Turken Gida – Chapter Forty-five
by JanaftyGanin hankula sun kwanta ya sa ranar wata laraba Yallaɓai na gidana muna falon shi bayan mun gama ƙaryawa. Yumna na hannun shi yana yi mata wasa tana ta bangala masa dariyan su na yara.
“Yallaɓai.”
“Uhm”
Ya amsa mini hankalin shi na wajen Yumna ɗaga ta sama yake yi yana cillata tana dariya. Yallaɓai ba ya ba ni mamaki in dai akan yara ne, haka yake zai iya ɓata lokacin sa mai tsawo shi da yaran shi ba shi da wannan damuwan in dai yana gidan to Yumna na hannun shi su yi ta kara kaina a kanta shi da Baby.
“Ya maganar koya mini mota? Kyan dai alƙwari cikawa. Yanzu na haihu ba ni da ciki”
Na faɗa ina kallon shi ina daga kujera mai zaman mutum ɗaya shi kuma yana zaune a saman mai zaman mutum uku ne shi da Yumna.
Kallona ya yi kafin ya ce” Ko ba ki da ciki ai kina da goyo ko?
“Goyo kuma? Yumna ce za ta hana ni koyon mota Yallaɓai?
Na faɗa ina cikin mamakin sa, har ina ɗan haɗe rai domin sai na ga kamar ba ya so kwata kwata ya koya mini motar nan to bai isa ba in ba zai koya mini ba ya ba ni dama na yi ma Musbahu ko Adnan magana su koya mini.
“Ki bari ta ƙara wayau zuwa ki yaye ta mana. Amma ai yanzu ba ki da natsuwar koyon tuki ko Yumna?
Ya faɗa yana kallonta sannan ya nuno mata ni yana faɗin”ki yi ma Umman ki bore wai za ta koyi tuki ba ki yi wayau ba! Ki ce baki yarda ba.”
Kamar tana ji sai ko ta fara wuntsila kafafunta tana wani abu irin na su na jarirai da suke cikin wattanin haihuwa ba su shekara ba.
“Yauwa. Yumna ma ta ce ba ta amince ba sai ta girma.”
“Tabɗijam! Ai lokacin ma na ƙware a tuki har Zaria ma ina tuƙa kaina in sha Allahu.”
Na faɗa cikin gatse har ina mele baki. Kallona ya yi ganin na haɗe rai ne ya sa ya fara ma yar da maganar wasa da dariya.
“Har garuruwa ma za ki riƙa zuwa kenan a motar kan ki?
“Ƙwarai da gaske. In sha Allahu.”
“To Allah Ya tabbatar. “
Ya faɗa yana yi mini dariya sai na shaka ina hura hanci na sake kallon shi ina faɗin” Za ka cika alƙwari ne ko kuwa ka ba ni izinin na nemo wanda zai koya mini a mutumce?
“Au ni kenan ba a mutumce zan koya miki ba kenan?
“Ni dai ban ce ba”
“Kin ce mana.”
Ya faɗa yana mai tsare ni da ido.
“To na ga sai kokarin yi mini wulaƙanci kake yi da na yi maka zencen koyon mota.”
Sai ya yi murmishi kafin ya ta so daga in da yake zaune ya zo kusa da ni ya zauna Yunma kuma ya ɗora mini ita a saman cinyata shi kuma sai ya saka hannunsa na dama ya sagalo kafaɗata.
“Uhm to mene kuma na fushi? Ni na isa na ce ba zan yi miki abin da kike so ba?
Ina tura baki na ce” To gashi sai againsing ɗin maganar kake yi duk lokacin da na ta da maganar.”
“Ni har na isa? Ke ba ki san wasa ba ne. Ko shike nan ni ba zan yi wasa da matata ba?
Ya faɗa ya na jan kumatuna. Gyara ma Yumna zama na yi a kan cinyata lokaci ɗaya ina fadin” To yaushe za mu fara?
“Mu bari weekend ko?
“Allah Ya kaimu da rai da lafiya.”
Na amsa ina masa mirmishi.
Shima martanin mirmishi ya mayar mini, sannan ya ɗan ramƙwafa ya sumbaci ƙuncina lokaci ɗaya ya miƙe yana faɗin” Tukwaici me zan samu?
Ina dariya na ce” Me kake so?
“Abin daɗi mana.”
Ya faɗa yana kashe mini ido ɗaya na san manufar shi ya sa na miƙe ina saɓa Yumna a saman kafaɗata lokaci ɗaya ina faɗin”To ka bari anjuma zan yi maka kyakyawan Tanadi”
“Uhm ni yanzu na ke so.”
“Yanzu kuma?
Na faɗa cikin mamaki sabo da ko yau da asuba bai bar ni na huta ba. Amma wai yanzu ya na ƙoƙarin komawa ruwa. Matsowa ya yi kusa da ni ya rumgumo ƙuguna ya na faɗin” Muje ki ba ni, ina son na fita ne yau ina da baƙin da zan gani da ƙarfe sha ɗaya na safe.”
“To ka je mana. In ka dawo ai abin daɗin ba zai gudu ba”
Ƙirjina ya taɓa har yana ɗan matsaawa har sai da na kalle shi, lumshe ido ya yi sannan ya buɗe yana yi mini wani kallon ƙasa ƙasa.
“Wai ba ka gajiya ne Yallaɓai?
Har ya na wani miƙa yana ta da power hannun shi kafin ya ce” Gajiya? Taɓ ni ai yanzu na ke jin kaina ma.”
