Rayuwa Da Gibi – Chapter Nineteen
by NadminMASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
Snacks lodi guda jere akan trays Zahra da Salwa su ka dinga shiga dasu falo. Komai da zafinsa saboda yanzu aka soya. Sai sassanyan zoɓo da kunun aya sun sha ƙanƙara a cikin jugs.
“Zahra mun tayar dake tsaye ba notice ko? Da ba ki wahalar da kan ki ba. Yanzu mu ke shirin watsewa.” Cewar Ya Zulaiha.
Zahra tayi murmushi “ko yaya dai ya kamata ku ci. Abinci na so ɗorawa sai Salwa ta bani shawarar sayen frozen snacks daga Happy Taj.”
Zahra ta nuna Salwa ta sha mayafi “kin ganta nan tana dawowa ko zama bata yi ba ta hau suya. Da kun tafi ma sai an bi ku dashi har gida.”
Kowa dariya ya yi banda Ahmad da ya maka mata harara. Sai kuma Kamal da Taj da su ka kalli juna. Kamal ya yi dariyar tsokana don ya san ran Taj bai so ba.
Ya Hajiyayye tana shan zoɓo ta ce “Mungode sosai. Sai ku fara shiri ku ma. Baƙon gidanku ya yi aure yau.”
Kallon neman ba’asi Zahra ta yiwa Ahmad. Shi kuwa Salwa da ta tsaya cak yake kallo. Rawar kanta da baya so tayi yawa. Amma duk da haka sai yaji tausayinta ya tsirgs masa kafin ya iya bawa matarsa amsa.
“Taj aka ɗaurawa aure bayan sallar juma’a.”
Ita ma Zahran da yake ta gama harbo jirgin Salwa sai da gabanta ya faɗi. Ta waiga gefenta da sauri amma bata ga Salwan ba.
Ashe Ahmad na ambaton auren Taj ta bar wajen a guje.
“Me ya sami Salwa?” Wajen mutum uku su ka tambaya a tare.
Zahra sai ta faɗi abin da ya fara zuwa bakinta “ai kuwa samosa ta bari akan wuta.”
Da sauri tabi bayanta har ɗaki. Da shigar Salwan ta banko ƙofar da sauri ta murɗa muƙulli. Kan gado ta faɗa ta riƙe ƙirji. Kukan da take tunanin yi yaƙi zuwa. Sai ajiyar zuciya kawai da wani irin zafi a ƙirji.
“Ana wata ga wata” Zahra ta faɗi tana juyawa.
Ahmad ta gani a bayanta. Fuskar nan tasa babu salama. Tare gabansa tayi kafin ya fara buga ƙofar.
“Don Allah ka barta taji da abu ɗaya.”
“Wane irin rashin aji ne wannan Zahra? Ke haka kika yi?”
Bayansa ta kalla “Rage muryarka don Allah kada a ji.”
Kamar bai ji me ta ce ba ya cigaba da faɗa.
“Duk ta bi ta dami kanta akan wanda bai ma san tana yi ba. Da ta san da yadda yayi wannan auren ma sai ta godewa Allah. Na riga na faɗa mata da wuya Alhaji ya yarda ɗansa ya auri ƴar Mami.”
Tura shi Zahra tayi don maganganun ta tabbata za su ƙarawa Salwa zafi akan abin da take ji. Duk soyayyar da bata sami haɗin kan zuciyar da take muradi ba, abar a tausayawa ce. Lokacin da tayi ta dakon son Ahmad ta sha wuya. Allah ne Ya taimaketa ashe shima yana sonta. Ranar da ya faɗa mata sai da tayi sadaka mai kyau saboda farinciki.
Ƙanana cikin matan ne su ka wanke duk abin da su ka ɓata sannan aka gyara falon kafin su tafi. Zahra ta so su bari domin dai ƴan uwan mijin nata in baka yi bani wuri ne. Kowacce tana ji da boko da gayu. Don ko kina gama secondary aka aurar dake to fa Alhaji zai yi da wajewa da mijin. Ƴarsa dole tayi karatu kamar yadda ya yi. Aiki ko kasuwanci ko zaman gida kuma zaɓin mijin ne idan ta gama.
Yadda su ka zo haka su ka tattara su ka tafi gida domin ganawa da iyayensu. Taj kawai aka bari ya shige ɗakinsa ya kwanta. Addu’a kawai yake yi Allah Ya basu ikon yi masa uzuri kada laifinsa ya yi yawa. Zuwa Abuja already ya kama shi. Ya ma ƙudurce a ransa ba zai ɗauki wayar Amma ba ko ta kira. Gara su haɗu kawai ayi ta ido da ido.
Abin farinciki shi ne irin tarbar da iyayen su ka yiwa zancen.
“Nan da ku ka taho a ayari kun zo yi mana kwarjini ne? Alhaji ya riga ku fasa ƙwan. Har mun fara shirin biki.” Umma ta faɗi tana dariya.
Kamal ya ce “Tunda baku yi fushi ba mu ai Alhamdulillah.”
Kafin su watse Hajiyayye ta sake tado maganar lefe bayan iyayen sun tashi.
“Bishir kai zan bawa aikin buɗe mana sabon group a whatsapp. Sai a sake maganar a gaban waɗanda basu zo yau ba. Kada ka sako mana Taj dai kaji ko?”
Murmushi ya yi akan maganarta taƙarshe
“Zan kiyaye. Yanzu mece ce shawararki yadda idan na buɗe kawai zan rubuta inda aka kwana sai kowa ya faɗi ra’ayinsa.” Kowa ya yi na’am suna saurarenta.
“A nawa ganin ko sisi kada Taj ya kashe da sunan lefe. Na sani cikin gidan nan babu wanda bai mori arziƙin Taj ba tun baya gari. Mu da ƴaƴanmu kullum cikin hidima yake damu. To lokaci ya yi da za a ramawa kura aniyarta. So nake ayi lefe na kece raini amma babu kuɗin ango. Ya ji da muhalli da sauran abubuwan da su ka sauwaƙa kawai.”
