Turken Gida – Chapter Eleven
by JanaftyMun yi azumi ashirin da tara 29 ɗaya ga watan shawwal ya kama ranar asabar ne a ranar muka sallaci salla ƙaramar salla. Mun je idi mun sallaci salla tare da al’ummar Musulman duniya gabaɗaya ni da Yallaɓai da yara sai Marwa da ta yi salla tare da mu.
Bayan mun dawo idi na saka Marwa ta dafa jallop ɗin shinkafa mai nama. Tun a daran jiya muka gama duka soye soyen mu Saude da Marwa sun taimaka mini ƙwarai shi ya sa jiya da Saude za ta tafi da daddare Musabahu ya zo gidan da shi na haɗa su na ce ya kai ta gida tunda akwai motar Ya Usman a hannun shi tun lokacin biki bai koma da ita ba. Na dibar mata naman salla da kayan fulawan da muka yi sannen na ba ta ɗan kunne da takalmin sallar da na siya mata sai pant da bara da na siya musu tare da Marwa sannan na diɓa mata shinkafa kayan miya kuma na ba ta kuɗi na ce ta kai ma Mamansu ta siya kayan miya su yi abincin salla tunda na wajen nawa an niƙa gabaɗaya na tafasa.
Yallaɓai na gida bayan ya ci abinci da nama yana falo yana amsa wayar ƴan’uwa nima 5k ya saka min kati ya ce na kira barka da sallah. Na samu kiran wasu yan gidanmu waɗanda ba su kira ba ni na kira su Alhajinmu dai da Gwaggo su na fara kira Nene itama na kira ta yi musu barka da salla sannan na kira Inna Mariya da su Kawu Nafi’u na yi musu barka da sallah. Har Yaya Murja ni na kirata Ma’u ce dai ita ta kirani kafin ni na kirata. Amma na kira Baaba ban ji mamakin da ta ce ba ta gane ni ba. Domin ba ta da lambata sai da na faɗa mata sunana bayan ma na faɗan sai da ta ce.
“Wata Sadiyar?
Kai tsaye na ce” Ta Yaya Sulen.”
Sannan ta ce au muka gaisa sama sama su Jidda ta tambaya na ce suna lafiya daga nan muka yi sallama. Da ga ita na kira Baba Aminu da Baba Sani suma na yi musu fatan an yi salla lafiya. Da ga su sai Rahila sannan na kira Yaya Muntari shima na yi masa barka da sallah.
Bayan dangina sai na kira dangin Yallaɓai daman bayan su Alhajinmu na kira Nene na yi mata barka da sallah. Sai Mimisco Anty Maimuna na sameta mun gaisa amma Anty Bahijja ba ta ɗauka ba sai daga baya ta kirani. Na kira Faridan Tariq sai su Hauwa dukkansu na yi musu barka da salla Anty Zabba mutanen fatakol ita ta kirani muka gaisa har ta ke gaya min yara na nan gwammaja sun zo sallah. Da ya ke lokacin ya yi kusa an haɗu da biki ba lalle wannan sallan yan nesa su samu zuwa ba.
A ranar Yallaɓai sai yamma ya fita zuwa Gwammaja kuma bai daɗe ba ya dawo washegari lahadi ban je ko’ina ba saboda ƴan yawon sallah. An kawo min su Sahla sai yaran Munnira sannan Jawaheer ta zo tare da ya’yan Anty Zabba da suka zo daga fatakol. Daga ɓarayina ƙannen Marwa ne kaɗai su ka zo min yawon salla daman su sun saba zuwa ban saka rai da su Antin Yaya Murja ba domin na san in da suke zuwa. Na ba su nama da kayan fulawa sannan na yi shinkafa da miya da salat suka ci da za su tafi da yamma na ba su kuɗin adaidaita sannan da kuɗin barka da sallah. Sun tafi kenan sai ga su Firdausin Anty Balki su biyu ita da ɗiyar ƙanwar babanta suka ce mini daga gidan Yaya Abubakar suke har ina yi musu tsiyan sai da yamma ne za su zo mini? Su bari sai gobe mana. > Janaftybaby: Suna dai sunne kai ba su ce komai ba, Allah ya taimaka bayan mangariba sai ga Musabahu da Adnan daman ina ta tunanin wanda zai kai min su gida tare da Yallaɓai suka shigo gidan.
