Search
You have no alerts.

    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
    Irin rawar jikin da Anisa da Anti suke yi da Taj tuni ya sha jinin jikinsa. Shi da ya zo don su haɗu a sirrance ya zame ashe Hajjo tayi masa handsfree da alama. Kuma a ɓangarensu zancen ya sami karɓuwa.

    Ɗakin Hajjo aka kaisu. Tana ganinsu ta washe baki tana tarbar Kamal.

    “Sai ga Haffiness ɗin Haffi a Abuja. Sannu da zuwa Kamalu.”

    “Har kin ƙara masa wasali a sunan nasa kenan.” Taj ya faɗi yana zama akan kafet. Ƙafafunsa ya miƙe da yake jin sun sage saboda zama.

    Kamar ba da ita yake ba.Ta cigaba da yiwa Kamal magana
    “Ya ka baro mutanen gida? Ya baban naku?”

    Kamal ya amsa ta sake sako wata tambayar. Taj ya gaisheta har sau biyu bata amsa ba. Ya dai gane fushi take dashi. Bayan kuma shi ya kamata ya nuna ɓacin ransa da tayi saurin sanya shi cikin tsaka mai wuya. Yanzu duk gidan nan za su so jin matsayarsa kan maganar Anisa. Tunda yarinya dai alamu sun nuna ta amince, ana jin zance ya sauya salo nan gaba kaɗan za a ɗora masa laifi.

    Share su ya yi ya kira uwayensa ɗaya bayan ɗaya ya sanar dasu sun iso lafiya. Sai kuma ya kira Abba shi ma. Su ka yi magana akan ɗan gyaran da za a ƙarasa a wurin da Taj ya kama musu kafin ya dawo.

    “Hajjo in kin gama gaisawa da Haffiness ɗin nima ki ɗan bani lokaci don Allah. Yau za mu koma. Bana son mu yi dare.”

    A sukwane ta juyo rai a ɓace “banten uba! Ku iso yanzu ka ce kuma komawa za ku yi?”

    “To ya za ayi? Aiki ya sako ni a gaba.”

    Dariyar Kamal a dalilin zolayarta da Taj yake sai ta gane ba tafiyar za su yi da gaske ba. Sha kunu gami da nuna masa yatsunta biyar.

    “Buhun ubanka Tajo.”

    “Toohhh” Kamal ya kalleta da rashin jindaɗi. Dole taji kunya don bata ga alamun yana da idanu a tsakar ka irin na Taj ba.

    “Ɗan uwan naka ne bashi da kirki Haffiness. Na yi masa maganar ƙanwarsa ya amsa rimi-rimi sai kuma ya shuka ni. Yanzu ma gajiya nayi ina ta tunanin ko yarinyar ce ta ce bata so shi ne na kira uwar na tambayeta.”

    Kai tsaye Tay ya tambayeta “Me su ka ce?”

    Hajjo ta danƙara masa wani irin kallo “me kuwa za su ce sama da murna. Ko kai makaho ne ya dace ace ka fahimci yadda ake ta nan nan da kai ya sha bamban da lokutan baya.”

    Shirunsa a yanzu daidai yake da cutar kai. Idan ya kuskura ya fita daga ɗakin nan bai faɗi abin da yake ransa ba to tabbas aurensa da Anisa da wahala in ba ayi ba. Gyara zama ya yi ya ce,

    “To ni dai gaskiya Hajjo…”

    Yau da gobe tafi ƙarfin wasa. Kuma dai Kamal ya riga ya san ba so yake ba. Amma akwai kunya da kawaicin malam bahaushe. Rashin girmamawa ne idan Taj ya kalli tsabar idon Hajjo ya faɗa mata baya son jikarta.

    “Hajjo magana ta gaskiya yanzu Taj tsoron ɗauko zancen aure yake.”

    “Saboda me? Yana da lalura ne?” Ta soma yi masa kallon ƙurilla.

    Ya girgiza kai “a’a, amma kin san matsalar da yake fuskanta daga wajen Alhaji.”

