Rayuwa Da Gibi – Chapter Forty-one
by NadminMASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
Ƙarfe tara da rabi Umma ta shiga ɗakin su Mubina. Hamdi kaɗai ta samu ta kashingiɗe akan abin sallah. Umman na shiga ta tashi zaune.
Umma tayi murmushi “ƙanwar Ango ina amaryar yayanki?”
“Tana banɗaki” ta amsa mata ita ma tana murmushin.
“Ai gara tayi wank…”
Caraf Mubina ta katse Umma daga cikin toilet ɗin da rawar murya. Tsoro muraran ya bayyana a tare da ita.
“Ba wanka nake yi ba. Alwala zan yi na fito.”
“Ai ba laifi ki ka yi ba Mubina. Ki yi wankan ki shirya a nutse Alhaji ya ce ni da Hajiyayye mu raka ki asibitin.”
“Na’am? Asibiti kuma” Ta buɗe ƙofar ta fito a firgice. Idanunta zuru-zuru sai ɓare-ɓare take yi. Mubina akwai ruɗewa sai a lokacin hakan ya bayyana.
Hamdi ta kalli Mubina sai taji wani tausayinta ya tsirga mata. Shi fa aure kwarjini gare shi na daban. Gashi dai da ƙafarta ta taho ƙasar amma yau ɗaya duk ta sauya saboda alhini.
Umma zama tayi akan gado ta yafito Mubina da hannu.
“Mene ne amfanin aure idan mace bata kasance tare da mijinta ba Mubina? Asibitin da kansu su ka ce sun yarje miki zama tare da shi tunda ke likita ce sannan sabon aure.”
“Umma ni dai don Allah” sai kawai ta fashe da kuka.
Umma ta tashi tsam ta rungume ta.
“Kamal ɗin ne ba kya so?”
Mubina ta girgiza kai.
“Aure a irin wannan yanayin ko? Ba haka aka saba ba na sani, amma faruwarsa a hakan ya sa naku ya zama special.”
Ba kunya Mubina ta ɓare baki “ni dai Mamana, Umma don Allah wajen Mamana zan tafi.”
Ɗago kanta Umma tayi ta ce “Tamɓali! Mubina? Shekararki nawa ne?”
Mubina ta sanya hannu ta rufe fuskarta tana kuka tana murmushi lokaci guda.
“Na fahimce ki” Umma ta sake yin murmushi “ƙarasa abin da ki ke yi ki kwanta”
Ta juya za ta fita Mubina ta kira ta kai a ƙasa saboda nauyinta da take ji.
“Umma ba za ku yi fushi ba?”
“Haba dai. Mubina ba na jin Kamal zai taɓa samun soyayya irin wadda ki ke yi masa. Kin haɗu da shi a halin ciwo kin so shi. Sannan a lokacin da dukkan wata ƙofa ta ƙulle sai Allah Ya yi amfani da ƙudurinki na biyo shi domin…” muryarta ta karye “ku yi sallama sai Ya kawo mafita. Hamdiyya kina ganin akwai…” ta juya ko sama ko ƙasa babu Hamdi sai kawai ta kama dariya “wannan ƙanwar taki ta san yakamata sosai Mubina. A duk lokacin da take jin ana buƙatar keɓewa cikin magana sai ki ga ta bar wajen da dabara.”
“Nima na kula Umma.”
“Idan ku ka rayu tamkar ƴan uwa tare da sauran yaran namu da matar Ahmad haƙiƙa kun gama yi mana komai.”
“In sha Allahu.”
“To amarya sai da safe.”
Umma ta fita fuskarta babu komai sai annashuwa. Mubina kuwa wata ajiyar zuciya ta saki mai ƙarfi ta faɗa kan gado. Yanzu da Umma ba mai fahimta bace kawai sai a wuce da ita asibiti tinƙis-tinƙis. Gobe kuma a dinga zuwa dubiya ana ganinta a ɗakin Kamal. Ai da kunya!
‘Kamal’ ta maimaita sunan a zuciyarta. Yanzu fa wai ya zama mijinta. Wani juyi tayi na farinciki tana ƙara yiwa Allah godiya.
*
Hamdi na fita ɗakinsu da Taj ta wuce da niyyar ta ɗauko kayan baccinta ta dawo wajen Mubina. She was just smiling idan ta tuna yadda ta baro Mubinan. Tana ji a jikinta Umma ba za ta matsanta mata ba. Nata key ɗin ta saka ta buɗe ɗakin. Tana shiga taji anyi sama da ita. Ta buɗe baki za ta yi ihu Taj ya sauketa ya jingina bayanta da ƙofar ɗakin. Ya tare mata hanyar wucewa.
“Kina yi su Alhaji za su zo kinga sai mu taru mu yi musu bayanin me ya firgita mu.”
Ta harare shi “abin da ya firgita ni dai.”
“Da na sani ma a toilet na ɓuya sai kin fi tsorata.”
Hango irin tsoron da za ta ji tayi ta yi murmushi “da kuwa mai raba ka da yayana sai Allah.”
“Kinga ki kiyaye ni da zancen yayanki ɗan kalen dangi. Yana can gadon asibiti me zai iya? Taj will do what Taj wants.” Ya ƙare magana girarsa ɗaya a sama.
Kai ta girgiza “Gobe idan mun je ka maimaita abin da ka ce yanzu in koma gefe in sha kallo.”
“You are looking for my trouble fa, and I will give it to you har sai kin ce ya isa.”
Dariya ya bata ta kama ƙugu da hannu guda.
“Bring it on.”
Janyota ya yi su ka nufi 3 sitter ɗin ɗakin su ka zauna. Ta ɗora kanta a ƙirjinsa shi kuma ya sake rungumeta.
“Ƴar caras matar Tajuddeen.” Ya kira ta affectionately.
“Uhmmm.” Ta amsa muryarta can ƙasa-ƙasa.
Kasancewarsu tare ya saukar mata da nutsuwa fiye da kullum a yau. Jikin Yaya yana ta ƙara kyau. Sai yanzu ta sami damar appreciating zuwa ƙasa mai tsarki a dalilinsa.
“Yau ban ce miki ina son ki ba Hamdi na. I love you.”
“Ni ɗin kake so ko ƴar caras?” Ta tambaye shi bayan ta zauna su na fuskantar juna.
“Why do you ask?”
Baki ta tura kafin ta ce “Tun ina yarinya ake cewa jiki zan yi idan nayi aure. Wai ƙirar mu ɗaya da ƴaƴan Anti Zinatu.”
“Ƙira kuma sai ka ce wata mota?”
“To dai ance zan yi ƙiba. Kai kuma har wani ƴar caras kake cewa. Kada na fashe nan gaba na daina burge ka.”
Damuwa sosai yake iya gani tare da ita. Ya yi dariya ya kuma zolayarta.
“Ki fashe kamar wata kwalba?”
“Happy manaaaa” ta buga ƙafa a ƙasa.
He hugged her tightly sannan ya yi magana a hankali.
“Ko me za a ce mi ki, ko me ki ka zama a gaba Hamdiyya ki sani cewa Taj is your home. You can be anything as long as Hamdin Abba Habibu ce ina son abata. Hamdi ƴar tsinke” ya fara ƙirge da yatsansa “Hamdi ƴar doguwa, Hamdi ƴar gajera, Hamdi ƴar lukuta, Hamdi mai tumbi, Hamdi shafi mulera…”
Yana kaiwa nan wata wawuyar cakuma yaji ta kai masa tana rigima ya kwashe da dariya.
“Wai ina faɗa ne don ki san cewa ke nake so ba jikinki ba.”
Daga nan ya lallaɓa abarsa su ka kwanta. Sai shabiyu saura Hamdi ta farka firgigit kamar an tsunkule ta.
“Mubina tana jira na mu kwana tare. Ya Subhanallah.” Ta tashi tana neman hijabi.
Sai da ta saka tukunna Taj ya ce “to amara ƙirjin biki dawo ki kwanta. Amarya tana wajen Angonta.”
“Anya kuwa? Ban ga alamun za ta tafi ba.” Ta faɗa masa iya abin da ta gani da Umma taje ɗakin.
Taj ya soma dariyar mugunta. Hamdi tun tana mamaki har ta koma kusa da shi tana jiran ya faɗa mata me ya kawo dariyar.
“Kaza gashin Najeriya” ya ce da ƙyar dariya na cin sa.
“Ban gane ba fa.”
“Yayanki…” dariyar harda ƙwalla.
Hamdi ta kama baki “yau ina ganin ikon Allah.”
Da ƙyar ya saisaita kansa “ana cewa an ɗaura auren nan yayanki ɗan kalen dangi ya sa ni fita neman kaza. Wai bai dace amarya ta zo babu wani abu da zai tuna mata al’adar gida ba.” Yana kallonta ya cigaba da cewa “kin dai sanni da faɗin gaskiya ko Hamdi na…to haka na aje kunya a gefe na nuna masa rashin fa’idar nemo kazar nan saboda kada amarya ta fassara shi yana kwance magashiyan.” Ya sake yin dariya.
“Ba ka da kirki fa” ita ma ta soma dariya don ta hango inda zancen zai dire.
“Rawar kai irin ta ango sabon shiga ya ce bai yarda ba. Babe, tun la’asar nake neman kaza don ya ce dole na nemo gashin Najeriya mai ɗan ƙuli-ƙuli da yaji. Kuma bai yarda na tambayi su Bishir ba duk da sun fi ni sanin gari wai kada a raina shi. To cut the story short naji a jikina. Wurin ana layi haka nayi ta zama har na samo.”
