Search
You have no alerts.

    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    Sautin amsa sallamar cika wajen ya yi kamar zai fasa kunnuwa. Kusan a lokaci guda Hamdi, Salwa da Anisa su ka toshe kunnuwansu. Sakamakon ƙatuwar sipikar dake kusa dasu wadda ta ƙara ƙarfin sautin. La’akari su ka yi da toshe kunnen da su ka yi a lokaci guda sai su ka kama dariya.

    Anisa dakatawa tayi da ta kalli fuskar ƴan matan dake gabanta. Bata san Salwa ba, amma ta so ta tuna Hamdi. Ita ma Hamdin sai aka yi dace ta kalleta a lokacin. Mamaki ne ya kama ta domin kuwa babu yadda za ayi ta ce ta manta kamanni da sunan Anisa.

    Girarta ce ta ɗage tana mai yi mata kallon sani ta ce “Anisan Abuja?”

    Gaban Anisa ya yi wani mahaukacin faɗuwa. Ba wai son ganin Hamdin ne bata yi ba. Abin da ya kawota taron buɗe restaurant ɗin Taj wanda bata manta ba shi ya dinga rarrashinta a waya har su ka isa inda take a lokacin nan. Kada dai irin abin da take karantawa a social media a ce vendor tayi snatching miji ko saurayin costumer ne zai sameta?

    Hamdi kuwa tunda gari ya waye sai yanzu tayi dariyar da ta kai mata zuci. Fuskarta ta haskaka da farincikin da yake ranta.

    “Allah Sarki. Naji daɗin sake ganinki. Lokacin da mu ka haɗu bani da waya. Daga baya da nayi kuma Anti Labiba ta ce ashe bata yi saving number ɗinki ba.”

    Da ƙyar Anisa ta haɗiyi yawu ta ƙirƙiri murmushi. Yanayinta na rashin nutsuwa duka a idon Salwa. Har ta kai ta matsu da son sanin me ya kawo wannan canji a tare da Anisan. Zuwan Sajida da Zee wajen ne ya taimakawa Anisa ta samu ta daina murmushin dolen da take ta yi.

    “Hamdi zo mu zauna ga seat Yaya Kamal ya ce sai an gama speech za a buɗe ko’ina a shiga.”

    “Har Kamal kin sani?” Anisa ta ce a gigice, sai kuma tayi saurin canja zancen da taga suna kallonta da rashin fahimta “kuna da alaƙa da Kamal?”

    Hamdi bata da amsar bayarwa don Kamal ɗin ma bata taɓa gani ba. Sunansa kawai ta sani. Ta kalli Sajida tana jiran tayi bayani sai jin baƙuwar murya tayi tana yiwa Zee magana.

    “Abba Habibu ya shigo kuwa Zee? Taj ke tambayar….”

    Kasa ƙarasa magana yayi. Ya tsaya kallon Hamdi ba shiri da irin mamakin da ta gama na ganin Anisa. Ya kalleta, ya kalli Sajida da Zee sannan ya yi magana.

    “Ke ce Hamdi?”

    Murmushi tayi da kunyar tuna abubuwan da tayi a gabansu wannan ranar.

    “Ina wuni?”

    “Ba zan amsa ba don naga alama da gangan ki ka dinga wasan ɓuya don kada mu haɗu.” Ya kalli saman stage inda Taj ya juya musu baya yana magana “bari Happy ya gama speech ya zo ya ga mai kukan bolt.”

    Ba don hayaniya ba da sai kowa yaji sautin wucewar wani abu kamar dutse da ya tokarewa Anisa wuya tun ɗazu. Maganganun Kamal sun tsefe mata zargin da zuciya ta fara kitsa mata. Ba kunya ta saki fuska tana dariya harda cewa,

    “Ai kuwa na san zai yi mamaki.”

    Kamal kuma ya dubi Sajida bayan ya gabatar musu da Salwa a matsayin ɗaya daga cikin ƙannensa.

    “Na jima ina son tuna inda na taɓa ganin mai kama daku na kasa. Da yake ban ma riƙe sunanta ba lokacin haɗuwarmu a Abuja shi yasa ban taɓa alaƙanta ku ba.”

    “Ikon Allah kenan. Muma fa ta bamu labarin haɗuwar taku.” Sajida ta faɗi tana kallon yadda duk wani haske na fuskar Hamdi ya ɗauke kamar an ɗauke wuta.

    Taɓota tayi sai tayi firgigit ta dubi Kamal ta sake kallon saman stage inda Taj yake tsaye. Dutsen da ya bar ƙirjin Anisa ashe nata ya koma. Ya haɗe mata da wani irin ɗaci na tsagwaron disappointment. Kallon mutumin da ta kasa cirewa daga ranta har rana irin ta yau a matsayin Happy Taj kawai take yi. Ubangidan Abbanta wanda take baƙincikin shigowarsa cikin rayuwarsu da ƙara ingiza mata uba ya cigaba da girki. Daina jindaɗin komai tayi a wajen sai tsananin son ta ganta ƙudundune akan katifarta a ƙuryar ɗaki. Ƙafafunta su ka koma tamkar leda don ji tayi kamar ba za su ɗauketa ba.

