mini zuciya shi ya sa da ya shigo mini sallama zai tafi ina saka ma Yumna Pampers lokacin da ya ce mini zai tafi sai da safe ko amsa shi ban yi ba shima ya san tsiyar da ya yi sai bai damu da ya tsaya ba ya fice na raka shi da uwar harara.
Ni fa akan iyakata da Yallaɓai ke nuna mini akan matarsa haƙurina ya kusa ƙarewa. Ni ina yi mata kara amma ni ba ta yi mini kuma yana gani bai taɓa magana ba, sai a kaina ne sai ya riƙa cin kasuwarsa yadda ya ga dama to bai isa ba. Kwana na yi da takaicin Yallaɓai tun asuba da muka tashi ba mu kwanta ba saboda tafiyar Jidda. Ban shirya ba mutumin da ya ce wata ta rigani ai in na shirya sai ya tozartani a gabanta shi ya sa sai na kama kaina amma fa bai ci bulus ba wallahi. Ƙarfe tara da wani abu suka shigo gidana shi da Gimbiya da su Khalipa da suka sha gayu, Gimbiya ce ta ba ni mamaki cikinta fa ina jin ya kusa shiga wata na takwas amma ita ya zaɓe ta taje tun da ita yake so, ni kuma banza a banza ba zan je ba. Ko daga ganin yanayin dressing ɗin da ta yi na san ta shirya ma tafiyar. Ta ci wani leshi doguwar riga ta ɗora ɗauri ta zubo kitson ta na baya da ta yi, fuska ta sha kwalliya har da jan baki mayafi a saman kafaɗa tana wani cin cimghm ita yar iska. Ban ji haushin ta ba kowa ya jawo mini wannan renin ba sai Yallaɓai shi ya sa ni ko kallo bai ishe ni ba.
Har da abinci na ga sun zo da shi, shi ma shadda ya saka mai kalan sararim samaniya shi da su Khalipa suka yi anko. Yallaɓai har da babban riga an ci uban gayu sai na fahimci kawai ya fake da guzuma ne zai harbi karsara. Amma wannan tafiyar ba ta Jidda ba ne ta su ce shi da matarsa ne. Saboda ma ta ƙure ni tana ganina ban shirya ba sai da take ce mini.
“Madam ya na ga ba ki shirya ba? Ko ba za ki je ba ne?
“Ba zan je ba, haba mun yi yawa ga ki? Ke ma ai uwar Jidda ce in kika rakata kamar ni ce na rakata duk ɗaya ne.’ > Janaftybaby: Yallaɓai na wajen na yarfa musu magana shi da ita. Ni zai yi ma tozarci, shi ya sa ko gaishe shi ban yi, shima bai yi mini magana ba kamar da man can yana jin haushina.
Shi da ya fiffita da kayan suka loda a booth wasu ma sai da aka sanya su a baya. Baby na ta murna, Yumna ganin haka sai ta fara kuka na saka zani na goya ta domin ba na son ma ta fara yi mini rigima. Ban yi fushi ba haraba na yi musu rakiya Amarya an kame a gaban mota yaran na baya Jidda da ba ta shiga ba ta rumgumeni sai kuka nima har ta sakani hawaye duk dauriyana sai da na yi kuka.
“Ki yi hakuri Jidda kin ji? Karatu ne za ki je, za mu rika mgana ta waya ba matsala.”
“Umma”
Ta faɗa tana ƙara fashewa da kuka cikin dauriya na rabata da jikina ina share mata hawaye ina mai faɗin” Ki daina kuka kin ji ko? Ki riƙe manganganun da na yi miki kin ji ko? Ki kula da kan ki ban da kula maza. Ban amince ba in dai ba mgana ce ta karatu ba? Ki riƙe azkar da karatun Qur’ani domin daga Allah sai kan ki kike da shi a can kuma mganar zuwa gidan Ya Hamza za ki je weekend bayan sati uku huɗu haka ki je ki gansu ki huta kin ji ko?
Sai ta sake rumgume ni tana kuka, nima na riƙe ta ina bubbuga bayanta alamun lallashi sai ga Yallaɓai ya fito daga mota yana faɗin” Ki sake ta don Allah, ba na so mu yi dare a hanya”
Ko kallon shi ban yi ba na sake ta na raka ta har mota ba ta shiga ba sai ta sumbaci kumatun Yumna da ta fara barci tana faɗin za ta yi kewar mu.
“Mu ma za mu yi kewarki Jidda. Allah ya ba ki sa’a.”