    “Alhajin me?” Ta fara sababi “in kai ma baka da labari ka sani daga yau. Kakarku wadda ta tsuguna ta haifi Hayatu aminiyata ce ta ƙud da ƙud. Duk taurin kansa bai isa na faɗa ya faɗa ba.”

    Kamal ya jinjina kai yana kallon Taj ko zai agaza masa. Shi kuwa shiru ya yi yana kallonsu.

    “Nima ba nufina zai ƙi maganar bane. Kawai dai shi Taj yafi son lokacin da zai yi aure ya kasance Alhaji ya daina fushi da shi. Baya son yadda ya kore shi daga gidan kuma ya hana ƴaƴansa shiga su ma.”

    Hajjo ta jinjina lamarin “da gaskiyarsa kuma. To amma indai auren gida ne irin wannan ai ita Anisan ta san komai. Ga ku duka kuna ta zumuncinku. Su Haj. Gambo ma dai ko da satar hanya na san za su fito ganin jikokinsu.”

    “Ko kin san zuwan nan har bakin mota Taj ya bishi amma su ka ja mota aka baɗe shi da ƙura? Shi ne ya yi alƙawarin ba zai yi aure ba sai Alhaji ya yafe masa.”

    Zancen ya fara shigarta. Kamal ya zama kamar wani lauya wurin jujjuya zance. A ƙarshe dai ya samu da kanta ta hango illar auren Taj a yanayin rashin jituwa da uba.

    “Abin da za ayi ko Kamalu, ni zan sa a kira min Hayatun muyi magana. Na san ko babu komai idan yaji daga gareni zai girmama zancen. Ba zai wulaƙanta min jika ba.”

    Tamkar ya sanya ihu haka yaji a wannan lokacin. Ashe duk ɓaɓatun da yake ita wani angle ɗin daban take kallo. Miƙewa Taj ya yi ya fice ya barshi yana ta kame kame.

    Falo ya koma inda ya yi sa’a babu kowa. Yana zama Kamal ya fito yana ta waigen baya.

    “This woman is too smart Happy. Kana ganin ta toshe duk wata hanyar da zan ɓullo don a kwantar da zancen nan.”

    Murmushi Taj ya yi “kaɗan ma ka gani. Shi yasa na so faɗa mata gaskiya. Kai kuma ka hana.”

    “Haba Happy, wani abin ai sai da siyasa. Kara wani abu ce”

    Kai Taj ya riƙe kawai. Kwanakin nan gajiya da damuwa suna yawan sanya masa ciwon kai. Tunda ya sami kan Abba abin ya ragu. Amma fa daga lokacin da su ka saka ranar zuwa Abujan shikenan bashi da wata walwala.

    “Kan ne dai?” Kamal ya yi tambayar da kulawa yana dafa shi.

    “Wallahi kuwa.”

    “Ka daina damuwa. Ba a yiwa namiji auren dole fa” Kamal ɗin ya yi murmushi.

    “Happiness bana son takura ne. Sannan bana son ungratefulness. Ƙinta tamkar ban godewa kyautatawarsu bane.”

    “Don ka taimaki mutum kuma bai kamata ka ɗora masa nauyin da zai takura shi ba. Ni shawarata kawai tunda Hajjon ta ɗan fahimta ka cigaba da jan ƙafa. Kuna fara magana a fito mata as unromantic as possible. Kada ka sanya mata false hope. In anyi sa’a ta gudu da kanta.”

    Sai a lokacin Taj yaji sanyi a ransa. Ya miƙawa Kamal hannu.

    “Happiness nawa ni kaɗai. Yadda ka ce hakan za ayi. Thanks bro”

    ***

    Hamdi bata taɓa shiga motar haya a Abuja ba ita kaɗai. Ko yawon da su ka dinga fita da Anti Labiba farkon zuwanta, yawanci mijin Antin ke kai su. Ko kuma Anti Labiban ta kira bold ko uber. Hankalinta kwance yake tunda akwai idon garin. Yau da take ita kaɗai ne dai duniyar tayi mata zafi.

