Search
You have no alerts.

    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    Lallai Alh. Mukhtar ɗinnan ya gamu da sharrin Mami shi ne abin da Alhaji ya fara rayawa a ransa bayan sun gama waya. Yadda ya dinga koro bayani akan irin son da ƴarsa take yiwa Taj da fatan amincewar Alhajin don ayi aurensu kai ka san kan ba ƙalau ba. Shi dai yana son ƴaƴansa, amma fa yana ganin babu ƴar da ta isa ta saka shi zubar da mutumci haka a gaban tsohon mijin matarsa. Irin waɗannan abubuwan ya fara gani da burinta na fin kowacce mace matsayi ta kowacce hanya yasa shi sakinta. Yana da labarin yadda matan Alh. Mukhtar biyu su ka fita bayan an aurota. Kuma duk wadda ya ƙaro bata jimawa za ta yi waje ita ma.

    Zama ya gyara da ya tuna yadda ya ce masa ya amince kai tsaye. Fakewa zai yi da guzuma ya harbi karsana. Ya san a taurin kai irin na Taj akan ya auri Salwa ya faranta masa gara ya saki Hamdi. Ana yin sakin da kansa zai ce masa ya janye batun auren. Duk da a iya saninsa Salwa yarinya ce mai saukin hali. Babu mamaki sirrin zuciyarta ta sanar da Mamin ita kuma tayi amfani da raunin ƴar ta ɗorata akan hanya mara ɓullewa irin wannan. Tsigar jikinsa har wanu tashi tayi da ya yi addu’ar Allah Ya tsare shi surukuta da Mami da lusarin mijinta kamar yadda ya laƙaba masa suna.

    Bai ga alamun Habibu Simagade zai iya wani kataɓus wurin raba yaran ba. Yanzu da ya sami dama shine zai yi amfani da ita. Ɗansa yake muradi ya dawo gida. Amma ba tare da iri ko jinin ɗan daudu a tare dashi ba. Saboda rashin son ganin Hamdi ranar da aka ce za ta zo gidan zamansa ya yi a kasuwa har ƙarfe tara. Shi ba abin ya ce kada ta zo ba matan gidan su soma tijara. Ya fahimci yanzu kamar ma jira suke ya ce kule su ce masa cass.

    Ahmad ya nema da yazo gida yana son ganinsa da daddare. Bayan ya taso daga office kai tsaye can ya wuce. Alhaji ya keɓe dashi yana tambayarsa alaƙar Taj da Salwa tunda duka a gidansa su ke.

    Tsoro ne ya bayyana a fuskar Ahmad.
    “Alhaji wata maganar ka ji?”

    “Ya zan yi maka tambaya ka amsa min da tambaya?”

    Da sauri ya bashi haƙuri tare da amsa tambayar da ya yi masa.
    “Babu komai a tsakaninsu amma kuma ba faɗa su ke yi ba. Shi Taj ma bai fiye zaman gida ba ai saboda kullum su ke buɗewa.”

    “Babanta, Alh. Mukhtar sunansa ko?” Alhaji ya faɗi da irin rashin damuwar nan.

    Ahmad baya jindaɗin yadda ake magana akan Salwa yanzu. Rannan ƴan uwansa ne su ka yi ana ta dariya. Yau kuma Alhaji ke tambayar sunan babanta kamar wani abin gudu.

    “Sunansa kenan.”

    “Ya kirani yana roƙon na amince Taj ya aureta.”

    Maganar ta dake shi sosai “Roƙo kuma Alhaji?”

    “Roƙo mana. Ya tabbatar min ita take son sa. Kaima yanzu ka ce babu komai tsakaninsu. To me zai sa ita babar taku ta amince harma mijinta ya kirani?”

    “Zan yi mata magana Alhaji.” Ya girgiza kai “Gobe in sha Allah zan mayar da ita Bauchin. Idan ma mijin ne su sama mata a can.” Tashi ya yi zai tafi. Alhaji ya ce ya dawo.

    “Babu daɗi mutum ya nemeka akan wata alfarma ka nuna masa baka so. Saboda haka na faɗa masa na amince. Saƙon da nake son baka shi ne ka sanar dasu cewa bana so komai ya wuce wata ɗaya indai da gaske su ke.”

    Yana magana ne yana kallon yanayin Ahmad. A ransa kuma yana addu’ar Allah Yasa ɗan nasa ya yafe masa. Da gangan yake maganar a haka saboda yana so idan Ahmad ya tashi kai saƙon ya nuna musu shi fa bai ɗauki maganar da mahimmanci ba. Sannan baya ɗokin haɗa zuri’a da ƴarsu. Ya sami wannan canjin ra’ayin ne bayan wani nazari da ya yi. A matsayinsa na uba sai hankalinsa bai kwanta da ya yi amfani da ƴar wani domin biyan buƙatarsa ba. Idan komai ya tafi yadda yake so ya dawo ya ce da Taj kada ya auri Salwa me kenan ya yi? Shi mai ƴaƴa da jikoki mata ya dace ya tozarta ƴar wani haka? Gashi saboda sanin halin babarta ya tabbatar idan ya yi sake ta auri Taj sai sun mayar masa ɗa abin wasan yara.

    Ba a raba hanta da jini. Hakan da yake yi ya san duka Ahmad zai faɗawa Mami. Kuma tunda yaro ne hankali zai yi ƙoƙarin nusar da ita illar bari a yiwa ƴarta irin wannan auren. Da bakinsa ne dai akwai nauyi bayan ya aminci ɗazu ya dawo ya ce ya fasa. Abin zai zama cin fuska sosai. Fatansa yanzu dai Allah Yasa iyayen suna da hankalin gane manufarsa.

    Da wannan damuwar Anti Zahra ta tarbi Ahmad. Juyin duniya tayi ta tambayarsa amma yaƙi faɗa mata abin da yake faruwa. Abinci ma kasa ci ya yi saboda baƙincikin yadda Salwa take zubar da darajarta ta ƴa mace. Gashi yanzu ta sa iyayenta biye mata. Don ma su Hajiya akwai kawaici. Babu mai zancen Mami a gidan ko a aibata ta. Amma yanzu da sun ji maganar auren nan babu abin da zai hanasu fitowa ƙiriƙiri su ƙi.

    Salwan ya kira tana ɗaki tana chatting da Ummi. Cikin sigar wayon da Alh. Usaini ya koya mata take ta jan Salwa tana dukan cikinta. Rai bai so ba ta katse hirar ta fita wajen Ahmad. Ɗakinsa ya kirata ba ma falo ba.

    “Kun yi maganar Taj ne da Mami?”

