Rayuwa Da Gibi – Chapter Twenty-nine
by NadminMASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
Kun kira
Kun turo saƙo
Kun zo dubiya har asibiti
Ni kuwa me zan ce da masoyan SonSo idan ba kyakkyawar addu’a da fatan alkhairi ba?
A yayinda da nake post babu abin da yake yi min daɗi sama da kyawawan addu’o’in biyan buƙata da ku ke yi min. Wannan addu’ar ita ce babban abin dake ƙarfafa min gwiwar typing ko da jikina baya min daɗi domin bawa bai san alkhairin bakin mutane ba. A yau ina mai ƙara godiya ga Allah da ku bakiɗaya. Na sauka lafiya na kuma sami lafiyar jiki bayan aikin da aka yi min. Ahmad Amir dani da duka ahalinmu muna godiya da karamcinku.
Nayi kewarku da sharhinku mai sanya ni nishaɗi. In sha Allah zan cigaba da posting sai dai ba zai zama kullum ba. Sai kun ƙara haƙuri saboda yanayi ya ƙara canjawa. Ga ƙaramin goyo, yara, ɗawainiyar gida da aiki. Duk da haka kada ku sare da tunanin jira zai dinga tsaho. In Allah Ya yarda labarin zai cigaba cikin amincin Allah.
SonSo
***
Idan kaga yadda ake shiga gidan Alh. Hayatu sai mutum ya rantse gayyar mutane ce masu zuwa biki. Nan kuwa kaf ɗinsu ahalin gidan ne. Babu bare ko ɗaya sai masu aiki. Ƴaƴansa ne da jikoki. Kuma a haka wasu ba a nan za su kwana ba. Falon kamar ba zai ɗaukesu ba saboda yawa. Da yake an gama gajiya, rabon wajen kwana kawai aka tsaya yi.
“Duk wanda ya san ya fita ya bar kaya a falo ko cikin ɗakuna tun wuri aje a kwashe. Ba za ku dame mu da cigiya ba gobe.” Cewar Ummukulsum ga jikokin. Ita ce babbar ƴar Yaya Hajiyayye kuma jika ta farko a gidan ta girmi Firdaus ƴar ajin su Hamdi.
“Ni dai ban ga kayana da na ajiye a nan ba…”
Cigiyar da take gudu tunda ta san komai wajenta ƙannen za su zo nema mazansu da matansu aka fara yi daga rufe bakinta. Kula su ka yi falon a gyare yake. Aka tambayi masu aiki kowacce ta ce ba ita tayi ba kafin su tafi. Abin da mamaki dai.
“To ko dai Alhaji ne? Naga motarsa…”
Hamɓare bakin mai maganar Yaya Samira tayi kafin ta kai ƙarshe.
“Baban namu ne zai yi muku gyaran falo don rainin wayo?”
“Gani Mugenbo shugaban marasa kirkin duniya ko?”
Muryarsa su ka ji kafin su gan shi yana fitowa daga ƙofar ɓangarensa dake cikin falon. A gurguje masu ƙuruciyar ciki su ka yi kansa saboda sabon da su ka yi dashi. Ƴan matasan kuwa su ka shiga sunne kai.
Manyan kuma dariya su ka yi. Su sun fi sanin baban nasu akan ƴan baya baya da su ka taso lokacin da ya fara fushi da Taj. Tsaurin ra’ayinsa bai hana shi kamanta mu’amalantar iyalinsa yanda addini ya tsara bakin gwargwado a lokacin ba. Dalilin da yasa ma ya sami damar iya tafiyar dasu akan ra’ayinsa kenan koda zuƙatansu basa son abu. Ya yi ƙoƙarin toshe duk wata kafa da zata sa iyalinsa su butulce masa.
Cikin jikokin wani ɗan shekara biyar zuwa ya yi jikinsa ya tsaya yana fuskantar wadda ta ce ko Alhaji ne ya kwashe kayan.
“Alhaji ba ya yin aikin mata. Shi ba ɗan daudu bane.”
Tsit falon yayi. Kunya ta kama su aka rasa mai kwaɓarsa. Alhaji ya jinjina maganar musamman da ya karanci yadda kowa ya sha jinin jikinsa. Duk sai yaji babu daɗi.
Murmushi ya yi na jin kunyarsu ya dafa yaron “kwashe kaya da ninkewa ai ba aikin mata bane kaɗai Amir. Duk wanda zai iya saka kaya ya kamata ace zai iya ninke su.”
“Laahhh, Uncle Taj ma ba ɗan daudu bane kenan ko?”
“Me yasa ka ce haka?” Alhaji ya tambayi yaron da sakakkiyar fuska don ya bashi amsa.
“Saboda duk wanda ya iya cin abinci shi ma ya kamata ya iya dafawa.”
Mahaifiyar Amir kasa tsayuwa tayi saboda tsoron me Alhaji zai yi bayan jin amsarsa. Ta kalli yayyenta su Yaya Kubra tana neman ceto.