    Na farko dai direban motar a ƙoyasinta zai yi biyunta. Ga jiki da bai ɓuya ba. Sannan babu tantama ba bahaushe bane. Inda zasu je kuma bata sani ba. Anti Labiba dai ta ce mata zasu bi ta titin hanyar Central Mosque ɗin da su ka taɓa zuwa. To gashi an fi minti shabiyar a titi amma babu masallaci babu alamunsa. Banda hawa da sauka akan wasu gadoji da ko wuƙa aka ɗora mata ba za ta gane ko ɗaya ba, babu abin da yake yi. Ga gudu da ta lura yana yi kamar walƙiya.

    Hanjin cikinta su ka sami wuri su ka cure wuri guda. Zuciyarta tana harbawa kamar za ta fito waje. Sai kuma bisa rashin sa’a aka kira shi da wata wayar ba wadda take gabansa tana nuna hanya ba. Ya sanya earpiece a kunne ɗaya yana magana da yaren da bata ji. ‘Passenger’ da kuma ‘get ready, I will be there soon’ kaɗai ta iya tantancewa.

    Habawa, duk wani labari da ta taɓa ji game da satar mutane sai da ya dawo mata. Jikinta ya dinga rawa. A hankali ta kama shessheƙar kuka don bata so yaji. Ta fiddo wayar da Anti Labiba ta bata da za ta taho ta tura mata message.

    (Anti zai sayar dani a hanya ban san inda muke ba amma titin yayi kama da bayan gari)

    Ta rubuta a jere ko waƙafi babu tsakanin rubutun. Gashi tana zama a motar ya danna lock ta gaba. Gilasai duk an ɗagesu an sakar mata AC.

    Anti Labiba na kashingiɗe a falo message ɗin ya shigo. Ta tashi zaune a gigice. Ta dinga kiran Hamdi wayar taƙi shiga. Cikin matsanancin tsoro ta kira nambar Anisa da su ka yi magana ɗazu.

    *

    Abinci ta shiryo a tray ta fito dashi wayar ta shigo. Bata ɗauka ba sai da ta ajiye tray ɗin a gabansu Taj. Ta ɗauki wayar daga kan tray ɗin.

    “Dama yanzu nake shirin nemanki. Naga bata iso ba har yanzu.”

    Anti Labiba ta ɗora hannu a ka “bata zo ba? Sun kusa minti arba’in da biyar da barin gida fa.”

    Anisa da bata da saurin fushi tayi musu uzuri da cewa “maybe hold up ne. Kin san yamma tayi. An fara dawowa daga office.”

    “Uhmm uhmm dai. Bari na turo miki message ɗin da tayi min yanzu. Zan nemi maigidan na sanar dashi.”

    Zama Anisa tayi don ta gama kawo komai falon. Ta sha kwalliya sosai tayi kyau. Ta buɗe abincin tana tambayar Taj me za ta zuba masa wayar Anti Labiba ta sake shigowa. Tambayarta tayi taga text ɗin ta ce yanzu za ta duba. Ai tana karantawa ta kama salati.

    “Me ya faru?” Taj ya zare wayar a hannunta don jikinta rawa yake yi.

    “Anti! Anti!!” Shi ne sunan da take kira hankali a tashe.

    Antin ta fito da mayafi a hannu don kiran ya tsorata ta. Taj da Kamal su ma duka babu mai nutsuwa.

    “Wai yarinyar da na bawa aikin snacks ce ta taho tun ɗazu amma kinga bata ido ba.”

    Anti ta ja tsaki “haba Anisa. Shi ne ki ke min wannan kiran mai firgitarwa?”

    Wayarta ta soma lalube Taj ya miƙa mata bayan ya gama karantawa. Ta damƙawa Antin. Itama tana karantawa su ka kira Anti Labiba. Kuka ma take a lokacin.

    “Wayarta ko ta shiga bata ɗauka. Innalillahi wa inna ilaihi raji’un.”

