Rayuwa Da Gibi – Chapter Thirty-three
by NadminMASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
Rashin walwala da kuzarin Taj har su ka idar da sallah yasa Hamdi wasu irin tunani marasa daɗi. Me tayi masa? Ko wani abu ne ya same shi? Ko kuwa wani abu yaji wanda bai yi masa daɗi ba? Idan sun haɗa ido sai ya yi murmushin da iyakarsa fatar baki. Cikin idanunsa fargaba take gani. Tayi zaton mata ko ace amare ne kaɗai su ke shiga yanayin tsoro a irin wannan dare. Ashe harda maza. Kai, amma bata zaton haka a wajen Taj. Anya kuwa irin abin da yasa zuciyarta tseren da take yi tun ɗazu shi ne a ransa?
Suna zaune kowa akan abin sallarsa ta zuba masa idanu. Abu ne da bata taɓa samun damar yi ba a baya. Indai suna tare shi ne da kallon. Ko satar kallonsa ta so yi da wuya ta sami cikakken minti guda kafin ya sake juyowa. Amma abin mamaki yau da ake zaton wuta a maƙera sai aka sameta a masaƙa. Tafi minti goma tana nazartarsa bai sani ba. Daga zaune ta ja jiki ta matso kusa dashi tunda dama babu nisa tsakaninsu.
Muryarta a tausashe ta ce “Wani abu ne ya faru?”
“Me ki ka gani?” Taj ya faɗi yana miƙe ƙafafunsa. Sannan ya sanya hannunsa a kafaɗarta ya dawo da ita jikinsa.
“Babu komai tunda baka son faɗa min.”
“Am fine Hamdi. Gajiya ce kawai.”
“Allah Ya warware. Ka kwanta kayi bacci zuwa safiya za ka ji sauƙi in sha Allah.” Bata yarda ba. Kuma ta san cewa shi ma da ya faɗa ya san bata yarda ba ɗin.
Neman abin cewa yake yi wanda zai kwantar mata da hankali sai wata ƙaƙƙarfar atishawa ta zo masa. Sau biyar yayi ta a jere. Kowacce ta fito sai ya ce Alhamdulillah. Ita kuma ta bi masa da YarhamukAllah.
Tabbas a cikin ambaton Allah akwai rangwame ga bayi. Tun a ta uku Taj ya soma jin ƙamshin ɗakin da na jikin Hamdi sun cika ƙofifin hancinsa. To dama sihirin ba ayi shi don ya kama shi da wuri ba. Musamman Alh. Usaini ya nemi wanda zai shiga sannu a hankali saboda Taj ya zata cuta ce. Idan haka ta faru asarar dukiya kawai zai yi ta yi wajen neman magani. Babu lallai in shi ko wani nasa ba masu yarda da harkar sihiri da bokanci su yi tunanin neman karya aikin da Ayar Allah.
Shi dai tunda yaji wannan ƙamshin ya tashi da ƙarfinsa ya sungumi Hamdi yana faɗin Alhamdulillah.
“Wai don Allah me ya faru?”
Hancinsa ya ɗora akan nata tana cikin hannuwansa ya ce “its nothing” ya kama juyi da ita. Daga nan ya manta da komai ya kuma mantar da ita. Daren ya zama tarihin Tajuddin da Hamdiyya su kaɗai.
***
Wai bahaushe ya ce kayi da kanka kafin ayi da kai. Tunda Kamal ya faɗawa Yaya Kubra cewa Alhaji da Ahmad sun san da ciwonsa ta kasa samun kwanciyar hankali. Gani take kowane lokaci Alhaji zai iya kiranta. Abin da zai biyo baya kuwa sai Allah. Ilai kuwa wajajen goma na dare sai ga text ɗinsa. Bangajiyar biki ya fara yi mata sannan ya rubuta
(Ki nemi izinin mijinki. Ina son ganinki gobe da safe.)
