Rayuwa Da Gibi – Chapter Thirty-six
by NadminMASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
Kwana biyu a ƙirgen Hamdi tana lura da duk wani motsin Taj. Ta riga taji a jikinta tun randa ya koma Happy Taj bai dawo gidan da irin jovial spirit ɗin da ya fita dashi ba. Aura ɗinsa gabaɗaya is down amma a zahiri babu wata alama ta ciwo. Ta tambaye shi me ya faru tun a lokacin ya nuna babu komai. Da dare kafin su kwanta ta sake maimaita tambayar sai ya shashantar da zancen.
Jiya ma haka aka yi, domin da ya dawo bai sake fita daga ɗaki ba. Ya ce mata mura yake ji tana neman kama shi. Tayi iya yinta ta rabu dashi. Haka su ka kwana kowa ya juyawa ɗan uwansa baya. Sai da asuba da farka ne ta ganta tayi matashi da ƙirjinsa ya rungumeta sosai. Shi kenan aka cigaba da ranar lafiya ƙalau kafin ya fita. Da ya dawo
Yau dai yana fita ta kira Abba Habibu. Kunya ta so hanata tambaya. Tana ta juya zancen a zuci. Kamar ya sani sai ya ɗauko maganar komawar Taj ɗin aiki.
“Ance maigidan naki ya soma fita ko?”
“Eh, ashe ba ku haɗu ba.” Ta amsa da sauri.
“Satin nan ban fita ba. Kin san yana ta matsa min da na ajiye aikin. Ni kuma ban saba zaman haka kawai ba. Na fahimci saboda yana aurenki kamar zai takura idan ina ƙarƙashinsa…duk da tun a baya bai taɓa ci min fuska ba. Na rasa shawarar yankewa Hamdi.”
Hamdi tayi murmushi “Abba indai ka san wani aikin za ka nema idan ka bar Happy Taj ɗin gara kayi zamanka.”
“Ba za ki ji komai ba?”
Numfasawa tayi da rawar murya “ba zan ji ba. Wanda nayi a baya ma don Allah ka yafe min Abba.”
Kafin ta karyar masa da zuciya har ya kai ga kasa ɓoye rauninsa ya ce “ba ki min komai ba. Har abada babu riƙo tsakani na daku in sha Allah. Allah Ya yi muku albarka.”
“Amin Abbana” tayi maganar cikin farinciki.
Hira ce ta kankama tsakaninsu wadda duk akan tafiyar Yaya ce. Kafin su yi sallama ne ta daure tayi masa tambayar duk da gudun kada yaga rashin kunyarta.
“Abba wani abu yana faruwa a Happy Taj ne?”
“Me ki ka gani? Me ya faru?” Ya tambayeta da sauri kuma cikin tashin hankali. Ba komai ya janyo hakan ba sai lura da yayi yanzu kullum Baba Maje sai ya yi masa tambayar da ta shafi Happy Taj da kuma lafiyar Hamdi da Taj ɗin.
Amsar tasa ta ishe ta samun gamsuwa “Kullum idan ya dawo yanayinsa babu daɗi. Na fahimci kamar daga can ne matsalar.”
Wayancewa Abba Habibu yayi tunda bai san mene ne manufar tambayoyin Baba Maje ba. Shi yasa bai sanar da ita ba.
“Anya kuwa? Da wani abu ya faru zan ji. Amma ki bari zan tambaya.”
Taƙaita zancen yayi cikin sauri da su ka gama wayar ya kira ɗaya daga cikin ma’aikatan kitchen ɗin Happy Taj. Babu wani ɓoye ɓoye ya ce ya fađa masa abin da yake son ji. Yaron bai musu ba. Don ya ce dama sun yi niyar kiransa da kansu ma.
Labarin da yaji bai yi masa daɗi ba. Kwana uku a jere girkin Taj ba ya ciwuwa. Duk abin da zai ɗora sai an sami matsala. Haka nan indai ya taimaka musu da nasu aikin su ma ba ya tafiya daidai.
“Yau bai saka mana hannu a girki ba. Da za ayi serving wasu baƙi sake yin taro a ƙaramin conference room wallahi Abba Habibu baka ga ɓarin da yayi ba. Trolley (food trolley) ɗin gabaɗaya ya kifar a gabansu.”