    “Ki ce ta turo numbar mutumin tunda dole akwai numbarsa akan app ɗin da zai yi magana da passenger.”

    Da gaggawa Anisa ta faɗi saƙon. Anti Labiba ta tura musu.

    ***

    Direba na tafiya ya fara jin sautin kuka na tashi kaɗan kaɗan. Gabansa ya yanke ya faɗi da ya ɗan leƙa ta madubi ya tabbata yarinyar da ya ɗauko ce take yi.

    Dama ana cewa fa wasu fasinjojin ba da alkhairi suke zuwa ba. Wasu ma sharri su ke ƙullawa mutane. Kaddai irinsu ya ɗauko yau?

    “Madam, what is wrong?” Ya kwantar da murya ya tambayeta.

    Ita kuma jin ya kirata sai kawai ta fashe da kuka sosai.
    “Please take me home.”

    “We are almost at your destination. Did something happen?”

    Hamdi ta kalli titin. Babu sawun mutane sosai. Ita da zai sayar ko ya cirewa sassan jiki zai yiwa daɗin baki?

    “Zan sauka…drop me here.”

    Direba ya kalli wajen sai yaji fargaba ta dirar masa. Bisa shawarar map ɗin bolt da yake bi an nuna akwai hazard akan hanyar da tafi saurin kai mutum inda zai je. Hazard ɗin kuwa yana iya zama hatsari, lalacewar mota ko goslow ɗin da ya hargitsa titi. Sai map ɗin ta zaɓar masa wata hanyar daban. Shi kuma baya son bi saboda nisanta sosai. Kuskurensa shi ne da ya ɗauke hanya bai yi mata bayani ba. Kukan da take a firgice ne ya tuna masa da hakan. Ya soma bata haƙuri da rarrashi. Amma fir Hamdi taƙi yin shiru. Ita dole ya sauketa. Shi kuma yana tsoron buɗe motar bai san me zai faru ba. Mutane ma yanzu basu fiye bincike ba. Wanda yafi rauni yana faɗin abu sai kawai a hau a zauna.

    Suna haka Anisa ta kira shi. Tambayarsa tayi game da fasinjar da ya ɗauko. Cike da farinciki kuwa ya faɗa mata abin da yake faruwa.

    “Let me talk to her.”

    Ai ko wayar ƙin yarda tayi ta karɓa. Karshe sai speaker ya saka yadda za ta ji.

    “Ki kwantar da hankalinki. Ya ce hanya ce bata da kyau shi yasa ya canja wata. Amma yanzu zai kawoki.”

    “Ni dai ki zo ki karɓi kayanki don Allah. Daga nan in ya kuma tada mota Allah ihu zan masa. Tun ɗazu fa muke yawo…” ta fashe da wani kukan.

    Anisa ta rasa irin bayanin da za ta yi mata. Sai kawai ta bawa Taj wayar.

    “Naji kamar yarinya ce, please ka ɗan kwantar mata da hankali Yaya.”

    A tsiwace Hamdi ta ce “ni ba yarinya bace. Na yafe kuɗin. Ku zo ku ɗauka ko na bar masa a mota.”

    Ita a wautarta in ta nuna bata tsoro ƙila a haƙura da cutar da ita.

    Yadda take magana sai ya bawa Taj dariya. Kai kana ji za ka san a mugun tsorace take. Wayar ya kara a kunnensa.

    “Big girl.”

    Anisa da Kamal harma da Anti su ka yi dariya. Da ta amsa abinta.

    “Na’am.”

    “Ni yayan Anisa ne. Yanzu zan sa direban ya turo min location ɗin ku. Sai na zo na kai ki gida. Haka ya yi?”

    “Eh, amma don Allah minti nawa? Kaga fitsari ya matseni.”

    Ɗaga kai ya yi sai yaga duk sun yi alamun tausayawa gareta.

    “Zan yi sauri in sha Allah.”