    “Eh” ta amsa masa babu wannan girmamawar da ya santa da ita.

    Yadda su ka yi da Alhaji ya faɗa mata. Babu kunya ta kama murmushi. Baki har kunne.

    “Da ni ne ke Salwa da na haƙura da mutumin da bai damu dani ba. Wane irin aure za ku yi yanzu? Shi baya so kuma na tabbata da wahala ƴan gidanmu su so.”

    “Ai ba da su zan zauna ba.” Ta ce da tsiwar da bai santa da ita ba. Wai duk so ne ya canjata ko kuwa dama can halinta ne da bai sani ba?

    “Shikenan. Zan kira Mami na faɗa mata. Duk abin da ya biyo baya kada ki ce ban yi warning ɗin ki ba.”

    Da ƙunƙuni ta tashi tana cewa “alkhairi zan gani.”

    Daina bashi mamaki tayi. Ya ce mata ta haɗa kayanta gobe za ta koma gida. Ƙarfe tara za su kama hanya. Tana fita ya kira Mami ta rangaɗa uwar shewa. Mantawa tayi da wa take magana ta ce,

    “In ya san wata ai bai san wata ba. Har ni zai wulaƙantawa ƴa saboda yaci sa’a tana son shi?”

    “Mami ana dole ne? Aurensa duka-duka sati ne fa da ƴan kwanaki. Ni dai da za ku ɗauki shawarata da kin ce mata ta haƙura.”

    Da faɗa Mami ta ce “to mai halin ubansa. Wanda baya kishina da na ƴaƴana. Idan ta haƙura kai za ka aureta?”

    “Allah Ya baki haƙuri.” Kawai ya ce.

    “Amin. Kuma ka tanadi abin da za ka bani don a wata guda ko babanta ba zai iya haɗa abin da ya dace ba.”

    Allah Ya sani bashi da irin kuɗin da ya san idan ya bata ba za ta raina ba a yanzu. Sabon wata ne kuma farkon term an koma makaranta. Ɗa ɗaya amma ɗawainiyar karatu sai dai kawai a dinga yiwa iyaye addu’a. A bisa tsarin gidansu kuma tunda su ka soma kawo ƙarfi sun ɗaukewa Alhaji abubuwa da dama. Ba kuma don bashi da kuɗin ba. Ko a danginsa babu kamar shi har yanzu. Suna yi ne don neman albarka. Kayan abinci, kayan buƙata na gida irin su sabulu da kuɗin kashewa ga iyayensu. Duk masu aiki da masu kasuwanci suna contributing. A matsayinsa na babban namiji duk da cikin matan akwai waɗanda samunsu yafi nashi, amma yana ƙoƙarin ganin ya yi bajinta. A haka kuma yake bawa Mamin dubu talatin duk wata.

    “Kai, Ahmad. Baka ce komai ba.”

    Ya ma manta waya yake.
    “Allah Ya hore. Sai da safe.”

    Ko minti goma basu yi da gama wayar ba ta sake kira. Ya san zancen ba zai wuce na kada ya dawo da Salwa ba. Shi yasa yaƙi ɗauka. Zai kaita gida gobe in sha Allahu.

    Ƙarfe bakwai da rabi Anti Zahra ta same shi a ɗaki wai Salwa ta fita.

    “Bangane ba. Ina ta tafi?”

    “Ina ta tambayarta tana kuka. Da alama bata son tafiyar. Da ka ƙyaleta.”

    A harzuƙe ya tashi yana ta faɗa. Sai a lokacin Anti Zahra taji me yake faruwa. Ta ma kasa comprehending wannan al’amari.

    “Don Allah kayi shiru kada Taj ya ji. Kwanansa biyu yana fama da zazzaɓin nan mai zafi. Sannan ko babu komai ka haɗa uwa da ita. Mutumcinta abin karewa ne a wajenka komai rashin daɗin da abin ya yi maka.”

    “Gidan wa zata da safiyar nan? Idan tana tunanin zan bita ne wallahi tayi kuskure.”

    “Naji. Ka san ba za ta wuce gidan ƙanwar babanta ba ta Sheka. In ba nan ba kuma ƙila ta wuce Bauchin.”

    “Ita ta sani.”

    Sai dare ya ɗauki wayar Mami. Ta ƙare masa tanadi kuwa. Shi kuma ya tsaya akan bakansa na cewa indai Salwa ta dawo gidansa to Bauchi zai maidota. Ba zai zauna da mara kunyar da bai isa ya faɗa mata taji ba. Mami da taga yaƙi tanƙwaruwa ta haƙura.

    “Shegen yaro mai halin ubansa.”

    ***

    A kwana biyun nan kullum Hamdi sai ta kira Taj. Zazzaɓi ne irin wanda ya kan zo gama gari mai shiga gida gida. Ita kanta tana mamakin yadda ta damu da ciwon nasa da kuma rashin ganinsa. Da Zee ta tsegumtawa Sajida halin da take ciki haɗuwa su ka yi suna tsokanarta.

    Zee ta ce “Salman Khan ya sallame zuciyar Hamdi.”

    Ita kuma Sajida tana dariya ta tuna mata tsohon ƙudurinta.

    “Ta dai gama cika bakin bata son namiji mai girki. Yanzu gashi nan mai gidan abinci ya hanata sukuni.”

    Da yake a wayar Zee ake ta bidirin, gajiya tayi da kare kanta ta tsuke bakin nan.
    “Aljannar mace dai tana ƙarƙashin ƙafar mijinta. In kuma kuna baƙincikin kada na samu ne sai in ji.”

    Sajida da Zee me za su yi kuwa banda dariya. Ashe rana irin wannan za ta zo musu a kurkusa haka basu sani ba.

    Ƙyalesu tayi ta koma kitchen wajen girkinta. Tana aiki tana tunaninsa. Yau ce rana ta uku tun zuwan da ya yi ta kira masa Kamal. Wayar ma idan sun yi ba wani jimawa su ke ba. Gaisuwa ce da jin yaya jikin nasa. Ɗan wasan nan duk ya daina.

    “Ke!”

    A firgice ta kalli Yaya. Bata san tun yaushe take tsaye tana yi mata magana ba.

    “Jikin nasa ne har yanzu?”

    Wayancewa tayi kamar bata gane ba “wa?”

    “Garinku in kin san shi. Wa ma za ki ce min?”

    Ƙasa ta kalla a kunyace. Fuskarta babu walwala. Yaya ta fahimci har yanzu a kwance yake.

    “Jiya dama Abbanku yake zancen zuwa a dubo shi. Zan sake yi masa magana yanzu in sha Allah a waya.”

