Rayuwa Da Gibi – Chapter Twenty-seven
by NadminMASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
Shirin fita zuwa wani katafaren wurin gyaran jiki da Amma ta biya kuma ta ce za ta turo direba ya ɗauki Hamdi kafin ƴan kawo lefe su iso take yi. Zee da ƙanwar Anti Labiba mai suna Fadila ne ƴan rakiya. Komai cikin mutuwar jiki take yinsa musamman da jiya bata sami isashshen bacci ba. Tayi ibada kuma tayi kuka sosai. Yawanci akan ce asiri birkita tunanin mutum yake yi har ya kasa gane taƙamaimai me yake damunsa. Halin da take ciki kenan yanzu. Tana son Taj, sannan kuma tana gudun kasancewa inuwa guda da shi.
A daren jiya ne da tana addu’a ta fara mamakin wannan sabon al’amari da ya tunkaro su. Alaƙarta da Taj ba irin wadda ake shan wahalar farata bace. Lokaci guda su ka yi clicking kamar hagu da daman mayen ƙarfe. Irin wannan rashin sakewar kafin a saba duk basu fuskanta ba. Lokaci guda su ka karbi juna a sabon matsayin da Allah Ya ajiyesu.
“HAMDIYYA!”
Firgigit ta dawo hayyacinta da jin kiran Yaya da ƙarfi.
“Tunanin me kike yi haka?”
“Babu komai” ta miƙe tsaye tana neman mayafinta.
“Me ki ke nema?” Yaya ta tambayeta.
“Mayafina.”
“Wanda ki ka yafa kuma fa”
Kallon jikinta tayi ta ce “au…”
“Zauna Hamdi. Magana za mu yi.”
Bata kawo komai ba tunda a tunaninta ta ɓoye yanayinta sosai ta zauna. Yaya ta tsareta da tambayar me yake damunta kwana biyu. Ta fara rantse rantse Yaya ta ce bata san zance ba.
“Idan ba wata uwar gareki a waje wadda ta dace da sanin damuwarki ba ina son sanin me ya sanyaki kwana kina sallah da kuka.”
Gaban Hamdi faɗuwa ya yi. Ba za ta iya faɗawa kowa Taj ya mareta ba. Haka kawai take ganin kamar za su yi rabuwa ta har abada idan aka sani.
“Yaya babu komai.”
“Kina ganin saboda lalurata da yanayin Abbanku bamu isa mu share miki hawaye idan kina da damuwa ba ko?”
Ɓacin ran uwa abin gudu. Nan da nan hankalinta ya tashi ta soma bata haƙuri.
“Ki daina faɗin haka. Wa nake da shi bayan ku?”
Da wata irin murya mai ban tausayi Yaya ta ce “Ba yau ki ka fara ba. Tun ƙuruciyarki na san kin tashi da ganin kamar bamu cika iyaye ba.”
Kuka sosai Hamdi tayi. Wannan banzan tunanin tun yaushe ta ajiye shi. Ummi ta ankarar da ita girman mahaifinta a lokacin da take ganiyar gudun a alaƙantasu. Yaya ce dama tun farko bata taɓa rainawa ba. Tana son abarta a yadda take. Wannan furucin da tayi ne dai ya sake karyar mata da zuciya tayi ta kuka tana bata haƙuri.
Bayan wani ɗan lokaci da Yayan ta ce ta haƙura shi ne ta faɗa mata rabin gaskiyar zancen. Akwai mai son Taj, ta dawo da wayar da su ka taɓa yi ta ce ai matar har kiranta tayi ta tsorata ta.
“Wai idan na yarda na tare sai ta illata rayuwata.”
Dariya taga Yaya tayi kafin kuma ta ce,
“Shi ne kike kuka? Kodayake Allah ki ke gayawa. Ya isar miki akan komai. Duk da haka cewa Yayi ka tashi In taimakeka. Kada ki yarda wata mace ta zama silar hawayenki a gidan miji.”
“Ko da yafi sonta?” Hamdi ta tambayeta tana kuka.
Da yake Yaya bata saba ganin ƴar tata ta nuna rauni irin haka ba sai take ganin son da take yiwa Taj ne kawai bata son abin da zai shiga tsakaninsu. Kalaman da za su kwantar mata da hankali ta zaɓo. A cikin ranta kuma tana ƙudurta yi mata addu’a da sauran ƴan uwanta akan kada Allah Ya haɗa mazajensu da matan banza.
“Yafi son nata ya aureki? Ko kin manta ba tayinki aka yi masa ba?”
“Haka ne.”
“Ki cigaba da addu’a sannan ki dage ki ƙwaci kanki a gidan aure. Mu bamu san boka da malami ba. Kuma bamu san makirci da sharri ba. Indai kin tsaya a tarbiyar musulunci ta zaman aure da kuma riƙo da dabarun zaman duniya za ki ga baki da yawan damuwa.”
Kai tsaye ta ce “Yaya kin koya mana dabarun zaman duniyar ne?”
Yaya tayi dariya “Hamdi kenan. Da gaske ki ke son kare martabar aurenki. Hakan ya yi kyau. Lusarar mace bata taba burge miji dama.” Ta gyara zama “su dabarun zaman duniya yau ce take koya maka. Sai kuma amfani da dama idan ta zo da kuma zurfafa tunani da hangen nesa. Sauri ko gaggawa a komai ɓata lamura suke. Saboda haka don wata ta kira ki tana surutu kada ki yarda ya zama dalilin da za ki ce kin gama aure ko kin bar mata miji. Ki ƙoƙarta. Sai idan kin yi naki kin ga mijin ƙwallon mangwaro ne sannan za ki jefar dashi ki huta.”