Abinka da gidan yawa. Amincewar tasu kaɗai sai da ta kawo amsa kuwwa a falon. Wai a haka ma don mata sun fi yawa. Sun tsayar da shawarar yadda Bishir zai tsara jawabin. Sai kuma a bawa kowa damar faɗin me zai kawo daidai ƙarfi.
Wasu don zumuɗi tun kafin a tashi su ka fara faɗin nasu. Haɗin kansu gwanin ban sha’awa. Ɗakin Mama yafi kusa da inda suke zaune saboda haka taji duk abin da su ke cewa. A zuciyarta ta raya lallai wannan zaman lafiya da ƙullewar zumunci tsakanin matan gida da ƴaƴa shi ne mafi girman arziƙin Alhaji. Ba don haka ba da tuni gidan yafi ƙarfin duk wani zafin rai da tsare girarsa.
***
Yawan mutane ƴan Allah Ya sanya alkhairi a gidan ya mantar da Abba damuwar da ya tsinci kansa ɗazu a dalilin Alhaji. Murna ake taya shi da zuciya ɗaya. Cikin hikima ta Allah ya aurar da duka ƴaƴansa ba tare da tsumi ko dabararsa ba.
Amaren ne ma dai Sajida ce kawai take walwala. Zee kuka, Hamdi kuwa ba a cewa komai. Tana can ɗakin Halifa ta rufe ƙofa tana fama da ciwon kai saboda uban tunani. Dukan ne goma da ɗari ba ma ashirin ba. Ita ta sani sarai cewa haɗuwar farko ta kamu da son Taj. Irin son nan mai shigar farat ɗaya. A haɗuwarsu ta biyu lokacin ta tabbatar da gaske zuciyarta take. Sai gashi haɗuwa ta uku da ya dace su yi musayar zuƙata ya zo ba a yadda take so ba. Tarin ƙaunar da take masa take ta bi iska saboda sana’arsa. Kuma don abin haushi bai tsaya a nan ba shi ne harda sake dulmiya mata uba cikin sana’ar da tafi tsana. Me namiji zai yi da girki don Allah? Ita mace da tun ƙuruciya ake horata da ayyukan gidan miji da girki ake farawa. Komai manya za su ce game da aure da maganar ɗa’ami suke farawa ko su ƙare. Sai dai kaji ana kiran tsafta, iya kwalliya, ladabi da biyayya…sannan uwa uba girki. Shi fa girkin nan sai an ƙara masa UWA UBA saboda mahimmancinsa. Shi ne zai zo ya koya har ma ya fita iyawa. Don tayi imani girkinsa da nata zai sha bambam. Ya riga ya ƙwace abin tinƙahon da taƙamar. To ita me za ta yi? Shara da wanke-wanke?
Muskutawa tayi tana sauke numfashi da ta tuna rashin kunyar da tayi masa rannan da irin abubuwan da ya ce mata shima. Ba shiri ta tashi ta zauna tana sakin murmushi.
“Da kansa ma zai sakeni tunda ba sona yake ba.” Ta faɗawa zuciyarta.
Da wannan tunanin taji wani irin kuzari na shigarta. Tunda Sajida tayi aure ai nata ba dole bane. Salin alin za su rabu. Haka kawai ba za ta iya rayuwar uba girki, miji girki ba. Duniya ma sai tayi mata dariya. Abin da tafi gudu da ƙi ace shi ne a tare da ita muddin rai? Inaaaa!
Kamar ba ita ba ta fito tsakar gida. Ana ta taron yinin Sajida. Ita da Zee taji ana cewa tunda ko kamu ba ayi musu ba, za a jira mazajensu su faɗi lokacin da su ke so su tare. A zuci tayi dariyar sai dai su kai Zee ita kaɗai. Sai ta kalli Zee ɗin. Idanunta luhu luhu sun kumbura. Tayi zuru zuru ba a buƙatar likita wurin gane bata da lafiya. Tausayin ƙanwar ya kama ta. Gashi tana ganin wannan auren mai raba shi sai Allah. Irin amincin gidajen nasu biyu da soyayyar da aka ce Baballe na yiwa Zee bata hango mata fitowa ba.
Da su ka shiga ɗaki, dafa ta tayi cikin rarrashi ta ce “Allah Sarki Zee. Allah Ya sanya soyayyar Baballe a ranki. Na kula yana da mutumci da sanin darajar mutane.”
Zee ta sake fashewa da kuka “kema kin ga babu alamun auren nan zai rabu ko? Yaya zan yi?”
“Ki kwantar da hankalinki. Bawa bai isa ya ƙetare ƙaddararsa ba. Wani ba ya auren matar wani. Yanayin yadda aka yi auren kaɗai ya ishe ki ishara.”
Kasaƙe Zee tayi tana sauraron nasihar Hamdi kafin tayi magana.
“Ke baki da matsala kenan da auren? Kodayake me zai sa ki ƙi Taj? Nima ba don abin da Ummi ta yiwa Abba a school ɗinku ba da na haƙura.” Wayarta ta miƙawa Hamdi “kin gani. Tun ɗazu yake ta turo min message.”
Saƙonnin har guda shida duk abu guda biyu su ke ɗauke da shi. Na farko haƙuri Baballe yake bata akan rashin sanar da ita da neman yardarta. Na biyu kuma yana jaddada mata ba auren alfarma bane tsakaninsu. Sonta yake. Kuma yana fata za ta bashi dama ya koyar da ita son shi ita ma.
Murmushi sosai Hamdi tayi. Bata taɓa sanin soyayya za ta burgeta ba a zahiri sai yanzu. Da alama Baballe zai yi saurin siye zuciyar Zee ta ce a ranta. Tsarin kalaman sun taho da rarrashin da mai karatu zai ji a jikinsa. Ai dole ma ta rabu da Taj. Ko don rashin irin wannan text ɗin na Zee da wayar da Safwan ya yiwa Sajida ɗazu yana ƙara bata haƙurin abin da ya faru.