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un. Yanzu yana ina?”
“Ya ce kwastoman ƙarshe na fita mu tashi. Idan akwai sauran abinci a bayar.”
Jiki a sanyaye Abba Habibu ya ce “Nagode.”
Allah Ya taimake shi Yaya bata nan. Ita da bata da son fita yau ta nemi Zee ta rakata unguwa…gidan Baba Maje ta tafi yi musu bangajiya na musamman duk da an riga anyi a waya. Ta sayi atamfa da shadda masu kyau da tsada za ta basu na kyautatawa.
***
“Wai ni ina Ummi ne? Ba za ta fito mu gaisa ba?”
Cewar Yaya bayan an sami kimanin awa gida suna hira da Iyaa. A ƙofar gidan daga cikin adaidaita su ka rabu da Zee don ta ce ba za ta shiga ba. Cikin gari gidan ƙanwar kakansu ta gudu. Idan Yayan ta gama za ta dawo su tafi.
Iyaa ta numfasa “tun ɗazu nake ta addu’ar kada ki yi cigiyarta.”
“Allah Yasa lafiya. Indai ƙalau take ba sai kin yi min bayani ba.” Yaya ta faɗi tana murmushi.
“Jinjin kenan. Kina da kawaici sosai. Yanzu idan naƙi faɗa miki ba za ki ji haushi ba?”
“Banda abin ki ai ba ayi ciki domin tuwo ba kaɗai. Kuma idan bamu zama murfin sirrin ƴaƴanmu na farko ba to wa zai zama? Kada ki ji komai. Allah Ya dafa mana akan yaran nan kawai.”
Daga bayansu su ka muryar Baba Maje “sirrin Ummi ba zai rufu ba saboda lokacin bankaɗo shi ya yi.”
Kallonsa Iyaa tayi tana girgiza kai. Duk lalacewar Ummi ba za ta so hakan ba. Ba kuma don tana goyon bayan abin da tayi ba. Ko kusa! Duk duniya ko Baba Maje bai kai ta son shiryuwar Ummi ba. Kuma ta yarda da Yaya ɗari bisa ɗari amma dole tayi kwaɗayin sakayawa indai ba ya zama dole ba.
“Sakaya kan ki Habibu zai shigo.”
Jin haka Yaya ta juya ba shiri ta kalle shi. Murmushi ya yi kawai mai tarin ma’anoni ya fita.
Me zai kawo Abba a wannan lokacin? Wannan ita ce tambayar da ta yiwa kanta kafin su shigo tare da Baba Maje.
Babu zancen gaishe gaishe. Kai tsaye Baba Maje ya soma magana.
“A waya kayi min tambayar me yasa kwanakin nan kullum sai na tuntuɓeka game da lafiyar Hamdi da mijinta.”
“Shi ne kuma za ka ce in zo gida na same ka?” Abba ya tambaye shi domin shi ma ɗin ya shiga duhu.
“Inda zamu je yafi kusa da nan shi yasa. Kafin mu tafi amma zan so sanin me ya ankarar da kai har kayi min tambayar. Na san don ina yawan tambayar lafiyarsu ba zai zama abin tuhuma ba.”
“Ƙwarai kuwa. Sai dai keɓe Hamdi ba tare da yawan bibiyar lafiyar su Sajida ba shi ne yasa da naji wata magana game da Taj na neme ka. Amma ka sani ban yi da wata mamufa ba sai son jin ko kana ɓoye min wani abu ne don kada na shiga damuwa.”
Hankalin Iyaa sai yafi na Baba Maje tashi. So kawai take taji me yake faruwa da Taj ɗin. Abba Habibu ya faɗa musu abin da yaji daga Hamdi da ma’aikacin Happy Taj.
Da yake Yaya akwai dauriya idan ka kalli fuskarta ba za ka fahimci yadda wannan zance ya kaɗa ta ba. Iyaa kuwa kukan baƙinciki take yi. Wannan abin da yake faruwa akwai hannun Ummi. Wace uwa ce za ta yi alfahari da haka?
Baba Maje ya labarta musu rigimar da ta faru tsakanin Ummi da Salwa.
“Tun ranar babu wanda yaje a cikinmu. Rayuwar da ta zaɓa ce take yi mata horo tun yanzu. Gara a barta da duniya ta koya mata hankali.”
