Search
You have no alerts.
    Cover of Rumbun Qaya Complete

    Rumbun Qaya Complete

    by Nadmin

    Tafiya me tsawon gaske ta iso da su Kano daga Yolar Adamawa, tun tana dauki da mararin zuwa har ta soma sarewa ganin tafiyar ba ta kare bace. Kallon tagar motar tayi lokacin sun iso garin na Kano ana gaf da kiran sallar magriba, karo na biyu kenan da tazo Kano tun bayan barin su, wanchan zuwan din ma ba zata iya dorar da komai akai ba dan bata da cikakken wayo. Motsa kafarta tayi da tayi mata matukar tsami ta tuno gwagwarmayar da aka sha da Dada kafin ta amince ta bar ta, ta taho bautar kasa Kano, sai da aka tabbatar mata da idan bata bar ta taje Kanon ba toh fa kudu za’a tura ta tunda bata da aure kanon ma sai da Lamido ya shiga ya fita sannan aka samar mata. Ala dole babu yadda ta iya ta hakura. Tunda suka dauko hanya take shan kira daga wajen yayyen nata, da Hamma Hydar ya kira sai Bobbo Sadeeq shima haka Lamido kuma duk Dada ce take sakasu kiran taji ya tafiyar tasu. Yanzu ma motar su na tsayawa a tasha kiran Lamido yana shigowa,dagawa tayi tana murmushi tace

    “Yanzu muka iso gamu a tasha.”

    “Toh Masha Allah, ki kira Addan ki fada mata kun iso.”

    “In sha Allah, ina isa zan kira Dada nah, Hamma kace mata ta kwantar da hankalin ta.”