“Allah Zee kada ki tada hankali da yawa. Na san irin auren nan babu daɗi. Amma ki godewa Allah da mai sonki aka haɗaki. Kuma kina ganin yadda Abba da Yaya ke ta murna. Yawan kukan zai sa su ji babu daɗi.”
Sajida ce ta shiga ɗakin a lokacin. Ta kalli ƙannen nata tana murmushi.
“Su Hamdi malaman aure. Irin wannan huɗuba haka? Ko dai dama soyayya ku ke da Ya Taj bamu sani ba?”
Idanun Hamdi hango mata Taj su ka yi a gaban tukunya sai taji tsigar jikinta na tashi. Wannan aure ba da ita ba. Ba dai za ta iya labartawa ƴan uwanta niyyarta bane saboda kada yanzun nan su kaita gaban iyayensu.
“Gani nayi an riga an ɗaura. Gara mu haƙura kawai. Kukan ciwo zai sa mata.”
“Da gaskiyarki. Amma ni ke ce damuwata. Jiya da baki san da naki auren ba sam baki da damuwa sai tamu. Yau kuma an ɗaura naga kin yi saurin haƙura kamar ba ke ce ki ka suma ba ɗazu… Don Allah mene ne tsakaninki da shi?”
Da Sajida da tayi tambayar, da Zee idanu su ka zuba mata. Tana son gilla musu ƙarya amma ta rasa wadda za ta fi dacewa. Allah ne Ya taimaketa ƴan matan danginsu su ka shigo ɗakin ana tsokanar amare. A dalilin Abba dukkaninsu basu da wasu ƙawayen kurkusa da su ke shawara dasu. Su ne dai ƙawayen juna sai cousins ɗinsu.
Gabanin Magriba da baƙi su ka sarara ne Hamdi ta shige ƙuryar ɗakinta da wayar Sajida da tata a hannu. Numbar Taj ta kwafa ta gama karanto addu’o’in neman nasara ta kira shi.
***
“Happy kana ganin ka kyauta kuwa? Duk fa irin yadda Yaya ya damu da mu ita ma Salwa jininsa ce.”
Kamal ne yake yi masa wannan tambayar a yayinda yake shiryawa zai je ɗaukan Abba su je wurin Alhaji. Yadi ne ya saka mara nauyi ruwan bula mai kyau. Rigar tasa kaɗan ya rage ta ƙarasa gwiwa. Hannunta kuma ya ɗan zarce gwiwar hannu kaɗan. Aikin wuyan da aljihu da aka yi ruwan madara ba mai yawa bane. Hula ya ɗora a kansa lokaci guda ya zama kamar ba shi ba. Ya yi kyau sosai. Sai da ya gama fesa turare sannan ya juya ya fuskanci Kamal.
“Ya kake so nayi da ita? Me ma nayi mata? Banda na bi shawararka ka san Allah da ko text ɗin da take yawan yi min ba zan kula ba.”
“Na sani. Amma yanzu da ta shige ɗaki tun ɗazu ya dace ka kirata ka ɗan rarrasheta.”
Taj ya ware idanu “in yi me? So ka ke tayi zaton aurenta zan yi? Gaskiya Happiness ka rage sauƙin kai. Zai iya kai ka ya baro.”
“To ko Yayan ka ɗan yiwa magana mana. Sharewa kamar baka san komai ba fa ba daidai bane. Please.” Kamal ya ce da damuwa. Baya son rigima irin wannan ta cikin gida. Su duka ƙannen Ahmad ne. Amma ana iya samun dalilin da zai sa Ahmad ɗin ya zaɓi ɓangare guda ya ƙuntatawa ɗayan.
“Yanzu dai bani key mu je. In na dawo zan yi masa magana in sha Allah.”
Da murmushi Kamal ya ce “ko kai fa.” Sai kuma ya sako wani zancen “Goben dai za ka tafi Abuja?”
“In sha Allahu. In Amma ta tsine min tas za ta bini. Gara naje na daidaita da uwata.”
“Ba ka yi fushi ba dai da na ce ba zani ba ko?” Kamal ya faɗi yana sosa ƙeya.
Ƙwafa Taj ya yi “Kaf ɗinku na san zaman da nake da ku. In matan suna da mazaje ai ku za ku iya zuwa. Amma har Naja da Rukky dake Abuja duk sun zame wai babu mai zuwa rakani.”
“Naja fa ta ce za ta turo a ɗaukoka daga airport.”
“Wannan ma laifi zai zama a wajen Amma. Cewa za ta yi wato har na fara neman ƴan uwana na barta.”
“Allah Ya fito da kai lafiya. Daga nan zan taya ka addu’a. In kaje dai ka gaishe da Anisa.” Yana dariya ya yi maganar.
Wata kwafar Taj yayi don ya san tsokanarsa yake. Shi ya tuƙa motar. Suna hanya yaji wayarsa tana ta ringing. Idan kiran ya katse a sake binsa da wani. Bai ɗauka ba sai da ya tsaya a danja kafin a bada hannu. Baƙuwar lamba ya gani. Kira har huɗu a jere dole ya bi.
Hamdi na ganin sunansa da hasken waya ko ringing bata fara ba ta ɗauka.
“Assalam alaikum wa rahmatullah” ta faɗi da ladabin da ya bawa Taj mamaki. Shi da ya sa rai da tsiwa da rashin kunya. Har ya gama tanadin yadda zai ɓullo mata. Sai gashi tana yi masa gaisuwa irin wannan. Haka kawai zuciyarsa ta hana shi soma murna. Gara yaji da me ta zo. Hamdi ce fa. Wadda ta faɗa masa ƙiri ƙiri bata son sana’arsa.
Basarwa ya yi ya ce “Wa alaikum salam. Wa ke magana?”