Ganin su ya sa na ce su jira su in za su tafi su a jiye min su a anguwansu ko daga bakin titi ne. Sai wajen tara na dare suka tafi tunda bayan sun ci abinci suna falo suna hiran su na ƴan’uwa acan falon shi. Amma sai da na kira Yaya Balkin na faɗa mata su Firdausi na gidana zan saka a dawo da su. Jidda da Baby daman a gidan Mimisco suka yi ni ta kira ni ta ce Direba zai dawo da su. Gwammaja kuma sai zuwa gobe za mu je can mu yini. Su Musbahu sun tafi da Firdausi ba daɗewa sai ga Direba ya dawo da su Jidda gida da Nama da yawa a leda da cake har da su lemuka da kuɗi da yawa sabbin yan ɗari ɗari suka ce Daada ne ya ba su wato mijin Mimisco daman sunan da ƴaƴan shi da ita kanta Mimiscon suke kiran shi kenan.
Ranar litini ya kama ukun salla tun asuba na tashi ni da Marwa waina za mu yi saboda zan kai Gwammaja zan kuma aika da shi Ɗorayi da Gandun albasa. Saude na kira waya na ce ta zo da safe ta taya mu aiki. Saboda ina da mataya ko kafin sha biyu na rana mun gama toya waina duka miya daman tun safe na haɗa ta. Yallaɓai ya siyo mana manshanu daman na zuba a cikin miyan ga kayan ciki ga naman rago sannan ga ƙashi. Miya sai tashin kamshi ta ke yi Yallaɓai na sauri zai fita Rano zai je za su haɗu da Uncle Abba da Tariq da suka zo sallah sai na zuba masa ya ci ya na santi sannan ya tafi amma sai da ya ba ni goron salla ta na 10k sabbin yan 200 goron salla da kuɗin kwalliya domin na yi masa ado kuma ya burgeshi.
Muna gamawa su Marwa suka gyara gidan saboda rage kaya Yallaɓai na ce ya yi mini gaba da su Jidda zuwa Gwammaja da wainar su ni daga baya sai mu taho da Marwa. Saboda daman ranar a can muke yini sai washegari yinin salla na huɗu kowacce sai ta je gidan su. Saude ma kuɗin a daidaita na bata bayan na diɓar mata na su wainar sai kuma na bata na gidanmu a babban kula na waina sai ledan da na saka Nama da kayan fulawa na ce ta kai ma Gwaggo in ji ni. Ni kuma sai da na sake wanka na sauya kaya na saka leshin da Yallaɓai ya yi mini na yi amfani da mayafi da jaka da takalmi kalan adon leshin jikina na saka ɗan kunnayena masu kyau da yarari na fito na yi ras da ni na san duk in da na shiga ba wanda zai raina ni.
Da muka fito daga gida ba Gwammaja muka fara zuwa kai tsaye ba sai da na biya Gandun Albasa gidan su Mama na kai musu abincin salla da Naman salla sai kayan fulawan da na yi ban jima sosai a can ba duk na ga su Inna Mariya da sauran yaran su muka gaisa na yi musu rabon barka da sallah daman duk sallah ina kai musu abinci kuma ina zuwa tunda ni kaɗai ce mace a kano Amina ta yi nisa sai in wani abu ya faru ta zo. Ni ɗin ce na ke ƙoƙarin sada zumunci suma kuma suna da kirki duk abin da zai faru damu suna zuwa sannan Ya Auwal ma in ya zo garin ya kan je ya gaishe su kuma taimako dai dai gwargwardo ya na yi musu abin da bai gagara ba.
A can Gandun albasa muka yi azahar sannan muka wuce Gwammaja. A can na iske su Hauwa da Munnira gida cike da ƴa’ƴa da jikoki. Domin kaf ɗin su yaran gidan sun zo sai dai waɗanda ke nesa irin su Jafar da Muhammad sani Yaya Usman daman sai yaran shi kawai ne suka zo. Su Anty Bahijja gabaɗaya suna nan da gayyarsu ban ga Gimbiya ba sai na ji Anty Maimuna na faɗin ta tafi Rano ɗazu da safe. Naja’atu ta zo amma ina gidan ta yi shirin tafiya gidan iyayen mijinta can za ta ƙarishe yininta Halima ma ta zo da yaranta ta yi kiɓa ita da jajariyarta mai kyau da ita har na ɗauke ta.