Taɓe baki na yi bai ƙyale ni ba sai turani gaba da ya hau yi da hannayensa a saman kafaɗuna. Bai kuma ƙyaleni ba sai da ya sake ɓaro mana wani ɓarnan ruwa sai bayan mun gama ne ya yi wanka da zai fita har yana faɗa mini saura na anjuma in ya dawo. > Janaftybaby: “Wani anjuman? Malam tuƙwaicin har guda nawa ne?
Da hannushi ya ƙirga mini guda uku, hararan shi na yi kafin na ce” Kai dai Yallaɓai sam yanzu ba ka yi mini abu don Allah sai ka dawo ka fanshe ko?
Maganata ta saka shi dariya har yana ƙyaƙyatawa.
“Na ji ba komai. Duk cikin cika sunnar ma’aiki ne(SAW)”
Ni da Yunma muna haraba mun rakosa ya karɓeta ya yi mata wasa ya sumbaceta sannan ya miko mini ita bayan ya haɗamu duka ya rumgume.
“Ki kular mini da kan ki Abar ƙaunata.”
Ya faɗa yana kai mini sumba a gefen bakina.
Nima na mayar masa da martani kafin na ce.
“A dawo lafiya Allah Ya ba da sa’a.”
“Amin My Sady.”
Muna tsaye ya shiga mota ya ta da. Daman ya buɗe get ya fita sannan ya dawo ya rufe get ɗin duk muna tsaye ina ɗaga masa hannu shima yana ɗaga mini sai da na ji ƙara tashin motarsa sannan na koma cikin gida ni da Yumna.
Haka ko aka yi weekend na shiga Yallaɓai ya ce na shirya. Ranar farko ba da Yunma muka je ba wajen Baby na bar ta. jidda ba ta nan ta ta fi Tahfezz suna ta ƙoƙarin haɗa haddarsu ne gabaɗaya ba ta samun zama sosai. Ranar farko haka na yi ta rawan jiki da na hannu ban yi wani abun arziƙi ba da ya ke wani fili ne can gabanmu Yallaɓai ke koya mini anan, haka rana ta biyu tare da Yumna tun da Baby ta je Hadda itama Yallabai ke rike da ita ni kuma yana nuna mini yadda ake fara kunna mota da sauran su sai na yi kamar na gane in ya sakar mini sai na yi shirme kuma motar Auto ce shi ya sa za ta yi mini wahala amma ya ce wani sati zai saka Salisu ya kawo ta hannun shi tun da ita Munual ce za ta fi mini saukin koya.
A satin dai haka muka gama ban gane komai ba Yallaɓai na ta yi mini dariya amma daga baya da ya ga na damu sai ya bar dariyan ya koma ya na lallashina da ban baki. Ni har cewa na yi an ya ina da rabon tuka motar kaina kuwa! Tun da gashi nan ma motar ta gagare ni iyawa. Shi kuma yana lallashina da cewa zan iya in sha Allahu. To satin na biyu motar hannun Salisu ya karba ita dai kan an ga sauyi tun da ranar lahadi har ya sakar mini sitiyari amma fa da na fara tafiya sai na ruɗe na kasa yin kwana na saki kan mota Allah ya sa Yallaɓai na gefe riƙe da Yumna ya yi saurin rike kan motar da na halakamu, duk na ruɗe sai da kuma koma gida ya yi mini faɗan na daina ruɗewa na riƙa natsuwa ne in ba haka ba zan daɗe ban koyi abin da ke da sauƙi ba, kuma ya fahimci ina da tsoro to na fara cire wannan tsoron in ba haka ba, to ba zan iya ba.
Haka dai haka dai duk sati muna ta lallaɓawa kuma cikin ikon Allah na fara iya mota. Yallaɓai na sakar mini har na dawo damu gida ma. Ina ta murna da farimciki na iya mota na faɗa ma su Jidda suna ta mini ihun murna suma kar da Baby ta ji labari yan gidanmu kuma na ce mamaki zan ba su sai na yi mota na tuka kaina zuwa gidajen su su sha kallo. Sama da wata biyu Yallaɓai na koya mini mota kuma Alhamdulillah hannuna ya faɗa soaai fiye ma da tunanin shi tun da har cikin gari muna shiga na tuƙa mu, kuma na mayar da mu gida. Sannan har motarsa ma ina iya tukata yanzu lafiya lau.
Ranar wata lahadi ni kaɗai na fito, tun da motar yara saboda ina amfani da ita ya sa tun ranar Jumma’a in Salisu ya ɗauko su daga makaranta sai ya ba ni key sai kuma Monday zai dawo ya karɓa. To in dai Yallaɓai ba gidana yake ba kafin ya ƙariso in na gama ayyuka gida zan ɗauko Yumna mu fita a motar ina ɗan zagaya anguwa daga can sama zuwa kasa saboda dai hannuna ya ƙarawa faɗawa. To ranar ma ni kaɗai na fita kuma a gida na bar wayata sai da ina kan hanyar dawowa na haɗu da Yallaɓai a kasa yana tahowa lokaci ɗaya yana waya sai magana yake yi yana ɗaga hannu bai ma ganni ba ni ce na hango shi yana sanye da jallabiya da dogon baƙin wando. Jallabiyan mai kalan ruwan kasa ne har da wata hula ya saka rabin kai na rasa a ina Yallaɓai ya samo wannan hulan tun kwanakin nan na ga yana saka ta lokaci bayan lokaci. > Janaftybaby: Daga nesa na ke kallon shi, tun da na ɗan rage gudu. Yumna na kalla daga kwance a kan kujeran mai zaman banza. Sai na yi mirmishi kafin na ce” Yunma ga baban ki can”
Na faɗa ina mai ƙara kallon shi ta cikin gilashin mota tumbin da ya fara tarawa yake shafawa ya na faman magana a waya lura da yi bai ganni ba, kuma ni ya fito nema tun da ya je gidan ba na nan ya san na fito ne.