“Shi ne kake yi masa dariya?” Ita ma fa dariyar take yi.
“Sai da yasa na dawo na ɗauko masa aron kayana. Ga ciwo ga wahala amma haka ya dage na saka masa shadda harda hula. A table ɗin gefen gadon na jera masa kazar amarci, juice, youghurt da biryani. Kaiiiii, wa zai cirewa Happiness kayan nan? Ko dai in kira shi ne? Ba za su yi daɗin bacci ba.”
Hamdi dariya, Taj dariya. Sai sun yi kamar sun gama da sun haɗa ido sai a sake daga farko.
“Harda turaren angwanci yasa na nemo masa mai mugun tsada ya feshe jikinsa.”
Hamdi ta goge ƙwallar dariya da yatsa “Ni damuwata akwai fridge a ɗakin?”
“Fridge kuma? Akwai.”
“Yauwa dama don kada kazar ta buga.”
Su ka sake tuntsirewa da wata dariyar that was just contagious. Da mutum zai shigo ɗakin dole ya taya su. After 1am Taj ya raka Hamdi ƙofar ɗakin Mubina. Ta shiga ta sameta tana sallah. They just smiled at each other sannan Hamdi ta ɗauro alwala ta zo ta tayar a kusa da ita.
***
Yau dukkanninsu su ka tafi asibitin domin daga nan za su wuce su shiga jirgin ƙasa zuwa birnin Madina. Hajiya dai ta ce da Abba Habibu babu inda za ta har sai Yaya ta fara tashi da kanta. Anyi-anyi da ita ta tafi saboda akwai kulawa sosai a asibitin amma ta rufe ido ta ce su ƙyaleta. Alhaji ya goya mata baya tunda shi ma ba tafiya zai yi ba. Kamal kuma za a bar masa Abba da amaryarsa. Duk wannan zancen kafin su fito aka gama yinsa. Alhaji ya ce da Mubina idan tafi son fara yin Umrarta a nutse cikin ƴan uwa babu damuwa. Sai kawai ta duƙar da kai. Mama ta fassara masa da cewa ta amince da zaman ne. Kuma hakan yake a zuciyarta. Tun asuba mahaifiyarta ta kira ta su ka yi magana akan yin abin da ya kamata. Wasu lokutan mutum ya kan ajiye kunya da tsammanin al’ada ya yi abin da ya dace da halin da yake ciki.
Daga ɗakin Yaya su ka rankaya ɗakin Kamal. Ango ya dinga cika yana batsewa. Taj ne kaɗai ya san dawan garin. Ya yi ƙoƙari sosai bai yi dariya ya tona masa asiri ba. Sun fara yi masa sallama a zaton sa harda Mubina a tafiyar sai ya kaɗa baki ya ce,
“Mubina matso mu yi sallama, sannan ga kazar ki nan ki tafi da ita.”
“Innalillahiiii….” ta tattaro numfashi kafin ta dire “wa inna ilaihi raji’un.”
Ji tayi kamar ya tsomata a cikin ruwan sanyi saboda kunya. Ɗaki ya yi tsit kamar ruwa ya cinye su na wucin gadi.
“Ku fita mu tafi. Kamal, Allah Ya ƙara sauƙi.”
Ahmad ya yi ta maza ya kawo ƙarshen kallon-kallon da ake yi. Ai kamar jira su ke yi su ka fita a layi ko waige babu. Mubina ko motsi ta kasa yi.
“Da alama anaesthesia bata sake shi ba har yanzu doctor. Lamarin Happiness sai kin haɗa da haƙuri. ” cewar Taj.
Kowa ya watse. Babu mutum guda da ya kalli Mubina ko ya yi murmushi ko da ƙasa-ƙasa ne kuwa. Ba su isa ba ne. Duk barkwancin yayyensu sun san Yaya Kubra ko Yaya Hajiyayye ce ba za ta ɗaga mata ƙafa ba. Sun san wasan da ya kamata su shiga da wanda bai dace ba.
“Ashe haka ka ke Kamal?” Ta faɗi baki buɗe don har yanzu tana mamakin wannan magana.
Ya juya mata ƙeya “Me na yi?”
“Babu komai.” Ta rage murya tana magana a hankali amma yadda zai ji “dama Taj ya ce na lallaɓa ka da sauran allura a jikin ka.” Ta sami wuri ta zauna akan kujera ta juya masa baya ita ma. Ɗakin ya koma shiru.
Da ya ga babu Sarki sai Allah sai ya sauko. Yana magana abin tausayi.
“Jiya ba ki kyauta min ba. I waited.”
“Shi ne yasa ka bani kunya a gaban ƴan uwanka?”
Briefly ya labarta mata yadda jiya ta kasance a wajensa. Mubina ta dinga girgiza kai ita a dole ya bata tausayi. Ya gane sarai abin nata harda tsokana.
“Kar ki yi min dariya.”
That was it! Magiyarsa tamkar zuga ta koma a gareta. Dariya ta kufce mata ta kare baki ta yi.
Kamal samun kansa ya yi da zuba mata idanu kamar haɗuwar farko. She looked so cute tana wannan dariyar. Ya ji zuciyarsa tana neman cika masa ƙirji saboda farincikin da ya samu daga abin da take yi yanzu. Da ta gama dariyar tashi tayi ta dudduba ɗakin bata ga alamun nama ba.
“Ka saka min rai kuma ni ban ga kazar ba.”
“Laifin naki kenan.”
“Me kuma ya na yi?”
“Na zama abin tsokana dai da alama. To ki kwantar da hankalin ki domin kema kin shiga one chance yadda na shiga jiya.”
Ƴar dariyar da take yi ta daina babu shiri ta dawo kujerar gefen gadon ta zauna. Kamal ya sosa ƙeya.
“Ba na faɗa miki sai da na sa Happy ya canja min kaya ba?”
“Yesss”
“Kaya dai har sai da su Alhaji su ka shigo yi min sai da safe su ka ganni da su, na kasa cirewa. Shi da Abba Habibu ne su ka cire min. It took more than 10 minutes saboda su na tsoron fama min ɗinki.”
“Ya Rahman” Mubina kanta sai da taji kunya.
“Da su ka gama ne Alhaji ya ce sai na biya ladan wahalar da jikin girma. A gabana su ka cinye naman nan. Harda cewa ranar da za ki tare zai biya mu.” Ya ɗan cije baki “Saboda Allah me zai sa ya yi min zancen tariya? Don na ɗan yi kwalliya shikenan sai a fassara ni? Ko ni na kawo fitina duniya ai dole in jira nayi healing ko?”
“Ni dai na shiga uku.”
“Wallahi kin shiga. Kazar amarci surukan ki maza sun cinye. An barwa ƴaƴa tarihi.”
Kamar za ta yi kuka ta ce “to ni yanzu yaya zan yi?”
Kamal ya ware hannuwansa yana kallon cikin idanunta.
“You can start by giving me that first halal hug.”
Bata san abin da zai ce ba kenan da ba za ta zauna a kurkusa yadda kunyarsa za ta kama ta da yawa haka ba.
“Idan ka warke kayi da kan ka.” Ta faɗa a ciki-ciki.
“Mubina” ya tsare ta da ido.
“Na’am.”
“Now please.”
Magiya ce ko umarni? Ita dai bata gane ba. Abin da ta fahimta kawai shi ne zuciyarta tana muradin yin abin da mamallakinta yake so. She gave him the warmest hug. Zuciya da gangan jiki su ka sami kyakkyawar nutsuwa.
A lokacin da Kamal yake tunanin Mubina ta gama biyansa da alkhairi, she brushed his lips lightly da nata. Tsokana ta so yi, reshe sai ya juye da mujiya. Happiness got his happiness and he wasn’t willing to let go easily.
Kamal da Mubina Allah Ya ƙara lafiya da zaman lafiya!
***
Wani irin kuka Inna Luba ta fasa daga ɗaki mai firgitarwa. Malam da yake ririta ta tun jin Yaya ta tafi Saudiyya ya fito daga banɗaki da zariyar wando a hannu.
“Luba me ya faru? Mutuwa aka yi?”
Inna Luba kuka kawai take yi babu ƙaƙƙautawa. Amarya duk jarabarta jikinta ya ɗan yi sanyi. Shi yasa bata faɗi magana mara daɗi ba da ta fito. Banda haka da tuni ta fara domin tsufa bai rage mata komai ba. Da ƙyar Malam ya samu cikin kuka Inna Luba ta faɗa masa wayar da aka kira ta daga Kano.
“Surukar Abdulƙadir ce ta kira yanzu wai za ta yi min jaje.”
“Waye kuma Abdulƙadir?”
“Ƙanin Habibu mana.”
“To, sata aka yi ko gobara wani cikinsu ya yi?” Amarya ta tambaya tana jin haushin tsurkun da ta fito kuma da alama labarin ba zai ƙayatar da ita ba.
“Yarinyar nan ce…”
Malam ya dafa bango jiki na rawa. Sai ka rantse bai taɓa nunawa Yaya ƙyama ba. Ya marairaice sosai gwanin ban tausayi.
“Lubabatu bar zancen nan haka. Zuciyata ba za ta iya ɗaukar zancen mara daɗi akan gudan jini na ba.”
