Search
You have no alerts.

    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    Saɓanin baƙin jiya da bata gama sabawa dasu ba, yau da yake Yaya Hajiyye da Firdaus ta zo sai Hamdi tayi saurin sakewa. Ga albishir ɗin tafiyar Yaya da ya sake faranta mata rai. Kitchen su ka shige da Firdaus suna ƙusƙus. A falo kuma Taj ne da Yaya Hajiyayye su ke tasu hirar.

    “Wai ka san Kubra tare su ka tafi da Alhaji? Ko ni kaɗai ce ban san da tafiyar ba?”

    “Bana son jin kowa na faɗin bai sani ba. Sai nayi ta wasu irin tunani.” Taj ya faɗa da damuwa a tare da shi “kamar wani abu ake ɓoyewa.”

    “Kai ka san Alhaji bashi da wannan. To ma me zai ɓoye? Kawai maybe taji maganar ne ta ce ita ma zata sai ya barta.”

    “Amma ta kasa faɗa a Home group?”

    Waya Yaya Hajiyayye ta ɗauko ta dubi Taj “zan yi sanarwa yanzu. Duk mai ƴan matsabbai da lokaci da kuma niyya ta shirya sayen ticket mu bi su.”

    “Ayi min alfarma. Jiya na kai Hamdi anyi passport. A jira ya fito a sami visa.”

    “Gaskiya za a iya jimawa. Mu tafi za ku taho?” Ta ce don akwaita da wutar ciki. Bata son ɓata lokaci idan aka ce za ayi abu.

    Taj ya bata amsa da cewa “Alfarma na nema” yana sa ran komai zai samu da wuri in sha Allahu.

    Basu gama hirar ba Salwa ta ƙwanƙwasa ƙofa. Taj ya tashi zai buɗe sai ga Firdaus ta fito daga kitchen. Maimakon ya koma wajen zamansa sai yayi kitchen.

    Ita kuwa Firdaus hannun ƙofar ta kama da murnarta tana cewa “Ko ƴan gidanmu ne?”

    Wani irin kallo na rashin fahimta ta yiwa Salwa da ta gani a tsaye taci kwalliya irin wadda bata taɓa ganinta da ita ba.

    “Anti Salwa ke kaɗai? Ina Anti Zahra da su Hayat?”

    “Ni kaɗai ce. Ya Taj yana nan?”

    “Eh, shigo ciki.”

    Ƙamshin turarukan da Salwa ta yiwa fesawar Allah tsine saboda yawa ya doki hancin Yaya Hajiyayye da Taj. Ta dinga taku ta shigo ciki da kwarkwasa. Ta kuma rasa inda za ta zauna sai kusa da Taj dake zaune akam two-sitter. Shi da yayarsa tsayuwa ganin ikon Allah da tana nufo shi suka yi. Shi yasa babu wanda ya iya dakatar da ita.

    “Ya Taj ina wuni?” Tayi magana da wata zuƙaƙƙiyar murya.

    “Lafiya ƙalau.”

    “Ka ganni sai yau ko?”

    Tashi ya yi tsaye da yaji me ta ce ya ce “mun yi dake za ki zo ne?”

    Ko a jikinta ta sake kashe murya ta ce “Noooo, I thought you want to see me. Miss me?”

    “Ba sai kin canja harshe ba Salwa, gidanmu babu wanda bai yi karatu ba.” Yaya Hajiyayye ta ce tana jifan Taj da wata muguwar harara “akwai wani abu a tsakaninku ne?”

    Duk da ya gane tambayar domin abin da Salwa take yi da kalamanta kowa zai harbo jirginta da wuri.
    “Me ki ka gani?”

    “Me ta zo yi gidanka a haka?” Yaya Hajiyayye ta nuna ta sama da ƙasa.

    Danne ɓacin ranta tayi ta ɗauke kai ta dubi Taj.

    “Ya Taj a ina za mu yi magana?”

    Gajiya da sauraronsu Hamdi tayi ta baro ƙofar kitchen ɗin inda take tsaye ita da Firdaus tun bayan ta faɗa mata baƙuwar da aka yi.