Hon na yi masa lokacin da na kawo kusa da shi, sai da ya juyo sannan na ɗaga masa hannu ina dariya. Sai ya rike baki yana kallona kafin ya yanke wayar. Tsaya wa na yi lokaci ɗaya ina sauke gilashin gefen da Yumna ke kwance.
“Hy ɗan saurayi ji mana “
Na faɗa ina kashe masa ido ɗaya. Sanye na ke da wando baki plazo da riga ƙarama amma na saka after dress a saman kayana na saka brieziya hijab na Baby ne ma na maƙalashi da zan fito. Yumna ma ta sha gayu abin ta sai tashin ƙamshi take yi.
“Eye Yan matana irin wannan cakarewa haka?
Ya faɗa yana yi mini mirmishi, lokaci ɗaya yana rike hannuwan Yumna itama ta rike shi gam ganin shi ya sa har ta fara wuntsila kafa tana masa gaurancin su na yara. Wai ita nan ta san me yi mata wasa haka take yi musu ita da Baby ta riga ta gane su in dai wajen yi mata wasa ne.
“Ya son ranka Ɗan saurayi.”
“Raina fesa. Da kyau Hajiya ta.”
Ya faɗa yana nuna mini babban yatsa alamun jinjina.
“Shigo na rage maka hanya.”
Na faɗa ina masa dariya shima yana ta ya ni, buɗe masa motar na yi shi kuma ya shigo bayan ya ɗauki Yunma a saman jikinsa sai da muka fara tafiya na ji yana yi ma Yunma cakulckuli tana ta dariyan su na ihu irin na yara sannan na kalle shi ina faɗin” Yunma har ta gane ka kai da Baby in dai wajen wasa ne, in ba kwa kusa ta yi mini zillo tana son wasa ni ko na ce ba zan iya ba yarinya ki ji babanki ya zo.”
Yana dariya ya ce” Me ya sa ba za ki yi mata wasa ba?
“Ban iya ba”
“Kin iya. Ke dai ba ki san yi mata ne, Yumna Umman ki ta iya wasa ba ta son yi miki ne kawai saboda haka kisan zaman da za ki yi da ita yauwa.”
Kamar ta na jin sa ta yi zuru tana kallon shi, ni da shi muka kwashe da dariya ganin yadda ta wani yi nakwa nakwa da fuska kamar za ta yi kuka.
“Kar ka haɗa ni da uwata.”
“To ki riƙa yi mata wasa. Irin wannan”
Ya faɗa yana shilla ta sama ya kuma caɓeta sai ga ta, tana bangala masa dariya.
“Aikin kenan daman shi ya sa in ta ganka ta yi ta zillo duk ka koya mata mugun wasa Yallaɓai.”
“Dai dai kenan ma”
Muna tafe muna taɓa hira, ta kofar gida muka wuce mun kai farkon layi na sake kwana muka dawo sai a lokacin na lura ban ga motarsa ba.
“Ka shiga da motar ka cikin gida ne?
“A’a ba da ita na zo ba. Tun jiya tana gareji bakin mai ke zuba sai na kai ta aduba mini. Adaidaita na hayo.”
Sai na gyaɗa kaina ban yi magana ba muna tafe sai ya kalleni kafin ya ce” Ehe Madam hannu fa ya faɗa.”
Ina masa fari da ido na ce” To ya ka gani?
“Lafiya lau. Yanzu kam ba in da ba za iya tukamu ba.”
“To Alhamdulillah saura motar kaina in sha Allahu.”
“Akwai kuɗin siyan motan ne har yanzu?
Ya faɗa yana yi mini dariya ban ba shi amsa ba sai da muka isa gindin wata bishiya na yi parking na kashe motar sannan na kalle shi ina faɗin” Babu kam. Duk na ruguza jarina. Ina tunanin na riƙe wannan ko kai yara makaranta ne sai na rika kai su ina zuwa ina dawowa da su, tun da ina gida ba abin da na ke yi.”
Bai yi magana ba amma dai ya kalleni, sai kuma ya ma yar da hankalin shi kan yi ma Yumna wasa.
“Ko Yallaɓai? Kafin na samu kudin siyan motar ko?
“A’a ba zai a yi haka ba”
“Me ya sa to?
Na tare shi ina mai kallon shi, sai ya dawo da hankalin shi kaina lokaci ɗaya yana faɗin” Saboda tuntuni motar nan tana hannun Salisu kuma kin ga ya tambayi izini tun a shekarun baya ya na ɗan haya da ita nan ƙauyakun kusa damu yana ɗan samun na cefane kawai sai rana tsaka na ce zan karɓa motata kin ga hakan ya dace?
Sai na yi shuru ina kallon shi ban yi magana ba amma dai gaskiya ya faɗa bai kyautu a karɓa ba. > Janaftybaby: “Shi ya sa ba zan karɓa ba. Kuma kin ga ya daɗe yana aiki tare da ni tun mashin ɗin sa har ya zo ya rasa mashin ɗin bayan na sauya mota sai na bar mishi wannan a hannun shi ba saboda kai su Jidda makaranta ba ne, saboda shima ya taimaki kan shi ne kin ga ne?
Sai na gyaɗa masa kai kafin na ce” Haka ne.”
“To kin gani. Ki kwantar da hankalin ki in sha Allahu abubuwa suna ƙara warware mini zan siya miki mota in sha Allahu.”