Lokacin da na zo Nene ta kwanta sai da ta tashi muka shiga muka gaisa na kai mata Nama da kayan fulawan da na zo da shi ta yi ta saka mini albarka.
“Sadiya Tafida ya kawo mana waina. Sannu da aiki Allah ya saka da alheri.”
Na amsa da Amin haka Nene ta ke komai sai ta yi maka godiya. > Janaftybaby: Daman su Hajiya iya duk na shiga mun gaisa na kai musu na su Naman salla, tunda haka na ke yi duk shekara sai dai Yallaɓai in ya je ya ji suna masa godiya nima haka suka yi ta min godiyar waina, Suwaiba har tana min tsiyan shi ya sa Yaya Tafida ya fara ijiye tumbi ashe daɗin girki na ne ina ta mata dariya. Maman farko ta ce ai ta diɓa ta boye za ta ɗumama ta ci da daddare wainar ta yi mata daɗi. Da ya ke shekara biyu kenan ban yi waina ba wancan shekaran tuwo na yi musu da miyar agushi wannan ne na ce bari na yi waina saboda a sauya baki.
Kowa ya ganni tare da Marwa sai ya ce Sadiya ina kika samo yar budurwa mai hankali da kunya haka? Saboda da yara sun ɓata ɗakin Nene za ta ɗauko abun shara ta share. Ga shi ta na son yara goye take ma da ɗiyar wajen Halima har Nene sai da ta yi mgana na ce ɗiyar Yayata ce Marwa na tuna ma Nene ai ta na zuwa gidana hutu kuma na sha zuwa da ita gidan nan.
Nene cikin mamaki ta ce” Allah Sarki girman ɗan mutu ba wuya. Ita ce ta girma haka? Ina dariya na ce ma Nene wallahi ita ce. Nene ta yi ta saka albarka Anty Bahijja ta saka mana baki da tambayan a ina take karatu na ce a tsafe makarantar koyin aikin jinya sai ta taɓe baki ba ta yi mgana ba ni kuma ban damu ba sanin halinta akwai son ta ji ƙwaf kuma in an faɗa mata ta nuna kamar ba ta so ta ji ba.
Ganin ɗakunan su Nene cike da ƴayansu zuwa jikokinsu sai mu surukan gidan muka tsame kan mu zuwa ƙasa shashen su Jawahir ba ta nan ma tun safe an ce ta tafi can gidan kakaninta na bangaren uwa ita da Adnan. Da ni da Hauwa da Muniira muka zauna acan muna ta hira muna shewa. Muna ƙara ma junan mu sani kan abin da bamu sani ba. Muna mgana kan kayan gyara ne Munnira ke faɗin rabon ta da wani gyara tun haihuwan Mufeedan ta.
Cikin mamaki na kalleta kafin na ce” Ke kam Munnira me ya sa me ki? Mufeeda yanzu ai ta shekara uku ko Hauwa?
Na faɗa ina kallon Hauwa wacce kafin ma ta bani amsa Muniiran ta karɓe da faɗin” Shekaranta uku da wata biyu.”
Jinjuna kai na yi kafin na ce” Ki ce waje duk ya yi tsatsa. Gaskiya ba ki kyauta ma Nasir ba.”
Na faɗa ina hararanta ita kuma tana dariya kafin ta ce” Ke ni fa gani na ke yi duk ba sa wani yi asara ne. Kuma ni in dai ba shi zai ba da kuɗin a siya ba sai na ke ƙyashin fidda kuɗina na siya wallahi.”
Mamakin Munnira ya kamani daman har yanzu akwai mata masu tunani irin na Munnira? Ko dai ta yi ma kalmar gyaran mummunan fahimta kamar yadda wasu matan suka yi ma kalmar. Ban samu zarafin mgana ba Hauwa ta karɓe mganar da cewa” Haba Munnira ke da kan ki ma? Mata ai yanzu sun waye kowa ta san abin da za ta sha ya gyara ta ba wai kuma wanda zai zama cuta gare ta ba. Kuma kin manta hausawa na cewa in kana da kyau sai ka ƙara da wanka? Kina da yaƙinin tun gyaran da kika yi da haihuwan Mufeeda ya na nan a jikin ki? Haba ai yakamata dai ko yaya ne ki ɗan ƙara gyarawa ko dai baki sha komai ba yan kayan marmarin nan da za su ƙara miki cika da Ni’ima.”