Bacci ɓarawo da tarin gajiya ne su ka yi awon gaba da ita ba don ta so ba. Maigidan nata ta faɗawa komai a hali na tashin hankali.
“Wallahi ba ya son ɓoye ɓoye. Goben nan ban san me zai yi min ba.”
“Baki kyauta masa bane kema kin sani. Ba don ya neme ki ba da nima zan nuna miki kuskurenki na biyewa Kamal. A wautarsa gata yayi muku na yin shiru. Amma a zahiri cutar kansa ya yi. Ance a problem shared is a problem solved. Bamu san ta inda za a dace ba da ya faɗa da wuri.”
Wannan magana ƙara dagula mata lissafi tayi. Washegari a daddafe ta jira ƙarfe bakwai da rabi tayi ta kama hanya ta tafi gida. Waya ta ɗauka ta kira Alhaji. Yayi mamakin sammakonta.
“Idan kina da aikin safe ne ki wuce Kubra sai na same ki a office idan na shirya.”
“A’a Alhaji. Na san akan abin da kake nemana. Babu aikin da zan iya idan baka fahimceni ba.”
Katseta yayi da ya gane me take nufi.
“Jira ni a ɗakin Kamal.”
“To Alhaji. Kayi haƙuri don Allah.” Ta faɗi da rawar murya.
Ko amsata bai yi ba ya kashe wayarsa. Yaƙi jinin ƙumbiya ƙumbiya. Shi yasa yake jan su a jiki tun basu da wayo. Ko fensir wannan bai yarda wani ya zo ya ce wane na buƙata ba. Ya fi son ka je da kanka ka faɗa.
“Ban faɗa masa komai ba.”
Kamal ya tabbatar mata da ta shiga ɗakin.
“Nafi tunanin gaya min zai yi. Gara da na faɗa masa gaskiya a waya don ban san yadda zanyi na fidda kaina a gabansa ba.”
Sai bayan kimanin minti sha biyar Alhaji ya shigo tare da Bishir da Abba. Kana ganinsu ka san basu san me yake faruwa ba. Sun dai kama bakinsu tunda sun san koma mene ne yanza za su ji. Ita dai Yaya Kubra tana haɗa ido da Alhaji ta sunkuyar da kai. Daga daren shekaranjiya zuwa yau ya faɗa. Dakakkiyar shadda ce a jikin shi ruwan toka. Babbar rigar a ninke Abba ya rataya a hannunsa. Kwarjini iya kwarjini sai Alh. Hayatu.
Da kakkausar murya ya ce mata “Kin kyauta.”
“Alhaji don Allah…” ta fara cewa tana zamowa daga kan gado.
“Ya isa.” Ya zauna a inda ta tashi. Yaran nasa su ka zagaye shi a ƙasa banda Kamal da ya hana motsawa daga kan kujera.
“Wace gudunmawa shirunki ya sama min?”
Iya bincikenta na ƴan uwansu na kurkusa (gidansu Alhaji da Hajiya) ta sanar dashi. Abin al’ajabi cikinsu babu mai blood group AB(-). Ana bikin Taj ta tura musu survey link na google form inda ta buƙaci su cike da cewar research (bincike) ne take yi da ya shafi aikinta. A ciki tayi tambayar da mutum sai ya saka sunan dangin da ya fito. Ta haka ta rarrabe kowa.
“An sami masu rhesus negative mutum huɗu.”
Alhaji ranƙwafowa yayi kamar da haka ne zai ji me za ta ce sosai.
“Biyu ba za su iya yi masa amfani ba domin ɗaya A ne, ɗayar kuma B.”
“Ina jin ki Kubra.”
“Masu O negative biyu da za su iya taimaka masa, ɗaya ɗiyar ƙanwar Hajiya ce.”
“Mata suna iya bayarwa ne?” Alhaji ya tambayeta hankalinsa a tashe. Bishir da Abba su ka sake shiga duhu.