“Wannan kam dole sai ka ji. Wai anyi mata aiki an cire mata ƙoda guda ɗaya an dasawa wani yaro.”
Da wani irin zafin nama Malam ya zabura kamar ba tsohon da yake taku da ƙyar ba saboda ciwon ƙafa.
“Me???”
Yadda taji ta maimaita. Dama su kan gaisa a waya da ita a matsayin surukai. Ashe duk gargaɗin ds Abdulƙadir ya yiwa matar tasa akan ɓoye zancen sai da ta sanarwa ƴan gidansu kaf. Ita kuwa Mamansu da bata san ɓoye zancen ake yi ba ta kira Inna Luba domin ta jajanta mata. Jinjin ta bayar da ƙoda an dasawa wani ɗan balarabe a Makka.
“Jar uba! Kin ga kira Ɗandaudun nan ki haɗa mu kawai. ” Baba Malam ya nuna kansa yana jijjiga jiki “Ni za a ha’inta? Ɗiyar tawa za a feɗe daga zuwa ibada? Dama can ban yarda yana da kuɗin kai Jinjin Saudiyya ba. Matsiyaci mai tafiyar mata. Ina yi masa kallon wanda ko ƙuda ba zai iya kashewa ba ashe ja’irin ƙodar ɗiyata zai sayar. Allah Ya isa Habibu!”
To Inna Luba dai babu bakin kare Abba Habibu domin kuwa bata san gaskiyar me yake faruwa ba. Ana haka gida ya kaure da tsine-tsine da zagin bawan Allah Abba Habibu sai ga wani ɗan saurayi cikin jikokin Amarya. Inna Luba ta miƙa masa wayarta ko zama bai yi ba.
“Ya’u maza lalubo min lambar Sajida ka kira.”
Ya’u ya yi abin da ta ce ba tare da tambayar komai ba duk da mamakin da ya cika masa zuciya. Kiran na shiga ya miƙa mata wayar sai dai kafin ta ankara Malam ya karɓe ya manna a kunne yana masifa.
“Maza-maza ki yiwa ubaki waya ki ce ya kira ni yanzun nan.”
“Baba Malam me a ka faɗa muku?” Sajida ta fahimci ba lafiya ba “don Allah ka tsaya nayi maka bayani.”
“Ƴal ƙwal uba har ki na da bayanin da za ki mani? Me ya hana ki neman mu kafin yanzu tunda da alama kin san komi” ya yi ƙwafa “wato kun haɗa kai da baban ku za a kawo muku kuɗin jini ku wanki biyar ku tsoma biyar, ni da na san zafin haihuwarta kuma a barni da kukan rashin ɗiyata. To wallahi ba ku isa ba. Nemo shi ki ce masa lallai a mayar mata da ƙodarta.”
Sajida ta sake kwantar da murya
“Baba Malam ka yi haƙuri. Ba abin da ka ke tunani bane. Yaya taimako tayi da ceton rai.”
“Da ƙodarta? Ke Sajada, kada ki raina min wayau mana don kawai kin ga ina rayuwa a ƙauye. Tun Kaka da Kakanni ban taɓa jin an cire sassan jikin wani an dasawa wani ba. Zancen nan bai yi kama da wanda hankali zai ɗauka ba.”
Haƙurin ta sake bashi ya ji haushi ya surfa mata zagi daidai wa daida. Ya ce kuma ta saka a ranta cewa Yaya na dawowa zai maka Abba Habibu a kotu a raba auren su. Jin haka Inna Luba ta karɓe wayarta ta ce da Sajida tayi maza ta nemi Abbansu.
“Idan bai kira ni ba to nima zan bi shawarar Malam.” Ta katse kiran.
Hankalin Sajida ya tashi sosai. Ranar kwanan su Taj biyu da tafiya Madina ta kira ta sanar da Abba Habibu yadda su ka yi da su Baba Malam. Murnar sauƙin da su Yaya ke samu sai ta koma ciki domin kuwa nasa hankalin ba ƙaramin tashi yayi ba. Alh. Hayatu ya yi Allah wadai da halin surutun wasu mutanen.
“Wani lokacin sai ka yi tunanin akwai masu ɗokin zama ƴan yaɗa labari mara daɗi. Suna rawar jikin zama farkon waɗanda za a ji mummunan labari daga bakinsu. Banda haka wane irin rashin nazari ne zai sa a kira tsohuwa a tayar mata da hankali irin haka?”
“Yanzu ta ina zan fara? Ta yaya zan yi musu bayanin da za su fahimta?”
Abba Habibu cikin damuwa, Yaya kuma tana ta kuka. Tausayinsu ya kama Hajiya, musamman da ta tuna rayuwar ɗanta ce ta janyo mu su.
Jikin kowa yayi sanyi. Sun kira su Inna Luba amma ko kusa Baba Malam bai bata wayar ba. Shi kaɗai ya dinga faɗa kai ka rantse tunda Yaya ta taso bai taɓa juya mata baya ba. Maganganunsa duka ana ji domin faɗa yake yi iya ƙarfinsa. Har cewa Yaya ya yi ta tabbatar ta karɓi takardarta kafin su dawo. Hajiya dai sai da tayi kuka mai isarta. Yanayin ɗakin ya koma wani abu daban a tsukin lokacin.
Ana haka sai ga kiran tawagar Madina. Dama kullum sai sun kira an gaisa. Hajiya na karɓa ta ce a bawa Yaya Kubra wayar. Sai da ta fara gargaɗinta akan kada maganar da za su yi ta fita musamman zuwa kunnen Hamdi sannan ta tambayeta shawara.
“Ke ce likita Kubra. Me ya kamata mu yi? Ta ina za mu ɓullo mu su ta yadda za su fahimci girman taimakon da Yaya tayi har ma su yaba mata?”
“Hajiya turo min numbar da zan same su.”
“Bari na karɓa sai na turo miki. Amma don Allah ki kiyaye.”
Kallo su ka bita da shi har ta tura numbar sannan tace musu su duka babu mai ilimin da zai iya yin bayanin da su Inna ba za su ɗauka son zuciya ba.
“Mu bata dama tunda ɓangaren aikinta ne. Na san Kubra, za ta yi abin da ya dace.”
*
Gidan Baba Malam fa babu lafiya. Inna Luba kwanciya tayi zazzaɓi ya rufe ta yayinda maƙota su ke ta zaraf-zaraftu a ƙofar gidan ana ta zuwa jaje da ganin ƙwaf. Amarya ce ta fice fit ta fesawa waɗanda ta san za su tayata yaɗawa. Kafin wani lokaci gari ya ɗauka. Abin ne da mamaki ace mutum ya bayar da ƙoda sukutum kuma yana nan da rai.
Waya na ringing Inna Luba ta tashi da sauri ta ɗauka. Yaya Kubra ta gaishe ta a ladabce sannan ta buƙaci Innar ta haɗa ta da matashi ko matashiya idan akwai a kusa.
“Yarinya ko me za ki ce ki faɗa min kawai.”
“Don Allah ki yi min wannan alfarmar Inna. Ki taimaka.”
Ba don ta so ba ta fito tsakar gidan. Cikin sa’a tayi kiciɓis da Ya’u. Har yanzu bai koma gidansu ba tunda ya san me yake faruwa. Rigimar kakarsa Amarya da Inna Luba ba sabgarsa bace. Yana ɗasawa da kowa a gidan.
“Inna kina buƙatar wani abu ne?” Ya matso kusa da ita da sauri.
“Gashi” ta bashi wayar ta koma cikin ɗakinta.
Ya’u ya saka waya a kunne ya ce “hyalo?”
Kai tsaye Yaya Kubra ta bijiro masa da buƙatarta bayan ta gabatar da kanta kuma taji daga ɓangarensa. Yadda take magana kaɗai ya yi masa kwarjini don jikinsa har rawa yake wajen amsa mata.
“Aiki ka ke yi ko karatu?”
“Aiki ne. Ina koyarwa a wata pravet a nan kusa da mu.”
“Masha Allah. Mal. Ya’u nawa ne albashin ka tsakani da Allah?”
“Et fife (8,500) ne.” Ya amsa mata cikin basarwa. Ba ya so tayi tunanin shi ɗin cima zaune ne.
“To zan baka dubu ashirin a yau in sha Allah idan buƙata ta ta biya.”
Gigicewa yayi sosai yana ta doka murmushi ba ji ba gani. Ta gama da shi da tunaninsa kaf.
“Me ki ke so nayi?”
“So nake ka samo min waya mai yin bidiyo call na whatsapp.”
“Shike nan?” Ya tambayeta da mamaki.
“Ƙwarai kuwa. Idan an samo ka bani lambar in saka data domin wayar za ta iya ɗaukar lokaci.”
Ya’u baki har kunne don farinciki ya ce “wayata tana yi sai dai bani da data sannan wassof ɗin ma ya yi ispiya.”
“Wannan layin?”
“Eh.”
Cikin minti biyar Ya’u yaga 25G. Gani yayi abin kamar wani mafarki da zai iya tashi kodayaushe. Shi da ya saba saka datar naira ɗari zuwa ɗari biyu sa’i da lokaci ina zai kai wannan? Ya yi updating komai da sauri sannan da kansa ya kira. Dr. Kubra Hayatu tayi masa wani irin kwarjini. Ya durƙusa har ƙasa ya gaisheta sannan ya kaiwa Inna Luba wayar. Kafin a fara jawabi Baba Malam da Amarya suma sun hallara. Ya’u yana gefe Yaya Kubra ta zauna tayi mu su gwari-gwari game da ciwon Kamal, zuwan Yaya asibitin, bayar da ƙodar da ma zuwan Abba Habibu.
