Turken Gida – Chapter Fifty-five
by Janafty*MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE*
Ni dai har ga Allah bayan fitan Yallaɓai masallaci na ji kamar ƙaran fashewar abu amma sai ban mayar da kai ba tunani kunnuwa ba su jiyo mini sautin daidai ba. Ashe ko acikin gidan ne tun da Yallaɓai ya ce har ya fita sallar asuba motar na nan lafiya ba abin da ya same ta. Kenan bayan fitan shi ne koma me ya faru ya faru ɗin.
“Innalillahi ko jifa aka yi ne daga waje Yallabai?
Na faɗa ina riƙe baki saboda duk mun fito haraba har da su Baby gabaɗaya ana ta jimami amma Gimbiya ba ta ko buɗe ƙofar shashenta ba.
“Wani jifa? Wannan aikin da gangan ne, da kuma niyya aka yi shi an fasa gilashin gaba an fasa gilashin window just imaging fa Sadiya”
Ya faɗa yana zagaye motar yana dubawa, Rabi’atu ta yi tsaye da hijabi ta kasa magana wannan shi ne ta ga samu ta kuma ga rashi.
“To waye ya yi wannan aikin?
“Ko waye ma za mu sani yanzu.”
. Yallaɓai ya nufi wajen Megadi Yumna ce ke zillo daga hannuna ya ce kar na sauke ta saboda gilasan da ke watse a wajen.
Mu dai muna tsaye da ni da Rabi’atu da Baby ina riƙe da Yumna muna jajantawa Baby faɗi take yi” Za a iya gyara motar Anty Rabi’atu kar ki damu.”
Nima ganin ta damu ina ta ce mata kar ta damu za a ce a saka wasu gilasan ba damuwa ba ce ni fa har tunani na yi ko tsawa ce sai na tuba ba damuna muke ba, amma ban taba kawo ma kaina Gimbiya ce ta aikata wannan ɗanyen hukuncin ba.
Muna nan tsaye sai gani kawai muka yi Yallaɓai ya dawo daga wajen megadi a fusace kamar zaki ya zo ya wuce mu ina ts kiran shi amma bai saurareni ba. Kofar shashen Gimbiya ya fara bugawa kamar mahaukaci yana kiran sunanta da tsawa abin da ban taɓa ji ba, ina jin ko ita Rabi’atu ba ta taɓa jin muryan sa cikin fushi haka ba.
“Saudatu!. Saudatu! Saudatu!”
Haka yake kiranta lokaci ɗaya yana buga ƙofa kamar zai balla na ruɗe na biyo shi ina faɗin” Subhanallah lafiya Yallaɓai?
Ko kallo na bai yi ba sai ma ya matsa baya kaɗan ya fara tokarin ƙofar da ƙafarsa.
“Haba Yallaɓai wai miye haka ne?
Na faɗa ina ƙoƙarin rike shi ya fizge jikinshi yana ce mini na matsa baya.
“Ɓalla ƙofar kuma za ka yi?
“E ina ruwan ki? In ma na ɓalla ma ba gidana ba ne?
Hake ya ce mini a tsawa ce sai na yi shuru kawai na kasa mgana ina kallon shi.
“Ki koma baya in ba za ki yi zama yar kallo ki koma bangaren ki “
Na sake yunƙurin mgana ya kira sunana a tsawace kafin ya ce” Kar ki sake yi mini mgana.”
Tsawa ya yi mini sai da na yi baya Yunma ta tsorata ta fashe da kuka ai sai na yi gefe ina maimaita innalilllahi a ƙasan raina ina tunanin meke faruwa ne? Ganin ni kaina an yi mini tsawa ya sa Rabi’atu ma ba ta matso kusa ba, balle Baby da ta maƙale a bayanta jikinta na rawa.
Duk wannan bugun da hayaniyar Gimbiya na ji ba ta buɗe ba, har ta window ya je yana kiran sunanta sai da ta ga dama sannan ta buɗe bayan har handle ɗin kofar sai da Yallaɓai ya kar ya shi wajen jan shi, ta fito daga ita sai rigar barci doguwa a cikinta da hula mai raga raga ta fa gan mu duk tsaye ga uban gayya na huci kamar zaki amma duk ba ta sha jinin jikinta ba.
“Topha! Lafiya na ga an taru a ƙofar bangarena?
Ta fada tana mai kallon mu ɗaya bayan ɗaya.
Mamaki ya hana ni magana shi kuma Yallaɓai ban san dalilin ba ina tunanin shima dai mamakin ne sai cije baki yake yi alamun yana ƙoƙarin sarrafa ɓacin ran shi ganin haka yasa na yi saurin tare ta da cewa.
“Ke yanzu duk ba ki ji abin da ke faruwa ba?
“Ban ji ba me ya faru?
Ta faɗa cikin halin ko in kula. > Janaftybaby: Motar na nuna mata ina faɗin” Motar Rabi’atu ne muka wayi gari an yi mata haka’
Sai ta wani kama baki kamar na mamaki da firgici kafin ta ce” Subhanallah garin ya ya haka ya faru?
“Shi ne ake son sani yanzu”
Na bata amsa sai na ga ta wata dariya ta ce” Ikon Allah! To ko aljanu ne suka yi haka?
“Aljanu ko ke da kanki?
Yallabai ya katse mata mgana a fusace, sai na kalle shi jin abin da yace ita ko sai ta ware ido kafin ta ce” Ni kuma?
“E ke”
Ya faɗa yana takawa kusa da ita ƙokarin kare rabin jikinta take yi da ƙofar ya saka ƙafa ya tokari ƙofar ta buɗe sai ta yi baya da sauri tana faɗin” Ban gane ba daga ganin abu sai kawai ka ce ni ce na yi? Ina ruwana?
