Son Rai – Chapter Ten
by Aysha A Bagudo..A k'alla Umma ta kusan minti goma tsaye a bayan kofar , kafin daga baya cikin firgici ta maida idanunta da hankalinta a kan Yesmin dake daf da kaiwa k'asa towel d'in dake d'aure a jikinta na k'ok'arin zamewa kasa .
A matukar tsawace Umma tace "ke Yesmin ....wata irin zabura tayi ta saki razananniyar k'ara ta k'arasa zubewa k'asa kirjinta na dukan uku uku , jikinta na kyarma runtse idanunta tayi gam saboda tasan mai afkuwa ya rigada ya afku....
tasan Ummanta ta rigada ta gama ganin komai....
"yau k'arshenta yazo "me. . .