Kallon sa na ke yi domin ni na san alƙwarin Yallaɓai haka ya yi mini na buɗe shago har yau bai iya cika alƙawarin da ya ɗaukar mini ba.
“Kin yi shuru?
Sai na sauke ajiyar zuciya kafin na ce” Uhm Allah Ya sa.”
“Amin ko ba ki yarda da abin da na ce ba ne? Wallahi zan siya miki ba ni na ce ba.”
Ƙureni da ido ya yi ganin ina kallon shi ban ce komai ba.
“Ki yi mini magana mana ba na son wannan shurun fa”
“Yallaɓai ni dai ka daina yi mini alƙwari in dai ka san ba za ka iya cika mini ba”
Sai ya zura mini ido kawai bai yi magana ba.
“Ka daina lasa mini zuma a baki kuma ka tafi da sauran zumarka ban ƙara ganin ta.”
“Wani alƙawari na yi miki ban cika ba Sadiya?
Ya faɗa a muryansa a natse ba maaganar wasa nima ko na gyara zama ina faɗin” Suna da yawa amma babban ciki ne na buɗe mini shagon Saloon. Ka samu damarmar maki da yawa a baya Yallaɓai amma ba ka cika mini alƙawarin da ka yi mini ba, duk da ba kyauta za ka buɗe mini ba da kuɗaɗena a hannunka amma abu ya gagara ko da yaushe sai dai ka ce kai ka yi alƙawari za ka buɗe mini amma shuru. Duba fa ka gani Gimbiya a bayana ta zo gashi yanzu har ta buɗe shago business ɗin ta na ta bunƙasa amma ni sai dai ka yi ta lasa mini zuma a baki. Ba domin na ɗan kama ma businness ɗin hijaban nan ba da har yau ina nan ina zaman jiran warrabuka.”
Na gama faɗa a tsume, ban so na yi magana ba amma yau ne ya kai ni bango. Na gaji sai ya zauna ya yi ta cewa zai yi mini kaza zai yi mini kaza amma ya kusa cika alƙwari ko ɗaya da ya yi mini sai maganaa a fatar baki.
Shuru ya yi ya kasa mgana har yana dukar dakai.
“Ka yi haƙuri ban so na yi maganar nan ba. Ta kama ne.”
“Kallon maƙaryaci ashe kike yi mini Sadiya ban sani ba?
Ya faɗa yana mai kallona.
“Ni dai ban ce ba.”
“Haka ne mana. Kina mini kallon makaryaci sannan mara adalci ke ban buɗe miki shago ba amma na je na buɗe ma Daughter ko?
“Ni fa ba haka na ke nufi ba.”
“Haka ne mana. Ga shi kin faɗa mini da ba ki fara ma sana’ar sai da hibajai ba da har yanzu kina nan kina zaman jiran warrabuka ko?
Ko ba haka kika ce ba?
Shuru kawai na yi ganin yana neman sauya mini mgana ta.
“Muje gida sai mu yi maganar a can”
Na faɗa ina kokarin ta da motar tsawa ya daka mini sai da Yumna ta firgirta ta fashe da kuka.
“Ba in da za mu je, anan kika fara ta kuma anan za mu ƙarƙare ta.”
Ya faɗa da karfi har ya na buga kujeran mota ni gani na yi ma yana neman sakar mini da yarinya da ya sa da sauri na saka hannu na karɓeta ina rumgumeta ganin ta firgita tana ta kuka.
Rigata na ɗaga ina zaro mata Mama saboda in ba shi na ba ta ba, ba za ta daina kuka ba.
Ina ba ta Nono Yallaɓai ya ta sani a cikin motar nan yana ta yi mini masifa saboda ba ya son gaskiya. Eh mana rashin gaskiya in ba haka ba ai bai cika alƙawarin ba. Kawai yana kunfar baki ba shi da abin faɗa ko da zai kare kan shi da shi.
“Ni kike yi ma kallon maƙaryaci sannan macuci tun da kin ce abu ba kyauta ba tun da na cinye kuɗin ki kuma ban buɗe miki shago ba.”
“Ni fa ban ce ka cinye mini kuɗi ba Yallabai ka tsaya ka fahimci maganar nan don Allah”
“Me zan fahimta! Bayan wanda na gama fahimta. Wato ke dai yanzu ma kina tunanin na zalunce na cinye miki kuɗi ban cika miki alƙawari ba ko?
Ya faɗa yana mai tsareni da ido.
“Haba mana Yallaɓai.”
“Haba ko gaskiya”
Ya faɗa a fusace ni kawai sai na yi masa shuru ganin ya harzuƙa.
“To na gode ban taɓa tunanin irin kallon da kike yi mini ba kenan amma yanzu tun da kin furta mini kuma na ji zan yi lamarin tufkan hanci. Ki faɗa mini nawa ne kuɗin ki da kike tunanin na cinye, zan biya ki kuma ba na son ki yafe mini ko naira biyar a ciki in kuma kika yafe mini to ni wallahi ban yafe miki ba”
“Yallaɓai.” > Janaftybaby: Na faɗa ina buɗe baki cikin mamakin kalaman shi. Daga magana sai ciɓi ya zama ƙari duk tsawon wannan shekarun da ban taɓa masa magana duk bai ga hallacin da na yi masa sai yau ne zai ce ni ce butulu saboda kawai na faɗa masa gaskiya.
“Kuma maganar buɗe shago kuma ni na yi niyya alƙawari ne kuma zan cika in sha Allahu. Na yi kuma ranstuwa da Wallahi tallahi zan buɗe miki shagon Saloon na muka mallaka miki shi halak malak in sha Allahu Sadiya.”
