Turken Gida – Chapter Forty-nine
by JanaftyLokacin da na fito daga gida na san ba ni da kuɗi a tare da ni amma hankalina bai tashi ba
sai da muka kai titi. Sannan na fahimci daga ni sai kayan jikina da hijabi na fito. Takalmin kafata na silafas ɗin cikin gida ne, tsabar a yanayin da na fito ba mai daɗi ba ne. Marwa na kalla da ke biye da ni, ga Afra sai ƙananun kuka take yi tana faman jijjigata.
“Marwa kin fito da ƙudi?
Na tambaya ina jan majina. Saboda tun fitowarmu har bakin titi hawayena bai tsagaita ba.
“E na ɗauko ƙaramar jaka ta”
Ta faɗa tana nuna mini jakar sai na sake jan hanci irin na masu kukan nan, mun ɗan jima kafin mu samu Adaidaita muka shiga na ce Ɗorayi zai kai mu.
Muna tafe shuru sai kukan Afra ni dai ina ta goge hawaye lokaci bayan lokaci ina jin nono na yana zuba kenan har yanzu Yumna ba ta daina kuka ba. Sai na ji tausayinta kamar in koma in ɗaukota amma kuma gwara da na barta shima ya ji in da daɗi.
“Umma.”
Marwa ta kira sunana tana kallona, nima da rinanun idanuwana na kalleta.
“Me ya faru?
Ganin ta ƙura mini ido amma ta kasa mgana.
“Umma me ya sa kika taho?
Da kin tsaya kun fahimci juna da Kawu “
Wata uwar harara na jefa mata sai ta yi saurin kama bakinta ta yi shuru.
“Kika sake yi mini maganar shi zan kwasa miki mari Marwa.”
Na faɗa ina huci ni kaɗai har ya yi mini wannan tozarcin kuma take tunanin na zauna mu fahimci juna? Mutumin da ya ce na bar masa gida ai ya gama magana.
“Ke ko a ranki ba ki ji haushin tozarcin da ya yi mini ba. Amma kina maganar wai da ban taho ba na zauna mu fahimci juna. Tun da ke a yanayin da kika gan shi kin ga alama yana buƙatar hakan.”
“Ki yi haƙuri Umma “
Ta faɗa a sanyaye amma ni sai na ji kamar ana hura ma ɓaçin raina wuta ma na cigaba da faɗa ta in da nake shiga ba ta nan nake fita ba, saboda ni gani nake yi goyon bayan Yallaɓai take yi ni kuma tana ganin laifina domin na bar masa gidan sa kamar yadda ya buƙata.
“Umma da kin taho da ko Yumna ne?
“Ba zan taho da ita ba ɗin. Lokacin da ya auro ni ai ba da ita Alhajinmu ya haɗo masa ba. Su zauna gidan ubansu nima gidan nawa uban za koma.”
“Umma tana ta kuka fa”
“Ke zan ci ubanki fa Marwa in ba ki ƙyale ni da waɗanan mganganun naki ba. Kina ƙara tunzarani.”
“Allah Ya ba ki haƙuri”
Ta faɗa tana sunkuyar da kai kamar munafukar tsabar yadda ta ba ni haushi kamar na kai mata duka.
“Namiji ya yi maka irin wannan wulakancin kuma don ba ka da zuciya sai ka cigaba da zama? To ko ke Kawu ya yi ma haka ni uwarki na ba ki Umarnin ki baro mishi gidan shi ki dawo gida domin ya san ubanki na da gida ba a daji ya auro ki ba.”
Ba ita kaɗai har mai Adaidaitan sai da ya juyo yana kallona na haɗe rai ina harare harare.
“Hajiya a dai yi haƙuri. Rayuwar auran yanzu duk ɗan hakuri ne.”
Hararan bayan shi na yi, domin ni yanzu duk wani namiji na gama sallama shi wallahi. Duka halin su ɗaya ba su da adalci sannan butulai ne. In za ka yanki naman jikinka kana ba su suna ci wata rana sai sun nuna ma duniya kai ne mara amfani a wajen su. Ni yau Yallaɓai ya kalla ido cikin ido ya ce ina da mugun nufi a kan matarsa wai har yana faɗin an targaɗa masa mata a sanadina. Ai na ɗauka yadda ya zo yana cika yana batsewa zai rama mata ne, sai wataƙila ya ji huce daga raɗaɗin taba matar so da aka yi. Ban ga laifin su ba duk mganganun da suka shirya masa in har ya yi amfani da hankalin shi da tunanin shi bai kamata ya fara da haka ba, da sai ya fara yin bincike kafin ya zartar da wata mgana.
Har muka sauka a Dorayi ni kadai na ke cika ina batsewa ina karkaɗa kafa. A bakin titi muka sauka Marwa ta biya shi kuɗin shi da taka da kafarmu muka ta ka zuwa gida. Lokacin ana ta kiraye kirayen sallar isha’i a wasu masallatan anguwan. Ai ban ji wani kukan baƙin ciki ya taho mini ba sai da na ji kafafuwana sun taka zauren gidanmu. Bayan shekaru ashirin da wani abu yau Yallaɓai ya bar mini tarihi. Tarihin ma mai nauyin da na ke jin sa har a cikin zuciyata. > Janaftybaby: Ni ce a gaba Marwa na bin bayana. Ba wutar nepa amma akwai hasken tocila a tsakar gida sai da muka ƙariso tsakar gida sannan na ga Alhajinmu duke yana alwala. Gwaggo ce ke tsaye tana haskamai da fitila. Ni na yi sallama amma muryata ta shaƙe da farko, sai da na sake yi kamar a tare ni da Marwa.
Gwaggo ta amsa lokaci ɗaya ta nai mai hasko fitila cikin mamaki.
“Sadiya.’;
Gwaggo ta faɗa cikin mamaki da har ya bayyana a muryanta
Alhajinmu kuma sai da ya idar da alwala sannan ya miƙe yana mai kiran sunana.
“Dubu”
Kamar yana tantama ɗin ce ko ba ni ɗin ba ce.
“Na’am Alhaji.”
Na faɗa cikin karyewan sauti kafin lokaci ɗaya na fashe da kuka.
Gwaggo ta ce” Subhanallah ke da waye haka?
Alhajinmu kuma duk ya ruɗe faɗi yake yi.
“Maimuna kama ta ku shiga ciki. Ba lafiya”
Kamar haɗin baki sai ga nepa sun kawo wuta tsakar gidan ya yi haske ɗau.
“Marwanatu.”
Alhaji da Gwaggo suka haɗa baki wajem ambaton sunan ta.
“Na’am.”