Ji tayi kamar an sauke mata dutse daga zuciyarta. Ta faɗa jikin Yaya tana dariya mai haɗe da jin kunya. Yaya ta rungume abarta tana shi mata albarka. Da Zee ta leƙo domin ta faɗa musu zuwan direban da zai ka su tayi mamakin yadda ta gansu.
“Wallahi nima sai anyi dani.”
Ta daka tsalle dama idan shirmenta ya motsa sai addu’a, ta faɗa kansu. Sai washhh ɗin Yaya kawai kake ji tana cewa su tashi za su ɓalla ƙashin da bashi da ƙwari.
***
Cikin ginin wani kamfanin robobi wanda a halin yanzu shi ne dukiyar taƙamar Alh. Mukhtar da iyalinsa direban Alhaji ya shiga. Akwai mota a gabansu ta wasu manyan ƴan kasuwa guda biyu wanda su ma direba ne ya kawo su. Su ne su ka yi musu jagora har wurin.
Da su ka firfito da girmamawa su ka zo wajen motar Alh. Hayatu su ka sske tarbarsa tunda dama a hanya su ka haɗu da farko.
“Alhaji ni fa ka sanya ni a duhu da ka ce mu faɗawa Alh. Mukhtar lallai ya tafi kamfani yau duk da asabar ce kana son ganinsa. Allah Yasa lafiya dai.” Cewar guda daga cikinsu.
Fuskar Alh. Hayatu babu fara’a ko ɗigo ya ce masa “lafiyar kenan. Yana da kyau mutum ya dinga zaga dukiyarsa ne saboda halin rayuwa.”
“Shakka babu uban Kantin Kwari da kewaye.” Ɗayan ya ɗaga hannu yana jinjina masa
“Ka san na faɗa muku akwai wata alaƙa tsakanina da shi.”
“Ƙwarai kuwa. Saboda ka ce kuna da dangantaka. Lokacin kuma mu duka bamu shirya barin kasuwa mu zauna a nan ba mu ka bashi. Yanzu gashi cikin ikon Allah ya mallaki kaso ashirin da takwas cikin ɗari. Kasuwa tayi albarka, shi yasa mu ka bari ya zama partner ɗinmu.” Na farkon ya yi bayani a taƙaice.
Alhaji ya gyaɗa kai yana tuno wasu ƴan shekaru a baya. Lokacin Ahmad bai yi aure ba amma idan ka ganshi tamkar mai mata huɗu da ƴaƴa goma. Ya fige tamkar kazar mayu. Kullum yana rama ga zafin nema kai ka ce wani yake ciyarwa. Matan gidansu su ka shiga damuwa. Alhaji ya tsananta bincike domin a lokacin Ahmad ƙin faɗa masa gaskiya yayi. Ashe karayar arziƙi ce ta sami Alh. Mukhtar. Mami ta taso shi a gaba. Ashana wannan idan suna buƙata sai ta kira Ahmad. Ita bata yarda tayi rayuwa daidai da samun mijinta ba a lokacin. Ta ƙuntatawa yaron iyakar ƙuntata. Duk wata kadara da Alhaji ya mallaka masa ya sayar ya bata kuɗin. Idan babu yawa tayi ta bala’i da kiran za ta tsine masa.
Ranar da Alhaji ya san gaskiya sai da ya yiwa ɗansa hawaye saboda tsabar tausayinsa da yaji. Gashi kuma ya san cewa ba huruminsa bane raba ɗa da uwa. Shi yasa bai taɓa hana Inna mu’amala da Taj ba. Gidansa kawai ya hana shi shiga. To dama ya san da maganar buɗe kamfanin robobin. A wurinsa ma su ka ranci kuɗin. Shi ne ya basu shawarar ɗauko wanda ya yi boko sosai wato Alh. Mukhtar aka yi masa MD. Yana fara samu Mami ta sakarwa Ahmad mara. Babu wanda ya san maganar nan har yau.
“Ku kaini ofishinsa. Ina son magana dashi.”
Da rawar jiki su ka yi gaba. Har yanzu akwai wajen kaso talatin da biyar na kuɗin da ya ranta musu da basu gama biya ba. Hankalinsu in ya yi dubu to a tashe yake.
Sun isa ofishin MD inda Alh. Mukhtar na ganinsu shi ma ya tashi da rawar jikin ganin iyayen gidansa. Aka gaisa su ka zauna. Ya miƙowa Alh. Hayatu hannu yaga babu fuska ko alamar zai karɓa. Ba shiri ya ja da baya.
“Wurinka Alhaji ya zo. Ka gane shi ko?”
“A’a” Alh. Mukhtar ya faɗi da gaskiyarsa “sai dai fuskar kamar na san mai irinta.”
Muryar nan ta Alhaji a dake ta fito ya ce “Ɗana Ahmad Hayatu Sule Maitakalmi ko?”
Idanu Alh. Mukhtar ya zaro “Alh. Hayatu? Kai ne? Ikon Allah.”
Ɗaya daga cikin Alhazan da su ka zo tare Alhaji ya cewa ya yi bayanin matsayinsa a garesu. Tiryan tiryan kuwa ya yi duk da sun cika da mamaki. Bayan ya gama kana ganin Alh. Mukhtar ka san ya gama rikicewa don gumin da yake ko ruwan sama albarka. Alhaji ya ce waɗancan biyun su ɗan basu wuri. Su na fita ya soma faɗa.
“A lokacin matarka ta so sabauta rayuwar ɗana. Shi yasa na ajiyeka a nan domin in kare Ahmad. To yau kuma an wayi gari taje tayi abin da ta saba tana neman shiga tsakanin wani ɗan nawa da matarsa.” Ya yi maganar cikin ɗaga murya.