“Ya Taj ni ce. Hamdi ce. Don Allah magana nake so mu yi” Ta wani ƙara sauke murya ita a dole mutuniyar kirki.
“Ina tuƙi yanzu. Idan na tsaya zan kira ki in sha Allah.” Duk da idan ya so zai iya sanya earpod ɗinsa ya amsa wayar, jikinsa ya bashi dalilinta na nemansa. Shi yasa ya katse mata hanzari.
“To babu komai. Nagode. Nagode. Zan jira ka don Allah.”
Jira ya yi ta kashe wayar kafin ya soma dariya. Ya labartawa Kamal rigimarsu ta ranar buɗe Happy Taj da kuma randa ya koma gidan.
“To dai mata sai da lallaɓawa. In kana son shawo kanta sai ka ajiye taka rigimar.”
“Ashe ba za mu daidaita ba. Kallo ɗaya nayi mata na gane rigimammiya ce. Tana yi min zan rama don gidan abin ta zo.”
Da takaici Kamal ya kalle shi “Kai Happy. Matarka ce fa kuma yarinya ba abokiyar faɗa ba. Ko ina sai ka nuna hali ne?”
“Take takenta kamar cewa za ta yi na saketa. Haka jikina yake bani. Ni kuma wallahi sonta nake kamar babu sauran mata a duniya.” Ya ƙare magana yana kanne ido.
Shi ma Kamal da shaƙiyanci ya ce “Shege…mutumin ya fola tsundum. Allah Yasa kada Alhaji ya kawo cikas dai kafin mu kwashi ƴaƴan love.”
“Za ka yi bayani. Bari dai hankalina ya dawo jikina in mun shirya da Amma. Ko da duka ne sai ka fađa min sunan budurwarka. In kuma babu sai muje wajen Baba Malam (yayan Inna) ayi maka ruƙiyya. In ma wata jinnu ce ta ƙyasa ayi waje da ita.”
“Aljana sai dai a kanka. Ni kam ƙalau nake.”
“To in ba tsoro ba ka faɗa min. Idan kuma kasa ka aka yi ne gara na sani. Sai na baka tips na shawo kan ƴan mata. Ka san mu masu auren nan komai mun sani.”
“Daga ɗaurawa? Ka rufa mana asiri dai kada ƴar mutane ta tare da ciki.”
“Sai kace wani namamajo” Taj ya sha kunu.
“Da meye?”
Da irin wannan faɗan nasu na wasa su ka isa gidan Abba. Idan ka kallesu sau ɗaya dole ka ƙara. Alhaji ya tara arziƙi a gidansa. Ba mazan ba, ba matan ba. Shi kan shi ya san wannan.
Waya Taj ya yiwa Abba bayan sun fito daga motar. Ba a jima ba kuwa ya fito da shirinsa harda babbar riga.
“Ko shigo ciki ku gaisa da mutan gidan mana. Dama can an zama ɗaya balle kuma yanzu. Kuma mazajen ƴan uwanta ma sun zo. Sai ku san juna ko.” Ya nuna ƙofar yana murmushi.
Bayansa su ka bi Taj yana sunne kai shi a dole ya shiga gidan surukai. Kamal ya faki ido ya ɗauke shi a hoto ya adana domin duk ranar da ya bashi haushi ya tura group ɗinsu na gida.
*
Hamdi na zaune da waya a hannu tana jiran kiran Taj a ɗakin Halifa ita kaɗai. Falonsu kuma Safwan ne da abokansa biyu. Sai kuma Baballe da iyayensa. Ga Yaya da amare Sajida da Zee. Tsakar gidan kuwa ƴan uwa ne na kurkusa su ke ta aikin kayan miya na girkin gobe saboda sun san dole a sake zuwa kafin ƴan ɗaukar Sajida su zo. Musamman waɗanda basu ji auren Hamdi da Zee da wuri ba.
Abba ya shiga falon da sallama aka amsa. Taj da Kamal su ma su ka yi. Yaya jan mayafi ta ƙara yi. Bakinta har kunne. Duk yadda take son nuna kunyar surukai abu ya gagara. Allah Ya gatance mata a lokacin da bata yi zato ba.
Musabaha su ka yi da duka mazan. Sannan su ka gaisa da Iyaa da Yaya. Abba ya sake gabatar musu da juna.
“Safwan ai ka san Taj ko?”
Safwan ya yi murmushi “sosai Abba. Tun kafin ya dawo ma ta haɗa mu. Abokina ne ko in ce ɗan uwa ma.”
Sajida ta sunne kai tana murmushi. Safwan ɗin dama ɗan ayi ne na gaske.
“To ina jin duka dai Baballe ne baku sani ba. Sunansa Abubakar kuma ɗan amini na ne.”
Baballe ya taso ya sake basu hannu.
“Ni ne dai ɗan autanku. Ina fata zamu yi zumunci mai ɗorewa.”
Iyaa taji daɗin yadda ɗan nata ya yi. Sai da ta yi dariya da Safwan da Taj su ka ce sun ɗauki girman. Aka ɗan yi raha sannan Baba Maje ya juya dama da hagu.
“Ina Hamdiyya ne? Mijinta ya zo ba za ta leƙo su gaisa ba?”
“Yi maza ki kirata Zee.” Iyaa ta faɗi ganin Yaya ta sunkuyar da kai.
A ɗakin Halifan ta sameta. Ta rasa gane zaman me take yi ita kaɗai bayan ta nuna musu ita bata da damuwar auren.
“Ki zo ku gaisa da Ya Taj. Amma ki yi sauri don fita za su yi da Abba.”
Kafin Zee ta gama magana ta fice da ƙaton hijabin da tayi sallar magariba. Falon ta shiga da sallama. Idanunta Taj su ke nema. Shi ma kuma ƙofar yake kallo. Su ka haɗa ido ta kasa yakice nata.
