Search
You have no alerts.

    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
    A cikin yanayin ciwo da gajiyar jiki Kamal ya buɗe idanu ya miƙa hannu zai ɗauki wayarsa. A gadon asibiti yake inda yake samun kulawa ta musamman. Da yake dokar asibitin ba a zaman jinya, shi kaɗai ne a ɗakin. Alhaji da su Ahmad suna hotel kusa da asibitin. Tafiyar just ƙafa ke kawo su. Tare dashi su ke wuni sai takwas na dare idan an buƙaci duka baƙi da masu ziyara su fita sannan su ke tafiya. Kwanaki goma aka bashi ya gama shan magani da allurai kafin a fara dialysis.

    “Happy lafiya dai ko?” Ya ce cikin bacci da firgici domin kuwa ukun dare harda kwata lokacin.

    Kamar an tsunkuli Taj ya ɗaga kai ya kalli kyakkyawan agogon bangon falon. Baki ya buɗe gami da girgiza kai.

    “Don Allah Happiness kayi haƙuri. Kasan Allah ban duba time ba. Ashe past one. A nan uku ta wuce ko?”

    Kamal ya gyara zama ya ce “Eh…mene ne ya faru? Haka kawai ba za ka manta lokaci ba.”

    “Gobe sai muyi magana in sha Allah. Am very sorry.” Taj ya ce har zuciyarsa.

    “Taj” Kamal ya kira shi da ɗan ƙarfi “me ya faru?”

    Roƙonsa Taj ya fara yi akan ya jira safiya don har ya katse kiran amma ya sake kiransa. Su ka ɗan yi ja’inja ɗinsu sannan Taj ya faɗa masa abin da yake faruwa dashi game da ɗaukewar ɗanɗano da jin ƙamshi ko wari wasu lokutan.

    “Zuciyata tana bani Covid ce. Nayi browsing naga ɗaukewar sense of smell da taste suna cikin symptoms ɗinta. Ni bana mura amma bayan magrib ina ƙirgawa sau bakwai Hamdi tayi atishawa.”

    Kamal yayi ƴar dariya “sannu Doctor.”

    Taj ya ɓata rai “Happiness its not funny.”

    “Na sani. Shi yasa nake mamaki da kana zaune a gida ka yankewa kanka cutar dake damunka.”

    Murmushi ne ya kama shi. Tabbas asibiti ya kamata yaje amma fargaba ta hana. Ba kuma kansa yake jiyewa tsoro ba. Idan ta tabbata yana da corona shikenan Hamdi ma ta samu. Daga tarewa ya haɗata da ciwo.

    “Gobe zan je in sha Allah. Thank you and sorry.”

    Sai da safe suka yiwa juna. Kamal ya ce yana jiran jin sakamakon idan ya dawo daga asibitin. Da ya koma ɗakin a dunƙule waje guda ya sami Hamdi. Ta dawo tsakiyar gadon tana baccinta hankali kwance. Sama ya kalla ya sake yin addu’ar da ya wuni yana yi. Allah Yasa ba covid bace. Idan kuma ita ce yana fatan Hamdi bata samu ba. Sai dai abin da kamar wuya. Yadda su ke manne da juna ana amarci ai taimakon Allah ne kawai zai hanata kamuwa. Kwanciya yayi a can gefe. Ko minti biyu bai yi ba yaji Hamdi a jikinsa ta ɗora rabin kanta a ƙirjinsa. Wani ɗan murmushi yayi ya sake shige mata har yayi bacci.

    ***

    Yawan kallon wayar da Kamal yake yi ne yasa Alhaji tambayarsa kira ko saƙon wa yake jira. Shi kuwa ya faɗa masa yadda suka yi da Taj a waya.

    “Result ɗin nake dubawa ko ya turo.”

    Shiru Alhaji yayi na wani lokaci yana tunani kafin daga bisani yace idan ya faɗa masa yana son ji shi ma. Zuwa la’asar kuwa bayan Taj ya turo ya faɗawa Alhajin cewa ba corona bace.