“Alhaji ban sani ba wallahi…”
“Ta yaya za ayi ka sani bayan kaima juyaka take yi?”
“Kada kasa su koreni. Ina da ƴaƴa wallahi.” Ya ce hankalinsa na neman gushewa.
“Ka ce ni Hayatu na ce ta karya asirin. Ita ko wani nata sun yi kaɗan su tarwatsa rayuwar zuri’ata. Taj ba ɗanta bane. Idan na ƙyaleta akan Ahmad saboda haƙƙin uwa ne. Amma muddin ta sake shiga rayuwar wani nawa wallahi sai ta ɗanɗani kuɗarta. Ni da kake gani kaza ne akan ƴaƴana. Ina iya taka abuna idan sun min ba daidai ba domin su gyara. Amma idan wani ya kamanta zai sha tsatstsaga har sai anga jini. Ina fata ka fahimceni.”
Jikin Alh. Mukhtar babu inda baya rawa. Bai taba ganin mutum mai ban tsoro da kwarjini kamar Alh. Hayatu ba.
“Na gane. Don Allah ka yi haƙuri.”
Alh. Hayatu ya tashi “ina son ganin canji a tattare da Taj kafin sati mai zuwa. Ta karya koma me tayi don ta sanni farin sani. Akwai irin abin da bana yafewa. Taɓa min ƴaƴa yana sahun gaba. Sannan ka tashi tsaye kamar kowanne magidanci ka nemi tsari daga sihirice sihircen marasa tsoron Allah.”
Ko kallon Alh. Mukhtar bai sake yi ba ya fita. A waje ya yi sallama da alhazawan nan ya kama hanyar Kano ko ruwan garin bai sha ba. Sallah kawai su ka yi su ka tafi.
***
Abu na maza, babu wanda ya yi tunanin raini ko surutu akan gidan Abba Habibu. Irin abin da mata za su yi ta gutsiri tsoma ana cewa me ya kai shi auren wadda bata kama ƙafar arziƙinsa da na iyayensa ba. Ahmad da Kamal sun zo. Sai ƙanin Inna da kuma ƙannen Alhaji guda biyu. Irin tarbar arziƙin da Abba ya yi musu ba ƙaramin daɗi su ka ji ba. Sun riga sun san ko waye, ba a ɓoyewa kowa ba. Ga amininsa Baba Maje, sai ƙaninsa Abdulƙadir da wasu ƴan uwansu maza da su ka lallabo su ka dawo rayuwarsa bayan ganin luɗufin da yake samu.
Abinci ne na gani da fađa su Ƴar Ficika su ka yi. Kuma kamar yadda ya yi alƙawari tuntuni ko hanyar gidan basu zo ba shi da yaransa. Baba Maje ya yi rawar gani ya kawo dubu ashirin a bayar tukwici. Abdulƙadir ma ya kawo sha biyar. Abba ya cike ya zama hamsin. Ƴan kawo lefe kuma su ka ƙi karɓa. Sai da Abba ya ce rainawa su ka yi saboda sun gan shi a haka. Ba shiri su ka karɓa aka rabu a mutumce.
Ko rabin awa basu yi da tafiya ba gidan ya soma cika da ƴan kallon kaya. Gashi Zee bata nan. Sajida ce kaɗai take ta fama. Sai ga Iyaa ta zo da Siyama da Ummi. Ta kuma umarcesu da taimakawa Sajida wajen saka ido akan kayan da kuma aikin buɗewa mutane.
Ƙiris ya rage Ummi ta haɗiyi zuciya ta bar duniya. Dama Baballe ne ya taho dasu a motarsa. Dolenta ta taho. Yawan akwatunan da irin kayan da ta gani ya birkita mata lissafi. Zuwa yanzu ma dai sakin aure ya kamata su ji anyi. Maimakon haka sai wannan uban kaya kamar za a buɗe shago. Dole ma ta kira Salwa idan sun koma gida.
Abin baƙinciki yadda Iyaa ta ɗora mata aikin kula da wata ƙaramar jaka da aka shaƙare da sarƙoƙin gwal, awarwaraye, zobba da kuma sarƙoƙi na fashion masu matuƙar tsada. Sai da Iyaa ta ƙirga komai harda sanya Siyama ɗauka a hoto sannan ta miƙa mata.
“Ko kwali ne ya ɓata to ku ɓata tare. Ki kula dasu sosai. A nunawa mutane arziƙin Hamdi amma a kula da masu ɗan hali da mahassada.”
Ummi za ta iya rantsuwar maganar mahaifiyarta da harshen damo ta fito. Bata sani ba ko tsagwaron baƙincikin da take ji a zuciyarta Iyaa ta gani. Haka nan ta karɓi jakar ba don tana so ba. Irin baƙincikin da take ji ba wai so take ta mallaki kayan ko ta sace ba. Ita da ace za su ɓace ko su ƙone ƙurmus Hamdi ta rasa da ko miliyan biyar aka damƙa mata ba za ta yi farinciki kamar haka ba.
*
Bayan tafiyar Alh. Hayatu, karatun ta nutsu Alh. Mukhtar ya yiwa kansa. Ya dinga haɗa ɗaya da biyu yana lissafin yadda yake aikata abubuwa da yawa bisa umarnin Mami kuma ba a son ransa ba. Ya yarda hannunka mai sanda Alhaji ya yi masa da zancensa na ƙarshe. Ji dai maganar Taj ɗin da ta ce dole ya auri Salwa. Gashi takanas akan yaron mahaifinsa ya zo ya yanka masa gargaɗi mai kyau.