Sai kawai na gyaɗa kai ban ce komai ba, na mai da kaina da hankalina wajen ba ma Yumna, saboda na fahimci ko magana na sake yi ba zai taɓa fahimta ta ba.
“Nawa ne duka kudin ki da ke hannuna?
Ko kallon shi ban yi ba saboda haushi.
“Ki rubuta ki tura mini cikin satin nan zan tura miki kuɗin ki ba na so ki sake yi mini kallon wanda bai yi miki adalci ba.”
Tsaki na so na ja masa sai na fasa ni na ɗauka ma zai ce ne yau yau ɗin nan zai tura mini kudin ganin yadda ya yi zuciya.
“Sai maganar Daughter kin ce wai ita da ta zo a bayan ki ga ta nan na buɗe mata shago businness ɗin ta na ta haɓbaka. To ina so na faɗa miki ko na ce tunasarwa ce tun da kin sani sai dai in kin runtse ido ne saboda wata munufarki, ko da na auri Daughter da kuɗin ta na ganta mijinta ya mutu ya bar mata gado. Da kuɗin ta da buɗe shago, ni dai na taimaka mata wajen neman shago da sauran su amma wallahi tallahi ba sisi na a cikin kasuwamcin ta ban rantse miki domin ina jin tsoron ki ba sai domin na fita daga zargin da kike yi mini na rashin adalci.”
Ban san tsakin da na ke riƙewa ya fito ba sai da na ga ya kalleni cikin mamaki kafin ya ce” Ni kike yi ma Tsaki Sadiya? Ni Yusuf?
Da zan ce ya yi haƙuri sai na fasa na yi masa banza. Na gama ba ma Yunma Nono na rufe rigata na ɗora ta a saman jikina na ja key zan ta da mota Yallaɓai ya make mini hannu yana yi mini ihu a saman kaina.
“Ni kike yiwa Tsaki Sadiya? Rashin kunya za ki yi mini?
Sai kawai na koma na jingina da kujeran mota ina sauke numfashi, sai tsorata mini yarinya yake yi da ihun shi.
“Na gode kin ji ko? Tun kina yarinyarki ba ki yi mini rashin kunya sai yanzu da girma ya kama ki ko Sadiya?
Ya faɗa har ya na nuna ni sai ma ya ba ni dariya har sai da na ɗan dara shi kuma sai ya jijjiga kansa kawai bai ƙara maagana ba sai ma ficewarsa da ya yi a motar ban kira shi ba na ta da mota na zo na wuce sa, na koma gida ina ta jiran shi duk da wata zuciyar na faɗa mini ba zai dawo ba tun da ya yi fushi haka ko aka yi bai shigo gidan ba daga can ya yi gaba da man a gidan Gimbiya yake, sai washegari ne zai dawo gidana kuma har sai washegarin da dare na gan shi, haka ya shigo mini gida a daƙune ina gaishe shi da kyar ya amsa kamar na faɗa masa cuta.
Daga shi sai yaran shi ya riƙa mgana. Shi da Jidda sun kai har wajen sha biyun dare yana mata solving Quention paper na Neco wancan shekaran. Tun da sun kusa gama WEAC bai wuce paper biyu su gama ba za su fara Neco kafin babban salla shi ya sa ba ta samun natsuwa ko da yaushe cikin karatu suke yi. Ni dai ganin ba a yi da ni ya sa na kama kaina na ja jikina ni da Yumna muka shiga ciki muka kwanta sai cikin dare da na farka ne na gan shi rumgume da Yumna ni uwar Yumna tun da ana fushi da ni, ni kaina kamar jikina ya sani duk mugun barci yau ban ganganra jikinsa ba. Da safe ma haka ya yi mini wani nuku nuku da fuska ni dai ina ganin ikon Allah har ya koma gidan Gimbiya ba ma yar daɗi da shi, da farko na so na biye masa a yi zaman doya da manjan sai daga baya na zauna na yi tunanin ban kyauta ko domin tsakin da na yi masa shi zai fi tsaya masa a rai. Shi ya sa ranar da zai dawo gidana na ci kwalliya saboda ina son sulhu.
Ba ƙaramin kai zuciyata nesa na yi ba ina bashi haƙuri yana yi mini cin mgani. Kallona ya yi kafin ya ce” Uhm ni yau na ke magana Sadiya ki kalle ni ki yi mini tsaki? Haka na lalace daman a idanuwan ki?
“Ka yi haƙuri tsakin ya suɓuce mini ne.” > Janaftybaby: Duk da haƙurin da na yi ta bashi bai saka ya hakura duka ba amma dai ya ɗan sassauta tun da har a daran ma ya neme ni mun yi ɓarnan ruwan da safe kuka ya tashi ya na sake yi mini cin magani ni dai na ce ai na ga ta kaina. Bai saki ba sai da ya fi sati yana yi mini isa isa daga ƙarshe dai ya haƙura don kan shi ya sauko amma ko yaya abin ya faɗo masa a rai sai ya yi ƙyafci a cewarsa ba abin da ya kai tsaki reni. Ya tsani ko wanda ya girme shi ne ya yi masa tsaƙi ballanta ni da nake ƙarƙashinsa ni dai nawa cewar ai ban haƙuri ne, ya dawo yana yi mini burga na yi lissafin kuɗina ya biya ni na yi banza da shi, daman can jin ta baki ne muna shiryawa sai shuru kuma bai ƙara ta da maganar ba. Shike nan na samu faɗan mu ya wuce sannan maganar biyan bashi dai ya sha ruwa daga lokacin da man can ba biya na zai yi ba, barazana ne kawai.