    Fuska mai tona asirin zuciya. A take fuskar Hamdi ta washe. Yaya ta kama baki tana salati.

    “Anya dama ba shirya maganar auren nan ku ka yi da Taj ba? Cikin ƴan kwanaki kin zurma haka?”

    “Ni ban zurma ba Yaya”

    “Tsiwar ma ai naga ta ragu. Allah Ya yiwa aure albarka. Amma ki rage murna don ba dake zai je ba. Halifa zai ɗauka.”

    “Kai Yaya, ni yaushe na ce zan je?”

    Dariya tayi “nima wasa nake miki. Ai na san ko tayi aka yi miki za ki ce a’a.”

    Bata ƙara magana ba tunda ta gane Yayan ma tsokanarta take yi. To ita har me tayi da ake mata wannan fassara?

    *

    A ɓangaren Taj abin da ya zata zazzaɓin gajiya ne ashe combo ne na typhoid da maleriya. Ciwon da ya manta rabonsa da yi. Shi ne ya yi masa rubdugu irin wannan. Kuma da yake zafi ake yi sai ya haɗu goma da ashirin. Dalilin zazzaɓin ne ma su Mama su ka tsahirta da sanya lokacin biki. Shirye shirye dai sai abin da ba a rasa ba. So su ke amarya ta shiga ɗakinta nan da sati uku ko wata guda. A nasu shirin idan ta tare da wuri za su ɓata shirin Alhaji. A ganinsu dama wata ukun nan da ya bayar ya yi ne saboda sanin cewa da wahala ace Abba Habibu yana da abin da zai yi bikin wata ƴar nan kusa.

    Sosai Ahmad yake bashi kulawa. Musamman bayan tafiyar Salwa. Fushin da ya fara akan yadda aka yi mata dole ya kau da ya gaskata ita ce ta janyowa kanta.

    Kamal ne dai tun ranar da ya kai shi asibiti ya ƙirƙiri tafiya washegari. Ciwo ke neman kayar dashi kuma baya son kowa ya sani. Haka ya tattara ya tafi asibiti. Mubina ta kwantar dashi. Magunguna tana iya bakin ƙoƙarinta. Bata so su fara dialysis domin ana kaiwa wannan matakin, transplant (dashe) shi ne best option ɗin da zai rage.

    Ranar da ta kwantar dashi bayan ya zama stable ta kira Yaya Kubra. Dama kullum jiran wayarta take yi. Tana gani kuwa ta bar ayyukan gabanta ta tafi asibitin.

    “Akwai shirin da ki ka fara yi ne Doctor saboda in san next course of action?”

    Yaya Kubra ta gyaɗa kai “na fara bincike ta bayan gida. Wata questionnaire na ƙirƙira a google form nace ta research ɗina ce. Ita na tura a groups na family ake ta cike min. Harda families ɗin duka matan gidan mu. Kuma da yake da suna so far na sami mutum huɗu that are rhesus negative.”

    Idanun Mubina harda ƙwalla ta ce “Masha Allah. Amma dangin kusa ne?”

    “Surprisingly daga dangin Hajiya na sami uku. Ɗaya ne a dangin Umma. Ai jinsi baya hana bayarwa ko? Duka huɗun mata ne.”

    Mubina ta ce gender baya hanawa.
    “Amma fa Kamal A negative ne. Indai ba irin nasa ba kinsan sai dai O ko AB negative ko?”

    “Dukkaninsu O negative ne. Yanzu su Alhaji ya rage su sani sai a tuntuɓe su.”

    “Muje ki ganshi. Akwai Nephrologist da na fara magana dashi daga Port Harcourt. Idan an sami nasarar samun mai bayarwa sai naji yaushe zai iya zuwa.”

    Godiya Yaya Kubra tayi mata har ta rasa kalmar faɗa. Mubina ta shige gaba zuwa ɗakin da Kamal yake. A hanya tayi ta nanata mata don Allah ta daure zuciyarta idan ta ganshi. Wannan yasa zuciyar Yaya Kubra ga tsinke tun kafin su shiga.

    Mubina ce ta fara shiga da sallama. Yana kwance gaɓoɓi da fuskarsa sun kumburo sosai. Shi kaɗai ya san irin azabar ciwon da yake ji. Amsa sallamar ya fara da muryarsa can ƙasa kawai sai ya yi tozali da Yaya Kubra. Ya yunƙura ya tashi zaune kafin ta ƙaraso.

    Hannu ta ɗora akan bakinta don kada tayi kuka mai haɗe da ihu da taga yadda ya koma.

    “Kamal?” Ta kira shi da rawar murya.

    Ya miƙa mata hannu, kwarmin idanunsa yana ziraro hawaye ta riƙe. A gefen gadon ta zauna su ka rungume juna. For the first time tun bayan ciwon nan ya same shi ya fashe da kuka mai ban tausayi. Duk wani ciwo, ƙunci da damuwa da yake ɓoyewa ya bari ya nuna kansa a wannan lokacin. Shi ɗan dangi yana ta fama da damuwa shi kaɗai. Abin da gidansu basu saba ba.

    Yaya Kubra tana kuka tana shafa bayansa da lallashi. Mubina kuwa ficewa tayi don bata son karyar masa da zuciya fiye da halin da yake ciki. Mara lafiya baya son ganin rauni a tattare da likitansa.

    Tsahon minti goma zuwa shabiyar kafin yaji sanyi a ransa ya daina kukan.

    “Kiranki tayi ko?” Ya tambayeta yana nufin Mubina.

    Faɗa ta soma yi masa “Me yasa ka zaɓi wannan rayuwar Kamal? Bamu da mahimmanci a wurinka? Ko kana ganin ba za mu damu da lalurarka ba?”

    “Irin wannan kallon kamar kina yi min sallama shi ne bana son gani. Wannan kukan zamu dinga yi kullum har lokaci…”

    “In sha Allahu za a dace. Ina nan ina bincike.”

    “Bata faɗa miki cewa ko dialysis ba zai iya riƙeni na tsayin lokaci ba?”

    “Na sani Kamal. You need a new kidney. And we’ll find one in sha Allah” ta share masa hawaye da hannunta.

    Alƙawarin riƙe masa sirri ya roƙeta har zuwa lokacin da za ayi bikin Taj. Sannan ƙanwarsu mai shirin haihuwa ko yau ko gobe ita ma ta sauke.