Rasa tudun dafawa yayi ya kira babbar ƴarsa da wani tunsni ya zo masa. A gidan take shekara talatin da huɗu duk wanda ya zo da maganar aure da kansa yake gudu. Ita da duka sauran ƴan matan gidan su huɗu da samari biyu babu uwayensu mata biyu da yake aure kafin zuwan Mami sun fita ta ƙarfin tsiya. Ƴaƴan Mami a gidan huɗu ne. Salwa da ƙannenta maza biyu.
“Bushra ki ce da Mami wai na kira ban sameta ba. Kowa ya fita daga gidan zan turo mai feshin maganin sauro. Ke kuma ki zauna ki jirani. Idan akwai aikin yi ko share share bayan an gama sai ki yi.”
Saƙon nasa ta faɗawa Mamin da umarninsa na ta zauna tayi aiki. Mami ta saki murmushi. Yadda ta farraƙa shi da ƴaƴan yana burgeta. Gashi yau ko tishin tauna layar bata yi ba amma ya aikata da kansa. Salwa ta kira su ka fita. Samarin dama basa nan. Ita kuma Bushra ta sanar da ƴan uwanta duk su ka tafi maƙota. Ba a jima ba Alh. Mukhtar ya dawo.
“Faɗa min gaskiya Bushra, Mami tana da kayan asiri a gidan nan?”
Rawa jikinta ya fara. Idanunta su ka ƙara girma don tsoro da firgici.
A ƙagauce ya ce “Ba mu da lokaci. Ki faɗa min idan akwai.”
Kai ta gyaɗa. Ya ce idan ta san inda su ke maza ta nuna masa.
“Ban sani ba. Sai dai mu duba.”
Babbar rigarsa ya ajiye a kan kujera ya ce ta saki jiki su yi aiki da sauri. Ai kuwa yaga zafin nama. Duk gidan sun gaji da rayuwar da Mami ta ƙaƙaba musu.
Ɗakin Mamin suka fara zuwa. Yana karanto surorin neman tsari ya watso duka kayan cikin wardrobe ɗinta da kowacce durowa. Sun tsinci ƙulle ƙulle da wasu ƙwarya da tarkace guda biyar. Aka koma ƙasan gado nan ma akwai. Daga nan sai ɗakinsa. Abu ya ƙazanta. Kansa har ciwo ya dinga yi saboda tashin hankali. A ɗakin ƴaran gidan ne dai ba a sami komai ba. Kitchen ma Bushra ta nuna wani ruwa da ta kan ga Mami ta tsiyaya musu a girki. Ya ɗauka ya tuttular. Kit ɗinta inda take ajiye abubuwa masu mahimmanci ya ɗauka ya muƙa da ƙasa sai gashi ya buɗe. A nan ya tsinci laya mai sunansa da ake taunawa. Sai kuma masu sunan duka ƴaƴansa banda nata. Da kuma sababbi a leda ɗaya Taj, ɗaya Zainab (Inna).
“Wallahi Baba wannan take sakawa a baki ta ce kayi mana abu kuma sai kayi. Ko ranar da ka ce in na kuma fita zance za ka tsine min da ita tayi magana.”
Haƙuri ya bawa ƴar tasa. Ya rasa matakin ɗauka na gaba. Ita ta bashi shawarar su ƙona komai. Ya ce kada ta taɓa. Da tsintsiya da abin kwasar shara ya tattara komai ya tara a tsakar gida. Ya kawo fetur ya zuba sannan ya kira Mami ya ce su dawo.
“Har maganin ya fita?”
“An fasa, sai gobe.”
Masifa ta yi masa na katse mata baccin yamma sannan su ka taho gida. Ana buɗe musu gate ta hango shi daga shi sai ƴar shara a jikinsa ya sanya wasu tarkace a gaba. Su ka fito daga mota ta taho inda yake. Jikinta ne ya saki lokaci guda da ta gane mene ne a gabansa.
“Alllll….hhhhajjii? Mmmmene nee wannnnan?”
Haɗe rai ya yi sosai ya tura mata ashana da ƙafarsa.
“Ɗauki ki cinna musu wuta.”
Jikinta rawa ya kama yi sosai. Tana ta gumi ta rasa abin yi.
“Ɗauki mana!” Ya daka mata tsawa.
Ta kasa motsi sai ƙullewar ciki. Salwa da taga halin da babarta ta shiga ita ma tsorata tayi. Tunda bata san kayan mene ne ba durƙusawa tayi ta ɗauki ashanar.
“Baba ni bari na ƙona.”
Kafin Mami ta iya tare ta har ta ƙyasta ashana. Tana cillawa kuwa kayan nan su ka yi wata mahaukaciyar ƙara tamkar tashin gurneti. Mami tayi zaman daɓaro a ƙasa tana ihu.
“Kin kashe ni. Salwa kin kashe gidan nan.”
Da faɗa Alh. Mukhtar ya ce “ta dai kashe ki ke kaɗai banda gidana.”
“Mami kayan meye?” Salwa ta tambayeta ganin kuka take haiƙan. Bata sami amsa ba sai daga bakin babanta.
“Nagodewa Allah da Ya turo Alh. Hayatu gareni ya farkar dani mugun baccin da nake yi. Sai yau na gane ashe zaman waɗannan abubuwan muke yi ba aure ba.”
Mami kuka kawai take yi da gurnani. Hankalinta ya kai ƙarshen tashi. Idan ya saketa bata da tudun dafawa. A zaune ta ja jiki zuwa inda yake za ta kama ƙafarsa ya janye da sauri.
“Ka rufa min asiri.”
“Ki rufawa kan ki dai” ya dubesu ita da Salwa dake tayata kuka “yauwa, Alh. Hayatu ya ce in faɗa miki ki warware abin da ki ka yiwa ɗansa har su ke rigima da matarsa. Idan ba haka ba kuma ki jira martani daga gare shi.” Ya wuce ciki.
Mami ta zauna tana tumami da kuka kafin ta tashi ta bishi ciki da sauri.
“Wane ɗan? Taj? Wallahi ban yi masa komai ba.”
“Ki daina saurin kama sunan Allah tunda baki san shi ba. Da idona naga laya da sunansa.”
Mami ta kwantar da murya “Ayyaaa Alhaji, bamu yi amfani da ita ba. Dama na ajiye ne sai sun yi aure da Salwa. Ai ban baki ba ko….”
Ta juya babu Salwa babu dalilinta.
“Salwa? Alhaji ina Salwa?” Tayi maganar kamar wata zararriya. Tsoro take ji kada ƙona kayan nan ya janyowa ƴarta wani abu. Don dai tabbas malaminta ya sha yi mata kashedi akan kada ma wani ya gani balle a taɓa.
Ɗakunan gidan ta duba bata ganta ba. Tayi wajen gate tana faman kiranta ko kallon titi bata yi. Bata yi aune ba mota ta ɗebe ta tayi sama ta dawo. Maigadin Alh. Mukhtar da ya biyota yana son faɗa mata Salwan ta fita ne ya koma ya sanar dashi abin da ya faru. Ya fito su ka wuce asibiti tare da mai motar da ya bugeta.
Salwa kuwa tunda taji saƙon babanta hankalinta ya tashi. Indai Alhajinsu Taj ne ya yi waccan maganar kenan asirin ya kama su. Matsalar kawai tunda ake zargin Mami a hankali zsi gano ita ce. In haka ta faru kuma zai hana Taj aurenta idan su ka fara soyayya. Tasha ta wuce tunda da atm a jikinta ta ciri kuɗi sai Kano. Wurin Ummi za ta je ta taimaka mata da wanda za a rufe bakin Alhaji.
Motarsu ko fita gari bata yi ba Alh. Mukhtar ya kirata ya faɗa mata abin da ya sami Mami. Don baƙinciki sai da tayi kuka. Haka ta sauka daga motar ta tafi asibiti.
***
Mai shawara aka ce aikinsa ba ya ɓaci. Duka abubuwan da Inna ta sa Taj yi ya rungumesu hannu bibbiyu. Ƙuncin zuciyarsa ya ragu sosai. Duk da ya kan ji haushin Hamdi yana taso masa lokaci zuwa lokaci tunda fitar asiri sai a hankali, amma a zuciyarsa ya sani cewa ba zai taɓa iya rabuwa da ita ba kamar yadda ya dinga ji a kwanakin baya. Banda yawan addu’a, Inna ta sa yanzu ya ware plate goma na abinci kullum sai sun bayar sadaka. Ba wai ragowar na mutane ba. Mai kyau da an gama dafawa ake packaging. Ranar farko ma na mutum ɗari biyu su ka yi aka kai asibitin gwamnati. Kusan zai rantse ma daga ranar ya fara jin canji sosai. Ciyar da mabuƙata ba ƙaramin abu bane.
Duka wani jere da gyaran gidan amarya an gama shi a farkon sati. Duk wanda ya shiga kamar kada ya fito. Hatta kayan da za su saka Kamal ya kai wa Hamdi nata ana jibi fara biki. Bayan ta shiga gida ta gwaggwada ta dawo ta same shi. Ta faɗa masa babu wanda yake buƙatar gyara. Sai kuma tayi godiya sosai.
“Yanzu yaya kike ji game da ɗan uwana?”
Kai ta sunkuyar tana murmushi. Da ya sake yin tambayar ta ce “Alhamdulillah.”
“Kina ganin faɗa ya ƙare? Za ku iya zama babu tashin hankali?”
“Ban sani ba ko daga wurin shi.” Ita ce amsar da ta bayar da ƙaramar murya.
“Nayi magana da shi. Ke nake tambaya kuma.”
Kunya ce ta isheta ya ce gara ma ta daina domin tunda ta shigo danginsu ta sani cewa bayan shi yanzu ta sami ƙarin ƴan uwa. Kuma kowa zai tsaya mata idan Taj ya yi nufin cutar da ita.
“Zan iya in sha Allah.”
“Alhamdulillah. Kamar yadda na faɗa masa ku bi komai a sannu. Kada ku ce dole a yau ko gobe ku ke son ganin alaƙarku ta dawo kamar da. Wannan zai janyo muku too much expectation, wanda kuma rashin samunsa zai sa ku zama disappointed.”
“In sha Allah zan kiyaye.”
“Hamdiyya”
Mrs Happy ya saba kiranta. Shi yasa Hamdiyyar ya faɗar mata da gaba.
“Na’am Ya Kamal.”
“Don Allah ki riƙe min Taj amana. Abubuwa da yawa sun same shi. Yana buƙatar inda zai sami kwanciyar hankali.”
Ɗan murmuhi tayi “ai kana nan Ya Kamal sai mu dinga shawara. Ka fini sanin abin da ya dace da shi.”
Murmushin da Kamal ya mayar mata mai matuƙar rauni ne. Da ace idanunsa ma take kallo za ta ga sun kaɗa.
“Yanzu ke ce mafi kusa dashi.”
“Ba zan shiga tsakaninku ba in sha Allah” ta faɗi da sauri.
“Rayuwa da yau da gobe za su iya shiga. Ni dai na baki amanar Happy. Please Hamdiyya, give him the happiness he deserves.”
Har ya tafi tana juyayin maganganunsa masu kama da sallama. Anya lafiya kuwa?
