Search
You have no alerts.

    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
    Kyakkyawan envelop Yaya Babba ya miƙawa Alhaji ya kuma bishi da kallo a tsanake don son karantar yanayinsa. Kamar yadda ya yi tsammani duk wani annuri da walwalar da yake tare da ita a farkon zamansu tsaf ya kau. Duhun da yake zuciyarsa ya sami damar nuna kansa a fuskar. Disappointment ɗinsa akan Taj ya kashe masa jiki da zai yi magana.

    “Kawo maka ya yi?” Da Yaya Babba ya gyaɗa kai sai ya ce “to me yake so?”

    Kallon tausayi Yaya Babba ya yi masa. Mutum mai kafiya irin ƙaninsa yana da wuyar sha’ani. Wani zubin ya tabbatar yana sanin cewa ba a kan gaskiya yake ba amma don kada ya sauya baki sai ya cigaba da riƙo da hujjojinsa masu rauni. Sai dai a yau ya ƙudiri niyar amfani da girmansa karo na biyu ya tanƙwara ƙanin yadda yake so.

    A nutse yadda zai fahimta ya labarta masa zuwan Taj gidansa kwanaki uku da su ka wuce. A lokacin sun kusa wata biyu da dawowa daga India. Sakamakon gasar girkin nan ne Wakili ya taho masa da certificate ɗinsa na ɗaukar na ɗaya. Sannan ga admission letter kamar yadda aka yi alƙawari. Shi ne ya kai masa ya gani amma ya roƙe akan kada ya sanar da kowa domin ko iyayensa mata bai nuna musu ba. Ya kawo ne saboda ya nuna masa godiya akan shige masa gaba da ya yi har ya sami damar ƙarasawa. Sai kuma Wakili da ya nuna son zuwa ya gaishe da iyayensa kafin ya wuce Minna. Shi ne ya kai masa shi inda aka yi masa tarba mai kyau. Da yaji daɗi har mahaifiyarsa sai da ya haɗa da Yaya Babba su ka gaisa.

    Alhaji ya gama jin zancen da bai gamshe shi ba ko kusa ya ce “mece ce manufar nuna min tunda ya ce baya son na sani?”

    Yaya Babba dakewa ya yi babu alamun wasa ya ce “ina son ka sanya masa albarka ne domin idan Allah Ya kaimu lokacin fara karatun ni zan mayar dashi da kaina.”

    “Kada mu yi haka da kai Yaya.”

    Alhaji ya furta da ƙaramar murya yana jin wani irin yammm a sassan jikinsa. Yana matuƙar ƙaunar Taj sannan burinsa a duniya yaron ya gaje shi. Idan hakan bai samu ba ya yi zarra a duk sana’a ko aikin da ya nema amma banda GIRKI. Yadda rayuwar Habibu ta sauya salo a kan idanunsa ba zai taɓa lamuncewa ɗansa ya faɗa wannan hanyar ba. Shi fa ko duk jikinsa kunnuwa ne ba zai yarda girki ba wani nau’i bane na daudanci.

    “Idan Allah Ya bamu yara masu biyayya, amfani da ƙarfin iko wurin hanasu farinciki ba zai taɓa haifar da ɗa mai ido ba Hayatu.”

    “Haka ne.”

    “Ka amince?” Yaya Babba ya tambaye shi yana murmushi.

    “Ai ka ishe shi uba Yaya Babba. Ba za ka taɓa faɗin magana na musanta maka ba in sha Allahu.”

    Da zuciya ɗaya Yaya Babba ya miƙa masa hannu su ka yi musabaha cike da farinciki. Bai san cewa magana ce mai harshen damu Alhaji ya yi masa ba.

    “Allah Ya ja kwana baban Tajuddin. Nagode da karamcin nan da kayi min. Da yardar Allah sai mun yi alfahari da zaɓinsa.”

    “Uhmm” kawai Alhaji ya iya cewa don bakinsa ya bushe kamar an shanya a rana. Samu ya yi ya bar gidan kamar babu abin da ya riƙe a ransa.