    “Ga hanyar ɗakinsa can ku je can ku yi.”

    “Ba laifi, gara na san yadda yake tun yanzu kafin na dawo cikinsa.” Ko shakka bata ji ba ta bada wannan amsar tana murmushin cin nasara.

    Zuciyar Hamdi kamar ta fashe ta juya za ta bar wajen Taj ya damƙo hannunta. Ta ja za ta fizge ya janyota gabaɗaya jikinsa yayi mata wata irin kyakkyawar runguma a gabansu. Ta kuwa fashe da kukan da Anti Labiba ta faɗa mata a gida ana yiwa miji. Da gatanki da tarin soyayya a zuciyarsa ake yinsa don kawai an isa. Kissa adon mata! Da aka faɗa tayi zaton shegantaka ce za ta sa mace kuka babu duka ba zagi daga miji. Ashe ba haka bane. Shi ma kukan yana sanin lokacin zuwansa yayi.

    Tayi nasara fiye da tunani. Taj ya shiga tashin hankali sosai. Bayanta kawai yake shafawa yana faɗa mata kalaman kwantar da hankali.

    Wannan abu ya tayar da hankalin Salwa fiye da ƙima. Me yake faruwa ne? Ya dace zuwa yanzu hankalin Taj ya koma gareta. Ko zuwan nan, tayi ne don son ganin rigimar da take sa ran sun fara.

    “Ya Taj…” shiru bai waigo ba, yadda ka san Hamdi ce kaɗai a duniya. Ƙirjinta ya kama hawa da sauka cikin kiɗima ta ce “magana nake fa.”

    “Kana ji tana kiranka. Ni gidanmu zani. Da na sani ban…” Hamdi ta soma faɗi cikin kuka.

    Yaya Hajiyayye ta hanata ƙarasawa da cewa “Hamdiyya ki yi haƙuri kinji ko. Taj ya ci albarkacina kada ki yarda ki ɗaga masa hankali akan Salwa. Ƴa na ɗauke ki ba matar ƙani ba. In har na isa to don Allah ki barni da ita.”

    Hamdi ta ɗaga kai ta ture Taj da ta farga da yadda su ke ta ce “Kin isa Yaya. Wallahi kin isa.”

    “Salwa baki da lafiya ne ko me? Haka kike dama ko kuwa wani abu ne ya same ki?” Yaya Hajiyayye tayi tambayar tana kallon ta.

    Kasa magana tayi. Idanunta na bin Hamdi da kallon tsana. At the same time tana jifan Taj da nasa salon kallon na bege. Ta kasa gane ya aka haihu a ragaya. Yardar da tayi da aikin yasa bata kawo haka zai iya faruwa ba. A karo na uku dai ta sake gwada sa’arta ta gani ko akwai dama.

    “Ka bani minti biyar mu yi magana Ya Taj. Wurinka na zo don Allah.”

    Haɓa Yaya Hajiyayye ta kama tsabar mamakin wannan ƙarfin hali. Muryarta a kausashe kuwa ta ce,

    “Wuce ciki da matarka yanzun nan.” Ta dubi Firdaus “koma kitchen ki kula da girkin.” Sannan ta dawo da dubanta ga Salwa “ke kuma kama gabanki yanzun nan kafin in gwada miki ni wace ce.”

    “Allah na tuba sani kuma na nawa zan yi miki Yaya Hajiyayye? Kishiya ta hanaki zama a gidanki na farko. Alhajinku ya ƙaƙaba wa yaronsa ke aka haifi waɗannan” Salwa ta nuna Firdaus tana yatsina fuska.

    Wani kukan kura Firdaus tayi, tayi kan Salwa. Kafin ta kai mata duka Hamdi ta riƙeta da iya ƙarfinta. Firdaus na ƙoƙarin ƙwacewa Taj ya ɗaga hannu zai kai mata mari shi ma Yaya Hajiyayye ta riƙe nasa hannun.

    “Jinin Alh. Hayatu da dukan mace? Allah Ya kiyaye.”