Sallar babban salla ne ke ta matsowa muna ta shiri. Daman da sallar ne muke haɗuwa gabaɗayanmu a gida wannan ma salla hakan ce ta faru an hadu gabaɗaya an yi hiran zuumci an yi wasa an yi dariya an yi faɗa an kuma shirya. In ka ganni ni da Ma’u ba za ka taɓa cewa mun taɓa samun matsala ba a baya. Ma’u ta na faɗa mini Amarya da Hajiya Zainab sun haɗa mata kai, na ce ta yi haƙuri duk ta kau da kai haɗuwa in ba ta Allah ba ce tana zaune za ta ji kan su. Duk da ta fara kwantar da hankalinta amma har yanzu Ma’u ba ta mai da jikinta ba, sannan Alhajin ya daina rawan jikin da ya ke yi a kanta a da duk in da Ma’u za ta je in bai kai ta direba zai kaita amma yanzi har ta saba yawo a cikin adaidaita. Ni da na ga ta yi fari ma na ɗauka tana da ciki ne sai da na tambayeta ta rantse mini ba ta da ciki a lokacin ma jini take yi. Marwan Ya Aina ce cikinta har ya fito ita ke gaba sai Rahila ta kunsa ƙarami.
Sai a Gwammaja muka haɗu da Gimbiya rabo na da ita tun wani zuwa da na yi gai da Nene bayan sunan Yunma muka haɗu sai da salla kuma muka sake haɗuwa. Ta yi fari ta ƙara zama wata katuwa ni dai sai na ga kamar ciki gare ta ban dai furta ma kowa ba. Da man ai ta yaye Anwar yana yawon shi ko’ina suna ganina da ga shi har Khalipa suka rumgumeni suna kiran Umma daman haka Khalipa ke kirana saboda ya ji a bakin su Jidda. Shi ya sa sai Anwar shima ya kama sunan. Nan muka yini gabaɗaya ni ban bi ta kanta ba tun bayan da muka gaisa muna ɗakin Maman farko ni da su Munnira muna ta hiran mu sai dare Yallaɓai ya zo ya ɗauke mu daman gidanta yake, mu aka fara saukewa sannan suka yi mana sai da safe suka wuce gidan su.
Nun yi babbar salla a watan june ne. Lokacin Yunma na cikin watan ta na bakwai ne har ta fara wayau tun yaushe har ina koya mata zama. Tana wayau tana ƙara zama burtuka yanzu Baby da nishi take iya ɗaukanta. Jidda tuni har sun fara Neco Baby ce kawai ke zuwa makaranta kullun ita in ba su da paper tana gida. Ta ɗauke mini komai ita ke aikin gida gabaɗaya ni sai dai kawai na ci na kwanta, Yallaɓai ya yi ta mini tsiya wai daman abin da na ke so kenan na ce to sai dai ya yi haƙuri tun da raina ya kai kuma na haifa.
Ni bai faɗa mini Gimbiya na da ciki ba amma tun ganin da na yi mata da salla na zargi haka. Sai da Jamila ta shigo anguwar mu wani gaisuwa gidan abokin mijinta ta shigo gidana ta ke faɗa mini ashe kuma Gimbiya ciki gareta? Na ce ban sani ba wallahi.
“Tab ciki ko gashi nan har ya fito ba ki gan shi a jikinta da salla ba ne da kuka haɗu?
“Ban lura ba”
Na faɗa ba tare da na sake yin wata magana.
“Ai ko ciki gare ta. Da Suwaiba ta yi magana ta ce ba an ce likita ya ce ta huta ba Anty Bahijja ta ce likita ai ba Allah ba ne. Lafiyan ta ƙalau kuma za ta iya haihuwa da kanta gwara ta yi ta haihuwa tun da Mijinta mai son ƴaƴa ne”
“Ba shakka”
Na faɗa ina jinjina kai, na rasa me zan ce ma. Ita dai Gimbiya haihuwa ce a gabanta ita a dole sai ta fini yawan ƴaƴa a raina na ce ta yi ta haihuwa ko duniya za ta haifa ba ta gaba na. Na tuna ko bayan haihuwan Anwar ni da Yallaɓai mun yi magana ya ce za ta yi planning ko na shekara biyu saboda dokar likita ban sani ba ko ba su yi tsarin iyalin ba ne. > Janaftybaby: Shuru na yi da bakina na yi kamar ban ji ba ko Yallaɓan da bai faɗa mini ba nima ban nuna masa na ji ba, kowa kuma ban yi maganar da shi hatta ko da su Munnira. Sai ma Hauwa ce ta kira ni a waya ta na faɗa mini a Rano ta ji labarin Gimbiya na da ciki na ce mata e da gaske ne.
“Ba likita ya ce ta huta ba?
“Ba ta son hutun ne Hauwa. Ki barta ta yi haihuwanta.”
“Allah ya sauwake.”
Haka muka rufe maganar muka shiga wata, mun ɗan jima muna magana kafim mu yi sallama Munnira ma da ta ji ba ta yi mini maagana ba sai da na je gidanta ranar daga asibiti na kai Yumna tana da fama da ciwon ciki, shi ne muke maganar da ita.
“Ai kishiyar nan taki munasura ce Sadiya. Ta ce ita haihuwa yanzu ta fara a gidan Tafida ba ta ma yi komai ba tukunna.”
“Allah haka ta ce?
Munnira ta ce”Haka ta ce, ta ke faɗa a gidan su nima Hauwa ce ke faɗa mini da ta je gidan su ta ji maganar.”
