Search
You have no alerts.
    The Den of Novels
    Chapter Index

    *Ƙarshe*

    Yau ta kama asabar ɗin karshen mako ne tun bayan da na idar da sallar asuba na koma barci kamar ƴar maye, sakamakon a gajiye na ke, wancan satin muka yi bikin yar gidan Ya Aina ƙanwar Marwa ta biyu, tun da satin bikin ya kama ba mu huta ba muna ta zirga zirga da shirye-shirye, sannan Amarya Katsina muka kaita ni da Ma’u da Rahila muka je, bayan mun dawo kuma aka yi mana rasuwa a Yashe ƙanin Muntarin Rahila ne ya rasu magidanci kwanan mu uku acan sai jiya da daddare muka dawo, na kuma dawo gidan na iske Yallaɓai baya nan yana Abuja kan wani project da man mun yi mgana a waya ya ce mini sai yau asabar yake saka ran dawowa.

    Barcin gajiya na ke so na yi shi ya sa ma da safe da Baby ta ce za su je Gwammaja su yini na ce ta tattara yaran su tafi gabadaya. Yan biyu kaɗai aka bari wajen uwarsu, Gimbiya kuma ba ta fita kwana biyu megidan ke faɗa mini ta yi ta fama da zazzaɓi sannan itama da ta kira ni ta ƙara yi mini gaisuwa na ji muryanta shake nan take ce mini ba ta da lafiya mura da zazzabi. Jiyan dai da na dawo sun shigo ita da Rabi’atun sun yi mini barka da dawowa.

    Su Baby na tafiya na rufe kaina a ɗakin barcina na kuma kashe wayata na kwanta ina ta barci ban san meke faruwa ba sai da na ji ana ta buga mini ƙofar bedroom lokaci ɗaya ana kiran sunana.

    “Umma”

    Can a cikin barci na ji buga ƙofar bayan na ɗan motsa sai kuma na ji kiran sunan nawa, da hanzari na miƙe zaune ina mutsike idanuwana.

    “Maman Jidda”

    Na ji an sake kira sai na diro daga saman gado ina laluban hular da zan rufe gashin kaina, ina kuma tunanin waye? Kamar ban ɗau muryan ba.

    “Waye?

    Na faɗa ina isa kusa da kofar, hannuna guda ɗaya ina ƙara tusa gashin kaina da ya hargitse cikin hulan da na sanya yanzu yanzu.

    “Ni ce”

    “Salima?

    Sai da ta ce ita ce na ganeta.
    Na buɗe kofar lokaci ɗaya ina kiran sunanta.
    Salima ce ƙanwar Rabiatu.

    “Lafiya kuwa Salima?

    Na fada cikin mamakin ganin ta har ƙofar ɗakin barcina abin da ba ta taba yi ba iyakarta falo ko ɗakin Baby.

    “Anty Rabi’atu ne da Maman Khalifa suke faɗa.”

    Ta faɗa tana haƙi, ai sai na yi sansarai domin kamar an mantar da ni ma ko su waye sai daga baya na fahimci mganarta.

    “Faɗa? Innalillahi a ina?

    Na faɗa ina yin gaba sai da ta biyo bayana lokaci ɗaya tana faɗin” A can bangaren Maman Khalifa.”

    Ban tsaya ko saka takalmi ba, daga ni sai rigar barci Allah ya taimaka ma doguwa ce, kuma tana da kauri haka na fito haraba na kwashi gudu zuwa bangaren Gimbiya Salima na bin bayana hankalina a tashe.

    Ban ɗauka lamarin ya lalace haka ba ni da ta ce suna faɗa na ɗauka cacan bakin da suka saba ne, ashe ashe abin ya yi muni ko da na shiga bangaren Gimbiya a tsakiyar falon ta na iske Gimbiya kan ruwan cikin Rabi’atu tana kilarta, Rabi’atu na kuka tana neman ɗauki Gimbiya ko maruka take kai mata lokaci ɗaya tana faɗin.

    “Don ubanki na yi miki kama da sa’arki ce? Ni za ki ja da kokuwa? Yau sai na nuna miki bambamcin aya da tsakuwa.”

    Da gudu na yi kan Gimbiya ina salati ina ƙokarin ɗagata amma tana fizgewa.

    “Subhanallah. Gimbiya me ye haka? Don Allah ɗagata haba mana.”

    Amma ba ta jini ba kai mata duka kawai take yi itama bakin Rabi’atu bai mutu ba.

    “Allah ya isa muguwa, an ja ki da faɗan ke din banza.”

    Sai da na ce Salima ta matso tare da ita muka samu muka ɗaga Gimbiya daga kan Rabi’atu.

    “Haba Gimbiya me ya kai ki yin dambe da Rabi’atu? Ba girman ki ba ne wallahi sannan kar ki manta ba ke kaɗai ba ce fa.”

    Na faɗa ina rike ta, tana haki ta fizge hannunta tana gyara wuyan riganta.

    “Bar ni Maman Jidda, yadda yarinyar nan ta raina ni gwara da nuna mata ƙyaleta na ke yi amma ba ta fi ƙarfina ba.”

    Lokaci ɗaya tana hararan Rabi da Salima ta taimaka mata ta ɗagata.

    “Me ya faru ne? Ke Rabi’atu me ya sa wai ba ki jin mgana ne?

    Kawai sai ta fashe da kuka tana faɗin” Ai ita ce ba ta da gaskiya daga na zo ina mata mgana shi ne ta shiga zagina.”

    Gimbiya ta tare ta da faɗin” Maƙaryaciya. Yarinyar nan yar bariki ne,”

    “Wai me ya haɗa ku ne?

    Na fada ina katse su saboda na gaji da hayaniyarsu. > Janaftybaby: “Kan turaka dai Maman Jidda, shekaranjiya da zan karbi girki haka na iske shashen kaca kaca ta fita ba ta gyara ba, ban yi mgana ba na gyara nima ko yau de zan fita na ce ba zan gyara ba na bar mata shi ne da ta je shashen ta gan shi haka ita ishasshiya ta zo har shashena tana faɗa mini mganar banza. Na je na gyara yau Mijinta zai dawo ban isa na kwana da miji ta yi mini bauta ba, ni kuma sai na ce ai bauta ta gama tun da sai da na jagwalgwala na ba ta take suɗewa daga faɗin haka sai yarinyar nan ta ce wai in ban tashi na je na gyara ba zan ga abin da zai faru ni kuma na ce in ta fasa, saboda tsabar ta raina ni kawai ta jawo ni ina kan kujeran nan sai da na faɗo ƙasa ni ko da raina ya ɓaci ina miƙewa na kifa mata mari shi ne ita ishasshiya ta jani da dambe shi ne na nuna mata ba ta isa ba.”

    Gimbiya ta gama bani labari tana faman haƙi

    Kallonsu kawai na ke yi ina mamaki har yauahe ne za su daina fada kan wancan turakan da Yallaɓai ya samar da ita a cikin gidan nan ne? Shi kamar ma jin daɗi yake yi suna ta kara kaina akansa.

    Kai na girgiza kafin na ce” Haba don Allah wai mene ne da Turakan nan? Ko da yaushe a kanta ne kuke faɗa?

    Na faɗa ina kallon su gabaɗaya

    “Ita ta ja, da ta san ba ta gaskiya me ya sa ba ta tashi ta je ta gyara ba? Kuma ai Abba ya ce duk wacce za ta fita ta gyara abin da ta ɓata.”

    “Ba zan gyara ba, ke da kika fita a gyaren kika bar mini? Sai ke ce mai bakin mgana? To na ƙi na gyara ki ɗau matakin da za ki ɗauka.”

    Gimbiya ta faɗa har tana sake rike kugu, ga cikinta har ya fito amma ba ta ko jin nauyin jikinta.

    “Za ko ki gani wallahi.”

    Rabi’atu ta faɗa tana cije baki, har ya tasa ga jini a lebenta ta daku, ganin ga Salima a wajen yasa na kalleta ina faɗin” Salima koma bangaren Rabi’atu ki zauna da su Ayush.”

    Sai ta amsani da to ta sake ta Rabi’atu sai ta ce tare za su tafi ni kuma na ce ta tsaya ina da mgana da su ita da Gimbiya sai da Salima ta fice sannan na kalleta ina faɗin”

    “A wannan rigimar gaskiya ke ce ba ki da gaskiya Rabi’a.”

    “Ni kuma”?