    “Hamdi lafiya kuwa?”

    Anisa ce tayi tambayar ganin ta dafe kai gami da runtse idanu.

    Ƙaryar da ta fara zuwa kanta tayi musu.
    “Jiri nake ji. Haka kawai kaina ya soma ciwo.”

    Da tausayawa Kamal ya kalleta “muje in sama miki inda za ki huta ba tare da hayaniya ba.”

    “Gida zan tafi” ta faɗi tana mai danne kukan da taji ya taso mata. Abin takaici bata ma sani ba kukan na mene ne yake barazanar kunyata ta a gaban mutane.

    “Yanzu wajen nan fita ma aiki ne. Ki huta ɗin dai zai fi. Maybe kema ba mai son taro da hayaniya bace kamar Happy.”

    Kwatanta ta da Happy ɗinnan ƙara mata ciwo ya yi a zuci. Kamal ya ce su Zee su zauna zai je ya dawo. Sajida ta so bin su ya nuna gara ta zauna da ƙannenta. Zai nemi mai zama da Hamdi har taji sauƙi ta fito.

    Suna tafiya Salwa ta gallawa Anisa harara irin wadda ake cewa aikin banza harara a duhu domin babu wanda ya kula. Sai ta ja tsaki da ƙarfi sannan ta bar wajen. Babu abin da bata sani ba game da Anisa a cikin gidan Ahmad. Hirar su ka yi da su Taj a waya a gaban Zahra. Ita kuma saboda yadda take ganin Salwa taƙi haƙura dashi shi ne ta faɗa mata anyi masa mata a gidan Amma.

    Su Zahra da sauran ƴan gidansu Taj ta tafi nema. Ita ma Anisa ta tafi wajen su Anti. Zee da su Sajida ma su ka koma daga gaba inda za su ji kalmomin godiya da Taj yake yiwa duk wanda ya zo.

    *

    Ta wata ƙofar baya Kamal ya buɗewa Hamdi ainihin ginin Happy Taj. Wani ni’imtaccen sanyi da ƙamshi mai kwantar da hankali ya baƙunceta. Mantawa tayi da ciwon kai ta zuba ido tana kallon yadda aka ƙawata wajen kamar ba a Kano ba. Kodayake dama bata taɓa zuwa wajen da ya kama ƙafar wannan a kyau da tsari ba.

    Sama ya su ka hau. A nan taga banda jerin tebura da kujerun masu cin abinci akwai ƙofofi a rufe. Ƙofa ɗaya ya buɗe mata ya tsaya daga gefe.

    “Akwai ruwa da juice a fridge. Ga key sai ki rufe ta ciki. Idan kin ji ƙarfi za ki iya fitowa kawai ki ƙulle.” Kujera ya nuna mata ta cushion mai irin ɗuma-ɗuman nan a can gefe da pillow na alfarma “ki kwanta a can. Ko kina so zan turo wata cikin ma’aikatanmu ta taya ki zama?”

    “A’a nagode” ta sake kallon wajen “ni da ka barni na tafi gida ma.”

    “Not an option. Kina fita ƴan uwanki za su bi ki. Kinga kin shiga haƙƙinsu ko?”

    Murmushi yayi ita ma ta mayar masa. Bata ga alamun samun nasara a tare da shi ba. Yana tafiya ta ƙulle ƙofar ta zare muƙullin tana juya shi a yatsanta ta haye kujerar ta kwanta. A gaban kujerar akwai two seater da one seater ɗinta a gefen hagu da dama. Tsakiya teburin gilas ne wato center table akan lallausan kafet sai TV da tarkacen kallo a kan wata irin tv stand ta alfarma mai kallo ƙofa. Ɓangaren lungu ya shige ta yadda ba a ganin mene ne akan kujerar sai an zagayo gabanta.

    Da yake a office ɗin ba a jin hayaniya sosai shiyasa wajen ya yi mata shiru. Tunanin yadda aka yi mutumin da ta gani a makarantarsu ya zama Taj ɗin da ya karaɗe bakunan ƴan gidansu ta fara. Sai dai bai je ko’ina ba bacci ya yi awon gaba da ita saboda daɗin waje. Gajiyar jiya da yau da su ka kusa kwana yin meatpie da samosa ce ta dirar mata gadan-gadan.