    Maganarta ta farko yaji ta jan hannun Hamdi domin su bar falon. Zamansa tabbas zai janyowa gidansu abin faɗa. Da Firdaus ya haɗa su ka shiga ɗakin Hamdi ya ce su zauna shi kuma ya sake fitowa. Daidai lokacin Yaya Hajiyayye tana yiwa Salwa magana.

    “Ki tafi gida Salwa. Wannan abin da kike yi ba zai taɓa baki abin da ki ke nema a mutumce ba.”

    Taj gaban Salwa ya ƙarasa ya tsaya fuskarsa a murtuke
    “Salwa na taɓa cewa ina son ki?”

    Shiru tayi. Zuciyarta cike taf da uwar kunya sai dai son zuciya ya riga yaci ƙarfinta. Sunanta kawai da ya kira sau da ya saukar mata da kasala da ƙarin son sa.

    “Tunda baki da amsa to ina roƙonki this should realy be the last time. Ina raga miki ne kawai saboda Yaya Ahmad.”

    ‘Ko dai shafa masa turaren zan yi in kuma yi masa magana a lokacin?’ Salwa ta raya a ranta. Wanda yake hannunta da ta shafa a bakin ƙofar falon ta duba ta hanyar mitstsika yatsunta. Tana ɗaga hannuwa ita kuma Yaya Hajiyayye tayi tunanin rungumarsa za ta yi shi yasa tayi saurin shiga tsakani ta tsinketa da mari tasss. Kunnuwan Salwa sai da su ka ɗauke wuta na wucin gadi.

    “Ke jakar ina ce kike ƙoƙarin rungumar baligin namiji mai aure?”

    Caraf maganar a kunnuwan Hamdi. Ta yunƙura za ta tashi Firdaus ta ce ko ta fita kada ta saka baki.

    “Ki barta da Mama. Wallahi yau ko me take ji dashi ta tara ta samu.”

    Hannuwa duka biyu riƙe da kumatu su ka sameta. Taj ya kasa kallonta. Zama kawai yayi ya dafe kansa.

    “Bata da lafiya Yaya Hajiyayye. Wannan ba abin da mai lafiyayyar ƙwaƙwalwa zai yi bane.”

    “Babu wani hauka a tare da ita. A nono ta zuƙa kuma in sha Allahu gidanmu nan gani nan bari.”

    Tana rufe bakinta ta dannawa Ahmad kira.

    “Yaya please zan kira ki anjima kaɗan…” rashin samun Salwa a waya ne ya kiɗima shi. Ya rasa wa zai kira ya tafi asibitin. Mami da danginta amma tamkar wadda ta faɗo ita kaɗai saboda baƙin halinta ya kori kowa.

    “Ai koma mene ne uzurin indai ba sallah bace to ka saurare ni. Batun wannan yarinyar ne Salwa…”

    Katse ta yayi da saurin sa “gidan ki ta zo?”

    “Ina fa. Gata a gidan Taj.”

    “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un. Yaya Hajiyayye tun ɗazu nake kiranta ina nemanta.” Ya ce a sanyaye gwanin ban tausayi.

    “Ta ina za ta ɗauka bayan ta fito yawon zubar da mutumci?”

    A tsiwace Salwa ta ce “ni da aure nake son shi ba…”

    “Rufe bakin ki” Yaya Hajiyayye ta daka mata tsawar da Hamdi ma sai da zuciyarta ta kaɗa. Firdaus kuwa ta san halin mahaifiyarta dama. Akwai ban dariya da iya zolaya amma kada ka shiga huruminta. Yanzun nan za ta birkice.

    “Kana ji na Ahmad? Albarkacin ka zan sassauta mata. Amma lallai ka ja mata kunne. Idan ma hauka ne to tayi a wani wajen.”