    Ta fada tana wani tura baki, na ko haɗe rai ina faɗin.” ƙwarai ke fa, ai ke ce ƙarama, yau ko da Gimbiya ce mara gaskiya ya dace ki biyo ta bangarenta kina yi mata rashin kunya? Ban da Yallaɓai da auro ki ya goga kafaɗarki da ta mu ke kin isa ma ki haɗu damu a hanya ki yi mana mgana ballanta har sa’in sa ya haɗa mu? Na fahimci kwana biyu nan kina ji da rashin kunya to ki kama kanki ko ba aure Gimbiya ba sa’ar yin ki ba ce ballatana tana gaba da ke a gidan nan, abin da kika yi ba dai dai ba ne, tun da kin yi itama ta rama ba shike nan ba? Amma saboda fitina sai ki biyo mata har bangarenta ki ja ta da Dambe? Ai gashi nan kin sha wuya gaba ma sai ki ƙara.”

    Kawai sai yarinyar nan ta saka kuka tana faɗin” sai ki yi son kai ki goyi bayan ta ? Sai kawai ki yi ta mini faɗa akan gaskiyata ai Abba ne ya ce kowa ya ɓata ya gyara.”

    “E an yi miki faɗan, kin yi ba dai dai ba ba za a gaya miki ba? Abba ya ce wacce ta gyara ta bata kema kin ɓata ta gyara itama ta ɓata ba sai ki gyara ba? Da gaske ne ba ki da kunya ki kuma daina wannan halin ba zai ɓulle da ke ba, ni dai gaskiya na faɗa miki.”

    Kawai sai ta juya har tana yi mini tsaki.
    “Mtswww. Bari Abba ya dawo wallahi sai na faɗa masa.”

    “To in kin fasa faɗa masa kin raina kan ki. Shashaaha kawai.”

    Raina ya baci daga faɗan gaskiya bayan fitan kan ta Gimbiya na koma ina ta mata fadan me ya kai ta dambe da wannan yarinya a ga shi nan ta raina ta nan gaba ko a ina ne ba za ta ji shakkar jan ki da faɗa ba

    “Da ko da ta daku wallahi kambu”

    Ƙaramin tsaki na ja kafin na ce” Ba ki kyauta ba me ye sa kika biye mata ba.”
    “Har fa ɗakina ta biyo ni? Sai na raga mata?

    Ni haushi ma ya hana ni mgana na bar mata bangarenta na koma nawa, ina barcina sun hanani sukuni, dole na yi wanka na iske Baby ta soya doya da ƙwai sai na hada tea na ci da shi, ina yi ina tsaki saboda takaici da man kwana biyun can rashin kunya na fahimci Rabi’atu na fama da shi, ba kuma kowa ya ja ba sai Yallaɓai shi ya ja mana wannan wulaƙancin, ya sa ƙaramar yarinya tana ganin ɗaya take damu, ni wallahi daga Yallaban har matan na shi da gidan sun fita > Janaftybaby: daga raina, ina can cikin yan uwana na ma manta da wannan hatsaniyar.

    Yini na yi a bangarena ban fita ba, har yamma daga Gimbiyar har Rabi’atun ban san isalinsu ba, su Baby sun dawo ba daɗewa sai ga Yallaɓai ni da na ga ma Yamma ta yi ban ɗauka a ranar zai dawo ba sai ga shi, kuma a turakarsa ya sauka, ni kuma ban yi rawan jiki zuwa na gaishe shi ba, ina idar da sallar mangariba na zauna ina duba wayata, Baby da sauran yaran suna shashen Gimbiya.

    Kawai sai ga kiran Yallaɓai ban kawo ma kaina har Rabi’atu ta kai mganar nan ba sai da na ɗaga kiran na ji shi a fusace har yana yi mini ihu a waya.

    “Ki zo bangarena yanzu Sadiya.”

    Kuma yana gama faɗin haka ya katse wayar, wayar na koma ina bi da kallo cikin mamaki kafin na furta a fili” Ikon Allah!.

    Na yi niyyar zuwa a lokacin amma ina miƙewa sai cikina ya karta, shi ya sa na tsaya sai da na shiga tiolet na rage ciki ina fitowa da man na yo alwala jin ana kiran sallar isha’i na tsaya na yi sallata ina yi ko sai kiran wayata ake yi tun kafin na sallame na san shi ne, ban ɗauka ba saboda na san ihu zai yi mini shi ya sa da hijabin jikina na fita zuwa bangaren Yallaɓai.

    Ina shiga na gan su tsaye a falo cirko-cirko shi da matansa, Gimbiya na tsaye kiƙam rike da kugu shima haka hannayensa a bayan shi yana ta kai gauro da mari a falon Rabi’atu kuma na zaune tana sunne kai, falon na sake bi da kallo kaca kaca, alamun dai Rabi’atu ba ta gyara ba kamar yadda ta rantse.

    Tun kafin na kariso ciki Yallabai ya tare ni da hargagin shi da ya koya yanzu.

    “Sadiya ni za ki wulakanta? Ni za ki yi ma wulaƙanci?

    “Me na yi kuma?

    Na faɗa cikin mamaki, domin ganin su Gimbiya kawai na tabbatar mini da Rabi’atu ta kai masa labarin abin da ya faru ɗazu.
    Ni ko ina ruwana da zai sako ni a ciki don Allah?

    “Ban sani ba. Na ce ban sani ba kar ki raina mini wayau kin ji ko?

    Kallon shi na yi ganin shi a fusace kamar yana jirana ina kokarin danne abin da ke taso mini na ce” Gani ina fatan lafiya?

    “Ko lafiya lau ya dace na kira ki sama da minti talatin ki shanya? Kin kyauta kenan?

    Ina yamutsa fuska na ce” Ka kirani ina shirin zuwa cikina ya motsa na shiga makewayi, bayan na fito na ji ana kiran salla shi ne na tsaya na yi salla, ban ɗauka ai kana jirana ba ne”

    Na faɗa ina mai zaman kan kujera mai zaman mutum ɗaya domin na gaji da tsayuwa.

    Kasa mgana ya yi yana kallona ni ko na haɗe rai domin na yi alƙawarin yau ba zan yarda na ɗaukin renin wayau Yallaɓai da matan shi ba wallahi, gwara na tsage musu gaskiya in ba haka ba zai san ina yi mishi kawaici da kara ba ne.

    Ya gama cika yana batsewa sannan ya kalleni kafin ya ce” Me ke faruwa ne a cikin gidana wanda ban sani ba?

    Na yi kamar ban ji ba, saboda sai na ga tambayar ba ta shafe ni ba, tun da ya ce gidan shi a matsayin shi na megida ya saka ido mana ni ina ruwana.

    “Da ke fa na ke mgana Sadiya kin yi mini banza”

    “Ni?

    Na faɗa ina nuna kaina.

    “Aa ni “

    Ya faɗa a fusace, ban bari ya sake ɗauko wata mgana ba na tare shi.

    “To ai na ga tambayar kamar ba tawa ba ce shi ya sa na yi shuru. Gidan nan fa naka ne in ma wani abu na faruwa kai ne shugaba kai ya kamata ka fara sani ba ni ba”

    Wani kallo ya yi mini kafin ya ce” To na ji ni ina yini a gidan ne? Ke ce walikiyata duk abin da ya faru ki tsaya ki wakilceni in na dawo kuma ki zo ki sanar da ni.”

    “Ko?

    Na faɗa ina kallon shi, sai ya kasa mgana su kuma sun yi shuru suna jin mu.

    “E shi ya sa yau kika ɓata mini rai, ya za a yi har a yi dambe a gidana ba ki kira ni kin faɗa mini ba? Sannan kuma kika yi hukunci har kina zagin Rabi’atu kina cewa ita ce ba ta da kunya? Ita Gimbiyar kin binciketa kin san abin da ta yi mata har ta kai su ga Dambe?

    Ya faɗa yana kallona ni baki na saki ina kallon shi, na jinjina kai na juya ina kallon Gimbiya itama sai ta kalleni baki a buɗe.

    “Koma me ta yi mata ya dace ta yi dambe da ita! Sa’arta ne? Ban da siyar ma da kai mutumci, ji yadda ta kumbura ma matata baki? Koma me ya faru ba za a iya jirana na dawo ba ne?

    Ya faɗa yana tsare ni da ido, mamakin shi na ke yadda idanuwanshi suka rufe akan Rabi’a..

    “To ni yanzu me ye nawa a cikin wannan mganar? > Janaftybaby: Na tambaye shi ganin kamar ni ya fi jin haushi.

    “Naki shi ne ba ki yi hukuncin kan gaskiya ba, kin goyi bayan Gimbiya tun da kuna tare, sannan ni ba ki kirani kin gaya mini ba? Kin kyauta kenan? Girman kenan?

    Na buɗe baki haa ina kallon Yallaɓai Gimbiya ta saki sheewa ta tafa hannu ni ko na ma kasa mgana tsabar mamaki.