Matan gidan ne ƙarshen shigowa dama. Saboda haka daga baki bakin ƙofa suke tsaye. Hajiya tana kallon idon Alhaji ta yiwa Amir tambaya.
“Kai ka san waye ɗan daudu?”
“Eh mana” ya amsa da karsashi na yaron da aka yiwa tambaya mai sauƙi “sune masu yin haka…” ya ɗaga hannuwa ya tafa da iska “ahayyyeee cass, rass… ko?”
Hannuwansa Bishir ya yi saurin riƙewa ya ce “dare ya yi, ayi shirin bacci a kwanta haka nan.”
Da sauri sauri su ka dinga watsewa aka bar Alhaji a tsaye cikin tunani da wata irin kunya. Yau kuma yaro ɗan shekara biyar ne ya shiga sahun masu faɗa masa gaskiya? Kuma wannan karon a gaban mutanen da yake jin ya isa dasu ta kowacce fuska!
“Alhaji na ce Allah Ya bamu alkhairi.”
Da muryar Umma tunanin da ya fara ya kau ya dawo da hankalinsa ga matansa. Hajiya ma sai da safen tayi masa ta shige yayinda Mama tayi masa tambayar ko ya gama da kwanukan abincin dare da ta ajiye masa domin ta kwaso. Amsa ya bata sannan ya mayar da dubansa ga neman Inna don tunda su ka shigo ko tari bai ji tayi ba. Jiran ta ce masa sai da safe kamar ƴan uwanta yake sai yaga bata wajen.
‘Fushi take? Me kuma nayi? Ba na bada izinin yin bikin ba? Sai da safen ma yau ban isa ace min ba?’ Ya ayyana a zuciyarsa.
“Ba tare ku ka shigo da Abu bane?” Ya tambayi Mama.
Yanayinta yaga ya sauya sannan ta ce masa ya shiga ɗakin Innar ya sameta. Hankalinsa tashi ya yi don ko bata faɗa ba yaji a jikinsa babu lafiya. Tabbas Hajiya da Umma ma basa cikin walwalar da yayi tsammanin za su dawo da ita.
Ɗakin ya shiga kai tsaye ya tarar da ɓangarenta da ƴan kwana. Wuce na falon ya yi ya shiga ainihin ɗakin baccinta inda nan ma wasu ke ciki. Sai dai suna ganinsu su ka fita. Zai yi magana ta riga shi ta hanyar miƙa masa wannan layar.
Ya miƙa hannu zai karɓa kenan sai Inna taga ya yi baya da hannunsa da sauri yana zaro idanu.
“A’uzubillahi…”
“Ka san ko mene ne kenan?” Ta ajiye layar a wajen madubi jikinta a sanyaye.
“A ina ki ka samo ta?” Ya tambaya cikin matsanancin tashin hankali fiye da wanda tayi tsammani.
“Sal…”
Kafin ta kai ƙarshen sunan ya gane wa za ta ce. Ya ɗaga layar yaga sunan Taj. Ransa kuwa ya yi mummunan ɓaci.
“Ɗana? Me matar nan ta taka da har take tunanin zan zuba ido ta mayar min da ɗa mutum mutumi?”
Inna na jin haka nata hankalin ya sake tashi.
“Mugun tsafi ne ko? Innalillahi. Tun a wajen naga ya fara runtse idanu.”
Maganarta sake tunzura zuciyar Alhaji tayi. Sirrin da ya sakayawa Mami albarkacin Ahmad ya dawo masa tar cikin ransa. Haƙiƙa kamar sauran matansa ita ma so ya saka shi aurenta. Ta zo da fitina da neman rigima. Kullum cikin takalar Hajiya da Mama faɗa dake gidan a lokacin take. Aka mayar masa da gida filin kai ƙara. Wani abin idan tayi shi kan shi sai ya yi mamakin mene ne abin tashin hankali a ciki da har za ta nemi faɗa. Abin mamakin ma shi ne kasancewar shi ɗin jajirtaccen namiji ne amma ko zai ari baki wajen yi mata faɗa da nasiha anjima ko gobe ma sai ta ƙara. Sannu a hankali ya shiga karantarta inda ya fahimci ashe asiri take yi masa, kuma yawan rigimarta tana yi ne domin aunawa taga ko sihirin ya ci. Bai gama tsinkewa da lamarin ba sai da yaga wannan layar da yaji da kunnuwansa ranar da Zabba’u ta kawo mata tana cewa sunanta Raƙumi da akala. Har tana yi mata rantsuwar idan ta tauna ko me ta umarce shi zai aikata. Burinta a lokacin tunda ta haifi Ahmad yana ƙarami ta fitar da su Hajiya.
Ƙin nuna musu ya gani ya yi. Ya kuma bari tayi amfani da ita. Ranar ta yiwa Hajiya ɗiban albarka ajin ƙarshe duk yana jinsu daga ɗaki. Zuciyarsa kamar ta fito ta baki amma ya kasa fitowa saboda a kan idonsa ta saka a bakin ba tare da ta san yana gani ba. Ta tauna ta umarce shi da ya zauna a ɗaki kada ya fito ko me zai faru.