“Kada ka ce haka. Babu ɗan da aka taba barwa duniya aka ga daidai. Kuma ita ma yanzu da ka ƙyaleta idan ta haɗu da waɗanda su ka fita fitina fa?”
“Ummi ce fa! Babu wanda ya lalata ta sama da biyewa ruɗin zuciyarta. Indai bata ɓata ɗan wani ba, to kuwa babu wanda zai ɓata ta. Da kanta ta mayar da halayenta irin wanda mutane ke gudun yaransu su yi abota da ita.”
Su huɗu su ka rankaya police station ɗin da aka rufe su Ummi. Wani tsamurmurin Kofur ya fara yi musu surutu akan rashin zuwa tun ranar da aka kawo su. Baba Maje ya ce barinta yayi a ladabtar da ita. Kuma ko yanzu ba beli ya zo yi ba.
“Ɗakin da muke tsaron nasu fa a cunkushe yake. Tunda rigima ce kawai ta mata za a iya baku su.”
Ɗauke kai daga gare shi Baba Maje yayi. Ya ce yana son ganin wanda ya dace domin a fito da Ummi su yi magana. Aka dangana su da ofishin DPO inda a nan ne aka fito musu da Ummi.
Kwanaki uku kacal!
Ummi ta zuge ta fita hayyacinta. Babu wanka babu wanki. Kayan jikinta kamar tsummokara. Kumatunta sun yi shatin hawaye dabbara dabbara. Gabaɗayanta babu kyawun gani. Haka ta ƙaraso gabansu tana ɗingishi. Wanđanda su ka tarar a cell ɗinsu sun yi musu duka ita da Salwa.
Kamar haɗin baki. Babu wanda ya nuna damuwa akan ciwukanta. A gaban DPO ɗin dai Baba Maje ya ɗauko zancen Taj.
“Ki faɗa min gaskiya Ummi. Me ki ka yiwa mijin Hamdi har ya fara fuskantar irin waɗannan matsaloli daga komawa aiki?”
Allah Ya sani ta gaji da wajen nan don haka ba za ta wahalar da kanta wurin ɓoye ɓoye ba. Abin gudun ya riga ya faru. Kwana uku babu baccin kirki, ta fannin abinci ma sai addu’a. Wurin zagayawa kuwa tun tana amai har ta daina. Gashi don bala’i cikinta ya rasa lokacin lalacewa sai a nan. Bugu da ƙari ƴan cell ɗin nasu sun ɗora mata karan tsana. Daga ita har Salwa sun daku amma nata yafi yawa saboda ita ce mai ramawa da farko.
“Salwa ce ba ni ba.”
“Wace ce Salwa?”
Kofur ɗin ɗazu ya ce “ita ce aka kawo su nan tare. Ace ƴar mutum tana sakaye amma bai san ma ita da waye ba sannan babu waiwaye.”
Fuska a haɗe DPO ya kalle shi ya ce “Kofur Ɗanliti yaya haka ne? Me ma kake yi a nan?”
“Yallaɓai wasu iyayen ne sam ba sa gane illar barin ƴaƴansu mata a station.”
“Kai dai naka ƴaƴan suna gida ko?” DPO ya ce a harzuƙe.
“La shakka.”
“To jeka ka kawo Salwa ɗin ka kama gabanka.”
Wani sassanyan murmushi Kofur Ɗanliti ya yiwa Ummi da zai fita. Harda cewa ta kwantar da hankalinta. Yanzu gaskiya za ta yi halinta. Ƙila ma a yau ta sami damar tafiya.
Tsawar da DPO ya daka masa ce tasa shi gaggawar fita yana ƙananun surutai akan ƙulle mutane ba bisa haƙƙi ba. Ita kuwa Ummi wata muguwar harara ta galla masa da ya juya. Tun zuwansu yake ta rawar ƙafa a kanta. Matan da suka yi mata duka ma ya so basu horo irin yadda ake yiwa masu laifi saidai yana ganin shugabarsu ya fita yana Allah Ya isa. Matar regular ce kuma tantiriya. A tsaye ta fishi nesa ba kusa ba.