    “Ni fa Abba abu ɗaya ya yi mini zafi, wai Maman Jidda ta ce ina yi musu rashin kunya! Kuma ni wallahi ba wacce cikinsu na ke yi ma rashin kunya Maman Khalifa ce yau daga zuwa na yi mata mgana ta fara zagina”

    Ta karishe faɗa har tana shessheƙan kuka, kawai sai Yallaɓai ya juya wajenta yana faɗin” Ki yi shurun ki ai na san halin kowa a cikin ku, tun tuni ba ki yi rashin kunya ba ne sai yanzu? Da man ita Saudatu fitinnaniya ce, na san za ta aikata ita kuma Sadiya ban san ta da bangarenci ba sai yau, amma duk zan yi mganin abin yanzu nan.”

    Ya faɗa yana nuna mu da yatsa, a kausashe, Gimbiya ta sake sakin shewa kafin ta ce” Za ka sake mu ne? Shi ne karshen mganin mu da ka ce za ka yi ko?

    Ta faɗa tana tsare shi da ido, shi kuma sai ya taso mata tana faɗa yana faɗa, har yana ce mata hakuri kawai yake yi da ita darajan iyayansu. na gaji da hayaniyar sai na saka baki.

    “Don Allah ku yi hakuri wannan fa ba girman ku ba ne.”

    Daga ba da hakuri kawai nima Yallaɓai ya dawo kaina yana yi mini masifa.

    “Ai duk laifinki ne, haɗa kai kuka yi za ki kashe mini mata ko? Don kun gan ta yarinya ko?

    Ban san na mike ba sai da na ganni tsaye kan kafafuwana.

    “Dakata.”!

    Na faɗa da karfi ina ɗaga ma Yallabai hannu idanuwana har rufewa suke yi saboda bacin rai da bakin ciki wallahi tun da bai san ina yi masa kara ba yau sai na yi ma yallaɓai wankin babban bargo.

    “Ka dakata Yusuf..”

    Na sake faɗi cikin ɗaga murya, saboda raina ya baci zuciyata ma tafasa take yi a lokacin.
    Ba shi ba, har matan na shi tsayawa suka yi suna kallona saboda mamakin tsawar da na daka masa.

    “Ni kike yi ma ihu Sadiya??

    “An yi maka Ihu, an yi maka ihun Yusuf ka yi abin da za ka yi don Allah Haba.”

    Na faɗa ina yarfa hannu, bayan na nuna shi da hannu, sai na ga kawai ya tsaya yana kallona cikin mamaki.

    “Maman Jidda yau ba Yallaɓan?

    Gimbiya ta faɗa cikin mamaki.

    “Na bi yallabai da gudu, haba ka isheni a cikin gidan nan da fitinarka, na yi maka shuru na yi maka shuru amma na fahimci ba ka san kara ba, kuma ba ka san ina yi maka kawaici ba, to wallahi na gaji, na gaji da jidalinka da na matanka na gaji Yusuf”
    Na ƙarishe faɗa ina ƙara daga murya saboda a lokacin ji na yi zuciyata ta yi duhu ko gani ma bana yi saboda bacin rai.

    Sai falon ya yi shuru ganin na harzuƙa.

    “To yi hakuri zauna mu yi mgana.”

    Yallaɓai ya faɗa cikin sigan lallashi ganin yadda na taso masa ya san halina in na fusata ba ni da kyau.

    “Ba zan zauna ba, lokacin da na ke zaune ba ka so a yi mganar cikin laluma ba, yanzu sai dai kai ka koma ka zauna ka saurareni domin ni ce zan yi mgana.”

    Ban jira cewarsa ba na cigaba da faɗin” Yusuf auren soyayya ne a tsakanina da kai, a shekarun mu har zuwa matakin yau ba ka taɓa fahimtar cewa ina yi maka kara ba ne? Ba ka taɓa jin cewa a ranka kana yi mini wasu abubuwan da suka yi kama da cin fuska ina kyaleka ba! Mene ne ba ka yi mini ba, mene ne ba ka faɗa mini akan auran ka da Gimbiya ba? Wani baƙincikin matanka ne ban ƙunsa ba? Wani takaicin yan’uwanka ne ban ƙunsa a cikin zuciyata ba? Mun yi aure tun ba ka da komai muka yi gwagwamaryan arziki tare, daga baya da me ka saka mini? Ka yi mini gorin haihuwa na yi haƙuri, ka yi mini na gida na yi hakuri, ka yi ta mini alƙawaruka amma ba ka cika ba, na yi maka mgana? Ka nuna mini bambamci a kan matanka na taɓa yi maka mgana? Ka goyi bayan yan uwanka a kaina na yi maka mgana? Gimbiya ta yi mini abubuwa ta ci kasuwa a kaina kala kala amma duk ban ɗaga kaina ba, saboda kai Yusuf. Saboda karan da na ke yi maka, shi ya sa duk kake yi mini wasu abubuwa ba na ɗaga kaina, ba wai don bana jin zafi ba ne, sai domin ina kauda kai saboda kai, saboda ina daraja zaman mu da kai, ina daraja auran mu da soyayyarmu, ina kambama tarbiyan da iyayena suka ba ni, sabo da ina girmama bautar ubangijina, ka danne mini > Janaftybaby: haƙƙi, ka yi mini wulaƙanci akan matanka, ka tozartani a kan su na taɓa yi maka mgana? Ka taɓa zama ka yi tunanin abubuwan da kake yi mini rashin kyautawa ka ware rana ɗaya ka ba ni haƙuri? Don ina matarka uwargidanka sai na zama bolarka, don ina haƙuri da kai sai na zama mazubin sharan da kai da matan kuke zuba duk dattin ku a kaina? Ɗauka ka ke yi alfarma ce ka ke yi mini da na ke zaune da kai? Wallahi tallahi na rantse da wanda raina ke hannun shi Darajan aure ne, bautar ubangiji ne ya sa na ke raga maka, amma ba domin haka ba wallahi tallahi ba ka isa na zauna kana cin kasuwa a kaina ba. Ba ka isa ba Yusuf ba ka isa ba wallahi, daga kai har waɗanan matan da ka ajiye a cikin gidan ba ku isa ba.”

    Na karishe fada ina nuna shi da yatsa manuniya, bayan shi suma na nuna su ɗaya bayan ɗaya cikin baƙin ciki, domin gabaɗaya na rasa control a kan ɓacin raina ji na ke yi auran na Yusuf kwata kwata ya fita kaina da gidan shi da matan na shi duk na yi nisa da su ko zan samu salama da kwanciyar hankali.

    Na sake buɗe baki in yi mgana na kasa Kuka ne ya taso mini da ya sa na kasa ƙarisawa, su ko gabaɗaya sun yi shuru sun kasa mgana dukkansu sun nemi waje sun zauna saboda mamakin maganganuna.
    Ina da tabbacin ko shi da muka kwashi shekaru tare, bai taɓa ganina na yi masa hauka ba, sai yau balle su da suke baƙin ganin ɓacin raina.

    Ina kuka na cigaba da faɗin.

    ” Sha’anin matanka da komai na su ka sanyani shiga ciki, na shiga saboda ina yi maka kara, lokacin da za ka auro Rabi’atu ka yi abubuwa ba domin na kauda kai ba da ba za mu kawo yanzu ba, ka aurota ka ce na ja ta a jikina na bi umarninka, in ba domin kai ba ita ta isa ne? Ba ta isa ba amma saboda ina yi maka kara bana daga kai akan komai da kake yi mini a cikin gidan nan, ita kanta ta sani bana kishi da ita kamar Jidda na ke kallonta amma ita ka tambayeta ni kamar uwar jidda take kallona?? Ka bata dama tana cin kasuwa a kaina, duk bai isheka ba sai kaima ka zo ka ci kasuwar ka a saman kaina? Komai ya taso na matanka sai ka danganta shi da ni? Ina ruwana a ciki? Na san an yi? Ba sai da suka yi faɗansu sannan salima ta zo ta faɗa mini ba? Ka ce na yi son kai na shigar ma Gimbiya saboda muna tare, ka ce mun taru za mu kashe maka mata, Yusuf kai kake faɗin haka? Da bakin ka? Yau ko ba auran ka a kan Gimbiya ya dace Rabi’atu ta yi faɗa da ita? Sa’arta ce? Balle tana gaba da ita a shekaru, tana gaba da ita a wajenka da gidan nan, in har ina da mutumci da daraja a wajenka ya dace a gaban matanka ka kirani kana yi mini ihun cewa ban yi adalci a kan matanka ba? Ya dace? Me kake nuna musu? Ban da daraja kuma cewar da kake yi ni ce wakiliyarka duk karya ce tun da kalamanka na yanzu sun bayyana yadda ka ɗaukeni.”

    Na dakata ina sauke numfashi, saboda ina mgana ne zuciyata na zafi saboda bacin rai murya ta har ta dishe saboda kuka.

    “Sadiya ki bar mganar nan ki yi hakuri kin ji ko?

    Yallaɓai ya faɗa cikin lallashi har yana tasowa zai rikeni na matsa baya ina mai ɗaga masa hannu lokaci ɗaya ina faɗin.