Ta faɗa cikin rashin kunyar da ta saba da shi a kwana biyun nan.
“Saboda ke ɗin ce mai muguwar zuciya a gidan na.”
Ya faɗa yana mai kallonta kamar ya jawota ya fara dukanta a yanayin shi.
“Oho dai kai ne mai mugun zuciya wallahi. Ban da rashin adalci tun yaushe na ke bin ka da ka saiya mini mota amma kaƙi shi ne ko kunya za ka siyo ma matarka mota ni ba ka siya mini ba! Hakan da ka yi adalci ne? Wallahi kai ne ba ka da zuciya mai kyau kuma duk cutata da ka yi saboda wannan yarinya Allah na sama.”
“Bum!!”
Ya saka hannu ya buge mata baki kafin ta karisa magana sai da na ji tsoro ganin abin da ban taɓa gani ba. Yallaɓai na kai hannun shi jikin mace.
“Tun kafin Megadi ya tabbatar mini da ke ce da man naa ji a zuciya ke ce kika yi haka? Ni za ki yi ma asara saboda shegen kishin ki na banza da wofi?
“Wallshi da man na ce sai dai kowa ya rasa”
Ta sake faɗa har tana rantsuwa sai a lokacin na gama fahimtar komai wato dai Gimbiya ce ta yi wannan ta’asan.
“Ba ka yi adalci ba sai ka siyo biyu in kana so a zauna lafiya ko ka fara siya mini bayan an kwana biyu sai ka siya mata amma ko kunya ba ka ji ba ka je ita ka siya mata ni kuma ko oho? Wallahi ba ka isa ba in dai ina gani ba wanda ya isa ya yi mini rashin adalci ban yi magana ba.”
“An yi miki rashin adalci ki yi duk abin da za ki yi”
Ya faɗa a fusace kafin ya ce” Kuma wallshi ki sani ba ni kika yi ma asara ma kanki kika yi mawa. Sai kin biya duk abin da kika bannatar kin ji ma na rantse.”
“Wallahi ba zan biya ba. Rashin adalcin ka ya jawo maka asara “
.
Ta faɗa har tana rikr kugu ina so na shiga na yi magana amma ina tsoron kar ya haɗa da ni amma hayaniyarsu ta fara yawa ga su Khalipa har sun fito suna tsaye sannan ita bakin ta yaƙi yin shuru shima haka tana fada yana faɗa.
Ganin haka yasa na ce ma Baby ta tattara yaran su koma shashena. Rabiatu ma da na duk ta tsorata na ce su shige ciki sai da na samu sun shige ciki sannan na koma wajen su Gimbiya abin har ta kai ga tana kiran shi Azzalumi kuma sai Allah ya kama shi.
“Alhamdulillah na ji ni azzalumi kuma kin ga ba za ki cigaba da zama da mai zalunci ba. Zo ki fice mini daga gidana Saudatu wallahi nima na gaji da zama dake.”
Jin haka yasa na yi zaraf na shige tsakaninsu ina faɗin” Haba Yallaɓai.”
“Ta zo ta fice mini dags gida na ce ko!
Ya sake maimaitawa, ita kuma jin haka sai jikinta ya yi sanyi ta fashe da kuka.
“Ni yau kake kora a gidan ka Yusuf?
“Na kore ki gidan ki ne ko gidana? Wallahi na gaji dake da halin ki, da man tun tuni ya da ce na kore ki, kin fara yi mini asaran dukiya wata rana rai za ki kai ma hari.”
“Duk abin da ya faru kai ne sila. Domin da ka yi adalci da haka ba ta faru ba maimakon ka yi nadama amma sai ka kore ni? Ni za ka tozarta a kan wancan yarinyar?
“Ba sunanta yarinya ba. Sunan ta Rabi’atu ce matatace kamar yadda kike matata. “
Gimbiya ta sake sakin kuka kafin ta ce” Saboda ita yau kake kora ta?
“E saboda ita ne domin ita ba mahaukaciya ba ce kamar ke”
Sai Gimbiya ta fara kururuwa har tana zama a kasa hannu a saman kai tana faɗin Yallabai ya zageta ya ce mata mahaukaciya.
“E na faɗa in ba mahaukaciya ba wacece za ta yi abin da kike yi? Ita yarinyar da kike kishi a kanta wallahi na tabbata ba za ta yi haukan da kike yi ba. To tun da ni ba ki bani farimciki nima kuma ima zaluntarki gwara ki zo ki tafi garin ku na gaji”
A fusace ta mike tana faɗin” Nima wallahi na gaji “
“Ni na fara gajiya” > Janaftybaby: Yallabai ya faɗa har yana sakin tsaki, ina so na yi magana sun hanani da wannan ya dire wannan zai ɗauka.
“Sai ka sake ni domin na je ma da iyayema da shaida.”
Gimbiya ta faɗa tana tsiyayan hawaye duk sai jikina ya yi sanyi.
“Sakin kike bukata?
Yallaɓai ya faɗa idanuwansa sun yi jajir.
“E ina buƙatar shaida.”
“Fine. Zan ba ki shaida.”
Ya faɗa yana mai juyawa da gudu na fito na sha gaban shi ina kiran sunan shi amma ya raɓa ni ta gefe ya wuce na riƙe bayan rigan shi ina faɗin.
“Don Girman Allah Yallaɓai kar ka yanke hukumci cikin fushi.”
Fizge rigan shi ya yi kawai ya shige bangaren Rabi’atu na taho ya banko mini kofa a fuskata sai na yi sororo, ba. Buga masa ganin mun riga mun bar ma Megadi abin faɗa duk da bai fito ba amma yana cikin ɗakin sa yana jiyo duk hayaniyar dake faruwa.
