Son Rai – Chapter Seventeen
by Aysha A Bagudo"Cak yesmin taja ta tsaya ta kasa cigaba da tafiyar da take , ta tsaya kawai tana kallon shigowar motarsa ,har sanda motar ta k'arasa shigowa harabar gidan , ta nufi inda aka tanada domin ajiye motoci,
bata d'auke idanunta a kan motar ba ,yayinda faruk shima ya ja ya tsaya, ya kasa barinta, yana jiran ta motsa su k'arasa shiga cikin gidan .
Shi kuwa Dr jamil bak'aramin tashin hankali da hargitsi zuciyarsa ta shiga a lokaci ba, saboda ganin da yayi musu ,duk da shi da kanshi ya bawa zuciyarta damar samu wani ,har ma da yi. . .