“Eh, amma…amma da wuya a samu nata. Widad ce. Yaranta biyu tana da cikin na uku” Yaya Kubra ta faɗi, ita ma kanta tana cikin jin ciwon hakan.
Kamal ya dube su. Irin wannan abin yake gudu.
“Alhaji don Allah…”
“Ka rufe bakinka Kamal” ya tsawatar masa. Ya juya ga Yaya Kubra “Sai wa kuma?”
“Ɗan Widad ɗin na farko mai shekara biyar. Yayi ƙanƙanta.”
“Wai me ake buƙata ne Yaya Kubra?” Abba ya gaji da jin maganar da bai fahimta ba kuma yana ganin masu yinta cikin rashin nutsuwa.
“Ƙoda ce Abba. Duka ƙodojin Kamal ciwo ya cinye su.” Alhaji ya bashi amsa da kansa.
Innalillahi wa inna ilaihi raji’un. Abba da Bishir kuka su ka fashe dashi. Alhaji ko hanasu bai yi ba. Kowanne yana cewa a cire tashi. Da su ka ji ba da ka za a ɗauka ba nan ma sun sake shiga tashin hankali. Kamal mai ciwon shi ya koma rarrashinsu.
“Amma fa ni ban gane ba. Me yasa masu A da B ba za su iya bashi ba, bayan kuma su ma ɗin negative ne? Jiya fa nayi ta bincike Kubra. A da B duka donors ne.” Cewar Alhaji da sanyin jiki.
“Haka ne Alhaji. Mai B ɗin sickler ce.”
Alhaji ya ce “Ita ma mace? Bana ma son a kai ga ɗaukar na mace. A ɗin fa?”
“Ɗan Kawu Sayyadi ne (ƙanin Hajiya). Shi kaɗai ne bayan mu nan wanda ya san da ciwon Kamal. Naje na same shi. Ban ko roƙa ba ya ce a shirye yake da aje a cire tasa. Shekaranjiya kafin naje wajen bikin test muka fara zuwa aka yi masa.” Ta ja numfashi sannan ta ce “yana da Hepatitis.”
“A taƙaice dai …Ya Rabbi….Allah na” Alhaji ya danne ƙirjinsa da ya kama wani irin ciwo.
Duka su ka rufar masa. Yaya Kubra ta tashi zata koma mota don motar likita ba ta rabuwa da kayan bada kulawar gaggawa.
“Dawo ki zauna.” Alhaji ya tashi ya dafa kafaɗar Kamal “akwai Allah kaji ko.” Ya dubi Abba “ka haɗa muku kaya kai da Kamal akwai jirgi gobe. Yanzu zan sa Ahmad ya sayi ticket ku tafi Saudiyya.”
“Alhaji ni fa? Me zan yi?” Bishir ya tashi tsaye da zafin nama yana goge ƙwalla.
“Tare zamu bisu jibi da Ahmad. Bana son iyayenku su gane komai. Kawai zan ce musu Umra zamu ni da yarana maza.”
“A nan za ku barni Alhaji?” Yaya Kubra ta soma sabon kuka.
“Kina da visa ne?” Da sauri da amsa cewa akwai “ki tattaro komai na asibitinsa a wajen Dr. Mubina jibin sai mu tafi. Ki san me za ki faɗawa iyayenki tunda kin ƙware a rufa-rufa.” Kai ta sunkuyar.
“Me zan faɗawa Taj?” Kamal ya yi tambayar ga Alhaji.
“Zai yi zargin baka haƙura ba shi yasa baka haɗa da shi ba.” Inji Bishir.
Alhaji wayarsa ya ɗauko daga aljihun gaban rigarsa ya dubi lokaci. Yayi wuri ya kira mai sabon aure. Sai ya ce da Kamal,
“Ka faɗa masa zamu je Umra amma ba da shi ba. Yaje ya yiwa matarsa passport a nemi visa a sanar dani sai su tafi daga baya.”
