Search
You have no alerts.
    The Den of Novels
    Chapter Index

    *MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE*
    “Da man na san za ta kira.”

    Ya sake faɗa lokaci ɗaya da ƙwatanƙwacin irin mirmishin da ya yi a farko lokacin da na ce an kira wayarsa.

    Gabana ya sake faɗi ras! Ba tunanin komai na kawo ba sai tunanin Yallaɓai ko dai ya fara bin mata ne? To ni dai ban san wannan yarinyar ba sai yau amma shi a yanayin da ya nuna kamar ya jima da sanin ta. Sannan fuskarsa ta bayyana asirin zuciyarsa na yadda take da muhimmaci a wajen shi koda bai furta da fatar baki ba.

    “Yallaɓai.”

    Na faɗa jikina na rawa tare da zuciyata ban san ma na sauke kafafuwana daga harɗe sun da na yi ba sai da na ji suna karkawa, tare da dukan junansu saboda tsoron tunanin da ya shige ni yanzu nan.

    “Na’am.”

    Ya faɗa yana mai kallona fuskarsa ba alamun wani firgici ko nadama.

    “Me ya faru?

    Ya faɗa yana mai sake kure ni da ido, sai na ga kamar yana neman raina mini wayau bayan ya san abin da ya faru amma kuma yana sake kallona yana tambayata me ya faru?

    “Wa ce ce Rabi’ atu?

    Na fada da sigar tambaya amma a rarrabe saboda fargaban amsan da zan ji ya faɗa mini. Ni fa cikina har curewa ya yi waje ɗaya nima ina jin kamar in na yi motsi zan iya barkewa da zawo saboda zullumi.

    “Wata ce ba ki san ta ba.”

    Ya faɗa yana sauke rigar hannunsa a saman gado. Sai kuma ya saka hannu ya ɗauki wayarsa yana dubawa.
    Mirmishi yake yi alamun yana karanta saƙon nata ne.
    Ban san ina da wannan ƙarfin ba sai da na ganni tsaye kan ƙafafuwana lokaci ɗaya kuma na saka hannuna da ƙarfi na fizge wayar daga hannun shi.

    “Wace ce Rabi’atu Yusuf ina tambayan ka kana faɗa mini wai ban santa ba. Wace ce wannan yarinyar ehe?

    Na faɗa ina mai ɓoye wayar a bayana sannan cikin ɗaga murya nake maganar. Ni fa na gama tunanin kaf na haɗe shi waje ɗaya Yallaɓai ya fara neman mata a waje shi ya sa yanzu ba shi da lokacin mu.
    Innalillahi Wa’inna alaihirraju’un. Nake nanatawa a cikin zuciyata lokacin da na ga kawai ya kalle ni amma bai yi magana ba.

    “Yusuf wace ce Rabi’atu?
    Kar dai a ce abin da zuciyata take zargi akan ka gaskiya ne?

    Na faɗa ina jin zufa na taruwa a saman hancina tsabar tashin hankalin da nake ciki.

    “Me zuciyarki ke tunani na a kaina Sadiya?

    Ya faɗa hankalin shi a kwance har yana karya hannayensa a saman kirjinsa alamun bai damu da yanayin da na shiga ba.

    “Yusuf neman mata ka fara yi? Mu har ka gama moran mu ka fara hango matan bariki?

    “Subhanallah wannan mganar bai da ce ba Sadiya. Allah ya tsare ni da aikata ɓarna. Ban yi da ƙananun shekaru ba sai da girma ya kama ni Sadiya?

    Ya faɗa a yanayin muryansa da ɗan bacin rai kaɗan. Domin har yana sauke hannuwan shi ya nufe ni da su yana faɗin.

    “Taho mu zauna na yi miki bayani.”

    Da sauri na ja baya domin ni kawai idanuwana suna hango mini Yallaɓai wasa yake son yi da tunanina shi ya sa.

    “Na saurare ka? Me za ka faɗa mini? Tun farko me ya sa da na tambayeka wace ce ita ba ka faɗa mini ba?

    “To mun bar ɗakin nan ne kika ga ban faɗa miki ba? Da man ko ba ki gani ba ina da shirin sanar dake a kwanakin nam.”

    Sai kawai na saki baki ina kallon shi, a gefen gado ya zauna hankalin shi kwance.

    “Na ce ki taho dai ki zauna mu yi magana.”

    Ya faɗa yana nuna mini gefen sa, sai na ɗauke kaina kafin na jijjiga jikina ina faɗin” In ba ka yi lalacewa kana matashin ka ba, yanzu da ka haɗu da yar iska yar bari..”

    “Ya isa haka Sadiya.”

    Ya ɗaga mini murya sannan ya ƙara da ɗaga mini hannu abin da ya hana ni ƙarisa maganar da na ɗauko. > Janaftybaby: “Me ya sa kika kasa shaida na ne Sadiya? Ashe ba za ki iya rantsuwan a kan bayan ku da kuke gonakin da Ubangiji ya hallata mini ba, ba zan iya shinshinar gonar da ba mallakina ba ne? A she ni ba za ki iya mini wannan shaidar ba?

    “Ɗan Adam mai sauyawa. Tun ballanta jinsin Namiji. Me ye kake ɓoye-ɓoyewa in ba wata yar bariki ka samu a waje tana ɗauke maka hankali ba?

    Na katse shi nima ina taso masa sai kawai ya yi shuru amma ya kalleni yadda na firgice da zargina shi ya sa sai ya gyaɗa kai kafin ya ce” Ko dai mu jinsin maza muna sauyawa amma ba sauyawa ta wannan bangaren ba Sadiya. Ba maganar yar bariki kuma ki daina faɗa, ba ki san wace ce Rabi’atu ba, sabo da haka ki daina danganta da sunayen banza.”

    “Ƙarya na yi. Wace ce ita in ba yar bariki me bin mazan wasu a titi ba?

    “Ba ita ce ke bi ni ba. Ni ne ke bin ta Sadiya.”

    Ya faɗa yana kallona. Kamar an iska ya wuce ta gefen kunnuwana haka na ji kamar sautin wani abu ya wuce.
    Shuru na yi ina kallon shi, shima ni yake kallo.