    “Me yasa? Wallahi ka san ba za ka burge Taj ba. Infact ni ba zan so ganin ranar da zai sani ba. Za ku yi faɗa Kamal. Za ku yi faɗa sosai. Ko jiya da naje duba shi sai da yayi ta zancen wai ina duba maka magungunan allergy kuwa.”

    Jingina ya yi da pillow don ya gaji da zaman. Ya yi ajiyar zuciya.

    “Na sani. Amma Happy zai tsayar da duka uzurin rayuwarsa ne. Zuwa yanzu kin san mutum ne mai sanya abu a rai. Amma kina gani saboda mu ya mayar da komai ba komai ba tsakaninsa da Alhaji. Kuma hakan fa ba ƙaramin ciwo yake yi masa ba.”

    “Tsakanin uba da ɗa ne wannan. Ina maganar Happy da Happiness. Sai ka shiryawa duk abin da zai biyo baya.”

    “In ya ganni a haka kina tunanin zai iya yi min mita? Kuka kawai za mu zauna mu sha abinmu.”

    Yadda yake maganar kai ka san akwai tsantsar tawakkali. Yaya Kubra a nan ta wuni har tara na dare sannan ta tafi. Ta amince za ta yi shiru amma ba don Kamal ba. So take ta samu cikin dangin wanda idan ta bijiro da buƙatar ba zai ƙi ba. Maganar neman donor ta hanyar gwamnati ba zai yiwu ba. Waɗanda su ke kan list sun yi yawa sosai.

    Tsakanin Kamal da Taj a waya sai ta whtsapp. Kamal ya cire simcard da sunan baya ƙasar. Wai ya tafi China odar takalma. Taj harda mitar me yasa bai faɗa masa shirin tafiyar ba. Ya ce wanda ya bawa sautu ne ya sami matsala. Gashi kuma komai ya kammala. Ana buƙatar mai kaya. Abinka da rashin sabo da yi. Taj bai kawo komai ba ya yarda. Iyaka dai in suna waya ya dinga kiran wash wash kenan don kawai yaji Kamal yana sannu kamar ya ari baki. Bai san ciwon Kamal ɗin ya ninka nashi ba.

    ***

    Kamar yadda Anti Zahra tayi hasashe, Salwa gidan ƙanwar babanta ta tafi. Gidan da tun farkon karatunta baban ya so taje amma saboda Mami ta raina arziƙinsu ta rufe ido ta ce bata san zance ba. Wannan tafiya da tayi sai ta sami lasisin fita yadda take so tana haɗuwa da Ummi. Gwaggonta kuma bata iya yi mata magana saboda tsoron jarabar Mami.

    Bayan bugun cikin da Ummi tayi mata sai ta nuna mata cewa tana jajanta mata rashin samun soyayyar Taj. Ta kuma yi mata alƙawarin za ta taimaka mata ta sami biyan buƙata indai tana so.

    “Mamina ma ta gama komai har an fara maganar aurenmu” ta faɗawa Ummi da farinciki.

    Taɓe baki Ummin tayi “in an ɗaura muku auren kina tunanin kin yi nasara ko me? Mutumin da baya sonki kuma igiyar auren tana hannunsa.”

    A tsorace Salwa ta ce “kuma fa haka ne. Amma ba sona bane baya yi. Haɗuwarsa da matar da aka aura masa ƴar ɗan daudu duk shi ya lalata komai. Da muna waya normal.”

    A zuci Ummi tayi tsaki. Wannan Salwan irin matan nan ne da sakarci ya rinjayi tunaninsu. Gashi dai ta san cewa ta girmeta amma irin shirmen da take yi da sunan soyayya ita ko da wasa ba za ta yi ba.

    “Ni naga sharrin ƴar ɗan daudu. Akanta aka koreni daga makaranta sannan aka fasa bikina. Gidanmu kowa ya tsaneni akansu. Wallahi da zan haɗu da Hamdiyya Habib sai na rama abin da tayi min ko yaya ne.”

    Idanu Salwa ta zaro tana kallonta “Hamdiyya? Ai kuwa ita ma sunanta kenan. Babanta yana aiki a Happy Taj.”

    “Ni ban san a ina yake ba. Amma dai shi ma sana’ar girki yake yi. Kin ganta. A yadda suke matsiyata bana jin ko iskar da mai Happy Taj yake shaƙa ita ma za ta shaƙa wataran.”

    Hoton Hamdi ta nuna mata wanda ta samu ta ɗauka daga wayar Siyama na ranar aurensu. Salwa ta dinga sallallami gami da rantsuwar ita ce. Ita ma Ummi ta nuna nata mamakin ƙwarai.

    “Indai Hamdi ce nayi miki alƙawarin zan bada nawa taimakon na raba su da masoyinki.”

    “Nagode. Ni kam alkhairi ne ashe ya kai ni Glory mall rannan.”

    Ummi sai dariyar yaƙe kawai take yi. Ita kanta duk fitinarta abin da Alh. Usaini ya tanadarwa Taj ya yi mata hatsabibanci da yawa. Ta riga ta nuna masa tana tare dashi bata da hanyar guduwa. Haka kawai take tsoron mutane irinsa waɗanda za su iya yin komai domin biyan buƙatarsu. Rashin kunyarta bata kai nan ba. Domin kuwa duk iya shegenta akwai abubuwan da take tsoron yi don kada su koma kunnen iyayenta. Tunda Allah Ya kawo Salwa sai ta bashi shawarar amfani da ita don ya cimma burinsa.

    ***
    Jinyar sati guda Taj ya yi kafin ya farfaɗo sosai. Har ya faɗa kuwa. Abba yaje duba shi har gidan Ahmad. Kuma ya sami tarba ta mutumci daga gare shi. Wannan ya sake daɗaɗa ransa akan halin ƴaƴan Yaya Hayatu. Da zai tafi ne Taj ya yi masa maganar Hamdi.

    “Abba don Allah ina neman alfarma a gareka.”

    “Indai zan iya in sha Allahu zan maka.”

    “Maganar rabani da Hamdi. Don Allah ka cire komai a ranka ka bimu da addu’a.”

    “Innalillahi…” Abba ya riƙe kai “faɗa maka tayi? Ban san Hamdi da surutu ba wallahi.”

    Taj ya yi murmushi “ba ita ta faɗa min ba.” Ya tuna maganar da Salwa tayi ya ce “Yaya Ahmad ne ya faɗa. Amma ya ce kada na damu in sha Allah su Inna ba za su bari ba.”

    “Lamari na iyaye…”

    “Allah bai bawa iyayenmu damar kashe mana aure ba. Musamman idan raba auren cutarwa ne ba hanyar samun maslaha ba.”