Daga ni har Munnira baki muka saki muna kallon Hauwa. Sai da ta gama bayaninta ta ga irin kallon da muke yi mata sai ta ji kunya ta kauda kai tana faɗin” Me ya faru kuke kallona? Ko ba gaskiya na faɗa ba.”
Ina ɓoye mirmishina na ce” Kin faɗi gaskiya Hauwa uwargida a gidan Mutaƙƙa shi ya sa har gobe bai kallon kowa sai ke ashe sirrin da kika riƙe kenan? To mu ma a ɗan gaya mana sirrin mana ko Muni?
Na faɗa ina kallon Munnira da ta kwashe da dariya har ta na bani hannu muna tafawa cikin dariya ta ce” Shegiya Hauwa ta zama yar gari. Maza gaya mana sirrin.”
Hauwa na dariya ta ce” Shawarwarin ku ne fa, sannan daga Rano akan ɗan aiko mini da gumba da sauran abin da ba za a rasa ba. Sai wacce Sadiya ta haɗa ni da ita na kan ɗan siya mganin infection sai kaza in na samu kuɗi kuma Alhamdulillah ina ta ganin canji.”
“Allah Hauwan Mutaƙƙa ?
Na faɗa ina kallonta sai kawai ta ɗaga mini kai. Tare muka saka dariya Munnira har ta na ɗaga kafa saboda dariya kafin ta ce” Ke Sadiya yaushe Hauwa ta yi baki haka? Kuma abin ɗanwaken zagaye ne? Hauwa kaɗai kike so ta gyara ban da ni ko? > Janaftybaby: Ina ɗaga hannuna sama na ce” A’ah ita ta min mgana ta ce tana so saboda ranar tana gidana aka aiko min da saƙon. Sai ta ce min tana so sai na haɗa su kema in kina so ai ta kwana gidan sauƙi waya kawai za a yi mata.”
Munnira sai ta gyara zama kafin ta ce” To wai kuma yana yi sosai?
Na kalleta ban yi mgana ba Hauwa ce ta ba ta amsa da cewa” To ai ke tunda kin riga kin saka wasi wasi ko kin siya ba zai yi miki aiki ba.”
“Ko?
Haka ta ce tana kallon mu ni ko sai na gyara zama ina faɗin” Gaskiyan Hauwa. Kuma son kuɗi ne ba zai barki ki yi gyaran ba karki kashe kuɗi ko? Zauna Nasir ya samu wasu ƴan kudaɗe ya nemi chanji lokacin za ki yi bayani ne.”
Tana dariya ta ce” Haba. Ai ya yi ƙanƙanta da Mata biyu. Yallaɓai dai ke kan hanya daman ana ta cewa tunda Yaya Usman ya buɗe hanya Yallaɓan ki ne zai biyo baya.”
Wani kallo na yi mata sai ta kama dariya Hauwa na taya ta. Nuna ni take yi tana faɗin” Ta firgita ta. Kin gan fa Hauwa.”
Ta faɗa tana nuna ni ture hannunta na yi ina faɗin” Firgitan me? A kaina za ta zauna? Allah ya kawo ta lafiya.”
Hauwa da Munnira na ta danne dariya haushi ya kamani na ce” Wai dariyan na menene kuma? Ko kin ji labarin auren ne ni ban sani ba?
Da sauri Hauwa ta ce” A ina? Wallahi wasa ne kawai ba abin da muka ji.”
Hararan su na yi domin na ga sun maida ni abin zolaya. Munnira ce ganin na haɗe rai ina faɗin” Ko za a mini kishiya sai an yi miki Munnira in sha Allahu.”
Da karfi ta amsa da cewa” Wallahi ba Amin ba. Cab”
Ina mirmishi na ce” Au ashe ba daɗi? Sai ta marairai ce tana faɗin” Daga Wasa? To a bar mganar kawai.”
Ni kuma na ce sai an yi ta. Munnira uwar kishi ta ce ita fa ta tsani labarin kishiya. Ganin na na ce ina cewa Nasir sai ya yi aure nan kusa in sha Allahu Hauwa na taya ni sai kawai ta sauya mganar da cewa” Na ce ba ya mganar kayan gyaran can ɗin? Ina ga zan siya nawa nawa ne?
Ni da Hauwa har muna tafawa saboda dariya sai da na gama ja mata aji sannan na yi mata bayanim ingancin kayan gyara na Hajiya Surayya Halin yau.