Inna Luba tayi kuka babu adadi ba. Muryarta duk ta dashe.
“Yanzu ƴar nan kina da tabbacin rayuwar yarinyar nan ba za ta tawaya ba?”
“In sha Allahu babu abin da zai biyo baya sai tarin alkhairi. Addu’a da kulawa kawai take buƙata.”
Baba Malam kuwa cewa ya yi “Idan gudan ƙodar ta sami matsala fa?”
Yaya Kubra ta jinjina tambayar don ta san da wuya a rasa mai yi.
“Komai na Allah ne Baba. Addu’a da kulawa kaɗai za ku iya yiwa Yaya. Sanin gobe kuma sai Allah maɗaukakin Sarki. Abu guda nayi imani da shi, Allah ba Ya taɓa barin wanda Ya fawwala Masa al’amuransa ya taɓe. Mu kyautatawa Allah zato, in sha Allahu babu nadama a cikin sadaukarwar Yaya.”
“Allah Ya sa ƴar nan. Allah Ya dawo mana da ita lafiya.”
Yaya Kubra ta tausayawa Inna Luba matuƙa.
“Inna na san Yaya a ƙalla za ta yi wata a ƙasar nan kafin ta sami sahalewar shiga jirgi daga hukumar lafiya. Saboda haka ki fara haɗa jaka. Zan yi magana da ƙannena ma za mu ji yadda za ayi a samar mi ki passport da visa.”
“Allahu Akbar. Ni ɗin?” Ta kalli Baba Malam “wai Saudiyya zan tafi. Ikon Allah. Allah Buwayi gagara misali. Ni dai Lubabatun ko wata ƴar nan?”
Yaya Kubra ta sha dariya kafin su gama waya. Tana kuma ankare da fuskar Baba Malam. Yaƙe kawai yake yi.
Alhaji ta kira ta tura masa lambar Ya’u ta ce ya kira ya haɗa su Yaya da Innarta. Haka kuwa aka yi. Sun ji daɗin ganin juna. An dai sha koke-koke da addu’o’i. Har Kamal sai da su ka gaisa da shi. Ya yi musu godiya sosai da alƙawarin zuwa har gida idan ya dawo in sha Allah.
***
Kwanci tashi babu wuya a wajen Allah SWT. Yau kimanin sati uku kenan da yiwa Kamal dashen ƙoda. Sauƙi ya samu sosai domin duka an sallamo su daga asibiti. Likitoci dai sun hana su barin ƙasar domin suna buƙatar kulawa sosai har na tsahon wata biyu zuwa uku.
“Ina ganin gara na kama mana gida kawai. Zaman hotel ba zai yiwu ba” Alh. Ya ce da matansa suna zaune duka su huɗun tare da shi a ɗakin hotel.
Inna ta ce “Hakan ma shawara ce, amma kafin nan ya kamata a san masu zama don a kama ɗan daidai. Sauran yaran nan su zo su koma gida haka nan.”
“Kamar kin shiga zuciyata akan raguwar nan. Mata sun baro mazajensu sun tare a asibiti ayi ta hayaniya kullum” cewar Mama.
“Kamawa fa tayi.” Umma mai ɗan sauƙin ta ce tana murmushi.
“Tunda dai suna samun lafiya mu kanmu sai mu ragu. Ko kuwa Alhaji?”
“Wannan shawarar ku ce. Ni dai ƙafata-ƙafar Habibu da iyalinsa.” Ya gyara zama yana sauraron su.
Hajiya aka bawa dama. Ta zauna ta gama lissafinta ƴan uwanta su ka yi na’am. Umma za a bari tare da Bishir. Sai kuma Taj da Hamdi saboda zamanta kusa da Yaya yana da mahimmanci. Mubina ma babu inda za ta je. Sauran kuwa Alhaji ya ce da kansa zai faɗa musu su shirya nan da kwana uku su za su tafi. Sannan akwai wanda zai nema a samar mu su gida.
“Dr. Hadifi ya ce yana son ganin mu ni da Habibu. Idan mun dawo zan yi magana da su.”
*
Bakin Abba Habibu ya kasa rufuwa bayan fitar Dr. Hadifi daga ofishinsa inda ya barsu su yi shawara kafin a bashi amsar batun da ya zo da shi.
“Habibu ba ce wani abu mana.”
Abba Habibu ya girgiza kai “wallahi bani da abin cewa. Ni dai abin ya yi min girma. Anya zan karɓa kuwa?”
Alh. Hayatu ya ce “me zai hana? Roƙa kayi?” Ya yi gyaran murya “ba ka ganin kamar wata dama ce daga Allah SWT?”
“Har na isa a bani abu makamancin wannan?”
“Kada ka yi saɓo mana. Kowane bawa da arziƙinsa Allah Ya ke halittarsa. Kuma rabon mutum baya taɓa wuce shi. Ko dai ka je da ƙafarka ko ya biyo ka har inda kake.”
“Haka ne. Allah Ya zaɓa mana abin da yafi alkhairi.”
“Amin amma don Allah ka yi shawara mai kyau.”
Abba Habibu ya yi murmushi “Zan yi istihara in Allah Ya yarda.”
*
Zuwa yamma kowa yaji abin alkhairin da ya sami Abba Habibu. Dr. Hadifi ya yi masa kyautar gidan abinci sukutum a nan cikin birnin Jeddah. Tsohon ginin na Kawunsa ne ya saya ashe zai yi masa amfani. Abinnda Yaya tayi ya burge shi matuƙa, sai kuma ya tuna a hirarsu Abba Habibu ya ce ya taɓa sana’ar abinci a nan.
A hoto ya nuna musu gidan. Kusan komai na kayan aiki akwai, gyaran da za a yi kaɗan ne sai kayan abinci da za a tanada. Yayi masa alƙawarin yi musu igama shi da Yaya da duka ƴaƴansu. Sannan zai yi masa gyare gyare da kuma zubin kayan abinci na farko kafin ciniki ya kankama.
“Ku buɗe Nigerian restaurant wanda yake serving abincin ku na gargajiya.” Ita ce shawarar da ya bashi.
Kamar haɗin baki duka shawararzu guda. Ya karɓa. To dai ya karɓa ɗin ranar da ragowar masu tafiya za su wuce. Ba su tafi ba sai da su ka je aka ga waje aka sanya albarka.
A gida ma ƴan uwa da su Zee anata murna da rawar jiki.
“Ki bar tunanin tafiya dai kina da aure. A daure a koyi larabci saboda idan na dawo zai yiwu na daina jin Hausa.”
“To nima ai ba yanzu za ayi biki ba sai na kai level 4.”
Daga cikin ɗaki Anti Zinatu ta ɗago murya “to uwar iya. Ke da yanzu ki ke jarabawar gama sakandire kike kiran level 4 saboda sallamamme ne ya aure ki? To bari iyayen naki su dawo naji ko da yawunsu ki ke wannan saɓon mai girma. In baki yi wasa ba wallahi ranar asabar zan ce da Baballen ya zo ku tafi.”
Hankalin Zee tashi yayi tana neman yin kuka. Halifa kuwa dariya harda ƙyaƙyatawa.
***
Godiya da kyautatawar da Ahmad ya yi wa Zahra ba a cewa komai. He truly appreciated kulawar da ta bawa Mami duk da irin zaman da su ka yi a baya. Da ya fito daga wajen Mamin ne ya yi mata zancen Salwa.
“Babanta ne ya damu wai naje naga gidanta.”
“Hakan ne ya kamata dama. Ba fa a canjawa tuwo suna.”
“Ina ki ka baro amala da fufu? Ko duk ba ƴan uwan juna bane?”
Tayi dariya “ba zan yi musu da kai ba. Don Allah ka ɗauki matsayinka na babba ka wakilce kowa ka je ka ganta. Babu mamaki ma kaga ta sauya. Aure ai ba wasan yara bane.”
“Allah ko? Shekararki nawa ne a ciki tuna min.”
“Lokaci ɗaya mu ka yi da kai.” Ta zolaye shi.
*
Da yamma Ahmad ya kira Salwa ba don ya so ba. Ita kuwa da azama ta ɗauka don ta fidda ran sake ji daga gare shi. Gashi tana jin kunyar zuwa gidansa. Alh. Usaini har gorin dangi yayi mata. Bata yi shawara da kowa ba ta kira Anti Zabba’u. Ai kuwa ranar taga tashin hankali. Irin haukan da su ka yi a gidan Ahmad su ka kwatanta a nan. Alh. Usaini ya zo ya gani ya ci musu mutumci la’ada waje daga su har ita. Banda Mami ta jawo musu ai da yanzu dangi sai sum ture na uwa da uba. Kai ba don abin da tayi ba hatta iyalin Alh. Hayatu sai sun fitar da ita kunya.
Purewater ta ɗauko guda ɗaya ta sako akan plate ta zo ta ajiye a gaban Ahmad. Ya bi ta da kallo ita da ruwan ya watsar.
“Ɗauke abin ki ba ruwa na zo sha ba.”