    “To Alhamdulillah. Ince dai bai hanaka faɗawa kowa ba? Zan kira shi nayi masa ya jiki.”
    Da jindaɗi Kamal ya ce Taj bai hana ba.

    Alhaji bai tashi kiran Taj ba sai bayan sun koma masaukinsu ya shiga ɗakinsa. Bayanin yadda yake ji ya buƙaci ya yi masa.

    “An baka magani?”

    “Eh Alhaji. Sun ce stress ne kawai”

    “To Allah Ya ƙara lafiya. Ciwon da ya shafi harshe da hanci a wajenka ba abin ɗauka da wasa bane duba da irin sana’arka. Ka mayar da hankali wajen shan magani.”

    Taj ya yi godiya yana cike da murnar wannan kulawa ta Alhaji.

    *
    Wando ne tight ruwan zuma a jikin Hamdi. Jikinsa yana da wani irin laushi ga rashin nauyi. Ta ɗora shirt ɗin Taj baƙa mai maɓallai a gaba da dogon hannu. Maɓallan gaban guda huɗu ne kaɗai a ɓalle ta bar na farkon. Hannuwan kuwa tsayawa tayi naɗe su har dantsen hannu. Ga gashinta da bata taje ba ta tattara tayi packing bai shige sosai ba. Fuskarta ko ɗigon kwalliya babu. Sai ƙamshi kamar a ɗauketa a gudu don daɗinsa.

    Duka wannan saurin shirin saboda sun gama sati yau za ta fara shiga kitchen ne. Ta kwana tana tsara me za ta dafa saboda baƙin da zasu yi daga gidansu Taj. Shi kuma kawai yana tashi ya ce ta faɗa masa me take son dafawa.

    “Ki kwanta ki huta in dafa.”

    “Ka dafa?” Ta juya tana kallonsa “ni ce fa amaryar.”

    “Ni kuma angon amarya ba.”

    “Girkin nawa ne baka son ci ko baka yarda dashi ba?”

    “Taimako ne fa kawai. Besides na gaji da zaman nan. I miss my kitchen.”

    Wata uwar harara ya samu wadda ta sanya shi tuntsirewa da dariya.

    “Me kuma nayi? To ki bar min aikin duka idan rabawa ne ba kya so mu yi.”

    “Yanzu don Allah baka san kowacce amarya jiran wannan ranar take yi ba? Ranar da za ta fara yiwa mijinta girki. Sai kawai kace in bar maka kayi?”

    “Nayi zaton murna za ki yi fa. Ki ce yau ga ranar auren Taj” ya ɗage gira.

    “Ni kuma to da me zan burgeka? Girki a wajen mace ni dai a wajena abin alfahari ne.” Hamdi ta ce idanunta a kan shi.

    Hannunta ya kama su ka shiga kitchen ɗin.

    “Ke ce sarauniya a nan. Ni kuma bafade mai neman suna a wajen uwarɗakinsa.”

    Murmushi Hamdi tayi. Ta buɗe store Taj yana kallonta shi ma yana murmushi.

    Juyawa tayi ta kalle shi “kada in yi shinkafa da miya ko? Its too common.”

    “Dafa shinkafar ki bar min miyar. Sai in yi chicken curry maimakon stew da potato salad.”

    Abin da take ta gudu da alama dai shi zai faru a gidan nan nasu. Girke girken ƙwalisar da ta koyo a wajen Abbanta ƙarshenta duk ba za su burge shi ba.

    “Na fasa ma. Kullum shinkafa ake ci. Naga akwai macaroni shape daban daban…”

    Don tsokana kawai Taj ya ce “ni yanzu ba abin in ce miki pasta ake cewa ba ki ji haushi. Macaroni is just a type of pasta.”

    Hamdi ta sha kunu shi kuwa ya ɓoye dariyarsa.

    “Ka gama faɗa ai, wato ko fashewa zan yi babu ruwanka?”

    Laɓɓansa ya ɓame gami da alamar yiwa bakinsa zip. Ita kuma da yake tana son yin shawara dashi don kada tayi gaban kanta sai ta sake yi masa tambaya.