    Bai ji daɗi ba amma kuma bai ji haushin yayar tasa ba saboda ya san gaskiya ce take faɗa. Kuma Salwa ce ta jawo wa kanta
    “Ƙalau take wallahi. Tsabar son zuciya ne da rashin tawakkali. Idan tana da zuciya ko aurenta ya ce zai yi ai ta ce bata so a yanzu. Saka ni a speaker”

    Yaya Hajiyayye ta saka. Ahmad ya kalli inda Kamal yake kwance ya ƙara jin nauyi a zuciyarsa. Ga damuwar gaske amma haka kawai Salwa tana tayar masa da hankali.

    “Idan kin fita ki koma asibiti ko ki wuce gidan ubanki kin ji ko. Na gaji. Ba ni na haife ki ba saboda haka ba za ki saka min hawan jini ba. Duk abin da ki ka zaɓarwa kan ki daga yau ya rage naki. Kada ki yarda ki koma gidana.”

    Bai jira jin ta bakin kowa ba ya katse call ɗin. Salwa ta bi su da kallo ɗaiɗai. Ta muzanta ajin ƙarshe. Haka ta miƙe ta yi ƙwafa da ƙarfi ta fita.

    “Ƴar banzar yarinya. A dalilin ki yau har rungume rungumen ango da amarya sai da na gani.” Yaya Hajiyayye ta cigaba da mita.

    Taj ya kama dariya. Hamdi kuwa hanyar ɗaki ta nufa, Firdaus na yi mata dariya. A lokaci guda falon ya mamaye da ƙaurin girkin da ya rasa kulawar waɗanda su ka ɗora shi. Su huɗun dake falo a tare su ka yi hanyar kitchen ɗin.

    ***

    Tsinuwa da zagi da mummunar addu’a babu irin wanda Salwa bata yiwa Ummi ba da ta fito. Ta tari adaidaita sahu amma ta rasa ina za ta ce ya kaita. Sai da ya yi shirin tafiya tayi saurin faɗin sunan unguwar da za ta. Suna tafe a hanya tayi mamaki ƙwarai da ta gane gidan. Sau ɗaya ta taɓa biyo Ummi a baya bayan sun tashi daga wata haɗuwa da su ka yi kafin bikin su Hamdi.

    Zuciya tana ta ingiza ta. Baƙinciki da ɓacin ran da take ciki ya yi yawa. Da ta ƙwanƙwasa ƙofa Siyama ce ta buɗe.

    “Ummi nake nema.”

    “Wa zan ce mata?” Siyama ta tambaya a tsorace. Fuskar Salwa abin tsoro. Kana ganinta ka san ba da alkhairi ta zo ba.

    Daga tambayar Salwa ta gane Ummi tana ciki. Bata ɓata lokaci ba ta hankaɗe Siyama gefe ta faɗa cikin gidan tana ƙwala kira.

    “Ummi. Ummi. Ummi…”

    A firgice Ummi ta fito daga ɗakin Iyaa inda aka saka ta gyaran wardrobe. Gabanta ya faɗi da ta tabbatar Salwa ce ba muryar ke mata gizo ba.

    “Me ya kawo ki gidan mu? Wa ma ya nuna miki?” Ummi ta ja hannunta su ka koma ƙofar gida.

    Iyaa da Baba Maje fitowa su ka yi daga ɗakinsa da Baballe inda su ke tattaunawa akan ginin gidansa inda Zee za ta tare. Wajen su ka je amma Ummi da Salwa basu ankare da su ba.

    Salwa ta cakumi wuyan Ummi “Ni za ki ha’inta? Turaren da ku ka bani dama ba wanda zai sa Ya Taj ya saki wannan ƴar ɗan daudun bane ya aure ni?”

    Tsohuwar bully an saba dambe. Ummi mantawa tayi da inda take ta doke hannun Salwa ita ma ta riƙe mata wuyan riga.

    “Banza a banza…duk soyayyar da za a siya da asiri wallahi na raina ta. Turare kuma ba na kashe aure bane.”

    Don baƙin ciki Salwa harda kuka ta ce “Na mene ne? Me ku ka sa nayi?”

    “Ummi…”

    Iyaa ta fara kiranta horrified da jin abin da su ke cewa. Sai dai da wuri Baba Maje ya yi mata nuni da tayi shiru. Abin kunya har mutane sun fara taruwa.