    .”Me ha kan ke nufi?

    Na faɗa ina mai raba bakina saboda rawan da ya fara yi mini.

    “Sadiya Rabi’atu ba karuwa ba ce sannan ba ƴar bariki ba. Yarinya ce da ta fito daga gidan tarbiya da dattako.”

    Ni fa duk ba nan na ke so ya je ba. Matsayinta a rayuwarsa na ke son sani.

    “Ni na ganta na ce ina son ta.”

    Sai na yi ma Yallaɓai zuro kamar na warke makanta.

    “Kuma AURANTA zan yi in sha Allahu “

    Shike nan ƙurungus kan kusa. Ni gabaɗaya na sha’afa idanuwana sun rufe na manta cewa bayan biyu. Ubangiji ya ce su cike huɗu in har za su yi adalci, na sha’afa da cewa bayan mu akwai guraben mata biyu, tunanina da zuciyata kawai suna hasko mini Yallaɓai ya fara neman matan bariki saboda yana da kuɗi. Su kuma matan bariki da man in har kana da kuɗi shike nam za su tallata maka ƙofar lalacewa.
    Na manta yadda ya aure ni ya kuma auri Gimbiya. To watan wata rana in ya yi ra’ayi zai iya auro wata ko wasu ma biyu bayan mu. Na manta ko na ce ban ɗauka yanzu ba ne. Kamar yadda auran shi da Gimbiya ya shammace ni haka labarin wannan auren ma ya sake shammata na.

    Na kasa motsi daga in da nake tsaye. Zuru kawai na yi ina bin Yallaɓai da kallo shi kuma ganin haka sai ya taso ya zo ya kamani ya zauna da ni a gefen gado sannan ya kuma ya zauna a gefen har yana dafa kafaɗata hannunsa na rito a wajen kirjina.

    “Bayanin da nake so ki zauna na yi miki ne tun farko kika kasa zama ballanta ki fahimce ni.”

    Ya faɗa yana mai kallon fuskata. Nima shi nake kallo, na tuna ni ce nan na sha cika bakin cewa in Yallaɓai ya tashi kara aure ba zan damu ba domin ni ya gama yi mini kishiya, Gimbiya ce ke da wannan ƙuncin ba ni ba, ban tabbatar ma da kaina kishi sunan shi Kishi ba sai yau, domin sai na ji wannan ƙullutun abin da ya taɓa tsaya mini a ƙahon zuciya a daran da na samu labarin Yallaɓai ya auri Gimbiya. Irin shi ne na ji ya tokare mini zuciya. Ya yi sanadiyar rufe bakina da kassara sauran kuzarina.

    “Ba ki ji komai ba Sadiya ta?

    Ya faɗa yana leƙen fuskata. Kamar an ƙwato numfashina haka na ji na saki ajiyar zuciya mai ƙarfi sannan na kalli Yallabai. Sai ga ni jiki a sanyaye ina mai mikar masa wayar sa, ya saka hannu ya karɓa.

    “Ka yi haƙuri ban san haka maganar take ba.”

    Na faɗa cikin sanyin murya. Sai na ji kwarmin idanuwana suna cika da kwallah. Sai ya fara dariya yana faɗin” Me ya faru? Ni ba ki yi mini laifin ba ni haƙuri ba na ji daɗi da kika zama mace ta farko da kika fahimci ina boye miki wani abu.”

    “Gimbiya ma ta sani.”

    Na faɗa ina kallon shi, sai ya kalle ni cikin mamaki.
    A hankali na warware mishi yadda muka yi da ita.
    Sai ya jinjina kai kafin ya ce” Allah Sarki ƴan mata na. Ina son ku wallahi.”
    Ai ni ko jin sa ban yi ina cam na tafi duniyar tunani.
    Aure. Aure fa Yallaɓai ya ce zai ƙara, in a da ina raba shi da kwana biyu ne yanzu fa sai dai kwana huɗu. Kai innalillahi.

    Haka nake faɗa a ƙasan zuciyata. Gabaɗaya jikina ya yi sanyi kamar an yi mini duka.

    “Da man lokaci na ke jira na same ki mu yi maganar nan. Wallahi tallahi ban da ke ko Nene da yan uwana ba su san da labarin Rabi’atu ba.”

    “Nima ai ban sani ba, ba ka faɗa mini ba sai da na gani da kaina.” > Janaftybaby: Na faɗa kamar zan yi kuka sai ya rumgumo kafaɗata yana faɗin” Allah shi ne shaida na. Niyyata cikin satin nan na ke da niyyar faɗa miki, kin san ba ni da wata abokiyar shawara sama dake. Ni da ke mun kai wani matakin da ba zan iya ɓoye miki komai ba, da man na ce sai na yi magana da ke sannan zan je na yi magana da Nene.”

    “Uhm”

    Kawai na faɗa domin na kasa magana ko na ce ba ni da ta cewa ne kwata kwata kamar an shafe manganganun dake cikin ƙwaƙwalwata.

    “Da gaske na ke yi Sadiya ta “

    Ya faɗa yana wasa da yatsun hannuna guda ɗaya da ya kama ya riƙe.

    “Ko da gaske ne ni na isa na hana ka ƙara aure ne? Ai kamar yadda ka yi na farko ban iya hanawa ba wannan ma sai dai na sake yin maka fatan alheri.”

    “Na san baki isa ki hana ba. Amma ai kin isa na yi shawara da ke ko?

    “Sabo da mene?

    Na faɗa ina kallon shi.

    “Saboda ke kin zama TURKEN GIDA na. Ban isa na zartar da wani hukunci ba tare da na nemi shawaran ki ba. Duk da ba ki isa ki hana ba amma kin isa ki nuna mini abin da nake ƙoƙarin yi in mai kyau ne ko akasa sa, Sadiya kina da wata daraja mai girma a zuciyata da na ke girmama manganganunki. Na ke kuma kambama tunanin ki a kaina. Na tabbata ke mai adalci ce mai kau da kai mai haƙuri da hangen nesa. Kamar yadda kika saba ba ni shawara da zuciya ɗaya yau ma ina da yaƙinin da zuciya daya zaki ba ni dukkan shawarwarin da na ke son samu daga gare ki”

    Koda a ce daɗin baki ne na Maza to ni dai wallahi ya yi tasiri a kaina, har ban san ina ta mirmishi ba kaina ya yi girman da na ji ashe nima na isa a wajem mijina ban sani ba.