    *

    Taro ya yi taro. Iyaye da yara, matasa da dattijai kowa ka gani nishaɗi da farinciki kawai yake yi in banda Salwa. Tunda ta ga Anisa taji komai ya rikice mata. Yarinyar bata da makusa ko kaɗan. Daɗinta ɗaya shine gani da tayi ta fita haske nesa ba kusa ba. Anisa black beauty ce. Idanu dara dara da hanci mai tsini. Sai ɗan bakinta madaidaici. Ita kuwa irin fararen nan ne da mazan Kano a wancan lokacin su ke fatan samu ko da mayya ce. Maminsu tana da haske bakin gwargwado. Amma mahaifinsu bafullatani ne fari tas daga garin Dambam. Ƴaƴansa duka babu baƙi. Ga kwantaccen gashi da kyawun fuska. Ɗan murmushi tayi. Babu yadda za ayi Taj ya tsallaketa ya so wata Anisa. Da wannan yaƙinin ta saki ranta aka cigaba da sha’ani cikin walwala.

    Kamal ɓangaren boutique ɗinsa ya nufa inda ake ta ruwan ciniki. Shi da yaran shagon babu wanda ya sami kansa balle ayi batun nutsuwa. Tuni ya manta da Hamdi da ya kai office ɗin Taj.

    Ana kiran la’asar mutane su ka fara gangarawa kyakkyawan masallacin dake kusa da garden ɗin wurin. Wani hafizin matashi Taj ya samu zai dinga limanci a wajen. Saboda haka ko babu niyar siyayya sawu ba zai ɗauke ba ga ƴan unguwa da su ka sami masallaci mai kyau irin wannan.

    Yana jin kiran sallar ya so tafiya yin alwala amma abu ya gagara. Kitchen ɗin nasu ya rikice da aiki duk da sun gama tanadin abinci kafin a fara zuwa. Ba shi ya sami kansa ba sai biyar saura.

    “Subhanallah” ya furta hankalinsa na tashi “Abba ku ƙarasa zan je nayi sallah.” Ya ce da Abba Habibu da ya naɗa Sous Chef, wato mataimakinsa.

    Masallaci ya yi niyyar tafiya sai yayi tunanin mutane za su tare shi. Musamman ƴan uwansa da su ke ta son ayi hoto. Ciki ya koma. Ya hau sama da bibbiyu. Nan ma a cike yake da mutane. Ɗakunan taronsu ne kaɗai a rufe. Ƙofar office ɗinsa wanda Hamdi bata kula da label ɗinsa ba da za su shiga an rubuta EXECUTIVE CHEF.

    Da sauri ya buɗe office ɗin ya shige ya rufe ƙofar don kada wani ma ya ganshi. Ya faɗa toilet yayi alwala. Rigar uniform ɗinsa ta chef dake fitar da ƙamshin kitchen ya ɗan tattaro ya kara a hancinsa. Guntun tsaki ya yi ya ɓalle maɓallan da su ka ƙawata ta daga wuya har ƙasa, daidai saman cinyarsa inda yake daura apron. Wurgi ya yi da ita kan cushion chair ɗin da ta bashi baya ya nufi closet inda yake da irinsu spare har goma sha ɗaya. Kowacce set ce farar riga da farin wando. Jerin round maɓallen ne kawai baƙaƙe. Wata rigar ya ɗauko, ya zare ta daga hanger ya mayar da wandonta.

    Baccin Hamdi ya soma nauyi don ta fara mafarki mai daɗi taji wani abu ya faɗo a fuskarta. Ƙamshin turare mai ɗan karen daɗi ta fara shaƙa sai kuma taji na girki. A hankali ido har lokacin a rufe ta sake danna rigar a hancinta. Ta soma murmushi ita kaɗai sai kuma ƙwaƙwalwarta ta farka ta tuna a ina take. Bata san lokacin da ta ture rigar da sauri ta kuma ƙwalla salati da ƙarfi ba. A tsorace ta tashi ta kallo bayan kujerar.

    Taj ma saitinta ya kalla da riga a hannu. Allah Ya so shi akwai vest a jikinsa wadda ya yi tuck-in da ita a cikin wandon.

    “Abbanaaaaaa” Hamdi ta faɗi tana kai hannu ta ɗauki throw pillow ɗin kujerar ta jefa masa. Sakin rigar ya yi ya cafe pillon yana cigaba da ƙarasowa inda take. Kallo ɗaya ya yi mata ya ganeta. Mamakinsa dai me take yi a office ɗinsa kamar aljanna?

    Da hannu ya dinga yi mata alamar tayi shiru amma taƙi.

    “Shhhh, zan miki ihu nima.”

    Kama bakinta tayi ta ɓame. Sannan ta lura da bashi da riga. Ba shiri ta ɗauki wadda ya wurga kan kujerar ta cilla masa.

    “Ya Salam!” Ya ce da sauri don ya ma manta yanayin da yake. Ya koma ya ɗauki wadda ya fiddo yanzu ya saka. Baya su ka juyawa juna daga inda su ke tsaye har ya gama ɓalle maɓallan.