Cikin mamaki Munnira ta ce” Da gaske suna da kyau? Ba su dai cutarwa ko?
Kai tsaye na ce” In da suna cutarwa da tuni sun cutar da ni. Ke Munnira ki cire wannan tunanin a ranki na matan da ba su san kansu ba. Yanzu mata sun fahimci muhimmamci gyara a jikinsu wanda ba zai zama cuta a gare su ba. Kin ga mganin infection ɗin nan yana da kyau duk bayan wattani uki mace ta riƙa shan shi. Saboda shi infection 90% na mata muna dashi sannan mu ke zuwa gidajen biki da suna muna mu’alama da banɗakuna mabambamta. Kin ga kowani lokaci za mu iya ɗauka sai mun dage da mgani sannan maganar gyara Munnira ba wanda zai cutar dake ba yar gumbar nan ta mata ɗan kazan nan na haɗin uwargida ba komai a cikinta sai itatuwan maganin da zai ƙara miki Ni’ima. Bayan nan za ki riƙa gyaran ki a cikin gida kayan marmarin nan ki riƙa shan su madara su rage kayan ganye da sauran su duk suma suna taimakama wajen dawo da ruwan jikin mu kin gani nan duk bayan wata uku sai na siya mganin infection na sha sannan na bi da kayan gyara bayan kuma ina yin nawa dubarun a cikin gida hatta fatata ban zauna ba bayan wani lokaci ina siyan mayukan gyaran jiki domin kaina da kuma Mijina. Ba kuma domin shi ɗin ba sai domin ka riƙe wannan martaban da Allah ya ba ka na ƴ’a mace. Sannan yana da kyau ka yi gyara domin ka farantama mijinka Munnira ba sai an kawo maka wata ka haukace ba. Wanda ko da watan ta zo sai dai ita ta yi gasa da ke ba dai ki yi da ita ba tunda komai ta zo ta iske ki kin san shi kuma kina yi saboda haka ki yi ma kanki faɗa ki gyara jikin ki da kanki saboda martaban ki Munnira”
“Gaskiya ne Sadiya mganar ki Haƙƙun.”
Hauwa ta faɗa tana mai jinjina kai. Munnira da ta yi tagumi ta na saurerena sai ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce” Kuma gaskiyan ku ne. To zan dage in sha Allahu. Kuma kamar na fara ganin wani alamu a wajen Nasir duk da bai yi mini mgana ba.”
“Alamun me? > Janaftybaby: Na tambaya ina kallonta.
Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce” Yanzu ba ya daɗewa da mun fara mintina goma sai ya sauka kuma da ba haka ya ke yi ba”
Ni da Hauwa muka kalli juna kafin na maida kallona kan Munnira ina faɗin” You see. Akwai sanyi ajikinki kuma a yadda na fahimta ba ya wani jin daɗin ki yana dai yi ne saboda fita haƙƙi ki sai kin dage Munnira”
Tuni ta natsu tana faɗin” To zan dage gaya mini mafita. Allah Sadiya ba na ƙaunar kishiya”
Yadda ta yi mganar ne cikin tausayi ya sa muka tsintsire da dariya ni da Hauwa kamar za ta yi kuka ta ce” Don Allah ba dariya ba. Ku taimaka mini.”
Sai na gyara zama ina faɗin” Za mu taimake ki amman ke ma sai kin miƙe kin taimaki kanki.”
Sai ta ce ta ji duk za ta yi nan take na ɗauko wayata na kira Hajiya Surayya Halin yau. Bayan mun gaisa sai na ce zan haɗa ta da Munnira domin ta yi mata bayani ina ba ta wayar sai na ce ta shiga ciki yadda za ta samu damar yi mata bayani sosai. Sun ko jima suna waya sannan Munnira ta kawo min wayar nan Surayya ke faɗa min za ta fara shan na infection kafin haɗin kayan gyaran ya biyo. Mun rabu akan Munniran za ta karɓi lambar wayarta su ƙarishe mgana.
Washegari ma ta ce za ta aiko ma da Munnira saƙon ko ba ta saka kuɗin ba tunda ta hannuna ne.
Duk mai bukatar mganin infection sadidan, ko mganin gyaran uwargida da amarya contact Surayya Halin yau.
+234 803 277 3332.
Kano Nigeria.
