Son Rai – Chapter Eleven
by Aysha A Bagudo... A hankali ya k'ai bak'insa daidai saitin Kunnenta ya soma rad'a mata magana Cikin Sanyayyiyar muryan shi mai tsananin kashe mata jiki, da tsuma zuciyarta .
"Yesmin...... bazan i'ya abinda kike tunani ba a halin yanzu da zuciyata take cikin garari da tashi hankali ,bama haka ba har a cikin zuciyata bana so wani abu ya sake Shiga tsakanina dake..... nayi nadama har a cikin Zuciyata, Nayi nadama! nayi nadama!!!
" bana son wata halaka ta sake shiga tsakani na dake matukar baki kasance mallakina ba ....
"Add'ua ta da fatana a halin yanzu in san yadda zanyi. . .