    Bayan fitarsa Yaya Babba ya kira Mummy (Ɗaharatu) matarsa kuma yaya ga Mama ya sanar da ita anyi nasara. Ta kama murna tana cewa hakan shi ne daidai.

    “A neman haram ake yin fito na fito da burin ƴaƴa. Yadda Taj ya rame ya sanya abu a ransa ko ya zauna ba daɗinsa za su ji ba. Allah Yasa matakin nasara da samuwar alkhairi mu ka ƙulla.”

    “Amin” Yaya Babba ya faɗi yana gyara zaman gilashinsa.

    Duk cikin zuri’arsu shi da wata ƙanwarsu Jamila ne ake yiwa laƙabi da ƴan boko. Matarsa ɗaya da yara biyar waɗanda huɗu sun yi aure saura namiji ɗaya. Mutum ne da ya yarda da displine ɗin yaron da ya kauce hanya amma sam bai yarda a tauye haƙƙinsu ba. Ita kuwa ƙanwar tasu da yara ke kira Amma likita ce. Sai da ta gama karatu tayi aure har ana ganin da gangan taƙi yi tun farko. Mijin mazaunin Amerika ne a can yake aiki. Bayan aurensu da ta bi shi ita ma ya sama mata take aikinta a wani asibiti. Yaransu biyu mata.

    ***

    Ɗaki Alhaji ya kira Taj bayan ya koma gida. Ya yiwa ɗan nasa kallo na ka bani kunya sannan ya miƙa masa envelop ɗin. A take kuwa jikin Taj ya kama rawa.

    “Ba da wata manufa na kai masa ba Alhaji.”

    “Ka ji na ce wani abu ne?”

    “A’a.”

    “Madalla” ya gyara zama “Yaya Babba ya ce ka haɗa kayanka ka koma gidansa kafin lokacin fara karatun naku.”

    “Wane karatun? Ba service zamu tafi ba?” Ya tambaya da faɗuwar gaba.

    A ransa Alhaji gani yake rainin wayo ne kawai Taj yake son yi masa amma ya san komai. Ƙarshenta ma shi ya roƙi Yaya Babban da ya taimaka masa ya sami komawa makarantar.

    “Idan ka dawo sai ka zo kayi service ɗin. Ina yi maka fatan samun nasara da alkhairi. Allah Ya yi maka albarka. Tashi ka tafi.”

    Kansa sake ƙullewa ya yi amma babu halin tambaya. Sai ma ƙarin bayani da Alhajin ya yi masa cewa ya bari jibi zai kai shi da kansa don ya sami damar hađa kayansa.

    “Ba na kuma son jin zancen nan a bakin kowa har matan gidan don na san za su so hanaka tafiya.”

    “To Alhaji” ya amsa a ladabce.

    Kamal kaɗai ya sanarwa abin da yake faruwa. Da taimakonsa ma ya gama haɗa kaya. Ranar da za su tafi Alhaji ya faɗa masa zai dawo daga kasuwa da azahar sai ya kai shi.

    “Happy” Kamal ya kira Taj suna zaune a ɗaki “ba ka mamakin chanjin ra’ayinsa?”

    “Ni fargaba ce ma tafi damuna. Naga ko kaɗan bai nuna fushi ba duk da Allah Ya sani ba da wannan manufar na kai wa Baba Yaya takardun ba.”

    “In sha Allahu ma babu komai. Dama tsoron da naji da ka ce wai ya ce kada a faɗawa kowa.”

    Bugun ƙofa gami da sallamar Bishir ce ta hana Taj sake yin magana. Saƙon Alhaji ne yana jiransa a mota.

    A take yaji gabansa ya yanke ya faɗi. Ya tashi jiki a mace sai Kamal da Bishir ɗin ne su ka ɗauko masa kayansa. Kowa yaga ana loda kaya a booth ɗin Alhaji sai ya yi mamaki amma an rasa mai tambaya don babu fuska.