Tabbas Taj ne mafarkinta, amsar addu’arta kuma zaɓin zuciyarta. A wannan ɗan taƙaitaccen kallon makaman yaƙin neman sakin su ka fara saukowa ƙasa da kansu. Buɗar bakin Inna Luba da shigarta falon kenan sai cewa tayi.
“Mu dai Tajo idan mun zo ɗakin amarya ba girkinta za mu ci ba. Ranar zagewa za ka yi ka girka min don ni ce da gidan ba ita ba.”
Dawowa daga duniyar da taso mantar da ita waye Taj tayi. Ta kuwa tura baki tana kumbure kumbure. Shi kuwa dariya ma ta so bashi. Yana ta lura da rikicikin yanayin dake bayyana a kyakkyawar fuskarta. Wani irin farinciki na shigarsa. Wannan yarinyar matarsa ce. Bai san lokacin da ya yi murmushi ba.
“Ku je daga soro ku gaisa mana kafin Habibun ya fito.” Baba Maje ne ya yi maganar. Hamdi bata ɓata lokacin bin umarninsa ba saboda son samun damar yiwa Taj magana.
Ita ta fara zuwa soron kafin ƙamshin Taj ya yi masa iso. Ƙasa ta durƙusa da ya shigo don so take kawai a yita ta ƙare yanzu.
“Ina wuni Ya Taj?” Ta furta cikin sabon salon ladabinta gare shi.
“Lafiya ƙalau. Tashi mana.”
Ƙin motsawa tayi “dama haƙuri nake son baka akan rashin kunyar da nayi maka rannan. Don Allah ka yafe min. Wallahi ba hali na bane.”
‘Irin wannan ladabin na neman buƙata ne’ Taj ya ayyana a ransa. A fili kuwa cewa ya yi “ya wuce. Nima ki yi haƙurin abubuwan da na ce miki.”
“Babu komai wallahi.” Ta ce da murmushinta.
“Uhmmm, dama…na ce…dama…wai ko za ka…uhmmm” ta dinga in’ina saboda kalmomin sun ƙi haɗuwa.
Shi yasa ta so su yi maganar a waya. A haka duk yabi ya yi mata kwarjini. Kamal ne ya fito a lokacin.
“Happy ga Abba nan. Ya ce kada lokaci ya ƙure.”
Taj ya dubeta. Duk tayi laushi. Fuskarta kuma tayi fayau da alama tayi kuka.
“Zan kira ki in sha Allah. Kamar ƙarfe nawa ki ke kwanciya don kada na tashe ki?”
“Zan jira ka. Don Allah ka kira.”
“Okay.” Har zai fita yaji ya dace ya ɗan bata assignment ɗin da zai sa tayi tunaninsa ko bata so “aapna khayal rakhna.”
Ai kuwa a take ta ɗinke fuska. Taj ya kalleta ya saki murmushi. A babu yadda ta iya dole ta mayar masa tunda tana da buƙata a wajensa. Da ta koma ciki maimaita kalmar kawai take yi tana addu’ar kada Allah Ya kawo ranar da zai zage ya yi rawa da waƙa kuma.
***
Kamal ne ya sanar da Alhaji zuwansu. Daga nan ya yi tafiyarsa ɗaki. A gajiye yake sosai. Ga wata yunwa da bai ma san yana jinta ba sai da ya shiga gida. Agogonsa ya kalla bayan ya cire. Ya san a ƙalla yana da minti shabiyar kafin su gama tattaunawa. Don ba zai iya baccin ba tare da sanin me zai faru da ƙaninsa ba.
Ledar wasu magunguna ya ɗauko daga ƙarƙashin gadonsa. Ya ɓalli iya wanda yake buƙata ya zuba a wata ƴar roba sannan ya fita zuwa cikin gidan domin samun abin da zai ci.
A waje kusa da gate inda Taj ya yi parking Alhaji ya zaɓi ganawa dasu. Gashi dare ne. Kuma lokacin zafi. Sannan wurin akwai shuke shuke. Saboda haka sauro ya far musu. Abba ya lura Taj a takure yake.
“Da ka sani ka barni na taho ni kaɗai Taj. Yanzu haka ma Alhaji yana iya jin babu daɗi in ya ganmu tare.”
“Idan ka ɓata amaryata ba za ta yafe min ba.” Salati ya kama a jejjere “Abba tuba nake. Ba da kai nake ba.”
“Kaji nayi magana?” Dariya su ka yi tare.
“Abba ko mu koma mota ne? Sauron nan yanzu sai ya tayarwa mutum da maleriya.”
“Kai Taj, maleriyar ma tashi take?”
Da gaskensa ya ce “ni dai tawa tashi take. Tunda na dawo bana jimawa ban yi zazzaɓin nan ba.”
Da damuwa Abba ya ce masa “kayi a hankali. Ba a sakaci da lafiya. Mataki za ka ɗauka don shi dai sauro bai san mutumci ba.”
Dariya su ka sake yi a lokacin da Alhaji ya doso inda su ke. Ya kuwa murtuke fuska saboda baƙinciki. Yaushe rabonsa da hira da Taj wadda za ta saka su dariya haka? Ya ma rasa da wanda zai yi sai Habibu.
Duƙawa Abba ya so yi tunda ya fuskanci Alhaji na ƙyamar taɓa shi sai Taj ya taro shi da sauri.
“Ai kun gaisa ɗazu.”
“Yawan gaisuwa ai yafi yawan fađa Taj.” Abba ya ce sannan ya dubi Alhaji “barka da dare Yaya Hayatu.”
“Hmm” kawai ya ce daga maƙoshi a matsayin amsa sannan ya ce Taj ya basu wuri.
Ba don ya so ba ya tafi. Zuciyarsa tana ta fama da wasiwasin kada ya barsu Alhaji ya sake yi masa abin da yafi na ɗazu.
Gyaran murya ya yi bayan tafiyar Taj ya yiwa Abba duba na ƙyama.
“Habibu!”
“Na’am” ya sadda kai yana sauraronsa.
