Son Rai – Chapter Eighteen
by Aysha A BagudoBayan sun gaisa da abban yesmin , Dr Jamil ya d'an saurara ,yaji ko yesmin zata gaishe shi kamar Koda yaushe .
amman yaji tayi shiru taki cewa komai ,hakan ne yasa shi maido hankalinsa da idanunshi har ma da natsuwarsa inda take zaune kusa da mahaifinta ,ya tsura mata idanunshi masu matukar kyau da tasiri a jikinta har ma da zuciyarta ....
"Zuciyar ce ta dinga dokawa da mugun karfi , sakamakon idanunshi da take jin yana yawo a sansar jikinta, cikin wani irin yanayi na bugawar zuciya ta d'ago kanta ta tsura masa nata ido ,shiru kawai tayi tana kallonsa. . .