Da ya fita ya kulle musu ƙofar ɗakin sai ya sami damar barin zazzafar ƙwallar da ya danne a gaban ƴaƴansa saukowa. Sau ɗaya ya haɗa ido da Kamal yaga yayi masa murmushi na wanda ya karɓi ƙaddararsa hannu biyu.
“Ya Allah ban isa ba. Ba iyawata bace ta bani ƴaƴan nan. Allah nagodewa ni’imominKa gareni. Da rauni da gazawata na zo gareKa cikin ƙanƙantar da kai. Ka ceci rayuwar ɗana Ya Ubangijina.” Bayan shekaru masu ɗimbin yawa ya sami kansa da fashewa da kuka mai ciwo da cin zuciya. Yana ƙaunar ƴaƴansa kamar rai. Waɗanda ya rasa a ɓari da biyu da su ka tafi da ƙananun shekaru har yau yana jin abin a ransa.
Tsayuwarsa ya yi a wajen yana neman nutsuwa amma idan ya tuna haƙuri irin na Kamal sai yaji zuciyarsa tana zafi. Duk gidan shi ne yafi kowa damunsa akan maganar Taj. A dalilinsa ya haƙura ya bar iyalinsa suna mu’amala da Taj ɗin. Domin da fari niyarsa ya yanke shi daga jikinsa gabaɗaya.
Ƙofar ɗakin Yaya Kubra ta zo da shirin fita taji sautin da mahaifinta yake dannewa. Bata san lokacin da ta koma da baya ta ɗora kukan ba. Abba da Bishir su ka kara kunnuwa su ka ji. Kowa ya koma ya zauna da kuka. Shi kuma ya koma ciki ya shige ɗaki ya rufe ƙofa.
“Magana ake ta Kamal yana da rai har yanzu. To me hwaru?” Kamal ya faɗi yana dariya.
“Ni ban taɓa tsanar wannan kalmar ba sai kamar yau.” Abba ya sha kunu.
Yaya Kubra tayi murmushi “dole ka sako wasa kafin Taj yaji wannan maganar.”
“Don Allah ki bar tayar min da hankali. Da me kike so in ji? Ciwon ko tararrabin abin da zai zo yayi?”
***
“Siyama kin tabbatar duk abin da Iyaa ta faɗa min gaskiya ne?”
Yadda Baba Maje ya ɗauki zafi sai da gaban Siyama ya faɗi. Ta dai san cewa ba gulma ta kawo ba tunda cutar da mutum taji za ayi take son hanawa da ikon da Allah Ya bata.
“Da gaske ne Baba.”
“Kirawo min Ummin”
Tashin muryar iyayen nata ne ya fito da ita daga ɗaki inda taji Baba Maje na rantsuwar sai ya karya Ummi. Iyaa kuma tana tare shi. Da ƙyar ta samu ya nutsu shi ne ta ce masa,
“Taurin kai gareta ka sani. Idan baka bi komai a hankali ba wallahi ko me zai faru ba faɗin gaskiya zata yi ba.”
Bai daina faɗan ba sai dai ya haƙura da zancen zuwa ya tasheta da duka. Hankalin Siyama sai ya tashi shi ne ta fito yake tambayarta.
“Ita hayaniyar nan bata tasheta ba?” Ya faɗi yana girgiza ƙafa da kallon ƙofa.
“Yanzu zan taso maka ita. Amma don Allah ka bi komai a sannu.”
Ɗakin nasu Iyaa ta shiga ta taso Ummi. Har ta fara kiran bacci bai isheta ba Iyaa ta daka mata tsawa. Haka ta biyota tana zumɓura baki. A zatonta aiki ne za a saka ta. Sai gata tayi ido huɗu da Baba da su ka sauko ƙasa.
“Ke Siyama hau sama ki ɗauko min wayar Ummi.”