Haka kuwa aka yi. Rigima ta kaure amma duk yadda yaso haka ya zauna a ɗaki. Don baƙinciki har hawaye sai da ya yi. Sai kuma ya shiga karanto addu’o’in tsari tunda ya gama gano illar layar. Lallai idan ya zauna da ita rayuwarsa za ta zama mara amfani.
Shigowa Mami tayi da aka gama faɗan tana kumbure kumbure.
“So nake ka saki Haj. Gambo yanzu yanzun nan.”
Ko ɗaga kai ya kalleta bai yi ba ta sake maimaita umarnin amma shiru. Dama layar na hannunta sai ta ɗaga ta juya masa baya za ta mayar cikin bakin. Bata yi aune ba taji ya damƙe hannun ya zare layar.
“Ki je gida na sake ki saki uku.”
Farat ɗaya ya faɗi maganar don kada a sami matsala. Ta kuwa dafe ƙirji a gigice.
“Haj. Gambo nace…”
Ƙarfin gwiwarsa ya dawo gare shi ya ce “ni kuma ke nace.”
“Wallahi baka isa ba…wayyo Allah. Na shiga uku. Alhaji ina zani? Ina kake so nayi da Ahmad bayan ka san ni marainiya ce?”
Gabaɗaya kamanninta sauyawa suka yi a take. Tana wannan hargagin ya kira Mama ya ce ta ɗauko Ahmad duk inda yake a gidan ta goya shi.
“Idan ba ni ba kada ki bawa kowa har uwar da ta haife shi.”
Mafarin da goyon Ahmad ya koma hannun Mama kenan. Ba a raba ɗa da uwa amma bai san sunan da za a kira shi ba idan ya bari jininsa ya tashi a gidan shirka. Haka ya nunawa iyalinsa cewa faɗan da ta takali Hajiya ne yasa shi sallamarta. Ya kuma yi ne don kyautata ƙimar ɗansa a gidan. Daga lokacin bai sake shiga harkarta ba sai da ta fara ɗorawa Ahmad ɗin buƙatun da su ka fi ƙarfinsa yaje ya samawa mijinta aiki. Baya son haɗa inuwa da mushiriki kuma wanda yake tu’ammali da tsibbu. Shi yasa ya nesanta kansa daga gareta. Baya bari komai ya haɗasu. To amma yau dai tura ta kai bango. Idan tana cin ƙasa lallai ta kiyayi ta shuri. Ƴarta ko ita ce autar mata kuma masoyiya ga Taj ba zai taɓa sahale masa aurenta ba.
Wayarsa ya ɗaga da sauri ya kira Taj…abin da rabonsa da yi har ya manta.
***
Ƙirjin Anti Zahra dukan tara tara ya kama yi da ganin wannan rashin hankali da ake yi mata a gida. Inda su ka sami ƙarfin halin iya shigar mata kitchen su ka yi binciken kayan abinci da girki shi ne babban abin mamaki. Gashi an zuzzubar da shinkafa akan kafet. Yaran babbar ƴar Anti Zabba’u sun tattake wata a wurin. Ƙarnin kifi kuwa ba a magana. Maiƙon duk an shafe a kujeru da centre table don ƙeta. Wata ma remote ne a hannunta na daman. A hagu kuma tana riƙe da kofin da aka keɓe domin maigidan ta cika shi da juice.
Shi kuwa Ahmad Anti Zabba’u da Salwa yake kallo yana neman wadda za ta yi masa bayani. Saboda yadda ransa ya ɓaci kuwa Adam’s apple ɗinsa hawa da sauka kawai yake yi ya kasa magana. Gani yake duk kalmar da za ta fito bata da ƙarfin nuna yadda yake ji a zuciyarsa.
Anti Zabba’u ko a jikinta domin da shirinta ta fito. Ta saki rai tayi musu maraba kuma bata damu ba da basu amsa ba. Sai ma kaɗa baki da tayi ta ƙwalawa ƴarta da ta tafi kitchen ƙaro musu juice tayi. Ita ce ake so Ahmad ya aura yanzu.
“Habitti (Habibty take kiranta saboda tafi ƴan uwanta kyau, sunan sai ya bita) fito ga yayan naki ya dawo.” Ta kalle shi “tun ɗazu take damunmu da mitar ka ƙi dawowa.”
Daga cikin kitchen ɗin aka ƙwala ihu duk wai na murna sannan wata ƴar tsumburburar budurwa ta fito da sassarfa cikin farinciki. Sanye take da matsatsen wando skin tight wanda daga gani a can ƙasan dilar gwanjo aka samo shi. Ta ɗora masa wata yarbatsulan riga mai rawa a jiki da wasu irin igiyoyi. Sai da ta tabbatar ta haɗa ido da Anti Zahra sannan ta buɗe hannuwa.
“Yaya Ahmet oyoyo.”
Saurin shiga tsakaninsu Anti Zahra tayi don ta kula Ahmad bashi da niyar kaucewa.