    “Uhmm” ya yi gyaran murya “how did you get here?”

    Muryarsa kamar yadda ta tuna ta ba ta mata bace. Irin deep masculine voice ɗinnan wadda sautinta yake ratsa zuciyar mai saurare.

    Gwanar a tsiwace ta amsa. Ba don zuciyarta ta so hakan ba. Sai don kawai tana son yakice shi daga ranta. Saninsa bashi da wani amfani. A dalilinsa yau wanda bai san Abbansu ba ma ya sani. Kuma ta tabbata haka za a tafi ana cewa ɗan daudu ne.

    “Wani Kamal ne ya kawoni da ina jin jiri.”

    “Subhanallah, kin ji sauƙi yanzu? Ko a je asibiti?” Taj ya ce da kulawa.

    “Na warke.”

    “Alhamdulillah. Allah Ya ƙara sauƙi. Da alama kema ba kya son gatherings. Ni kaina da zan iya da zamana zan yi. Taron mutane indai ba costumers bane bana so.”

    “Allah Sarki. Amma ni ina son taro, ciwon kan na gajiya ne” Hamdi ta yi magana tana yamutsa fuska.

    Taj yana lura da ita. Bai san dalilinta na yin hakan ba. Uzurin rashin lafiyar kawai ya yi mata.

    “Bari nayi sallah na baki wuri.”

    “Hhhhh” ta buɗe baki tana kallon agogon office ɗin. Biyar saura minti uku. Kamar za ta yi kuka ta ce “ban yi sallar ba nima.”

    Toilet ya nuna mata. Ta tsaya turus tana kunyar shiga banɗaki a gaban shi. Murmushi ya yi kawai ya fice. Ita kuma tayi alwala ta fito tayi sallah. A kullum idan sallah ta kama ta a waje tana yiwa Allah godiya da Yasa iyayensu tilasta musu shiga da mutumci. Idan ka gansu dole su burge ka. Ga kyau ga sanin darajar kai.

    *

    Magariba Taj ya so taro ya watse sai gashi kamar a lokacin ake tuttuɗu mutane. Shi da ma’aikatan sun gama kaiwa maƙurar gajiya. Tun suna dafawa a marmace har idan sun ga sabuwar oda sai su ji kamar su ce ba za su karɓa ba.

    “Don Allah ku saka CLOSE sign a ƙofar restaurant ɗin.” Cewar Taj yana fiddo wayarsa daga aljihun wando. Shugabannin bakery da masu nama ya kira ya ce idan sun gama da mutanen dake gabansu su fara shirin rufewa. Yana gama wayar Abba ya ce masa da ya sani bai ce a sallami mutane ba.

    “Albarkar da muke nema ce ta samu kake neman ture ta?”

    Taj ya sadda kai “ba manufata ba kenan Abba. Naga gobe za mu fara aiki officially. Idan bamu sami isasshen hutu ba zamu iya farawa a ga gazawarmu.”

    “Ko kusa. Dagewar yau ita za tasa ma’aikatanka su gane aiki ka ke so ba wasa ba. Maimakon a sallami mutane mu bari komai na yau ya ƙare. Babu yafi daɗi akan mun tashi.”

    Taj yaji daɗin shawarar Abba. Shi yasa ake cewa tafiya da gwani da akwai daɗi. Sannan iyawa kaɗai ba ta tafiya daidai sai an haɗa da experience. Tsarin wasu ƙasashen ya sani akan harkar restaurant. Abba kuwa ya jima cikinta a gida Nigeria kuma garin Kano.

    Suna haka aka dinga kiran Abba amma yaƙi ɗauka. Aikin gabansa yake son kammalawa. Taj sai ya ƙarba. Haƙuri yaji ya bayar da alƙawarin an kusa tashi. Da ya gama ya dubi Taj yana murmushi.

    “Hamdi ce uwar rigima. Wai in fito mu tafi tana jin bacci.”

    Taj sai yaji babu daɗi. Tara saura amma kamar yanzu aka fara aiki.
    “Shi yasa nace a tashi. Dare na ƙara yi.”

    “Kada ka damu, muna fita za mu sami adaidaita sahu. Bana son su tafi su kaɗai ne dai tunda duhu yayi. Nayi zaton zamu iya gamawa da anyi magariba.”

    “Bari na kira Kamal ko sun gama. Motarsa ai za ta ishe ku ko?”

    Abba ya yi dariyar jin ana tambayarsa ko mota za ta ishe su “Adaidaita ɗaya ma yana isar mu. Zee a sama, Halifa a kusa da direba. Mu uku a tsakiya.”

    “A sama kuma? Saman nan dai na bayan seat?”

    “Eh mana.”