    ” Ba mganar hakuri ba ne, hakuri ai na yi shi da ban yi ba, da ba ka ganni zaune a gidanka ba. Da a ce ina riƙe da irin cin kashin da kake yi mini na rantse da Ubangijina da tuni wata rana ka wayi gari ka ga bana cikin gidan ka.
    Kawai ina so ka san cewa kawaici na ke yi maka, kuma shi ne kuskure na, yau da ban nuna maka zan ɗauka ba, da duk wannan cin mutumcin bai biyo baya ba.”

    “Don Allah ki yi haƙuri.”

    Ya faɗa cikin lallashi kamar zai yi kuka, ashe karyan iskanci ne abin na shi.

    “Ki yi hakuri Maman Jidda.”

    Gimbiya ta faɗa jiki a sanyayye.

    “Ki yi hakuri.”

    In ji Rabi’atu ita kanta jikinta ya yi sanyi.

    “Ba komai ni ce na yi sakacin da komai ma ya faru. Ni na sabama Yallabai da hakan shi ya sa ba ya jin shakkar yi mini ihu akan matan shi, amma ina so ku sani daga yau sai yau, ba ruwana da abin da ya shafe ku, kai ma kar ka kara sakani cikin sha’anin matanka, mganar ni ce wakilayarka ba ta, gida na ka ne dukkanmu muna karkashinka ne, kar ka sake kirana akan su ko ka ce za ka yi mini ihu ko ka faɗa mini mgana nima ba zan sake shiga hurumin su ba, duk kawaicin da na ke yi maka na daina > Janaftybaby: domin na fahimci baka daraja haka.”

    Ina gama faɗin haka na juya da gudu na bar falon ina jin sa ya biyo ni yana kiran sunana ban jiyo ba sai da na fita haraba na saita kaina har na kai bangarena duhu duhu na ke gani saboda bakinciki, ina shiga na kulle kaina a bedroom ina ta kuka, ya zo ya yi bugu yana yi mini magiyan na buɗe ban buɗe ba, har Gimbiya ta so itama da magiyan na yi hakuri na buɗe itama na yi mata banza Baby ta zo tana kirana da Umma ki yi hakuri ki bude itama na yi mata banza, har Jidda dake makaranta ina jin Ubanta ne ya kirata ta yi ta kirana a waya ban ɗauka ba, kukana na sha, har na koshi sannan na lallashi kaina da alƙawarin Yallaɓai ya gama cin kasuwa kaina in dai akan matan shi ne.

    Sai da safe na buɗe kofa na fito fuska a kumbure, Yumna da Baby suna rige rigen gaisheni fuska ba yabo ba fallasa na amsa, ba su zauna ba suka shirya direba ya kwashe su zuwa Tahfez tun da jiya ba su samu zuwa ba.

    Tea kawai na sha, na koma falo na kwanta, da na kuma san Yallabai zai shigo mini da ɗaki zan koma amma sai ya ritsani, Yallaɓai duƙa mini yayi har ƙasa akan gwiyoyinsa
    yana bani hakuri faɗi yake yi

    “Ki yi hakuri Sadiyata. Wallahi na san ina yi miki wasu abubuwan na kure hakurin ki amma baki taɓa mgana ba. Na sani kina yi miki kara da kawaici ban kyauta ba don girman Allah ki yafe mini.”

    “Ai da ba yafiya Yusuf da ban sake kallonka ba, da ban sake ba ka wata dama ba
    kawai ka kiyaye kar ka ƙure ni na yi abin da ban saba ba.”

    “Ba zan kure ki ba in sha Allahu. Ki yafe mini Sadiyata”

    Duk yadda ya so bai ga dariyata ba, da gaske na ke yi na daina yi masa alfarma kuma ya san haka shi ya sa ya ruɗe, bayan fitan shi sai ga Gimbiya itama hakurin ta yi ta bani.

    “Ba komai fa, abin da ya wuce, wani abun ai da ba a hakuri da ba a kawo wannan matakin ba maman khalipa”

    Itama Rabi’atu ta zo tana bani hakuri itama na ce mata ni ba komai, domin in da ban yi hakuri ba da ba ta zo ta iske ni ba, tun daga ranar na tsame kaina daga sha’anin Yallaɓai da matan shi, kuma daga lokacin na samu sauki daga shi har matan na shi suka fara shakkata domin gabaɗaya na dauke musu wuta, ashe da gangan ne Yallabai ke yi mini wulakanci sai da na buɗe bakina na yi mgana na fahimci yana sane da abin da yake yi, tun daga ranar na shata masa layi sai na zauna lafiya ya kiyayeni suma suka kiyayeni, kuma abu in dai ya shafeni yana rawan jiki, suma haka matan na shi, saboda yadda na fidda kaina daga duk abin da ya shafe su na gyara kuskuren da na yi sakaci tun farko.

    Aka ce mai hali ba ya fasa halin shi, ya riga ya saba da kwaso mini ko wata mgana amma yanzu da ya zo ya fara, kallo kawai in na yi masa zai shiga taitayinsa, in ma ban kalleshi ba, banza na ke yi da shi har ya gama ɓaɓatun shi kanzil bana cewa, in ya gaji sai ya ce Sadiya ta ba ki ce komai ba! In ma na ɗago na yi masa wani sakaran shi da kan shi ya ke kama kanshi ya tashi yana kame kame, wallahi aure bauta ne ba domin bautar ubangiji ba da Yusuf bai isheni kallo ba wallahi. Shima ganin yanzu ya fita zuciyata shi ya sa duk wani abu na kyautatawa ba wanda ba ya yi mini. Ni ce wai Yallaɓai ke yi ma tsaraba in ya fita bini bini Sadiya ta ko kina son wani abu? Kafin na yi mgana ya yi mini alheri jikinsa na rawa da zuciyarsa a kaina ni ko bai san na riga na gama sanin shi ba ba kuma wani yaudaran da zai zo da shi ya sake ruɗata. Ni dai tun da sun kiyayeni daga shi har matan shi shike nan na samu salama da zaman lafiya.

    *

    *BAYAN SHEKARA ƊAYA DA RABI.*
    NOVEMBER, 2025

    Alhamdulillah Rayuwa ta miƙa Ubangiji ya ara mana dama. Ya ba mu rai da lafiya sannan ya azurtamu. Ba abin da za mu ce sai godiya ga Ubangijin mu. Yau da jiya da gobe ba su bar komai ba tun muna kirga kwanaki mun koma na wattani ga shi muna kirga shekaru ashirin da huɗu cikin na biyar da auren na da Yallaɓai. Rayuwa ta zama sai godiya kawai mun faro gwagwamarya kuma ba za ta kare ba har mu koma ga Allah amma dai muna fatan ko da yaushe mu yi kokuwa da matsalar mu mu ga bayan ta ba wai ace ita ce za ta ga bayan mu ba. > Janaftybaby: A halin yanzu shekaruna na haihuwa arba’in da biyar Yallabai kuma girma ya zo an gangangara gidan hamsin da biyu har da ɗoriya. Rayuwa ba za ta koma jiya ba sai ta yi ta gaba kana karuwa a fuskantar yarintarta ka. shekarun mu sun mika amma kuma mun samu wadatar rayuwa sai godiya. A shekara ɗaya da rabin da suka gabata abubuwa na alheri da aka sin sa duk sun faru amma na alherin da farincikin sun fi yawa.

    Gimbiya ta haihu ta samu yarta mace ta ji sunan Hajiyar Tafida. Ahalin yanzu ma Rabi’atu ta na da ciki kimannin wattani biyar. Tuni har ta yaye yan biyu tun da suna cikin shekaru na biyu ne. A gidan Yallabai tsakanin Gimbiya da Rabi’atu ne ake gasan haihuwa da kishi ni kam na koma gefe na zama Umma, sai dai na ba da shawara ko na raba in na ga abin da bai kamata ba.
    Na yarda na amince ina da wani hali da ba zan iya barin shi ba, duk yadda na kai ga kauda kaina ga sha’anin Yallaɓai da matan shi in na ga abin da bai kamata ba, ba na iya shuru sai na tanka, na ɗauki hakan a matsayin hallita ce ta Ubangiji, ba ni da riƙo sannan kyakyawan zuciyata ba ta barina na daɗe ina jin haushi wani a cikin zuciyata.

