Muwaddat – Chapter Thirty-seven
by Aysha A Bagudo…Dif numfashi da zuciyoyin rayuka had’u suka tsaya na wuncin gadi ,sakamakon jin saukar maganar dady da suka ji tamkar saukar aradu acikin kunnuwansu .
gabad’aya a firgice sannan a gigice suke bin junansu da kallo mai cike da tsantsar mamaki, kana suka sake maida idanunsu akan dady dake tsaye a gabansu fuskarshi babu yabo babu fallasa .
kallonsa suka cigaba da yi domin neman k’arin bayani yadda hakan ta kasance ,barin ummi wacce gabad’aya ilahirin jikinta ya d’auki rawa ….
Kusan ta fi kowa farinciki da murnar wannan a’lamarin …..
Sautin muryar dady ne ya sake karad’e parlour’n
” Tabbas gaskiya ne abinda kunnuwanku suka jiyo muku daga bakina ,a gidan nan Kuma acikin wannan parlour’n nawa na d’aura auren muwaddah da Muhammud auwal ,bisa yardata da yarda wakilin auwal wato umar kanin mahaifinsa da Kuma shi kansa mahaifin auwal din wanda ya kasance amini gareni …….
“a lokacin da aka d’aura auren abokina alhaji safyan na nan ,sai baba mai gadina gashi can da ransa bai mutu ba akirasa, sai umar da shi kansa alhji ishaq din, dan haka yara ba zina suka aikata ba sunan suka aikata …
“Kamar umar yasan abinda zai faru gaba kenan , yazo min da zance ,alokacin naso naki amincewa bisa wani uziri nawa a she umar ya hango abinda mu muka kasa hangowa ……
“Dan haka sai mu
godewa Allah, da Allah yasa da au…….
“Babu wani aure anan dady……. yaya akram ya furta hakan kansa a sunkuye zuciyarsa na farfasa had’e da bugawa …..
“A zahirin gaskiya dady kuskure ne irin wannan auren , yanzu da ba dan ina nan ba, da an tafi akan kuskure wanda mafi yawa daga cikin mutane suke aikata shi da siga aure ,alhalin ya haramta ….
“yanzu misali wakilin auwal ne yazo tambayar auren muwaddah a gurin waliyin muwaddat, suka taru suka amince, har suka had’a aure hakan ya hallata , Tabbas wannan tabbataccen aure ne da muslinci ya yarda dashi ,amman irin aurensu auwal da muwaddat sam bai hallasta ba, kuskure ne mai girma a muslince , domin bazasu kusanci junansu ba har sai sun san cewar su din ma’aurata ne ,saboda an d’aura auren batare da sanin su ba ,saboda yakamata ne kafin su fara saduwa da junansu su kasance sun san cewar su din ma’aurata ne ,idan har basu San cewar su din ma’aurata bane niyyar su ,niyya zina ce babu aure.
Numfashi da ajiyar zuciya ya sauke alokaci d’aya ,kana ya cigaba da cewa “tabbas wannan zina suka aikata kuma laifin yana komawa ne kan waliyansu bisa kuskuren su na rashin sheida musu cewar su din ma’aurata ne ………
Tun da yaya akram ya soma zayyano magana daki daki babu wanda ya sake bud’e baki yace dashi “uffan “
gabad’aya parlour’n da mutanen dake zaune acikin parlour’n suka sake d’aukar shiru na wani lokaci …
gabad’aya cikin ahlin babu wanda zuciyarsa bata buga ba tsabar tashin hankali da firgicin bayanin yaya akram, sannan sai alokacin hankalin dady abi har ma da sauran mutane dake parlour k’ara tashi dukkaninsu tsuma suke , tabbas abinda akram ya zayyene a halin yanzu tabbass haka yake a cikin addini , to yanzu me ye abun yi ?