    Abin ɗaure masa kai ya yi ya ce “Ninke ta za ayi ko lanƙwasawa?”

    Abba ya dinga dariya. Har su ka gama Taj na mamakin zancen zaman sama. Da su ka fito sai yaga har gara wurinsu. Boutique ɗin Kamal ya cika da samari da ƴan mata. Muƙullin motarsa ya karɓa ya ce masa zai kai su Abba gida.

    “Za ka iya dawowa kuwa?”

    “Me ka mayar dani ne? Zan dawo mana.”

    Kamal ya yi dariya “a dinga haɗawa da in sha Allahu dai.”

    Da ya fita shima Abba tambayar da ya fara yi masa ita ce ko zai gane hanyar dawowa. Ya nuna babu wata matsala sai su ka tafi. Abba na gaba, ƴaƴansa na baya. Hamdi tana ta faman kumbure kumbure don ita bata son ma a gaba ace suna cin arziƙi.

    Waya Abba ya gama da Yaya ya sanar da ita suna hanya. Ya duba missed calls.

    “Ashe kin yi ta kira bayan wadda na ɗauka Hamdi? Ban ji ba ne.”

    “Ai Abba ƙiris ya rage ka fito kaga tana kuka. Ka san yadda bata son zuwa taro.”

    Saurin kallon madubi Taj ya yi kamar ta sani kuwa ita ma ta kalla. Maimakon taji kunyar ƙaryar da tayi masa sai ta juya idanu ta murguɗa baki.

    “Kin yi kyau.” Ya furta idanunsa har lokacin a kanta ta madubin.

    “Wa?”

    Abba ya faɗi yana kallonsa. Su Sajida ma duk sun zuba masa ido su na jiran amsa.

    “Wata mota ce ta wuce yanzun nan. Ba don motata ta kusa isowa ba da ita zan saya.”

    A haka zancen ya mutu. Lokaci lokaci suna haɗa ido ta madubi tana harararsa. Sai bai damu ba. Zuciyarsa tana raya masa tabbas ya yi mata laifi ne. Laifin da yake ganin ba zai wuce na rashin nuna mata ya santa ba lokacin da su ka haɗu a Abuja.

    Ya kai su gida lafiya amma komawa ta gagara. Ƙarshe sai Abba ya kira saboda rashin dacewar neman ƴan mata sha ɗaya da rabi na dare. Da kwatancem Abban ya fita daga unguwar. Yana tafiya a hanya yana nanata ‘in sha Allah ba zan kuma ɓata ba.’

    ***

    Satin farkon buɗe Happy Taj lokaci ne da Taj da Kamal ba za su taɓa mantawa dashi ba. Sun sami ciniki da yawaitar al’umma fiye da tunaninsu. Taj gani yake hakan ba ya rasa nasaba da addu’ar da Alhaji ya zo ya yi musu daren da za a buɗe wajen. Da kuma ta iyaye. Sai kuma saukar karatun da su ka yi shi da Kamal da sadaka domin neman Allah Ya sanya musu albarka. Kuma Ya tsaresu da wurin kansa daga zamewa al’umma fitina.

    Duk da ya yi sanarwar gama ɗaukan ma’aikata to amma fa har lokacin mutane basu fasa kawo takardun neman aiki ba. Ya rufe ido ya ƙara ɗaukar masu shara da wanke toilets. Da kuma masu wanke-wanke da shara. Irin aikinka, irin uniform ɗin da za a ɗinka maka da suna idan an ɗauke ka. Bakery ne kawai ya bar space ɗin Hamdi. Da gaske yana son yin aiki tare da ita. Ya yabawa iyawarta sannan yana kusancinsu zai taimaka masa ya sami soyayyarta.

    Baya son yin garajen fara nuna mata soyayya a yanayin da ake ciki. Bai san yadda Abba ma zai ɗauki maganar ba don ya kula yana da gudun rigima. Balle kuma Alhaji. Idan ya ƙyaleta haka kuma tabbas zai ji labarin wani ya yi masa shigar sauri. Da wannan shawarar ya tunkari gidan ranar wata lahadi, ana saura kwanaki huɗu kamun Sajida.

    Cikin gidan ya fara shiga su ka gaisa da Yaya. Bayan sun ɗan taɓa hira ya tashi ya ce ta turo masa Sajida. Kuma sarai ya san Sajidan bata nan. Tun zuwansa aka ce tana wajen gyaran jiki. Zee kuma ta tafi karɓo ɗinki.

    “Daddawar ɗaka ce kawai a gidan.”

    Kamar bai san wa take nufi ba ya ce “gaskiya a ƙannena babu daddawa.”

    “Ashe baka san Hamdi ba. Kana kallo dai tun shigowarka ta shige ɗaki. In ba kiranta nayi ba kuma da wuya ka sake ganinta har ka tafi.”