“A gabana? Baki da hankali da alama.” Cewar Anti Zahra cikin fushi “nayi miki kama da matan da za su ɗauki wannan ɗabi’ar ta wasan banza tsakanin cousins?”
Da wani salon shagwaɓa Habitti ta ce “Ya Ahmet kana jin matarka ko?”
Ko kallonta bai yi ba balle tasa ran yaji ƙorafinta. Hankalinsa ya tattara ya dubi matarsa.
“Me yasa ki ka shiga tsakaninmu Zahra? Da kin barta ta ƙarasa abin da tayi niyya.”
Anti Zahra taji wani abu ya soki zuciyarta. Ita kuwa Anti Zabba’u har ta fara murmushin ƙeta sai taji ya cigaba da magana.
“…ni kuma sai na nuna mata idan tana taƙama ta sha nonon hauka to nima na tsotsa tunda duk tushenmu ɗaya.”
Siɗe hannu Anti Zabba’u tayi da sauri ta miƙe tana taro zanin da ta kwance domin taji daɗin yin lodi.
“Ahmad ni ce mahaukaciya?”
“Kin ji na ambaci sunanki?!”
Yayi magana muryarsa a sama. Yau da yarinya ce tayi masa haka da wahala idan bai zane ta ba.
Ita da ƴan matan duka jikinsa sanyi ya yi don ba haka su ka zata ba.
“Rashin kunya za ka yi min don na zo gidanka jinyar mahaifiyarka?”
“Jinya ki ka zo? Wa ya kira ki?” Ya buɗe mata wuta.
Anti Zahra sai da taji babu daɗi ta ɗan taɓa hannunsa “ƙanwar Mami ce fa. Ka sassauta harshenka a kanta.”
“Kin fini saninta ne?” Ta girgiza kai da sauri don bata taɓa ganin fushinsa irin wannan ba. Anti Zabba’un ya sake kallo “cikin wađannan ƴaƴan naki babu wadda za ki je gidan aurenta ki yi wannan abin ba tare da mijinta ya yi muku kallon rashin nutsuwa ba. Kin kuma sani amma shi ne ni ki ka yi min saboda ga karkatacciyar kuka mai daɗin hawa ko?”
Hankalinta sake tashi ya yi don yau tv ta sayar daga lokacin da Salwa ta kirata ta haɗa kuɗin aikin da aka yiwa Habitti.
“Saboda uwarka tana kwance shi ne za ka ci min mutumci?”
“Idan da ƙalau take ba ki isa ki shigo gidan nan ba wallahi. Yau nayi aure? Ƴaƴana biyu fa! amma ko sau ɗaya babu ke babu waɗannan abubuwan…” ya nuna matan da jikinsu ya gama laƙwas sama da ƙasa.
Babbar ce ma Hansatu ta ɗan taɓuka abin kirki ta tashi tsaye “idan ka cigaba da faɗawa mamanmu magana fa ba za mu yarda ba.”
Da wutsiyar ido ya kalleta sai gata tayi tsit ita ma. Ya juya ga Salwa da ko tari bata yi ba tun shigowarsu. Babu shiri tayi ƙasa da kanta ta kama hanyar ɗaki za ta wuce sumsum.
“Idan kin wuce ciki wane mahaukacin ne zai yi min bayanin me yake faruwa da gidana? Ban soke batun zuwan nasu kafin na fita ba?”
“Yaya…”
“Ina raga miki ne kawai saboda ke mace ce, ba don haka ba da tuni na sauke miki abin da yake damun ƙwaƙwalwarki. Shashasha wadda bata san ciwon kanta ba.”
Rasa da me za ta ji tayi. Da ɓacin ran Ahmad wanda bata saba gani ba, ko kuwa da ganin da Innar Taj tayi mata dumu-dumu a wajen dinner akan abin da take shirin yi? Haƙuri ta buɗe baki za ta bashi ya ɗaga hannu ya dakatar da ita.
“Ku haɗu ke da su ku kwana a ɗakin da ki ke. Gobe da safe…” ya ciro dubu goma daga aljihunsa ya ajiye akan centre table yana kallon su Anti Zabba’u “ku ɗauki wannan ku yi kuɗin mota kuma a gyara min gida kafin a fita.” Ita kuma Salwa ya ce “ke kuma zan kira babanki ya turo mai ɗaukarki ki koma gida. Kuma wallahi kin ji na rantse idan ki ka fita daga gidan nan kafin lokacin tafiyarki sai na baki mamaki.”
Yana gama magana ya shige ɗakin Salwan ya ɗauko Mami kamar jinjira don duk ta zuge. Kai tsaye ɗakin Zahra ya wuce da ita kowa yana ganin hawaye shaɓe shaɓe da su ka jiƙa fuskarta. Duk abin da aka yi tana ji. Tafi kowa sanin dole ƙanwarta ta zo da wata manufa. Takaicinta da ko magana bata iyawa sosai yanzu sai dalalar yawu. Da ko zama a gidan Zabba’u bata isa tayi ba. Sai kuma murnar Ahmad ya nunawa duniya ya haifu. Wannan sauƙin kan nasa da take ganin za a iya cutarsa yasa ƙafa ya ture. Ya nuna mata shi ɗin jinin Alh. Hayatu ne babu ƙarya.