Ta amsa itama a sanyaye. Ai sai Alhajimmu ya kalli Gwaggo itama ta kalle shi Allah kaɗai ya san mai suke sakawa a zuciyarsu amma in zan iya karantar fuskokin su, sun bayyana damuwa tare da mamakin ganin mu a tare a wannan daren.
“Dubu lafiya? Me ke faruwa ne? Me Marwanatu ke yi tare da ke?
“Alhaji ƙafafuwana sun fara rawa. Allah ya sa dai lafiya.’
Gwaggo ta faɗa cikin damuwa.
“Ina fa lafiya. Ba lafiya Maimuna “
Alhajinmu ya faɗa shima a muryansa har ta bayyana damuwa.
Muna tsaye ni da Marwa mun kasa mgana, gwara ita ba kuka take yi ba ni kuka na ke yi har yana ba da sauti.
“Shin ba ku faɗa mana abin da ke faruwa ko sai kun sarƙe mana Numfashi da zullumi?
Gwaggo ta faɗa tana ɗan karisowa in da muke tsaye.
“Ke Sadiya bar kuka. Taho mu je abin da ke faruwa.’
Ta faɗa tana riko ni, ina jin ta taba ni sai na faɗa jikinta na ƙara fashewa da kuka ina faɗin” Gwaggo Yallaɓai ne ya ce wai na bar masa gidan sa”
“Innalillahi wa’inna ilaihirraju”un.
Gwaggo ta yi salati.
“La’ilahaillalahu.”
Alhajinmu ya karɓa.
“Muhamadan rasulillahi.”
Gwaggo ta ƙarishe cikin wani yanayi
“Da kika yi masa me zai kore ki da girman ki da kuma daren nan?
Gwaggo ta tambaya daga jin muryan ta za ka san hankalinta ya tashi.
“Ban yi masa komai Gwaggo a kan matar shi ne ya ke son ya wulaƙanta ni.”
.
Na fada ina shessheƙa. Gwaggo ta na bubbuga bayana alamun lallashi ta ce”Kai jama’a. Me ya sa Yusuf zai haka? Da girmansa?
To ita Marwanatu ba na gan ku tare a wannan daren?
“Suna ta zo. Gimbiya ce ta haihu yau suna suka taho daga Rano ɗazu da rana”
Ina jin Gwaggo ta sauke numfashi kafin ta ce” To da sauƙi ai na ɗauka itama wata matsalar ce.”
“Umma ce ta ce na taho mu tafi. Mun baro Baby da Yumna na ta kuka.”
Marwa ta faɗa kafin Gwaggo ta yi magana Alhajinmu ya ɗan murmusa yana so ya yi magana sai kuma ya yi shuru.
“Alhaji ya ka murmusa? Ka na ji surukin naka da ɗazun nan ka gama yabon sa ya baka kunya ya koro maka y’a kusan shekaru ashirin da aure cikin dare.”
“Ho Mata kenan ku dai ba a rabaku da son kai. Ni daman na san ai ta tsuniyar gizo ai ba ta wuce ta ƙoƙi ko?
“Ban ga ne ba Alhaji. Kuka fa Sadiya ke yi?
“Duk na ji. Kamata ku shiga ciki bari na je masallaci na dawo sai mu zauna mu yi magana. Allah ya rufa mana asiri.”.
Ta amsa da amin ya fice ni kuma Gwaggo ta rike ni zuwa falon Alhaji Marwa ta bi bayan mu. Zama muka yi a saman kujera mai zaman mutum biyu ni da Gwaggo.
“Wai shi Yusuf din ya ce ki bar masa gidan shi!
“Wallahi shi ya ce Gwaggo “
Na faɗa ina jan hanci irin na masu kuka.
“Me kika yi masa da zafi haka? Gaskiya ya ba ni mamaki ai ko mai kika yi masa bai kamata ya yi miki haka ba “
Ina goge hanci ina zayyana ma Gwaggo abin da ya faru ina hawaye ina faɗin” Abin takaici Gwaggo wai ni Yallabai ke kallona ya ce ina da mugun nufi a kan matarsa saboda tana haihuwan yaya maza ni kuma mata shine ina bakin kishi da ita na kasa hakuri na saka an dakar masa mata shi ne ya zo yana ta faɗa mini mganganu son ran shi daga ƙarshe ya ce na bar masa gidan shi” > Janaftybaby: Gwaggo ta yi salati ta dire kafin ta ce”oH ni Maimuna. Ashe yarinyar makira ce? Ina ganinta shuru shuru kamar ta Allah. Su suka shirya masa komai, shi kuma laifin sa ɗaya rashin bincike sannan na ga ɓakin sa da ya iya buɗe baki ya ce ki bar masa gida Haba. Ai ba ki cancanci wannan tozarcin ba.’
Uhm”
Kawai na iya cewa saboda zuciyata suya take yi. In ina tuna abin da ya faru.
“Umma ba cewa fa ya yi ki tafi ba. Ke kika ce mai za ki tafi ya ce shi ba zai hana ki ba “
Marwa na ƙura ma ido cikin takaicinta da bakin ciki. Na ma kasa mgana saboda na rasa abin da zan ce mata. Ina tunanin ba ni ce ƙanwar uwarta ba Yusuf Muhammad Inuwa ne.
“Af to me ya rage? Ai duk ɗaya. Mata ai mu haka Allah ya hallice mu, wata ƙila ta fadi haka ne ta gwada zurfin matsayinta shi kuma sai bai ba ta kunya ba, ya nuna mata iya na shi tattalin a kanta ya ce ta tafi ba zai hana ta ba. To ai shike nan bari Alhaji ya dawo sai ya ji shi ne da an tashi hira sai ya ce mijin Dubu dabam ne ina ganin ƙimarsa. To ai yau ga ƙarshen ƙima nan ya kore masa ƴ’a gabanin mangariba da isha’a da girmanta da komai, bai yi miki haka kina da kuruciya ba sai da shekaru suka fara gangarawa.”
Gwaggo sai faɗa take yi ni sai na ga ma ta fini ɗaukan zafi. Har a ƙasan raina ban ji daɗin da ma zo gida na buɗe cikina ba amma kuma ai shi ya ja. Da bai yi abin magana ba da ba a yi magana ba. Alwala muka yi ni da Marwa muka yi salla muna cikin sallar Alhajinmu ya dawo shi ya sa muna idarwa Gwaggo ta zo ta kira ni, da man a ɗakin Mama muka yi sallar.
falon Alhajinmu na koma yana zaune ga kwamukan abinci Gwaggo ta jera masa amma bai taɓa komai ba. Duk da ya nuna kamar bai damu ba amma na san ya damu ya kasa yin wani abu ba tare da ya ji damuwata ba. Allah sarki Alhajinmu ina son shi saboda in dai matsala ta tunkaro iylanshi shi baya samun natsuwa sai ya ga ya yi maganin matsalan nan. Dattijo ne mai juriya da jajircewa. Sai a lokacin na ji nadama da tunanin me ya sa na taho gida na ɗaga musu hankali? Da man ban zo ba, ssi wata zuciya ta ce gwara da kika zo a karon farko yau dai Yusuf zai fahimci ba da gidan shi kaɗai kika dogara ba.