    Yallaɓai har gobe bai dai na faɗin bai cire rai ba bai kuma haƙura ba yana fatan bayan Yumna na sake haihuwa ni kuma na kan ce masa na gama. Ga su Gimbiya nan dai su yi ta cika mana gida da yara Alhmdulillah. A tsawon zamana da Yallaɓai ya yi mini tarin alhern da suka goge sharrinsa a wajena amma babban abin da ya yi mini da ya ƙara samun daraja a cikin zuciyata shine ya biya mini kujeran makka a wannan shekaran na je na sauke farali sannan ina dawowa na yi cukun_cukun buɗe shagon Saloon ɗin da na ke buri, domin na fahimci Yallaɓai ba zai iya cika mini alƙawari ba, Musbahu na saka a jagoranci sai dai Yallaɓai ya ji labarin an kama shago a wajen ƙaninsa domin ni ban faɗa masa ba, sai ga shi ya zo yana borin kunya shi da man yana da niyyar da na dawowa daga Saudiya ya buɗe mini shago shi ne target ɗin shi, har yana faɗan me ya sa na yi masa haka? Ni ko na ce kar ya damu ba komai ai na san abubuwa ne suka yi masa yawa, ba na ce ban gode masa ba ne na gode tun da ya yi sanadin da na je ɗakin Allah, amma mganar buɗe shago bana son tunawa saboda tsabar renin wayau da renin hankali Yallaɓai ya yi mini shi, tun yaushe? Mgana ce tun auran mu, yana da shi ba wai ba shi da shi ba ne, kawai bai yi ra’ayin cika alƙawari ba ne shi ya sa na kuɗiri niyyar sai dai ya ga ana yi, da jarin hijabaina da kudaɗen hannuna na haɗa na kama shago na yi siyayyan wasu kayan shi kuma Gogan sai ya ji kunya ya dunkule 800k ya bani da na ce ma ba zan karɓa ba wajen Alhajinmu ya kai ni kara shi ya tursasani na karɓa sannan a ɓoye ya saka aka yo mini oder ɗin kujeru da sauran kayan injinan shagon sai dai na ga an kawo sannan ya shiga ya fita sai da aka gyara shagon nan ya ga komai ya kamallah, har yana yi mini mganar ko zai kama mini wani babba ne! Ya ga kamar wannan ya yi ƙarami na ce na gode ƙaramin ma ya ishe ni.
    Gabaɗaya dai kunya ta hana shi suƙuni ni kuma ko a fuska ban nuna masa ba, shi ne dai ya san bai kyauta ba yana ta kame kame na yi banza da shi. To ni Yallaɓai ai ya daina damuna, na tattarashi da sha’aninsa na watsar tun a baya.

    Da shago na ya kamallah mai suna S.S YASHE BEAUTY SALOON.
    Na yi Farinciki da ban san iyaka ba da man ina cikin farimcikin ne na je na ga ɗakin Allah A shekaran tare muka je da Alhajinmu Hajji da Ya Hamza da Ya Auwal suka haɗa kudi suka kai shi sai Ya Usman da Anty Zabba Allah ya taimaka a masauƙi ɗaya muka sauka. Yallabai ya girmama ni tun da ya ce ni ce uwargidan shi ni zan fara zuwa amma daga baya ɗaya bayan ɗaya zai kai su Gimbiya. Suma ɗin ba su nuna damuwar su ba sun yi fatan Allah ya sa suna da rabon zuwa ita Gimbiya ma ta taɓa zuwa Umra tsohon mijinta ya taɓa kai ta, Yallaɓai ma a shekarslan da ya biya mini ya je Umra ya dawo. > Janaftybaby: Kamfanin Yallaɓai ya shahara fiye da tunanin mai tunani yanzu haka yana ma shirye-shiryen buɗe reshe ne a jihar Kaduna. Yanzu in dai kamfani ne na gine-gine da zane-zane in sunan kamfanin Yallabai bai shiga gaba to zai jera a na biyu. Dukiya kam ya nema da aiki tuƙuri kuma ya sa mu, yanzu haka dukkan mu ya siya mana sabbin motoci, ni da Gimbiya da Rabi’atu ni tawa Ta kamfanin toyota ne, tawa kuma ta fi tasu tsada ni fara ya siya mini.

    Na su kuma na kamfanin camry ne, duka kalan ruwan toka.
    Sannan can Gwammaja an sake gyara gidan an ƙawata shi ya siya ma Nene mota har da direban da zai riƙa zirga-zirga da su ya ɗaukan musu. Ba abin da suka nema suka rasa sai godiya.

    Munnira Nasir ya samu aiki a Taraba ya koma can daga baya ya zo ya ɗauke mana Munnira suka koma can sai dai mu yi magana ta waya. Daga ni sai Hauwa da itama Alhamdulillah Mutaƙƙa ya samu buɗi da rufin asiri. Duk sun sake haihuwa har Marwa yanzu yayanta uku ta zama uwar mata. Datti ma matarsa ta haihu gidan mu na ɗorayi shashen farko su Ya Hamza sun rushe shi sun gina shashe mai kyau in da suke sauka da iyalansu in sun zo. Cikin gida ma komai ya sauya Gwaggo ta na nan kwance ta samu ciwon ɓarayin jiki Baaba ce ke kula da ita amma Alhajinmu har gobe yana nan da ƙarfinsa.
    Ma’u ta sake haihuwa amma ta samu matsala har sai da aka cire mata mahaifa ta fi wata a asibiti tana jinya daga baya ta ji sauƙi ta koma gida. A yashe mun yi rashi shima Baba Aminu mun rasa shi mahaifin Ya Muntari rayuwa sai godiya. Bayan rasuwar Baba Aminu ko wata shidda ba a yi ba mahaifiyarsa ta saka shi ya auro ɗiyar kanwarsa tana nan gida ɗaya da Rahila. Auran da ya sha mganganu ita kanta Rahilan har cewa ta yi sai Muntari ya zaɓa ko ita ko amaryan da zai aura. Da nasihan Alhajinmu da shawarwarin irin mu Rahila ta haƙura domin na sha faɗa mata ta yi haƙuri wata rana za ta ci riba. Su Ya Aina kowa sai hamdala rayuwa ta yi kyau ana lallaɓawa. Amina ma ta sake haihuwa ƴaƴanta biyar kenan tana zaune cikin farinciki da mijinta. Ya Abubakar ma ya ƙara aure tun da shima ya kama babban aiki yanzu ba gida ɗaya suke da Amaryan ba tuni Zaituna ta shiga taitayinta ta gyara bayan lokaci ya kure mata.

    A yanzu haka Jidda na Aji huɗu ne za ta je biyar a jami’a. Kuma tana da shekaru ashirin da huɗu ne, an sanya mata ranar aure shekara mai zuwa ita da Uncle ɗin kawarta Ummu Salma auta ne a ɗakin mamanta. Sun yi bikin yayar Ummu salman Jidda ta je musu biki anan ya ganta. Abdullahi pilot ne matukin jirgin sama ne. Kuma ba jira ya nemi soyayyar Jidda ta amince ganin duk abin na gida ne an zama ɗaya tun da har bikin na je ni da Baby sai ya gabatar da kansa a wajen Yallaɓai.

    Sai ga shi Yallaɓai na zuwa da wata magana wai ba yanzu zai aurar da y’arsa ba sai ta gama makaranta. Ƙiri-ƙiri fa yana abu kamar wani ɗan fari ni ko ganin zai yi mana salalan tsiya ga Jidda na son abin ta na kai shi ƙara wajen Ya Usman kai tsaye ya ce na ba ma yaron lambarsa ya neme sa. Ai sai dai Yallabai ya ji labari daga baya Uban Jidda Alhaji Usman ya ba ma Abdullahi dama ya cigaba da neman Jidda. Ba shi da bakin mgana balle da Tariq da Kawu suka ji labari kamar su tsire shi, suka ce ya yi musu katsalanda ina ruwan shi ai sune ma su ba da auran yar su. Hakan ne ya sa ya koma gefe ko maganar auren da saka ranar Ya Usman ne da su Kawu anan Kano ya zo aka karɓi maganar a Gwamnaja aka saka rana wattani goma ma su zuwa. Baby da ta ke aji ɗaya a BABA AHMAD UNIVERSITY KANO tana da manemin ta. Shi kuma yaron ƙanwar mijin Mimisco ne likita ne an asibitin Aminu Kano. Shima Yallaɓai ya fara faɗa wai Babyn nawa ta ke? Ba ta isa fara samari ba shima sai da na yi masa ido da ido sannan ya bari Hafiz na zuwa duk Weekend suna ganawa da Baby tun da na gida ne amma fa ya sha sharuɗɗa kamar zai auri wata gold Yallaɓai fa ya ƙaro wulakanci wai shi nan haushi ya ke ji duk za a tattare mai ya’ya lokaci ɗaya. Ina dariya na ce wanzami ba ya son jarfa shi amma ya tattare ya’yan mutane a gidan shi? > Janaftybaby: Sai an yi mgana ya ce ƴaƴan shi ba su isa aure ba sai sun gama karatu. Su Musbahu suna nan an zama magidanta Mubeena ya’yanta biyu. Ga Adnan ma yan baya baya matarsa ta haihu shima.