Nuna Gwammaja har wajen ƙarfe goman dare. Domin da mazajen namu suka shigo gidan can bayan sallar isha’i gabaɗyansu suna falon Nene da ƴan’uwansu suna ta hira a tsakaninsu. Mu kuma muna ƙasa mun yi sallah mun koma muna ta zaman hira. A lokacin mganar haihuwa muke yi sun sin ina son na ƙara haihuwa ko daga yadda na ke kan hanyar yawon asibiti. Hauwa ce ke tambayata ya ake ciki ne yanzu? Kai na rausayar kafin na ce” To ana dai kan gwaje gwaje duk da kamar guda biyu suka rage amma Likitan tana ta ba ni tabbacin ba matsala ko ma akwai ba wacce za ta gagare su ba ne.”
Tare da Munniran suka haɗa bakin faɗin” In sha Allahu ma ba wata matsala.”
Sai na amsa da Allah ya sa cikin wani yanayi na ce” Yallaɓai na son yara sosai. Biyu sun yi masa kaɗan ni na sani.”
Hauwa ta ce” Amma ai ba ya nuna damuwa ko?
Sai na gyaɗa mata kai Munnira ce ta karɓe da cewa” Yallaɓai fa bai da damuwa. Damuwar su ne su Anty Bahijja. Ni da na ji ma wani batu amma dai ba ri na yi shuru.”
Sai na kalleta gabana ya faɗi saboda na san tabbas abin da ta ji ya shafe ni.
Da sauri Hauwa ta ce”Gwara ki yi shurun Munnira. Ni ma da na je Rano cikin azumi na ji batun a gida.”
Sai kawai na kallesu kafin na yi mgana Munnira ta ce” Au kema? To me za a ɓoye mata ai mgana ce ba cewa muka yi ya tabbata ba. Kuma zaman tare kenan gwara mu faɗa mata ta san halin da ake ciki ko da ta faru ma ta san in da za ta bullo ma lamarin.”
Cikin ɗauriya na ce” Wai menene? Ku faɗa min ai ban isa na hana Allah ya yi ikon shi ba.”
Hauwa ce ta kalleni kafin ta ce” A bakin Autar gidanmu na ji wai ƙannen Gimbiya ke faɗin Tafida za ta aura. Da na ce ban san da wannan mganar ba Innamu ta ce itama ta ji kuma a bakin makusantan ita Hajiyar Tafidan an ce daman tun farko Hajiya Nene da Hajiya tafidan sun so su haɗa zumunci na auran Gimbiya da Tafida Allah bai yi a wancan lokacin ba. Mutuwar mijinta ya nuna cewa rabon Tafida ce.”
Ina kallon Hauwa amman na kasa mgana Munnira ta karɓe da cewa” Nima haka na ji wallahi. Kun san wacece ta min mganar?
Hauwa ce ta girgiza mata kai ni dai ko motsi ban yi ba
“Suwaiba ce fa kwanaki da ta zo gidana ta ke min zencen. Wai Anty Bahijja ta ce wannan karon Gimbiya Rabon Tafida ne. Shi ya sa ma wai ƙila aka dawo da ita wajen Nene.”
Hauwa ta ce” Ni kaina na yi mamakin dawowarta. In aiki ne ai ba kullum ta ke zuwa ba kuma tunda tana da mota za ta iya zuwa a ranar kuma ta koma gida.”
Munnira ta ce” Har Nasir na yi ma mgana ya ce mini shi bai sani ba gulma ce ta mu ta mata. Amma wallahi Sadiya na hango gaskiya ba rami me zai kawo mganar rami? Da man ta yi ta shige masa ni fa wallahi haushi ta ke ba ni.” > Janaftybaby: Hauwa ta yi tagumi kafin ta ce” Ni kaina na fara hango hakan. Mganar fa daga bakin ƙannen Gimbiyar ta fito. Kin ga ko sun ji ana mganar ne.”
Ganin yadda na yi shuru kawai ina sauraran su ya sa Hauwa ta dafa kafaɗata tana faɗin” Kar ki damu Sadiya. Ni na san ko auranta Yallaɓai ya yi ba za ta sha gaban ki ba.”
Munnira ta taɓe baki kafin ta ce” Ni wallahi da wata ta waje ne wacce ba a sani ba. Amma wannan Gimbiyar fa ban so. Sai Sadiya ta zama mujiya Allah su Anty Bahijja ware ta za su yi daman ya ya a ka cika?