“Ina son Tajuddin. A cikin ƴaƴana ma ban haɗa ƙaunarsa da ta kowa ba. Abin da ya shiga tsakaninmu har na kore shi bai rage min son abuna ba.”
Murmushin jindaɗi Abba ya yi “Alhamdulillah. Allah Ya ƙara kawo muku daidaito.”
“Daidaito kam ana gab da samu sai ka zo ka shiga tsakani.”
Hankalin Abba tashi ya yi sosai. Taj bai ɓoye masa komai game da rabuwarsa da mahaifinsa ba. Da kuma burinsa na son ya dawo gida kamar kowa.
“Indai don ina aiki a gidan abincinsa ne wallahi zan ajiye…kai na ma ajiye. Ba zan so na zama sanadin sabunta ɓaraka tsakaninku ba.”
Wani irin murmushi Alhaji ya yi “idan ka bar aikin ma zai maye gurbinka da na wani. Bani da matsala da aikinka.”
Fahimta ce ta ɗarsu a zuciyar Abba. Ya dubi Alhaji a firgice.
“Hamdi? Ƴata ce ba ka so tare da shi?”
“Ƙwarai.” Ya amsa idanunsa na kallon sararin samaniya.
Auno halin da Yaya za ta shiga ya yi. Jikinsa ya soma rawa.
” Ka taimaka min Yaya Hayatu. Wallahi nayi musu tarbiyya bakin gwargwadon iyawata. Duk da ni na haifeta amma na sani bata da wani aibu na halayya sai abin da ba a rasa ba na ajizancin ɗan Adam.”
“Ita kuwa take da aibu tunda kai ne ubanta.” Ya haɗe rai “Habibu, na baka wata uku ka kashe auren nan. Cire zuri’arka daga jikina shi ne kaɗai abin da zai sa na dawo da Taj gidana. In har da gaske ka damu da shi ba za ka bari rayuwarsa ta ƙare a bin gidan ƴan uwa idan yana son ganawa da mahaifiyarsa ba.”
Duk dauriya sai da yaji ƙwalla na neman zubo masa.
“Me yasa ka yarda aka yi auren?”
“Saboda banga alamun idan naƙi zai haƙura ba. Ka riga kayi tasirin da maganarka tafi tawa a wajensa. Zai iya yin komai domin fitar da kai kunya a yadda ya zo min.”
Gumi sosai Abba ya dinga yi. Allah Ya sani yafi jin Yaya akan Hamdi. Wannan tsananin farincikin da ta shiga idan ya koma baƙinciki kamar ba za ta iya ɗauka ba. Mutane da yawa za su yi musu dariya. Wadda za ta fi yi mata ciwo kuwa ta ƴan uwanta da su ka haɗa uba ce da ta mahaifin nata da har yanzu yake aibata halittarta da aurenta da đan daudu.
Ya sake kallon Alhaji sai dai babu wata fuska ta yin magana. Magana ɗaya Alhajin ya ƙara yi masa kafin ya koma ciki.
“Ina fata za ka nuna dattako ka riƙe maganar nan tsakaninmu. Dabarar kashe auren tana hannunka. Ni dai kawai nan da wata uku magana ta ƙare.”
“In sha Allahu.”
Jikinsa rawa ya dinga yi shi yasa ya kasa komawa motar har sai da Taj ya fito. Kafin ya ƙaraso Abba ya yi composing kansa.
“Yau dai na shanyaka da yawa. Muje kada dare ya ƙara yi.”
Kasa haƙuri yayi ya tambaye shi “Babu matsala ko Abba? Me ya ce maka?”
“Ban sanka da haka ba Taj. Tattaunawa ce dai ta yaushe gamo da kuma rashin jindaɗinsa da bamu tuntuɓe shi da maganar auren ba sai a makare.”
Kallon rashin yarda Taj ya yi masa. Sai dai Abban ya toshe duk wata ƙofar da zai fahimci matsalar. Sun kama hanya za su koma motar Taj yaji Kamal na kiransa. Da ya juya sai yaga Inna tare da Kamal ɗin.
Fuskarsa ta haskaka da wani irin annuri. Ya ce da Abba “Innata ce.”
Kamal juyawa ya yi bai biyota ba. Ta ƙarasa kusa da gate ɗin. Idanunta cike da ƙwalla. Taj kuwa tuni ya yi laushi don ya kwana biyu sai dai su gaisa a waya.
“Baki kwanta ba?”
“Ina fa. Ina ta fakon shigowar Alhaji ne idan kun gama.” Sai kuma tayi murmushi “ango ka sha ƙamshi.”
Dariya ya yi ya rungumo kafaɗarta. Ba shiri ta ruɗe tana fama ture shi gami da waigawa don kada a gansu.
“Ga Abba…surukinki.”
Abinka da sabo. Ƙasa ya yi zai gaisheta.
“Subhanallahi. Haba don Allah. Tashi mu gaisa. Ai mun zama đaya kuma.”
Duk da bata so amma a mutumce su ka gaishe da juna. Yana ta bata girma.
“Da farko zan fara da baka haƙuri don nayi imanin ko me Alhaji ya faɗa maka ba mai daɗi bane. Sannan don Allah kada ka wahalar da kanka wajen yiwa ƴata komai. Tunda ka iya bawa yaron nan ƴarka in sha Allahu ba zan bari ta kuka da komai ba. Nagode da karamcinka a garemu.”
“Ikon Allah. Hajiya ai nine da godiya da Taj bai ƙyamaci zuri’ata ba.”
“Wanda ya baka ƴa ai ya gama maka komai.” Ta faɗi tana murmushi “idan babu damuwa ina son ya kawo mana ita cikin sati mai zuwa. Zan karɓi numbar mamanta mu yi magana kafin na zo. Ka san Alhajin naku sai da lallaɓawa.”
Murmushi ya yi shi ma “kada ki damu. Hamdi ƴarki ce kuma ikonki. Ina ƙara godiya.”
