Muwaddat – Chapter Thirty-three
by Aysha A Bagudo…tun da muwaddat taji sautin muryarsa yana furta kalmar “abi ummi ku daina wahalar da kanku ciki na ne.. … zuciyarta ta tsaya cak ta daina aiki na wunci gadi….
kafin daga baya zuciyarta ta soma bugawa da karfin gaske,maganarsa ba’a iya kunnenta kad’ai suka samu nasarar tsayawa ba har ma da gangar jikinta da koina take jin saukar furucinsa tamkar saukar aradu ….
yi tayi kmr ta kwasa da gudu ta bar parlour’n domin tsira daga wannan taskon tashin hankalin data tsinci kanta mai tattare da abun kunya , amman babu halin aikata hakan sakamakon gabobi Jikinta da take jin tamkar ba’a gangar Jikinta suke ba , ahankali jikinta ya sake d’aukar rawa kamar mazari, hawayen idanunta suka tsananta gangarowa bisa kuncinta , da kyar ta juyo inda ummi da abi wad’an da sukayi mutuwar zaune agurin suka dawo tamkar matattu suna duban bunayya ,mamaki ne ko kuwa dimuwa ce tasa me su alokacin, ita dai bata sani ba, dan tashin hankalin da take ciki ya ninka nasu…..
Cikin tsananin matsanancin tashin ahankali bakinta ya cigaba da maimaita kalmar inna lillahi wa inna ilaihi rajiun jikinta na wani irin kyarma .
wannan kalmar da muwaddat ke maimaitawa a fili itace ta dawo da ummi da abi cikin hankalinsu suka shiga kallon ita kanta muwaddat din, kallo kuma irin na tsantsar mamaki da al’ajabi da tashin hankalin.
“da gaske ne abinda kunnuwansu suka ji ya fito daga bakin tilo d’ansu ko kuwa karya ne ?
ummi ta tsaida kallonta akan bunayya sosai tana son ya karyata mata abinda taji ya fito daga cikin bakinsa cewar karyar ne ba gaskiya bane….
amman sai taga yayi shiru yaki cewa komai illa wayarsa daya rike gam kmr za’a kwace daga hannunsa , yayinda a bad’ini kuwa ba za iya misalta kalar tashin hankali da shi kansa yake ciki ba…
da kyar ummi ta had’iye abinda taji ya tsaya mata a makoshi ta kira sunansa cikin wata irin murya wacce bai ta’ba sanin umminsa dashi ba “bunayya ……
cikin jikin muwaddat kai kayi shi ko kuwa kunnawanmu ne suka jiyo mana sa’banin haka?
A sukwane ya d’ago kansa ahankali zuciyarsa na wani irin bugawa da karfin gaske ya tsurawa umminsa da hawaye suka gagara tsayawa akwarnin idanunta ido yana kallonta , kafin daga baya ya d’an lumshe tsumammun idanunsa ya bud’esu fesss akanta ya janyo numfashi da kyar ya fitar hankali, sannan yace “eh ummi cikina ne kuma ina son abuna plz ku bar min shi……
” inna lillahi wa inna ilaihi rajiun shi yayi nasarar katsewa bunayya hanzarinsa.
“cikinka ne kuma kana son abunka ,abar maka shi bunayya?
Ummi ta furta haka tana kuka ,ya d’aga mata kai ala’mun eh, ai ko ta sake rushewa da wani sabon kuka…..
kuka ummi take sosai tamkar ranta zai fita tana dafe da kirjinta da take jin tamkar zuciyarta zatayo waje.
“wace irin bakar rana ce yau gareni ?
“Meke Shirin faruwa da rayuwata data ahlina ?
“Ya Allah kasa zantuttukan bunayya su kasance cikin mafarki nake jiyo su ?
“Allah Allah kasa karya ne ,karka nuna wannan bakar ranar acikin rayuwata “me zancewa duniya …….. ?
“Me duniya zata fad’a akaina ?