    “Ki jira ki gani amma tabbas soyayyarsa ba ta ciki.”

    “Wani aikin ku ka saka ni?”

    “Alh. Usaini dai ya saka ki. Ni mene ne nawa a ciki?”

    Cikin karaji Salwa ta ce “Waye Alh. Usaini? Me nayi Ummi? Turaren mene ne?”

    “Turaren kassara sana’ar mijin Hamdi.” Ta amsa mata da yanayin tsokana.

    Ai tana rufe baki Salwa ta daddage ta kai mata wawura. Kan kace meye wannan dambe ya kacame a tsakaninsu. Duka harda yaga riguna a gaban mutane. Iyaa hawaye kawai take zubarwa. Baba Maje kuwa cikin gida ya koma yana mai jin kunyar abin da ƴarsa tayi na zubar musu da mutumci. Baballe duk zafinsa akan Ummi shi ma komawa yayi yana mai jan hannun Siyama. Ƴan unguwa su ka yi ƙoƙarin rabasu abu yaci tura. Wani kawai sai ya kira ƴan sanda. Daga cikin gidan su ka ji jiniyar motar. Baba Maje ya ce kada wanda ya fita.

    Aka tattara su sai Police station. Nambar Baba Maje Ummi ta bayar. Da aka kira shi akan case ɗin ya ce zai zo. Suna gama magana ya kashe wayarsa gabaɗaya. Ya kuma ce da su iyalinsa kada wanda ya amsa kiran baƙuwar namba. Ummi ta zauna ta koyi hankali.

    Salwa ta fi Ummi tsurewa. Kwana a nan abu ne da ba za ta iya ba. Gashi ita ɗin mai laifi ce. Ta kasa bada numbar Zahra saboda gudun tashin hankalin da za su yi da Ahmad. Garin Kano cike yake da dangin Mami, yau ga ranarsu amma babu wanda za ta iya kira kai tsaye saboda ba ayi mu’amalar arziƙi ba. Ƙarshe nambar babanta ta bayar. Aka kira shi sau biyar baya kusa bai ɗauka ba.

    “Tunda baku da kowa mu bamu rasa masaukin baƙi. A wuce dasu su shiga su huta.” Cewar DPO ya na barin inda su ke.

    Hankali a tashe Salwa ta ce “Don Allah ka sa a sake kiran Babana. Ni wallahi ba zan iya kwana a nan ba.”

    Ummi kuwa ko gezau. Bata shaida ta shiga one chance ba sai da aka haɗa su cell ɗaya da wasu yan daban mata. Ashe damben su da Salwa wasa ne. Irin dukan da aka yi musu a cell đin ya ƙazanta. Babu wadda jikinta bai amsa ba. Kafin wani lokaci kowacce fa kama kukan gaske.

    ***

    Saboda yawan kiran waya sai da kunnen Ahmad ya yi zafi. Duk wasu ƴan uwa Mami na kusa da na nesa ya dinga kira yana neman taimakonsu akan kula da itaa asibiti. Duk wanda ya kira suna yabon yadda ya kiyaye zumunci amma kowa da irin labarin cin kashin da Mami tayi masa a baya. Bottom line dai babu mai zuwa. Ya shiga damuwa sosai. Kamar ya faɗawa Alhaji sai dai yana tsoron me zai faru. Daɗin daɗawa ga Kamal a kwance sai na’u’rori. Kansa ya ƙulle.

    Lokaci guda wata shawara ta zo masa. Ya kira likitan Mami ya ce a bashi Nos guda da za ta zauna da Mami tsahon sati ɗaya kafin ya dawo. Zai biya ko nawa ne. Aka tsadance ya tura kuɗin a take su kuma su ka tura wadda za ta iya ɗakin. Sai lokacin ya sami nutsuwa ya kira Baban Salwa ya tambayi ko ta koma.

    “Bata dawo ba amma zan kira ta. Ina so ka zare hannunka a kanta. Zan yi maganin abin da kaina.”