Kunyar taji ta ce “Ko na fita na siyo maka mai sanyi? Ko zoɓo?”
“Zauna.”
Zaman tayi tana godiya ga Allah da bai nemi hakan ba don ko sisi bata ajiye ba. Sadakinta ma ta nema ta rasa a cikin gidan. Ta san wanda ya ɗauka amma a yanzu tsoron tada maganar take yi.
Ahmad ya sami damar ƙare mata kallo daga sama har ƙasa. Abin tsoro. Auren da bai fi wata guda ba duk ta ƙare tayi baƙi sai idanu a cikin loko kamar mujiya da haƙora gayau. Falon da ta ajiye shi babba ne irin wanda kowacce amarya za ta yi farinciki da mallakarsa. Fitilu na alfarma, POP ceiling da dukkan wani abu da zai sa ace gida ya haɗu akwai shi. Abin da babu shi ne funiture da electronics. Kuma da alama har cikin ɗakuna da kitchen haka abin yake. Shima a yanzu akan tabarma yake zaune. Ɗakin kwananta ma tabarmar ce. A cikin ɗakin Alh. Usaini kuma katifar maigadi ya ɗauko bayan mahaifinsa ya kira maigadin ya ce ya bar aikin gidan.
“Salwa wannan rayuwar ce ashe take jiranki shi yasa ki ka kasa kwantar da hankalinki akan rashin samun biyan buƙatar zuciyarki ko?”
Ta ina za ta fara faɗa masa tayi nadama amma a lokaci irin wannan da bata da amfani? Yanzu ta gane cewa idan so cuta ne da gaske haƙuri magani ne. Da ta haƙura da Taj da tuni Mami ma bata gamu da hatsarin nan ba. Everything would have been fine. Rayuwar gidan Alh. Usaini babu daɗi ko kaɗan. Har yanzu bata gabansa, hakan bai dame ta ba kamar yadda ta zame masa wajen huce haushi idan ya fita bai samo komai ba. Mahaifinsa bai barshi da komai ba sai gidan nan albarkacin auren da ya yi. Duk inda yake ajiya a banki ya sa an rufe masa da dogon gargaɗi akan kada ya kuskura ya tada maganar.
“Na san irin wadaƙar da kayi min da dukiyata. Idan zan bi kayana na tabbata baka da kuɗin biyana saboda haka magana ta mutu a tsakaninmu. Duk ranar da ka dawo mutum ni kuma nayi maka alƙawarin dawo maka da komai naka. Idan ba haka ba kuwa sai dai ka jira gado in na riga ka.”
Yanzu rayuwarsa ta koma bibiyar abokai da tsofaffin yaransa yana maula. Wataran a dace wataran kuma a wulaƙanta shi. Da ya gaji ne ma ya goranta mata rashin gara da kayan ɗaki. Ita kuma saboda ɗanyen kai ta kira Anti Zabba’u. Ranar anyi sa’a ƙanwarsa ta zaga ta bayan idon iyayensu ta aiko masa da kaji da jallof ɗin shinkafa ta gaske. Kafin ya dawo daga wajen abokinsa sun cinye tas. Ita kanta Salwa bata ko ɗanɗana ba. Tana ta magiyar kar su taɓa aka rasa mai sauraronta ma. Ɗan uwa aka ce rabin jiki. Ahmad ya tausaya mata sosai. Kayan ɗaki da electronics babu abin da bai tanadar mata ba amma ta watsa masa ƙasa a ido.
Suna zaune ya danne fushinsa yana ta yi mata nasiha tana ta kuks sai ga Alh. Usaini. Takalman namiji kawai ya gani ya yi jifa da ledar hannunsa ya zare belt ya afka musu. Salwa na ganin shi ta tashi ta tsaya a gaban Ahmad ta bubbuɗe hannuwa da ƙafafu ta kare shi. Ai kuwa belt ta sauka a jikinta ta gantsare don azaba. Ya sake ɗagawa karo na biyu Ahmad ya miƙe. Kwarjini da cikar mutumtakarsa su ka sanya Alh. Usaini yin laƙwas kamar dafaffen alayyahu.
Ahmad ya riƙe belt ɗin tare da hannunsa ya nuna masa Salwa.
“Duk abin da za ka yi, musamman wanda ya shafi mu’amala da mutane kaji tsoron Allah. Da kai da ita da gurɓatacciyar rayuwarku ku ka haɗu amma hakan ba yana nufin da ita za ku ƙare har ƙarshen rayuwa ba in kun so.”
Ficewa yayi ko waige babu. A waje yaci karo da ledar da Alh. Usaini ya yar. Taliya ce leda ɗaya sau mai, maggi da kayan miya na naira ɗari biyu. Wani abu yaji ya tokare masa wuya. Yanzu Salwa ake ciyarwa a haka? Lallai kowa yaƙi sharar masallaci zai yi ta kasuwa.
Ya koma gida cike da damuwa. Ya kira Abban Salwa akan maganar kayan ɗaki ya ce ya rabu da ita. Darasi yake so ta koya a cikin auren nan. Hujjojin da ya bashi duka ya gamsu da su. Duk da haka washegari ya tura ƴar ƙurƙura gidan shaƙare da kayan abinci.
“Idan da kuɗi a wayarka don Allah ka bani aro na kira Yaya Ahmad nayi masa godiya.”
Tsaki ya banka mata ya tashi ya fita da sauri ya bi bayan mai ƙurƙurar nan da gudu. Sai da ya kusa ƙarshen layi ya tsaya. Yana faman haki ya ce ya taimaka masa da numbar wayar wanda ya aiko shi. Mutumin ya karanto masa ya kwafa. Da numfashinsa ya daidaita ya kira shi.
“Dama godiya na kira nayi maka.”
“Ku dai ku ji tsoron Allah daga kai har Salwa. Rayuwar da kuke ciki Allah Ya azurta masoyanku da fin ƙarfinta. Cikin minti guda za a iya canja komai ma rayuwarku amma Allah bai bayar da iko ba. Hakan kaɗai ya isa ya zame muku izina. Allah Ya kyauta.”
Tunawa yayi da wani kalamin da yaji daga bakin Abban Salwa wanda shi kuma Baban Alh. Usaini ne ya faɗa masa a lokacin da ya nemi shawararsa game da makomar rayuwar yaran nasu.
“Yunwa, ƙishi da rashin kayan more rayuwa zai sa su yi laushi harma ka ga nadama nan ba da jimawa ba a tare da su. Biyewa wannan ba ƙaramin ganganci bane. Yunwa ta ishi kowane shege darasi. Yanzun nan za ka ga mutum ya shiga taitayinsa. To amma fa ƙoshi shi kuma yana fito da ɗan iska cikin mutane. Da zarar tumbi ya ɗauka sai kowane rashin daraja ya biyo baya indai mutum ba nagari bane. Shin Alhaji ba ka ganin yadda almajirai su ke rashin mutumci a unguwa idan abinci ya wadace su? Wani fa a ƙofar gidanka zai zubar da abinci ya ce ka bashi gaya ko babu nama.”
Abban Salwa ya gyaɗa kai “wannan gaskiya ne.”
“Ina son Usaini amma nafi son gyaruwarsa. Idan mu ka yi saurin karaya akan su to ka sani komawarsu gidan jiya abu ne mai sauƙi. Irinsu bayan addu’a da nasiha dole a bari su gane cewa kyautatawa ce daga Allah privileges ɗin da su ke samu ba wai dolensu bane don sun isa. Suna buƙatar duniya tayi musu atishawar ƴan tsaki!”
Abu ne mai wuya iyaye su iya ɗauke kai idan ƴaƴansu su ka shiga irin wannan yanayin to amma fa wani lokacin dole a tauna tsakuwa don aya taji tsoro.
***
“Zancen Port Harcout naji tana yi a waya wallahi. Don Allah kayi wani abu kafin ta ƙarasa shiga duniya mu shiga uku.”
Iyaa ke wannan maganar da Baba Maje tana kuka sosai. Sababbin tsare-tsare Baba Maje ya kawo cikin gidan bayan fitowar Ummi daga police station. An karɓe babbar wayarta sannan ba a barinta ta fita ko ƙofar gida. Ƙawayenta tun daga soro ake sallamarsu. Dangi kuma aka sami abin so. Kowa ya buɗe baki a gidan biki ko suna zancenta ake yi ana aibata halinta. Isassu ma har gidasu ke zuwa su faɗi maganganu son ran su. Yarinya a cikin gidansu ta zama mujiya. Tsangwama ta ko’ina fuskantarta take yi.
Watarana Iyaa ta fita sai tayi mantuwa. Ta dawo za ta wuce ɗakinta sai taji Ummin tana waya tana faɗawa wanda su ke magana ya saya mata ticket ɗin luxurious bus za ta fito nan da kwana huɗu. Iyaa ta sulale ta fice bata bari ta san da zuwanta ba. Sai dare ta sami Baba Maje ta faɗa masa.
“Ummi tamkar ba jinin mu ba. Yarinya sai azabar taurin kai da son zuciya. Duk abin da yake faruwa bata saduda ba” Tana kuka tayi maganar.
“Kada ki yi furucin da zai kai ki ga nadama akan Ummi. Ni dai na fahimci hanyoyin da muka ɓullo ba za su haifi ɗa mai ido ba. Ina kuma tsoron ace jini na ta shiga duniya.”
“To yanzu meye abin yi?”
