
Rayuwa Da Gibi
MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
Page 1
Wanki take a tsakar gida tana sauraron hirar mahaifiyarta da ƙanwarta Zee. Ba ta saka musu baki saboda tun ainihinta ba mai son hayaniya bace. Sai murmushi kawai idan sun yi abin dariya.
“Wannan wankin naki zai sami shanya kuwa Hamdi?”
Sararin samaniyar da Yaya ta kalla ita da Zee su ka zuba wa ido. Ga dai rana ana gani tana haska ko ina. Amma idan mutum ya miƙar da ganinsa zai yi tozali da baƙin hadarin da yake ta gangami daga nesa. Tunanin taƙaita wankin ta soma yi yadda wanda ta gama za su sami wuri akan ƙofofin ɗakunan gidan su ka ji sallamar wasu mata.
Da farinciki Yaya ta tashi daga kan tabarmar da take zaune ta nufi zaure tana cangala ƙafarta ta hagu wadda shan inna (polio) ya cinye. Da alama baƙin da aka kwana aka wuni ana zancen zuwansu ne su ka ƙaraso.
“Maraba lale da Altine.”
Shewar Yaya da baƙuwar su ka ji daga zauren da taje ta taro su kafin su dawo tsakar gidan hannun da baƙuwar a kafaɗarta.
“Oh ni jikar mutum huɗu. Ashe rai kan ga rai Jinjin? Ya bayan rabuwa?” Matar ta jero mata tambayoyi su na daga tsaye.
“Sai alkhairi. Rayuwar nan sai godiyar Allah.” Su ka sake rungumar juna su na dariya.
Ƴan matan da baƙuwar tasu mai suna Altine ta zo dasu da kuma Hamdi da Zee sai su ka tsaya kallon abin al’ajabi. Labaran da su ke ji game da juna ashe gaskiya ne don ga zahiri sun gani. Iyayen nasu sun yi zumunci sosai kafin a haifesu lokacin suna zaman Agege a Lagos. Abubuwa da dama sun faru waɗanda su ka yi sanadiyar dawowar su Jinjin garin haihuwarsu Kano. Ƙarancin hanyoyin sadarwa da faɗi tashin yau da gobe ya dakusar da wannan zumunta ta makwabtakar gidan haya ɗaya. Shekara bakwai kenan da dawowar su Altine Kano su ma amma basu taɓa haɗuwa ba sai da Allah Ya haɗa mazansu da wani da ya san duk su biyun. A wurinsa su ka sami labari harma da lambobin wayar juna.
Altine kakkaurar mata ce mai fara’a kamar gonar auduga. Mijinta Maje mahauci ne yana sana’arsa ta fawa. Da yake kakanninsu ɗaya duk su na da billensu na gadon sana’ar a kuncinsu. Akwai ta da kazar kazar don in tana abu sai ka rantse wannan jikin ba nata bane. Da wannan yanayin nata ta ja Jinjin a jiki duk da farkon zuwanta saboda yanayin mijinta da lalurarta bata sakewa da kowa. A gidan nasu na iyali goma sha biyu ƴan ka zo na zo aka taso ta a gaba da tsokana. Don ma maigidan nata ba ƙyalle bane. Bakinsa kaɗai ya ishe su ƙwatar kai. Idan ya fita ne dai ko banɗaki ta fito zagawa an dinga dariyar tafiyarta kenan. Sai da Altine ta gama lura da ita ta gane tsoron ƴan gidan da su ke duk hausawa take yi. Sai ta zame mata baki harma da hannuwa. Don idan abin bawa hammata iska ya kama dukan tsiya take yiwa mace la’ada waje. Ɗan Altine ɗaya lokacin ita kuma Jinjin da ciki su ka rabu.
“Ina Baballe kuwa?” Cewar Yaya cikin yanayi na kewa.
Da jindaɗi Altine wadda ƴaƴanta su ke kira Iyaa (kamar yadda Yarbawa su ke jan sunan) ta bata amsa.
“Ya tafi bautar ƙasa Binuwe (Benue)”
“Allah Sarki. Shekara kwana. Yaron da na tafi na bari yana tatata”
Dariya su ka yi farinciki da jindaɗinsu ba zai kwatantu ba. Duk wannan abin da su ke yi Hamdi da babbar cikin ƴan matan Iyaa kallon gane juna su ke yi. Ganewa mai cike da tsoro da fargaba a ɓangaren kowacce bisa dalilai daban daban. Kamar iyayen sun sani kuwa su ka zaɓi wannan lokacin wurin gabatarwa juna ƴaƴan nasu.
“Kina nufin da cikin Hamdi ku ka taho?”
“A’a, yayarsu dai Sajida. Tsiranta da Hamdi ma ya kai shekara biyar. Bata nan ne. Ta tafi Abuja gidan ƴar yayata da ta haihu.”
Iyaa ta murmusa “Allah Sarki” ta nuna babbar ƴar “Sajidan ce sakuwar Ummi kenan, don baku jima da tafiya ba na haifeta.”
Yayinda Yaya take da ƴaƴa huɗu, Sajida, Hamdiyya, Zinatu (Zee) da Halifa, na Altine uku ne. Baballe, Ummi da Siyama.
Sai da su ka nutsu da gaishe gaishen Yaya ta aiki Zee.
“Maza jeki gidan Lami ki ce ta baki lemukan da na bata ajiya.” Ta yiwa Iyaa bayanin sace musu transformer da aka yi kusan wata uku babu wuta sannan ta fuskanci Hamdi “ke kuma ki je wajen babanku ki faɗa masa Altinen Maje ta iso.”