    Daga ɗakin Hamdi ta zumɓura baki da kwance zanin da Yaya take yi mata.

    “Sai ki fito don na san kina jina.” Yayan ta ɗaga murya.

    Taj bai ji ta amsa ba har ya isa zauren ya tsaya. Ya sa rai za ta jima sai gashi bai fi minti biyu ba ta fito. Bakin nan a gaba.

    “Kya hua Hamdiyya?” Ya zolaye ta.

    Shi yake yaren ita take jin kunya.

    “Ba na jin indiyanci.”

    “Na ga mata suna son movies ɗinsu. A nan ku ke tsintar kalmomi. Sisters ɗina dai na san haka su ke.”

    “To banda ni. Ba na kalla. Kuma namiji mai gani ma ba kula shi nake ba.”

    “Allah Ya so ni kenan.” Taj ya ce yana neman haɗa ido da ita amma ta ki yarda.

    Mamaki ya bata don bata yarda da furucinsa ba ta ce “Ba ka gani?”

    “Ko Salman Khan ɗin da ki ka kirani rannan ban sani ba.”

    “Allah ban yarda ba” ta ce kai tsaye.

    Taj ya yi dariyar da amonta ya zauna daram a zuciyarta. Bata sani ba ko ana kiran maza cute. Ita dai da yana dariyar nema ya yi ya sauke mata bangon da take ginawa a tsakaninsu. Shammatarta da ya yi da tambayar da fito daga bakinsa ce ta yanke mata shagalar da ta so yi.

    “Laifin me nayi miki ne da ya zamana tsakaninmu babu kallon kirki sai harara? Ko don ban faɗa miki na san ki ba a Abuja?”

    Shiru tayi. Ya sake maimaita tambayar amma sai ta kawar da kanta. Bai yi fushi ba ya ajiye girma da matsayinsa ya faɗa mata abubuwan da su ka wakana tun lokacin da Firdaus ta faɗa masa sunanta da biyota gida da ya yi.

    “Dalilinki na zo gidan nan amma yanzu ba don ke kaɗai na nemi kusanci da Abba ba. Ina ji a jikina zamu amfani juna in sha Allah.”

    Kasa magana tayi. Sai tunani da yawa da take fama dasu. Da yaga tayi shiru ne ya nemi jin ta bakinta. Sai ta faɗi abin da bai taɓa tsammani ba.

    “Da Abbanmu ya rasa wajen sana’arsa nayi murna ni dai. Na so ace wata sana’ar ya samu ba komawa girki ba.”

    Taj yaji tamkar ta watsa masa ruwan zafi.
    “Kema ba kya son namiji mai girki ne? Ko kuwa wanda ya taɓa rayuwa irin ta Abba?”

    “Mene ne maraba? Duk namijin dake girki ba ɗan daudu sunansa ba? Har yanzu ba sunan da ake kiran Abbanmu kenan ba saboda yaƙi yin wani aikin sai na mata.”

    “Daina magana irin haka Hamdi” Taj ya kwaɓeta “yanzu har za ki iya aibata sana’ar da mahaifinki yake yi miki komai cikinta kuma wadda Allah bai haramta ba?”

    Kuka ta saka masa “Baka ji muryarsa ba? Idan yana tafiya meye marabarsa da ma…”

    “Ya isa…” ya kaɗa kai yana mamakinta ƙwarai da gaske “indai za ki iya waɗannan maganganu akansa to waye a waje ba zai yi ba? I thought idan kowa ya ƙyamaci mahaifin mutum shi yana son abinsa.”

    “Nima ina son sa. Amma wallahi bana son sana’arsa.” Ta kalle shi ido cikin ido “kuma bana son duk wanda zai taimaka masa akan cigaba da sana’ar girki.”

    Tunowa da Alhaji ya dinga yi da kalamanta masu ɗaci. Cikin ɓacin rai ya ce “nima ban ce ina son ki ba. So kada ki yarda ki min rashin kunya akan sana’ata. I am a Chef and I love what I do.”

    Bata san ta ɗaga murya ba ta ce “to wa ya hanaka dama? Meye na sanya Abbana a ciki?”

    A ganinsa bata ma cancanci ya faɗa mata kuɗurinsa na taimakawa Abba ya rage ko bai daina duka abubuwan mata ba. So yake ya nuna masa zai iya sana’arsa cikin nutsuwa ba tare da ya yi koyi da mace ba. Shi yasa ya ɗauki riƙaƙƙun maza waɗanda ko magana su ka yi sai an san namiji ne na gaske aiki. Girki daban, daudu daban. Wannan abin yake so hausawa masu fahimta irin ta Alhaji da wannan mara kunyar yarinyar da yake jin soyayyarta har yanzu su gane.

    “Saboda na isa.” Ya faɗi don taji haushi.

    “Me kake nufi? Abbana yaronka ne?”