“Aure zan yi mata.”
“Da wa? A dangin mu wa za ka tursasa ya bari ɗansa ya aureta?”
“Kofur Ɗanliti zai auri Ummi” Baba Maje ya faɗi da wani sense of relief.
Iyaa tayi shiru kafin daga bisani ta ce “haka ne.”
“Ko kina da wata shawarar? Irin wannan auren ba shi mu ke yi mata sha’awa ba tsakani da Allah.”
Magana su ke yi ƙasa-ƙasa cikin alhini gwanin ban tausayi.
Iyaa ta numfasa “yanzu za ayi ta aibata auren ana yamaɗiɗi da mu a cikin dangi da unguwa idan aka ga mijin da ta aura. Wasu ma su ce Allah Ya ƙara pi.”
“Sai mu toshe kunnuwanmu tunda ba a canjawa tuwo suna. Mune dai iyayen Ummi duk inda za a je a dawo.”
“Amma kana ganin za ta zauna? Mutum irin Kofur ɗinnan yana da abin riƙe mata sama da guda?”
Shima kansa Baba Maje ba wai son zaɓin nasa yake yi ɗari bisa ɗari ba. Da babu ne dai gara babu daɗi.
“Haka za mu haƙura don sau dubu gara ace abinci ne bata da shi a gidan miji da dai ta shiga duniya. Indai da rai da lafiya ba zan bari yunwa ta kama ta ba alfarmar Annabi SAW.”
“Wahala za ta ƙaru a kan ka. Ba gara mu nemi wata dabarar ba?”
“Ummi bata jin magana kema kin sani. Kuma wannan shawarar da na yanke ba rashin so bane ya janyo. Ban san yaya lahira take ba amma a iya abin da Allah Ya hore min in ji a duniya game da iyalina, sai nake ganin ko aljanna na samu ba zan ji daɗinta ba idan wani cikinku bai riskeni ba a can. Ina tausayin makomar ƴata idan ba ta yiwa kanta karatun ta nutsu ba.” Kawai sai ya soma hawaye.
Kusa da shi Iyaa ta koma su ka riƙe hannu suna kuka mai ratsa zuciya.
“Bawa baya sanin matsayin ibadarsa sai ya koma ga Allah. Kuma muna yi ne cikin kyautata zato da cikar yaƙini to amma bamu san baɗini ba. Yaya kike ji za ta kasance ace duka gidana babu wanda ya dace balle ya ceci sauran? Ai ance ana bawa salihan bayi ceto ko? Shi yasa na damu sosai.”
“Kafin ma a kai ga lahira ba ka ganin kamar iyalin Habibu sun ja baya da mu? Ka duba fa hatta aikin da aka yiwa Jinjin sai Baballe ne ya ji a wajen Zinatu.”
“Kai anya kuwa? Kada mu ɗauki haƙƙinsu.” Baba Maje ya faɗi duk da yafi yarda da zancenta.
A sanyaye ta ce “nima bani da tabbas, hasashe ne kawai duba da abubuwan da su ka faru. Ka san Allah da Siyama ce ta auri yaron da ya fito daga irin gidan nan namu sai na sa an sako min ita. Zan ji tsoron kada Ummi ta cutar da ita.”
“Kamar kin shiga zuciyata. Ina ta tunanin ko dai in sa ya sauwaƙe mata. Ƙila sun kasa faɗa mana ne saboda kawaici.”
“Allah Yasa bai taɓa musu ƴa ba. Ka san yaran yanzu da mugun rashin haƙuri.”
“Zan tuntuɓe shi. Tunda auren dama ba na soyayya bane. Zumunci mu ka so ƙullawa kuma da alama ba zai yiwu ba.”
Wani abu Ummi taji ya wuce mata mai ɗaci. Ta juya a hankali ta koma ɗakinsu. Ɗazu ta ga fitar Iyaa sai ta zargi ko ta ji wayar ds tayi. Shi ne ta biyo ta da Babansu ya dawo. Jikinta ɓari ya dinga yi har ta isa ta faɗa kan gado. Da yake zuciyar ta jima babu tunanin komai sama da son kai, hassada da sharholiyar duniya, sai ta kasa kuka. Ta kuma rasa addu’ar da ya dace tayi. Haushin kanta kawai take ji da takaicin jin wayarta da Iyaa tayi.
*
Kofur Ɗanliti har gida ya zo neman auren Ummi bayan fitowarta da kwana ɗaya. Ta zauna ta sille shi da rashin albarka iri-iri. Baba Maje sai ya bashi haƙuri ba don komai ba kuwa shi ne yadda yake gudun me zai je ya dawo. Ummi idanunta a buɗe suke. Kada tayi wa Ɗanliti abin da auren zai zo ya mutu da wuri. To amma da alama zai iya riƙonta duk botsarewarta. Haka dai yake gani amma bashi da tabbas. Saboda haka bayan shawararsu da Iyaa, sai ya kira shi su ka yi magana.
“Me yasa kake son auren Ummi duk da ka san wani abu cikin halayenta?”
Ɗanliti ya yi murmushi da confidence “ina sonta ne Baba.”
“Me yasa kake son mace irinta?”
“Haɗi daga Allah. Kuma da naji laifinta sai na tuna da tawa samartakar.” Gyara zama ya yi domin jindaɗin abin da zai faɗa.
“Baba ni fa tsohon ɗan daba ne.”
Kallon Baba Maje yayi yana jiran ganin tsoro ko firgici sai yaga babu ko ɗaya. Neman ƙarin bayani kaɗai yake iya gani. Ɗanliti sai ya yi masa tun kafin ya tambaya.
“Nayi dabanci da shaye-shaye sannan na taɓa tsibbu.” Baba Maje yaji hankalinsa ya tashi amma kuma a yanzu dai bashi da wani zaɓi.
“Abubuwa ne da na san za ka sami labarinsu idan ka tashi bincike a kaina shi yasa nake faɗa maka. Na riga na tuba tuntuni ina aiki kamar yadda ka sani.”
Wata zuciyar tana ƙwanƙwasarsa akan ya fasa yayinda wata take tuna masa da me zai iya faruwa idan Ummi ta shiga uwa duniya.
“Na baka amanarta. Don Allah idan ka ga abin yafi ƙarfinka ka dawo da ita gida. Bana son a kai ƙadamin da za ta gudu domin yanzu ma iƙirarin da take kenan.” Yanayinsa ya nuna tsantsar damuwarsa “ba na son zama abin nuni da kwantace ace ƴata ta shiga duniya.”
“Ba za ta shiga ba da yardar Allah. In Allah Ya so sai kayi alfahari da bani ita.”
Da daddare a ranar ya faɗa mata shirinsa a kanta bata ce komai ba. Abin ya bashi mamaki sosai. Haka dai yana ta tsoron kada a wayi gari ta gudu kafin auren amma yaji shiru. A fuska da baɗini bata son auren amma ta rasa gane me yasa ta kasa kataɓus. Auren tubabben ɗan tsubba zata yi bata sani ba. Surkulle da siddabaru babu wanda bai iya ba, kuma babu wanda bai shirya yi ba a kanta domin ya samu ta zauna dashi. Ko bayan zuwansa na farko ba wai haƙura ya yi ba, shiri ya tafi sakewa.
Ƴan uwan Baba Maje da ya neme su akan bikin sun yi murna ƙwarai. Ashe kowa na tsoron kada ya roƙi alfarmar haɗata da nasa ɗan saboda mugun halinta. A ranar da ya kamata ta gudu, a ranar aka shafa fatiha tsakaninta da Kofur Ɗanliti.
***
BAYAN WATA UKU
Taj da Kamal sun duƙufa aikin gyara ko ace jeren sabon gidan Abba Habibu da Yaya. Hawa na uku kuma na ƙarshe a ginin gidan abincin da aka bashi ya mayar gida. Ko sisi basu bari ya kashe cikin kuɗin da Dr. Hadifi ya ba shi ba. Iyalin Alh. Hayatu musamman Kamal su ne suka yi komai.
An sallamo su daga asibiti jiki ya yi kyau sosai. Duk da haka Taj ya hana shi ayyukan ƙarfi. Shi da Abba su ke ta kai komo. Abba Habibu da Alh. Hayatu kuma sun fita ana ƙarasa cike-ciken takardun shaidar mallaka da sanya hannun hukumomin da su ka dace.
A can gidan da Alh. Hayatu ya kama kuma Inna Luba da Baba Malam (Alhaji ne ya biya masa) sun iso kwana biyu da su ka wuce. Su Amma da Yaya Babba ma duk sun zo amma sun wuce Madina. Sai an gama gyare-gyaren gida da restaurant gabaɗaya za su rankaya dukkaninsu su tafi gida. Su Abba Habibu za su koma su kimtsa a tsanake sannan su koma a fara sana’a.
Hamdi da Mubina sun biyo su amma sun fita saya musu abinci. Da su ka dawo da ledoji niƙi-niƙi masu sauke kaya duk sun tafi tare da Abba. Babu kowa sai mazajensu.
Ɓata fuska Hamdi tayi suna shiga falon ta zube ledojin hannunta.
“Happiness kaga rigima ko? Don Allah ban ce su zauna in siyo abincin ba? Yanzu gashi nan ta dawo tana wani ɓata rai.”
Kamal ya tashi cikin nutsuwa don har yanzu baya yarda ya saki jiki kamar da.