    “Ka shiga ka yiwa uwayenka sallama.” Alhaji ya umarce shi da ya fito.

    Inna bata gida. Sai su Hajiya. Su ka biyo shi waje kuwa su na tambayar Alhaji me ya faru Taj zai koma gidan Yaya Babba. Cewa ya yi su koma. Idan ya dawo zai yi musu bayani.

    A mota haka su ka tafi ko numfashi mai sauti Taj baya iya ja. Kamar tare su ke don ana buɗe musu gate su ka ga Yaya Babba yana fitowa daga mota. Dawowarsa kenan daga office. Yayi mamakin ganin Alhaji kaɗai ko direba babu da Taj. Sai dai wannan ba komai bane a yayin da yaga ya buɗe booth Taj na sauke kaya.

    “Hayatu me yake faruwa ne?” Ya matso kusa dasu don jiran su gama su shigo ciki ma ba zai iya ba.

    Alhaji ya dubi ɗan uwansa yana mai baƙincikin yadda yayi masa katsalandan a cikin harkar gidansa. Shi kuwa Taj yana jin haka wani irin tsoro ya kama shi. Kenan Baba Yaya ba shi ya nemi ya dawo gidansa kamar yadda Alhaji ya faɗa masa ba.

    “Ga Taj nan. Suna na ne kawai addini bai halatta min cire masa ba amma daga yau na bar maka shi.”

    Yaya Babba ya girgiza da furucinsa matuƙa. Fuskar ƙanin nasa a haɗe take kamar baƙin hadari.

    “Me ya yi zafi? Don na ce zan mayar dashi makarantar da yake so?”

    “Ai ban hanaka ba tunda ka isa. Shi ma da na isa dashi ina mai umartarsa kada ya dawo min gida.”

    “Hayatu bana son rashin hankali.” Yaya Babba ya fara faɗa.

    “Ai kuwa bai kamata ka kira biyayyata gareka da rashin hankali ba.” Ya cigaba da magana kai tsaye babu tauna lafuzza don yau dole ya amayar da ɓacin ransa “saboda gudun shiga haƙƙi ban taɓa yiwa kowa iko da ɗansa ba. Amma sau biyu Yaya kana bawa yaron nan abin da nake son hanawa. Hakan ba komai zai janyo min ba illa baƙin jini daga gare shi. Koda yayi min biyayya zata zama bisa tursasawa ba don son rai ba. Maganin kar ayi, kar a soma. Tunda ka nuna masa za ka iya bashi abin da na hana sai ka riƙe shi na bar maka.”

    “Ni kake faɗawa magana Hayatu? Ashe zumuncinmu bai kai nayi umarni ko hani ga tsatsonka ba tare da ka ɗaga kai ba?” Yaya Babba ya faɗi yana mai jin ciwon maganganun da kunnuwansa ke ji.

    Musayar yawun da suke ba ƙaramin tadawa Taj hankali tayi ba. Ya durƙusa a ƙasa yana kuka yake roƙonsu da su yi haƙuri.

    “Wallahi ba zan sake tada zancen nan ba har abada. Ku yafe min don Allah.”

    “Baka isa ba! Karatu ko ba kyauta aka baka ba sai kayi shi. Tunda ka iya raina ƙoƙarina akanka ka haɗani da ɗan uwana dole ka cika burinka.”

    Taj na kuka ya riƙe ƙafar mahaifinsa yana roƙon yafiyarsa. Yaya Babba ma idanunsa sun kaɗa sun yi ja. A haka ya ja girmansa don gudun rigima ya bashi haƙuri.

    “Kayi haƙuri. Ban yi zurfin tunani ba, da ban shiga huruminka ba. Don Allah ka ɗauki ɗanka ku tafi.”

    “Na gama magana. Wallahi daga yau Taj ya bar gidana…”

    “Kada ka rantse.” Ya yi nufin dakatar dashi sai dai ya makara.

