Son Rai – Chapter Sixteen
by Aysha A Bagudo"Yayinda a hankali suka sakarwa junansu murmushi mai tsuma zuciya da aikawa ruhi wani sako na daba .
" lokaci day'a kuma murmushin yesmin ya koma kuka cikin sanyin murya mai cike da kuka ta soma magana "why D ?
"Me yasa ka min haka ?
" Me yasa kayi nisa da rayuwata alhalin kasan zuciyata bazata iya d'aukar rad'adin hakan ba ?
" lumshe idanunshi yayi saboda wani irin yanayi daya tsinci kanshi na zallar shaukinta ,
muryarsa a kasalance yace "Kiyi hakuri yesmin di nah , Ni kaina ban so tafiyar nan ba, amman babu yadda zanyi da rayuwata dole nayi nisa dake da. . .