Iyaa ta sanar da ita ai babansu Ummi na sauke su a ƙofar gidan ya yi waya da maigidan nata.
“Ina jin ya kwatanta masa wurin sana’ar tasa don ya ce can zai je sai su taho tare.”
Cigaba da hirarsu su ka yi wanda hakan ya bawa Ummi damar yiwa Hamdi inkiya da su tashi tana son magana da ita. Ita kuwa sai ta ɗauke kai kamar bata gani ba. Hakan ya tunzura Ummi matuƙa sai kawai ta miƙe tsaye ta ce tana son shiga banɗaki. Hamdi na jin haka ta san kwanan zancen. Cikin ɗakinsu ta gayyato ta ba don ta so ba. Duk da gidansu mai tsakar gida ne amma kowanne ɗaki da banɗakinsa a ciki. Wannan tsarin babansu ne da ya ce baya so ace komai dare, ruwa ko iska sai an fito tsakar gida idan za a zaga.
- Rayuwa Da Gibi – Chapter One 14 Words
- Rayuwa Da Gibi – Chapter Two 1,978 Words
- Rayuwa Da Gibi – Chapter Three 1,970 Words
- Rayuwa Da Gibi – Chapter Four 4,735 Words
- Rayuwa Da Gibi – Chapter Five 2,857 Words
- Rayuwa Da Gibi – Chapter Six 2,506 Words
- Rayuwa Da Gibi – Chapter Seven 4,415 Words
- Rayuwa Da Gibi – Chapter Eight 3,627 Words
- Rayuwa Da Gibi – Chapter Nine 3,669 Words
- Rayuwa Da Gibi – Chapter Ten 3,234 Words
- Rayuwa Da Gibi – Chapter Eleven 2,405 Words
- Rayuwa Da Gibi – Chapter Twelve 2,963 Words
- Rayuwa Da Gibi – Chapter Thirteen 4,519 Words
- Rayuwa Da Gibi – Chapter Fourteen 4,431 Words
- Rayuwa Da Gibi – Chapter Fifteen 4,960 Words
- Rayuwa Da Gibi – Chapter Sixteen 5,355 Words
- Rayuwa Da Gibi – Chapter Seventeen 4,442 Words
- Rayuwa Da Gibi – Chapter Eighteen 4,045 Words
- Rayuwa Da Gibi – Chapter Nineteen 6,651 Words
- Rayuwa Da Gibi – Chapter Twenty 3,837 Words
- Rayuwa Da Gibi – Chapter Twenty-one 5,012 Words
- Rayuwa Da Gibi – Chapter Twenty-two 4,966 Words
- Rayuwa Da Gibi – Chapter Twenty-three 6,753 Words
- Rayuwa Da Gibi – Chapter Twenty-four 4,699 Words
- Rayuwa Da Gibi – Chapter Twenty-five 7,323 Words
- Rayuwa Da Gibi – Chapter Twenty-six 5,735 Words
- Rayuwa Da Gibi – Chapter Twenty-seven 6,329 Words
- Rayuwa Da Gibi – Chapter Twenty-eight 5,923 Words
- Rayuwa Da Gibi – Chapter Twenty-nine 5,599 Words
- Rayuwa Da Gibi – Chapter Thirty 3,514 Words
- Rayuwa Da Gibi – Chapter Thirty-one 3,121 Words
- Rayuwa Da Gibi – Chapter Thirty-two 8,612 Words
- Rayuwa Da Gibi – Chapter Thirty-three 4,312 Words
- Rayuwa Da Gibi – Chapter Thirty-four 3,834 Words
- Rayuwa Da Gibi – Chapter Thirty-five 3,302 Words
- Rayuwa Da Gibi – Chapter Thirty-six 3,566 Words
- Rayuwa Da Gibi – Chapter Thirty-seven 3,902 Words
- Rayuwa Da Gibi – Chapter Thirty-eight 6,530 Words
- Rayuwa Da Gibi – Chapter Thirty-nine 5,211 Words
- Rayuwa Da Gibi – Chapter Forty 5,857 Words
- Rayuwa Da Gibi – Chapter Forty-one 10,676 Words
-
Zafin Kai Chapter 2: 2 Samirah ta rasu ne bayan da azabar tayi masu yawa ta girmi tinani da dauriyarsu harma da duk jarumtar da suke tinanin sunada ita, Cikin tsakiyar dare guraren…
-
Zafin Kai Chapter 1: BismillahirRahmanirRaheem Allah yabamu ikon gamawa lafiya 1 Gyara tsayuwarta tayi ahankali tana sauke idanuwanta daga kallon dattijuwa kuma tsohuwar matar dake…
-
Nihaad Chapter 3: ~ 3 8months earlier… Zaune yake saman farar kujera dake kusa da dakin mai gadi, ya fi awa daya xaune wajen, lkci lkci yake goge zufan fuskarsa da…
-
Nihaad Chapter 2: ~~ 2 Dumbin gaisuwa da fatan alkhairi xuwa ga iyayen gidan Khaleesat’s Palace, my die hard fans🥰😍 Su Hajjaju Chamo me gwala-gwalai duk da jarin ya…
-
Nihaad Chapter 1: ~ 1 All thanks to Allah SWT for giving me the ability and privilege to present to you this book. My mother Hajiya Hajarah Allah ya karo farin ciki da kwanciyar…
-
(Download) NiDa Ya Ahmad – Complete by AsmaLuv: ABUJA A hankali manya manya motoci ke tafiya saman titi jiniya ce ta kardaye saman layin da xai sadaki da gwarinfa acikin garin abuja daga ganin motocin xaka…