“Angel me ya sami ƙanwata ne?”
Mubina ta kalle shi ta mayar da dubanta ga Hamdi wadda abin mamaki ta fashe musu da kuka.
“Kun gama da ɗakunan?” Mubina ta tambayi Kamal.
“Eh amma me ya same ta?”
Shi da Taj duk sun shiga damuwa. Taj ya koma kusa da ita yana son ɗago mata kai taƙi yarda. Mubina ta nuna hanyar ɗakunan da ido, Kamal ya fahimta sai ya tashi ya bi bayanta. Suna shigewa ciki Hamdi ta faɗa kan Taj ta sake dasa kukanta daga farko.
“Don Allah ki yi min bayani mana. Me na yi miki?”
Cikin kuka ta labarta masa “naje sayan ice cream wai sai da aka zo kaina mutumin ya ce babu chocolate.”
Mamaki ya kama Taj “shi ne kike kuka? Yaushe ma ki ka fara son chocolate flavour ɗin?”
“Yau shi nake so.”
Tashi ya yi “bari na fita na nemo miki I am sure ba za a rasa.
“Ba zai zama irin nasu ba. Ni shi nake so.”
Taj yaga abin na gaske ne sai ya koma lallaɓata.
“Ko in yi miki? Mine will taste even better.”
“Na su nake so” ta tura baki.
“Ahhh to gaskiya Mubina ta zo ta duba min ke. Alamu sun nuna rigimar nan ba nan kusa za ki daina ta ba.” Ya rungumeta yana dariya.
Ture shi tayi “ni lafiyata ƙalau kawai ka samo min chocolate ice cream.”
“In ki ka ce nima na zama cream ɗin ai zama zan yi maman babyn Taj.” Ya dinga kashe mata ido.
Kunya taji ta rufe ido tana dariya.
“Auuuu. Kin ma sani kenan. Tun yaushe?”
Leɓenta ta taune tana murmushi “a hanya Mubina ta sa mu ka tsaya a clinic.”
Rungume juna su ka yi Hamdi tana tunanu. Yanzu haihuwa za ta yi ta zama maman wani? Kuma idan an ɗaga baby a ce na Taj ɗinta ne. Lallai Allah ne mai juya al’amura yadda ya so.
Katse mata tunani ya yi “zo mu ci abinci.” Ta zauna ya ce “mun kusa komawa gida na sami ƴancin dafa miki abin da ranki yake so.”
“A baki za ka bani.”
“An gama.”
A cinyarsa ya ɗorata. Rabi cin abinci rabi rarrashi da kalamai masu daɗi.
*
Murnar ƙaruwar da za su samu su ka gama yi sannan Kamal ya langaɓe kai ya ce
“Doctor zo ki gani ban warke ba har yanzu?”
Tayi dariya “Sai nan da wata uku.”
“Come on Angel. Kada fa ki fara ɗaukin haƙƙina. Ni dai gaskiya so nake ki tare.”
“Yanzu ba tare muke ba?”
“Tariyar gaske nake nufi. Ni ma so nake ki fara rigimar ice cream.”
“Sai dai hot cream.”
“Wasa ma ki ka mayar da maganar ko? Do you even love me Angel?”
Mubina ta koma gabansa ta durƙusa a gabansa ta kwantar da kanta a cinyarsa sannan ta sanya hannuwanta ta zagaye shi.
“Har ka fara kokonton son da nake maka?”
“I ….I am sorry.” Ya shafa fuskarta “na fiye rashin haƙuri ko?”
“No, ni ce dai na fiye tsoro. I just don’t want to take any chances.”
“Ke ce likitan, dole nayi biyayya. Allah Ya kai damo ga harawa dai kawai.”
Dariya tayi “In ce amin kuwa? Wannan addu’a kamar ana yi min tanadin cin zali.”
“Meye wani cin zali? Ai kawai ki ce addu’ar mugunta nayi miki.”
“Ni dai ban ce ba”
“Ni na ce”
Sun ɗauki lokaci suna zolayar juna da nunawa juna soyayya kafin yunwa ta hana su sukuni. Ya tashi zai je falo ɗauko mu su nasu abincin Mubina ta ce ya yi haƙuri domin kuwa bai kamata ya je inda ƙannensa su ke ba a wannan lokacin.
“Kema dai kin fiye assumptions. Ina gidan ai babu abin da zai faru.”
Mubina ta ce “do you want to bet?”
“Happy fa ba kunya gare shi ba. Na haƙura.” Ya koma ya zauna yana yamutsa fuska.
Sai da Mubina ta gama yi masa dariya sannan ta tuna masa da za su iya kiran su a waya. Taj ɗan duniya sai cewa yayi wai Kamal ya so yiwa Mubina horon yunwa ne, if not me ya hana shi fitowa?
“Mu da har muna tunanin rufo muku ƙofa on our way out.”
“Ni ne fa Happy, na san ka farin sani. Mayar da maganar kaina kake son yi?”
Mubina da Hamdi dariya su ka dinga yi musu kawai.
***
Sati biyu ya rage bikin Zee wanda aka sanya wata shida bayan komawar su Abba Habibu Saudiyya. Sajida a lokacin watanta guda da haihuwar Ihsan mai sunan surukarta. Gidan Abba Habibu ya sha gyara amma ba mai yawa ba tunda yanzu babu mai zama.
A zuwan su na farko Abba Habibu ya nunawa Baba Maje rashin jindaɗinsa da ya tayar da maganar raba auren nasu. Aka tambayi Zee ko tana son rabuwar ta ce a’a.
Su Yaya sun nuna musu cewa zumunci yanzu aka fara in sha Allahu. Har gidan Ummi ma sun je. Babu alamun yunwa a tare da ita amma fa ba sai an faɗa ba fuskarta ta nuna bata jindaɗin rayuwar auren. Duk masifarta dole ta sanyawa zuciyarta haƙuri domin kishiyoyinta sun dama ta sun shanye. Uwargidan ma ƴar sara suka ce kafin aure. Ta biyun kuwa ƴar damfara ce ta buga misali. Da su ka shigo hannun Kofur Ɗanliti zance ya sha bamban. To ga Ummi ma ta zo hannu. Jiki magayi!
Da za su koma da Zee da Halifa aka tafi. Abba Habibu ya gayyato Ƴar Ficika da wasu cikin yaransa masu igama su ka koma tare. Nan fa sana’a ta kankama babu kama hannun yaro. Ta ƙarfin cin tuwo su ka canja akalar rayuwarsu daga ƴan daudu abin ƙyama zuwa maza masu sana’ar abinci. Sai ga Ƴar ficika ya sami mata, wata ƴar dattijuwar takari. Mata ta zage ana ta sana’a da ita maimakon yawon unguwa unguwa neman abin yi. Cikin watanni kacal rayuwarsu ta sauya gabaɗaya. Duka kuma albarkacin sadaukarwar da Yaya tayi wadda bata taɓa tunanin wani mahaluƙi zai saka mata a kai ba.
*
Dinner ta ƴan boko, ƴan gayu kuma masu kuɗi Kamal ya shiryawa Zee. Bai yarda ko sulai biyar wani ya saka masa ba. Taj ya ce zai ɗauki nauyin abinci amma yaƙi. Zama ya yi aka yi lissafi ya cake wa Happy Taj kuɗinsu. Ango Sadiq wato Baballe kuma ya sha gargaɗi da jan kunne akan ya riƙe amanar ƙanwarsa. Abin na Kamal dai harda ƴar barazana.
Yaya saka shi tayi a gaba saboda ɓarin kuɗin yayi yawa.
“Kamal don Allah ka saurarawa kanka haka nan. Wallahi domin Allah na baka ƙodar nan. Kana saka ni jin nauyinka da na su Hajiya. Ɗawainiya da kashe kuɗin ya yi yawa.”
“Yaya da ke ki ka haifeni za ki ce kyautatawar da nake muku da ƙannena ta yi yawa?”
Yaya tayi shiru.
“Yaya da kin san yadda ɗan Adam yake ji idan ya hango ƙarshen rayuwarsa kuma babu hanyar gudu da baki ga wauta ta ba. Ga ciwo ga tashin hankalin sanin bani da wata mafita.” Idanunsa su ka yi jawur amma bai bari ƙwalla ta zubo ba “ga kuɗi, ga dangi amma babu mai ceto. Yaya, a wannan lokacin ban dinga tuna komai ba sai ranar da kowa zai juyawa masoyinsa baya saboda tsananin tashin hankali. Duk wanda Allah bai taimaka ba a lokacin to dole ya cire rai da samun kowane irin taimako.” muryarsa ta soma rawa “na hangowa kaina rayuwar barzahu da tashin hankalin da mara rabo zai riski kansa… bani da tabbacin tsallakewa. Komai ya zo gab sai Allah Ya kawo ki. Yaya babu tunanin taki makomar da ta iyalinki ki ka kwanta aka cire taki ƙodar domin na sake shan iskar duniya. Domin iyayena su share hawayensu…” ya miƙe tsaye “ban isa na biya ki ba amma kuma ba zan taɓa gajiya da yi miki hidima ba in sha Allahu. Kin isa, kin cancanta. Don Allah kada ki sake nuna rashin jindaɗin ki idan nayi wani abu.”
