Son Rai – Chapter Nineteen
by Aysha A Bagudo...madadin ya cigaba da magana kamar yadda ya soma sai yayi shiru tare da runtse idanunshi da suka rikid'e suka canza kala , yana jin nauyi da kunyar abinda zai fad'awa amininsa ,yadda bakinsa ya kasa furta komai haka zuciyarsa ta daina aiki na wucin gadi , gabad'aya ya ma rasa me zai fad'a masa ,"ce masa zaiyi ya d'auki lokaci yana saduwa da diyar cikinsa har ya kamu da matsanancin soyayyarta , ko kuma cewa masa zai yi ,yana sonta ne ya bashi aurenta ?
Ya tambayi kanshi yayinda 'Kwa'kwaluwarsa ta shiga cajin neman mafutar abinda zai. . .