“Dubu.”
Alhaji ya kira ni kamar yadda ya saba. Ina mai zama gaban shi na tankwashe kafa na amsa masa.
“Na’am ina yini Alhajinmu.”
“Lafiya lau. Sai kika baro mini mata can tana kuka?
Kaina na kasa na kasa mgana.
“Bai kamata laifin wani ya shafi wani ba Dubu. Rukayyatu nawa take da za ta fara karban hukuncin da ba na ta ba? Ba mama take sha ba har yanzu?
“E Alhajinmu.”
“Kin ji ko? Me ya sa kika yi haka Dubu? Koda na sanki da fushi ai ban san ki da rashin tausayi ba ko?
“Ka yi hakuri Alhaji na yi kuskure.”
“Kin yi kuskure babba. Domin kin ɗauki alhakin ran da bai ji ba, sannan bai gani ba, kar ki ƙara irin haka komai zai faru kar ki yi hukunci a in da bai dace ba. Ina ruwanta? Ta sam ne babanta ya yi miki? To ko domin wata rana ki yi aikin hankali kin ji ko?
“Na ji. In sha Allahu ba za a sake ba.”
Na faɗa ina wasa da gefen hijabina.
“Yauwa. In kin baro ita Mai sunan Gwaggon ta ku ita babba ce. Amma Rukayyatu kin ɗauki haƙƙin ta.”
Ni dai na yi shuru, saboda sai a yanzu da Alhaji ya sake jadadda mini sannan na sake fahintar ban kyauta ba. Ina jin nonuwana suna cika na san tana can tana rigima.
“Allah ya kyauta na gaba.”
Na amsa da Amin shuru na wani lokaci kafin Alhajinmu ya sske kiran sunana.
“Halima.”
Tun da na ji haka na san mganar mai girma ce.
“Na’am”
“Me ya haɗa ki da Yusufa har ya ce ki taho gida a daran nan?
Nan da nan na gyara zama cikin natsuwa na warware ma Alhajinmu komai tun daga farko na haihuwan da ta yi ban je barka da wuri da abin da ya faru yau. Har mganganun da muka yaba ma juna na fada masa, ni fa duk a tunanina Alhajinmu zai goya mini baya in ji ɗibar albarkar da Yallabai ya yi mini saboda matarsa.
“An faɗa masa ƙarya da gaskiya daga can Alhajinmu kawai yana zuwa gida ba bincike bai ji ta bakina ba kawai ya fara mini masifa da faɗa kamar zai dage ni.”
Na ƙarishe faɗa ina goge ƙwalla da gefen hijabina. Domin ina mai da yadda aka yi hawaye suka kece mini. > Janaftybaby: Alhajinmu ya yi shuru ni na ma ɗauka ko wani abu ne sai da na dago kaina na ga kallona yake yi na wani lokaci sannan ya gyaɗa kai ya yi wani mirmishin su na manya kafin ya ce.
“Dubu ba dai kina so ki faɗa mini rashin kunya kika yi ma mijin naki ba?
“A’a. Kawai dai raina ne ya baci nima na ma yar masa da martani Alhajimmu.”
Sai ya yi dariya wannan karon mai sauti kafin ya ce” Hohoho hausawa suka ce ko shekara ɗari ka yi baka haɗu da mutum ba. In ka fara ganin shi tambayi halin shi, domin hali zanen dutse ko zai iya sauya komai to ba zai iya sauya wannan halin na shi ba.”
Na yi kasaƙe saboda ina so na fahinci in da maganar Alhajinmu ta dosa.
“Dubu na san ki sarai bakin ki ba ya iya shuru. Kina da saurin hasala da faɗa. Kina so na ce kinyi daidai da abin da kika yi ne? To ba zan ce kin yi daidai ba sai ma na kira sunan ki ki amsa na sanar da ke da kaushin murya da cewa ba ki kyauta ba.”
Baki na buɗe ina kallon Alhajinmu. Duk da na san halin shi amma ban tsammaci zai iya cewa wai ban kyauta ba? Me na yi na rashin kyautawar?
“Na san a cikin zuciyarki kina ta tamtaman me kika yi na rashin kyautawa ko? Duk buɗe kunnuwanki da kyau Dubu. Kin yi rashin kyautawa da yawa a cikin duka abin da ya faru. Kuma hukuncin da Yusuf ya so yankewa yana kan daidai ne shima. Tun da ba a gaban shi komai ya faru ba shima faɗa masa aka yi, kuma da bakin ki kika ce daga can gidan abokiyar zaman taki an faɗa masa ƙarya da gaskiya. To ke me ya sa da ya zo gare ki, ba ki zaunar da shi kin faɗa masa gaskiyan abin da ya faru ba?
“Alhajinmu bai ba ni da mar haka ba faɗa kawai yake yi ta in da yake shiga ba ta nan yake fita ba.”
“Shi ne kuma yana faɗa kina fada. Har kika yi masa rashin ɗaa da gatsen ko yanzu ya ce ki bar masa gida za ki ta fi ko? To menene abin kuka don ya yi miki abin da kika bukata Dubu?
Ai sai na kasa mgana na dukar da kaina kasa. In Alhajinmu ya saka a ɗaki tun kana jin kana da gaskiya sai ka sare ka fahimci kai ne ba ka da gaskiya saboda irin kalaman da yake amfani da su wajen jawo hankalin mutum
“Ni da ke nan da Yusufa zai ƙara aure na kira ki, a wannan falon kika zauma kamar haka na yi miki nasiha? A cikin duka nasihin da na yi miki wata kalma na yi ta jadadda miki da in kika rike ta zaki rabauta?
“Haƙuri. Ka ce na je na yi ta hakuri wata rana ni ce zan zama mai riba.”
“To ashe ba ki manta ba? To me ya sa yanzu kika kasa haƙurin kika kuma kasa rabauta da sakamakon masu hakuri?