    Suna ji suna gani Alhaji ya juya ya shige motarsa yayi gaba. Taj ya bi motar a rikice kafin ya sami wuri kusa da akwatinsa ya zauna cikin wani irin yanayi na rashin kuzari. Zuciyarsa wani irin ƙunci kawai ke yawo a cikinta. Bai san lokacin da aka kwashe kayansa ba. Sai hannuwa da yaji na ɗan uwansa, ƙaramin ɗan Yaya Babba wanda ya kasance sakonsa ya tayar dashi. Da ƙyar ya yarda ya shiga gidan. Mummy tana kuka tana bashi baki tare da alƙawarin gobe Yaya Babba zai mayar da shi.

    ***

    A wannan rana ko gyangyaɗi Taj bai samu ba. Kuma haka ta kasance a ɓangaren Baba Yaya da Alhaji da Inna. Don bayan ta dawo gida da ya sanar dasu hukuncin da ya ɗauka har suma tayi. Gidan ya rikice da koke koke. Iyalin Alh. Hayatu su ka taru su ka juya masa baya daga matansa har ƴaƴansu. Hakan kuwa bai yi masa komai ba face ƙara tsanar turbar da Taj yake son bi. Da kuma abin da Yaya Babba yayi masa.

    Washegari duka ƴaƴan Marigayi Alh. Sule su ka taru a gidansu dake Soron ɗinki inda mata guda ɗaya da ta rage musu a matsayin uwa take. Ita ce mata ta uku cikin matansa. Zama irin na da yasa ita da ƴaƴan sauran abokan zamanta su ka cigaba da zumunci tamkar lokacin da mahaifinsu yake da rai.

    Ita Yaya Babba ya kaiwa ƙarar Alhaji tun a jiya. Tasa aka kira mata kowa dake kusa. Amma ma dake nesa dama ta iso kwana huɗu da su ka wuce hutun shekara. Tana Abuja da niyar tahowa bayan sati guda. Amma kiran Gwaggo yasa ta biyo jirgin ƙarfe tara na safe.

    Bayan an zazzauna Yaya Babba ya mayar da iya abin da ya faru ta ɓangarensa. Tun daga wayar da Mama ta yiwa Mummy da suna India har zuwa yadda ta kasance jiya. Aka tambayi Alhaji sai kaɗa baki ya yi ya ce bashi da abin sake tofawa.

    “Yanzu Hayatu har kayi girman da za ka nuna mana iko akan ƴaƴanka?” Yayarsa mace mai bin Yaya Babba wadda daga ita sai shi tayi maganar da ƙwalla a idonta “na zata za ka yi farinciki da zumuncin da muke dashi wanda mu ka ɗora ƴaƴanmu da jikoki. Kai ba abin alfaharinka bane ace ɗanka yaje neman sauƙi a wajen ɗan uwanka? Shi kuma bai bashi kunya ba ya share masa hawaye.”

    Ransa sosuwa ya yi da har suke ganin laifinsa.
    “A cikinku akwai wanda zai bar ɗansa namiji ya ɓata lokaci a jami’a yana koyon girki da yadda ake sarrafa kayan abinci?”

    “Me zai hana tunda ba haramun bane” wani ƙaninsa ya amsa kai tsaye. Wasu duk su ka amsa da za su iya.

    “Wallahi ƙarya kuke yi. Ni ban taɓa ganin namiji a arewa mai sana’ar abinci ba wanda baya abin mata.”

    “Saboda al’adar bahaushe ta mayar dashi aikin mata kaɗai ba. Amma a kudu da sauran ƙasashen duniya maza nawa ne su ka yi fice da girki kuma in ba faɗa su ka yi ba sai ka rantse ma ƴan dambe ne.”

    “Ni yanzu me kuke so daga gareni?”

    Gwaggo ta dube shi. Haƙiƙa akwai ciwo wurin iyaye idan ƴaƴansu su ka ƙi bin umarninsu. Gashi mutum mai aƙida wanda baya son ko yaya aga gazawar nasa. Kuma dole yanzu yaga kamar an haɗe masa kai. Don ko ita idan zata yi rantsuwa ta san babu kaffara da matuƙar wahala in ka cire Yaya Babba da Amma a sami mai barin ɗansa namiji ya yi wannan karatun.