    Cikin mintuna kaɗan kuwa direban ya tura masa da location ta whatsapp ɗin Anisa. Su ka shiga motar Kamal su uku. Kamal ɗin ke tuƙawa. Anisa tana baya. Lokaci zuwa lokaci kuma Hamdi sai tayi flashing da wayar direban. Ta ma manta ko bashi bata yi ba. Sai ya rabu da ita tunda ta daina kukan.

    “Kun kusa?”

    “Saura kaɗan.”

    Anisa ta kira Anti Labiba ta ce mata za su kawo Hamdi gida.

    “Don Allah ku yi haƙuri. Baƙuwa ce a garin.”

    “Ban ji haushi ba. Ni tsorona ma firgitar da tayi kada ya zauna mata a rai.” Cewar Anisa.

    Wasa wasa sun yi minti shabiyar kafin su isa. Unguwannin ne da tazara a tsakaninsu.

    Motar na doso su Hamdi ta kama handle za ta buɗe. Shi ma direban duk ya ƙagu. Yana ganin sun yi parking a bayansu ya cire lock. Babu takalmi haka ta jeho ƙafafunta waje ta fito. Mayafin da ta yafa akan riga da siket ɗin jikinta ya rufe rabin fuskata. Wayar Anti Labiban ma bata ɗauka ba ta fito da sauri.

    Mayafin da ta gyara ne ya bayyana fuskarta sosai. Taj yana fitowa su ka haɗa ido. Zuciyarsa sai da tayi wani irin abu saboda ganin abin da bai taɓa zato ba.

    “Hamdi?” Ya furta a can ƙasan maƙoshi shiyasa babu wanda yaji.

    Ita kuwa bata ma gane me ta kalla ba. Burinta dai ya cika ta fita daga motar mutumin. Kamal ya ƙarasa wurin direban ya bashi haƙuri tare da cewa ƙanwarsu ce. Shi ma ya bada haƙurin rashin yi mata bayani wanda ya janyo wannan ruɗanin.

    “Ga kayanta” ya ce da yaga suna shirin tafiya.

    Kwalaye ne madaidaita guda biyu. Ɗaya doughnut. Ɗayan kuma meatpie da samosa. Sai kuma ledar youghurt wanda Hauwa ce da kanta tayi.

    Anisa ce ta kula Hamdi bata da takalmi da ta zauna a baya. Za ta fita ta ɗauko mata sai Taj ya ce ta zauna. Shi ya ɗauko harda wayar yana ta mamakin wannan coincidence. Ashe tana Abuja. Shi yasa baya ganinta a gidansu. Murmushi kawai ya dinga yi har su ka soma tafiya. Hanyar gidan da ba ganewa za ta yi ba shi ma Anti Labiba ce ta turo kwatance. Anisa ta ce ta gane. Idan sun isa unguwar za ta kira sai ta kwatanta gidan.

    “Shhh” Hamdi ta fara yi da baki saboda fitsarin da ya gama matsarta. Tun a na farko Taj ya ji. Hankalinsa gabaɗaya yana bayan motar.

    “Step on it Kamal (ƙara sauri)” ya ce a hankali don kada taji kunya.

    Kamar a kunnen Anisa ya faɗa sai cewa tayi “eh kuwa. A matse take sosai” tana kallonta.

    Ko a jikin Hamdi. Burinta kawai a isa gida. Ƙafafunta sun kasa zama waje guda. Komawa gidan tayi mata nisa saboda uzurinta. Finally bayan ta gama gumi su ka shiga estate ɗin su Anti Labiba. A guje ta fita da Kamal ya tsaya. Ta sake barin takalma da wayar da dama Taj bai miƙa mata ba.

    Anisa ta bita cikin gidan su kuma suna waje. Anti Labiba da yara sun taso da murnarsu ta wuce su ta shige banɗaki. Bata ma kula harda maigidan ba sai da ta gama ta fito.

    “Washhh Allah na.” Ta furta da ta dawo hayyacinta. Sai kuma ta rungume Antin tana kuka.

    “Mene ne na kuka kuma? Ba gashi kin dawo ba.”

    Ta kalli maigidan da su ke kira Uncle.
    “Na zata ba zan sake ganinku ba.”

    “Ke dai anyi matsoraciya.” Cewar Anti Labiba tana dariya.

    “Ko nice fa zan tsorata. Bata san wuri ba kuma an bi hanya daban.” Anisa ta kare mata.

    Murmushi ta yiwa Anisan gami da bata haƙurin rashin cika alƙawarin kai kaya.

    “Wa yake ta kaya baiwar Allah? Ai tunda dai kin dawo gida nima buƙatata ta biya.”

    Kiran sallar magrib aka fara Anisan ta ce tare su ke da yayyenta. Uncle da kansa ya fita ya kira su cikin falo domin su yi sallah bayan an kai musu ruwa sun yi alwala a waje.

    Suna idarwa Anisa ta ce za su tafi. Anti Labiba dake kitchen tana haɗa zoɓo ta hana. Sai da ta haɗa komai ta kawo ta nemi Hamdi a falon ta rasa. Maigidanta ta tambaya ina take ya ce ai tun shigowar su sallah bai ganta ba.

    Ɗaki Anti Labiba ta bita. Ta sameta zaune a bakin gado da zumbulelen hijabinta.

    “Ki zo ki sake yi musu godiya za su tafi.”

    “Anti rawar fitsari fa na dinga yi a motar. Ni dai wallahi ba za ni ba.”

    “Harda saurin rantsuwa?”

    “Baki ganni bane” ta faɗi tana takaicin abin da tayi.

    Falon ta dawo bata san Hamdin na bayanta ba. A bayan labule ta maƙale ta ɗan leƙo da kanta. Hira Uncle yake da su Taj inda a nan su ka gane su ɗin duka ƴan Kano ne. Ya nemi su dinga zumunci domin an zama ɗaya.

    Ta bayan labulen ta sake haɗa ido da Taj domin yaga tsayuwarta tun farko. Baki ta buɗe don da wannan kallon ta gane shi. Zuciyarta ma bata manta ba saboda irin harbawar da tayi da sauri. Ta sanya hannu ta rufe bakinta. Za ta gudu taji muryarsa da ta gane tun a wayarsu ta ɗazu.

    “Kamal bani key na ɗauko mata takalma da wayarta.”

    Anti Labiba ta waiga ta hango shatinta a labulen.

    “Zo ki je ki karɓo mana. Ko sai ya biyoki dasu kuma?”

    Sumi-sumi ta fito kai a ƙasa. Kamal ya tsaya bawa Uncle numbar wayarsa. Ita kuma Anisa santin zoɓo take tana kuma wasa da yaran gidan.

    Da faɗuwar gaba ta isa bakin motar. Taj ya buɗe ya ɗauko mata takalman da wayar. Maimakon ya miƙa mata sai ya jingina da motar yana kallonta.

    “Kin gane ni yanzu ko?”

    Murmushi tayi ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta.

    “Ashe nan ki ka gudu shi yasa ban ganki ba.”

    Kallonsa tayi a fakaice “nema na kake yi?”

    “Na san inda zan same ki Hamdi. Kawai ganinki ne ban yi ba a wajen.”

    Shi mai maganar da ita da ake yiwa duk jikinsu tamkar anyi musu duka. Zuƙatansu ke aikin wucin gadi na tsananin murnar sake haɗuwar bazata irin wannan.

    “Ina? Makaranta?”

    “A gida.”

    Daina ɓoye fuskarta tayi. Ta kalle shi da mamaki. Muryoyin su Anisa yaji sai ya bata kayanta.

    “Sai mun haɗu a Kano. Take care.”

    Motar ya shiga amma bai rufe ba har su ka iso. Hamdi ta sake yi musu godiya sannan su ka shiga mota su ka tafi.

    Daren ranar mutumin da bata san sunansa ba ne ya cika mata zuciya da tunani. Bata da wani aiki sai murmushin da bata san lokacin da yake zuwa ba.

    A ɓangaren Taj kuma suna yin sallar isha ya ce bacci zai yi. Abincin da Anisa ta dafa Kamal ne kawai ya ci. Shi kuma ya sanya snacks ɗin Hamdi a gaba. A take ya yanke shawarar sanyata a ɓangaren snacks ɗin restaurant ɗin shi wanda Kamal ya yiwa suna da HAPPY TAJ. Kuma ba shi kaɗai ba. Kowa ya ci sai yaba daɗin kayan.

    Wayar da su ka dinga magana ɗazu ya kira sai yaji muryar direban motar. Ba yadda ya iya. Godiya kawai ya sake yi masa ya katse kiran. Kenan ba da wayarta su ke magana ba? Yayi guntun tsaki. Babu matsala tunda samunta ba zai yi masa wahala ba. Zuciyarsa wasai ya kwanta.

    *

    Tun asuba Taj ya faɗawa Kamal cewa a yau za su koma Kano. Zai yi magana da Anisa kafin su tafi.

    Ba musu ya amince ” gara haka don zamanmu ma zai iya sanyawa ayi tunanin wata soyayya ku ke bugawa fa.”

    Da yake da wurwuri ta tashi ta haɗa musu breakfast. Shi ya taimaka masa wurin samun ganinta da wuri.

    Ta zauna a falo ta sunkuyar da kai ƙasa. Gabaɗaya sai ya dinga jin babu daɗi. Hajjo taje kawai ta sanya mata rai.

    “Anisa.”

    “Na’am Yaya.”

    “Kinji haɗin da Hajjo take son yi mana ko?” Kai ta gyaɗa da murmushinta.

    “Bani da abin cewa game da karamcin gidan nan naku sai godiya. Anyi min komai a lokacin da na rasa soyayyar mahaifina.”

    Ta dube shi da tausayawa “kayi haƙuri. Komai zai daidaita in sha Allah.”

    “Haka nake fata. Amma saboda halin da nake ciki Anisa bana son yin aure yanzu.”

    A razane ta dube shi. Gabanta na faɗuwa kada ya ce baya sonta. A ransa hakan yake son faɗa ko don ta bawa wasu dama. Amma yana gudun me zai je ya dawo.

    “Ina son lokacin aurena Alhaji ya halarta ba don anyi masa dole ba. Idan na sami ƴaƴa in kai masa ya yi huɗuba yadda yake yiwa ƴaƴan ƴan uwana. Ya kuma sanyawa abin da na samu suna.” Yaja numfashi “hakan ba zai samu ba yanzu saboda bai haƙura ba.”

    “Kana nufin na nemi wani kenan?”
    Ta tambaye shi da sanyin jikin da ya sanya masa tausayinta.

    “Ina nufin mu bi komai a sannu sannan mu nemi zaɓin Allah. Bana son in yi miki alƙawarin da ba zan iya cikawa ba.”

    Murmushi tayi ga ƙwalla ta taru a idanunta “na fahimceka, zan kuma cigaba da yi maka addu’a.”

    “Nagode” yaji zuciyarsa maimakon ta rage nauyi ƙarawa tayi. Reaction ɗin Anisa na sauƙin kai ya kwaɓa masa lamari. Shawarar Kamal ta biyu zai bi. Ba zai yarda ya nuna mata kulawar da za ta saka rai da samunsa ba. Amma abin da kamar wuya domin Hajjo ba za ta sakar masa mara ya sha iska ba. Shi ya san da wannan.

    ***

    Sati guda ya ƙara a Kano ya tattara ya tafi. Ayyuka ne har biyu su ka taso masa na bukuwan manya wanda suka ƙi yarda su nemi wani chef ɗin duk da baya nan. Sun tsara abubuwa da dama da Abba kafin tafiyar tasa.

    “Ka cigaba da training ɗin yaranka kafin na dawo. Idan sun yi passing test ɗina zan yi retaining ɗinsu.”

    Abba ya ce “shagon fa?”

    “Ku cigaba da girkinku kafin a ƙarasa wancan.”

    Gidan Abba Habibu kowa ya yi farinciki da cigaban da ya samu. Wurin yanzu yafi na da komai da komai. Hamdi ce kaɗai da labari yaje mata ba kunya ta ce ko waye Taj ɗinnan bai burgeta ba. Idan taimako zai yi ai da ya samarwa Abba wata sana’ar. Kuma da yake a idanunta wani matashin ɗan daudun take gani, sai taji duk ta tsane shi tun kafin su haɗu. Haka kawai ya zo ya yi amfani da halin rashin da suke fama dashi wanda ya hanata shiga jami’a ya sake dulmiya mata uba.

    Har ta dawo Kano bayan wata uku da ko sau ɗaya bawan Allahn nan da ya gama da zuciyarta bai nemeta ba. Tun tana damuwa don ta sa rai za ta sake ji daga gare shi har ta haƙura. Sana’ar snacks ta kama ka’in da na’in wadda kuma Allah Ya sanyawa albarka. A ɗan tsukin wajejensu tayi suna. Biki ko suna kowa Hamdi yake kai wa aikin kayan fulawa. Kuma tana yi Abba ya sayar mata a wurinsu. Kafin wani lokaci sai ya zamana su uku suke yi. Zee ta fi ƙwarewa a yin youghurt kamar ita Luciousbites ta koyawa. Abinsu gwanin ban sha’awa.

    Taj yana yawan kira ya gaishe da Yaya. Wani lokacin ta wayar Sajida. Idan aka yi mata tayin gaisawa da shi sai tayi ta zillewa. Idan Yaya bata wurin kuwa wasu lokutan har tsiwarta yana ji ta wayar Sajida. Har mamakinta yake yi. Idan ance masa tana da baki haka zai ƙaryata saboda shi dai da fuskar salihai ya ganta.

    Su kuma ƴan uwan nata komai su ka ji game da shi ko a hira ne sai sun faɗa mata. Idan aka ce Kamal ya zo kuwa bata yarda su haɗu. Ita fa komai nasa akai kasuwa kawai. Ranar da Zee ta ce mata ya iya indiyanci babu irin shaƙiyancin da bata yi ba. Da aka kwana biyu ya kira wayar Yaya sai ta ɗauka. Amma bata saka a kunne ba. Kawai domin yaji haushi ya fita daga rayuwar gidansu tayi magana.

    “Yaya ga Salman Khan ɗinku ya kira.”

    Taj ya kawar da wayar daga bakinsa ya gama dariya sannan ya maƙe murya ya kirata.

    “Hamdiyya.”

    Tsigar jikinta ta tashi. Muryar bata yi irin ta mata sosai ba tunda bai saba ba. Amma dai ya kamanta don ji tayi kamar ta yar da wayar.

    “Aap kaise hain?”

    “Na’am?” Ta ce da takaici. Ƙila ma har rawa da waƙa ya iya.

    Ya sake maimaita tambayar wadda take nufin ‘yaya kike?’

    Ta taɓe baki “zindagi choringe…ba dai shi ne indiyancin ba?” Ta shiga falo da sauri “Yaya ungo wayarki Taj ɗinku ne.”

    “Zan ci mutumcinki akan yaron nan Hamdiyya. Ke da zaki ganshi sai kin raina kanki.” Yaya ta faɗi ba tare da sanin Hamdin ta ɗaga kiran ba.

    Zee ta ƙara da cewa “ƙila ma ta ce tana son shi.”

    “Wuce nan wallahi. Wanda nake so namijin gaske ne.”

    “Lahhhh” Yaya ta faɗi tana jifanta da maficin hannunta “ni kike faɗawa haka ko mara kunya”

    Hamdi ta fice da gudu suna dariya ita da Zee. Ɗakinsu su ka koma su ka sami Sajida tana farinciki.

    “Me ya faru?”

    Rungume ƙannen nata tayi a tare “Safwan zai turo ranar asabar.”

    Haɗuwa su ka yi su uku suna tsallen murna. Yayinda Yaya take waya da Taj wanda yake cike da nishaɗin jin muryar Hamdi.
    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    Note
    error: Content is protected !!