Firgigit duk wani baccin iya shege da hammar ƙarya su ka gudu.
“Wayata Baba? Ke tsaya Siyama.”
Siyama ta dakata. Baba ya zaro mata idanu ta kama bin bene ba shiri.
“Baba me nayi? Don Allah kada ka duba min waya.” Ummi ta juya za ta hau benen.
“Ki ka kuskura ki ka hau benen nan sai nasa Baballe ya karyaki.”
Cak ta tsaya “Baba me nayi?”
Bai kulata ba don bata cancanci hakan ba har Siyama ta sauko ta bashi wayar.
“Ɗakinku ɗaya. Ki faɗa min gaskiya, akwai wata ko babu?”
Mugun kallo Ummi ta watsawa Siyama. Ita kuma jikinta ya ɗan yi sanyi.
Iyaa ta ce “Baki ji me aka ce miki bane?”
“Akwai”
“Ɗauko min.”
“Baba don Allah…” Ummi ta zube a ƙasa tana magiya. Abubuwan dake cikin wayar dake ɗakin sun fi ƙarfin me wayar. Dukkan wata mu’amalarta ta waje da fitintinunta suna ciki.
Ba jimawa Siyama ta sauko saboda a ƙasan filo Ummi ta ajiyeta da ta raba dare tana dannata jiya.
“Zan saurari Habibu don nayi imanin indai wani abu ya faru gidan ƴaƴansa ba zai ɓoye min ba. Idan abin da Siyama taji kina ƙullawa ya tabbata to ki kuka da kanki. Sannan in ki ka saka ƙafa a ƙofar gida to kada ki dawo na yafeki.” Ya kalli Iyaa da Siyama “duk wanda ya bata aron waya ba da yawuna ba.”
Wayoyin ya kashe a gabanta ya tashi ya shige nasa ɗakin. Ummi ta rasa gane kuka ya kamace ta ko me. Abin da yake taso mata yafi ƙarfin hawaye ko kalaman da take jin tana son zazzagawa Siyama.
***
Ahmad ya so ƙwarai ya kira baban Salwa akan ya turo a ɗauketa. Da wannan niyar ya shiga ɗakinta inda ya mayar da Mami bayan tafiyarsu Anti Zabba’u ya shiga da ya gama wayar. Ɗakin wari yake yi mai ɗauke numfashi. Ya yi mata kallo ɗaya ya juya. Nan ya barta tana so tayi kuka amma bakin ma ya karkace sai dai hawaye kawai. Kallon da yayi mata na takaici ne da baƙincikin halin da ta saka kanta kuma su ma ta jefa su.
Mami bata da kowa sai ƴan uwa waɗanda ta jima da barranta kanta daga garesu saboda abin duniya. Bata zuwa sabgar kowa sai dangin dangiro da abokan arziƙi masu kuɗi. Jininta dai ta datse zumunci da rashin mutumci saboda ita tana gidan mai kuɗi. Yau ga ranar ƴan uwa amma babu wanda zai nema ya taimaka masa da kula da ita. In ya ɗorawa Zahra wankin kashi da fitsarinta ba ƙaramin rashin adalci hakan zai zama ba. Yau da gobe sai Allah. Gashi Mamin a baya bata nuna mata ƙauna saboda akwai wadda ta so ya aura. Wannan tunanin yasa shi fasa neman Salwa ta tafi. Ita ce mace kuma dolen Mami. Zai saka mata ido kafin ya sami wadda zai dinga biya.
Shawarar da ya yanke ya faɗawa Zahra. Ta bashi goyon baya da alƙawarin za ta dinga taimakawa ita ma.
“Ni ban san me yasa ka damu da komawarta ba tun farko. In don Taj ne ina ganin yanzu ai ta haƙura.”
“Ke dai ayi shiru kawai. Allah Yasa ta haƙura ɗin. Ni dai duk ranar da ta fita daga gidan nan idan bana nan ki kirani.”