Ba a jima ba su ka shigo da Salwa. Ta tsaya musu ƙerere tana harararsu. Ta gane iyayen Hamdi ta kuma gane iyayen Ummi daga kamanninsu.
“Durƙusa” Kofur Ɗanladi ya ce da tsawa saboda haushinta da yake ji.
DPO kai ya girgiza kawai don ya ɗago shi ya ce Ummi ta maimaita abin da ta ce. Nan kuwa ta nuna sam bata san komai akan Taj ba. Salwa ke son shi kuma ita ce tayi masa asiri.
“Lallai ma. To a ina na samo turaren? Ba ke bace ki ka bani?” Salwa ta kalli DPO “Wallahi cewa tayi idan na shafa masa zai saki Hamdi ya aure ni.”
“To yanzu me ya haɗa ku faɗa?”
Salwa ta ce tayi amfani da turaren yadda aka ce amma Taj wulaƙanta ta ma yayi fiye da yadda yake yi a baya.
“Ummi har kin san bin bokaye kuma?” Iyaa ta fashe da kuka.
“Nima bani aka yi Iyaa. Don Allah ku tafi dani gida.”
Ba a wani sha wahala ba ta faɗi cewa Alh. Usaini ne ya bata. Kuma a zahiri ga abin da ya ce mata zai faru da Taj saɓanin yadda su ka faɗawa Salwa.
“Aikin ku nayi muku kenan? Kin san mutanen da na rabu dasu saboda tunanin zan sami Taj?” Salwa tayi kan Ummi cikin ɓacin rai.
Kofur Ɗanliti yayi saurin anjige ta kafin ta cakumi Ummi ta faɗi a ƙasa. Abba Habibu da Yaya sun ga ikon Allah. Bayan Ummi ta kwatanta inda za a sami Alh. Usaini. Ta tabbatar musu da cewa akwai chats ɗinsu harma da recording ɗin wayoyinsu a wayarta.
“Damma kin shiryawa rana irin wannan ne?”
“A’a, na dai kula idan muka gama chatting yana bin duka abin da ya turo ya goge. Shi yasa na soma yin screenshot saboda kada a gaba wani abu ya faru ya zame ya barni.”
“Allah ma Ya sa kina da wayonki. Irinsu haka su ke amfani da marasa wayo su cuce su.”
Ayyanawa Ummi tayi a ranta cewa indai Kofur Ɗanliti yayi gigin cewa yana sonta, za ta nuna masa rashin mutumcin da zai jima yana yi masa ciwo. Idan ba karambani ba ai shi ma daga gani ya san su ba sa’annin juna ba. Duka duka bai fi rabinta ba a faɗi. Tsayi kuwa ba zai wuceta ba.
Gida Abba Habibu ya buƙaci Yaya ta koma tunda kawo Alh. Usaini zai ɗauki lokaci. Babu musu ta tashi. Jikinta yayi matuƙar sanyi. Ka haifi đa ya zama silar zubar mutumcin mutum babu ruwansa da gazawar tarbiyya. Wani duk ƙoƙarin iyayensa sai ya janyo musu magana hankalinsa yake kwanciya.
Baba Maje ma ya ce Iyaa ta tafi ta nuna zama za ta yi. So take taji ƙarshen wannan abu da Ummi ta zama sakarya wajen jagosarsa.
Minti ashirin bayan tafiyar Yaya sannan aka zo da Alh. Usaini. Tun a waje yake ta bala’i da zage zage. Da yaga Ummi sai ya taɓe baki.
“Kina da shaidar nunawa kice da hannuna?” Ya kalli Salwa “ke kin sanni ne?”
“Kaga ka ajiye wannan surutun zai amfane ka a kotu.”in ji DPO
“Kotu??” Salwa da Ummi su ka maimaita cikin tashin hankali.
“Ƙwarai kuwa. Kafin lokacin muna buƙatar shi Taj ɗin a nan.”
Ranar har dare suna station dai. Taj da Hamdi su ka zo aka maimaita komai. Ya dubi Alh. Usaini ya ce masa da shi da su Salwa duk ya yafe musu ya juya ya fita. Fitarsu ke da wuya mahaifin Alh. Usaini ya je. Bayan ya gama zagi da ci masa mutumci a gaban mutane yace ba zai bashi shugabancin komai cikin kadarorinsa ba. Gado ma ba don Allah ne Yayi da Kansa ba tabbas da ya ce ba zai gaje shi ba. A ƙarshe ya fice. Su Baba Maje ma su ka kama gabansu. Abba Habibu ne ya karɓi Ummi albarkacin iyayenta. Salwa ma an saketa amma ko da ta fito ta rasa inda za ta tafi.