***
Idan ka ji yara na waƙar gobe Juma’a, kuturu dariya yake ko zai sami ɗan kwabo to lallai ranar ta kama Alhamis. Ta wannan satin ita ce ranar Kamun amarya Hamdi wadda iyayen ango Taj su ka yi rawar gani wurin tsara taro na burgewa. Biki ne na ƴan kasuwa kuma ƴan boko. In baka yi bani wuri. Sun tsara abinsu na yau ma mata kawai. Mazan gidansu ko mutum ɗaya ba a yarje masa zuwa ba. Daga DJ ɗinsu kuwa har mai hoto da MC duka mata ne. Daga cikin wani katari da Alh. Hayatu ya sake yi a rayuwa harda dacewa da kyakkyawar tarbiyar ƴaƴansa akan sunnar Fiyayyen halitta SAW. Ba dai a rasa nono a ruga, wani dole sai ya bauɗe. To amma dai majority a gidan sun ginu da wannan tarbiyar ta iyayensu mata. Wannan yana daga cikin dalilan da su ka sa Alhaji ya kan kasa yiwa wanda ya kuskure uzuri. Shi fa kusan komai Allah Ya bashi. Bai san wani nau’i bane na gwajin rayuwa. Idan ya ƙanƙantar da kai ya yarda rahama ce daga cikin taskar Ubangijinsa sai Allah Ya ƙara masa da lada mai gwaɓi. Idan kuwa girman kai da jin cewa isarsa da iyawarsa ne su ka bashi kamar yadda ya tsinci kansa yanzu, to dama Allah barin mutum yake da iyawar tasa.
Ƙarfe ɗayan rana mai kwalliya ta zo ta fara rangaɗawa Hamdi bayan tayi sallar azahar. Jiki ya sha gyara na gaske saboda haka in ka ganta sai ka ƙara kallo. Ga ƙamshi wanda da kanta ta ce a bar turara mata jiki haka nan saboda kada ta fara ɗaukar zunubi a cikin mutane.
Tana idar da sallar la’asar ta saka kaya aka ɗaura mata ashoke. Da ta fito daga ɗaki Yaya tashi tayi ta bar wajen. Bata son kowa yaga ƙwallar da ta cika mata idanu. Yau ita ce Allah Ya nufi ƴarta da auren gata irin wannan. Da bikin Sajida abin bai yi armashi sosai ba saboda tangal tangal da auren ya soma yi tun kafin a ɗaura shi.
Leshi ne haɗaɗɗe mai laushi aka yi mata ɗinkin gargajiya wato buba da zani. Ado da kyan leshin kaɗai sun wadata ba sai an ɓata ɗinkin da tarkace ba. Ruwan toka ne da adon ja kaɗan a jikin zare sai navy blue ɗin fulawoyi. Ta riƙo jar ƙaramar jaka ta amare tana kuma sanye da jan takalmi mai tsini da maɗauri. Ashokenta na ka da na kafaɗa navy blue da silver. Sai wata danƙareriyar sarƙa mai duwatsu navy blue su ma da ja. Make up ɗinta na hankali bata koma aljana a kwaba ba.
A tsakar gidan aka tsaya ana ta ɗauke ɗauken hotuna da ƴan uwa. Bata sani ba ashe Taj ya kirata ya kai sau shida. Amma ce ta turo shi ɗauko musu amarya. Fitowar tasa ma sai da tayi da gaske. Anti Zahra tun safe ta bar gidan. Su na can gidan Alh. Lurwanu yayan Inna don a nan za ayi Kamun. Saboda ƙurewar lokaci basu iya samun event centre ba.
A waya ta faɗa masa cewa ana la’asar yaje ya ɗauko Hamdi. Hankalinsa a take ya tashi. Wato ƴan kwanakin nan da ya soma dawowa daidai babu abin da yake gudu kamar haɗuwa da amaryar tasa. Da wane baki zai bata haƙuri akan marin da ya yi mata? Inna bata ce masa komai akan asiri ba tunda Yaya Malam ya gargaɗeta da zargi. Gani yake girmansa ya gama zubewa a idanunta. Namiji mai dukan mata bashi da wata daraja a idonsa.
“Bari na faɗawa Happiness ya shirya mu tafi da wuri.”
“Kai Happino. Nace happino” Amma tayi magana a fusace “ɗauko matar auren naka ma sai da shi? Ince ko daren farkon ma tare za ku.”
Da mamaki ya ce “Amma me ya yi zafi? Kamal nake nufi fa.”
“Shi ɗin fa! Ku yanzu sam baku iya lissafi da zurfin tunani. Dama me yasa ake haɗa angwaye da ƴan rakiya? Ai saboda gudun fitinar zamani ne. Ku kuwa tunda an riga an ɗaura aure me za ka yi da ɗan rakiya?”
Dariya sosai ta bashi ya ce “to Allah Ya baki haƙuri. In kina so ma sai na ɗaukota na kai muku ita har kujerar da za ta zauna.”
“Ɗan banza mai bakin tsiya. In baka yi wasa ba wallahi har wurin zaman sai in ce ka kawota mu ga ƙarshen rashin kunya.”
“Cewa dai za ayi tarbiyarki ce.” Ya ce da tsokana.
Ita ma da ta san hali bata san me ya sa ta biye masa ba. Rabuwa tayi da shi bayan ta tuna masa ƙarfe biyar daidai su ke son farawa.
Da ya faɗawa Kamal yadda su ka yi a wayar dariya su ka dinga yi son ransu. Kamal na cewa Happy ya girma shi kuma yana baya so.
“Ni wallahi kunyar haɗuwarmu ma nake ji.”
“Hamdi fa bata da matsala. Kawai ka bata haƙuri a wuce wajen.”
“Kaga last faɗanmu kuwa da na kai mata kati? Tana faɗa ina yi kamar wasu kaji. I am seriously ashamed og myself.” Ya rufe fuska da tafukan hannayensa.