“In sha Allah”
Taɓe baki Salwa tayi. Zancen ba a bayan idonta ake yi ba. Tana kitchen kuma suma sun san tana jinsu. Ba za ta nuna ɓacin rai don an barta zaman jinyar Mami ba. Za ta kwantar da kai ta bi Ahmad sau da ƙafa domin zamanta a gidan shi ne babban hujjarta da rufin asiri a Kano. Kafin nan dai da lokacin aurenta da Taj dole tana buƙatar gidan zama. Idan yaso in tayi aure sai taga wanda Ahmad zai ɗorawa aikin Mami idan ba Zahran ba.
Wayar Ummi ta sake kira bata samu ba. Ta doka tsaki ta ajiye wayar ta cigaba da wanke wanke.
***
Tsaye tayi a ƙofar banɗakinta dake cikin ɗaki tana kallon sauyin da gadon ya samu. Taj ya canja bedsheet ya gyare gadon. Halin da take ciki na ciwo da zazzaɓi bai hanata yaba kyawun setin american bedsheet da duvet ɗin da ya shimfiɗa ba. Navy blue da red flowers ne a jiki wanda kalar farkon ta dace da ta labulen ɗakin nata. Ita kam me za ta ce da Inna? Duk wani abu da uwa za ta yiwa ƴa ita ma anyi mata na gata. Akan sayen zannuwan gadon Inna da kanta ta kira Yaya ta faɗa mata sun saya a wadace. Indai ba akwai wanda ta tanada ba tuntuni to kada ta sayawa Hamdin wasu. Bayan wannan wayar sai ta turo aka kawo guda shida. Duvets biyu, normal bedsheets huɗu ta ce a rabawa Sajida da Zee. Sajida ta dinga murna kuwa da taga sunan dake jikin ledar.
“Ni fa a instagram nake following ɗinta (@nafs_beddings). Ashe zan ga kayanta zahiri.”
“Kyau garesu ko me?” Cewar Zee da bata san murnar me take yi ba.
“Kyau ma ai faɗar ɓata baki ne. Ki je shafinta ki gani. Ina maganar quality ne. Ki taɓa ki san kin haɗu da kayan ƙwarai ba jabu ba. Yadin sam ba ya tashi ki ga yayi kurajen nan kamar pimples a fuskar budurwa.”
Hamdi bata manta yadda su ka dinga dariya ba. Sai yanzu ta gane ashe dai da gaske ne maganar Sajida. Zama tayi tana shafa laushin duvet ɗin tana jindaɗin mallakarsa. (Kamar kullum ni ɗin ganau ce don har baby Ahmad na sayawa baby set a wajenta. Kayanta speak for themselves. Don Allah ku nemi Nafisa Tofa 08034581454 ku rabu da jabon zannuwan gado.)
Kwanciya tayi ta rufe jikinta. Bata ji motsin Taj ba. Ta dai yi tunanin ƙila yana nasa ɗakin. Gara ya yi zamansa a can. Bata son abin da zai sake janyowa su haɗa ido. Tashinta da yayi da asuba ma don babu yadda za ta yi ne. Zancen zuci ta cigaba da yi wanda gabaɗaya ya ƙare akan baƙuwar rayuwar da ta tsinci kanta a ciki jiya. Taj ya nuna mata so da ƙauna kamar ya haɗiyeta. Wata zuciyar ta ce mata ya kuma saka ki kuka kamar zai ƙarar miki da hawaye ba.
Tunaninta na kaiwa daidai nan ya buɗe ƙofar da sallama ya shigo. Da sauri kuwa ta sake yin ƙasa da kanta ta rufe ko ina.
Taj murmushi ya yi ya je bakin gadon ya soma buɗe lulluɓin da tayi. Bata bari ya gama ba ta kama duvet ɗin da nata ƙarfin. Sai ya saki, ya hau gadon daga gefenta ya turata ciki ta hanyar matsawa yana rufa shima.