    “Da gaske Yallaɓai na?

    Na faɗa ina yi masa mirmishi duk da a ƙasan zuciyata nauyi na ke ji, amma bai hana daga can sama wata tsoka ta jin daɗi ta motsa mini ba.

    “Haba. Kike tantama? Ke ce fa mafarin Yusuf, ke ce da shi a shekaranjiya da jiya har da yau. Bayan iyayena ke ce macen ta farko da zan nuna da ta yi ma rayuwata hidima. Ki sani ke ɗin ta musamman man ce a wajena. Anan ƙarƙashin nan na ke jin tarin hidimarki a gare ni “

    Ya faɗa yana taɓa wajen zuciyarsa da hannuuwana da ya riƙe, sai gani kamar shashasha ina ta dariya da mirmishi.

    “Na gode da Martabawa Yallaɓai.”

    “Nima da na gode da hidimantawa My Sady”

    A tare muka kalli juna sannan muka yi mirmishi sai na faɗa jikinashi ya rumgumeni cikin rumfar hannayensa masu zame mini garkuwa a koda yaushe.

    “Wata shawara kake buƙata daga gare ni?

    Na faɗa ina kwance a saman ƙirjinsa.
    Sai ya dago ni muna kallon juna kafin ya riƙe dukka hannayena guda biyu ya fara faɗin.

    “Rabi’atu yar maiduguri ce amma zama ya kawo ta nan Kano. Akwai Baffanta a nan garin ƙanin mahaifinta kenan bayan rasuwar mahaifinta shi ya karbeta ta dawo hannun shi tun tana JSS3 Ga shi yanzu har tana karatu anan BUK ajin ta ɗaya.”

    “Ina jin ka.”

    Na faɗa ina kallon Yallaɓai domin ganin yadda ya natsu kamar Nene ce a gaban shi ba ni ba.

    “Mun fi wattani biyu da haɗuwa. Kuma ni dai yanzu ina matakin na gabatar da kaina a wajen Baban nata ne.”

    “A ina kuka haɗu?

    Na samu kaina da yi masa wannan tambayar
    Saboda ni dai a sanina ba ruwan Yallaɓai da yan mata amma sai ga shi ya zaunar da ni yana ba ni labarin budurwa.

    “A bakin BUK new site. Na je yi ma wani abokin karatun mu murna ya samu koyarwa a wajen shi ne bayan na fito na haɗu da ita tare da ƙawayenta su biyu.”

    “Sai ka rage musu hanya ko?

    Na faɗa ina kallon shi sai ya fara dariya kafin ya ce” E. Ranar alhamis ne, daga cikin makaranta za su je gida Weekend. Sai na rage musu hanya na kai ƙawayenta gida itama na kai ta daga baya.”

    Sai na samu kaina da yin mirmishi kawai.

    “Kuma suka yadda suka shiga motarka ba su san ka ba?

    “Ni na yi ta bin su ina yi musu magiya.”

    Ya faɗa mini gaskiya da na ji da man ban tambaya ba. Da man bayan ni akwai wata macen da Yallaɓai zai iya yi ma magiya! Kin manta da Gimbiya? Wata zuciyar ta tunasar da ni.

    “To kin ji yadda muka haɗu da Rabi’atu”

    Sai na kalle shi, na ɗauka bayan ni Yallaɓai ba zai ji daɗin faɗin sunan wata mace ba, sai ga shi a gabana yana kiran sunan wata macen cikin shauƙi da muradi.

    “A hostel take zaune kenan?

    “E. Can take zaune sai bayan sati uku take zuwa gida Wekeend” > Janaftybaby: “Can kake zuwa taɗi kenan?

    “E to wani lokacin. Amma har gidansu ina zuwa.”

    “Can Maidugurui?

    Sai ya zaro mini ido kafin ta ya ce” Gidan Babanta dake Kano dai, Maiduguri wataƙila sai mun je ɗaurin aure.”

    Sai na jinjina kai na ma kasa mgana. Yallaɓai ya riga ya gama tsara komai shi da yarinyar.

    “Kana son ta ne haka sosai?

    Sai ya fara sosa gira. Sai kawai na yi mirmishi kafin na ce” Ko ba ka faɗa ba labarin zuciyarka fuskarka ta bayyana mimi.
    To ita nata sonka kamar yadda kake son ta?

    “Ofcourse. “

    Sai muka kalli juna sai ya rage zumudin ya dan saussauta murya kafin ya ce” Na ce mata bana som auram ya wuce wata uku ta ce ta amince.”

    To da mam za ta ki ne, me Yallabai ya rasa? In ba ya faɗa ba ba mai ganin sa ya ce ya kai shekaru arba’in da tara, yana nan a matashin sa, kamar ɗan shekara talatin da ɗoriya. Balle ga ƙudi ga rufin asiri ga iya gayu ga kalamai ta same shi me za ta tsaya jira ban da ta amince?

    “Me kika ce?

    “Me zan ce?

    Na faɗa ina kallon shi.

    “Kice koma me za ki ce”

    “Ba abin da zence sai fatan alheri. Allah ya tabbatar Allah ya haɗe kawunan mu ya kauda da fitina.”

    “Amin Amin My Sady. Amma wattanin ukun ba matsala?

    “Babu tun da ka shirya.”

    “Gida ne, kuma in ba su ƙarisa ba zan ce a gyara mata shashe ɗaya ta fara tarewa. In ya so bayan bikin in an gama gyara na ku ke da Daughter sai ku tare a lokaci ɗaya.”

    Sai na kalle shi kafin na ce” Kana ganin Matarka za ta amince?

    “Me ya sa ba za ta amince ba? Ai ba cewa na yi ba za ku tare gabaɗaya ba. Kuma tun da kika amince itama za ta amince in sha Allahu.”