Taj ma godiyar ya yi mata. Abba ya dubi uwa da ɗan su ka bashi tausayi. Me yafi wannan ciwo ace uwa tana son ganin ɗanta amma sai dai ta saci hanya ta fito kamar mai laifi? Dole zai san yadda ya yi da Yaya da Hamdi a raba auren cikin lumana.
***
Har ƙofar gida Taj ya kai Abba. Su ka yi sallama ta girmamawa. Taj yana ta sake tambayarsa ko babu matsala game da ziyarar da su ka kaiwa Alhaji. Shi kuma ya tabbatar masa babu komai.
“Gobe in sha Allahu zan tafi Abuja. Idan komai ya tafi yadda nake so ba zan wuce kwana biyu ba in sha Allahu.”
“Kada ka damu. Happy Taj zai tafi kamar kana nan da yardar Allah.”
“Ba manufata ba kenan” Taj ya faɗi yana sosa ƙeya “dama akan …”
Gira Abba ya ɗage gira “matarka ko? In turo ta ku yi sallama ne?”
Da sauri Taj ya koma mota yana ta dariya shi ma Abban ita yake yi. Da gangan dama ya yi tsokanar don kawai ya kawar da damuwar da yake gani a tattare da shi tun a gidansu.
Hamdi na jin shigowar Abba ta leƙo yi masa sannu da zuwa. Ya kalleta ya kalli Yaya da ita ma fitowar tayi da sauri.
“Suruka da matar Taj jiran me kuke yi min ne?”
“Jin inda magana ta kwana mana.” Cewar Yaya.
Ita kuwa Hamdi wayancewa tayi ta gudu. Ɗakinsu ta koma amma akwai mutane. Sai ta zaga bayan gidan amma bata yi nisa ba. Ta zauna akan wani bulo ko tsoro bata ji ta kira Taj.
Murmushi ya yi da call ɗin nata ya shigo. Ko tada motar bai yi ba don ya tsaya duba wani saƙo a waya. Ya bari sai da ta gama ringing sannan ya kirata.
“Za mu iya magana yanzu?” Ta furta a hankali bayan ta kuma gaishe shi.
“Yes.”
Raba kanta tayi da dogon tunani ta faɗi abin da ya kamata duk da ba shi bane ranta yake so.
“Dama cewa nayi tunda Ya Sajida tayi aure namu ba dole bane ko? Kada ka takura kanka saboda gidanmu.”
Kamar bai fahimceta ba ya ce “Ban gane ba. Wani abin ne ya faru?”
“Uhmmmm. Dama wai ko za ka sakeni” tayi saurin ƙarawa da “tunda ba sona kake ba. In aka ce dole ka zauna dani za a shiga haƙƙinka. Kaga kuma hakan bai dace ba. Ace mun takura maka ta wannan hanyar bayan duk irin taimakon da kake yi mana.”
Wannan yarinya da abin dariya take ya ayyana a zuci. Ji yadda take zuba zance kamar wadda ake karantowa.
Ita kuma kasa jurewa shirun nasa tayi ta ce “Baka ce komai ba.”
“To me zan ce? Naga kin gama yanke hukunci ke kaɗai.”
Haƙuri tayi saurin bashi. Sam bata so ta ɓata masa rai kada ya yi amfani da hakan a kanta.
“Wai dama tunda ba so ka ke ba…”
“Ni yaushe mu ka yi maganar nan dake har nace bana so?”
Gabanta ne ya faɗi. Kada fa yaƙi amincewa.
“Rannan ɗin nannnn. Ka tuna? Da nayi maka rashin kunya ka ce ai ba sona kake baaa.” Ta marairaice masa.
“Anya kuwa nine? Ban tuna ba Hamdi.” Ya danne dariyar da yake son yi.
“Allah kuwa ba ƙarya nake ba.”
Muryarta yaji ta fara rawa.
“Yanzu dai so kike a raba auren?”
“Eh.”
“Amma bai yi wuri ba? Kada sunanki ya ɓaci a gari.”
“Kaga bamu zauna tare ba. Ko mun rabu babu mai cewa don nayi wani abu ne. Za ma a fahimta sosai.”
“Tun yaushe ki ka fara wannan tunanin?”
Hamdi ta fara murnar jin muryarsa a sake.
“Tun yamma. Wallahi har ciwon kai da zazzaɓi sai da su ka kamani saboda neman mafita…au…saboda nema maka mafita. Bana son mutum ya takura saboda ni.”
‘Zan yi maganinki’
Lokaci ya duba a wayarsa. Tara da arba’in da biyu.
“Yaya jikin naki? In ba a rufe muku gida ba ki ɗan fito mana.”
Sai kuma taji faɗuwar gaba “takardar za ka bani?”
“Ina jiranki” kawai ya ce.
Da sanɗa ta fito tayi sa’a ƙofar soronsu mai ƙara idan an turata a buɗe take har yanzu. Ƙofar gidan ta buɗe tana sako ƙafa su ka kusa karo da Taj. Baya tayi za ta faɗi ya yi saurin riƙo kafaɗunta. Ita da shi duka wani sabon al’amari ya baƙuncesu lokaci guda. Sai da ta daidaita tsayuwarta ya ce,
“Sannu.”
Ta amsa da ka. Yawun bakinta ne a bushe. Tana tare da fargabar ko har ta saku. Bata yi aune ba taji hannun Taj a goshinta.
“Mene ne?”
“Zazzaɓin nake son ji. Da alama akwai saura. Zo mu je asibiti.”
“Na’am?” Ta waro masa idanunta.
Wayarsa ya ɗago “bari na kira Abba na faɗa masa za mu fita.”
“Dani ɗin?” Ta ce a gigice. Idanunta sun soma raina fata.
“Idan dare ya ƙara yi kafin mu dawo sai su rufe gidan kawai. Sai mu wuce gida mu kwana.”
Hanjin cikinta ya wani cure waje guda don tsoro “Wai da ni?”