“Matsa min, matsa min” ya dinga faɗi har su ka koma tsakiyar gadon sannan ya daina turata.
“Me ya hana ki bacci? Ko jirana kike yi?” Ya yi maganar yana rungumota gabaɗaya a ɓangaren damansa.
Hamdi ga tsoro ga tsiwa, ta haɗa biyun ta ce, “In jira ka kayi min me?” Da rawar murya.
Taj ya yi dariya “Hamdiyya matar Malam Tajo. Maida wuƙar ni ba wani abu nake nufi ba.”
“Waye kuma Tajo? Ɗan uwanku ne?” Ta harare shi.
“Ni ne shi, shi ne ni.” Ya nuna kansa.
Hamdi ta yamutsa fuska “A’a gaskiya.”
“To ke ce shi, shi ne ke?”
“A’a fa.” Ta ƙara da tura baki.
Abin ya burge shi ya kwanta a jikinta “To ya abin yake?”
Murmushi tayi na kunya “Ni ce kai, kai ne ni…shi kuma Tajo bamu san shi ba.”
“Taj ɗin ma in kin ce baki san shi ba sai a siyo rago a saka min sabo.” Ya faɗi maganar da wani shauƙi dake kwasarsa saboda shagwaɓar Hamdi “duk yadda kike so haka za a yi Mrs Happy.”
Wani sabon shafin ya so a buɗe ta ce sam bata san zance ba indai ba sumar da ita zai kuma yi ba. Ya dinga yi mata dariya. Su na ƴar hirarsu har bacci ya sake kwashe su. Ba su su ka farka ba sai da aka kira Taj.
Ƙanwarsa ce wadda a jerin haihuwarsu bayan Kamal sai shi sai kuma ita Rawda. Abincin amarya da ango na sati guda ta ɗauki nauyi saboda gidanta yafi na kowa yin kusa da na Taj. Kullum safe, rana da dare take turo yaron gidanta ya kawo a babur. Amarya da ango su ka sake samun lokacin shaƙuwa da sabo da juna.
Taj ya bar Happy Taj a hannun yaransa. Sai Abba Habibu dake zuwa amma ba kullum ba. Taj yayi yayi ya ɗauki hutu amma yaƙi.
Wata irin soyayya Taj da Hamdi suke yiwa juna wadda bata da shamaki ko basaja. Sak su ka fitowa juna tun farko, shiyasa alaƙar tasu tayi saurin ƙulluwa. Jin junansu suke yi tamkar tare da soyayyar juna su ka tashi. Ga Taj gwanin zolaya wadda a sati gudan nan Hamdi ta koya. Duk baƙon da ya shigo gidan sai ya fita da murmushi saboda nishaɗin da zai samu daga masoyan.
Abu biyu ne su ka so damun Taj amma dalilai sun sa basu yi tasiri ba. Na farko tafiyar su Kamal Umra bagatatan ko haɗuwa basu yi ba. Yayi mita kuwa kamar ya ari baki. A ranar da su ka tafi wadda ta kasance kwana biyu da tarewar Hamdi, da yamma ya tafi gida bayan wayar sallamar da Kamal ya yi masa daga cikin jirgi.
Cikin farinciki su ka gaisa da su Umma kafin ya hau sama da aka yi masa iso wajen Alhaji. Gaishe shi ya duƙa yayi Alhaji ya miƙa masa hannu yana girgiza kai.
“Kai ka san ba haka nake gaisawa da ƴaƴana ba.”
Da sauri Taj ya tashi ya ƙarasa gaban Alhaji ya miƙa masa hannu. Alhaji yayi murmushi sannan su ka zauna.
“Ina matar taka?”
Kai a ƙasa yana susar ƙeya Taj ya ce “tana gida. Ta ce na gaishe ku.”
“Ina amsawa idan da gaske kake.”