“To Allah ya ba ta masu albarka”
“Addu’a za ki yi mata?
“To zan ce ne kar Allah Ya ba ta masu albarka ne Munnira? Allah ya ba ta masu albarka ko ba komai ai ai ƴa’ƴan Yallaɓai ne. Kuma duk saurin ta sai dai a kira su ƙannen su Jidda ba dai yayyen su ba”
“Wannan gaskiya ne.”
“To kin gani. Ku bar ta lokaci ne wata rana sai labari.”
Har na baro gidan Munnira ba mu ƙara ma ta da hiran Gimbiya ba, ni ma da na dawo na cire abin a raina na watsar nima na gode ma Ubangiji tun da har ya ba ni biyu ya kuma ƙara mini a lokacin da na cire tsammani, ita takamar tana da ya’ya maza ita ce ta haihu ni tun da mata ne yarana ban haihu ba ko alama ba ta gabana harkan rayuwata kawai na ke yi. Kuma yadda shima ya yi shuru bai taɓa mini maganar nima ban yi masa ba sai ranar da ya ke gidanta har dare bai zo ya duba mu kamar yadda ya saba sai a washegari da safe ya zo yana faɗa mini a jiyan Gimbiya ce ba lafiya a asibiti suka yini, amma an sallamota tana gida in na samu lokaci na shirya mu je ni da yara mu duba ta a gida.
Kamar zan je sai mun samu lokacin sabo da ban manta wulaƙancin da ta yi mini da cikin Yumna ba ni ko ba zan ƙara rawan jiki a kanta ba. Na ce masa za mu je ranar da su Jidda ke gida na masa Allah ya ƙara lafiya amma ko gaisheta ban ce ya yi ba. Kwana biyu tsakani ranar lahadi Jidda na gida ta je Hadda ba ta dafe ba ta dawo tun da sun gama haɗa Qur’anin su suna bita ne kafin a yi musu waliman sauka. Daman a gidan ya kwana yana ganin su dukkansu a gida sai ya ce mu shirya mu je mu duba ta daman na kudira a raina ba zan je ba. Sai kawai na nemi waje na kwanta na ce ba na jin dadi wai to bari a fasa sai gobe in na samu sauƙi.
“A’a ku tafi kawai ku gaishe ta.”
Na faɗa ina daga kwance a saman gado
Sai ya ce to bari su tafi amma har da Yunma Baby ta ɗauka suka tafi, tun bayan la’asar sai dare suka dawo sai ga su da yara niki niki Anwar da Khalepa da kayan su, sannan ba su dawo da Jidda ba wai tana can za ta kwana saboda Gimbiyar ita kadai ce yaran ma tace a kawo mini su sun dame ta da hayaniya ga shi ba ta da lafiya.
“Topha. Ai nima ba ni da lafiyan kuma daman Jidda ce ƙarfin aikin gidan yanzu.”
Na faɗa a tsume bayan duk ya gama rattabo mini bayaninsa. Wato ga jaka dole ta ce a kawo mini yara.
“Ga Baby za ta taimaka miki da wani abun. Ita ma Jidda zuwa jibi za ta dawo tun da ranar laraba suna da jarabawa.”
Takaici ma ya hana ni mgana, tun da yaran nan suka zo hutu na ya ƙare tun da Jidda ba ta nan dole na ke tashi da safe na yi musu shirin makaranta. Har Anwar da ke ɗan shekara biyu an saka shi makaranta ajin yara ban sani ba da man a can uwar su ke kai su yanzu kuma tun da suna gidana Salisu ne.
Ko Yallaɓai in bai fita da wuri ba, sai da Jidda ta kwana uku ta dawo da na ke tambayanta Antyn ta su a kwance take?
Sai ta ce mini.
“Wani kwance Umma? Ta ji sauki fa ta yi ta chart da waye wayenta abinci ne ma in ta ci wani lokacin ta ke Amai.”
Jinjina kai kawai na yi, a raina na ce ban ga laifinta ba wanda ya samu rana ga igiya ai sai ya yi ta shanya. Yallabai ne ya ɗaure mata gindin yara kuma na yi magana ya ga ɓakina. > Janaftybaby: Amma me ya sa bai kai su gidan Naja ko Anty Bahijja ba? Sai ni ko wacce suka raina to ai ya yi kyau ni kaɗai ranar na rika masifa a cikin gida kuma har lokacin bai faɗa mini ciki gare ta ba, nima ban tambaya ba sai ranar da ya ke gidana har mun yi shirun kwanciya ya fita ɗakin yara sai ga shi ni kuma ina kwance ina ba ma Yumna Nono ta farka ta fara mini jananun kuka.
“Meke damun Gimbiya ne haka da take ta rashin lafiya?
Da gayya na yi masa tambayan ya na sauya kayan jikinsa zuwa na barci yake amsa mini.
“Laulayi ne.”
“Laulayi?
Na maimaita cikin sigan tambaya.
“E ciki gare ta. Ba ki sani ba?
Sai da na balla masa wata uwar harara kafin na ce” Na sani mana tun da ka sanar da ni.”
Sai ya yi dariya lokaci ɗaya yana hayo gadom har kusa da ni, hannunsa ya sa ya ɗan shafa fuskar Yumna zuwa jikinta.
“Kar ka ja ta da wasan ka. Ka ja mana tsayuwar daren dole.”
.
Dariya ya fara yi ni kuma na kanne ina fadin” Ahto domin kai zan haɗa da ita na yi kwanciya ta wallahi.”