    “Hayatu kaje gidan Jafaru ka ɗauko ɗanka maganar nan ta mutu daga yau.”

    “Ai nayi rantsuwa Gwaggo. Akan Taj wallahi ba zan yi kaffara ba.”

    Cikin fushi Yaya Babba yace “Nima kuma wallahi ba zan zama silar raba ɗa da iyayensa ba. Idan rashin albarka ya bishi a dalilinka duniya ni za ta zaga.”

    Gwaggo dai gajiya tayi da basu baki ta kama hawaye tana cewa don babansu baya duniya shi yasa su ke yi mata haka.

    Amma da bata ce uffan ba tun farkon zamansu ce ta katse musayar yawun da suke.

    “Gwaggo ki zama shaida. A gaban kowa duk sun yi rantsuwa ba za su zauna da Taj ba. To ni ina so kuma dashi zan koma. Zan taƙaita hutuna mu baku wuri ku sha iska.”

    Kallonta kowa ya kama yi kafin kuma mazan su nuna a gidansu zai zauna.

    “Jamila zai bi domin babu amfanin ya zauna a nan kowa yana yi masa kallon wanda uba ya kora.” Gwaggo ta kashe maganar.

    “Gwaggo ina so ki min shaidar ƙarshe. Yadda kowa baya son a shiga abin da ya shafe shi da đansa to nima kada wanda ya shigar min gonata. Zan yiwa Taj abin da zan yiwa ɗan cikina tsakani da Allah.”

    Kafin kowa ya sake magana ta tashi ta fice daga gidan gabaɗaya.

    Kamar wasa ƙaramar magana ta zama babba. Da kaɗan da kaɗan zance ya zaga zuri’ar gidan kowa ya san me yake faruwa. Wasu na goyon bayan Taj wasu na ganin laifinsa. Inna da Mama sun fi kowa shiga tashin hankali. Sai Kamal da ya kwanta ciwo sosai. Alhaji kuwa tunda Amma tace za ta ɗauke shi ya san sai abin da Allah Yayi. Bai fasa ganin laifin Mama ba akan zama mutum ta farko wajen haɗa shi da ƴan uwansa da kuma raba shi da ɗansa. Irin abubuwan da ya dinga yi mata sai da ya kaita ga yin yaji. Tana ficewa kuwa Inna ma ta kama gabanta. Butulci ne zai sa ta cigaba da miƙe ƙafa a gidan da mai son ɗanta ta kasa zama. Hajiya da Umma da basu tafi ba ba daɗinsu Alhaji yake ji ba. Abu sai da ya kai anyi zama na musamman da dangin kowannensu. An sasanta dai amma tunda Taj ya bar gidan kaso mai yawa na walwalar gidan ya kau.

    ***

    Tafiya Amerika yana buƙatar visa da dogon cike ciken takardu wanda Amma take ganin ɓacin lokaci ne. Saboda haka ta nemi visar India da passport ɗinta na ƴar ƙasa na Amerika. Nan da nan ta samu. Cikin sati biyu suka bar ƙasar. Dama Abuja ta koma dashi. Ita ta kai shi makaranta ta jira komai ya kammala bisa tsari. Zai cigaba da aikinsa a wurin Paaji a duk ranar da bashi da lecture kamar yadda ya yi lokacin degree ɗinsa na farko.

    Da za ta tafi ta kawo kuɗi ta bashi.
    “Kada ka kunyata ni. Kada kuma kayi abin da zai ƙara girmama rigimar Yaya Hayatu da Yaya Babba. Ka kiyayi duk wani abu da Allah baya so. Shi kuma ba zai bari ka taɓe ba.”

    Rufe ido ya yi yana kuka. Ta dungure masa kai “meye haka? Da Yaya Hayatu zai ga wannan kukan ai cewa zai yi abin da yake gudu ya faru.”