Sai da ya kwantar da ita sannan ya ce da Anti Zahra ta ɗauko duk abin buƙatarta da na yaran su koma ɗakinsa.
“Idan tana buƙatar wani abu fa?”
“Zan dinga leƙawa.”
Bai amince ta kwana ba don ya sani akwai cin zali ma idan yace sai ta kula da Mamin da ta ɗora mata karan tsana tun kafin aurensu.
*
Mummunar shaƙa Salwa taji a wuyanta. Gashi bata san ko wace ce ba domin ta bada baya tana shirin cire kaya.
“Sakar min wuya” ta ce da riƙon ya yi ƙarfi ta tabbatar ba na wasa bane.
“Mu za ki yiwa shigo-shigo ba zurfi ki sa a ci mana mutumci?”
Da mamakin muryar ta ce “Anti ni za ki shaƙewa wuya?”
“Haifarki nayi da ba zan shaƙe ki ba?”
Da zafin nama Salwa ta juyo ta doke hannun nata. Ganin ta buɗe baki tana shirin yi mata magana yasa ta ce “tunda baki haife ni ba nima ba zan kasa doke miki hannu ba.”
“Wato na kula shiri ku ka yi da Ahmet ki ka taso mu don ku wulaƙanta mu.” Cewar Habitti tana hura hanci.
Ba su san ran Salwa yafi nasu ɓaci ba saboda disappointments ɗin da ta kwasa. Shi yasa bata ji nauyin ramawa ba.
“Kwaɗayi dai ya kawo ku tunda uwarku na kira ba ku ba…”
Kiffff, taji saukar marin da yafi kama da gwaɓe baki don sai da laɓɓanta su ka amsa. A take kuma idanunta su ka kaɗa da ƙwallar azaba. A makance ta kai hannu domin ramawa akan Hansatu da tayi marin sai hannun ya sauka a kuncin Anti Zabba’u.
Ita kanta Salwa sai da gabanta ya faɗi da taga wa ta mara, sai dai kafin ta gama sanin me za ta yi ƴaƴan gwaggon tasu su ka yi mata rubdugu. Kowa na kai hannu aka lillisa mata jiki. Ihun ma da za ta yi don Ahmad yaji ya kawo mata ɗauki an toshe bakin. Sai da su ka tabbatar tayi laushi su ka barta da ta daina ƙoƙarin kare kanta. Abinka da waɗanda su ka saba da damben gidan haya.
Kukan da take fitarwa a hankali ga jini yana ta zuba daga hancinta ne ya sanya Anti Zabba’u cewa “Yanzu idan Ahmad ya ganta ya zamu yi?”
“Ba ma zai ganta ba. Kafin su tashi zamu kama gabanmu. Banda dare ai da babu abin da zai sa mu kwana” Habitti ta faɗi tana sake dungure mata kai.
***
Shiru motar ba ka jin komai sai hawa da saukar numfashin Hamdi dake baccin gajiya. Musu su ke da Taj yana tsokanarta da cewa yau shi ya haskata tana cewa ita ta haska shi. Can sai ji ya yi ta koma uhm da uhm-uhm idan yayi magana. Yana juyawa yaga ɗaurinta ya karkace saboda yadda ta kwantar da kai a jikin kujera. Mamaki da haushin ta rusa masa plans ɗinsa su ka kama shi.
“Lallai ma yarinyar nan. Bacci ma kike yi a irin wannan lokacin?”
Kafaɗarta ya girgiza a hankali ta ɗan buɗe ido ta kuma rufewa.
“Ko ki tashi ko in wuce gidanmu dake” ya faɗi yana karantar fuskarta.
Ko gezau bata yi ba wanda yasa shi tunanin tabbas bacci take yi. Don da ido biyu take ba za ta yi shiru ba. Ƙwafa ya yi ya kaɗa kai.
“Allah Ya kaimu gobe nima sai na rama. Idan an kawo ki a kwance ina bacci za a ganni akan gadon amarya.”
Nauyin baccin da ya rufeta bai hanata jin abin da ya ce ba. Murmushi tayi a ɓoye ta gyara kwanciyarta. Baccin kwanakin nan da bata samu ne ya yi mata kamun kazar kuku.
Taj cigaba ya yi da tuƙin yana yi yana kallonta. A baccin ma tayi masa kyau. Sai da ya kusa shiga unguwarsu ciwon kan da ya soma ji bayan Salwa ta taɓa shi ya dawo masa da ƙarfi. Abu kamar wasa sai gashi yana gumi. Da ƙyar ya iya ƙarasawa ya tsayar da motar amma bai kashe ba. Sai da ciwon ya lafa ya fita ya zagaya gefenta ya buɗe sannan ya ranƙwafa yana kallonta sosai.