“Na ji ba komai. Ai na iya reno nima.”
“Ka iya fa.”
Na faɗa cikin gatse,shi kuma yana ta mini dariya.
Ganin na gimtse fuska ne ya sa ya saussauta murya ya na faɗin” Da gaske ba ki san Daughter na da ciki ba?
“Na sani na ce ba ka faɗa mini ba?
Na faɗa ina masa wani kallo.
“Yi hakuri ma yar da wuƙar wallahi na ɗauka fa kin sani shi ya sa ba mu yi maganar da ke ba.”
Uhm”
Na faɗa kafin na ce” Allah Ya raba lafiya.’
“Amin ai da sauƙi ma bai wahalar da ita kamar cikin Anwar ba.”
Na yi masa banza na cigaba da ba ma Yunma Nono.
“Kin san likita ya ce ta huta. To da na yi mata mganar ko za ta yi tsarin iyali ne ai kin san mun ma yi maganar da ke ko?
Ya faɗa yana kallona sai na gyaɗa masa sai ya cigaba da faɗin” Sai ta ce ita ba za ta yi ba. Wai ba ta son yi saboda ba ta so ta yi itama ta samu matsala irin na ki.”
“Jar Uba!
Ban san na yi ashar ba sai da na ji ya fito. Yallabai ya yi ƙasake yana kallona. Cire Yumna na yi daga nono na kwantar da ita gefe ina kallon Yallaɓai.
“Zagi kuma Sadiya?
“Dole na yi ashar na ga matarka na neman rena mini wayau ne.”
“Na me fa?
Ya faɗa shima ya ɗan sauya yanayin shi.
“Saboda ta raina ni sai ta yi kwantance da ni ni kaɗai ce macen da ta taɓa tsarin iyali ya sakar mata matsala? Ko tsarin jikin mu da jinin mu ɗaya ne. Wata ƙila ita in ta yi sai ta wanye lafiya ai komai na Allah ne amma don tsabar renin wayau sai ta fake da ni? Ina ruwanta to da rayuwata”
“Ki tsaya ki fahimci ne ita fa ba haka take nufi ba.”
“Ya take nufi? Kar ka wani kare mata. To ni ba ni da wata matsala ba kuma zan gani ba in sha Allahu sako na baka ka sanar da ita ni Sadiya ba ni da matsala ban kuma tare da ita wanda ke ƙababa mini ita ma ya je Aniyarsa ta bisa wallahi.”
Na ƙarishe faɗa a fusace saboda raina ya gama baci ina gidana amma ta na can tana raina mini wayau.
“Topha ni ce Aniyata ta bi ni ko Daughter?
“Oho ni dai na ce ba ni da matsala mai neman kuma goga mini ita sai ta faɗa kan shi Ehe.”
Na fada ina sauka daga gadon gadon bi na ya yi da kallo ya yi kafin ya ce” Yi hakuri kar ki dake ni.”
“Ban isa ba kuma.”
“Kin isa ma tun da gashi kin rufe ni da faɗa daga mgana. Na gaji fa wallahi zan daina raga muku daga ke har ita ba daman in yi magana a kan ku da ɗaya daga cikin su sai cibi ya zama kari daga mai cewa ba na yi mata adalci sai yi mini tsaki, sai mai cewa in an cuceta Allah ya isa. Yau dai mai kankat kin ce ni din nan wai Aniyata ta bini, daga magana ko barina ma na ƙarisa maganata ba ki yi ba kin rufe ni da faɗa kamar wani ɗan ki.”
Ya faɗa a fusace, jijiyoyin sa na sake miƙewa kamar daman yana jira na ne.
“Kai ba ka ga laifin matarka ba?
“E ban ga laifin ta ba. Na faɗa miki daga yau ba zan ƙara raga muku ba. Ba ta yuyuwa ina mijinku kuna ƙarƙashina amma kuna ƙokarin rika sarrafa ni, saboda kawai ina muku kawaici? Kaina a ka fara auran mata biyu? Na gaji wallahi ku fita hanyata kafin wata rana ku harzuƙa ni na yi muku abin da ba ku yi tunani ba.” > Janaftybaby: Ganin yadda ya fusata ya sa sai na yi shuru, salaf salf na fice zuwa tiolet ina kunshe dariyata ashe itama can rufe shi take yi da faɗa a kaina. Ina ga ita ce ta yi masa Allah ya isa ni dai ba ni ba ce, kama ruwa na yi na fito ina saita kaina ko da na dawo ya ja Yumna ya rumgume yau sai dai na ci kaina kenan mirmishi na yi, na shafa ma hannayena da wuyana turare sannan na kashe fitilar ɗakin na kwanta muka saka Yumna a tsakiya na ja hannun shi ina so na sarke tare da hannuna ya ƙi ya damƙe hannun shi, na tsugule shi a hannun amma ya damƙe sai ma ya rike hannun Yumna cikin na shi na ya jimƙe.
Ni da na ke son rigima sai na taso daga in da na ke na haura tsakiya na raba shi da Yumna na shige jikinsa mamaki ya hana shi magana ina kallon shi ta ɗan hasken dake shigowa ta waje ya ɗan murmusa.
Ya rumgumeni, na kwanta a saman kirjinsa muna kallon Dama ni da shi dukkanmu mun sarƙe hannayen mu waje ɗaya mun rumgumo Yunma ina jin sa ya yi mana addu’an barci ya tofa mana. Ba mu daɗe ba ni da shi barci ya ɗauke mu, Yumna daman ta rigamu komawa tun da ta sha Nono ta koma barcinta.
Asuba ta gari. YUFSAD.