    “Ina jiye maka yawan saɓanin da kuke samu dashi. Hakan ba zai haifar da alkairi ba.”

    “Abba ina ƙoƙarin tsayuwa akan iyakar addini kan abin da ya shafi Alhaji. Duka abubuwan da yake fushu dani a kai shi yake nuna amincewarsa sannan ya zargeni da rashin kyautawa.”

    Shi dai Abba gani ya yi zai shiga tsaka mai wuya. Ya yi ta nunawa Taj illar dake tattare da zama cikin fushin iyaye.

    “Don Allah ka nemi sulhu dashi kafin lokaci ya ƙure.”

    Muryar Taj a raunane ya ce “na jima ina wannan amma yaƙi bani dama. Zan cigaba da ƙoƙari amma Abba kada ka kuma sako aurena a ciki don Allah.”

    Tausayi ya bawa Abban “na daina. Allah Ya kiyaye mana ɓacin rana.”

    “A sunnar Annabi SAW? Inaaa, Abba ai sai dai lada.”

    Nauyi Abba ya fara ji tun kafin Taj ɗin ya je inda bai dace ba ya ce “naga ka fara jin sauƙi. Bari na tashi.”

    Taj ya dinga dariya kamar ba shi ne yake kwance kafin zuwan Abban ba.

    ***

    Inna tana falonta ana yi mata kitso aka yi mata waya. Baƙuwar lamba ta gani. Ta ɗauka da sallama su ka gaisa da matar da ta kira.

    “Na san ba ki gane ni ba tunda bamu zauna tare ba. Mahaifiyar Ahmad ce. Ahmad babban ɗa namiji wajen Alh. Hayatu nake nufi.”

    Murmushi Inna tayi. Wannan ƙalau take kuwa? A take ta cire wayar daga kunnenta ta karanto Ayatul Kursiyyu. Ɗabi’arta ce haka. Duk abin da bata gamsu dashi ba koda bata aka yi sai ta tofe shi da Ayatul Kursiyyu kafin tayi amfani dashi. Yadda Mami ta gabatar da kanta sam bai yi mata ba.

    Sai da ta gama sannan su ka gaisa da ita.

    “Dama naji shiru ne ina ta sa rai da wayarki amma baki kira ba. Nace bari ni na neme ki naji me ake ciki.”

    “Wace magana kenan?” Tashi tayi daga wurin kitson ta koma ɗaki.

    “Auren Taj da Salwa. Alhaji ya ce baya son a wuce wata guda. Naga har an cinye sati.”

    Azkar ɗin tunkarar shugaban da kake tsoron cutarwa daga gare shi Inna ta karanto wannan karon kafin tayi magana.

    (Allahummak finihin bima shi’ta)

    “Wane Taj ɗin wai? Nawa dai sati biyu kenan da aurensa. Bani kuma da labarin zai ƙara wani.”

    Mami tayi kwafa a hankali tana raya duk za su zo hannu ne. Da ta san haka za ta yi mata tun farko ma da ta karɓo laya.

    “To ki tambayi maigidan naki. Sai mu yi magana daga nan.”

    Inna ce ta fara kashe wayar. Ta dinga karanto addu’o’i. Me yasa duk wata rigimar gidan akan Taj take kunno kai? Istigfari tayi da sauri sannan ta fita ta tafi ɓangaren Alhajin. Dama yana gida. Girkin Umma ne. Inna tayi sallama ta shiga falon bayan Umma ta amsa ta iske shi yana cin abinci.

    “Alhaji me nake ji daga bakin tsohuwar matarka?”

    Karo na biyu kenan da Inna tayi masa magana babu kyautata kafazi. Yana namiji sai da yaji wanibabu a ransa. Maganar Hajiya na neman tabbata da ta ce masa kada ya ƙure haƙurin Abu don mai haƙuri bai iya fushi ba.

    “Wani abin ne ya faru?” Ya tambayeta kamar bai sani ba.

    “Ka fini sani Alhaji. To amma ina so ka sani ka gama yi min hawan karkatacciyar kuka. Wannan juya min yaro da kake yi ya isa haka.”

    “Haba Inna. In ranki ya ɓaci kada ki bari hankalinki ya gushe mana. Da mijinki fa kike magana.” Umma ta ankarar da ita don muryarta tashi take sosai.

    “Me ya rage min? Yau ko agola ne Tajuddin ai iyakar abin da mijin uwa da baya sonsa zai yi masa kenan. Wai ni matar nan za ta kira ta ce ya maganar auren Taj da Salwa?”

    “Me?” Umma ma ta ɗaga murya ba tare da tunani ba.

    “Ah to, kema kya faɗa. Wai da Alhaji su ka yi magana.”

    Ya fa manta da maganar nan. Duk a zatonsa idan Ahmad ya faɗa mata yadda su ka yi za taji haushi ta ce basa so. Daga ranar da su ka yi maganar ko tunawa bai sake yi ba saboda rashin mahimmancin zancen a wajensa.

    Umma ta dube shi “Alhaji wai haka?”

    “Eh. Mun yi magana da mijinta ya bawa Taj Salwa. Sharaɗina kenan idan ba zai saki ƴar gidan Habibu ba. In ba haka ba kuwa…”

    “Kana son ya saketa kafin auren ya wuce wata uku ko? Ahmad, ɗan halak ya faɗa mana” Inna ta ƙarashe masa.

    “Tunda kun sani sai ku sa ya zaɓi ɗaya. Na gama magana.”

    “Ahaf. Ai babban kuskurenka da ka bari aka yi auren nan Alhaji. Shi ne mai wuyar. Ko yanzu ba abin mamaki bane ace Hamdi tana da juna biyu.”

    Ba Alhaji da ya kusa ƙwarewa da ruwan da yake sha ba, Inna ma zaro idanu tayi.

    “Kai Umma?”

    “Auren yanzu da ake yiwa yara bayan duk sun ƙosa. Ko mu nan nawa ne ƴaƴanmu su ka haihu wata tara ko goma da aure? Indai an bada sadaki ai magana ta ƙare. Don ma ba lafiya gare shi ba.”

    “Ai kuwa sati mai zuwa za ta tare.” Inna ta faɗi sannan ta dubi Alhaji “ka faɗawa tsohuwar matarka ta nemarwa ƴarta miji tun wuri.”

    Inna na fita Alhaji ya tsare Umma da tambaya. Shi fa daina gane komai ya yi daga inda ta ce bashi da lafiya.

    “Ciwo ne da Taj ɗin?”

    “Typhoid yake da maleriya. Satinsa guda ko aiki baya zuwa.”