Na tura mota na rufe ina ɗaga mata hannu, hawaye suka taho mini sai kawai na juya na shige cikin gida, ga baƙin cikin Wulakancin Yallaɓai ga kewar Jidda. Sun tafi amma Yallaɓai bai yi mini sallama ba haka na faɗa a raina da na ji fitan mota da rufe get sai kawai na kifa kaina a saman dining na fashe da kuka. Ban san shigowar sa ba sai ji kawai na yi an dafa ni a firgice na ɗago sai na ci karo da Yallaɓai yana kallona kawai sai na mai da kaina ƙasa ina cigaba da tsiyayan ƙwalla.
“Sorry ko za ki shirya mu tafi ne?
Ko kallon shi ma ban yi ba saboda takaici.
“Ga Jidda can tana ta kuka itana kema kina nan kina kuka. Shi ne Daughter ta ce ko kawai ki shirya mu tafi gabaɗaya “
Wani irin kallon da na yi ma Yallaɓai shi ya sa da sauri ya ce” Me kuma na yi?
Yi haƙuri.”
Kawai sai na ture hannunsa daga kafaɗata kafin na miƙe ina faɗin” Ka gama magana ka ce wata ta rigani. Saboda haka ku je kawai Allah ya tsare.”
“Ni fa wasa nake yi da wannan mganar”
Yallaɓai ya raina mini wayau. Wai wasa yake yi? Ya kirani ya ce na shirya ko da ya ga ban shirya ba. Bai damu ba ko mgana ma bai yi mini ba sai yanzu da matar shi ta yi magana. Ƙokarin riƙe ni yake yi na fizge jikina na bar masa falon ban san lokacin da ya ƙara gaba ba. Na yi ta tafasa ni kaɗai a gida saboda da zaran na tuna wulakancin Yallaɓai sai na ji ina tafasa ni kaɗai.
Haka na yini a gida daga ni sai Yunma sai can da azahar sai ga Mubeena da Musbahu shi yake faɗa mini daman Yallabai ya ce da Anty Gimbiya za su tafi ba da ni ba amma saboda munafunci ya zo yana ce mini wai wasa yake yi mini. Zuwan su ne ya sa na ɗan saki Mubeena ce ta yi mana girki, Yallaɓai ya kira ni da kan shi ya ce sun sauka suna ma cikin makarantar, sai na kira Khaleesat na faɗa mata da man ta ce za su leka su ga wajen ita da Ya Hamza.
Mun yi waya da Jiddan itama can da gabda la’asar da su Ya Hamza suka je, ita ke faɗa mini Yallabai da Antynsu sun tafi gidan kawar Anty ina jin haka na ce gidan wannan ne da Yallaɓai ya yi maganarta ranar. Wani abu ya taso mini daga kasan zuciyata amma dai na daure. Daga baya da muka yi waya da Khaleesat ta ke faɗa mini sai da suka jira su Yallaɓai suka dawo a bakin ta na ke jin sun yi dare nan za su kwana amma yara kawai za su bar musu Yallabai da Amaryansa Hotel za su kama.
Ni fa daman na faɗa, ni na san da wata a ƙasa. Namiji uhm ni Yallaɓai zai yi ma haka? To ai shike nan, shi gogan sai dare ya kira ni ina ga bayan ya sun gama natsawa a hotel ɗin da suka kama sannan ya kirani yana daidaiciyar mgana.
“Sadiya mun yi dare za mu tsaya mu kwana zuwa da safe.’
“Allah ya nuna mana goben lafiya.” > Janaftybaby: Na faɗa a yatsine, na yi kums shuru jin ya yi shuru har ina jiyo maganar Gimbiya amma ban san abin da ta ke faɗa ba.
Ina shirin kashe wayar ne na ji yana faɗin” Yara suna gidan Ya Hamza”
“Anty Khaleesat ta faɗa mini.”
Na faɗa da gayya domin ya san na sani.
Jin na ji labarin a in da suke yasa bai ja mganar ba ya yi mini sallama saboda bariki har yana rage murya yana faɗin” Na yi kewar Sadiya ta “
Ashar ne kawai a bakina shi ya sa na yi shuru domin in na yi magana zan zage shi ne shi ya sa na yi kamar ban ji ba.
“Ina Yumna ta? I miss her.”
“Ta yi barci.”
Na faɗa a gajiye ban bari ya sake magana ba na yi saurin cewa” Zan kwanta sai da safe.”
Ban jira cewarsa ba, na kashe wayata ina jan uban tsaki wayar na hannuna ina jin wani abu na taso mini. Ina tuna me na yi ma Yallaɓai da zai shirya mini wulakanci haka.