Ƙamshin turarensa da numfashin da yake yi daf da ita ne yasa tsigar jikinta tashi tun kafin ta buɗe ido. Yunƙurawar da za ta yi yayi daidai da sake matsowar Taj. Kawunansu su ka haɗu da ƙarfi.
“Ya Salam” Taj ya dafa kansa da hannu ɗaya, ya kuma ɗora ɗayan a goshinta inda yake tunanin ta nan su ka buge.
“Fasa min kai za ka….” Hamdi ta fara cewa sai ta kula idanunsa sun yi ja da taimakon fitilar waje ta gidansu.
“Kuka kake yi? Kan nawa da zafi ne?” Ta tambaye shi ganin yana runtse ido. Bata san fami ta yiwa ciwon kan nasa ba.
Yadda tayi tambayar sai da yasa shi yin murmushi.
“Abu kamar auduga ina zafi a nan?”
“Awwnnnn” ta ce tana yi masa murmushi da fari da idanu “wai irin abin nan ace tsabar soyayya ka buge ma baka ji zafi ba.”
Taj kasa jira ta gama magana ya yi. Tunda ta rangwaɗa kai ta ce awwnnn ɗinnan ya daina gane komai. Ɗan yatsansa ya ɗora akan bakinta yana zana leɓen wanda ya sanyata shirun dole. Sannan ya zame hannun a hankali ya kawo kansa daidai fuskarta.
” I realy tried to be a gentleman tonight Mrs Happy amma kin hana.”
“Me kuma nayi?” Hamdi tayi tambayar cikin faɗuwar gaba don ta fara tsorata. So take ta ganta a cikin gida kawai.
“Baki yi komai ba sai taɓa zuciyar Tajuddin.”
Wayancewa tayi saboda take takensa da take gani ta ce “Wai ka san ma’anar sunanka kuwa?”
Shi ma da gatse ya bata amsa “Ta yaya zan sani baki faɗa min ba?”
“Taj yana nufin crown, kaga Tajuddin yana nufin…” ta fara cewa ya katseta.
“Ina son ki Hamdiyya Habib Umar”
Sannan ya turo kanta ta hanyar turo kanta gaba da hannunsa da ya sanya a bayan kan. Sauran maganganun da su ke bakunansu basu sami damar shiga kunne ba saboda sabon al’amarin da Taj ya kawo musu. Tun hankalin Hamdi na kan ƙofar gidansu har ta manta a ina take. Sunan Taj ne kaɗai yake tafiya tare da bugun zuciyarta.
Kamar ba za su rabu ba. Taj ne ya yi ta maza ya ɗaga kai yana kallonta da murmushi.
“It seems like zama dani ya fara shafarki fa yarinyar nan. Haka ake so. Wani abin ma sai gobe ko?”
“Kai da ka ce bacci za ka yi kafin mu ci kaz…” kasa ƙarasawa tayi ta kama laɓɓanta ta ɓame da ta ankara da katoɓarar da take shirin yi. Ba za ta so ya fassarata da rashin kunya ba. Ta sunkuyar da kai tana faman matsa hannuwa kamar mai tausar gajiya. Sai dai ta makaro!
Haɓarta Taj ya ɗago a hankali ta kawar da kai gefe ido a rufe. Yana murmushi ya ce,
“Kalle ni nan.” Ya ɗage gira
“Ni fa ba haka nake nufi ba.” Hamdi ta ce kamar tayi kuka don wani kallon kya yi kya gama Taj yake yi mata.
“Me ki ka ji na ce?”
Cikin shagwaɓa Hamdi ta ce “to ka daina yi min irin wannan kallon.”
Amsar da ya tanada don ya cigaba da tsokanarta ya fasa faɗi da yaji kamar an kwaɗa masa guduma a ka. Haka kawai lokaci ɗaya abin ya ta’azzara.
Numfashi ya ja da ƙarfi sannan ya ce “Kira min Abba don Allah.”
“Ƙara ta za ka kai?”
Jikinsa nauyi ya yiwa ƙafafunsa sai gashi ya yo kanta gabaɗaya. Da fari ta zaci wasa ne sai da taji ya sakar mata nauyi yana jan hailala a hankali. Ruɗewa ajin ƙarshe Hamdi tayi. Ta tattaɓa shi tana kiransa bata ji ya amsa ba. Kansa ta ɗago ta sanya hannunta ɗaya ta dafa kumatunsa.
“Don Girman Allah ka tashi. Wannan ba wasa bane wallahi.”
Nan ma shiru sai numfashinsa da yake fita da sauri sauri. Da ƙyar ta yunƙura ta ɗauko jakarta ta zaro waya. Abba ta kira ya fito da gaggawa da yaji yanayin muryarta.
Da farko da ya hango ƙafafun Taj ta ƙofar gaba inda take zaune har zai koma. Kunya ta kama shi sai yaji Hamdi na kiransa da ƙarfi.
“Abba zo ka gani.”