    “Uba na ɗauke shi mai sawa ya hana. Wanda kuma da ni ya haifa ba zan guje shi ba.”

    “Na ce maka ina son Abbana. Girkin ne bana so.”

    Ya zata yi ya fahimceta? Indai Abba bai daina sana’arsa ba, gani take ba zai taɓa rabuwa da ɗabi’un da ya koyi girki cikinsu ba na daudanci. Idan mutum yana abu maras kyau a ganinta nesanta dashi, shi ne yafi alkhairi.

    Shi kuma Taj so yake ta gane cewa sana’ar ba ita ce ta mayar dashi haka ba. Haɗa biyun da mutane su ke yi, shi ne musabbabin da yasa mazan dake son girki da dama a ƙasar hausa su ke karkacewa su yi koyi da jinsin mata. A ganinsu kamar girki ba zai cika ba sai da waɗannan ɗabi’un.

    Ran kowa a ɓace su ka rabu. Don ko amsa bai iya sake bata ba ya fice abinsa. Ita kuwa tana shiga gida taji saukar lafiyayyen mari daga wajen Yaya.

    Huci take rai a ɓace “ki ka ce ba ki son duk mai taimakon mahaifinki akan sana’arsa Hamdi? Saboda kin tashi duk runtsi duk wuya bai taɓa ƙin kawo abin da za a ci a yi sutura ba? Ashe baki dawo daga rakiyar zuciya ta ƙyamar babanki ba?”

    Hannunta akan kumatu tana jin zafi har ranta ta ce “Yaya ku daina yi min irin fahimtar nan. Ina son Abba mana. Girkin ne kawai…Yaya har yanzu muryar mata gare shi fa”

    Sai kuka mai cin rai. Yaya ma kukan take yi. Duk cikin ƴaƴanta dama kafiya da sanya abu a rai babu wanda ya kai Hamdi. Kowa na zaton rigimarsu da Ummi ta kashe mata waccan ƙiyayya. Ashe har yanzu bata son sana’ar. To amma wacce take so ya yi? Bayan mutane suna da wuyar uzuri da ƙarɓar kuskure. A yanayi da ɗabi’unsa, duk inda ya sanya ƙafa neman taimako ko son fara sana’a sai ace ɗan daudu ne. Girkin ne kaɗai idan ya yi sai an bishi an saya. Da shi kaɗai yake tsaye a ƙafafunsa. Banda wauta da ƙuruciya me zai sa ta ƴarsa ta zauna ta faɗawa wanda ya killace mata uba daga gaban murhun da kowa yake ganinsa a da. Yanzu sai ya gama ya dawo iyakarsa kitchen. Ba a ganshi ba balle ma a aibata shi. Kuma saboda duka kitchen ɗin maza ne har ya fara ƙoƙarin gyara tafiyarsa.

    “Kin bani kunya wallahi.”

    “Yaya…”

    “Tashi ki bani wuri.”

    Ɗakinsu ta shiga tana kuka kamar ranta zai fita. Soyayyar da take yiwa Taj ta ɗauki sabon salo. Haushinsa kawai take ji. Ba ma ta son shi. Kuma ba za ta taɓa son nashi ba.

    “Aikin banza. Meye abin burgewa a namiji mai girki? To da me matarsa ma za ta burge shi?” Ta ayyana a ranta duk cikin kukan.

    Shi a ranar kasa gane kansa aka yi a Happy Taj. Da yaga komai ƙanƙantar abu sai ya yi faɗa sai ya koma office ɗinsa kawai ya rufe ƙofa. Kan 3 seater yaje zai kwanta ya tuna Hamdi ta taɓa kwanciya a kai sai ya tashi yana tsaki.

    “Ashe yarinyar nan bata da kunya? Na iya haƙura ma da Alhaji ya koreni balle wata ƙaramar yarinya?”

    Daga inda suke kowannensu ya dage yana sauke fushinsa ta hanyar ƙara faɗawa zuciyarsa girman laifin ɗayan. Shi dai Taj baya son wadda ta kasa ganin ƙoƙarin mahaifinta a matsayin da Allah Ya ajiye shi. Ita kuma Hamdi gani take tsabar mugunta ce ma za ta sa ya cigaba da ingiza mata uba akan hanyar da babansa ya kore shi a kanta.

    ***

    An yi Kamun Sajida ranar laraba cikin farinciki da taron dangi. Hamdi tuni ta ajiye wani Taj ana ta sha’ani. Wannan karon ko ciwon kai bata ce tana yi ba saboda tsananin farinciki. Sajida ta sami wanda take so kuma yake sonta ba tare da ya taɓa goranta mata ba. Damuwar su Yaya da tsoron ƴan matansu ba za su auro ba ta kau. Komai nasu na rufin asiri sun yi domin fitar da juna kai kunya.