“Dalla kada ka bada maza. Kawai ka sabunta mata karatu yau yau ɗinnan. Su fa mata kana rarrashinsu ka gama dasu.”
Taj ya gyaɗa kai “Allah bari in samu a kai min rigimammiyar nan gida. Zan yiwa su Mama famfo akanka sosai. Dr. Mubina will be Mrs Happiness.”
Kamal murmushin yaƙe kawai ya yi. Taj ya yi wanka ya saka shirt da wando abinsa ya zo zai fita.
“Wani sabon salon wulaƙanci ne wannan ko me? Ina kayan da Abba ya karɓo daga wajen tela?”
“Direba fa zan yi. Amma ta ce ba zan shiga ba. Kuma kawai sai na saka sababbin kayana su yamutse?”
“Kaina ciwo yake Happy. Bani da ƙarfin yi maka surutu. Kayi abin da ya dace ka fita.”
Kamar ya yi musu sai dai yaga babu alamun wasa tattare da Kamal ɗin. Dama kuma tsokana ce tasa shi saka waɗancan. Ya canja da wasu sababbi cikin na bikin. Sai gashi yayi kyau sosai. Ya tambaye Kamal ko zai sha magani ya ce a’a. Gajiya ce.
Taj na fita ya kira Mubina ya faɗa mata jikinsa fa babu daɗi. Tana hanyar zuwa wurin kamun ita da ƙanwarta don har gida Yaya Kubra ta aika mata katunan bikin duka. Dole ta juya ta koma asibiti. A hanya ta sauke ƙanwar ta ta tace mata patient gareta.
Ruwa ta saka masa da wasu magunguna masu ƙarfi har ya dawo daidai.
“Ban faɗawa Dr. Kubra ba saboda bana son raba mata hankali. Ciwon nan mun barshi tsakaninmu zuwa lokacin da za a gama bikin ɗan uwanka kamar yadda ka buƙata. Idan bata faɗa ba ni zan je har wajen Alhajinku wallahi.”
Ranta a ɓace yake. Kamal ya yi mata murmushi.
“Wannan faɗan duk don na hanaki zuwa cin shinkafar biki ne ko?”
Harara ya samu “Wasa ma ka mayar da abin?”
“Sorry Doc.” Ya ɗauko wayarsa dake gefen gadon “zo mu yi hoto.”
Yadda ya yi maganar ya taɓa mata zuciya. Tayi murmushi duk da tana ƙoƙarin nuna masa fushinta. Ya gyara zama ta koma gefensa ta zauna tayi musu selfie. Tana tashi ya ɗauketa wasu. Bai taɓa ganinta da kwalliya irin ta yau ba. Kasa haƙuri ya yi ya ce da ita,
“A misali da zan warke za ki iya aurena Mubina?”
Abin control ɗin gudun ruwan da take ƙara masa take dubawa da ya yi tambayar. Yasa ta kusa ture ƙarfen gabaɗaya saboda yadda zancen ya taɓa ta. Allah Yasa bayanta yake kallo da yaga halin da ya jefa zuciyarta. Tattaro nutsuwa tayi
“A’a.”
“Ni? Ni?” Ya nuna kansa kamar yato ya sanyata dariya “nayi tsammanin za ki bani amsar da zan ji daɗi.”
“Baka cancanci hakan ba Kamal. You are very stubborn. Rantsuwar dake kare alaƙar likita da patient ce kawai ta hanani yi maka handsfree.”
“Na nawa kuma? Ba kin faɗawa Yaya Kubra ba?”
“Da kai da ita akwai wanda zai rantse cewa na faɗa? Magani ta gani ta zo tayi tambaya.”
Kallonta kawai yake yi yana jin inama ƙalau yake. Da ita ma tana wajen Kamu ana kama masa ita.
“To da ace ni ɗin patient ne mai bada haɗin kai irin yadda kike so, za ki iya aurena idan na warke?”
Sai da ta kalli idanunsa sannan ta bashi amsa “Da gudu” sai kuma ta soma hawaye “please let us help you Kamal. Akwai dama indai mu ka sami donor. Kada ka ɗora min zawarci tun kafin nayi aure don Allah.”
Tana gama faɗin haka ta fice saboda kukan da take shirin yi a gabansa. Shi ma hawaye ya goge bayan ta fita. Yana tsoron sanya rai da rayuwa bayan samun lafiyarsa ba abu bane mai sauƙi. Shi yasa yake ta kaucewa sanar da mutane. Amma zai bi shawararta. Idan an gama bikin Taj da kamar sati ɗaya da kan shi zai faɗawa iyayensa.
*
Mota Sajida da Fadila su ka rako Hamdi bayan an rufa mata wani net ja wanda dama an faɗa musu da shi za ta fara shiga. Sai an yi kamun za a cire mata. Haka aka rufe motar gabanta yana matsanancin faɗuwa.
A hankali yake tuƙi cikin nutsuwa. Ƙamshin da take yi ya kwance duk wani notin arziƙi na kansa. Yana son yi mata maganar abin da ya faru amma yana jin nauyin hakan. Kamal ya ce ya bata haƙuri. Amma idan kuma ya bata ta sake yi masa maganar da wancan yanayin zai dawo fa?
Tsoron da yake ji bai kai nata ba. In ka cire gaisuwar da tayi masa a gaban su Sajida bata sake ko da ɗaga kanta ba. Kwata kwata bata yarda da bakinta ba. Yanzu dai lafiya ƙalau su ke tafiya. Idan kuma tayi magana irin kalaman nan dake fita da kansu su ka bar harshenta fa?