Ko da ya ƙarasa bai san lokacin da ya kai hannu ya ɗago Taj ɗin daga jikinta ba. Yadda duka gaɓɓanta su ke karkarwa haka nasa su ka fara. Da rawar baki Hamdi ta iya faɗa masa iya abin da ta san ya faru.
Ido Taj ɗin ya buɗe a hankali da yaji an ɗaga shi. Hamdi ta buɗe bayan motar Abba ya taimaka masa ya shiga.
“Bari na duba waye yake gida tsakanin yaran Mal. Baƙo da Halliru sai mu kai shi asibiti.”
Da sauri ya yi gaba zuwa gidan maƙotansa da su ka iya tuƙin mota. Tafiyarsa ke da wuya kiran Alhaji ya shigo wayar Taj. Da kansa ya zaro ta daga aljihu ya miƙawa Hamdi. Cike da dauriya da cije baki ya ce mata idan Kamal ne kada ta sanar dashi don baya son tayar masa da hankali. In sun je asibiti sai a faɗa masa.
Screen ɗin ta kalla lokacin kiran farko ya katse ta ɗaga kai domin faɗa masa sunan da ta gani sai kawai ya kwantar da nasa kan a cinyarta ya rufe idon.
“Ɗauki ko ki kashe. Ƙarar tana damuna.”
Ruɗanin ciwon nasa da wata fargaba da ta shigeta saboda tsoron mai kiran ne su ka sa ta kiransa da sunan da taga Taj ya yi saving numbar.
“Alhajina ina wuni?”
Alhaji ya cire wayar daga kunnensa ya duba sunan don ya fara kokonton wa ya kira.
“Alhajinki kuma?”
“Au…lahhh…Alhajinsa nake nufi” Hamdi ta sake gigicewa da ƙarfin amon muryarsa.
“Shi wa?” Ya tambayeta yana yafito Inna da hannu. Wayarta ya karɓa zai kira Taj ɗin. A zatonsa ko ya daina amfani da wannan layin da ya sani.
Aunawa tayi taga idan ta ce masa Taj kai tsaye zai ce bata da kunya. Kuma ita ma dai nauyin sunan take ji.
“Shi ɗin dai” ta ce da ƙaramar murya. Ta ƙara da ɗan bayani a fakaice “uhmm…Hamdiyya ce”
Kai tsaye kuwa ya ganeta ya ce “Hamdiyya ina Taj? Bashi wayar.”
Ɗan taɓa shi tayi ta ce masa Alhaji ne sai ya nuna mata kansa. Rabonsa da ganin sunan mahaifinsa a allon wayarsa ace ya kira shi ba zai iya tunawa ba. Sai dai kuma yau ya kira a yanayin da ba zai iya magana ba.
“Ba ya iya magana saboda ciwon kai.”
Katse ta ya yi kafin ta ƙarasa “bashi da lafiya ko? Me ku ke yi baku kai shi asibiti ba? Ba shi wayar na ce!”
Muryarsa da take tattare da tashin hankali ta fito mata da sauti na umarni kuma cikin faɗa. Sai ta share ta sanar dashi cewa ba zai iya tuƙi ba. Amma Abbanta ya tafi neman wanda zai ja motar a maƙota.
“Shi me yake yi da ba zai tuƙa motar ba? In bashi da ita ya ja ta Taj ɗin mana.”
Da ƙaramar murya ta amsa masa “bai iya tuƙi ba.”
Fargabar ɓata lokaci da halin da Taj zai iya shiga ne su ka saka shi juyawa ga Inna ya yi magana wadda ta shiga raɗau kunnuwan Hamdi “kinga illar daudanci ko? A shekarun Habibu ace bai iya tuƙi ba kamar ba namiji ba.”
Wannan magana ta sanya Hamdi jin nauyi da wani irin zafi a zuciyarta. Idanunta kuwa su ka soma zafi tunda dama kukan a kusa yake a dalilin ciwon Taj. Da hawayen ya zubo sai idon yayi kamar an baɗa barkono saboda tsananin ƙuncin da take ji. Abban nata yake faɗawa waɗannan maganganun? Ta tuna dama ya so a kashe auren. Babu mamaki sai da ya faɗa masa abin da yafi wannan ciwo a gaban idonsa. Kasa daurewa tayi tana ganin kamar in tayi shiru ta yarda mahaifinta bashi da daraja. Sai da ta kalli fuskar Taj taji kunya, amma duk da haka bata ji a ranta za ta fasa faɗa masar abin da yazo bakinta ba.
Numfashinta har canjawa yayi saboda ɓacin rai. Ta buɗe baki za ta yi magana Taj ya tashi zaune ya karɓe wayar. Jiran abin da zai ce tayi sai taga ya miƙawa Abba da ya dawo yana tsaye a baƙin ƙofa wayar.
“Alhaji ne” kawai ya ce ya damƙa masa wayar.
Magana su ka yi akan asibitin da za su haɗu su jira isowar Alhajin.