Sai kawai na sake fashewa da kuka ina fadin” Alhajinmu na yi ta haƙru wallahi ba ka san hakurin da na ke yi ba ne. Ko wani abu ne suka yi mini da na tuna da nasiharka na ke ma yar da komai ba komai ba. Yau ma ɗin ya ƙure ni ne shi ya sa na tanka masa.”
Na gama faɗa ina ta jan hanci saboda kuka.
“Du ka na ji kin yi haƙurin a baya amma abin da kika aikata yau duk ya kore wancan haƙurin na ki na baya “
Na ma kasa mgana na buɗe baki zan yi sai na ma yar na rufe. Ni fa na manta ne in dai Alhajinmu ne ba zai taɓa bani goyon baya ba da gaskiyan Gwaggo Alhajinmu na ganin ƙimar Yallaɓai a duk cikin surukansa ya sha faɗa ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba.
“Kina maganar ke ma da kika haihu ba ta zo ba kaza da kaza ina ruwan ki da wannan? Ke dai ba ki yi don Allah ba ai bai kamata,ki duba ita abin da ta yi miki ba. Ke kin yi mata domin Allah da zaman tare. Ruwanta ne ta ma yar miki da martanin Alheri ko sharri. Ke dai Ubangiji ya yi amfani da zuciyarki kuma ladan ki na wajen Allah. Ba hujja ba ce mijinki ya ba ki umarnin ki je asibiti ki dubata ki yi zaman ki, ki ƙi zuwa kin ga kenan kin saba umarninsa kuma mala’iku sun yi fushi dake matuƙar ba ki nemi gafaran shi ba. Sannan kuma abin da ya faru yau sanadin ki ne, ko da ruwan zam zam ba za ki iya wamke kanki ba tun da kin je wajen sannan waɗanda ke tare da ke ne suka yi hatsiyani ni da ke mun san ke ba ki saka su ba amma ba za mu ƙi gaskiyan cewa a sanadinki suka yi komai.”
“Wallahi ni Alhajinmu ban ce kowa ya yi faɗa saboda ni ba.”
Na fada ina ƙara rantse masa da Allah. > Janaftybaby: “Na ce miki ni da ke mun san ba ki saka su ba. Amma shi da sauran mutane in suka ji labarin za su yarda ba bakin ki a ciki! Ki yi tunani ki gani. A wannan gabar Yusufa ba shi da laifi abin da ya ji da shi zai yi amfani.”
Ina sharan ƙwallah na ce” Amma me ya sa ba zai yi bincike ba sai ya rufe ni da faɗa har yana ce mini ina da mugun nufi a raina?
Dariya na ga Alhajinmu ya yi kafin ya ce” Dubu ke kika jawo duk zargin da ya yi miki. Me ya sa kika bashi kofar ya fahimci kamar kina jin haushi da haihuwar da aka yi mass? Ki tuna shi ma fa ɗan adam ne yana da zuciya kamar yadda kike da ita. Sheɗan ne ya kawata masa a zuciyarsa amma ina da tabbacin ba haka yake nufi da gaske ba. Ai in da kima da mugun nufi akan matarsa da tun a farkon auran shi zai fahinci haka.”
Ni sai na ga kamar kawai ina zaune Alhajinmu na ta faman boye laifukan Yallaɓai yana bayyana nawa.
“Har fa ce mini ya yi wai ina kishi da tana haihuwan Maza ni kuma Allah bai ba ni ba “
Na faɗa hawaye na kece mini saboda takaicin kalamansa.
“Haka zai yi tunani haka ma kowa zai yi tunani. Haihuwa kuma na Ubangiji ne daman Allah ya faɗa mana wasu zai ba su maza da mata, wasu mata kaɗai wasu mazan kaɗai wasu ma har su koma ga Allah ba zai ba su haihuwan ba ki godema Allah kina cikin zabaɓɓun Ubangiji. Maganar ita tana yin farar haihuwa ki bar ta da tunaninta, tun da ai shi mijin na ku bai ce ba ya son matan ba duka yana so kuma duka ƴaƴan shi ne. Sai ki roƙi Ubangiji ya baki mai albarka daga Mazan ko daga matan.”
Kawai sai na cigaba da sharan ƙwalla domin ni dai Alhajinmu ya gama ƙure duka mganganuna.
“Ki yi haƙuri ki daina kuka ba wai ina goyon bayan shi ba ne a’a ina faɗa miki gaskiya ne a matsayina na adalin Uba. Ba wai don kina ƴ’ata na goyo bayan ki ba, a’a ni ke da shi duka ƴaƴana ne zan yi miki adalci kamar yadda zan yi masa. Ki daina kuka ya isa haka nan ba wani abu ba ne. Kawai sheɗan ne ya shiga tsakani ganin kun kasa samun fahimtar juna.”
“Alhajinmu ta ya ya zai fahimce ni?
“Ta hanyar amfani da kalamai na kwantar da hankali kar ki ɗaga sautin ki sama da na shi, na tabbata da kin yi haka da kun fahimci juna.’
“Uhm”
Na sha numfashi saboda na fahimci Alhajinmu ba zai gane karatun kurma ba.
Murmishi ya yi ganin na yi shuru yana kaɗa kai ya ce” Kukan ya isa kin ji share hawayen ki.”
Ban yi musu ba share hawayena.
“Yau kike so ki koma gidanki ko sai gobe da safe?
Na kalli Alhajinmu baki buɗe kafin na ce” To kore ni fa ya yi me ya sa zan koma?
“Ashe ba yanzu na gama yi miki nasiha na ganar da ke kuskuran ki ba? To za ki koma gidan auran ki in sha Allahu. Shima ai na san yana can cikin damuwa in bai zo a daran nan zai da safe ina da tabbacin haka”
Kallon Alhajimmu na ke yi na kasa mgana yadda kawai yake da confident a kan Yallaɓai ke ba ni mamaki. Don ba warware masa komai ba! Ai wallahi da ya san wani abu da tuni zai daina wani cika baki a kan shi.
“Har gobe ina ganin sa da ƙima. Tun bayan shekaru ashirin da doriya na ba shi amanarki dai dai da rana ɗaya bai taɓa kawo mini ƙaran ki ba. Ko da yaushe ya zo gaisheni godiya yake yi mini yana yaba miki. Duk da na san kina saɓa masa shina haka amma bai taba fada mini saɓanin alherin ki ba. Ya zauna dake cikin daɗi da rashin sa. Kema ai ba ki taba kawo mini ƙaran sa ba sai yau. To na yau ɗin ma duk kishi ne shi ya sa ban ɗauke sa wani abu mai girma ba. Ki koma gidanki ki daidaita da mijinki domin yana yi miki kara ba domin komai sai domin yana son ki. Ki je ki ba shi haƙuri ki kara haƙuri Mai hakuri in ya yi ta shan haƙuri ba ya kiɓa lokaci ɗaya amma watan wata rana zai zama giwa in har ya koshi da hakuri”
“Ki yi hakurin kin ji ko?