Shashen Gimbiya na koma tana cikin bedroom ɗin ta, tana haɗa kaya a cikin babban akwatinta tana kuka. Duk ta zubo su daga cikin wardrope ɗin ta. Hankalina ya tashi na fara tare ta ina hanata saka kayan a cikin akwatin da ta ɗauko sai na karɓe ina faɗin” Haba don Allah miye haka kile yi?
“Ba ji ji me ya ce ba ne? Ya ce na zo na bar masa gida tun da ba na bashi farimciki.”
.
Ta faɗatana mai ƙara fashewa da kuka. Duk taƙamar cikin mintina har ta fita kamaninta sai na dafa kafaɗanta ina lallashinta.
“Ki yi hakuri kema bacin rai ne shima haka in zuciya ta yi sanyi za a daidai ta.”
“A’a Maman Jidda ki bari kawai na tafi. Sakina fa yaje ya rubuto ya kawo mini zaman me zan yi?
“Ba zai sake ki ba. Ba aure ki don ya sake ki ban”
Na faɗa ina mai kara dafata, cikin kuka ta ce” Ya ce fa da kanshi ya gaji Maman Jidda. Ni wai yau Yusuf ke yi ma wulaƙanci saboda wata ƙaramar yarinya?
“Laifin ki ne me ya sa kika fasa motar nan? Duk da shima bai kyauta ba amma da kin yi shuru kin jira ki ga iya gudub ruwan shi. Sannan ai shi mijin ku ne shugaban ki, bai kamata yana faɗa kina faɗa ba. Duka ranku ya baci shi ya sa kuka yayyaba ma juna mganganu.”
Cikin hawaye ta kalleni kafin ta ce” Na kasa haƙuri a nan wajen na ke jin ƙuna in na ga Yallaɓai na fifita wannan yarinyar a kaina? Na kasa hakuri ne”
Ta faɗa tana mai nuna mini saitin zuciyarta sai kuma kawai ta yi zaman dirsham a ƙasa tana cigaba da gurzan kuka. Sai na bi ta nima na zauna a gefenta ina ɗan bubbuga kafaɗanta alamun lallashi.
“Shi ya sa na sha ce miki Gimbiya ki yi haƙuri domin duk abin da haƙuri zai ba ka rashin sa ba zai ba ka ba. Da kin yi hakuri don Allah duk wannan abin da ya faru zai zo ya faru?
Sai ta yi shuru ta kasa mgana sai kuka ni kuma sai na cigaba da faɗin” Kana gani za a cuceka ayi maka abu na rashin adalci amma sai ka yi shuru ka yi haƙuri ba wai don an fi karfin ka ba sai domin hakurin shi ya fi alheri. Tashin hankali ba shi da daɗi da a ce kin same shi ta lalaba kin tambaye shi Baban Jidda ni fa tawa motar sai yau she za ta zo? Duk amsar da zai wuce kema na ki na hanya ba ai yana da ilimi ya kuma san abin da yake yi. Ba ina kare masa ba ne amma ina so na faɗa miki gaskiya. Yallaɓai na kamanta adalci, nu ya faɗa mini zai siya ma Rabi’atu mota saboda makarantar ta, duk da bai yi mini bayani ba na san ya fara siya mata ne saboda ita ke ɓukata yanzu. Ke kuwa kina da shi canji kike so nima haka shi ya sa ya fara siya mata kafin ke daga baya.”
Sai na ɗan dakata ina kallonta ganin ta natsu tana saurarena amma ba ta shassheƙan kuka ba.
“Da kin yi abin cikin lalaba da duk wannan abubuwan ba su faru ba. Ga shi yanzu zuciya ta ɗebe ki kin aikata abu. Ran ki ya ɓaci shima na shi ya ɓaci fisalillahi ina daɗin shi.?
Cikin jan majina ta ce” na kasa hakurin ne. Wallahi na kasa.”
Ta fada hawaye suna mata ambaliya sannan ta sake kecewa da kuka kamar wata ƙaramar yarinya.
Duk surutun da na gama yi a banza domin Gimbiya ta miƙe ta cigaba da haɗa kayanta ta kuma ce sai ta bar masa gidansa tun da ya ce ba ta bashi farinciki.
Ganin ta ƙi saurarana ya sa na fita zuwa shashena na iske su Baby sun yi jugum har da ita kanta Rabi’atu ni saboda tsshin hankali na manta da yau suna da makaranta sai da Baby ta yi mgana. > Janaftybaby: “Kun makara ki shiga kitchen ki sama muku abin da za ku ci. Rabi’atu yau ba ki da shiga makaranta ne?
A sanyaye ta ce suna da lecture, sai na ce ta koma bangarenta ta shirya mana. Ta amsa mini ni dai na shige ƙurya na dauki wayata na danna ma Nene karon farko domin mi ban taɓa kiran ta da sunan wata matsala ba sai dai gaisuwa. Bayan ta ɗauka mun gaisa ba ɓata lokaci na zayyana mata duk halin da ke faruwa ta ja salati ta dire kafin ta ce” Ya sake ta ne?
“Ban sani ba amma dai ya shiga ɗaki ya rufe kansa.”
“Innalillahi Saudatu ba ta jin mgana. Sadiya don Allah ki hana ta tafiya bari na kira Zuwaira.”
Sai na amsa mata da to, muna gama wayar na fito sai na ga ba Rabi’atu Baby kuma tana kirchen yaran kuma sun saki suna ta wasan su sai na fita, haraba na ci karo da Rabi’atu tana buga ƙofar shashenta.
“Yana ciki ki yi magana in ya ji muryan ki zai bude.”
Ban tsaya ba na shige bangaren Gimbiya na same ta har ta gama haɗa kayanta ta zurma hijabi, na janye akwatin na ce ba ta za ta tafi ba.