Kowa kama bakinsa ya yi. Da Salwa za ta ga yadda aikinta ya yi tasiri a wajen nan da ta daka tsallen ƴan bori ta dire don murna.
Shirun damunsa ya yi ya kunna musu rediyo. Tashar farko da ya samu ya bari. Aka yi dace ko rashinsa domin kuwa a daidai lokacin mai tallan maganin gargajiya ce take ta kwararo bayanin maganin basir.
(Wato shi fa basir idan yaci jikin magidanci sai kaga ko kukan jarirai an daina yi a gidansa. Cikinsa kullum a ƙulle tamau kamar yarinya tana koyon ɗaurin zani. Da shi da matarsa babu maraba. A jaraba maganin nan domin kawo ƙarshensa. Akwai mai tsiro, da mai jini.)
Cikin kujera Hamdi ta shige saboda tsabar kunya. Mai magani ta cigaba da ɓaro zance mai nauyi. Aka barta da satar kallon Taj. Ɗan duniya da ya fahimci kunya take ji sai ya ƙara volume. Can sai cewa yayi
“Nagode Allah ni dai ƙalau nake. Masu fama kuma Allah Ya yaye musu.”
Shiru tayi tana ƙifta idanu. Gara yayi mata waƙoƙinsa akan wannan magana.
Kallonta ya yi ya saki murmushi. Wani irin jindaɗi da nutsuwa yake ji a ransa.
“Ko kina da shi in saya miki…”
“Innalillahi…” ta kalle shi babu shiri ta yaye lulluɓin.
Numfashi ya ja da ƙarfi da su ka haɗa ido. Tayi masa kyau ba kaɗan ba.
“Ni lafiyata ƙalau wallahi.”
A daidai lokacin mai maganin ta zaɓi ɗora zancenta da dawowa kan mata.
(Na dawo gareku matan gida. Ina da magunguna sahihai waɗanda mu ka gada tun kakanni. Maganin sanyi da magungunan mata masu gigita maigida.)
Hannu ta kai za ta kashe rediyon ya damƙe shi yana murzawa a hankali.
“Don Allah ka canja.”
“Shhh…an zo wajen naku. Bari mu ji.”
“A ji me?” Ta tambaye shi looking horrified.
(Mace sai ta bari sanyi ya gama cinye mata jiki. Sai miji ya mayar da ita bora sannan za ta fara neman magani. Ina mai fama da ƙaiƙayin…)
Hamdi ta dube shi kamar tayi kuka.
“Allah idan baka kashe ba zan iya yin kuka.”
“Allah Ya baki haƙuri. Daga taimako?”
“Ba na so.” Ta turo baki.
Soyayyarta da ta kwanta wucin gadi ta dawo masa sabuwa fil. Ba ƙaramin kewar wannan Hamdin yayi ba. Yana son faɗa mata amma sun riga sun iso gidan Alh. Lurwanu. Inda zai ajiyeta Amma ta faɗa masa bayan ya shiga ciki da motar. Yana hango masu rakata wurin zamanta su Zee da su Firdaus.
“Wanne zan saya miki? Kin dai ji ance mace bora take zama idan bata sha ba.”
Tsuke bakinta tayi. Sai da ya buɗe lock za ta fita ta yi magana a hankali yadda babu mai ji cikin ƴan rakiyarta.
“Nafi ƙarfin zama borar gida.”
“Za ki maimaita wannan maganar nan da saturday.”
“Allah Ya kaimu” ta faɗi sannan ta ƙifta masa ido don tsokana.
A tunaninta za ta samu guduwa ne a lokacin. Sai gashi su Firdaus sun dage sai sun yi musu hoto kafin a shiga da ita ciki. Fitowa yayi daga motar ya tsaya a gefenta.
“Kai Uncle Taj. Irin wannan hoton tun zamanin su Mama. Ku ɗan ƙara matsowa mana.”
Hamdi bata ankara ba taji ya janyota kusa dashi. Hannunsa ɗaya a tsakiyar bayanta. Jin kamar za ta faɗi sai ta ɗora nata hannuwan a kafaɗunsa.
“In miki waƙa?” Ya ce a saitin kunnenta. Hakan ya bada style na hoton masoyan da su ka yi nisa da ƙaunar juna.
Ta san tsokanarta yake yi shi yasa tayi dariya. A haka aka ɗauki hoton. Ya yi kyau sosai.
Bayan an gama taro mai ban sha’awa da Firdaus ta koma gida ta dinga ɗora hotunan kamu a status. Kuma wannan hoto shi ne na farkon da Salwa ta fara cin karo dashi. Zuciyarta a take ta ɗauki zafi. Ta juya ta kalli Mami dake kwance tana bacci ga yawu yana dalala ta gefen bakinta. Dole taje Kano ko ta wane hali. Wayarta ta ɗauko ta kira Ahmad ta faɗa masa hatsarin da Mami tayi da roƙonsa akan ya dawo dasu Aminu Kano Teaching Hospital saboda a nan Bauchi babanta yaƙi sakin kuɗi a dubata yadda ya dace (a ƙaryarta). Duk da baban nata ya gargaɗesu da ƴan uwanta da su yi shiru har sai ta farfaɗo saboda bai san me zai cewa Ahmad ɗin ba. Yana kunyar yaron kuma yana tsoron sake ɓatawa Alh. Hayatu rai.
“Me ya sa zai ce kada a faɗa min? Kwananku nawa a asibitin? Shi ne kullum idan na kira ki ke min ƙaryar ƙauye ta tafi” Ahmad ya ce cikin tashin hankali.
“Sharri aka yi mata wai tayi masa asiri.”
“Zan kira shi mu yi magana. Ku shirya, idan na zo gobe in sha Allah sai mu taho tare.”
MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