Ki koma ki cigaba da Biyayya aure. Domin Aljannarki tana a karƙashin diga digin mijin ki ne Dubu. In kin yi masa biyayya ki rabauta. In kin saɓa masa ki taɓe. Ni ba ruwana na riga na sauke haƙƙin Ubangiji na in kin bauɗe na faɗa miki gaskiya.”
Na yi shuru ban yi magana ba kaina na ƙasa amma na daina kuka.
“Kin ji ko? > Janaftybaby: Ya sake faɗa yana kallona sai na gyaɗakaina kafin na ce” In sha Allahu Alhajinmu na gode Allah ya ƙara girma.”
Ya amsa da Amin kafin ya cigaba da faɗin” Da dake da Rahila ne na ke yawan kafa misali da ku. Na kan ce tun da na aurar da ku ba ku taɓa tada mini hankali da korafin mzajen ku ba. Sannan suma ba su taɓa kawo mini maganar sharrin ku ba sai alheri. Amma sai ga shi a wancan satin nan in da kike zaune Muntari ya zauna yana karanta mini wani abu daga cikin na ƙuntata da Rahila ta ke yi masa ya kasa haƙuri ya kasa tanƙwasata sai da ya karya kaurin nan ya zo gabana yana faɗa mini na kira ta na yi mata faɗa. To kema ko sati ba a yi ga ki nan zaune kina kawo mini suka akan mijin ki, ke da Rahila kuna so ku ba ma misalina kunya ne?
Da sauri na ce” Ba za mu ba ka kunya ba in sha Allahu Alhajinmu.”
“To na ji daɗin haka. Allah ya sa. Allah ya yi muku albarka addu’ata a koda yaushe ya zaunar da ku lafiya sannan ya yalwata ma mazajen ku samun su yadda za su riƙe ku bisa gaskiya da amana.”
.
Na amsa da Amin kafin na yi tambayar da ke sosa mini rai.
“Alhaji me Rahilan ta yi ma Ya Muntari?
“Ina ruwan ki? Wannan tsakanina da ɗana ne. Ya faɗa mini kuma na sauke haƙƙi na kirata a wannan falon na yi mata faɗa ta yi mini kuma alƙawarin ta daina. Kamar yadda kema ba zan yi taɗin nan da kowa ba itama ba zan zo ina faɗin rashin kyautatarwarta ba. Ni kamar alƙali ne shi kuma alƙali ana son shi da gaskiya da rike sirri “
“Ai ni za ta faɗa mini Alhaji”
Na faɗa ina mirmishi shima mirmishin ya yi kafin ya ce” Wannan shima dai duk tsakanimku ne. In ta faɗa miki ba ta yi laifi ba. Domin tare kuka tashi kuka girma, akwai sirrukan masu yawan da zaku tattauna a tsakaninku na yan uwa.”
“Haka ne Alhaji.”
“To kin gani. Allah ya yi muku albarka gabaɗaya. Tashi ki je ki samu wani abu ki ci sannan ki kwanta da safe ki koma ɗakin mijinki ki tallafi yayanki. Ke da kika kusa kai ga suruki Dubu amaryata da na saka ana can jami’a ana ta karatu ko?
Ina dariya na amsa masa” E Alhaji amma ai ta ce ba ta ssku ba auranku na zoɓe ne.”
“Manta da ita, ga matata ta gaskiya me zan yi da ta roba?
Amma dai ina nan ina jiran ta a falon nan ta kawo mini suruki na ga ko na fishi dogon hanci.”
Me zan yi in ba dariya ba, da man shi Alhaji dariyan ya ke so na yi. Ya sallame bayan ya ce na ce Marwanatu ta zo su gaisa ita da wannan yarinyar na ta mai kukan tsiya duk ta cika masa kunni.
Na fita ina dariya na koma ɗakin Gwaggo na iske su suna ta hira na faɗa mata saƙon Alhaji sai ta sunkunci yarta ta fuce tana faɗin” Shi ta ke jira ya lallasheta.”
Bayan fttan ta Gwaggo ba ta matsa mini sai ta ji yadda muka yi da Alhaji ba amma dai na faɗa mata zan koma saboda Yumna.
“E gaskiya ya kamata baiwar Allah na san za ta sha kuka.”
“Wallahi Gwaggo Nonuwana har sun fara tasawa.”
“Wayyo sannu. Ko za ki sha panadol ne in kin ci abinci.”
“To Gwaggio”
Ita ta kawo mini abincin Tuwo ne miyar kubewa bushasshiya. Na ci da yawa muna hira ban gama ba Marwa ta dawo ta ce ma Gwaggo ta je ta ba ma Alhaji Tuwo kafin ya suma saboda Yunwa.
“Ai da man ke ce kika tsayar da shi, amma shi uwarhaka ai ya koshi ya kwanta.”
Muna ta dariya ta fice ta bar mu, Marwa ta zauna muka ƙarishe cin tuwo da ita ta fita da kwamukan ta ɗibo mana ruwa na sha mgani da shi.
Akwai katifa a ɗakin Gwaggo ita Marwa ta shimfiɗa za ta kwanta ni kuma na ce ina gado
Na yi mata sai da safe ganin waya a hannunta sai na yi tunanin mijinta za ta kira.
Har na juya ta kirani.
“Umma.”
Na juyo ina kallonta.
“Za ki koma ko?
Sai da na yatsina fuska kafin na ce” Alhaji ya matsa. Zan koma gobe in sha Allahu.”
Sai ta kama murna. Na yi shigewata na bar ta. Kayan jikina na cire, na samu wata rigar Gwaggo ta makka ce Ma’u ta kawo mata ita da daɗewa lokacin da mijinta ya koma. Gwaggo a lokacin ta ce ba ta so wai na yara ne muka matsa mata ta karba. Ashe za ta yi mini amfani ita na zuba mai taushi har kasa na ɗaure kaina dakallabi na haye gadon Gwaggo. Na daɗe ban yi barci ba kewan gidana kewar ‘ƴayana da mijina. > Janaftybaby: Su suka taru suka yi mini rufdugu na yi ta juye juye sai can barci ya kwashe ni har ina makara sai da na ji Gwaggo na kiran sunana.