Rantsuwa Taj ya fara sai yaga Alhaji yana murmushi. Da alama dai yayi furucinsa da zolaya ne. Sannan babu shakka yana sane da abin da ya yiwa Abba Habibu ya ɓata ran Hamdi. Ba dai zai ɗauko zancen ba saboda ba shi ya kawo shi ba. Yana da mahimmancin da shi ma zuwa da zama na musamman ya dace da shi.
“Alhaji maganar Kamal ce ta kawo ni.”
“Kayi aure Taj. Bai kamata ka zauna kana ƙunƙuni don ya tafi ba tare da kai ba. Ya dace ka fara sanin ragamar rayuwarka da ta ƴar mutane ce a wuyanka yanzu. Ba dole bane Kamal ya daidaita tafiya da kai ba.”
“Ba haka nake nufi ba” cewar Taj
Tausayi ya bawa Alhaji yadda ya yi maganar. Shi kuma ya katse shi ne kawai saboda baya son hankalin Taj ɗin ya kai ga abin da ake ɓoye masa.
“To ina jinka.”
Shiru Taj yayi. Alhaji ya sami kansa da yin murmushi. Yayi matuƙar kewar Taj da halayansa. Idan kayi masa faɗa alhali bai yi laifi ba, haka zai yi ta marairaicewa sai ka koma rarrashinsa ko babu niyya.
“Ashe baka canja hali ba har yau? Mijin aure fa kake.”
“To ai ba maganar tafiyar nazo yi ba. Duk da dai naji haushi. Ko ba a je dani ba da sai a faɗa min. Ɗan Adam ba ya rasa buƙatu a wajen Allah.”
“To ka roƙa mana a inda kake. Allah Yana ko’ina.”
“Amma dai ba kamar idan ana shafa Ka’aba ana ambaton suna na da buƙatuna ba ko Alhaji.”
Sake faɗaɗa murmushi Alhaji ya yi. Ya dubi Taj ya ce “welcome home.”
Tsabar daɗin da Taj yaji bai san lokacin da koma kusa da Alhaji ya rungume shi ba. Alhaji ya gama basarwa amma a ransa daɗi yake ji.
Da ya nutsu ne ya faɗa masa ainihin abin da yake tunani. Yana magana Alhaji shiru kawai yayi. Daga dawowa gida, bayan kwana biyu da tarewar matarsa ya zai yi idan yaji ciwon da yake damun ɗan uwa mafi soyuwa a gare shi?
“Baka yarda da ilimin Dr. Mubina ɗin bane har kake tunanin wani ciwon ne yake damunsa?”
“Ba haka bane Alhaji. Ban sani ba ko idanuna ne amma har wani kumburi naga yayi rannan. Yanayin bai yi kama da ƙiba ba.”
Shi da baya son ɓoye abu bai san dalilinsa na son bawa Taj ɗan lokacin samun farincikin aurensa ba kafin ƙwai ya fashe.
“Yanzu mece ce shawararka?”
“Idan kun tafi don Allah ka tilasta masa zuwa asibiti. Idan da kai ne dole zai je ayi masa thorough check up.”
Alhaji ya yi murmushi don ya ɓoye halin da yake ciki.
“In sha Allahu zamu je.”
“Nagode.” Ya dinga faɗi har ya fita. A zuciyarsa yana mai fatan Allah Yasa babu komai.
To tafiyarsu Alhajin ne kuma sau biyu ya sake samun kansa a yanayi na ɗaukewar jin ƙamshi da ɗanɗano. A na biyun da ƙyar ya iya ɓoyewa Hamdi ya shiga ɗaki yayi ta bulbula turare kafin daga baya abin ya daidaita. Ranar da ya tasar masa na ukun kuwa ana gobe za su yi sati ne. Saboda tsabar tashin hankali, yadda yaga rana haka yaga dare. Cikin tsananin kiɗima ya zame jiki daga wajen Hamdi ya koma falo ya kira Kamal a waya.
MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