    Ransa a ɓace ya ce “Kuma shi ne aka rasa wanda zai faɗa min?”

    “Taj ne fa. Ka damu da ciwonsa ne dama?”

    “Me kike nufi?”

    “Wai abin da ido ya gani baki ke faɗa.”

    Ta jima da fita daga ɗakin ta bar Alhaji da tunani. Me yasa sai akan Taj iyalinsa su ke yi masa irin wannan? Sai kuma maganar Salwa. Bai san har yanzu Mami bata da cikakken hankali ba. Ai da maimakon hannunka mai sanda sai ya fito musu a mutum kawai.

    Yana wannan lissafin tuni Mami ta garzaya wajen toshe ɓarakar da take hangowa. Magana ta yiwa Alh. Mukhtar. Ya kuma aiwatar duk da baya so.

    Alhaji sai waya kawai yaji. Ganin sunan mai kiran ya hanzarta ɗauka domin ya kashe maganar Salwa. Sai dai kafin ya ce komai Alh. Mukhtar ya yi masa dabaibayi.

    “Akwai wasu ƴan uwana mazauna Kano da muka yi magana mutum biyar. Ɗaya ma ƙanin mahaifina ne uwa ɗaya uba ɗaya.”

    “Wani abu ne ya same su?” Alhaji ya ƙosa yaji ƙarshen zancen ko ya sami damar yin nasa.

    “Lafiya ƙalau. Dama don a sama muku sauƙi ba sai kun taho har nan ba. Shi Baffan namu na sanar dashi za ku zo neman aure da biyan sadaki. In kun saka rana sai ka sanar dani. Na tura musu lambarka ma dai.”

    Alh. Hayatu mai baki sai yaji yawun bakinsa ya ƙafe. Ta ina zai fara cewa ya fasa? Abin da kamar wuya. Girmansa zubewa zai yi. Idan matansa su ka san halin da yake ciki ya tabbata dariya za su yi masa.

    “Idan na saka ranar zan sanar da kai.”

    “Yauwa to nagode.” Ya đan numfasa “don Allah kada a ja lokacin. Nima na gama shiri.”

    “To”

    Alhaji ya gyaɗa kai. Kuma har zuciyarsa sai yaji yana tausayin Alh. Mukhtar ɗin. Shi da zai iya dafa littafi mai tsarki ya yi rantsuwar matansa basa biye biyen tsibbu ashe a aljanna yake. Gudun faɗuwar girma ya janyo ya kasa kyautata musu akan abu guda da su ke buƙata daga gare shi.

    *

    Inna na dawowa daga ɓangarensa taci karo da wasu rantsattsun akwatuna manya manya guda huɗu a tsakiyar falo. Ƴan gidan an haɗu ana ta murnar yaushe gamo da Amma. Rabonta da shigowa gidan yayan nata an jima.

    “Takwara oyoyo” Umma ta ce daga bayan Inna da ta kasa magana.

    “Yauwa Takwara” Amma ta ce, ita da su Mama su ka bi Inna da kallo.

    Murmushin dole tayi musu gami da yiwa Amma sannu da zuwa sai ta shige ɗaki. Ta manta da mai kitson sai da ta ganta zaune tana jiranta. Kuɗin kitson ta bata sannan ta ce ta tafi za ta nemeta daga baya. Matar bata matsa ba don ta lura Inna bata cikin nutsuwa. Uwar ɗaka ma ta shige ta rufo ƙofa. Wayarta ta ɗauka ta kira babban wanta. Tana jin muryarsa ta fashe da kuka.

    “Me yake son ya mayar da rayuwar yaron nan? Shi ba fasiƙi ba, ba ɓarawo ko ɗan fashi ba. Amma ace duk wani abu dake nuni da ba a son mutum akansa yake ƙarewa?”

    Rarrashinta ya yi sannan cikin kuka ta labarta masa abin da ya tunkaro su kuma.

    “Ina jin lokaci ya yi da zan nunawa Hayatu bai fi ni zafin kai ba. Turo min lambar baban ita matar Taj ɗin. Sati na sama in sha Allahu za ta tare. Idan ya kuma barazanar rabasu kuma ni da kaina zan ɗauki mataki.”

    “Yaya ita kuma tsohuwar matar tasa fa?”

    Dariya ya yi ta manyan dattijai “kinsan Allah, barazana ce kawai. Hayatu da wuya yake yar da abu ya waiwaye shi. Abin da ya raba shi da Habibu kenan tun farko. A yanzu kuwa ban hango zai taɓa yarda babar Ahmad ta zama surukarsa ba. Rabuwarsu ba ta daɗi bace.”

    Nutsuwa ta samu da wannan wayar. Ta fito falonta don zuwa wajen Amma ta gansu duka zaune. Umma ta faɗa musu abin da ya faru. Su ka haɗu suna bata baki. Tun bata son nuna ai ɗan cikinta Alhaji yake yiwa haka har ya kai ta fito tana faɗa da bakinta.

    Su ka haɗu da Amma su ka bata baki. Auren ƴar Mami kuma ko Taj ne ya kwaso da kansa ba za su yarda ba. Suna wannan tattaunawar Alhaji ya shigo ɓangaren nasu. Ganin babu kowa ya tambayi ina su ke. Aka ce su na ɗakin Inna. Juyawa ya yi bakinsa alekum ya fice, musamman da yaji cewa Amma ta zo. Sake hargitsasu za ta yi ta zuge su tas. Ƙarshenta in bai yi da gaske ba sai anyi sa’in’sa a gaban mutane idan ya ce zai nemasu yanzu.

    ***

    Sai washegari Taj ya sami ƙwarin fita sosai. Jiya da su ka yi waya da Hamdi ya ce zai je Happy Taj ta ce ya bari ya ƙara hutawa.

    “Kin isa matar Happy. Dama tunda Happiness ya yi tafiya na san ba wani daɗin wajen zan ji ba sosai. Da ni ɗan gata ne dai sai ki zo ki tayani zama.” Yayi maganar a hankali.

    “Naƙi wayon. So ka ke Abba ya tsireni? Yana wajen sai na zo na wuce.”

    Marairaicewa ya yi “A misali da ba zai yi faɗa ba za ki zo? Uhmm? Allah naji jiki fa. Ga rama.”

    “Kullum fa ina kiranka.”

    “Kira daban, gani da ido daban. Kin san fa babu jinya mai daɗi kamar kayi a gaban matarka.”

    Hamdi tayi dariya. Da alama Taj kallon yarinya yake yi mata. Shi ne zai yi mata wayo.

    “Allah ko? Saboda me?”