Sannan na iya tashi na je na ɗauro alwala na yi salla nonuwana sun yi mini nauyi sun kwana a ba tsotsa ina jin kamar zazzaɓi zai kama ni amma haka na fita na share tsakar gidan nan tas na haɗa wamke-wanke Marwa ta karba sannan na je na gaida Alhajinmu ƙara jadadda mini yake yi da na ƙarya na shirya na koma gidana. Ni dai ba ni da ta cewa daman ai dole na koma ko domin Yumna amma a kasan zuciya ina cewa ba don halin Yallaɓai ba shima.
Ɗumamamman tuwon jiya muka ci da safe, na ƙara shan panadol na kwanta da niyar na dan runtsa barci ya sarkeni, tun wajen tara na kwanta ni ce sai wajen sha ɗaya na tashi. Shima ɗin tada ni Marwa ta yi wai tana faɗa mini ga su Kawu nan.
“Wani kawun?
Na faɗa ina mitsike idanuwana masu cike da barci
Kafin ta samu zarafin magana na ji kukan Yumna ai da sauri da diro daga saman gadon Gwaggo a ƙofar falo muka ci karo da Baby ɗauke da Yumna tana ganina ta rumgumeni tare da Yumma tana faɗin” Umma mun yi kewarki jiya. Yumna ta kwana kuka Abba ne ya yi ta lallashinta yana ta ba ta tea”
A zuciyata na ce da kyau na ji daɗi da ya ɗanɗana.
Ture Baby na yi baya kaɗan ina karɓan Yumna wacce ke ta miƙo mini hannu tana faɗin Uma.
Da sauri na karɓeta na rumgumeta ni da ita muka sauke ajiyar zuciya kamar mun shekara ba mu ga juna ba..zama na yi a saman kujera na fara ba ta nono. Allah sarki baiwar Allah ta karɓe da sauri tana sauke numfashi. Ina shafa kanta ina mai jin tausayinta. Sai na ga an yi mata wanka itama Baby ta yi wankanta.
“Ba ki je makaranta ba?
“Umma mun fa makara. Abba bai yi barci da wuri ba sai 7:30am muka tashi fa.”
Ta faɗa tana kirga mini da hannunta.
“Uhm wa ya yi ma Yumna wanka?
“Abba mana. Ni kuma na yi da kai na shi ya soya mana doya da kwai Umma.”
“Ya kyauta.”
Na faɗa ina jinjina kai Marwa na kalla ganin tana ta shiri alamun kamar ta yi wanka ne.
“Gida za ki leƙa?
“A’a tafiya za mu yi”
“Ke da wa?
“Ni da Kawu mana. “
Sai ta ga na yi shuru ina kallonta sai ta yi dariya kafin ta ce” Umma ni da Baban Abadallah.”
Sai na ware ido kafin na ce” Ya zo ne?
“Ya zo tun dazu tare muka zo da shi da Abba.”
Baby ta fanshe ta sai na fara tunanin ko wa ya faɗa ma Kawu ko kuma dai ya zo ɗaukan Marwa ne bai san abin da ya faru ba sai yau.
“Ni ba ruwana. Nima da safen nan ya ce mini zai zo Abban Jidda ya yi masa waya akan kum samu matsala.”
“Uhm”
Kawai na ce na cigaba da ba ma Baby Nono Jidda na ta yi mini surutu na yi kamar ban jiba. Wayata na gida ban san adadin waɗanda suka kira ni ba. Ba daɗewa muka ji muryan su a tsakar gida sai ga Gwaggo ta shigo da hijabinta tana faɗin”
“Ki ta so ta..'”
Ganina a zaune sai ta ce” Au ashe kin tashi? To maza ki shirya ga mijinki can na jiran ki.”
Baki na tura kafin na ce” To ban yi wanka ba zan tafi Gwaggo “
“Ba gidan ki za ki koma ba? In kin je can sai ki yi. Maza tashi kafin Alhaji ya ji ya leƙo da kansa kin san halin shi.”
Ba ni da yadda zan yi haka nan na yanke ba ma Yumna Nono Gwaggo ta karɓeta tana yi mata wasa.
Kayana na je na saka na ɗauko hijabina na saka. Baby tuni ta fita wajen babanta Marwa na yi ma magana ko yanzu za su wuce ta ce zai kaita gida ta gai da Ya Aina. Amma kafin su wuce za ta biyo gidan tun da akwai kayanta a can na ce mata toh. Na karɓi Yumna hannun Gwaggo na shiga yi ma Alhajin mu sallama.
“Allah ya yi miki albarka. Mijinki ya yi ta bani haƙuri sharrin shedan ne Allah ya tsare na gaba.’
Na ce Amin sannan ya yi ma Yumna wasa, har yana ba ta 500 ya ce kuɗin zance ne. Na karɓan mata ina masa godiya. Koda na fita kofar gida suna jikin motar Yallaɓai shi da Kawu suna mgana amma kowannen su da motar shi ya zo. Baby na cikin mota da alamu ni suke jira.
Ba domin Kawu ba wallahi shigewata mota zan yi amma saboda shi na tsaya ina gaishe shi.
“Lafiya lau Surukata. Ashe kuma abin da wannann mara mutumcin ya yi miki kenan?
Sai na kasa magana amma na kauda kaina bana son ma mu haɗa ido da Yallaɓai. > Janaftybaby: “Ai da kin kirani wallahi sai na shigar miki. Amma ko yanzu na yi mata faɗa na ce kuma ya gode ma Allah ma ya samu surukai na gari in wani ne Alhaji ai ko kallon sa ba zai yi ba. Maimakon haka ma sai ya karrama mu, muna bashi haƙuri muma yana ba mu.”
Nan ma na yi shuru kaina na kasa, Yumna ce ma ke miƙa ma Yallabai hannu tana faɗin Aba da sauri na janyeta ina ƙara haɗe raina.
“Ki yi haƙuri kin ji ko? Fushi ne da shedan suka yi tasri a kan shi amma ya tuba ya ce ba zai ƙara ba.”
Sai na ɗan kalle shi ta gefen ido kansa na ƙasa yana ɗan mirmishi kamar ba shi ne ya yi mini wulakanci ba jiya.
“Ba komai. Allah ya kyauta na gaba.’
Suka amsa da Amin gabaɗaya. Shi ya buɗe mini gaban mota na ƙi shiga na faɗa baya kusa da Baby. Mun tafi muka bar Kawu anan amma ya ce za su biyo kafin su wuce. Muna tafe a hanya yana ta kallona ta madubin gaban mota ni ko na yi cuɗun ciɗun da fuska bai ga fuskar ma wata mgana ba.