    “In dafa ita pasta đin?”

    Allah Ya sani ya ma manta, bai san lokacin da ya ce “Ki zauna in yi musu creamy chicken pasta kawai.”

    “Na fasa.”

    Rarrashinta ya kama yi “dafa abin ki, ba zan saka miki hannu ba.”

    “Naƙi wayon. Ban ma iya ba.”

    Fushin nata da ture turen baki dariya su ke bashi. Ya dai bata haƙuri ya ce kuma ba zai kuma magana ba.

    “Tuwon shinkafa ma zan yi.” Ta faɗi da murna don tana tunanin baya cikin abin da ya ƙware.

    Store ɗin ta shiga da wuƙarta a hannu za ta buɗe buhun shinkafar tuwo. Shiru Taj bai ce komai ba har ta soma farke buhun sai ta ɗaga kai ta kalle shi.

    “Don Allah baka iya tuwo ba ai ko?”

    “Uhmm” ya faɗi yana rufe baki.

    Ga mamakinsa kawai sai Hamdi ta ajiye wuƙar a kan buhun ta fito ta zauna akan wata kujerar kitchen a gefen sink mai ɗan tsayi ta kama kukan shagwaɓa.

    “Ban iya tuwo ba. Don Allah ki yi shiru. Da gaske ban iya ba.” Taj ya ce a rikice.

    Da dai ta san ta kunna shi da kukan sai taƙi dainawa. Yana lallaɓata tana mita.

    “To ni da me zan burgeka? Me yasa ka iya komai? Mene ne baka iya ba?”

    “Ban iya ɗan wake ba” ya faɗi da sauri don ta daina kukan.

    “Ahaaa…ashe ka iya tuwon” tayi maganar tana jinjina kai.

    Sai lokacin ya fahimci me tayi. Dole ace mata daban suke. Ƴar ƙaramar yarinya tayi masa wayo.

    “Ai ba sosai na iya ba. Ɗaki ma zan tafi har ki gama.” Ya saketa zai fita.

    Hannunsa ta kamo ya tsaya suna kallon juna.

    “Allah so nake na dafa maka abin da baka iya ba. Wanda in kaci za ka yaba min da zuciya ɗaya.”

    “Come on Love, ko me ki ka dafa kin san zan yaba.” Ya rungumeta yana shafa mata kai.

    “Honest review nake so. Ka yaba har zuciyarka ba don naji daɗi ba kawai.”

    “To shikenan. Maganar gaskiya na iya tuwo amma ban fiye yi ba.”

    “Da gaske don Allah.”

    “Da gaske.”

    Da murnarta ta nuna masa ƙofa “To ka tafi falo ko ɗaki ka huta.”

    “Ranki ya daɗe duba fridge ɗinki dai ki tabbatar babu abin da ki ke buƙata.”

    Da wani rangaji duk na jindaɗin cewa bai iya tuwo ba sosai ta tafi ta buɗe freezer. Nama kala-kala akwai. Ga kayan miya da aka wanke aka ɗaɗɗaura a ledoji. Ɗaurayewa kawai zata yi tayi blending.

    “To idan babu takura don Allah ina da saƙo.”

    “Yes Ma. Me kike so?” Ya tashi yana sauraronta.

    Ganyen ugu da alayyahu ta buƙata daidai yadda take jin zai isheta yiwa mutum biyar da za su zo da kuma su na gidan abinci.

    Bayan fitar Taj a bincikenta na store taga kwali na kayan annurfoods. Ta buɗe ta ɗauko garin tsaftatacciyar niƙaƙƙiyar farar shinkafa. Ta fito ta ɗora ruwan tuwo sannan a wata tukunyar ta ɗora nama. A ruwan tafasar bayan ta saka maggi da gishiri, sai ta sanya paste ɗin citta da tafarnuwa. Ta kawo mixed spices, da garin lawashi duka na Mrs Ghalee TK ta zuba. Ya kusa dahuwa ta zuba yankakkiyar ganda ƙanana da aka zuzzuba a zip lock aka ajiye mata. Sannan ta kawo albasa ta yanka da girma ta zuba. A gefe kuma ta tafasa kifi sama-sama a wata tukunyar ta ciccire ƙayar ba tare da ta fasa tsokar sosai ba. Tana yi tana azkar cikin kwanciyar hankali.