***
Da Hamdi ta shiga ɗaki a kwance ta sami Taj amma ya juya mata baya. A hankali ta lallaɓa ta hau gadon ta kwanta a bayansa. Hannunta ɗaya ta zura ta ƙarƙashin jikinsa, ɗayan kuma ta gaba ta haɗe su ta rungume shi.
“Kuka kake yi ne?”
“Tsokana ta ma kike yi?” Ya yi maganar ba tare da ya juyo ba.
“Ƙorafi dai na zo yi. Ta yaya zan aureka kuma ace safe, rana da dare duk ni ce a kitchen. Gaskiya da sake.”
Tashin da bai yi niyya ba yayi.
“Kin manta halin da nake ciki ko kuwa da gaske tsokanar ce?”
Hamdi ta ce “Ka faɗa min damuwarka ne? Ba da kaina na nemo amsar ba?”
“Da ki ka nemo ba ki ji tausayina ba?”
“Girkin ne ba za ka tayani ba kake tada zancen?” Ta kyaɓe fuska.
Taj ya riƙe baki da yaga da gaske idanunta suna neman zubo da ƙwalla “Abu ya same ni amma saboda ƙarfin hali ke ce da ɓata rai da shirin kuka?”
“Na fi ka shiga tashin hankali. Ka da aka mana aure hancin ka da baki duk suna aiki. Yanzu da haka ta faru sai anyi min cikon sadaki.” Tayi kicin kicin da fuska.
Taj bai san lokacin da ya soma dariya ba “cikon sadaki fa kika ce?”
Ta goge ƙwallar ƙarya “Eh mana. Na baka tausayi ko?”
“Haƙƙun.”
“Zan iya yafewa in za ka yarda ka fito daga ɗakin nan mu shiga kitchen.”
“Hamdi…”
“I’ll be your nose” ta tsaya akan gwiyoyinta akan gadon ta goga hancinta da nasa “and your tongue.” Ta rataya hannuwanta a wuyansa ta sumbace shi “I’ll be you har ka sami lafiya.”
Ƙanƙameta Taj yayi. Ta dage ta ƙi barin raunin zuciyarta ya bayyana balle tayi kukan da take ta dannewa.
“I love you.”
“Me too” ta faɗi har lokacin wuyanta na kafaɗarsa.
A ranar bata yarda sun sake komawa wannan zancen ba. Sai ma mitar da take yi wai ta rasa sunan da za ta dinga kiransa. Ya Taj ɗin da take jindaɗin faɗa shi taji Salwa na kiransa dashi. Yana dariya ya ce
“Ki kirani Malam kawai?”
Ita ma dariyar tayi ta ce “Happy ya ishe ni. “
***
Washegari Taj yaje gida ya faɗawa su Inna abin da ya faru. Da Salwa ta san illar baki da bata janyowa kanta abin da zai sa ta shiga bakin mutane ba. Hajiya bata yi ƙasa a gwiwa ba ta kira Alhaji ta faɗa masa. Hankalinsa ya sake tashi fiye da baya. Bayan sun gama jajantawa juna ya kira sauran matansa. Sun jima suna magana da Inna yana kwantar mata da hankali. Ya ce su dage da yin addu’a. Shi kuma zai san yadda yayi da Alh. Usaini. Yadda su ka ƙulla abin su za su kwance in sha Allah.
“Kun sa ranar dawowa ne?”
“A’a. Za mu yi magana daga baya.”
Ajiye wayar yayi yana ta juyayin abubuwa. Case ɗin Taj da Kamal ba ɗaya bane amma a ƙalla mahaifiyar Taj ta san abin da ya shafi ɗanta. Addu’arta tana kai masa. Hajiya fa? Ta ina zai fara? Duk da haka dole ta sani zuciyarsa ta faɗa masa.
Kamar haɗin baki a daren ranar Yaya Hajiyayye ta kira shi tana tambayar saura kwana nawa su dawo.