    Rayuwar gidan Yallaɓai sai abin da ya yi gaba. Domin Rabi’atu mace ce mai tsananin kishi har ta ce ma Gimbiya ba ta iya kishin ba, ga ta da wayau da iya bariki, duk yadda Yallaɓai ya kai ga bacin rai a kanta ta san lagon sa. Ita kuma Gimbiya abin da ke cutar ta har yau rashin haƙurin ta ne da shegen saka baki a komai na yi na yi na raba ta da wannan halin na kasa sai na koma na zura mata ido. Ba sa sati ba su yi cacan baki ba lokacin ma ina Saudiya har Dambe suka yi Yallaɓai bai faɗa mini ba amma ita Gimbiyar da kanta ta faɗa mini. Kuma wai a kan yara ne ita Rabi’tu mace ce mai ƙulafucin ƴa’ƴa ba mai taɓa mata su a gidan nan ya zauna lafiya. Kuma suna ƙananu dole kan manya su taɓa su, masu taɓa su Yunma ce da Ammar iyayen mugunta ni wallahi ko suna yi ba na bi ta kansu ina bangarena Gimbiya ce take fitowa suna tanka tanka. Ga y’an biyun nan da tsiwa da tsokana su kuma su Yumna ba ɗaukan reni sai dai ka ji sun make su. In Rabi’atu na makaranta suna gida ƙanwarta Salima na wajenta tana makaranta tare da su Khalipa in tana gidan itama kamar yayarta ba ta bari a taba su in kuma yayar ta dawo ta faɗa mata ita kuma saboda rashin tunanin sai ta zo ta ce za ta rama musu. An ce hakan ce ya janyo faɗan Rabi’atu ta biyo Ammar har ɗaki wai za ta rama ma Ayush ya daketa. Gimbiya ta ce ba ta isa ba ta kai hannu za ta dake shi Gimbiya ta tare dukan ya sameta daga nan ta ce ita za ta daka ta saka hannu ta mareta sai Dambe. Yallaɓai na zuwa ya ce kowaccen su ta je gida shi gidan shi ba gidan Dambe ba ne shine suka je Gwammaja acan Nene ta kashe faɗan.

    Kowa ya san Rabi’atu ce ba ta da gaskiya amma su Anty Bahijja ita suka goya ma baya saboda ta kama su a hannu ta riƙe gam! Kamar ta yi musu sujuda shi ya sa in suka zo gidan nan wani abu ya faru shashenta suke shiga Gimbiya ce ke bin su can ta gaishe su ni dai ko sun ƙi ko sun so na zama turken gida a gidan Yallaɓai ba su da yadda za su yi da ni. Sun buga da ni sun gaji sun bar ni, na san ba zan taba fari a idanuwansu ba, nima ban matsa ma kaina sai sun so ni ba, da man ba kowa ba ne zai so ka, wani har gaban abada ba ya sonka, sai dai in ya gaji ya hakura da adawa da kai in ya ga kafi karfin shi.

    In sun zo gidan Har shashena za su leko sannan mu gaisa tun ballatana da suka fahimci ni yanzu ba na ta kansu sabgogina sun sha gabana.

    Rabi’atu Da Gimbiya sune faɗa kan turaka ƙananun mganganu dai ba sa ƙarewa. Ni kenan kullun ban hakuri ko faɗan aka yi in Yallabai ya dawo ko da Rabi’atu ce ba ta gaskiya ta iya lauya in ana ma yar da mgana sai dai ta zauna kanta a ƙasa tana kuka ita ko Gimbiya harshe a sama shi ake cutan ta Yallaɓai kuma ya tsani yana mgama tana mgana yanzu zai harzuƙa kuma da man kuranta ta yi kuka a wajen shi ya riga ya making ɗin ta a matsayin mace mai fitina, in kuma ranar da ya ke jin tsiya ne sai ya ce har da laifina wai yanzu ba ni da amfani a gidan ni ko ta kan shi ba na bi, to lokaci da na ke gidan kenan da na fara fita shago nima ba na gidan ban san sun yi ba,

    Kuma sun fi yi da daddare tun da Gimbiya ma na zuwa shagon ta itama Rabi’atun makaranta ba yini muke a gidan ba sai dare ya yi in sun haɗu a yi ta hararan juna. Ni wallahi dariya ma suke ba ni, Gimbiya ce duk ta bi ta raina kanta shi ya sa Rabi’ar ta raina ta Yallabai da man tuni ya dawo rakiyarta tuni aka daina kiran Daughter Saudatu ne itama Baban Khalipa ko Baban su Jidda. Ita kam Rabi’atu Abba ne ko Yallaɓan mu ni kuma da man yara da su kan su Umma ne har Gimbiya yanzu Umma ta ke kirana har Yallaɓan ma in yana jin nishaɗi Umma Sadiya ya ke kirana in kuma zai kirani har yau har gobe Sadiya ta ne ko abar ƙaunata nima ko shekara ɗari ya yi a duniya ba zan iya daina kiran shi da sunan Yallaɓai na ba, domin na riga na saba. > Janaftybaby: Matsalan da ke faruwa yanzu shi ne ita Rabi’atu tana ware ya’yanta tana nuna kamar dabam suke, shi kuma Yallaɓai ba zai aminta da haka ba ya yi mata faɗa ta ƙi dainawa ya faɗa mata ya’yan shi duk ɗaya ne kar ta zo ta nuna bambamci ta raba masa kan yara amma ba ta jin mgana. Ko a cikin satin nan sai da Baffanta ya zo kwana biyu ta hana yara fitowa a bangarenta take kulle su suna son fitowa su yi wasa da y’an uwan su ta ki barin su.

    Tun ballanta sun saba da wassanin su a haraba har raga na ƙwallo Yallaɓai ya saka aka saka musu a haraba in yana gida Weekend zai ta wasa da su shi ne su yi ƙwallo wasan gudu, chinese wasan ɓuya to yaran sun saba da wassani ko baya gida za su fita haraba su yi ta yi. Yunma ma da ke mace in ta ware kafa ta kai duka kamar wata namiji Yallaɓai duk ya gama koya ma yara wasan banza ko a jikin shi, mu kan mu in za mu fito zai so haka tuni ya ce mu riƙa fitowa muna rage kitse na ce ni kam ya ƙyaleni da kitsena. Ni ban ma kai su Gimbiya kiba ba su ne sun zama wasu Hajiyoyi da su ni dai na san na yi kiba amma ba ta yi mini muni ba, ko don bana haihuwa ne su kuma suna haihuwa da wannan ta sauke wannan ta ɗauka sun ma yar da abin na su gasa.

    *
    *RUFEWA.*
    Lahadi
    20 DECEMBER 2025

    A sati sau biyar na ke zuwa shago ina da mai ɗan taimaka mini Nana ce ɗiyar mai yi mini kitso Maman Nana ta gama sakandiri ba ta shiga makaranta ba. Yanzu haka muna stimin, saloon, wash and set, kitso gyara kafa na ke so mu fara tun da ina shiga clases ɗin online ina ƙarin sanin wasu abubuwa. Ba na zuwa asabar sai dai Nanan kaɗai ke zuwa duk na koya mata ba abin da ba ta iya ba. Sai Baby ta kan leka itama ranar asabar ko in ba ta shiga makaranta ba tun da itama ta yi sauka an yi musu walima a Tahfiz.
    Jidda ma in ta dawo hutu tana zuwa, ita yanzu ta yi ƙarfi wajen yin snaks, in dai ta dawo hutu tana yin na biki da na birthday.

    Ranar lahadi kuma muna gida ba ma buɗe shago. Haka itama Gimbiya dukkan mu muna gida muna kula da mijin mu da yaran mu. Yallaɓai ma ba ya fita ranar ta iyalai ce.
    Ranar duk muna gida gabaɗaya har Jidda na gida ta zo hutun karshen shekara.
    Da ni da su da yara tare da Gimbiya mun je min duba Hajiya Iya da hawan jini ya kwantar da ita mun ɗan jima a Gwammaja sai gabda mangariba muka dawo gidan Rabi’atu ba ta je ba, tana fushi da mu gabaɗaya daga mijinta ya yi mata faɗan in ba ta daina rufe su Ayush a ɗaki ba za su samu matsala ta bar su su fito su yi wasa da yan uwan su in ba haka ba ranta zai ɓaci shi ne ta yi ta kuka tana kumburi tun da ya yi mata faɗa a gaban mu shike nan ta daina ma fitowa shi kan shi mijin ƙamshi ake shakar masa sai dai ya bita cikin ɗakinta mu dai ba ma bin ta yara dai ta ji faɗa ta barsu yau ɗin ma tare muke je Gwammajan da su bayan mun dawo ma a shashena muka ya da zango. Yallaɓai dai ya ce yana ganin har da cikin da ke jikinta ke saka ta fushi, ga kishi ko mgana ce yanzu in ta ji mganar kishiya za ta sauya fuska ta fara kumbura. Ita a dole ba ta son wata ta shigo. Kuma duk abin ta in Allah ya so Yallaɓai zai cike ƙofa.
    Can kwanaki ma har ma’aikatan shi ta riƙa zuwa lokacin da ya dauƙi wata sakatariya, tun da yanzu kamfanin ya na ɗaukan ma’aikata mata, ba ta yi sukuni ba sai da ya maye gurbinta da namiji sannan hankalin Rabi’atu ya kwanta.
    Ko Gimbiya yanzu ta shafa ma kanta lafiya ba ta wani rawan ƙafa a kan Yallaɓai.
    Gabaɗaya ita ma ta tattara shi ta bar ma Rabi’atun.