    Alhamis aka yi sisters’ a wani event centre. Ranar dai har rawa Hamdi tayi tunda taron mata ne. Sai da Anti Labiba ma ta janyeta saboda ko gajiya bata yi. Ana canja kiɗa take komawa.

    “Wannan ko ke ce amaryar sai haka.”

    Wata ƴar uwarsu ta kare mata “barta tayi. Ranar nata auren ai ba yi za ta yi.”

    *

    Ana can ana shagalin biki wasu motoci biyu masu kyau su ka yi parking a ƙofar gidan Abba. A tsaye yake da Kamal da Taj. Kamal ne ya zo bashi tashi gudunmawar wadda ta kasance ta kayan abinci. Saɓanin ta Taj da ya bashi kuɗi. Yana ta cewa sun yi yawa da almajirai na kaiwa cikin gidan waɗannan motoci su ka tsaya.

    Ƴar Ficika ne ya fara fitowa daga motar gaban yana murnar ganin Abba a ƙofar gida.

    “Waɗannan mutanen ne su ka zo nemanka nace musu ai ka tashi daga wurin. To sai…” ya juya ya nuna wani Alhaji da ya nufosu yana takawa kamar baya so “wannan Alhajin ya nemi in kawo shi wurinka. Har za mu je restoran ɗin sai na tuna ɗazu ka ce min kana gida.”

    Abba ya yi murmushi “ai da ka sa wani ya rako shi ma.”

    “Yaran nawa duk basu san nan ɗin ba.”

    Abba ya miƙawa mutumin hannu domin su gaisa sai ya ƙi ɗaga nasa. Kallon wulaƙanci kawai yake yiwa Abban. Shi da ragowar mazan da su ka firfito daga motocin har su biyar.

    “Kai ne Habibu Simagade?”

    Abba ya ɗan murmusa “a da kenan.” Ya kuma miƙa hannun mutumin bai karɓa ba dai.

    “Ni ne uban Safwan mahaifi.”

    Mamaki ya bayyana a fuskar Abba. Tabbas ga kama nan. To amma ba wani abu bane tunda da ana neman aure kawunnansa ne su ka zo.

    “Allah Sarki. Bari nasa ayi shimfiɗa a ciki.”

    “Barshi. Zuwa nayi na faɗa maka cewa idan ka kuskura aka ɗaura aurensa da ƴarka gobe sai na ɗaure duka mutanen gidan nan.”

    “Alhaji me ya faru?” Abba ya ce da fargaba. Taj da Kamal ma hankalinsu tashi ya yi.

    “Meye ma bai faru ba? Ya faɗa min yana son wata yarinya nasa aka bincika aka ce ubanta ɗan daudu ne. A ranar na soke maganar. Shi ne ya haɗa kai da wan uwarsa aka zo aka nemi aure da komai a bayan idona. Suna ta ɓoye ɓoye basu san na sani ba. Dama bari nayi sai goben in ci muku mutumci duka a wajen ɗaurin auren. Sai yayansa ya shiga maganar” ya nuna babban ɗansa “shi yasa na zo yau. In kun je an ɗaura za ku ga abin da zai faru. Zuriata tafi ƙarfin haɗa jini da irinku. Ɓata gari, lalatattun mutane”

    Banda Innalillahi babu abinda Abba ke faɗi. Ƴar Ficika kuwa ihu ya saka kamar mace yana ta jan jallabiyarsa sama yana tumamin wai sun shiga uku.

    Baban Safwan ya kalle shi cikin takaici da baƙincikin anyi asarar namiji. Haƙuri Abba ya fara bashi ya dakatar da shi. Kamal da Taj su ka saka baki ya ce babu ruwansu. Ba su yi aune ba Abba ya dire gwiwoyinsa a ƙasa zai fara roƙo mutumin ya juya abinsa bayan ya yi tsaki.

    “Alhaji ka yiwa Allah kada ka hana auren nan.”

    Da sauri Taj ya kama hannunsa zai ɗaga shi amma yaƙi miƙewa.

    “Abba don Allah ka tashi.”

    “Idan auren nan bai yiwu ba gabaɗaya gidana laifina za su gani. Sajida bata taɓa saurayi ba sai akan shi. Sun saka rai Taj, kowa ya saka rai. Duniya za ta zage ni. Duniya za ta min dariya..”

    Babu wani tunani ko hangen nesa Taj ya ce masa “Abba indai ka amince za ka bani Hamdiyya, in sha Allahu gobe za ka aurar da ƴa.”

    “Taj?” Kamal ya kira shi gabansa na faɗuwa.

    “Ina son ta Abba. Saboda ita na zo gareka.”

    Abba Habibu rasa bakin magana ya yi. Ido kawai ya zubawa Taj har motar baban Safwan ta bar layinsu bai sani ba.
    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    Note
    error: Content is protected !!