“Kada ki damu. Zai fahimta. Mata ta ce so babu wani abu” ya bata amsa kai tsaye.
“Don Allah kayi haƙuri.”
“Ban yi wasa da ciwon wanda bashi da kusanci dani ba ballantana kuma naki.”
“Na warke tun da rana.”
Taj ya ƙanƙance ido “ki ka ce kuma da yamma.”
Da sauri ta ce “Eh, da yamman nake nufi. Kafin rana tayi sanyi.”
“Hamdiyya kenan. In tambayeki mana.”
“Ina ji.”
“Kina so na?”
Tsareta yayi da kallo. Ta sunkuyar da kai.
“Kada ki cuci kanki. Da amsarki zan yi amfani.”
“Ba za ka ji haushi ba?”
Taj ya yi murmushi “ko kusa.”
“Zan fi so mu rabu.”
“Ban yi miki ba kenan?”
Yau acting kamar daraktan kannywood ya bata training, ta marairaice masa.
“A’a, ba haka nake nufi ba. Naga kamar bamu dace ba. Ka fi ƙarfin ƴar talakawa iri na.”
“Zan sanar da Abba duk yadda mu ka yi….”
“Wane Abban? Nawa?” Ta ɗaga murya fiye da yadda ta soma magana saboda tsoro.
“Kinsan ina girmama shi sosai. Ba zan yi komai ba tare da shawartarsa ba.”
Ganin zai ɓallo mata ruwa ba shiri ta ce “to a bar zancen nan don Allah.”
“Kin fasa karɓar takardar?”
Ta sha kunu “na fasa.”
“Za mu je asibitin?” Ya kanne mata ido.
Murguɗa masa baki tayi “na ma zama abar tsokana ko?”
Ya rasa me yasa komai tayi yake burge shi. Wannan tsiwar ma da ba don dare ba da zai yi ta zurma ta ne tana yi masa.
“Gobe zan yi tafiya. Ki min addu’a don Allah.”
“Allah Ya tsare hanya” ta furta kamar an matse bakin.
“Baki roƙa min samun nasarar abin da zai kai ni ba.”
“Me zai kai ka?”
“Maganar aurena da wata ƙanwata. Tunda ke ba sona kike ba gara na kawo wadda za ta so ni, nima na so ta.”
Yana kallon yadda fuskarta ta haɗe kamar hadari. Ya gimtse harda yi mata sai da safe ya wuce. A mota ta sami damar yin murmushi mai haɗe da dariya. Ya gama ganota. Tana so tana kaiwa kasuwa. Birkita mata lissafi kawai zai yi ta haƙura don kanta ta karɓi zuciyar da ya jima da miƙa mata.
A nata ɓangaren tana shiga gida ta sauke ajiyar zuciya. Wato da ya miƙo takardar da take barazanar nema anya za ta iya karɓa kuwa? Ita kaɗai ta dinga saƙe saƙe. Sai kuma ta kama murmushi da ta tuna maganganunsu. Ko ba a faɗa ba ta san tsokana ce da shi. A ƙarshe dai ta gaji da kokawa da zuciyarta ta amince za ta bashi dama. She will give this pure feeling she has for him a chance.
Ƙofar ɗakinsu ta kama za ta buɗe taji kira daga Abba. Soro ya ja hannunta su ka koma don a nan ne kawai ya san babu kunnen da zai ji su. Ya gama ninke Yaya ya nuna mata babu matsala don ta kwantar da hankalinta. Tsoron da yaji yanzu shi ne na ganin dawowar Hamdi daga wajen Taj. Idan ya bari alaƙarsu tayi nisa ƴarsa zai bari da jidali. Ya rasa abin yi sama da faɗa mata halin da ake ciki. Cikin hikima ya bata labarin Taj tun daga farko har zuwa aurensu. Taji wani irin tausayinsa da kwaɗayin ya daidaita da babansa. Hankalinta bai ƙarasa tashi ba sai da Abba ya faɗa mata tsakaninsa da Alh. Hayatu da yadda aka yi aurensu. Da kuma sharaɗin da ya gindaya masa.
“Ko mahaifiyarku ban sanarwa gaskiya ba. Shi kuma Taj nayi imanin ba zai taɓa sakinki ba idan yaji daga ina umarnin ya fito. Zaɓi ɗaya ya rage min…”
Kuka take a lokacin ta ce “mene ne Abba? Me za mu yi?”
“Ki nuna masa na kya sonsa. Na tabbatar idan yayi tunanin da gaske kike zai sauwaƙe miki. Ni kuma zan baki goyon baya. In ta kama sai ya fita daga rayuwarmu bakiɗaya ya sami salama.”
“Abba kada ka saka kanka a ciki. Yanzu banda ƴan uwansa kana cikin waɗanda yake yiwa kallon uba. Ya ma faɗa min. Idan ka juya masa baya it will break his heart.”
“Ki yafe min Hamdiyya. Koma mene ne ni na cuceku. Rayuwa tana gaba amma kullum ana yanke muku hukunci da abin da na shuka a baya.”
Zuciyarta rauni tayi mara misaltuwa. Bayan shuɗewar lokaci tana gudun mahaifinta yau da kanta ta rungume shi tana kuka. Shi kaɗai yake ta haɗiyar abubuwa domin farincikinsu amma kullum ƙorafi take yi.
“Abba ka yafe min nima. Ba zan ƙara faɗin aibun sana’arka ba. Kuma in sha Allahu babu mai jin zancen nan. Zan yi ƙoƙari in ga ya haƙura da auren da kansa.”
“Allah Ya yi miki albarka. Allah Ya bamu ikon sakawa Taj da abin da yafi buƙata a rayuwarsa wato albarkar duka iyayensa.”
Amin ɗin a zuci ta iya faɗinta. Ta shige ɗaki ta kwanta tana zubar da hawayen damuwar da tafi ƙarfin shekarunta
MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