    Mun dawo mun iske Yallaɓai ba ya nan ya fita, ni ce ma na kira shi a waya sai ya ce mini ya ɗan fita ne zai dawo ba daɗewa ba. Da ya ke ni ke da shi a turaka shi ya sa muna dawowa na zage na shiga na share falon na gyara bedroom na wanke tiolet, na ɗauko sabon zanin gado na shimfiɗa wani ja mai love a saudiya na siye shi, sannan na koma bangarena na shiga kitchen na ɗora ruwan zafi a tukunya.

    Yau amarci na ke so mu tuna, rabon da mu hada shimfiɗa da Yallaɓai sama da wata uku, kwanakin baya in ranar girkina ne ban ma cika bin shi turakan ba in ya yi magana na ce barci ya dauke ni na manta, in kuma na je babu abin da na ke yi sai barci ko ma ya neme ni sai na kawo masa ƙorafin na gaji, tun da ya fahimci haka sai > Janaftybaby: shima ya ba ni lokaci amma ya shafa faɗa mini Sadiyata kin sauya, amma don Allah ina roƙon ki, kar ki sauya ni, har duniya ta tashi kar ki manta ruwa na mganin daula, shi ya sa yau na ce zan faranta mishi.
    saƙo na tura masa.

    “Yallaɓai na yau me kake son Sadiyarka ta da fa maka?

    Na ma ɗauka bai ga saƙon ba har tsawon mintina sha biyar sannan ya dawo mini da amsa.

    “Kin tuna tuwon shinkafar da kika taɓa yi mini kina Amarya? Har na yi ta gudawa? In kin tuna to ki yi mini irin shi Sadiya ta.”

    Da na ga saƙon shi sai da na yi dariya ina tuna lokacin. Na tuna kwana Yallaɓai ya yi yana zagayawa tiolet na zambaɗa ma miyar yaji. Rayuwa kenan.

    Tuni na mike na shiga kitchen Jidda ta shigo ta ce za ta taya ni na ce ta fita ta ba ni waje, yau girkina mijina zai ci.
    “Kai Umma”
    “E yau dai a fita a ba ni waje ni da kaina zan yi ma mijina girki”

    Jidda ta kwashe da dariya har tana kiran Baby tana faɗa mata abin da na ce suka zo suna yi mini shaƙiyan ci.

    “Umma kawo mu taya ki”

    “Bana son rashin kunya. Tun kafin ku zo duniya na ke dafa ma mijina abinci.”

    “Yau Yallaɓai sharr da shi”

    In ji Baby tana dariya na yi kamar zan kai mata duka suka fice suna yi mana dariya.
    Na duƙufa ina ta faman aikina ina da naman rago ga man shanu, sai da na tuƙa tuwo na je na yi salla isha’i, Yumna ta biyo ni tana kukan yunwa ta ke ji na saka Baby ta dafa mata indomie, Ammar ma yana gani ya ce zai ci su Khalipa ma suka ce yunwa suke ji, na ce su Jidda su ji da su ni dai ina ta mijina ne.

    “Umma ma su miji.”

    Ta faɗa tana dariya.

    “E ɗin na ji “

    Na faɗa ina murguɗa mata baki suka kwashe da dariya har suna tafawa da Baby.

    “Mara sa kunyan yara.”

    Gimbiya ta shigo da man ta kan shigo a yi hira ta iske ni ina ta aiki tana tambaya Baby ta ce” Yallaɓai ake yi ma girki.”
    Gimbiya ta zauna gefen su Baby ɗauke da Afiya tana faɗin” Lalle yau za mu sha gara.”

    “Yallaɓai kika ji an ce ba ku ba”

    Na faɗa ina haɗe rai Gimbiya da ya’yanta suka kwashe da dariya.

    “To Yallaɓai zai sha gara “

    “Yauwa gwara da kika gyara.”

    Faɗi take yi ta zo ta ya ni na ce ta yi zamanta wannan ba huruminta ba ne ina Kicthen ina kai da kawo sun haɗa kai suna gulmana.

    “Ku yi ku gama”

    Na faɗa ina kyfaci sai suka kwashe mini da dariya.
    Na yi banza da su na cigaba da aikina tas na lailaya tuwo a leda miya kuma ta ji nama da manshanu ga ganyen ogun da ya ke mun shukata muna da shi a gida na saka Baby ta ɗebo mini na yanka na wanke na yi amfani da shi.
    Zuwa takwas da rabi na gama tun da ba da yawa na yi ba bai kai ko leda goma ba ma tuwon
    Wanka na yi na shirya cikin wando plazo bakin wando da jan riga mai ratsin baƙi. Na gyara gashina da ya ke ban yi kitso ba na saka bakin dankwali na yi ɗauri da shi na feshe jikina da turare na fito falo ina tashin ƙamshi. Ihu suka saka mini yaran nan kamar wasu sa’ar su Gimbiya na ta ya su.

    “Su Umma manya.”
    In ji Jidda.

    “Umma an sha kyau.”.

    In ji Gimbiya na yi mirmishi na yi fari na ɗau wayata ina faɗin” Bari na kira Yallabai na ji ko yana ina ne?
    Baki suka sake suna kallona ina kiran shi ya daga.

    “Uwargida ta.”

    “Yallaɓai na “

    Na kashe murya kawai sai suka saka mini ihu sai na yi ɗaki da gudu ina dariya.

    “Su waye ke ihu?

    “Su Jidda ne da Gimbiya suna ta mini tsiyan wai yau na ce za mu tuna da zan yi maka girki mu sha soyayya “

    Yana dariya ya ce” Share su. Kazan amarci zan siyo mu ci mu sha mu kwana ɓarnan ruwa.”

    “Allah ya ja zamanin ka Yallaɓai na.”

    “Sai na iso.’

    Muka yi sallama cikin shauƙi
    Yallaɓai a muryan ma za ka gane yana cikin farinciki
    Ɗaure fuska na yi na fito suna kallona suna kunshe dariya. Jidda Abdullahi ya kira ta ta bar falon Baby ce suke hira da Gimbiya akan tana son ta yi ma Yallaɓai mgana za ta fara koyon mota.

    “Na ji yana mganar kuwa. Ki tuna masa.”

    “To Anty in sha Allahu.”

    Kusa da Baby na zauna muka saka ta a tsakiya muna ta hira. Gimbiya ta ce Rabi’atu fushin ne har da mu?
    ” Mijin ki ya jawo mana.”
    Mijin ki dai.”
    Gimbiya ta mayar mini da amsa dukkan mu muna dariya.
    Kamar wasa sai ga Rabi’atun ta shigo ita da Salima ina jin gajiya ta yi da zaman shuru yaran duk suna nan shi ya sa ta fito. > Janaftybaby: “Umma barka da dare. Sannu Anty Gimbiya.”

    Ta faɗa tana zama a kan kujeran da ke fuskantan mu

    Muka amsa mata cikin sakewa, ni dai ce na kara da cewa ta gama fushin ne? Sai ta rufe fuska tana dariya.

    “To mu da ba laifi ba an share mu.”

    Na faɗa ina dariya.

    “Ni fa ba na fushi.”

    “To mene na ɗauke mana? Kwana biyu kenan ko hira ba kya fitowa.’

    Sai ta ce ba ta jin daɗi ne muka yi mata fatan sannu hancinta ta bude kafin ta ce Umma na ji kamshi me kika dafa mana ne?

    Kafin in yi magana Baby ta ce tuwo ne mai daɗi amma na Yallaɓai ne”
    Rabi’atu ta ce” Umma wallahi ina son ci ki taimaka.”
    Ba ni da yadda zan yi na ce ita za ta ci Gimbiya ta ce itama sai ta ci na sawo musu ya’yansu suka ta so suma sai sun ci.

    “Ah ku na yi ma girki kawai.”

    Na faɗa ina tura baki.

    “Na mijina ne fa.”

    Na sake faɗa ina riƙe haba.

    “Umma ki ba mu kawai mu cinye Abba ya sha tea ya kwanta.”

    Jidda ta fada bayan ta dawo falon.

    “Ba ku isa ba”

    Muka ji muryan Yallaɓai daga sama ba ma wanda ya ji shigowarsa yaran na ganin shi suka ruga suna oyoyo Abba.

    “Jidda haka za mu yi da ke?