Haka muka isa gida ni ko jiran shi ban yi ba na yi wuce wata cikin gida. Ya biyo ni har ɗaki yana so ya yi mini magana na bar masa yarsa nan saman gado na faɗa tiolet na banko masa ƙofa ai ban fito ba sai da na ji ƙaran jan get alamin ya fita sannan na fito ina jan tsaki.
Sai da na yi wanka sannan na duba gidan. Kitchen dai ya sha kyau Baby na saka ta gyara shi ta goge da falon su. Falon Yallaɓai ko ta kan shi ban bi ba girki ma doya na ce Baby ta fre mana ta sulala mu ci da mai da yaji sai bayan azhar na duba wayata. Hauwa da Munnira sun kikkirani da Rahila sai Suwaiba.
Munnira na fara kira ba ta ɗauka ba sai na kira Hauwa. Ita ke faɗa mini Mutaƙka ya yi fata fata jiya akan abin da ya faru, ni tsabar haushi ban san lokacin da na ce.
“Ku fita hanyata ku fara aminta da Gimbiya shine faɗan na su.”
“Wani irin magaana ne wannan? Ai ba su isa ba. Shima ai na faɗa masa ba zai yuyu ba sai ya ce wai shi bai ne na rabu dake ba amma na daina wulakanta Gimbiya saboda ke Ya Tafida ya ce ba ya jin daɗin haka.”
“Kar Allah ya sa ya ji daɗin mana.’
Na faɗa cikin ɓacin rai, ban faɗa mata na je gida har na kwana ba amma na faɗa mun hau ramar da ba ta da ganye mun fado a jiya da daddare ni da Yallaɓai.
“Kai Gimbiya ba ta ji daɗi ba. Ta haɗa karya da gaskiya.’
“Daga shi har ita in sun fasa sun raina Ubangijin su.’
Sai da na faɗa sannan na rufe baki ina waige-waige ni kaɗai sai da na yi dariya Hauwa ma sai da ta dara.”
“Haushi take ji kuna tare da ni, ba ma ita ba har su Anty Bahijja ma. Kuma sai dai su mutu wallahi.’
Hauwa ta ce kwarai mun daɗe muna mgana kiran wayar Munnira ne ya katse mu. Ta ce mini Ashe ta koma tun safe,Marwa fa? Na ce mijinta ya zo ɗaukanta ta je gida ta dawo.
Munnira zage-zage ta dinga yi tana faɗa mimi hauka hauka ta yi ma Nasir jiya ya zo yana ce mata ita ke hassada fitina tsakanin matan Yaya Tafida.”
“Ai ko jiya ya ga tijara. Na fashe kamar tayagas faaa faaa. Haka nake yi ta in da na ke shiga ba ta nan nake fita ba. Ai daga karshe sai ya dawo yana bani haƙuri.”
Ina dariya na ce” Duk haka suke suna da son kan su. Amma ba su da laifi abin da Yallaɓai ya faɗa musu. Za a ce ke ce ke da fitina ya ja miki kunne.”
“To ai ba shi kaɗai ba hadda su Anty Bahijja, a group ɗin gidan su je ki gani sai abin da suka manta ba su fada mana ba, na fara ma yar da martani Mimisco ta kira ni ta ce kar na sake magama shi ya sa na yi shuru.”
“Au kuma?
“Wallahi kunna data ki sha kallo.”
Ba musu na yanke wayar na kunna data. Sai da na bari saƙonnin duk sun gama shigowa a group din gidan su Yallabai Iyalan Marigayi Muhammad Inuwa0 Mata ne kaɗao sai mi surukai a ciki mazan suna can na farkon.
An yi ta cin kasuwa akan mu har Yayar Gimbiya da ba ta zo ma sunan ba, tana ta mganar cewa ba za su yarda da duka ba ko su Anty Bahijja su ɗau mataki ko su su ɗauka da kan su.
Ita ko yar kanzagi Anty Bahijja ta ce ai Tafida tuni ya ɗauka mataki dukkanmu an ja mana kunne. Anty Maimuna ta fito ta ce ba lafin kowa ba ne sai ni Munnira ta ce ko gobe yarinya ta sake mata rashin kunya sai ta mata dukan tsiya. Anty Maimuna ta ce ta yi mata rashin kunya Nasir zai ji, group ya koma faɗi in faɗa har sun jj labarin abin da ya faru. > Janaftybaby: A cewar Jamila ta ce Gimbiya da bakinta tafaɗa mata ni da su Munnira taron dangin muka yi mata ita da yan uwanta Suwaiba ta yi taggin ta ce ƙarya ne tana wajen ta yi Vn wajen mimtina sha tana bayanin abin da ya faru ni ina fara ji ma haushi ya sa na kashe gabaɗaya.
An yi manganganu har Ant Zabba ta tanka ta ce in dai har gida muka je muka dake su ba mu kyauta ba.. amma ya kamata a yi bincike domim a samu sulhu. Mimisco ta tawatar ganin abin na nemen ya zama rigima ta ce kar wanda ya ƙara mgana. Ba ni da damar ma yar da martani shi ya sa na yi shuru.
Kafin ma na kashe datan sai ga kiran Mimisco na ɗauka muka gaisa sannan ta tambayeni abin da ya faru duk na zayyane mata, ta ce gaskiya suma ba su kyauta amma Munmira ma ba ta kyauta da tun farko ba ta tanka su ba. Ta yi mini faɗa sosai ta ce bai kamata ina barin ƙananun abubuwa suna shan gabana ba. Na yi gaba fa sai dai a biyo bayana. Na ji daɗin magana da ita shi ya sa duk cikin yayyen Yallaɓai Mimisco na dabam ce a wajena. Ta ce ko an buɗe gidan kar na tanka ma kowa na yi shuru kawai itama amsa ce. Nan take na yi mata alƙawarin ba zan yi magana ba ta yi mini godiya muka yi sallama.
Mun gama wayar kenan ina shirin ajiyeta bayan na kashe data Jidda ta kira ni kwana biyu ba mu gaisa.
Bayan gaisuwa da tambayan makaranta ta kira sunana.
“Umma.”
“Na’am Jidda.”
“Me ya faru tsakanin ki da Abba ne?
Cikin mamaki na ce” Me kika gani?
“To ya kira ni yanzu ba daɗewa yana faɗa mini ya yi miki laifi kina fushi da shi na kira ki na baki haƙuri”
“In ji baban na ki?
“E Umma. Don Allah ki yi masa haƙuri ba ki ji muryan Abba ba duk ya damu.”
Sai na yi mirmishi kafin na ce” Bayan nan bai faɗa miki komai ba? Bai faɗa miki laifin da ya yi ba?
Tana dariya ta ce.”Umma ba sai ya faɗa mini ni dai kawai ya ce kina fushi da shi na kira ki na ce ki yafe masa ki kula shi.”