    Tana tuƙin tuwo Taj ya dawo. Tayi masa sannu da zuwa ya sami wuri ya zauna.

    “Kada ki koreni please.”

    “To kada ka taɓa komai.”

    “No problem.”

    “Kuma kada kayi magana”

    Alamar yiwa baki zip yayi. Ya zauna yana kallon yadda take komai cikin ƙwarewa da kazar kazar. Duk motsinta burge shi kawai yake yi. Ta dami kanta akan iya girkinsa da tsoron kada ta gaza ta wannan fannin a idonsa. Bata san shi kuma cikar buri yake gani ba a tare da ita. Samun matar da ko bata iya girki ba za ta ƙoƙarta tayi masa a matsayinsa na mijinta ba ƙwararren mai sana’ar girki ba. Shi ma yaji shi isasshen namiji a cikin gidansa.

    A flask mai kyau ta jera tuwon da ta ƙulle a farar leda. Taj ya ɗaga hannu tamkar a aji. Hamdi ta yi murmushi. Dama ta san ba shirun zai yi ba.

    “Ina jin ka.”

    “Tuwon mene ne wannan don Allah?”

    Ta faɗa masa. Yace bai san ana yi ba. Sai ya kuma wata tambayar. Yana so ta faɗa masa miyar me za ta yi.

    “Miyar ganye.”

    Bai ƙara magana ba sai da yaga ta gama yanka ganyen daban daban ta wankesu da kyau sannan kowanne ta ɗora a tukunya daban da ruwa kaɗan. Za ta kunna wutar taga alamun zai yi magana sai ta dawo gabansa ta tsaya ta duƙar da kanta. Yayi zaton magana za ta yi. Sai ta shammace shi tayi kissing ɗinsa.

    “Na rufe maka bakin nan. Don Allah kayi shiru. I want to surprise you.”

    “Surprise ya wuce wannan?” Ya taɓa bakinsa “ai kawai ki kashe wutar ki zo in baki tukwici.”

    Guje guje su ka gama har falo tana zille masa. Da ta gaji ta jingina da bango ta dafe ƙirji tana mayar da numfashi.

    “Don Allah ka barni haka.”

    “Kin san me?” Ya faɗi yana zama “wallahi na fi ki gajiya.”

    Dariya suka yi sannan ya barta ta koma bakin aikinta. Kowanne ganye ta kunna shi ya soma tafasa kaɗan sai ta kashe ta tsane ruwansa tas. Ta haka ne miyar ba za ta yi ruwa ba yadda take so. Sannan kalar za ta fi kyau. Manja ta zuba a tukunya ta kawo garin daddawarta na annurfoods ta zuba a ciki. Ta zuba tumatir, albasa da attaruhu da tayi blending sama-sama. Ya fara suyowa ta ƙara da wata albasar da ta yayyanka mai ɗan dama. Ita ma tana yi mata daidai ta juye ruwan naman nan a kai ta ɗanɗana. Abin da bai ji ba ta ƙara ta bari ya haɗe jikinsa sannan ta fara zuba ganyen ugu da shuwaka ƴar kaɗan wadda Yaya da kanta ta wanke masu a gida ta busar. Jiķata kawai tayi da ruwan zafi ta taso. Ƙamshin girkin har falo. Ta zuba alayyahun da ugun yayi yadda take so sannan ta ƙara da kifin da ta riga ta gyara. Ta zuba garin crayfish ta rufe tukunya. Bayan minti biyar ta kashe ta saɓa murfin tukunyar.

    “Zuba min nawa yanzu.” Firgigit ta juya don bata ji shigowarsa ba.