“Idan wannan abu ya kasance gaskiya ya ..ya ..ta kasa k’arasa zancen zucin da take sai ta kama haki tana fidda numfashi sama sama ……
shi kuwa abi gabad’aya kasa magana yayi yana cigaba da kallon bunayya cike da matsanancin mamakin karfin hali irin nasa “wato dai sune suke masa kallon yaro k’arami wanda bai isa aure ba,a she shi tuni ya zarta inda suka ajiye matsayinsa?
“lallai yaran zamanin yanzu sai dai abarsu kawai ……
har lokacin abi ya kasa cire mamakin wannan a’lamarin acikin zuciyarsa ,wai muhammed auwal d’ansa d’an shekara 22 ne yayi muwaddat ciki, to a ina akayi wannan cikin……. ?
kwalkwaluwarsa tashiga caji da tunanin inda akayi ciki suna cikin gidan batare da sun sani ba.
Bunayya ya mike tsaye ahankali ya isa gaban ummi ya durkusa bisa gwiwowinsa yace “dan Allah ummi karkice zaki cire cikin nan wallahil azim ciki na ne ajikin muwaddat, kuma ina son kayana …..
tassss !tasssss!! tassss!!! Kake jin ta d’auke shi da wasu gigitattun maruka har guda uku ajere tana haki “ka min Shiru …. d’an iskan yaro mara d’a’a idan ka sake furta wannan kalmar agabana sai na tsi….
” kul…… ….abi yayi saurin katseta ta hanyar fad’ar haka , “baki ta’ba masa mummunar furuci ba a tsawon rayuwarsa kin dai ga abinda ya faru yanzu …..
“baki ta’ba furta wata kalmar banza garesa ba kinga aika aikan da ya aikatamana , hakuri zamu taru muyi gabad’aya tunda haka kaddarar tazo mana, amman batu na tsinewa ko zagi duk bai taso ba.
“Irin abinda nake hangowa kennan agareki mukarama kika mutsutsuke idanunki kika biyewa son zuciyarki yanzu wa gari ya waya ?
“Tabbass idan bunayya na da laifi namu laifin ya zarta nasa “
“Yaran nan suna son junansu sosai fiyye da tunaninki ,amman kika ce Sam ba haka muwaddat bata son shi yanzu ai Kinga karshen kiyayya tun da ga sakamakon nan ta haifar ,tun tuni na zubda makaman yakina akan lamarin sabida ba’a jayayya akan irin wannan lamari ‘a’a bunayya yaro ne bazan bashi diyata ba this and that ya k’arasa maganar yana furzar da iska tare da buga abun kujera yana zabgawa bunayya wani irin mugun kallo …..
Bunayya wanda idanunsa suka rikid’e sukayi ja tsabar tashin hankali da yake ciki ya mike ya nufi gurin abi ,”abi kayi hakuri dan Allah karka karawa ummina damuwa akan wanda take ciki “yi min shiru wa ya jawo ?
“Ai suk wanda ya sai rariya yasan zatayi zuba “Kai Kuma da yake ..sai yayi kawai yana sake furzar da iska mai zafi …
“Kuyi hakuri amnan tun tasowata nake son muwaddat Kuma da aure ,na cire kawaici da kunyarku amatsayinku na iyayena na bayyana muku abinda ke raina da burina amman kuka ki ,ni dai dan girman Allah ku bar min ci…..
Wani sabon mari yaji daga bayansa wanda yasa take ya had’iye abinda zai furta “shine akace ka mata ciki dan iska ?
“Nasani muwaddat ba zata ta’ba aikata hakan ba wallahi sai dai idan tursasa kayi .
“kayi Mata dole dan kawai kaga karshena ko bunayya ?
” Nasan kayi haka ne dan ka kuntata min amman sai numfashinta ya d’auke sakamakon hakin d’aya rufeta tayi kasa luuuuuuu zata Fad’i, bunayya yayi saurin tarota jikinsa Yana jijigata ,take hankalin abi da muwaddat ya sake tashi suka yo kanta atare suna Kiran sunanta muwaddat na kuka ta durkusa kusa da ummi ta kamo hannuta hawaye na bin kuncinta …
“ummi..!ummin….!!”ya rabbi dan girman Allah ummi karki mutu ki barmu a duniyar Nan ,idan wani Abu ya sameki a dalilin abinda na aikata bazan ta’ba ya fewa kaina ……..