    “Ana yi ana petting ɗin mutum. Ga pecks here and there. Sai ka manta ma da ciwon.” Ya bata amsa yana jin dama so samu ne.

    Baƙuwar kalmar da taji ta tambaye shi.
    “Meye kuma pecks?”

    Taj na jin haka ya tashi zaune yana ƴar dariya. Ashe ma wayon da take ta zillewa zai yiwu.

    “Peck ɗin ne baki sani ba? Ko dai kin faɗa ne?”

    “Allah ban san shi ba. Pecks naji ka ce.”

    Da fatan kada ta ɗago shi ya ce “Da yawa ne pecks. Gashi akwai nauyi da na ɗauko miki.”

    “Idan da rabo sai na gani watarana.”

    Duk a zatonta wani abu ne da ido zai iya gani kuma hannu zai ɗauka.

    Dama ce ta zo wa Taj bayan sun gama wayar da yamma. Mama ta kira Yaya ta sanar da ita za su zo washegari ita da su Amma. Wasu daliliai sun janyo suna son ayi biki sati mai zuwa. To dama su ma suna ta ɗan shirinsu don ba a zauna haka ba.

    Yaya sai ta kira Hamdi ta ce ta tambayi Taj ko gidan Sajida ne gobe ta tafi.

    “Idan baki je yanzu ba aka fara biki za ku kwana biyu baku haɗu ba.”

    Daɗi ya kama Hamdi. Tana ta murna ta kira shi. Sai ya ce ta shirya shi zai zo ya kaita.

    Shi ne fa yau ya shirya yau cikin nishaɗi. Happy Taj ya fara zuwa. Akan idon Alh. Usaini ya wuce. Nan da nan ya kira Ummi ya ce aikinsu zai iya yiwuwa yau. Da alama Taj ya dawo aiki. Tunda suna ta kula da shige da ficensa tun bayan sun gama shirinsu. Sai dai bai ƙara zuwa ba sai yau ɗin.

    Kai tsaye Salwa Ummi ta kira. Don dama Alh. Usaini bai yarda Salwan ta san shi ba. Ko ta kwaɓe sai dai su ƙare tsakaninsu da Ummi. Tana zuwa Ummin ta bata turarukan da Alh. Usaini ya bayar. Guda biyu ne masu wani irin ɗan karen ƙamshi. Ɗaya a yadda Ummin ta faɗa mata zai haddasa faɗa tsakanin Hamdi da Taj. Ɗayan kuma zai haɗa ƙaƙƙarfar soyayya tsakaninta da shi.

    “Amma me yasa ki ke taimaka min Ummi?” Salwa ta tambayeta bayan ta karɓi turarukan.

    “Saboda ba zan taɓa sanya ido Hamdi ta zauna a gidan miji alhali ni ta hana ni aure ba.”

    Da farinciki Salwa ta ce “Allah Ya bani ikon taimaka miki nima a duk lokacin da kike buƙata.”

    “Amin”

    Bayanin yadda zata saka turaren Ummi tayi mata. Ta fito za ta tsallaka ta shiga Happy Taj sai taga motar Taj ɗin yana fitowa. Hankalinta ya tashi. Ummi ta ce kada ta damu. Su jira zuwa la’asar domin indai ya shigo ko ya fita da wahala a rufe wurin baya nan. Jin haka sai ta sami wuri ta zauna su ka cigaba da ƙulla yadda za ayi bikin Salwa da Taj bayan sun yi nasara.

    ***

    Zee ce ta yiwa Hamdi light make up sannan ta shirya. Doguwar rigar atampa ta saka wadda take fitted daga sama. Sai kuma aka buɗeta daga ciki har ƙasa. Turarukanta na scentmania tabi ta shafe jikinta dasu.

    “Don Allah Ya Hamdi a dinga ragawa Salman Khan.”

    “Wallahi zan miki rashin mutunci akan kiransa Salman Khan.”

    Zee ta dinga dariya. Suna gama ɗaurin ɗankwali ya kirata. Yaya tana son yi mata ɗan gargaɗin manya amma kuma ta rasa me ya dace ta ce. Miji da mata wane gargaɗi kuma za ayi musu wanda ba zai shiga hurumin shari’a ba? Ƙarshe dai sai cewa tayi,

    “A kula da kai dai. Banda yin abin da bai dace ba.”

    Tunda ta fito ya kasa ɗauke ido daga kanta. Yana mamakin yadda ya mallaki wannan yarinyar da ya taɓa gani tana practicing speech. Ganin farko ta kanainaye masa zuciya. Ita ce first true love ɗinsa. Ya kuma yi sa’ar zama mijinta.

    Daga ciki ya buɗe mata ƙofa. Sai da ta zo shiga ta fara jin faɗuwar gaba. Ta kasa gane ta murnar ganinsa ce ko ta tsoron fitinarsa, ko kuwa ta wani abin daban da bata sani ba?

    Zama tayi ta rufe ƙofar sannan ta gaishe shi. Tana yi tana kawar da kai daga kallon fuskarsa. Ta san yanzu yana ganin kwalliyarta zai ce kama tsokanarta.

    “Mrs Happy yau kuma ƴar ɓoye fuska ce? Irin yanayin nan da Indians…”

    A gaggauce ta ɗaga fuska su ka haɗa ido.

    “Kada ka ƙarasa. Ka bar Indiyawa su sarara don Allah.”

    Lumshe ido ya yi ya buɗesu akan fuskarta.
    “Na barsu. Yau ko su basu da kalaman da zan yabawa Hamdina.” Yatsa ɗaya ya ɗaga a gaban fuskarsa “In ce awwnnn sau ɗaya don Allah?”

    Riga shi tayi harda fari da idanu “awwnnnnn”

    Taj ya sanya hannayensa duka a saitin zuciyarsa “yarinyar nan za ki kashe ni. That was just too cute.”

    “Tunda kaga ba kai kaɗai ka iya ba don Allah ka daina.”

    “Ban yi alƙawari ba. Atleast zan cigaba kafin na samu wani abin tsokanar taki.”

    Tuƙi ya fara a hankali suna tafiya Hamdi ta sake yi masa sannu da jiki.

    “Ka rame da gaske fa.”

    “Sauron garin nan wasa ne? Jiya na kira mai kula da gidanmu na ce su duba duk wata ƙofa ko window a saka net.” Don jin me za ta ce ya ƙara da cewa “ko mu je ki gani?”

    “Allah Ya baka haƙuri. So kake Yaya ta ce a biyoni da kayana kada na dawo gida yau?”

    “To ba shikenan ba. Kowa ya huta.”