    “Ka bari su iso mana tunda sun ce a nan za su yi azahar.”

    “Ko ki bani ta laluma ko in miki ɓarna a tukunya.”

    Hannunsa ta ja har bakin tukunyar ta ce ya ɗanɗana miyar. Ya zuba a plate ya ɗeɓi zallar miyar da bata yi ruwa ba ga kyau a ido ya ci.

    “Mrs Happy…”

    “Yes” Hamdi ta amsa da ɗoki.

    “Kin sami 100/100”

    Mamaki ta kuma bashi da ta kama rawa tana juya ƙugu. Ya kuwa dangwarar da plate ɗin ya kwasheta. Abincin da basu ci ba kenan sai da baƙinsu su ka zo. Suma kuwa su ka yi ta santin girkin amarya.

    ***

    Jiki na rawa Yaya ta kira Inna Luba a waya tana kuka. Innarta ta tada hankali tana ta tambayarta me ya faru.

    “Ke kaɗai Allah Ya bani Jinjin. Idan kika ɓoye min damuwarki waye zai faɗa min tasa? Ko ba kya son addu’ata?”

    Mijinta da kishiyarta suna tsakar gidan take wannan wayar. Su ka tsayar da hirar da suke wadda har yau basu sakata a sabgarsu suna sauraronta.

    “Hmmm, ƙarshenta ɗan daudun mijinta ko ƴaƴanta ne wani ya kwaso abin kunya.” Cewar kishiyar Inna Sarai.

    “Ko kuma ta cangala ƙafarta a inda bai kamata ba” Malam ya faɗi yana zungura baki irin shi dai babu ruwansa ɗinnan.

    Inna Luba ko ta kansu bata bi ba ta cigaba da cewa Yaya ta faɗa mata me ya faru. To dama Abba Habibu yana gefe yana dariya. Da yaji kukanta yaƙi yankewa bayan ta kira wayar shi ne ya karɓe wayar.

    “Inna kada ta tayar miki da hankali. Makka za ta je shi ne take kukan murna.”

    “Allahu Akbar kabiran” Inna Luba ta faɗi da dariyarta “Habibu wa ya biya mata?”

    “Ni ne Inna” Abba ya bata amsa yana murmushi.

    Yaya sai ta karɓe wayar “Inna ashe yana ta tarin kuɗi ban sani ba. Yaje domin ya biya mana kuɗin sun ƙaru akan yadds ya sani. Shi ne ya ce shi ya taɓa yi ni na tafi. Inna tarinsa na tsayin lokaci amma ya zaɓi ya tura miskiniyar matarsa akan yaje” ta sake fashewa da kuka.

    Inna Luba ma sai da tayi kuka. Ta dinga yiwa yayarta da mijinta Mal. Umaru addu’a. Sun ƙaunaceta, sun ƙaunaci gudan jininta. Yau gashi da ranta da lafiyarta take jin Jinjin za ta keta hazo taje ƙasa mai tsarki.

    Da ta gama wayar Malam dawowa yayi gabanta ya tsaya.

    “Naji kina zancen zuwa Saudiyya. Waye zai je?”

    “Yarinyar nan ce mijinta ya biya mata.” Ta bashi amsa tana miƙewa tsaye.

    “Wai Jinjin ɗin ko guda cikin ƴaƴanta?” Malam ya kasa ɓoye son abin duniyar da ya taso masa haiƙan. Idan ƴar cikinsa taje Makka tabbas ya sami abin cika baki da fankama cikin abokansa a ƙauyen. Bugu da ƙari yadda bata da rowa yasa rai da jallabiya, ɗan madina da tashi-ka-fiye-naci. Ƴar bagaruwan nan a gaban su Mal. Ya’u zai dinga ɓantara yana korawa da zamzam.

    Zuciyarsa ta luluƙa birnin tunani da yaji ita ce dai mai zuwa, Inna Sarai ta katse masa daddaɗan mafarkinsa.