Abi yasoma k’ok’arin amsarta daga hannunsa amman furrrrrr bunayya yaki sai Kiran sunanta yake cikin tsananin tashin hankalin .
Cike da matsanancin tashin hankali abi yace “wa. water ….. wani irin zabura muwaddat tayi ta nufi hanyar inda firdge din abi yake, ta bud’e ta d’auko ruwa mai tsanyi tun kafin ta k’araso ta soma k’ok’arin bud’e robar ruwan tana gama k’arasowa ta shiga tsiyayawa ummi tana wani irin kuka ..
gabad’aya sun gigice sun rud’e sun fita haiyacinsu kallo d’aya zakayi musu kasan cewa suna cikin tsananin damuwa , duniya da abinda ke cikinta sun taro sun cakud’e musu guri d’aya , barin muwaddat da ke jin rayuwata ita da babu duk d’aya ,addua kawai take a halin da take ciki Allah ya d’auki ranta a lokacin ta huta ,da kyar numfashin ummi ya dawo gangar jikinta.
tayi atishawa tare da sauke naunayen ajiyar zuciya Jikinta na wani irin rawa take suka shiga rigerigen yi mata sannu suna sauke numfashi “sorry ummina dan Allah karki tsine min bisa kuskurena ……
ummi ta bud’e idanuwanta da kyar hawaye na tsiyaya daga kwarnin idunta tashiga kallonsu d’aya bayan d’aya tana girgiza Kai kana ta runtse idanunta gam tana jin yadda dukkanin su ke jero mata sannu amman banda bakinciki babu abinda ke dawainiya daita da zuciyarta “me zatayi da wani sunnunsu “an rigada an cuceta an cuci rayuwar diyarta.. bunayya take kallo ta kawar da kanta tana hawaye su bunayya da muwaddat suma kuka suke har wannan lokacin .
Ahanksli bakinta ya shiga motsi al’amun tana son yin magana tana salati ..
hakan ya sake gigitasu suka sake matsowa gareta , abi da bunayya suka yi saurin kasa kunnuwansu daidai bakinta dan jin abinda zata farta …….sai Kuma tayi shiru .
Yayinda da komai nata yayi sanyi ,lokacin ne muwaddat ta tsilla ihu a hankali bunayya ya sake kafe ummi da idanunwansa ,yaga idanun ummi sun sake rufewa haka nan bata motsi bare numfashi ,cikin hanzari bunayya ya tashi da sauri Yana duban ummi dake Kwance ,can Kuma ya koma Jikinta ya rungumeta yayinda Kansa ke kan kirjinta abi da muwaddat tuni kuka ya gama cin karfinta …..
Cikin lokacin kankani bunayya ya burkice Yana shafa fuskar ummi yana magana “ummina duniyata hakika bani da tamkarki ,bani da mai Sona kamarki karki min haka ummi karki had’iye zuciya ki tafi ki barni ….ki taimaki tilon d’anki bashi da kowa daga Allah sai ke ,karki min haka ..
“Abi kace ta tashi wallahi na hakura da cikin …,a ciresa matukar ummina zata samu kwanciyar hankali ,wallahi a zim na hakura ,”ya sake kamkameta “ummi ..!ummi !!!wallahi na hakura ki tashi “Ina son ki ummina fiyye da abi ,da muwaddat duk duniya kace mutun ta farko da nake kauna …….
*Manage plz idona kaina, Kai koina ma ciwo yake min
Mmn sudais
MUWADDAT
~NA~
*AYSHA A BAGUDO*
~DEDICATED TO~
_AUNTY SALAMATU AYYUBA_
_(UMMIN KADUNA )_
warning!!!
don’t read this novel if you know you are not married… ❌❌❌coz this book contains only for mature people , if you read it, is for your own risk ……
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim