Son Rai – Chapter Twenty-four
by Aysha A Bagudo"Komawa tayi ta kwanta lamo akan katifarta hawaye na tsiyaya a gefen idanunta ,tausayin kanta da Dr Jamil take jin yana sake shigarta .
" Allah sarki rayuwa ,duk yadda Allah ya tsara maka rayuwarka babu yadda zakayi ka canzata , kaddara tana fad'awa bawa daidai yadda Allah ya hukunta gareshi ,sai ko addua ta sausauta kaddarar kan bawansa ,bata yi tsammani zata waye gari a matsayin matar wani ba uncle jamil dinta ba ..
Kuka Mai tsanani take sosai har da majina , numfashinta na sama da kasa tamkar zai bar gangar Jikinta ,yayinda sheshekan kukanta ke sake ratsa zukatan tsirarrun mutane dake. . .