    “Daga ji an fara biye biye kenan. Dama naji labarin auren jari aka yiwa yaran nata. Shi ne za ku fara kai mazajen ana mallakesu. To dai a dinga jin tsoron Allah.”

    Inna Luba ta dubeta da kallon baki ishe ni kallo ba ta kawar da kai.

    “An faɗa miki kowa irinku ne? Da mallakar namiji tana gabana ke kin isa Malam ya kalle ki? Ku da malaman tsibbu ku ka dogara. Ni kuwa kin san gidan Qur’ani da hadisi na fito. Har yanzu akwai irin ɗaliban babana da ko ƙwandala ba zan bayar ba za su ban mijin naki a tafin hannu.”

    “Ai wallahi ƙaryarki. Malam nan gani nan bari daga ke har musakar ƴarki.”

    Lokaci guda ga mamakin matan nasa ya daka tsawa.

    “Ba na son sakarci Sarai. Duk abin da za ku yi na kishi a daina haɗawa da ƴata.”

    “Jinjin ɗin? Mai shan inna” cewar Inna Sarai don tana ganin kamar bai gane ba.

    “Shan inna kika ce ai ko? Kowa ya san lalura ce ba ita ta ɗorawa kanta ba.”

    Wannan furucin nasa ya sanya duka matan kallonsa da mamakin da yafi na farko. Shin mafarki suke yi ko gaske ne. Inna Sarai haɓa ta riƙe daga baya ta koma tafa hannuwa. Inna Luba kuwa ƙare masa kallo tayi ta kama hanya ta wuce ɗaki. Tana jiyo shewar Inna Sarai tana kiran Malam mai kwaɗayi.

    ***

    Kamar kullum Ahmad yau ma da ya kira Zahra sai da ya nemi Salwa. Baya kiran wayarta saboda ya san yanzu yi masa ƙaryar taja gida ba zai bata wahala ba.

    Ta gaishe shi da ladabin kura ta saurari jawabinsa. Wai ya samo asibiti sun gama komai za a kwantar da Mami.

    “Ke za ki zauna da ita. Akwai wani yaron office ɗinmu da nayi making arrangement dashi akan kawo muku abinci idan Zahra ta gama”

    “To Yaya. Allah Ya dawo daku lafiya.”

    Babu wata ƙofa da Salwa ta bari a buɗe wadda Ahmad zai yi zargin wani abu. Zahra ma da su ke gida ɗaya bata ga komai ba. Duka su biyun har suna addu’ar Allah Yasa shiriya ce ta zo. Ta dawo hayyacinta. Salwan da su ka sani ce a gabansu.

    Ashe kwantan ɓauna tayi musu. A ranar da yamma su ka koma asibiti ita da Mami. Bayan tafiyar Zahra rufe ƙofa tayi tayi juyin murna son rai. A nan dai Ahmad bai isa ya ce ta bawa Mami su yi magana don ya tabbatar tana asibiti. Dama ce ta samu da za ta bi kadin aikin da tayi don ayi a wuce wajen.

    Bari tayi sai wuraren shabiyun rana washegari ta silla wanka ta ci ado tamkar a gidan biki take ba asibiti ba. Tayi nan tayi can tana ta shiri, Mami na aikin binta da ido. Sarai Salwa ta san tuhuma ce take mata da irin kallon da take binta dashi. Ita kuwa yanzu wannan kallon ya bar yi mata kwarjini. Mamin kanta ta jima da rasa martabarta ta uwa daga ranar da ta buɗewa Salwa sirrinta na biye biyen malaman tsibbu. Gajiya tayi da kallon da ake mata ta dubi Mamin tana mai taɓe baki.

    “Naga kina ta kallona. Unguwa zanje. Ga nurses nan za su kula dake kafin na dawo.”

    Mami ta girgiza kai. Tana takaicin yadda ta koma babu magana kuma babu damar yi da gaɓɓai. Da ƙyar ta iya girgiza kai ta kafe Salwa da ido da kallon gargaɗi. Ita kuwa tayi mirsisi tamkar bata san me Mamin take nufi ba.