    Cewa tayi bata yarda ba. Ya ce sai ya kaita. Dama ya kamata su gaisa da Amma. Tunda tana can da su Umma kafin su je wajen Yaya sai su haɗu. Hamdi ta rikice sosai don ya đauke hanya daga inda ta kwatanta masa gidan Sajida. Ya gama janta sannan ya ce Happy Taj za su fara zuwa.

    Narke masa fuska tayi “so dai kake dole yau nayi laifi ko?”

    “Ba zama zamuyi ba. I just realllyyy need to show you that peck.”

    Zazzaro masa idanu tayi “da ka bari ma kawai…”

    Taj ya kama dariya “yau wata za ta yiwa Abba bayani. Ki ka ce min baki sani ba.”

    “Muna gama waya na duba a google.” Ta bashi amsa da ƙaramar murya.

    “Wannan fassarar google ce. Ni dai sai na nuna miki.”

    “Don…”

    “Shhhhh. Ba a faɗa miki babu kyau roƙo ba?”

    Wanda baya jin magiya biye masa kawai ake yi. Daina zancen tayi ta karkata zamanta ta zuba masa idanu yana tuƙi.

    “Mene ne?”

    “Jira nake muje ka nuna min peck ɗin nan.”

    “Haaa, shi yasa nace kalarmu ɗaya. Ni dake duk fitinannu ne. Allah dai Ya shiryemu.”

    Juyo da abin kanta ya yi ya dinga tsokanarta har su ka isa akan idon Salwa don ta riga Ummi ganin motar tasa. Nan gabanta ya cigaba da faɗuwa kada su haɗu da Abba. Taj ya buɗe mata wata ƙofa ta baya wadda directly office ɗinsa za ta kai mutum.

    “Emergency exit ce for naughty people like us.”

    “Banda ni.”

    “Kin ganki fa.” Ya janyota ya rungumeta a jikinsa gabaɗayanta “ke da aka ce ki tafi gidan yayarki kin biyo miji office.”

    “Laifin wa don Allah?”

    “Naki mana” ya soma magana a hankali. Ƙamshin jikinta ya tayar masa da kewar sati guda “I miss you so much.”

    Idanunta sun soma raina fata don akwaita da tsoro ta ce “ka zo mu tafi.”

    “Uhm uhmm” peck ɗin da ta ce bata sani ba ya soma sauke mata a fuska.

    “Happy” ta daure ta kira shi. Tsoro ne fal a zuciyarta. Na zuwa wajen da kuma na shi kan shi mijin nata.

    “Mrs Happy”

    Daidai lokacin su ka ji an ƙwanƙwasa ƙofar. Hamdi ta ƙwace daga hannunsa a firgice. Shikenan, idan Abba ne ta gama yawo a wurin Yaya ba shi ba.

    Muryar wani yaronsa yake ji yana rantsuwar baya nan. Sai kuma ta mace da ya tabbatar Salwa ce tana cewa taga shigowarsa. A buɗe mata ta jira shi. To da yake yaron ya santa sai ya ce ta bari ya ɗauko spare key.

    Ita Hamdi ko maganganun bata ji da kyau. Ƙofar kawai da taji an riƙe yasa ta neman toilet.

    “Stay with me please. Ba Abba bane.”

    Ta girgiza kai ta gudu. Idan ba Abba bane ai dai zai iya samun labari.

    Tana shigewa Taj ya buɗe ƙofar. Salwa ya gani a tsaye yau ita ce da mayafi a kafaɗa ɗaya ɗan mitsitsi haka?

    “Ya Taj” ta kira sunan shi tana murmushi.

    Baya ya yi don ta samu ta shigo saboda kada ta faɗi abin da zai kunyata shi. Tana sanya ƙafarta a ciki ta rufe ƙofar.

    “Salwa me ya kawo…”

    Faɗo masa tayi a jiki kafin ya gama tambayarta. Hannunta hagu da dama kowanne da turaren da Ummi ta bata. Wuyansa ta riƙe da hannayen saboda ance lallai ta taɓa fatarsa da turaren ba kaya ba.

    Ya sanya hannuwansa zai cire nata sai dai kuma duka hannuwan ta shafesu suma. Saboda haka yana taɓawa abin ya sake shigarsa.

    “Sake ni Salwa” ya ce yana jin wani irin abu na shigarsa.

    “My Taj…” ta sake yunƙurin rungumarsa.

    Fincikota taji anyi ta baya don bata ji lokacin da aka buɗe ƙofar banɗakin ba. Ta juya za ta yi magana Hamdi ta tsinketa da mari.

    “Ke! Ni za ki…”

    Rai a matuƙar ɓace Hamdi ta sake marinta sannan ta saka hannu ta rabata da Taj.

    “Fita.”

    “Nace ki fita ko na tara miki mutane. Banza kwartuwa.”

    “Ya Taj warn this girl.” Salwa ta ce tana ƴar dariya “ko na kashe maka jiki ne?”

    Shi fa jiri ne ma yake ɗaukarsa. Amma idanun Hamdi sun rufe da ganin da tayi musu. Me zai sa ya bari Salwa ta rungume shi na tsayin lokaci har ta fito.

    Ƙofar office ɗin Hamdi ta buɗe ta kamo hannun Salwa ta janyota. Inda ta sami ƙarfin hali da na jiki ma bata sani ba.

    Ita kuwa dariya ma take yi ta ce “Baki ga komai ba ƴar ɗan daudu. Sai na zo har gida.” Ta yi murmushi ta fita.

    Idanu a birkice Hamdi ta juyo ta kalli Taj. Kan da yake riƙewa ma a wajenta ba komai bane illa pretense.

    “Abin da ka kawoni ka nuna min kenan?” Tayi magana tana hawaye masu zafi.

    “Hamdi ba haka bane.”

    “Dama ku maza munafukai ne.”

    “Ni ne munafukin? Ni?” Zuciyarsa ta harzuƙo da wani irin ɓacin rai.

    “To ko ɗayan zan kira ka? Wanda ya dace da mazan dake neman matan da ba nasu ba?” Ta faɗa kai tsaye.

    Rufe bakinta ke da wuya kuwa ya ɗaga hannu zai mareta.

    “Bismillah. In baka mareni ba baka haifu cikin uwa da uba ba.”

    Tassss.

    Shi da yayi marin da ita da ya mara su ka kama zubar da hawaye lokaci guda. Komai na jikinsu da zuƙata yana nuna musu illar kalamansu ga juna da abin da su ke yi. Amma kuma wani abu daga gefe yana ingiza su da jin haushin juna na ban mamaki.
    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    Note
    error: Content is protected !!