Shigowar sako daga waya ta, ya sa na duba Yallaɓai ne.
“Ki yi haƙuri My Sady kin ji?
“I love you.”
“Munafuki”
Na faɗa a fili kafin na dankwafar da wayar. Barcina ranar rabi da rabi ne, da na farka sai takaicin Yallaɓai ya taso mini da safe ina ganin kiran shi ba ƙi dagawa. Sai can da muka yi waya da Jidda ta ce sun ta so ba su haɗu ba saboda yau ta fara attending ɗin lactures na yi mata fatan alheri sannan muka yi sallama cike da kewa. Na san za su sauka a gidana shi ya sa ki girki ban yi ba suka dawo ga yunwa ba abinci sai fita Yallaɓai ya yi ya siyo abincin ai yadda ya ganni ina cika ina batsewa ya san in ya yi mini magana to zan fa fashe na fara masifa shi ya sa bakin sa alaikun ya fita ya je ya siyo kuma har ni ɗin ya siyo mawa na karba kuma na ci. Sai da yamma ya tara matarsa da yaran su ya mai da su gida da wuri ya dawo yana mini yar murya da labarin Jidda.
Kallo ni bai ishe ni ba, ya yi ya gama yaga ban tanka shi ba sai ya koma ban haƙuri.
“Kin ga ta ce mini za ta je bai kyautu na ce mataa a’a ba. Ni kuma ganin ba ki ce mini za ki je ba shi ya sa ban kawo da ke ba. Ki yi hakuri na san kina da kara kamar yadda kika ce ke da ita kun zama ɗaya.”
Ni kallon shi kawai na ke yi, domin ni ba zan ɓata ma bakina akan shi ba tun da na san duk yaudara ce ta maza. Da na ga zai dame ni sai na ce masa ni ba haushi na ji ba amma da zai ƙyale ni da maganar nan da ya samu zaman lafiya. Shi ya sa sai ya yi shuru da mganar, ranar dai ba mu yi kwanan daɗi ba sai washegari na ɗan saki muka shirya amma na daɗe ina kallon Yallaɓai da wulaƙancin da ya yi mini amma tun da ya karyata kansa sai na ƙyale shi ɓan kara ta yar da mganar ba..
Na ɗauki girman na yi hakuri na share, Jidda ana can an kwarari sati uku a makaranta ko da yaushe ina kiran ta na ji halin da take ciki. Yallabai ma ko da yaushe satin ma ya shiga Kaduna sai da ya biya ya ganta. Mu dai ta bar mana kewa koda yaushe Baby zencenta kenan Ya Jidda, ni kaina ina kewarta da sanyin halinta gida ya rage daga ni sai Baby sai Yumna.
*
Cikin Gimbiya ya shiga watan haihuwan shi a bakin Yallaɓai na ji, hankalin shi duk ba a kwance yake ba, ni dai in yana magana ina yi masa fatan Allah ya sa ta sauka lafiya.
EDD dinta ma bai cika domin karshen watan march ya ce mini za ta haihu amma a ba ta kai ba ranar wata laraba yana gidana da safe ta kira shi ba ta da lafiya ya fita. Tun da ya fita bai dawo ba kuma bai kirani ba sai ni ce can na kira shi , a lokacin ya ke faɗamini suna asibiti haihuwa ce amma har lokacin ba ta haihu ba.
“Aikin za a sake yi mata?
“A’a sun ce a dakata a gani za ta iya haihuwa da kanta.”
Fatan sauka lafiya na yi masa na kashe wayata. Da a baya ne tsab zan shirya mu je, ni kan ai Gimbiya ta gama yi mini hankali ban ko a raina zan iya zuwa ba. Har dare da Yallaɓai ya dawo ba ta haihu ba, haka muka kwana da shi bai yi barci ba ni dai barcina na sha to ina ruwana, ai ni na gama hana kaina zaman lafiya a kan Gimbiya. Washegari tun safe ya tafi asibitin har yana jirana ko zan je na duba ta na ce ya je zan yi ma Hauwa ko Munnira waya mu je tare nan ko ba zuwa zan yi ba kuma ban kira kowa ba. Ba ta haihu ba sai bayan la’asar kafin ya kirani a status ɗin Anty Bahijja namiji Gimbiya ta sake haifa. > Janaftybaby: Anty Bahijjan ma a ƙasan hoton ta rubutu mai farar haihuwa ta sake yo wata farar ƙal ma kuwa. Na yi taging na yi Allah ya raya domin ni ba na baƙin ciki.