“Maman Jidda ki bar ni na tafi, ya ce sakina zai yi”
“Shi bai ce ba ya dai ce ki bar masa gida amma bai ce zai sake ki ba ke ce kika furta haka”
Cikin kuka tace” To ai manufarsa kenan. Miye ma’anar miji ya kore ka daga gidan shi? An ya an taɓa yi ma wata mace tozarci kamar yadda yau Yusuf ya yi mini?
Ina mata mirmishi na ce” Nima mun taɓa faɗa da Yallaɓai na ce zan bar masa gidan sa ya ce na tafi bs zai hana ni ba’
Sai ta kalleni baki buɗe tana mai mamaki.
“Wallahi kuma a kan ki ne. Ban taɓa faɗa ma kowa ba ranar a gidanmu na kwana.”
Sai na ga ta koma ta zauna gefen gadonta amma na kasa mgana, ni ma sai na zo na zauna a gefemta amma ina riƙe da akwatinta a hannuna.
“Shi ya sa na faɗa miki haƙuri ake yi ba kyau yanke hukunci cikin fushi.”
“Ya ce ki bar masa gida? Ke ma ɗin!
Sai na gyaɗa mata kai ina dariya kafin na ce”Yes na kuma yi tafiyata saboda lokacin raina ya ɓaci komai ma zai iya faruwa.”
“Wa ya dawo da ke?
“Alhajinmu ya yi mini faɗa ya nuna mini kuskurena. Sannan shi kuma ya zo ya tafi da ni washegari da Safe.”
“Da man kuma samun sabani a kaina?
Na ɗauka ke ba ki da kishi Maman Jidda?
Ta faɗa tana kallo na kuma da gaske take yi abin da ke ranta ne ta faɗa. Ban san na kyalƙyalce da dariya ba sai da na ga ina yi.
“Da gaske ina ta so na tambayeki tuntuni. Miye sirrin ki da ke ba ki damu da mu ba? Lokacin komai matsala za mu samu ni ce zan zama sila ba ke ba. Kuma sai na ga kamar ba ki da kishi a kaina, ga ma Rabi’atu yadda kike mu’amalamta kamar ba kishiyarki ba, da gaskr nake yi na sha tunanin ko dai ba ki da zuciya ne? Ba kya jin irin zafin da muke ji in mun gan shi da ke?
Kai na girgiza ina faɗin” Me ya sa ba zan ji kishi ba ai nima mace ce Gimbiya ina da zuciya a kirjina.’
“Amma me ya sa ba ki nunawa?
“Nunawan ba shi da amfani in har ka bari wasu daga waje suma fahimta. Amma ina nunawa a yanayin da Allah ya hallice ni, mun sha yin faɗa ba adadi ni da Yallaɓai. Amma sirrina shi ne haƙuri gaskiya na saka haƙuri a kan komai ko na ji wani abu ya motsa mini sai na kira sunan Allah na danni zuciyata na yi haƙuri. In abu ya dsme ni Ubangijina na ke zama ina faɗa mawa ina, shi na kuma roƙa ya cire mini mugun kishi a zuciya na ce ya saka mini salama domin na samun zaman lafiya.”
Gimbiya ta buɗe baki ta rufe kafin ta ce” Ikon Allah. Ni fa sai nake ganin duk wanda ya ce na yi haƙuri kamar ba ya sona ne.”
Ta faɗa har tana yin tagumi.
“Haka za ki ji da farko. Amma in kika yi haƙurin wata rana ke ce da riba. Sai dai riban ya kan ɗau lokaci kafin a cinmma riban amma watan wata rana mai hakuri dai shine ke da riba.”
“Haka ne.”
Gimbiya ta faɗa cikin sanyin jiki, ni kuma ina ta mata dariya ta ce wai ko ba ni da zuciya ne bana kishin su.
“Kawai na saka ma raina ba don ni kaɗai Ubangiji ya hallici Yallaɓai ba. Kuma ni ban isa na hana shi abin da Allah ya ce ya yi ba. Sannan ina yi ma zamantakewar mu kara saboda nima ya yi mini kara, ya yi mini hallaci kamar yadda na yi masa shi ya sa nake tausan zuciyata ina karɓan duk wani abu da ya fito daga bangaren shi da zuciya ɗaya. ” > Janaftybaby: Kai ta girgiza alamun gamsuwa kafin ta ce” Ga shi kuma kina ta ganin riban haka. Ki yi haƙuri a da ina yi miki kallon kin gama da Daddy domin yadda yake darajs ko sunan ki aka kira abin mamaki ne. Ya taɓa faɗa mini bayan Nene ke ce macen ta farko da yake jin kunyar ki roƙi sa abu ya kasa yi miki. Ya taba ce mini ke ce ragamar gidan shi, wakilyarshi da ba shi da haufi a kan karan da kike yi masa. Ke ya taɓa faɗa mini cewa ke ɗin ta musammance a rayuwar shi da har gobe ba ki samu madadiya ba.”
Sai na kalleta ita kuma ta cigaba da faɗin” Ni ban gane ba na yi ta fada da shi a kan ki. Karshe dai ni ce ba na cin riba. Sannan su Anty Bahijja su yi ta nuna mini yana jin tsoron ki. Halima ma har ce mini ta yi in ban dage ba saboda ke Daddy zai iya rabuwa da ni.”
Bsn wani ji mamaki ba da man na san ai ba sa sona. Saboda haka ba za su faɗi alheri a kaina ba.
Kamar an matsi bakin ta nan ta shiga faɗa mini mganganun da suke fada a kaina ba daɗin ji, da bakin ta da ke cewa duk in da Halima ta zauna sai ta zage ni, ta ce mini Naja ce ma kr kwaɓanta wani lokacin amma su Anty Bahijja sai dai su yu ta zugi in abu ya kwaɓe su koma gefe. Ko a nan hatsaniyar auren Rabi’atu duk suka kai ta suka baro miji duk ya gaji da ita.