“Mene ne?”
“Alfarma zan roƙa ku ƙara lokaci. Nan da kwana shida zamu taho in sha Allah.”
“Ba na ce Taj ya bari Hamdiyya ta sami visa ba?”
Yaya Hajiyayye tayi dariya “ai ta samu. Surprise mu ka so yi muku. Yanzun nan nayi tunanin kada fa garin surprise mu yi saɓani.”
Farincikinsa ya nuna. Ya ajiye wayar sai yaji sanyi yana ratsa shi. Yaya zsi yi da matansa? Dama yana kusa ne da sauƙi.
Haka nan ya yi ta maza ya kira Hajiya. Tunda taji ya ce ta keɓe za su yi magana gabanta ya faɗi. Ya fara da wa’azi ds tunatarwa akan sharuɗan imani.
“Na yarda da ƙaddara. Ka faɗa min kawai me na rasa.” Ta ce da rawar murya.
“Baki rasa ba amma duk wani hope yana neman ƙare min.”
Jikinta taji yayi nauyi ta sami waje ta zauna. Duk yadda Alhaji ya so rage mata raɗaɗin da za ta ji ta hanyar amfani da kalmomi masu kwantar da hankali abu ya faskara. Kamal yana dab da rasa rayuwarsa saboda rashin dacen mai bashi ƙoda.
Yayi zaton za ta yi kuka sai yaji shiru. Can ta numfasa.
“Yaushe ne akwai jirgi kurkusa?”
“Zan bincika…”
“Ka duba ka biya mana. Innalillahi wa inna ilaihi raji’un.” Sai ta katse kiran.
Alhaji ya yi ta kiranta taƙi ɗauka. Mama ya nema yace su haɗu da su Inna yana da magana. Su ukun nan kuka suke yi babu mai rarrashin wani. Su ka shiga ɗakin Hajiya su ka sameta tana haɗa kaya.
“Ku ma ku gaggauta haɗawa domin ko gobe aka sami jirgi zamu tafi tare ko?”
Cikin kuka Umma ta ce “dolenmu Hajiya.” Inna da Mama kuwa ko bakin magana babu.
Basu bari yaran sun sani ba. A kwana uku aka gama yi musu komai. Yaran nasu suna ta mitar me yasa basu jira su tafi tare ba. Mama tayi ƙarfin halin cewa mijinsu ke nemansu. Aka mayar da abin shaƙiyanci ana dariya.
*
Tafiyarsu da kwana biyu shi ne lokacin tafiyar Yaya. A airport su ka haɗu da abokan tafiyarta. Su Hamdi su ka yi mata rakiya da mazajensu. Abin da ya bawa Taj mamaki da kuma tayar masa da hankali bai wuce ganin Dr. Mubina tana fitowa daga wajen check in ba. Ta rame sosai kamar wadda ta jima tana ciwo. Duk wasu alamun rashin kwanciyar hankali sun bayyana gareta. Da ta gan shi da farko gabanta ya faɗi kuma ya gani. Ta basar shi ma ya nuna bai gane komai ba. Hamdi ya kira su ka gaisa ya ce
“Ku fara ƙawance don da alama ita ce Mrs Happiness.”
Hamdi sai murna ta zolayeta
“Umra za ki ko Ya Kamal za ki bi?”
Dr. Mubina tayi murmushi kawai. Taj ya nuna mata Yaya ya ce ga ƙarin abokan tafiya ta samu tunda yaga kamar ita kaɗai ce.
“Na gode kuwa.”
Da aka kira su Hamdi da Taj na kallo Dr. Mubina ta haɗa akwatin ta da na Yaya tana ja. Sun ji daɗin hakan kuwa. A ƙofar jirgi inda ake nuna boarding pass Yaya za ta ɗauko nata ta haɗa da ƴar takardar da su Hamdi su ka gani wadda aka saka cikin passport ɗinta. Ita ce mai ɗauke da bayanin lalurarta da su blood group ko da wani abu na emergency zai sameta. Bata san ta yar ba tayi gaba. Mubina ce ta ɗauko mata. Tana shirin bata ta kula da bayanin da yake jiki. Zuciyarta sai da ta girgiza. Ta miƙa mata da rawar hannu.
MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