Ita dai Hamdi ta bi Taj da kallon da har zuciyarsa bai yi masa daɗi ba har Halliru ya tada motar su ka hau titi. Duka wayar yana iya jiyo abin da Alhajin yake faɗi. A daidai lokacin da take shirin bada amsa ya daure ya karɓi wayar saboda a ganinsa idan ta yiwa Alhaji rashin kunyar da ya tabbatar tana gab da yi, to babu makawa gazawar Abba zai cigaba da gani. Har ma ya ce ya kasa yiwa ƴaƴansa tarbiyya.
Hannunta ya riƙe ya ɗan matse ta zare abinta ko kallonsa bata yi. Ya dinga ƙoƙarin su haɗa ido nan ma ta fuske. Ba don an fara tafiya ba kuma ga dare da tabbas sauka za ta yi. Fahimta ɗaya ta yiwa abin da ya yi. Ya shigarwa mahaifinsa kamar kowanne ɗan halak, amma ita ya hanata tsayawa nata uban. Wata zuciyar ma tayi mata nuni da cewa ƙarshenta shi ma bai ɗauke shi cikakken namiji ba. Abin da take ji na baƙinciki yaƙi sauka. Har su ka isa banda sharar ƙwalla babu abin da take yi.
*
Da Bishir yana parking Alhaji bai yi mamakin ganin motar Kamal a wajen ba. Shi kaɗai ma ya lura sai bai faɗawa ƴaƴan nasa ba saboda a tunaninsa dama dole Kamal ya sami labarin halin da ɗan uwansa yake ciki.
Suna fitowa daga mota su Hamdi su ka iso. Bishir da Abba su ka ƙarasa bakin motar su ka taimakawa Taj ya fito.
“Ya kuke kama ni ne kamar wani gurgu. I can walk on my own” ya zame hannayensu daga kafaɗunsa.
Hannun wanda bai taɓa zato bane ya maye gurbin nasu. Inda Alhaji ya janyo shi jikinsa ya kuma tallafe shi ta hanyar riƙe kafadar damansa da hannunsa na hagu. Sai ya zamana Taj na manne da jikin mahaifinsa. Bishir da Abba kallon juna su ka yi cikin mamaki da jindaɗi. Shi kuwa Taj neman ciwon kan ya yi ya rasa. Komai ya tattara ya koma zuciyarsa. Inda ta cika fam da wani irin farinciki mara misaltuwa.
“Mu je ciki a duba ka.” Alhaji ya faɗa yana mai soma takawa a hankali don kada ya wahalar dashi.
Taj ya juya ya haɗa ido da Hamdi zai ce ta taho su shiga sai kawai yaga ta ɗauke kai. Abba da Halliru ta fuskanta.
“Abba ku taho mu tafi kada mu rasa abin hawa.”
“Ki bari mu ji abin da yake damunsa mana.”
Fuskarta a cunkushe ta ɗaga kai daga kallon wayarta ta kuma cewa “Shabiyu ta kusa fa kuma ba abin hawa garemu ba.”
“Hamdi ki kwantar da hankalinki na kira Bawalle (mai adaidaita sahu maƙocinsu) zai zo ya ɗaukemu.”
Abba Habibu ya faɗi yana duban Alhaji da yanayi na ban haƙuri game da kalaman ƴarsa. Kada ace bata damu da mijinta ba.
“Ba sai ka kira kowa ba. Zan kai ku da kaina ma” Cewar Bishir.
“Ka bar shi mun gode. Adaidaitan ma ya ishemu.” Ita ce amsar da Hamdi ta bashi kai tsaye.
Kallon nutsuwa Alhaji ya yi mata sai tayi saurin kawar da kanta gefe amma bai kasa gane tana cikin ɓacin rai ba. Bata so tayi kuka a gaban mutane. Cigaba da tsayuwarta a nan kuwa tana ganin yadda Abbanta yake takatsantsan hatta wajen yin motsi sai taji duk ta tsargu. Auren ya zo mata wuya har tana tunanin makomarsa. A haka ma bata da labarin alaƙarsu da juna kafin a haifeta. Ba a son ranta su ka shiga ciki har likita ya zo ya buƙaci ya shiga office ɗinsa.
Ko da Alhaji ya tayar dashi za su shiga wajen likitan can jerin kujerun baya inda ta zauna ya kalla yana sake nazartarta. A take kuma wata irin kunya ta saukar masa. Hamdiyya bata ce komai ba amma yanayin komai nata a yanzu yana yi masa nuni da cewa anyi mata abin da bata ji daɗi ba. Ba tare da tsawaita tunani ba ya san waye da wannan aikin.
‘Lallai Habibu ya haihu’ ya faɗa a ransa. Yayinda duniya take ƙyamar irinsu har ta kasa karɓar uzurinsu in sun tuba, ƴarsa ta ture girma da yawan arziƙin gidan aurenta tana mai nuna ba za ta lamuncewa taka darajarsa ba. Abin da bai taɓa zato bane yaji a ransa. Hamdiyya ƴar Habibu ta burge shi har wani sashe na zuciyarsa yana kamanta wannan hali nata da abin da yake tsammata daga jininsa.
MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