    Su kansu ma’aikatan asibitin sun yi mamaki sosai da ta fito zata tafi. Wata mai shara ta kasa ɓoyewa har sai da ta magantu da Salwan ta ce su dinga leƙa daƙin kafin ta dawo.

    “Baiwar Allah wace irin unguwa ce wannan da ba za ki iya jiran wani a ƴan uwa ya canjeki ba sai ki tafi?”

    “Au…” Salwa ta faɗi cikin murmushi sannan ta buɗe jakarta ta fito da wallet. Dubu biyar ta miƙawa ta kusa da wadda tayi maganar “gashi ku raba da duk wadda ta tayaki dubata. Ba wani jimawa zan yi ba.”

    Suna ji suna gani ta fita abinta. Wadda aka bawa kuɗin kamar ta karɓi wuta sai sannan tunaninta ya dawo. Zubar da kuɗin tayi ba shiri domin ta san dokar asibitinsu. Zuwa duba mara lafiya indai ba shara ce ta kaisu ba ba huruminsu ba. Sauran ma kowacce neman zillewa tayi. Sai a ƙarshe su ka yanke shawarar kai kuɗin wurin wata babbar metiron kafin ya janyo musu matsala. Ai kuwa tayi ta fađa da su ka je.

    “Mahaifiya babu lafiya ai ko jarabawa ce da ita ta haƙura tunda babu kowa.”

    Su dai sub-staff ɗin babu wadda ta sake magana. Suna kallo ta tashi da kuɗin a hannu ta tafi ofishin daraktan asibitin. Shi tashi yayi yaje yaga halin da Mami take ciki. Tayi fitsari har ya gangaro kan kafet. Idanun jajir tasha kukan baƙinciki. Ƴar cikinta ce ta banzatar da ita saboda nata muradin kamar yadda ta dinga yiwa nata ƴan uwan. Barewa ba tayi gudu ɗanta yayi rarrafe ba. Ko ma mene ne laifinta ne!

    Darakta ya bincika yaji likitan da yake kula da case ɗinta wanda aka haɗa da Ahmad ta waya har su ka yi magana kafin a kwantar dasu.

    A matsayin wurin na asibiti, fitsarin ba shi bane damuwarsu kamar fitar Salwa wadda ita ya dace ta neme su idan wani abu ya faru. Bai ɓata lokaci ba kuwa ya kira numbar Ahmad ta Saudiyya wadda su ke magana.

    “Laifi ne babba wani daga waje ya biya ma’aikatanmu su yi masa personal aiki kuma a cikin asibitin. In asibitin ne bai yi muku ba kuna iya ɗauke patient ɗin. Amma ba za mu yarda da negligence daga gareku ba tunda patient ɗinku mai buƙatar kulawa ce 24/7 sannan daga baya azo ana kuka damu.”

    Ran Ahmad yayi matuƙar ɓaci. Ya bawa likitan haƙuri da alƙawarin za a gyara. Wayar Salwa ya shiga nema ba ji ba gani.

    Lokacin bata jima da sauka daga adaidaita sahu a bakin gate ɗin gidan Taj ba. Ta fiddo wayar taga sunan mai kiran sai kawai ta mayar cikin jaka ta buga gate ɗin. Zuciyarta wani irin zillo tayi da maigadi ya buɗe mata ta shiga bayan ta tabbatar masa da cewa ita ƙanwar maigidan ce.

    “Allah Sarki. Gaskiya kuna da yawa Masha Allah. Jiya wasu sun zo. Yau ma kinga mota can…” ya nuna mata motar gidan Yaya Hajiyayye “ta ƴan uwanku da su ka riga ki isowa.”

    Wani abu Salwa taji a ranta. Kamar ta juya ta koma. Sai ta tuna da aikin da aka tabbatar mata da zai kama shi. Ta saki murmushi. A gaban ƴan uwansa shi ne wuri mafi dacewa da ya kamata ya nuna soyayyarsa gareta. Da wannan tunanin ta shiga gidan gaba gaɗi.
    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    Note
    error: Content is protected !!