Ƙwallarta ta goge tayi masa murmushi “idan da ni na haifeka zan karɓi duk abin da ka kawo min cikin farinciki amma duk da haka zan ce maka ka dinga yi saisa-saisa saboda kaima ka kusa zama baban wasu. Haihuwa ba a yi mata tanadin gobe ko jibi sai ta baka mamaki. Sayen pampas kaɗai ya ishe ka ka gane ba ka da wayo” ta ƙare maganar tana dariya.
“Ki yi min addu’a kawai, Allah Ya ƙara buɗa min. Tanadi kuma in sha Allahu zan kiyaye shawararki.”
“Allah Ya yi maka albarka Kamal banban ɗan Jinjin”
“Abu Khadija za ki ce.” Ya sunkuyar da kai yana susar ƙeya.
Tare su ka yi dariya sai ga Abba Hayatu nan.
“Agolan gidana me ka ke yi a nan ka zo ka saka min mata kuka?”
“Sirrin uwa da ɗa ne Abba.”
“Nima yanzu mu ka gama namu sirrin da Taj babban ɗana.”
Kamal ya ce “Sirikinka dai. Mijin ƙanwata.”
Yaya da Abba Habibu dariya su ka yi. Kamal ya fita ya shiga mota su ka tafi gida da Taj da yake gidajensu babu nisa da juna. Mubina tana gida laulayi ya make ta amma ta gama shiri Hamdi kuma ciki ya tsufa sosai. Haihuwa ko yau ko gobe.
*
Kukan Hamdi na huɗu kenan yau saboda Taj ya ce ba za ta je dinner ba. Da ya shigo kallon juna su ka yi kowa ya ɗauke kai. Yana fitowa daga wanka da gangan ya leƙo falo.
“Taso ki fito min da kaya.”
“Suna kan gado.”
“Turare fa? Wanne zan saka?”
Ta sake kawar da kai “Na fesa a jikin kayan”
“Body spray fa?”
“Akwai akan dressing mirror.” Ta san jan magana ne kawai tunda abubuwa ne da yake yiwa kansa.
Ya koma ya shirya cikin ankon su na shadda shi da su Kamal. A gabanta ya tsaya ya cika mata hanci da ƙamshi mai daɗi.
“Menene ne kuma?” Ta ce da muryar kuka.
“My goodbye kiss.”
Da kumburarrun idanunta ta harare shi “na ajiye a ƙofar gida.”
“Wannan kuma ba ki isa ba. Ki min kawai na tafi.”
“You are looking for my trouble.” Ta tura baki tana jan hanci.
“Yep.”
“Wai me nayi maka ne?”
“Kin kasa kallona saboda kina fushi ki ce nayi kyau.”
Satar kallonsa tayi ta ce “kayi kyau.”
“Ko ke fa. To tashi ki shirya mu tafi.”
Maganar a bazata ta shiga kunnuwanta. Ta tashi da ƙarfinta ta rungumo shi tana dariya.
“Da gaske kake?”
“Idan naƙuda ta taho ki tabbatar kin riƙeta tunda rigima ta sa ba ki son zama a gida.”
Da dariya Hamdi ta ce “ni fa ba bikin ne ya dame ni ba. Ƴan matan da za su ji ka burgesu nake son na hana samun dama. Ka sanni da kishi.”
Taj ya tuntsire da dariya. Ya zauna ya ce mata nan da minti shabiyar idan bata fito ba zai tafi. Da sauri ta dinga komai. Ta fito a minti ashirin da biyu. Taj yana zaune yana waya. Hannunta ya riƙe su ka fita daga gidan tare.
*
Biki yayi biki domin ya sami halartar mutane da dama cikin ƴan uwa da abokan arziƙi. Ƴan uwan Yaya da ƴaƴansu sun zo daga Batsari tare da Inna Luba. Ya’u ya zama na hannun daman Yaya Kubra domin har ta mayar da shi makaranta. Amma da su Anisa harda Hajjo su ma sun zo. Ƴar ficika da matarsa ba a barsu a baya ba. Haka dangin Alh. Hayatu da na matansa na kurkusa duk sun zo.
Ahmad ya taho da Zahra sannan ya ce Salwa lallai sai ta zo saboda shi bai ga amfanin ƙauracewa mutane ba. Idan ana haɗuwa ko yaya yau da gobe za a iya yafe mata.
To ashe Ummi ma da kishiyoyinta harda maigidan Kofar Ɗanliti su ma sun taho. Hamdi ta tako da ƙyar take ɗaga ƙafa taji kamar da mutane a gefenta. Ta juya hagu ta haɗa ido da Salwa gayauna. A ɓangaren dama kuma Ummi yangaura. Kowacce ta lalace ta fita hayyacinta. Su ukun suna yiwa juna kallon kallo su ka tsinkayi muryar Taj daga bakin ƙofar hall ɗin.
“Ke da na ce ki jira ni a mota in fara sama miki wurin zama? Na zo na ɗauke ki?”
Salwa da Ummi su ka bi shi da kallo. Ya fi Taj ɗin da su ka sani cika, kyau da ɗaukar ido. Aure ya karɓe shi kamar yadda ya karɓi matarsa. Ko me su ka ji a ransu ba su furta ba.
“Ka zo ka tayani tafiya dai.”
Taho wa ya yi Hamdi ta saƙale hannu a waist ɗinsa saboda support su ka dinga takawa tare har su ka ɓacewa ganinsu. Sai su ka sake kallon juna, kowacce ta buga tsaki. Za su fara cacar baki sai Ummi ta kula Alh. Usaini yana tahowa. Yadda Salwa ta fige shi har ya fi ta. Wata muguwar dariya ce ta suɓuce mata bata sani ba. Kamar daga sama taji muryar Kofur.
“Ummi ban hana ki dariya irin wannan ba?” A gefensa hagu da dama kishiyoyinta ne.
“Wai, sannu fa.” Salwa ta ce sannan ta rama dariyar da tayi mata.
*
A falon gidan Abba Habibu, shi ne da Alh. Hayatu su ke hira irin tasu ta manya. Hirar yawanci ta iyalansu ce da abubuwan da su ka shafi rayuwar yau da gobe.
Can dai Alh. Hayatu ya ce “ni kuwa Habibu akwai abin da nake sha’awar ci amma na kasa faɗawa iyalina tunda ban saba ba.”
“To ya aka yi ka san kana so tunda baka ci?”
“Ka san jikoki akwai kyauta. A baki aka zo aka bani rannan da aka yi. Si ka tayar min da kwaɗayi amma ban isa na nemi ƙari ba kada na zama abin surutu a gidan.”
Abba Habibu ya miƙe yana dariya “ban yi ritaya ba har yanzu. Ya sunan sa in dafa maka?”
“Wainar fulawa” Alh. Hayatu ya faɗa yana wani basarwa don kada Abba Habibu yayi masa dariya. Bai tsira ba kuwa don sai da ya yi masa dariyar sannan ya shiga kitchen.
Bayan minti talatin Alh. Hayatu ya ɗora babbar rigarsa a saman kujera wai kada ta ɓaci da manja. Ya zauna a kan kafet yana cin wainar fulawa yana jindaɗi sai ga wayar Kamal sun wai wuce asibiti da Hamdi shi da Mubina da Taj. Iyayensu sun biyo bayansu.
Ya kalli plate ɗin ko rabi bai ci ba kamar kada ya tashi don wannan tafi wadda aka yi a gidansa daɗi. Sai da ya ƙara loma guda sannan ya tashi su ka tafi asibitin. Suna shiga Mubina na fito musu da jariri.
Abba Habibu ya ce a miƙawa Alh. Hayatu. Yana karɓa sai cewa ya yi “wainar”
Abba Habibu ya yi saurin cewa “Wai ina wa?”
“Wai ina maigidan nata?” Alh. Ya wayance.
“Gamu nan fa Alhaji.”
Ya juya ashe sun wuce kowa a wurin bai sani ba. Farin kaya mai tonon silili Inna ce ta fara cewa
“Mene ne wannan a gaban rigarka Alhaji?”
“Ina babbar rigarsa za ki ce” in ji Mama.
Hajiya ta ce “Ƙamshin manja nake ji kamar wainar fulawa.”
Alh. Hayatu da Abba Habibu su ka soma kame kame duka wajen ya kaure da dariya.
Basu bar asibitin ba sai da aka fito da Hamdi kowa ya ganta lafiya. Alh. Hayatu ya miƙa mata jaririn da amarya Zee ta ƙanƙame bayan iyaye sun gama saka masa albarka. Ya miƙawa Hamdi bayan ta zauna akan gado.
” Hamdi ga Habib Tajuddeen Hayatu. Allah Ya raya shi bisa sunnar Ma’aiki SAW. Allah Ya sa ya yi koyi da kyawawan halayen mai sunansa.”
“AMIN” kowa ya amsa da farinciki.
Abba Habibu da bai taɓa zaton wannan karamcin ba ya rasa me zai ce sai kawai ya dinga murmushi yana godiya ga Allah da Ya nufe shi da ganin wannan rana.
Alhamdulillah bata gushe daga bakinsa ba har ya kwanta yana tunanin rayuwar duniya mara tabbas. Ace har ya yi ƙimar da za a yi masa takwara?
“Allah na gode Maka. Ya Rabbi Ka ƙara shiriya da albarka ga iyalanmu da mu kan mu. Ka raba mu da bin hanyar taɓewa. Ka dawo da ɓatattun cikin mu hanya madaidaiciya. Amin”
MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE.