“Kin gani ko? Kuma da abubuwan da kika yi ta yi ne yake tarawa shi ya sa ya ce ya gaji. Na sha faɗa miki ki yi hakuri domin hakiri shine mafitan ki, wata rana akwai wani abun da zai faru da za su nuna miki sun fiki kusa da shi akan ki.”
“Gaskiya ne”
“To gwara ki gyara tun kafin lokaci ya ƙure miki “
Sai ta yi shuru amma ta daima kuka sai jan majina. muna zaume muka ji ƙaran buɗe get sai na miƙe lna leƙe ts window ina faɗin” Ga ta man ina jin ta iso”
“Wa kika kira?
“Nene”
Na bata amsa sai ta ware ido ina dariya na ce” Ba ita ba ce ta zo Mimisco ta kira.”
“Na shiga uku Kin san faɗan Momi kuwa?
Gimbiya ta fada tana ɗora hannu a kanta.
“Ai gwara ta yi miki faɗa”
Kafin ta samu zarafin magana muka ji ana taɓa kofa ni na fara fita falo sai muka haɗe da Mimisco sama sams muka gaisa na yi mata jagora zuwa ciki yadda ta ga an yi baza baza da kaya ba sai ma ta tambaya ba.
“Me ke faruwa ne Nene ta kirani cikin damuwa da cewa na zo na gani Sadiya ta kira ta ce kun sami saɓani da Tafida har yana mganar saki?
Ta faɗa tana kallon Gimbiya ko zama ba ta yi ba.
Sai Gimbiya ta kasa mgana ta fara matsan ƙwalla.
“Ba kuka na ce ki yi mini ba malama”
Bakinta na rawa ta fara faɗa mata tana zuwa wajen fashe gilasan mota Mimisco ta ce” Amma dai ba ki da hsnkali ko Saudatu?
Sai ta fashe da kuka tana faɗin”Momi..”
Hannu ta ɗaga mata kafin ta ce” in kina hauka ne Tafida ya fi ki hauka. Saboda kishi ki jawo masa asara? Ina ruwanta ita ta siya motar! Ba kuɗin mijin ki ba ne?
Ke da Allah ya rufa ma asiri amma kina ma yar da kan ki baya? Kin taɓa jin an ce ga Sadiya can da Tafida suna rigima sabo da ku! Ko ita ba mace ba ce?
Ta ƙarishe faɗa cikin faɗa har tana yi mata tsawa.
“A yi hakuri Mimisco.”
“Sadiya Saudatu ba ta jin mgana gwara Tafidan ya sake ta ko za ta yi hankali.”
“Ba za a yi haka ba in sha Allahu.’
Sai a lokacin ta zauna a gefen gado tana faɗin'” Ina shi Tafidan?
Na ce mata yana bangaren Rabi’atu.
“Tun bai iya fada ba kin ko ya ma Tafida iya tsiya kala kala. Ina daɗin shi don Allah?
Ita dai Gimbiya tana ta kuka wayarta ta ɗauko jaka ta kira shi, har sau biyu bai ɗaga ba.
“Nima ya ƙi daga kirana.”
“Ki je ki same shi ne.”
“Mu je to ki rakani.”..
Ta mike tana faɗin haka.
“Ke kuma ki gyara ɗakin nan ki ma yar da wannan akwatin ƙaryan na ki.”
Ta ce ma Gimbiya da ke kuka
“Kukan me kike yi! Ai ba ki yi kuka in dai kr ba za ki ji magana ba! Me ye ban faɗa miki ba? Na ce ki yi haƙuri ki kauda kai, ki yi ko yi da Sadiya amma ba ki ji ba? Wallahi in yaƙi saurarena ba zsn matsa masa sai ki tattara ki tafi can Rano wajen Hajiya burin ki ya cika kina ta kawo mana matsaloli a dangi.”
“A yi hakuri Mimisco “
Na faɗa sai ta yi gaba tana faɗin” Sadiya lamarin Saudatu kamar ka yi ta dukan ta ne “
Muna tafe tana ta faɗa ni kuma ina bata haƙuri muna kofar shashen Rabi’atu take kara tambayata abin da ya faru na warware mata komai. > Janaftybaby: “Kin ki ko? Ina tarbiya mijin na faɗa kana faɗa? Ai bai burgeni ba da dukan tsiya ya yi mata ba kumbura baki ba.”
Sai da na yi dariya sai a lokacin na tuna ashe bakin Gimbiya da ya ta sa Yallabai ne ya make mata baki a ɗazu da suna mgana.
kiran shi ta sake yi aka samu sa a ya ɗaga sai ta ce ga ta nan a ƙofar shashen Rabi’atu tana jiran shi, ganin ta samu ya ɗauka sai na ce mata zan je na duba yara.
“Je ki Sadiya. Ni ba ri na yazo na ga ko zai saurare ni.”
“ZAi saurareki In sha Allahi.”
Na faɗa ina dariya.
“To tunda ke ma yau aka ƙi sauraran ki nima da sauƙi.”
Ni dai ina ta dariya na shige bangarena na iske Baby ta gama soya dankali da kwai suna karyawa ita da su Khalipa nima sai na bi bayan su bayan mun gama na ce Baby ta je ta yi musu wanka ni zan gyara wajen,.