    ***

    Kwanaki huɗu bayan nan Taj ya shirya zai koma Happy Taj. Hamdi ta dasa masa rigima kala kala. Rarrashi iri daban daban yayi mata. Ƙarshe ba shi ya fita ba sai ƙarfe goma da minti kusan arba’in. Ya fara kaita gida saboda suna sa ran tafiyar Yaya ta samu nan da kwana biyar. Yana zuwa yaran kitchen ɗinsa su ka ce yau gwaji za su yi masa su tabbatar aure bai mantar dashi girki ba.

    “Kada daɗin abincin amarya yasa ka manta naka.”

    Kowa yayi dariya kuwa. Shi kuma ya ƙarɓi ragamar dafa chicken kabsa. A lokacin ne kuma aikin su Alh. Usaini ya yi tasirin gaske. Ya haɗa spices ɗinsa tunda abin da zai dafa dama spices ne sinadarin sa. Komai ya ajiye a gefe yayi marinating kazar. Bai ḍanɗana ba tunda hannu ya gama sabawa. Cikin ƙwarewarsa ya gama hađa komai saura jiran dahuwar abinci. Yana duba list ɗin abubuwan da aka ƙaro da baya nan yaga wasu cikin ma’aikatansa sun shigo kitchen ɗin a guje.

    “Sir baka ji ƙauri ba?” Wani ya tambaye shi da ya ce me ya faru.

    Ya juya ya buḍe tukunyar. Ƙauri ya sake cika kitchen ɗin. Kowa na tari banda shi. Shinkfar tayi ɓaki ta ƙone babu abin mora a ciki. Abin ya ɗaure masa kai. Ya faki idonsu ya da dangwali gishiri ya lasa. Ko ɗigo bai ji ɗanɗanon sa ba. Ya sake ɗora wata shinkafar ita kuma da ya gama aka yi serving ga masu saye babu wanda yaci rabi. Haka aka dinga dawo da plates ɗin cike da abinci. Bakinsa still babu taste. Yasa yaran kitchen ɗin ɗanɗawa. Kowa ya kai baki sai ya gumtse abinsa ya dangana bakin shara ya tofar. Akwai wanda ya soma amai a gabansa ma.

    “Me kuke ji?” Yayi tambayar calmly.

    “Gishiri da garlic sun yi yawa sosai. Yawan daido duk dauriya mutum ba zai iya rufe ya ci ba.”

    Hankalinsa sayiwani irin tashi yayi. Bai yiwa kowa sallama ba ya fita. Yana zuwa gida ya buɗe fridge ya ɗauki mixed fruit juice ɗin da ya haɗa da hannunsa jiya. Nan ma shiru baki da hanci bai ji komai ba.

    ***

    Abba Habibu da iyalinsa suna tattaunawa game da waɗanda Yaya za ta bi saboda ta sami muharrami.

    “Abba dama dai ka jira ka samu wasu kuɗin kun tafi tare.” Cewar Zee

    “Yanzu Allah Ya kirata. Ku dai ku yi mata addu’a. Banda abin ku mijin Labiba ai ya zama ɗan gida. Yan uwan nasa da zai yi tafiyar dasu jiya har kirana su ka yi mu ka gaisa.”

    “To kun gani ko…” Abba ya ce da murna.

    Suna wannan hirar Halifa ya buɗe passport ɗin Yaya yana gani.

    “Laah Yaya wane irin blood group ne wannan O minus?”

    Hamdi ta karɓe ta kalla ” ya kamata in ɗan yi studying bambancin blood group ɗinnan. Nima anyi min test ɗinsa amma ban duba ba da shi da geno type.”

    “Da aka yi min sai da mutumin ya ce min wai jinina na musamman ne don yana wahala.”

    Zee da Halifa sai cewa su ka yi su ma ɗin za su je ayi musu. Daga wannan hirar Abba ya ce,

    “Hamdi ki bamu numbar Kamal ta can, idan ta isa sai ta kira shi su gaisa.”

    “Idan bamu da nisa in je dai mu gaisa zai fi.” Yaya ta faɗi tana murmushi.
    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    Note
    error: Content is protected !!