    Murmushi yayi ya katse kiran ta duk’a kad’an ta dauki jakar hannun ta sannan ta shiga jan akwatin ta zuwa hanyar fita daga tashar. Duk da kasancewar duhun dare ya soma yi amma garin tarwai yake da hasken fitilun dake haska kan titin. Tsayawa tayi daga nesa da Titin ta ciro wayar ta kira Addan. Napep tace mata ta hau ya kawota hotoro idan sunzo sai ta kirata. Maida wayar tayi cikin handbag dinta ta tsaida napep din ta fada masa in da zai kai ta, kasancewar unguwar ba boyayyiya bace yasa bata wani sha wahala ba suka iso, ta sauka ta bashi kudin sa ta sake kira. Tana tsaye a wajen yaron Addan Muhammad yazo ya tafi da ita dan daga titin gidan su layi daya ne ba nisa
      Da murna Adda maimuna ta tarbe ta, hakan yasa ta sakewa sosai dan dama ita tun asalin ta bata da duhun kai, kuma tana da masifar son mutane, sam bata san wani abu wai shi bacin rai ko kunci ba dan ita din yar lele ce a gidan su, duk abinda take so shi ake mata. Abinci taci tayi la’asar da magriba da suka risketa a hanya ta dan zauna kad’an ta jira isha sannan tayi suka cigaba da yar hirar su da Asmau ita ma yar gidan Addan tasu ce kuma zatayi kusan sa’ar ta a shekaru amma ita yanzu take 200 level a university. Kasancewar ita dukkan stage din karatun ta da wuri tayi shi shiyasa ta gama da wuri gashi har zatayi service. Sai dare chan suka kwanta dan hirar suke tamkar ba zasuyi bacci ba.
      Da safe ta tashi da dan ciwon kai kad’an saboda gajiya da rashin bacci amma zuwa gabannin azahar ta ware ta sake jera kayanta sosai da zata bukata a camp dan gobe iwar haka tasan tana Perm Orientation Camp dake Kusala Dam Karaye. Wajen la’asar suka fita tare da Amina ta rakata karshen layin suka karbo dinki sannan suka biya gidan wata kawar Aminan Hadiza anan suka kai har wajen magriba suna tutorial sannn suka dawo gida. Sallar magriba tayi ta zauna waya da Dada tana kara jaddada mata kama kanta da mutunci a duk in da ta samu kanta, maganar dai itace tunda aka soma maganar zuwa camp din dan har ga Allah Dada bata so dan karatun dai yazo da haka ne. Bayan ta gama wayar ta kwanta lamo tunanin Abbinta ta ya shiga zuwar mata, kasancewar ta a Kano babbar dama ce da zata je ta ganshi ita kadai ta gaishe shi, wannan shekaran ce shekarar da ake saka ran fitowar shi, duk karshen watan duniya Hamman ta suna zuwa su ganshi su kawo mishi abubuwan da zai bukata amma sam basa zuwa da ita sai dai idan sun je su kira waya a bashi su gaisa da ita, tana son mahaifin ta duk kuwa da ba zata dorar da rayuwar su tare ba dan ba wani wayo ne da ita sosai sanda abin ya faru ba, babban abinda ya jawo musu barin gari suka koma sabuwar rayuwa me cike da wahala. Hamman ta sun sha fama matuka wajen ganin sun gina rayuwar su ita da Dada sannan suma suka gina tasu har suka zama abinda suka zama a yanzu, basu taba barin ta, tayi kukan rashin uba ba, basu taba bari ta nemi abu ta rasa ba, zasu iya yin komai akan ta ga duk wanda yace zai sakata zubar da hawaye. Ita kanta bata san wani abu wai kunci ba, rayuwa take me cike da farin ciki har zuwa tahowar ta Kano wanda take ganin yana daya daga cikin cikar burin ta. Ko ba komai zata ga Abbinta yaga yadda Raihanan sa ta girma sosai ba a waya ba. Murmushi ne ya subce mata da ta tuna kalar farin cikin da suke ciki na fitowar Abbin, dan shine kadai damuwar su a yanzu, akwai abubuwa masu yawan gaske game da fitowar tasa, wanda ake ganin zai iya kawo karshen wasu mutane masu yawan gaske, sai dai zasu barshi ya sake jefa rayuwar sa a irin hatsarin da ya saka kansa a baya? Ko zai sake tsayawa gaskiya kamar wanchan lokacin? Manyan kasar basa san gaskiya ba kuma sa barin duk wani wanda zai fada musu ita. Cikin tunanin bacci ya dauke ta, dan bata farka ba sai kusan sha biyun dare, ko abincin dare bata ci ba haka ta tashi tayi sallar isha ta sake komawa dan baccin ne akanta sosai.
        Tunda suka tashi da asubah ta hau shiryawa, a sanyaye take komai sai take jin kamar ta fasa wani irin feeling, she’s nervous dan bata kuma san rayuwar da zatayi ba, haka ta daure ta karasa shiryawa dan ma Amina zata karata tare da Muhammad din, mota aka samo musu dama tun jiya drop da zata kaisu Lamido ne yayi duk wannan suna karyawa driver yazo suka fita, suka dauki hanyar Karaye suna dan taba hira har suka isa, sai da suka jirata ta shiga ciki bayan an gama duk arrangements din da akeyi a wajen gate sannan suka juyo suka barta da kewa. Rayuwar ta a sati ukun nan ta koyi darasin rayuwa sosai, sannan ta hadu da mutane kala-kala mabanbanta, kasancewar tazo da enough kudi yasa rayuwar bata yi mata wahala sosai ba dan har wasu suna mata kallon yar masu kudi saboda yanayin ta. Cikin nasara da kamewa ta gama sati ukun nan. Hamma Haydar ne yazo mata surprisingly tare da wannan driver motar da Muhammad wannan karon ba Amina dan tana da lecture, farin cikin ta ya gaza boyewa dan bata zaci zasu zo ba. Tare suka karasa komai suka dawo gidan Adda Maimuna daga nan ya koma dan dama zuwan nata ne hade da ganin Abbi dan Lamido baya nan sun yi wata tafiya a wajen aikin su, shi kuma Haydar ya zauna da Dada. Taso ta bishi amma dole ta hakura dan kwana uku aka basu zuwa ranar da zasu karbi posting letter din su.

    1. No chapters published yet.
    1. Zafin Kai Chapter 2: 2 Samirah ta rasu ne bayan da azabar tayi masu yawa ta girmi tinani da dauriyarsu harma da duk jarumtar da suke tinanin sunada ita, Cikin tsakiyar dare guraren…
    2. Zafin Kai Chapter 1: BismillahirRahmanirRaheem Allah yabamu ikon gamawa lafiya 1 Gyara tsayuwarta tayi ahankali tana sauke idanuwanta daga kallon dattijuwa kuma tsohuwar matar dake…
    3. Nihaad Chapter 3: ~ 3 8months earlier… Zaune yake saman farar kujera dake kusa da dakin mai gadi, ya fi awa daya xaune wajen, lkci lkci yake goge zufan fuskarsa da…
    4. Nihaad Chapter 2: ~~ 2 Dumbin gaisuwa da fatan alkhairi xuwa ga iyayen gidan Khaleesat’s Palace, my die hard fans🥰😍 Su Hajjaju Chamo me gwala-gwalai duk da jarin ya…
    5. Nihaad Chapter 1: ~ 1 All thanks to Allah SWT for giving me the ability and privilege to present to you this book. My mother Hajiya Hajarah Allah ya karo farin ciki da kwanciyar…
    6. (Download) NiDa Ya Ahmad – Complete by AsmaLuv: ABUJA A hankali manya manya motoci ke tafiya saman titi jiniya ce ta kardaye saman layin da xai sadaki da gwarinfa acikin garin abuja daga ganin motocin xaka…
    Note
    error: Content is protected !!