    Dariyar dole Taj ya yi. Ta rungume shi tana rarrashi. Duk da yaji bambarakwai amma sai hakan ya sanyaya masa zuciya.

    “Bana son ragwanta. In shagwaɓa ce dai I will indulge you amma ragon namiji baya burgeni kaji ko?”

    Murmushi yayi. A rayuwarsa zai iya ƙirga sau nawa ya haɗu da Amma. Ya san tana da kirki amma bai san halayenta irin waɗanda yake gani yanzu ba. Uwa da uba ya samu a dunkule a tare da ita. Ta ƙarfafa masa gwiwa sosai sannan ta faɗa masa zata yi ƙoƙari kafin lokacin hutu tayi duk abin da ya dace domin ya sami visa.

    Wannan shi ne mafarin zaman Taj a Amerika. Ƴaƴan Amma sun yi aure. Su suna Minnesota babbar Anisa kuma tana aure a Florida. Iman kuma a Lagos take zaune da mijinta. Yayinda maigidan yake yawo tsakanin Nigeria wurin amaryar da ya yi bayan ya yi ritaya da Amerika.

    Sai ya kasance bayan Taj ya gama karatu shi da ita ne a gidan kodayaushe. Sun shaƙu matuƙa. Tana aikinta shima yana yi awani restaurant da ya yi fice a abincin Asia da Afrika. A wurin ma’aikatan wurin ya koyo nau’ikan abincin gargajiya na Nigeria na ƙabilu daban daban. Cikin ɗan lokaci ya yi suna sosai. Takanas aka zo aka gayyace shi gasar da ta ciwo masa wasu maƙudan kuɗaɗe bayan ya sami nasarar yin na biyu. Da kuɗin da kuma tanadinsa tun na India yake son buɗe mall a Kano.

    Rashin zuwansa gida bai hana shi mu’amala da ƴan uwansa da iyaye ba. Musamman yanzu da aka sami cigaban hanyoyin sadarwa. Suna yawan bidiyo call ana ganin juna musamman yayin aure da haihuwa. Alhaji ne kaɗai baya ɗaukar wayarsa har yanzu. Amma ta tilasta masa tura masa saƙon gaisuwa kullum rana ta Allah na kar ta kwana. Sai dai da yake zuciya bata da ƙashi, ya riƙe uban a zuciyarsa. Ya ɗora masa alhakin raba shi da ahalinsa. Da nesanta fuskarsa da ta mahaifiyarsa. Shi yasa ya ƙudurcewa ransa ba zai sake taka gidansu ba sai Alhaji ya neme shi da kansa.

    ***

    Hutu ya ƙare lafiya. Ranar da ƴan makarantar kwana za su koma Hamdi bata samu ta runtsa ba. Tana fama da tararrabin yadda Ummi za ta kwance mata zani a kasuwa. Duk siyayyar da Abbanta ya yi mata babu abin da ya burgeta. Rashin fara’arta ya dami Yaya har sai da ta kai ga yi mata magana kafin Abba ya kaita tasha.

    “Sai da aski ya zo gaban goshi nake ganin alamun rashin son komawa a tare dake Hamdi.”

    Zee ma ta ce “Ya Hamdi ko kukan bodin za ki fara a term ɗin ƙarshe? In faɗawa Abba a dawo dake makarantarmu?”

    Duka Hamdi ta kai mata da wasa a ƙoƙarinta na danne damuwarta. Bayan fitar Zee daga falon Yaya ta muskuta kusa da ita.

    “Hamdiyya.”

    “Na’am” ta amsa a raunane.

    “Na san baki so zuwan iyalin Maje gidan nan ba tunda aka zo da Ummi.”

    A zabure ta kalli Yayan da tsananin mamaki. Ita kuwa tayi murmushi.

    “Kina mamakin yadda aka yi na sani?”

    Ta gyaɗa kai.

    “Kin guji gida saboda kada a san waye mahaifinki. Yanzu kuma gashi an zo an ganshi har gidan kina tsoron kada asirinki ya tonu.”