Sai daga baya angon karnin ya kirani ya faɗa mini ta haihu da kanta. Amma za su riƙe ta zuwa gobe ta zubar da jini sosai.”
“Ayya. Allah ya raya ya kuma ba ta lafiya”
Ya amsa da Amin Amin.
“Kin fito ne?
Sai da ya yi magana na tuna da karyan da na yi masa.
Da sauri na ce” Ban fito ba. Na kira su Hauwa sun ce mu bari gobe da safe kawai.”
Bai ce komai ba ya ce Allah ya kaimu. Ni ban kira su Hauwa da na yi ƙarya da su ba, washegari da safe da ya bar gidana asibitin ya fara biyawa sai ya iske Hauwa ni ina na sani ba sai da Hauwa ta kirani tana cewa.
“Sadiya me kika faɗa ma Tafida? Mun haɗu a asibiti yana ce mini ya na taho na bar ki alhalin kin ce masa tare zamu zo.’
“To sai kika ce masa me?
“Na kasa mgana. To ni me zan ce?
Na ciji yatsa kafin na ce” Kash! Kin kwafsa mini. Nan na ba ta labarin abin da ya faru.
“Ni fa ban yi niyyar zuwa ba ne”
“Ki tura mata Aniyarta ki zo ko saboda Yallaɓan.”
“To bari dai mu gani. Zan je na yi barka amma ba zuwan da na saba yi a da ba.”
Da muka gama waya da Hauwa na yi niyyar na je amma sai na kama ciwon ciki sai zawo, zan fita ne ina zawo na yi zama na a gida da daddare da Yallabai ya dawo sai da ya ce mini Hauwa ta je asibiti yau
“E. Ni na ce ta tafi kawai. Ban ji dadi cikina ke ta ciwo sai kuma na fara gudawa.”
“Sannu ya bari ko sai mun je asibiti?
Ya faɗa da kulawa sai na ce ya yi sauki, ni bai nuna mini komai ba shi ya sa nima ban damu ba.
Ban kuma samu zuwa ba sai washegari da yamma bayan an sallamo Gimbiyar da safe, Munnira na kira a waya na biya gida na ɗauke ta.
Sanda muka je yan Rano sun zo Mota guda su Naja da Anty Bahijja suna gidan ana ta shewa Anty Bahijja da ba ta gani ta ƙyale sai da ta ce mana.
“Jiya ɗayar ta ku ta zo ku sai yau ake ganin ku?
Wai Hauwa ce ɗayar mu. Munnira ce ta tsaya mata mgana ni gaisheta kawai na yi na wuce ciki wajen Gimbiya. Mun gaisa da yan uwanta na Rano sannan na karisa gefen gado na zauna muka gaisa na ɗauki Jaririn sak Khalipa yana jariri, na yi masa addu’a na bata shi ba wani jima ba muka tafi, daga nan na mai da Munnira gida da motata na koma gida ban faɗa ma kowa haihuwan Gimbiya hatta su Ya Aina Jidda ta kira ni tana cewa Abban su ya kirata yana murna yana faɗa mata sun yi ƙani na ce ai fa. Ta ce har hotuna ya tura mata. To ba abin mamaki ba ne tun da farar haihuwa ce aka sake yi masa.
Tun da na je barka ban ƙara komawa ba. Ga mamakina ana jibi suna Yallaɓai da zai fita sai ya ce mini na shirya na je na duba mai jego.
“Na je ai na duba ta.”
“Na sani. Ya kamata ki sake komawa kafin suna.”
Kamar zan yi magana sai ban yi ba, na ce to yana fita ko na ce ba in da zan je. Ranar yini na yi barci ma da ya dawo bai tambayeni amma na san ai ya fara biyawa ta gidan ta. Tun da Baaba Asma’u ta zo wacce ta zauna mata da haihuwan Anwar shi ya sa yake kwana a gidana. Ni ce da kaina na faɗa masa ban je ba ba na jin daɗi.
Na ga ya kalle ni amma ganin bai sauya fuska ba ya san ban damu ba.
“Allah ya sauwaƙe.”
Na amsa masa da Amin Amin
Kuma ko washegari ban je ba na yi zamana a gida. Munnira dai da Hauwa sun leka aikin suna ni dai sun kirani na ce musu ba in da zan je.
Ranar suna na yi niyyar lekawa shima ba da safe ba. Danan na cire mata atamfa ɗaya da pampers sai mayukan yara cikin saura na Yumna na saka a leda na ce in na leka goben zan kai mata.