“To.”
“Don Allah Umma.”
“Na ce to ko?
Na faɗa a ɗan hasale.
“To ai Umma na san halin ki ne yanzu sai ki fara gaba da shi, yana mgana kina yin banza da shi. Allah Abba abin tausayi ne fa Umma in dai a kan ki ne.”
“Ƙaniyarki Jidda.”
Na fada ina danne dariyata itama dariyan ta ke yi.
“Ke har kin san abin tausayi a kaina? Zan ci mutimcin ki fa”
“Wallahi Umma in ba ki yi masa mgana da ya ganki duk sai ya ruɗe”
“Sai anjuma Jidda”
Na faɗa mirmishi, jin tana yi mini shaƙiyanci.
“Umma a duba mini my Abbana don Allah.”
Kawai sai na yi tsaki na kashe wayar, har ta saka ni mirmishi wai Yallabai ne da kiran Jidda yana cewa ta ba ni haƙuri, ba ma wannan ba yaran mu fa yanzu duk motsin mu suna ankare damu ji dai Jidda da na ke ganinta shuru shuru ashe tana ankare da komai. Wayar da muka yi da ita sai na ji zuciyata ya ɗan sauka
Ina cikin ɗaki Marwa ta zo, ba ta wani daɗe ba amma ssi da na zuba mata doya ta tafin ma Kawu da shi tun da yana so amma ya ce ba za su tsaya ba akwatinta ta ɗauka na raka ta har haraba na ba ma Afra 1k na ce ita 500 Abadalla ma haka tana ta mini godiya. Kawu daman a can waje ya yi parking ɗin motar shi.
Yallaɓai na neman shiri da wuri ya dawo ana yin sallar mangariba ya siyo mini fura da kayan marmari ban sake masa gwiwa ba amma dai na karɓa kadahan kadahan. Lokacin na yi wanka abinci kuma daman farar shinkafa na dafa da daddaren ina da sauran miya, saboda na san muna faɗa sai na ji gayu na tsuke cikin riga da wando ina tafe mazaunena suna kaɗawa. Ai da ƙyar ya fita sallar isha’i yana dawowa ina ciki Yumna na wajen Baby ya ritsani yakulle kofa.
“Sadiya so kike yi na haukace a kan ki ko?
Ina tssye lokaci ɗaya ina ninke darduman da na idar da salla a kanta na ce” Sai dai in matarka ce za ta haukata ka. Amma ni Sadiya ai ban kai wannan matsayin ba.’
Ban san ya ƙariso gabana ba sai da na ji ya ruƙumƙume ni daga tsayen yana mai faɗin” Ki yi haƙuri ki yafe mini na yi kuskuren da na zo na yi miki magana cikin fushi. Am sorry please.”
Na yi banza da shi, amma dai ban yi ƙoƙarin kwace jikina ba. Ya juyo da ni muna kallon juna ya saka hannu ya zare mini hijabin jikina yana bina da wani kallo duk ban yi masa mgana ba. > Janaftybaby: “Kike cewa ba ki isa ba Sadiya ta? To wai wata kuma isar kike so na nuna miki da za ki san ni a wajena kin isa kin iss. Ke ɗin isa ce kafin ma isar ta iso.”
A tsume na kalle shi kafin na ce” ai ka gama nuna mini isata tun da jiya ka ce na bar maka gida.’
Sai kawai ya riƙo hannuna duka buyin cikin na shi ya matse yan faɗin” Na rantse da wanda raina ke hannun shi. Lokacin da kika ce in na ce ki tafi za ki tafi na faɗa ne domin na ga zaki iya tafiya ki bar ni Sadiya? Sai na ga wai kin tafi? Lokacin da kika fita wallahi ji na yi kaina ya yi wani girimgirim Sadiya na shiga tashin hankali. Me ya sa za ki yi mini irin wannan gatsen fisabillahi”?
“Gatsen me? Kai ka ce na tafi ba za ka hana ni ba.”
“Na gwada ne, na gwada ki na ɗauka kema a wasa kika faɗa “
Kallon sa na yi ina wata dariya kafin na ce” Wasa? Ni ka ga wasa a magana ne.”
“Wallahi ban gani ba. Kin ba ni tabbaci jiya. Ni dai kar ki ƙara yi mini irin haka bana so. Sai ki saka ai zuciyata ta buga.”
Na buɗe baki zan yi magana ya haɗe bakin mu waje ɗaya yana tallafo kaina na yi masa tsaye ƙiƙam shi ya sa sumbatar ba ta yi armashi ba.
“Ki tallafe ni ma Sadiya ta.”
Ya faɗa cikin karyewan sauti a yanayin shi kaɗai da na kalla na san tallafan yake so.
“Me zan maka? Yara na falo fa?
Ƙamƙameni ya yi yana faɗin” Na kulle ɗakin ba za su shigo ba “
Ganin ina kallon shi ya sa kamar zai yi kuka ya marairaice mini yana faɗin” Don Allah I need you sosai.”
Sai na kasa musa massa ya ja na ya yi zuwa kan gado yana mai ƙamkame hannuwana. Duk yadda na so na basar da shi na kasa Yusuf ne fa? Yusuf ɗin da na sani tun yana matashin sa. Sai kawai nima na tallabe shi, na saki jiki na ba shi abin da yake so.
Bayam mun natsa tun kafin mu kai ga wanka ina saman ƙirjinsa ya rumgumeni yana faɗin” Ki yi haƙurin kin ji ko? Ke mai hakuri ce ki ƙara akan na baya. Mimisco ta kira ni , Suwaiba ma duk sun sake yi mini bayani na gamsu. Itama Daughter zan yi mata faɗa kowa ya yi hakuri domin a zauna lafiya kin ji”
Na yi kamar ban ji ba sai da ya ƙara faɗn” Kin ji ko?
“Na ji.”
“Ba ki yafe mini ba ko?
“Uhm”
Sai ya sumbaci goshina kafin ya ce.
” Ina kaunar ki.”
“Ina sonka Yusuf ɗina.”
Na faɗa ina sake rumgumoshi kamar na saka shi a aljanma haka ya ƙamƙameni yana faɗin
“Na gode Abar ƙaunata Ubangiji ya bar mu tare har mutuwa. Mutuwan ma ta ɗauke mu rana ɗaya”
Ina mirmishi na amsa da Amin.
Mun so mu shagala sai muka ji kukan Yumna a kofar ɗaki tana kiran sunana.
Uma
“Uma.
Ni da Yallaɓai muka kalli juna muka kwashe da dariyan nishaɗi.