Sama da awa biyu ina bangarena ba wanda ya kirani har Baby ta yi ma su Khalipa wanda da yake akwai kayansu a bangarena ba su da matsala suna can falon su, suna ta wasannin su
Ni ko sai dai waya a hannua Jidda ta kirani muka gaisa ta ce tana ta kira Abban na su ba ya ɗauka na ce wata ƙila yana da bsƙi ne na yi mata ƙarya. Ta ba ni har Ummu Salma mun gaisa sannan muka yi sallama sai can Mimisco ta kirani ta ce na fito za ta fito. Na fito na gan ta tare da gogan yana ts wani cin mgani ko mgana bai yi mini ba a gabana ya sake rantsewa sai Gimbiya ta biya asaran da ta yi masa ita kuma ta ce ba damuwa za ta saka a zo a ɗau motar a kai wajen gyara.
“Shike nan?
Ta faɗa tana kallon shi, kamar ba ya son mgana ya ce” Shike nan amma dom ke ce. Da na sha alwashin sai ta bar ta je Rano ta yi wata tukunna za ta dawo.”
Mimisco ta yi dariya kafin ta ce” Na gode daka ji mganata. Ka yi hakuri ai ta baka hakuri kuma na ce ta sake baka.”
“Ya rage nata.”
Ya faɗa yana zakuɗa kafaɗa hannayen shi cikin aljihun wandon dake jikinsa.
Ni Mimisco ta kalleni tana faɗi ” Sadiya ki sake ba ma wannan rigimammen mijin naki haƙuri. Na samu ya hakura na hada su na yi ma Saudati faɗa ta kuma ji ta ce ta yi nadama na sakata ta duka ta bashi haƙuri ya ce ya wuce. Don Allah ki sake kwaɓar ta kin ji ko?
“In sha Allahu ‘
Na amsa mata ina mirmishi ganin Yallaɓai na ta hararata sai ka ce ni ce na yi masa laifi.
Direba ne ya kawo ta tace na gai da yara tana sauri ne yau baban su Naja zai bar kasar yana gida yans jiranta. Ta shiga mota direba ys ja suka fice daga gidan Yallaɓai ya juya zai wuce bai yi mini mgans ba.
“Yallaɓai.”
“Ba ruwanki da ni to.”
Ya faɗa yana haɗe rai sai na yi mirmishi kafin na ce”Allah ya baka haƙuri.”
“Ni da gidana duk hukuncin da zan yamke sai kin ce ba haka ba? Ki fita daga idona Sadiya Tam”
“In na fita idon wa zan shiga Yallaɓain?
Na faɗa ina masa wani kallo.
“Uhm za ki yi bayani ne.”
“Sorry Oga.”
Na faɗa ina dariya ganin yana mirmishi sai da ns saka shi ko dariya ƙarshenta ma bangarena muka koma tare ya je wajem yara ya daɗe a tare da su sannan ya zo ya na challagin ɗina wai me ya sa yaran shi ba su je makaranta ba?
Ina hararan shi na ce” Tun asuna ka fara mana yaƙi a gida ne za ka zo kana tuhumata.”
Sai ya fara dariya wanka ya yi bangarena ya shirya. Ya ce zai sauke Rabi’atu a makaramta zai wuce office tun ɗazu Musbsbu ke kiran shi akwai waɗanda ke jiran shi na yi masa fatan dawowa lafiya.
Bayan fitan su na rana na leƙa Gimbiya ta sha dai kuka amma dai an warware kaya. Ni dai na sake jadadda mata ta yi haƙuri in tana so ta zauna lafiya. Ranar girki ma duk Baby ta yi mana itama nan shashena ta ci abinci muna tare da ita har dare sannan ta kwashi yaran ta suka koma bangarenta.
A ranar Yallaɓai ys ƙarishe kwanan shi a ɗakin Rabi’atu washegari ya dawo ɗakina ya yi kwana biyu sannan ya koma na Gimbiya. Ni ban san halin da suke ciki ba na ɗauka komai ya daidaita ashe ba haka ba ne, Yallaɓai dai na kwana a bangaren Gimbiya in ranar girkinta ya zagayo shima a falo kuma baya jin abincinta baya mgana da ita daga gaisuwa sai gaisuwa. Ni ban sani ba sai da ta zo tana kuka tana faɗa mini na ce ta sake bashi haƙuri amma duk da haka bayan kwana biyu ta dawo ta ce mini ba abin da ya sauya. > Janaftybaby: Jin haka da zuciya daya na ce zan yi masa mgana amma in ɗauko magamar yadda ya fara yi mini ihu a saman kaina ne na san cewa Gimbiya ta gama ɓata ma Yallaɓai rai ya gama jin haushinta shi ya sa kallonta kawai yake yi.
“To tun da ta baka hakuri ka haƙura mana? Shi kenan ita ba za ta yi kuskure ka ba ta da mar gyarawa ba?
Kawai sai Yallaɓai ya ce tun da ni ce Nene na yi masa faɗa saboda na ce abin da yake yi bai kyauta ba Allah zai kama shi.
“Ki bari Ubangijin nawa ya kamani amma ba ke ba.”
Zan sake magana ya ɗaga mini hannu.
“In kika sake tare ni da mganar da ta shafi Gimbiya wallahi zan kai ƙaran ki wajen Allah. Haba kin dame ni? Kin fi sanin abin da ya kamata ne? Ko sai na ce Allah ya isa ne sannan za ki ƙyaleni da wannan mganar ne?
“Allah ya ba ka haƙuri. In sha Allahu ba zan ƙara mgana bam”
“Better for you.”