    Ya faɗa yana karisowa falon
    Baby ta tarbi ledan hannun shi guda ɗaya ya sakar mata ɗayan kuma ya ce” Wannan na ku ne ku da iyayen ku. Wannan kuma na My Sady ne.”

    Sai Jidda da Baby suka saka dariya.

    Gimbiya ta ce” Son kai dai kake nuna mana kamar yadda itama ta nuna mana yau.”

    “E ɗin an nuna muku son kai ɗin.”

    Ya faɗa yana zama a gefen Rabi’atu da take zaune a ƙasa tana cin tuwo Afiya na miƙa hannu sai ya ce A kawo masa ita Yumna ta mike ta ɗaukota.
    “Yauwa my super women ɗina.”
    Haka yake kiran Yumma a cewarsa tana da karfi.
    Sannu da zuwa muka yi masa gabaɗaya ya amsa yana kallon mu ɗaya bayan ɗaya har yaran yadda suka ba je a falo suna cin tuwo.

    “waye ya yo gayyar a cinye mini abinci.”

    Ina dariya na ce masa Rabi’atu na bashi labarin kwaɗayi ya sa ta jiyo kamshi ta bar fushin ta shigo.

    “Ai da man cikin nan nata akwai son daɗi”

    “Abba wallahi tuwon ya yi daɗi ka ce Umma ta karo mana “

    In ji Rabi’atu

    “Ni kuma sai ma ci me?

    “Ka sha tea mana.”

    “Hararanta ya yi kafin ya ce” Ke ki sha tea ɗin mana. Na ki wayau wanda kuka ci sabil ne”

    Na ce ƙwarai, dole suka haƙura aka ba je kajin da tsiren da Yallaɓai ya siyo suna ci suna hira, Yallaɓai ya miƙa ma Gimbiya ɗiyar ta ya miƙe yana faɗin.
    ” Sadiya ta mu je kin ji.”
    Ya fada har yana miƙo mini hannu na kama yaran nan suka saka mana ihu.

    “Kuna fita za mu cinye tuwon nan”

    In ji Gimbiya Yallaɓai na jin haka ya ce” To koma ki haɗo komai ki same ni a can”
    Ya wuce ya fita bayan ya ba ni ledan hannun shi. Na koma kitchen na hada ƙomai a saman ƙaton faranti na saka lulluɓi na fito ina faɗin” Jama’a mu kwana lafiya.”

    “Mu kwana lafiya Uwargidan Yallaɓai.”

    In ji Gimbiya Rabi’atu dai ba ta yi mgana ba ita har gobe ba ta iya boye motsuwar kishinta.

    “Umma sai da safe”

    In ji Jidda na amsa ina faɗin su rufe kofa in za su kwanta.
    Yumna ta biyo ni tana faɗin” Umma nima za ni wajen Abba”
    Yarinyar nan shegen wayau ne da ita haka nan na rasa yadda zan yi da ita da na ce Jidda ta kamata ma kuka ta saka haka nan na ta sa ta gaba muka tafi. Ko da na je har Yallaɓai ya shiga wanka sai na kunna mata cartoon ni kuma na shirya mana dining sai da na kira wayar Jidda na ce su kawo min kunin aya da na haɗa yana nan a fridge da Baby ta kawo ne na samu na yi ma Yunma wayau na ce ta ma yar mini da mayafina ganina nan zuwa.

    Sai da na gama shirya komai a falo sannan na shiga ciki na samu Yallaɓai ya fito wanka yana ɗaure da babban towel a ƙugunsa.

    “Sadiya ta.”

    “Yallabai na.”

    Muka kalli juna muna mirmishi.
    Ni na taya shi ya shafa mai ya saka jallabiya baka muka fita falo, a kasan cafet ya ce mu zauna nan muka ba je muna cin tuwo muna tuna rayuwar amarcin mu muna dariya.
    Ya shayar da ni kunun aya nima na shayar da shi.
    Ya zaunar da ni a kan cinyarsa ya ba ni kaza a baki nima na ba shi, bayan mun gama na kwashe komai na kai kitchen na gyara falon muka je tiolet muka wanke baki. > Janaftybaby: Na cire dankwali na bar masa gashin tunda yana so shima daga shi sai gajeren wando ya cire jallabiyan muka kashe hasken falon sai na tibi muka makale juna muna kallo muna kuma sumbatar juna.

    “Sadiya ta.”

    “Uhm”

    Na amsa ina kwance a kirjinsa.

    “Na gode’

    “Na gode.”

    “Godiyar ta mene ne?

    “Da kika zama ni na zama ke. Da kika yi ta hakuri da duk wani gwagwamaya har tarihin mu ya kawo yau. Na gode da zamowarki TUKEN GIDANA. na tabbata ban yi turken banza ba. Kin kasance mai karfon da duk matar da na auro a kan togacin ki za ta kafa na ta igiyan. Na gode a jiya da shekaranjiya na gode a yau na kuma gode miki a gobe.”

    “Kai ne turkena Yallaɓai na.”

    Na amsa masa ina mirmishi sai ya ɗago ni ya fara sumbatata nima sai na tallabe shi.
    Na tsawon mintina muka saki juna muna ma yar da numfashi.

    “Sadiya ta “

    “Uhm”

    “Har yanzu dai ruwa na mganin dauda.”

    Ina mirmishi na ce” Yana yi sosai ma.”
    Na faɗa ina shafa kirjinsa zuwa kasan maran shi hannuna ya riƙe jikinsa na rawa.

    “Sadiya. Ta”

    Uhm”

    “Yau zan shanye ki ne fa.”

    “Nima zan shanye ka.”

    Na faɗa cikin wani yanayi, a wannan daran a saman wannan kujeran Yallaɓai ya biga half time ɗin shi sannan muka ranka ya ciki ya buga roud ɗin shi da kyau. Ba mu muka yi barci ba sai biyun dare da asuba bayan ya dawo sai da ya ƙara saka muka yi facal-facal da ruwa. Ya kwanta barcin safe na fita na je na duba yara da kwana sai na tsaya na yi masa abin karyawa na yi wanka har Sadi direba ya tafi da yara makaranta Yallaɓai saboda gajiya bai fito ba.

    Na koma shashen shi domin na tashe shi ina shiga bedroom na ga baya nan na ɗauka ma yana tiolet ne ina jiyowa na gan shi a bayan ƙofa sai ya fara takowa gabana yana yi mini mirmishi.

    “Yallaɓai ka sake biya mini Umra ne?

    Na faɗa ina mirmishi har hakorin makkan da na sanya yana bayyana.

    “Assalamu alaikun farincikina!
    gani na zo gun mai haskaka raina !”

    Na kwashe da dariya ganin Yallaɓai ya dage yana yi mini waƙa.

    “Yallaɓai yau ka zama romie ne?

    ‘”kar ki manta ke ce kaɗai abin faharina.”

    Ya faɗa yana mai ɗaga hannuna yana juyi da ni ina ta dariya dariyan farinciki da muradi mai girma.

    “SADIYA KAR KI SAKE DA NI KO WATA RANA,…!”

    Ya faɗa yana mai sumbatar goshina.
    Shigewa jikinsa na yi ina mai ƙamƙame shi.

    “Ba zan bar ka ba ko wata rana Yallaɓai ko mutuwa ce ta bari sai mun tsufa sai ta ɗauke mu a tare.”

    “in sha Allahu.”

    “Ina son ki Halimatuna.”

    “Ina son ka Yusuf ɗina.”

    Sai na dago kaina na ɗage kafafuwana na tallaɓo kan shi na fara sumbatar shi, shi kuma sai ya riƙe keyata ya juyar da ni ya haɗa ni da jikin ƙofa ya fara mayar mini da martanin gayyatata da zafi zafi.

    “ALHAMDULILLAH*

    _ALHAMDULILLAH KARSHEN LABARIN TURKEN GIDA, ABIN DA NA RUBUTA NA DAIDAI ALLAH YA BA NI LADAN TARE DA KU GABAƊAYA. KUSKUREN CIKI ALLAH YA YAFE MINI, KU YI HAƘURI WATAƘILA, NA KARKACE TA WANI BANGAREN. KUN SAN ƊAN ADAM AJIZI NE, TARA NA KE BAN CIKA GOMA BA, NA GODE BISA JIMARIN BIBIYATA, NA GODE BI SA MARTABAWANKU, NA GODE BISA GIRMAMAWANKU, NA GODE BISA YARDA DA AMINCEWARKU GA RUBUTUNA, NA GODE UBANGIJI YA YI MA RAYUWARKU ALBARKA ALLAH YA BIYA KU, YA KUMA HAƊA MU A ALJANNA. NA GODE SOSAI._

    *SAI MUN SAKE HAƊUWA A WANI SABON LABARIN IN RAN MU YA KAI. NA GODE*
    *MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE*

    Note
    error: Content is protected !!