    “Yaya…” ta soma faɗi cike da kunya.

    “Ki koyi son abin da Allah Ya baki sai Ya ninka miki da wanda baki zata ba.”

    Yawu ta haɗiya “to.”

    Yaya ta cigaba da cewa “Ban taɓa nadamar auren mahaifinku ba saboda bai bani wannan dalilin ba. Irin kulawar da muke samu daga gare shi wasu masu kuɗin sai sun yi kishi da mu. Zaman lafiya yafi zama ɗan sarki. Hamdi sandar hannunka da ita kake duka kin ji. Hangen ta hannun wani ba naki bane don baki sani ba ko duk ƙaya ce ko bata ma da ƙwari.”

    Numfashi ta sauke ta sadda kai ƙasa ta bawa Yaya haƙuri. Ita kuwa da yake ba mace bace mai riƙo ko son ayi ta nanata zance sai cewa tayi a bar maganar.

    To a haka Abba ya dawo shabiyun rana ya sanar dasu Baba Maje na nan tafe zai kai su makaranta tare da Ummi. Ya ƙare da faɗin,

    “Tare zamu tafi.”

    Albarkacin Yaya dake zaune a wurin da nasihar da tayi mata ɗazu ne kawai ya hanata fasa ihu. Ta rasa inda zata tsoma ranta taji daɗi. Addu’a kawai ta kama yi Allah Ya kawo sanadin da zai fasa binsu don gudun kada ya dinga sakin baki a gaban Ummi.

    Addu’arta ta ƙarbu domin an fara zuba kayanta a motar Baba Maje sai ga wani dattijo yana sallama da Abba. Kana ganinsa baka buƙatar ƙarin bayani za ka gane ba mutumin kirki bane. Shadda ce yellow shar a jikinsa tana uban ƙyalli ga hula ya harbo gaban goshi irin na tsofaffin ƴan duniya. Taunar cingam yake cakakal-cakakal yana karkaɗa muƙullin mota. Ga wata uwar yatsina yana faman yi a yayinda idanunsa ke ƙarewa layin gidan kallo.

    “Maje anya ba za ku tafi ba kuwa? Ban san me ya kawo shi ba amma ina jin ba abu bane da zamu ƙare da wuri.”

    “Ba dai abokin sana’arka bane ko?” Baba Maje ya tambaya don yanayin mutumin babu sha’awar son kusanci da shi.

    “Agent ɗin wanda nake hayar gidan abincina ne.”

    “To ko dai mu jira?” Baba Maje ya sake cewa da ƴar damuwar yadda yaga abokin nasa kamar baya cikin nutsuwa.

    “A’a, ku tafi kawai.”

    Godiya ya yi masa akan biyowa ɗaukar Hamdi sannan ya juya wajen mutumin su kuma su ka shiga mota.

    Akan hanyarsu Baba Maje yayi ta ƙoƙarin haɗa hira tsakanin Ummi da Hamdi. Da yake Ummi akwai wayo sai ta fishi jan Hamdin a jiki. Ya kuwa ji daɗin hakan sosai.

    Abba da baƙonsa kuwa ba komai su ka tattauna ba illa ƙarin kuɗin haya da aka yiwa gidan abincin nasa. Kuɗin ya yi biyun abin da yake biya. Ya fara roƙon alfarma mutumin ya ce sai dai ya tashi. Dama kuma ya samo mai biyan wannan farashin ne. Ya kuma san babu yadda za ayi Abba ya biya. Shi ne ya zo masa da dabara.

    “Idan na tashi yaya zan yi da iyalina? Don Allah ka rage min wani abu.”

    “Sati biyu zan iya baka ka tattare komatsanka ka tashi. Idan kuma kuɗin sun samu kafin nan sai ka kawo a sabunta kwantiragi.”

    Yana gama faɗin haka ya shige motarsa ya tada ƙura ya bar unguwar. Abba ya koma gida da sanyin jiki ya labartawa Yaya halin da ake ciki.