Tun da ya yi mini haka na koma gefe itama Gimbiyar na faɗa mata tun da ta bashi hakuri ya ƙi haƙura ta fita batun shi in ya gaji zai seuko da kansa na faɗa mata nima irin tijaran da ya yi mini daga faɗan gaskiya. Gaskiya ne yanzu Yallaɓai ya zama masifaffe abu kaɗan sai ya fara faɗa yana yi ma mutane ihu. Maganar gaskiya Gimbiya ta ba ni tausayi duk ta rame ta saka ma kanta damuwa kuma Mimisco washegarin ranar da ta zo ta saka aka zo aka tafi da mota aka aka gyaro ta dawo kamar sabuwa. Kamar ma wani abu bai same ta ba Yallaɓai da kan shi yake sake koya ma Rabi’atu mota duk da iya amma hannunta bai faɗa ba, sannan abin da na ɗan fahimta Rabi’atu ta fara raina Gimbiya ba ta jin kunyar kallonta cikin ido kuma ba ta jin kunyarta kamar farko domin akwai rana tana shashena Gimbiyar ta shigo wallahi ba ta gaisheta ba sai da na yi mata mgana. Da man abin da na kr gudu kenan yarinyar nan ta zo ta fara raina ta, ba ta da yadda ta iya.
Ban san ta in da mganar abin da ya faru ya zaga dangin su Yallaɓai ba. Amma na fi tunanin Gimbiyar ce ba ta dandara ba ta fidda mganar. Sai ga Munnira ta kirani tana ba ni labarin jiya ta je Gwamnaja Anty Bahijja tana ta masifan wai Gimbiya mahaukaciya ce za ta jama Tafida asara ita sun lura kishinta na hauka ne da man shima ina ta jiye ma Gimbiya kar ta kai wannan lokacin sai ga shi da kanta ta zo har falona tana kuka tana faɗa mini Anty Bahijja ta je ta same ta a shago sai abin ta manta ba ta faɗa mata. Wai har tana cewa in haukan ta ya tashi ya tsaya a kanta kar ta sake gigin taɓa kayan Tafida tun da ita ba ta da hankali.
“Allah ya kyauta amma ni na san irin wannan ranar za ta zo”
Haƙuri na yi ta bata tun da ni kam ba ni da yadda zan yi da su Anty Bahijja nima ai haƙuri na ke yi da su. Na ji daɗi dai Gimbiya ta fahimci duk da tana na su akwai wani wajen da za su iya nuna mata Tafida ne ya fi kusa da su kuma tun ba a je ko’ina ba ta fara ganin haka har kuma lokacin Yallaɓai bai sauko ba ni na ba ta shawara ta kira Baba Tafida ta faɗa masa komai shi ya tako har gidanmu ya hada su ya yi musu sulhi mu ma ya tara mu ya yi mana faɗa. Dalilin zuwam Baba Tafida ys sa Yallaɓai ya sauko ya dawo yana sauraran Gimbiya amma ta ɓarar da alfarmanta mai yawa a wajen Yallaɓai
motar da ta gama faɗa a kanta tana ji tana gani Rabi’atu ke hawa motarta tana zuwa makaranta, tana kuma shiga gari da abin ta amma ita miji ke jin haushi har Rabi’atu tana ɗaukan Gimbiya a mai yi mata hassada tun da na san za ta faɗa ma dangin ta kuma kowa da maganar da zai kawo mata
Balle na ga tana da ƙawaye suna biyo ta gidan ni dai ba ruwana nawa ido ne tun da mijinta bai hanata tarkacen ƙawaye ni a wa? Iyaka dai in sun zo za ta kawo su har bangarena su gaisheni abinci ma ni nake ba su wani lokacin tun da in dai tana makaranta ni ke dafa abinci da ita ba kuma wanda ya sakani ni na saka kaina ganin wata rana sai yamma take dawowa ta gaji ba za iya wani girki ba shi ys sa nake yi dafa abincin da ita.
Mota kuma Yallaɓai ya ce bai siya ba in Gimbiya ta isa faɗan ya sa ya siya. Na ce ta yi shuru ta ƙyale shi, sai yanzu ne Gimbiya ke son dawowa jikina ta makara amma duk da haks ban gwasale ta ba. Ina ba ta shawara kamar yadda zan ba ma kaina kums ni daga ita har Rabi’atu daya na ɗauke su.
* > Janaftybaby: Mun yi azumin watan Ramadana mun yi salla. Jidda ta dawo gida salla amma ana fice sallata koma saboda za su fara jarabawa. A bayan salla muka muka yi auran Anti yar wajen Ya Murja Kaduna muka kai ta muna gama nata muka faɗa ma Firdausin Ya Balki. Ita kuma Funtua muka kaita auran gida babanta ya yi mata. Duk fa mun zama iyaye girms ya kams mu tun da mun aurar mun kai ga jikoki ma.
An saka ma zainab ƙanwar Ma’u rana itama dangin mahaifinta a can kura ne za su aurar da ita ga ɗan katsina.
Lokacin da muka yi sha’anin Rabi’atu ba ta nan ta tafi Maiduguri ganin gida, Gimbiya ce kawai ta zo mini biki da ƙannenta har da Maryama da muka taba samun matsala. Yanzu sai gaisuwar mutumci ina anfanin to rigima? Har su Munnira duk na ce su saki tun da itama ta saki a cewar Munnira wai da ta ga uwar bari ba, domin abin mamako har su Anty Bahijja yanzu Rabi’atu na zuwa gidajensu lafiya lau kamar ba su ne masu taya Gimbiya a dawa ba.
Da ta dawo daga maiduguri tazo da tsaraba ba wamda ba ta ba shi ba, ni kaina turaren wuta har ina kyautar shi.Yarinyar an yi mata huɗuban kyauta yadda za ta siye kowa to haka take yi ko Gwammaja za mu je ba za ta zuwa hannu rabbana sai ta riƙe ma su Nene wani abun. Cikin lokaci kaɗan Rabi’atu ta yi farimjini a dangin Yallaɓai wai har Anty Bahijja wata rana a ɗakin Nene mun je gaisheta ni da Gimbiya da yara ta zauna tana yabon Rabi’atu tana faɗin yarinyar akwai hankali sai daga baya ta yi ma Tafida uziri shi ya ga abin da ya gani. Har Nene yabon ta take yi in ta zo gida nan ta yi wannan ta yi wannan har kunshin su na yan maiduguri take zuwa na musamman ta ƙun sa ma Nene a kafa da hannuwana duk wani abinci da ta san Nene na so in za mu je za ts yi ta je mata da shi, wani abun ma ni ke faɗa mata. Mimisco da man ba ruwanta ko ita tafaɗa ta ce Yarinyar nan tana da wayau ta san dubarun zaman duniya.