Hauwa ta yi ajiyar zuciya kafin ta ce” Da wannan kuma da wanman.”
Munnira cikin jin haushi ta ce” Har fa wani suna take kiran shi Daddy shi kuma ya ce mata me ne ma?
“Daughter”
Na faɗa ina kallon Munnira da ta yi tsaki kafin ta ce” Ke kuma wai duk kika ƙyale? Suna waya to?
Sai na gyaɗa kaina kafin na ce
” Suna yi mana.”
Gabaɗayansu suka kalleni cikin mamaki sai na yi mirnishi kafin na ce” To ai ban isa na hana shi yin waya da ita ba tunda yar uwanshi ne ko da na aure shi suna tare. Hauwa Munnira daman tun da na ji Mijin Gimbiya ya rasu da irin hidiman da ta ke yi ma yarana na san gwara na shirya domin watan wata rana ko Yallaɓai bai yi tunanin auranta ba za a tusa masa tunanin. Bakomai in ma ya auro ta fatana Allah ya zaunar damu lafiya abu ɗaya na sani ba zan yi ma Yallaɓai baƙin ciki domin ya ƙara aure ba. Sannan ba zan yi faɗa da dangin shi ba amma na kudiri niyar in sun yi mini hallaci na yi musu in ba su yi mini ba wallahi ba zan yi musu ba sai dai gayyar ta watse.”
Munnira ta ce Hmm! Ta ma kasa mgana Hauwa ce ta ƙara ba ni hakuri da cewa kar na damu tana da tabbacin Yallaɓai ba zai taɓa juyamin baya ba. Kallonta kawai na ke yi amman ban yi magana sai dai kuma a cikin raina sai da na ce Namiji ne fa mai chanza launi daga baƙi zuwa fari lokaci bayan lokaci.
Muna cikin yin mganar ne Yallaɓai ya kira ni a waya ya ce na fito za mu tafi ya na faɗa min yara har sun yi barci. Jin haka yasa gabaɗayanmu muka fito zuwa ɗaƙin Nene muka yi musu sallama su Suwaiba nan duk anan gida za su kwana. Mu muka fara tafiya Hauwa Musbahu ne zai kai su gida ko a fuska ban nuna ma Yallaɓai wani abu ba har muka koma gida. Marwa na bari da Baby na ce ta yi mata shirin barci.
Ni da Yallaɓai muka wuce bedroom ɗim mu kafin mu kwanta sai da muka yi soyyyarmu sannan muka yi wanka muka kwanta duk da yadda na ke jin wani abu ya tsaya min a ƙasan zuciya amman ban nuna masa ina ƙoƙarin gaya ma kaina gaskiya. Ban isa na hana shi abinda Allah ya ce ya yi ba. Sannan ba zan yi masa baƙin ciki domin ya ƙara aure domin samin wasu zuru’an ba. Amman a ƙasan raina ina tunanin saboda akwai ta in da na gaza ne. Na gaza ta bangaren ba shi zuru’a masu yawan da ya ke fata.
Washegari tun safe muka shirya. Na yi abinci shinkafa da miya da nama sai salat ɗin da na saka shi a wani filet Babba muka rufe da leda Karfe goma a Ɗorayi ta yi mana Yallaɓai ya kai mu, ranar kaya iri ɗaya muka saka da ni da yara har Marwa Atamfar da Yallaɓai ya yi mana mai adon ja a jikin ta.
Na yi kyau sosai gashi daman na ɗan rame kaɗan sai kayan ya zauna a jikina riga da sikat na yi.
Duk sammakona sai da na tarar da Yaya Balki a gidan mun je ba daɗewa sai ga Ma’u itama da na ta gayyar yaran sai ƙanwarta Zainab sai Anti ƙila can ta yi mata salla Itama da abinci niki niki. Wannan sallar daman su Yaya Hamza ba su zuwa salla gida sun fi zuwa a sallar layya. Can ba jimawa sai ga Zaitunan Yaya Abubakar sai ga Yaya Murja ta ƙarshen ita ce Yaya Aina da ƙannen Marwa gifa fa ya cika ya yi albarka tun da kaf ɗin mun mun zo da yaran mu sannan har Datti a gida ya yi salla Alhajinmu ya ji daɗi bakin shi har kunnen gashi ga jikokinshi suna ta fira Gwaggo ma ta kasa zama sai ina za ta saka damu take yi.