    Sai na samu kaina da cewa Allah ya sa. Ban ce ina son ganin hoton ta ba amma sai da ya nuna mini a cikin wayarsa..
    Ba Yallaɓai da yake matsayin namiji ba har ni mace kyan yarinyar ya dake ni. Tabbas yar maiduguri ce fara ce tas ga gashi har gadon baya ga diri. Masha Allah hancin nan har baka, ga ta doguwa sai dai yarinya ce wannan ko za ta girmi Jidda da ƙadan ne.

    “Ta yi kyau. Allah ya sanya alheri.”

    “Amin Amin. Itama na nuna mata hoton ki.”

    Ban yi magana ba sai dai ina ta kallon shi.

    “Ta ce ganin ki ya fi jin ki.”

    Ya faɗa yana dariyan nishaɗi.

    “A ina take jin labarina?

    “A bakina mana. Ai ba za mu hadu mu rabu ba ta ji sunan Sadiyata a bakina ba.”

    Na yi zuru ina kallon Yallaɓai yana labarin budurwansa cikin nishaɗi.

    “Ta ce duk yadda aka yi ina ji dake. Na ce sosai ma ko ita na faɗa mata in har tana so ta kama babbar fada to ta kama kafa dake domin har ni juyanj kike yi “

    Ni kaina sai da na yi dariya kafin na ce” Kar ka jawo mini ta shigo da shirinta sabo da ni.”
    “Haba. Ai Rabi’atu ba ruwanta.”

    “Uhm”

    Na faɗa a ƙasan makoshi to wai ba ruwanta Yallaɓai da neman suna.

    “Tana ce mini Yallaɓai na ce ta bari kada ki ji ta. Ko a ma’aikatana ba mai kirana da Yallaɓai sai dai Oga ko Injiniya saboda ba na jin daɗin sunan a bakin kowa sai a bakin ki.”

    “Ai sai na bar mata sunan. Ita ce amarya mu ai mun tsufa.”

    Na faɗa ina kallon shi hAr na fara tausayin Gimbiya. Domin rawan ƙafan da Yallaɓai zai yi a kan yarinyaa nan, sai ya ce bai yi komai a lokacin auran ta ba.

    “Ta ce tana som sunan sai dai ku riƙa kirana ke da ita.”

    “A’a ni fa na bar mata sunan. Ai na ɗana ina laifi mun sha miya ita kuma yanzu take.”

    Yana wata dariya nishaɗi kafin ya ce” To ni kuma sai na koma wani suna a wajen ka?

    “Ah sunan ka mana.”

    “Yusuf gatsal?

    Ya faɗa yana waro mini ido sai na gyaɗa masa kai ina yar dariya.

    “Tab. Ban yadda ba, sannan ban amince da wannan maganar ba. Sai ita ta sauya amma ni ba zan sauka daga kam mikamina ba “

    Ni dai sai bin Yallaɓai nake yi da kallo ina jin abin a zuciyata. Yallaɓai na zaunar da ni yana ba ni labarin wata macen cikin jin daɗi da annushuwa.
    Da bakin shi yake faɗa mini yau na sun fita ne, ya je makaranta ya ɗauke ta sun je shooping daga nan suka biya restaurant suka ci abinci anan ne ya ci wani ferfesun kifi ya lalatamai ciki kwana ya yi yana gudawa. Sai da asuba na bashi sauran flajin ɗin da nake da shi ya samu ya sha guduwan ya tsaya amma har da ciwon ciki shi ya sa da safen bayan ya yi wanka ya fita ya ce zai fara tsaya ta asibiti a ba shi magani. > Janaftybaby: Sannan ya biya makaranta su Baby kafin ya wuce office tun da ya ce mata zai shigo makarantan na su yau.

    Har ya fita ya bar ni, ina cikin mamakin manganganunsa jiya, shi kenan kuma tun da ya faɗa mini sai ya samu kofa in dai yana gidana sai ya kawo sanadin da zai yi labarin Rabi’atu. Aikin sa kenan tana gaishe ni na ce ina amsawa, ban san yadda suka kare da ƴan uwan shi ba amma ni dai kawai ya ce mini ya yi magana da Nene, na san da man ba za ta hana shi ba shi ya sa ban matsa sai na ji amsarta ba. Ni dai ban yi taɗin da kowa ba ko su Munnira saboda na kasa iya sarrafa harshe wajen ba da labarin wai Yallaɓai zai ƙara auro zai auro yar yarinya ɗanya shakaf, mu kuma da man tafiya ta tafi jiya ba yau ba. Ko naƙi ko na so ba zan koma kamar Sadiya a jiya ba. Sai dai na koma Sadiya a yau har shekara arba’in da wani abu a duniya. Duk gyare-gyare na ban isa na koma kamar budurwa ko yarinya ba. Dole dai wajen ya saki tun da jiya ba yau ba ne. Itama Gimbiyar ni da ita duk samkal ne, tun da tsere yan mu a shekaru ba nisa sosai itama ai ta kama gidan arba’in. Tun da yana da kuɗi zai buƙaci canji yanayi.

    Duk ƙoƙarina na kar ƙarim auran Yallaɓai ya dame ni na kasa. Abin ya tsaya mini a zuciya amma ina ƙoƙarin yakicewa saboda na zauna lafiya. Yallaɓai da bakinsa ya faɗa mini Kawu zai zo za su je su gabatar da kansu wajen baban Rabi’atu. Kuma ya zo sun je ɗin ya dawo yana faɗa mini ya yi musu karamcin amma ya ce su je zai neme su da kan shi. Yallaɓai rawan ƙafa kawai yake yi bai ƙi a ce gobe ma an ɗaura auran nan ba gyaran gida kam tuni ya tsaya bangaren da Rabi’atu za ta fara tarewa ma’aikata suka raja’a duk da namun ma fenti ne ya rage sai tayels da za a sanya amma ita bangarenta har tayels ɗin an saka kaɗan yarage a ƙarisa. Da bakinsa yake sanar da ni in ma an gama da wuri ba zai bari a saka lokacin bikin ya kai wattani uku ba.