    ***

    “Ki fara kai min nawa kayan ɗaki don akwai abin da nake buƙata yanzu a ciki.”

    Ko minti biyar Baba Maje bai yi da barinsu da kayansu da za su kwashe su kai hostel ba Ummi ta rikiɗa ta koma annobar ƴan FGC.

    Wani irin kallon mamaki Hamdi ta bita da shi “ban gane ba.”

    “Au…kin daina jin hausa ne saboda mun shigo school? To jirani a nan. Zan aiko miki da yaren da za ki fahimta.” Da tafiyarta ta ƙasaita ta wuce ta bar Hamdi a tsaye.

    Ita kuma ganin ta tafi ta fara ɗaukar kayanta ta nufi hostel ɗinsu. Tana ajiyewa ta koma da sauri domin ɗebo sauran sakamakon garin da hadari saboda damina da ta tsaya sosai. Da isarta ta iske wata yarinya da ta tabbatar cikin ƴan koran Ummi take. Wata tsadaddiyar waya ta fito da ita daga ƙasan hijab ta yafito Hamdi da hannu. Da taga bata matso ba kawai sai ta danna wayar. Nan da nan wurin ya karaɗe da muryar Abba inda yake cewa (Altine kece haka? Ikon Allah) da muryar nan tasa da ko ita ƴarsa bata so.

    Hankalinta ya yi masifar tashi. A take ta jiƙe da wani irin gumi. Ta miƙa hannu a firgice za ta karɓe wayar sai yarinyar ta ja da baya.

    “Ummi ta ce ki kwaso mata kayanta idan ba haka ba duk makarantar nan kowa sai ya gani”

    “To” ta amsa da sauri tare da duƙawa ta fara ɗaukar kayan.

    Yarinyar ta yatsina fuska “no, ta ce da ɗai-ɗai za ki ɗauka.”

    “To” Hamdi ta sake amsawa da rawar jiki.

    Banda akwatuna biyu akwai manyan ledoji uku. Haka tayi sawu biyar tana zuwa hostel ɗin su Ummi. Bata ganta ba sai da ta kai ledar ƙarshe ta sameta zaune akan gadonta.

    “Ina za ki baki jera min ba?”

    Cak ta tsaya ta dawo da sauri ta jera kayan a kwanar Ummin. Ƴan ɗakin su ka zuba musu ido suna ganin ikon Allah. Bayan ta gama a gadarance Ummi ta ce mata gobe ta zo da wuri ta ɗebo mata ruwa. Ta amsa kawai ta fita.

    Da ta fita ko ganin hanya bata yi saboda hawayen da ya cika mata idanu. Da haɗa hanya ta isa inda sauran kayanta su ke ta kwaso. An soma yayyafi ga iska mai ƙarfi. Saboda haka akwatin da jakar sun yi buɗu-buɗu. Zuciyarta a ƙuntace ta tafi nasu hostel ɗin. Ajiye kayan kawai tayi ta hau gado ta dunƙule jikinta tana kuka. Nan da nan wurin ya cika da mutane ana tambayarta me yake faruwa amma ko ɗago kai bata yi ba. Sai wata ce da taga yadda ta dinga ɗiban kayan Ummi ta basu amsa.

    “Wannan hutun da alama ita Ummi Maje za ta takurawa.”

    Alhini da tausayi su ka dinga nunawa bayan ta faɗa musu me ta gani. Abin bai yi musu daɗi ba domin kuwa Hamdi bata rigima.

    “Lallai Ummi bata da sauran rabo don ko mu masu baki da take zalinta bamu yafe ba balle mara baki irin Hamdiyya.”

    Wadda tayi maganar tana rufe baki wata ma ta kama. Su ka taru su ka gama ɗebe mata albarka (mu guji irin waɗannan laifukan da bama ɗaukarsu a bakin komai. Babu wani haƙƙi abin rainawa) sannan su ka watse.

    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    Note
    error: Content is protected !!