Kuma ita ba ta ware kowa ba, kowa na ta ne, har su Suwaiba haka take girmama su shi ys sa cikin lokaci kalilan kowa ya san Rabi’atu har mazan fa in suka zo gidan haka za ta yi ta musu rawan jiki. Yallaɓai ko sai jin daɗi yake yi yana fahari Gimbiya ko sai kuka da nadama ba ta da yadda za ta yi ƙaramar yarinya ta zo ta sha gabanta.
Muna gidan Halima za ta zo ba ta shiga shashen Gimbiya ba ta yini a bangaren Rabi’atu ba abin da ba ta bata in dai ta gani ta ce tana so za ta ce ta ɗauka. Ni dai ta so ta sake shigowa jikina na ce nahi. Ai kin ci taliyar ƙarshe amma dai muna gaisawa sannan in ta zo gidan tana shigowa mu gaisa ni ce ba na sakar mata. Da baffan Rabi’atu ya je makka shi da Antyn ta, Har Nene da su Maman farko sun samu tsaraba Yallaɓai Jallabiya da Darduma da casbaha da dabino da ruwan zam+zam. Ni kaina an siyo mini abaya yara ma kowa da na shi har Jidda dake makaranta Gimbiya ma ta samu abaya. Ni kaina wayon yarinya na ba ni mamaki sumu sumu da ita ashe ta san abin da take yi.
Su Anty Bahijja ko duk an bi su da dabino da ruwan zam-zam suna ta taɗin suna jin daɗi. Ni dai ban damu ba da duk abin da take yi ba lokacin ta ne ta yi wata rana ba za ta yi ba mu kan mu ai duk mun yi wannan bin a farko muka gaji muka haƙura Gimbiya ce ke damuna kuma na faɗa mata ta yi haƙuri amma fa ba ta da yadda ta iya da Rabi’atu. Wacce ko zazzaɓi Nene ta yi kaf yan gidan su sun zo duba ta. Na cen maiduguri su kira waya me ya sa Yallaɓai ba zo so ta ba?
Nan da ya samu hatsari Allah dai ya tsare buguwa ya yi a hannu sai gocewa a ƙafa haka suke tururuwan zuwa duba shi danginta na nan Kano na can ko suna ta kiran waya. Kamar ta goya Yallaɓai haka take ki da shi, biyayya take yi masa ko abi za ta ba shi sai ta rusuna ni fa ina gefe ne amma ni kaina na san yarinyar nan bariki kawai take gwada mana. Ni kaina zuciyata na motsawa ballanta Gimbiya? Ga shi kaumar yaran mu take yi kamar ita ta haife su an ce mai ɗa wawa. Har ta su Khalipa yanzu in dai tana gida suna bangarenta ita kenan ba su abubuwa suna ciye-ciye an ce mai ɗa wawa Yallabai gani ya ke yi a kan Rabi’atu xai iya faɗa da kowa. > Janaftybaby: In Jidda za ta koma makaranta ba ta zaune ba ta tsaye sai ta ga ta koma ita ce kawo mata wancan ta ya ta wancan kuma duk ya gani kuma wallahi hakan yana tasiri. Baby ko daman ta zam yar ɗakin ta ko gidansu muka je wani abu ya faru ita da danginta kamar si goya mu. Itama in ta shiga damu dangin haka za ta daraja su. Maganar gaskiya sai dai ƙin gaskiya amma Rabi’atu tana da hallaya mai kyau. Ta bakin Gimbiya ta kan ce an yi ma Yallaɓai surkullrn yan maiduguri ya ruɗe kan yarinya na kan yi dariya na ce ba surkulle sannu ciwon kai ne kawai.
Mun yi babbar salla Rabi’atu ba lafiya ashe ciki ne. Yallaɓai kamar bai taɓa haihuwa ba Gimbiya baƙuwa a harkan mu ai mun zama yan gari. Haka yake kiran waya yana faɗa ma mutane Rabi’atu na da ciki. Tarewa gabada ya yi a bamgarenta yana kula da ita tun da laulayi take yi mai zafi, Ni ko duk abin da yake so a yi masa ni zai kira itama in tana son wani Umma kaza Umma kaza, na roƙi Allah ya cire mini kishin nan na hauka shi ya sa da ni ake renon cikin Gimbiya ko sai dai kuka a ɓoye in ta yi magana cibi ya zama ƙari lokacin da ya tare a bangaren ta yi magana da cewa ai muna gida ɗaya ba sai ya tare a wajemta ne zai kula da ita ba buɗe bakin Yallaɓai sei cewa ya yi ya tare ɗin sai ta hana shi ganin ya harzuƙa ya sa na shiga tsakani na lallaɓa shi ita kuma Gimbiya na ce mata ta yi bamza da shi duk abin shi dai ba zai dauwama a wajen ta ba.
Gimbiya faɗa mini take yi ba za ta iya jarumta na ba. Ba za ta iya juran ganin Yallaɓai na rawan jiki akan wata na da ciki ba. Na ce gwara ma ta saba domin yanzu aka fara. Wataƙila bayan Rabi’atu ma ya ƙaro wata itama ta zo tana gasar haihuwar to ya za ka yi in ba ka yi haƙuri ba?