    Duk wannan bidirin da yake yi ban sam bai sanar da Gimbiya maganar da wuri ba. Na ɗauka yadda ya faɗa mini itama ya same ta sun yi magana ashe bai sanar da ita da wuri ba, ni kuma gani na yi ba hurumina ba ne shi ya sa ban yi azaɓarɓaɓin bakin kiranta in faɗa mata tun da ba ni ba ce mijinta.
    Kawai sai wayarta na samu kwana biyu tsakani da zuwan su Yallaɓai gaban Baban Rabi’atu.

    “Maman Jidda kin manafunce ni.”

    Haka ta fara ce mini da na ɗauki wayarta da sallama.

    “Ikon Allah. Munafuncin mene kuma?

    Wataƙila kuka take yi domin tana ta jan hanci.

    “Ba ki faɗa mini Daddy aure zai ƙara ba. Sai da kowa ya gama jin magana sannan ya faɗa mini.”

    “Ai ba hurumina ba ne na sanar da ke. Shi ya sa ma kika ji ban yi miki maganar ba.”

    Na amsa mata, gaskiya na faɗa mata ba bangarena ba ne.

    “Amma ai mun yi magana da ke na ce ki bincika a bangarenki nima haka. Abin da muka sani mu faɗa ma juna me ya sa kika boye mini? Ahalin da bakin shi ya faɗa mini ke ya fara yi ma maganar kafin ma ya sanar da Nene?

    Sai na saki baki kawai kamar tana ganina saboda na ga kamar tana neman ta ɗora mini jakar tsaba ne.

    “Nima bai sanar da ni ba sai da na ga kiranta sannan na tambaye shi wace ce ya faɗa mini. Ki yi haƙuri in rashin faɗa mikin da ban yi ba ya yi miki ciwo. Na ga ba hurumina ba ne sanar dake shi ya sa”

    “Wallahi Daddy bai isa ya auro wannan yarinyar ba. Anty Bahijja ta faɗa mini yarinya ce ƙarama kamar sa’ar Jidda shi ko kunya bai ji ba? Da me muka rage shi?

    “Ta ɗan girme ma Jidda gaskiya.”

    Cikin mamaki a muryanta ta ce” Kin santa ne?
    “A’a ya dai nuna mini hoton ta na ganta. Kuma ya faɗa mini shekarunta.”

    Sai kawri Gimbiya ta yi wani jan numfashi kafin ta ce” Da man yana ta cika baki da cewa
    Ko a lokacin aurena ba ki bashi matsala ba wannan ma yana fsɗi da fahari ba za ki bashi matsala ba. “
    “To matsalan me? Ai ko na yi kishi da hauka ba shi zai saka ya fasa ba. Sai ma ni na zubar da ƙimata. Kema ina mai baki shawara ki yi haƙuri duk da akwai zafi amma in ka daure sai komai ya zo ya wuce.”

    “Tab. Wallahi ni ba zan yi munafunci saboda namiji ya so ni ba. Matsala kuma a wajena yanzu ya fara gani.” > Janaftybaby: Kafim na na yi magana ta katse kiranta sai na bi wayar da kallo kafin na furta” Ikon Allah!
    In na fahinceta ni ce mai yin munafuncin saboda Yallaɓai ya so ni, sai da na yi mirmishi Gimbiya kenan, ni fa ba zan yi tashin hankali da faɗa saboda Yallaɓai zai ƙara aure ba, yadda ban yi a baya ba yanzu ma ba mai sskani na saka kaina a cikin damuwa. Na san ba zai fasa ba kuma a yadda Yallaɓai ke ji da yarinyar nan wallahi Gimbiya ta ce za ta bashi matsala to shi zai iya nesa da ita saboda ya samu masalahan na shi muradin. Tana tunanin ina yin haka ne saboda ya yabe ni, ba ta sanni ba ne ni fa ban yarda na zubarma da kaina ƙima saboda namiji ba, a je dai a dawo suna ne zai yi tambari na bar ma kaina da ƴaƴana abin kunya daga ƙarshe ya yi auran shi to wa gari ya waya? Shi ya sa na koma ga Allah ina faɗa masa damuwa da fatan ya cire mini damuwa da tunanin ƙarim auren da Yallaɓai zai yi. Kuma Alhamdulillah na fara ganin canji.

    Yadda ko ƴan uwana ban yi zencen da kowa ba. Haka ƴaƴana kamar yadda ya sanar da su na auran Gimbiya wannan ma ya sanar da su da bakin shi. Jidda jarabawa ma suke yi jibi za su gama za ta dawo gida Baby kuma sun fara Jsce ta gama ajin ukun ƙaramar sakandiri. Duk ta buɗe tantanin budurci ya bayyanar mata. Wancan watan ta fara jinin al’ada gashi ta fi Jidda manyan gabbaina tun ba ta yi wani shekaru nanna sun cika mata ƙirji. Hankalina na mai da kan kula da tarbiyan yayana. Yallaɓai yanzu ba ma gaban shi hankalin shi da duka tunanin shi na kan yadda zai mallaki Rabi’atu ne shi ya sa nake yi masa uzuri.

    Ni ko da muka yi magana da Gimbiya ban yi ma ko Yallaɓai zencen ba, nima bai nuna mini a yanayin da suke ciki ba. Shi ya sa nima ban tusa kaina a cikin abin da ba ruwana. Jidda ta gama jarabawa ta dawo gida sai gidan ya yi daɗi na rage kaɗaici, har Yumna yanzu ta fi karsasshin wasa da dawowar Jidda har uban gayyar ma ya yi murna da dawowarta yana faɗa mata gidan ba daɗi da ba ta nan. Ban san me ya faru ba kawai na ga Yallaɓai ya kwaso mini su Khalipa da Anwar, na tamnaye shi lafiya? Ya ce ba komai. Ina maman su? Ya ce mini ta je Rano ta dawo. Ni kuma har ga Allah ban kawo ma kaina tunanin matssla suka samu da zuciya ɗaya na karɓi yaram gidan sai ya zama active saboda ɗan hayaniyarsu in sun tafi makaranta Jidda da Baby suna gida, in sun dawo gidan ya sake rikicewa da wasannin su tun ballanta Yunma da Yallaɓai ya gama ɓata ta da mugun wasa.

    Kwana uku tsakani ranar wata laraba Munnira ta kira ni a waya tace ko ina gida na ce mata ina gida. Sai ta ce mini gata nan zuwa, da maganar mu ba a daɗe ba sai ga ta tun da na ganta na san da magana. Na kuma san bai wuce labarin auran Yallaɓai da suka samu labari. A daran jiya yake faɗa mini Baban Rabi’a ya neme sa yau zai je su sake ganawa. Ina kuma da tabbacin ya gama binciken shi ne zai ce ya turo magabantan sa. Tun da Yallaɓai ba shi da abin ƙin daga asalin shi har rayuwarsa duk da ɗan adam tara yake bai gama cika goma ba.

    “Kwana biyu ke da Hauwa kun ɓoye?

    Na faɗa lokacin da na shigo falon, da man ina cikin bedroom ɗinna Jidda ta sanar da ni zuwanta.

    “Wallahi ya gida?

    Ta faɗa tana ɗaukan ruwan da Jidda ta kawo mata na gora ta zuba a kofi ta fara sha sai ni kuma na zauna gefenta ina faɗin” Ya yara?
    Kwana biyu ba mu haɗu ba.”

    Sai da ta gama shan ruwa ta dire kofin a saman centetr table ɗin dake falon sannan ta ce” Uhm ke ce ai kin ɓuya. Yanzu ma dalili ne ya sa na neme ki.”

    “Wai auran Yallaɓai?

    Na faɗa ina dariya.

    “Au ashe ma kin san abin da ya kawo ni.”

    Ina mata murmishi na ce” Na san dai yanzu shi ke trending.”

    “Uhm wai ashe Yallaɓai aure zai ƙara ba ki sanar da mu ba Sadiya?

    “Wallahi na kasa iya faɗa ma kowa. Amma na bari in an saka ranar sai na kira ku mu yi maganar.”

    “Da gasken gasken dai auren zai ƙara?

    Ta faɗa cikin tantama.

    “Ya wuce wai fa. Yau ma yace mini zai sake komawa Baban Rabi’atun ya sake neman shi.”

    Na faɗa ina kallonta.

    “Sunanta kenan? Rabi’atu?

    “E. Yar maiduguri ce amma an riƙeta anan Kano. Yarinya ce ƙarama ajinta ɗaya ma jami’a.”

    “Duk a ina kika san wannan labarin?

    “A ina kuwa? A bakin uban gayyae mana.” > Janaftybaby: Na faɗa ina dariya sai Munnira ta gyara zama tana faɗin” Ba Shakka.”
    Sai kuma ta yi shuru.
    “Ke a ina kika ji? Na tabbata dai maganar ba ta fita ba sosai.”

    “A bakin Jamila na fara ji, sannan jiya da daddare labari ya kawo labari Nasir ke faɗa mini. Ashe wai har sun samu matsala da mutuniyarki?

    “Wac ce?

    “Gumbiya mana.”

    Sai na ware ido kafin na ce” Subhanallah da shi Yallaɓan?
    Munnira ta yi dariyan mugunta kafin ta ce” Wai ita ana dole ba zai yi mata kishiya ba. Ta manta ke ma da ita aka yi miki kishiyar? Wanzami ba ya son jarfa”

    “Me ya faru ne! Ni wallahi ban sani ba. Na ga dai ya kwaso mini yara ya kawo mini da na yi magama sai ya ce bata nan ta je Rano.”

    “Af yaji ta yi “

    “Yaji?

    Na faɗa ina zaro ido.

    “Wallahi faɗa suka yi a yadda Nasir ya ce shi Ya Tafidan ya faɗa massa. Tun da ya faɗa mata zai ƙara aure ba su samu fahintar juna da zaman lafiya ba ranar kawai ta saci wayarsa ta dauki lambar yarinyar ta kirata ta yi mata zagin kare dangi. Ashe yarinya yar gari ce ta yi recording yana zuwa ta kunna masa shi kuma da ya dawo sai ya hau ta faɗa shi ne ta miƙe yana faɗa tana faɗa daga ƙarshe zai bar mata ɗakin ya ce ta ja masa riga har tana yaga masa, ta kuma ci kwalan shi ta ce in dai ya rantse sai ya yi auren nan da wannan yarinya ita kuma sai ya sake ta. A cewar sa ya yi ta ƙi sakin shi sai ya fizge kan shi ya ture ta gefe ta faɗi shine ta hau kuka wai ya daketa akan wata banza gari na wayewa ta tafi Rano har yau ba ta dawo ba shi kuma ya ce ba zai je ya yi bikonta ba tun da abin da ta yi rashin tunani ne.”

    Tagumi kawai na yi na ma kasa magana. Sai da na ce mata ta bi a hankali. Amma sai take ganin kamar ni ina goyon bayan Yallaɓai ne.

    “Na je Gwammaja jiya har Nene ba ta saka baki a maganar ba ta ce Gimbiyar ce ba ta kyauta ba.. aure ya ce zai ƙara ba wani zunibi ba”

    “Ina su Anty Bahijja?

    “Ohom musu. A bakin Suwaiba na ke jin Mimiaco ce kawai da Nene ke bayan Tafida. Anty Maimuma da Anty Bahijja duk yan bayan Gimbiya ne kar a yi mata kishiya.”

    Ban san ina dariya ba sai da na ga ina ƙyaƙyatawa.

    “Wato kar a yi mata kishiya tuj da ta su ce? Ni da bare ce ai suna gaba gaba wajen ba shi goyon bayan ni ya yi mini ko?

    “To da man. Ai ni farinciki na yi da zencen ƙarin auren na. Lokaci ya yi da Gimbiya za ta ɗanɗana abin da kika ɗanɗana ta ji in da daɗi.”

    “Wallahi. Welcome to the Game.”

    Na faɗa ina dariya har muna tafaww. Ba wai ina murna ba ne amma dai na ji daɗi a kallah dai za su san cewa yau gare ka ne gobe ga wanin ka jibi ma a kanka ne zai faru.

    Muna tare da Munnira har bayan la’asar sanman ta tafi, Yallaɓai da wuri ya dawo ya yi wanka aka saka manya kaya ana ƙamshi ya tafi. Tun kafin ya dawo ya kirani a waya da albishir ɗin Baban Rabi’atu ya ba shi da man ya tura magabantan shi. Murna kamar Yallaɓai zai yi hauka da ya dawo haka ya rumgumeni cak kuma ya ɗagani yana juyi da ni a tsakiyar falo gaban yara. Ni dai na daki kafadan shi ina faɗin ya sauke ni. Ai na ga abin mamaki haka ya bi su Jidda ɗaya bayan ɗaya yana rumgumansu cikin farinciki.

    “Abba me ya faru ne?
    Ko ka samu wasu kudaɗe ne?

    Jidda ta faɗa tana dariya.

    “Abin da na samu ya fi kuɗi daraja My Jidda. Ƙaramar Anty zan sake kawo muku.”

    Daga ita har Baby shuru suka yi kamar ba su gane ba.

    “Jidda Baby, aure zan ƙara. Baban Antynku ne ya ce na turo da magabatana.”

    “Allah ya sanya alheri Abba”

    Jidda ta faɗa cikin natsuwa its ko mara kai Baby sai ta fara tsalle tana faɗin” Abba yaushe bikin?
    “Ba zai ɗau lokaci ba?
    Ya faɗa yana shafa kanta falona ya kaure da ihun su har da su Khalipa da ba su san me ake ciki ba. Yumna ya ɗaga sama yana mata wasa kafin ya kalleni yana faɗin” Rabi’atu ta ce ita fa Yumna za ki ba ta.”
    “Ba dai uwata ba kam!
    Na faɗa da iya gaskiyata sai ya fara dariya.

    “Jidda zaki ba ta ko Baby?

    “Jidda ai ɗiyar Gimbiya ne. sai dai ko Baby ko Khalipa.”

    “Ta fi son mace ta ce mini. Kin san tana ganin hotin su a wayata. Ita dai Yumna take so.” > Janaftybaby: Ni tsabar mf zumuɗin Yallabai ya sa ban samu amsa masa ba.
    Abinci ma bai ci ya ce ya ci a can wai an kawo Baba ya ce sai ya ci shi kuma ya kasa yi masa gardama su Baba manya. Ina so na yi maganar Gimbiya ina jin tsoro kar ya ce na yi shisshigi, ganin yana cikin farinciki yasa na yi kumdunbala na yi masa maganar amma sai ya shashantar da maganar da cewa na ƙyaleta za ta dawo.

    “To ko za ka je ka dawo da ita ne? Ka yi mata uzuri kishiya fa zaka yi mata?

    Kawai ya taso mini kamar ni cw na yi masa laifin

    “Ke ba kishiyan na yi miki da ita ba, kin tada mini hankali? Ke da sai bayan an ɗaura ma kika sani kin sama mini zaman lafiya sai ita da na faɗa mata cikin lalama amma ba yadda ba. Kin ji irin zagin da ta yi ma Rabi’atu ba domin ta yi hankali ba ta biye mata ba daya kike tunanin lamarin zai tsaya? Kuma na so ina nuna mata kuskurenta amma daga ƙarshe ni ta yi attaking ina matsayin mijinta. Ban ce ta tafi ba amma tun da tafi wallahi kafata ba zai taka zuwa Rabo saboda ita ba kar Allah ya sa ta dawo ta gani in za a fasa komai ne saboda tafiyarta.”

    Ni dai haƙuri kawai na ke bashi domin na ga ya ɗau zafi da yawa.

    “Wallahi ko Nene na faɗa mata ta cire bakinta ba in da zan je kuma haka nan ta ƙyaleni . Kema abin sda zan ce miki kenan ki zura ido kawai ba ruwan ki a wannan maganar.”

    Tun da na ji har Nene ma an bata haƙuri ni a suwa sai na kama kaina..
    Yadda ma yake ta shirin turawan nan tuni ya shafe babin Gimbiya.
    Aure fa ya tabbata da gaske Ya Usman daga porthercout ya zo Kano saboda maganar. Shi da Tafidan Rano Baffan Gimbiya da Kawu Sa’adu da Kawu Abba da Tariq suka je neman ma Yallaɓai auran Rabi’atum

    Sun je da kudin gaisuwar iyaye dubu ɗari huɗu, ga kayan saka rana mota guda. An yanke musu sadaki dubu ɗari biyar, sanaan an yi maganar tana karatu zai barta ta cigaba. An saka rana wata ɗaya cikin na biyu. Ƙarshen January, shi Yallaɓai ma ya so ƙarshen watan Desember ne amma iyayenta suka ce aa a ba su lokaci suma ai suna da na su shirin sannan a garin maiduguri a gidan mahaifinta za a ɗaura auren
    . Duk da suka dawo a can gidan Nene suka yada zango. Ni kuma a bakin uban gayyar na ji labarin yadda ta kaya da ya dawo da daddare.

    “Ma sha Allah. Lamari ya yi daɗi Allah ya sanya alheri ya nuna mana lokacin da rai da lafiya.”

    “Amin Amin Abar ƙaunata.”

    Har yana sumbatar leɓena cikin farinciki, ranar a gaba ma Yallaɓai ya yi waya da Rabi’atun har ya na ba ni ita muka gaisa.
    Tana wani maƙale murya da na ce Allah ya sanya alheri ya nuna mana lokacin da rai da lafiya.

    “Amin Anty na gode.”

    Ta faɗa cikin sanyin murya. Ta tambayi su Jidda na ce suna nan gida an yi hutu.

    “Ina ta yi ma Yallaɓei magiyan ya kawo mini su ya ce sai ya tambaye ki “

    Ina kallon shi na ce” Ba ruwana ai shine shugaba abin da ya ce shi za a yi. Yadda ya dama haka muke sha.”

    Tana ta dariya ni kuma na yi mata alƙwarin in su Khalipa sun yi hutu zAi kawo mata su gabaɗaya sai da na ba shi wayar ya kashe bayan ya ce mata zai kira daga baya yake faɗa mini karshrn watan nan itama za ta je maiduguri. Sai dai ya kai su wani sati ta gan su.

    “Tana son yara na. Ko da yaushe sai ta yi mini ƙorafin na kai mata su. Jidda ma zan ba ta lambar wayarta itama zan ba ta nata su riƙa gaisawa.”

    “Hakan ya yi “

    Domin ni yanzu yar bi ce, in dsi akan auren nan na Yallaɓai nr, ga Gimbiya tana can har an saka rana shaida ba abin da za a fasa.
    Anty Zabba ta kirani a waya tana ta dariyan mugunta ta ce ai da Ya Usman ya faɗa mata ta buga guɗa. Itama har ta ji labarin Gimbiya ta yi yaji.

    “Sakara kawai. Wa ya faɗa mata ana cin riban namiji in har ya tashi ƙara aure? Ai da ta kwantar da hankalinta da ta ci riba.”

    Ni dai ban furta ba, domin har a cikin zuciyata ban ji daɗin tafiyarta ba ba ni da yadda zan yi ne. Maganar auren Yallaɓai ta fasu a gari tun da duk an sanar a groups ɗin su na gida,nima sai na faɗa ana gidanmu. Ya Aina ta ce af ita ai ta san za a rina Ma’u ta yi ta masifa wai Yallaɓai ya cika haɗa ma har Ya Auwal ya fito ya ce ba ma son gaskiya. Shima yana da niyyar sai ya yi huɗu in sha Allahu muna ta dariya. > Janaftybaby: Hauwa da Munnira sun yi ta ƙorafin me ya sa na amince amarya ta fara tarewa a sabon gida?

    “To miye a ciki? Mijin ma gabaɗaya za ta mu raba shi tare miye abin damuwa a gida. Ta tare can ya gama mararinta daga baya mu sai mu koma.”

    Daga haka na kashe bakin su, Gimbiya sama da sati biyu sannan ta dawo, shi kuma da kan shi ya faɗa mini har yana faharin shi bai je ba, su Anty Bahijja ne suke je suka dawo da ita Bayan Tafidan Rano ya yi mata faɗa sosai. Har kuma ta dawo su Khalipa na gida ba su koma ba, shi bai ma yar da su ba nima ban ce su koma ba na bar su ko itama za ta samu kwanciyar hankali. In da ta ji shawarata wallahi da duk haka bai faru da ita ba.

    Kwana ɗaya tsakanin faɗa mini da ya yi ta dawo. Ranar ma a gidan ta ya kwana da safe da ya ke ranar laraba ne su Khalipa na makaranta suna Jarabawa ne ina cikin bedroon su Jidda ke da gidan yanzu tun da suna nan daga ita har Baby ba na yin aikin komai sai dai na kwanta na tashi na ci kawai. Haihuwa mai rana
    Ina cikin ɗakin Baby ta zo ta ce mini ga Gwaggo Bahijja da Anty Gimbiya nan sun zo, na yi ta mamakin zuwan su. Ban ɓata lokaci ba na saka ɗankwali na fita falon Yallaɓai in da suke zaune

    Wallahi na tsausayama Gimbiya duk ta faɗa ta yi zuru zuru ba gayu yau. Na yi mamakin da muka gaisa da Anty Bahijja faram faram kamar ba mu taɓa samun matsala ba ashe alfarma aka zo ci dole a yi mimi haba haba.
    Wai Anty Bahijja ke faɗa mini mu haɗa kai da Gimbiya domin mu rusa wannan auren tun da Yallaɓai na jin maganata.

    “In ma auren ba zai fasu ba. To ku tabbata bayan an yi aurwn yarinyar nan ba ta ji daɗin zama da shi ba. Ku haɗe kan ku ke da ita domin ku tsira tare.”

    In ji Anty Bahijja.

    “Kuma ma har da maganar gida. Ke sai ki amince yarinyae can ta fara tarewa? Wallahi ba zan yarda da.”

    In ji Gimbiya.

    “Yauwa har maganan gidan ku haɗe kai ku ce ba ku yarda ba. Ko ya gyara ku fara tarewa kafin auren ko itama ya nena mata wajen zama ta jira ku tare gabaɗaya ko ba gaskiys ba.”

    Anty Bahijja ta faɗa tana kallona.

    “Gaskiya ne.”

    Na faɗa ina ƴar dariya ina mai kallon su a ɗage ɗaya bayan ɗaya..
    Sai yanzu ne suka san ina da amfani? Wato na haɗa kai da Gimbiya saboda su mafitarsu suke nema. Ni kuma wallahi ba wacce ta isa ta saka ni na zubar da girmana. Yallaɓai ya nuna ma yarinyar nan ina da daraja a rayuwarsa shima ya nuna ma duniya ina da ƙima a wajen sa saboda kishiyar da ba ta ɗauke ni a bakin komai ba ba zan yi wasa da mutumcima ba.

    “Ku yi hakuri zencen gaskiya ki cire ni a wannan lissafin ba zan iya aikata ko ɗaya a ciki ba ‘

    Na faɗa ina kallon su, suma ni suke kallo cikin mamaki.

    “Aurn da zai yi umarnin Allah ne. Maganar gida kuma gidan shi, don ya ce ga yadda za a yi ni ban isa na ce ba haka ba. Allah na tuba mijin ma aka yi sharing ɗin sa da ita sai gida ne zama abin damuwa ? Ni a ganina wannan ba hanyar ɓulllewa ba ce, hakuri shi ne kawai. Amma ba abin da za a fasa.”

    “Da man na faɗa miki ba za ta yadda ba. Ita fa jin dadi take yi Saboda ni za a yi mawa ba ita ba tana bashi goyon baya.”

    Gimbiya ta faɗa ma Anty Bahijja.

    “Naga alama.”

    Sai kawai na miƙe ina faɗin” Duk yadda kuka ɗauka dai dai ne. Ni dai Allah na gani ba zan yi hauka saboda Yallabai zai ƙara aure ba, in ke za ki yi haushi to ki yi shi kaɗai amma ba tare da ni ba. Sannan sai yau da zai ƙara aure na ke da amfani a wajen ku? Ai ba ki taba kawo ta ko ce mu haɗa kai ba sai yau. Saboda amfanin ku ne, to ba zan yi ba kowa tashi ta fishshe shi.”

    Ina gama faɗin haka na bar musu falon na san sun yi suman zaune da mamakina.

    Note
    error: Content is protected !!