“Meye mafuta acikin wanna lamarin ?
tambayar da dady ya soma aikawa ‘kwal’kwaluwarsa kennan gumi na keto masa …
Alokacin da umar yazo masa da zance har sanda suka yi komai suka gama atsakaninsu, bai yi tunanin kuskuren haka ba ,Kuma umar yaso kwarai a sanarmawa yaran shine mutun na farko daya yaki ba da goyon bayan aikata hakan, ya hana sheidawa yaran bisa wani tsautsauran ra’ayinsa, a tunaninsa ai baza su ta’ba kusantar junansu ba har sai lokacin da suka kammala karatunsu, sannan a sheida musu cewar su din ma’aurata ne ” a she babban kuskure suka tafka arayuwarsu without knowing….
“Wannan shine ga koshi ga kwana yunwa “
“Tun da yaya akram ya dasa aya ya kasa d’ago kyawawan idanunsa dake cike da ruwan hawaye ,zuciyarsa ce ke wani irin beting da sauri sauri, ahankali ya Kai hannunsa daidai saitin zuciyarsa dake bugawa da karfin gaske ,yana janyo numfashi da kyar yana fitarwa domin dai yasan iyayensa sunyi kuskure arayuwarsu , kuskure kuma wanda har abada bazasu daina dasun sani ba ….
Ba za ma su san, sun tafka babban kuskure arayuwarsu ba ,sai lokacin da nashi sirrin ya fito fili …
“Sai dai kafin zuwan lokacin zai so Allah ya d’auki rayuwarsar ya huta da ganin tashin hankali da zasu riski kansu ciki , don idan akwai abinda ya tsana a halin yanzu bai wuce iyayensa su san ya aikata zina arayuwarsa har ma yana da ya’ya a wata uwa duniya ..”
“yafi jin tausayinsu akansa, baya son tashin hankalinsu ,bayan son ganinsu cikin damuwa …
“su amince masa sun yarda dashi ,sun bashi dukkanin yarda da amanarsu, shi kuwa me zai ce musu idan hakan ta kasance ?
“Ya Allah ka d’auki rayuwata kafin zuwan wannan ranar,” Allah Allah ka d’auki rayuwata …..”
Haka ya dinga maimaita kalmar acikin zuciyarsa can kuma tari ya tsarke shi saboda kukan dake yunkuro fito masa ….
A daidai wannan lokaci sai ga uncle umar shi da bunayya, cikin hanzari bunayya ke bin bayan uncle umar, sai dai kallo d’aya zaka masa ka fahimci cewar a tsorace yake, bai ta’ba tsintar kanshi cikin jin tsoro da shiga tashin hankali irin na ranar ba, domin bai san abinda zuwan nasu zai haifar ba, rugujewar zumunci ko sa’banin haka “
Koda suka shiga parlour’n suka iske duk mutanen dake zaune a parlour’n sunyi jugun jugun, masu tagumi sunyi ,masu zubar da hawaye nayi ,haka ma muwaddah kuka take so tana d’aura dukkanin laifi bisa kanta ….
Yanayin fuskokinsu yasa jikin uncle umar yin sanyi ,ya k’arasa ga abi ya mika masa hannun kana ya Isa ga alhaj Mahmud wanda kansa yayi mugun d’aurewa ,da kyar dady ya mika masa hannu suka gaisa kana ya samu guri ya zauna kusa da dan’uwansa yana tambayarsa batare da ‘bata lokaci ba abi ya shiga zayyene masa komai …
Zaro idanuwa bunayya yayi waje, yana duban abi da gaske “muwaddat matarsa ce ?
“Kenan ba zina suka aikata ba ?
“Cikin jikinta ba d’an zina bane ?
“Kai Kai wannan wace irin rana ce garesa ?
So yayi ya isa ga masoyiyarsa ya rungumo jikinsa ya rarrasheta akan kukan da take , sai dai yana jin tsoro aikata hakan ,ba zai iya sake d’aukar fushin umminsa ba ,ta azabtu matuka da abinda yayi mata ,shi kansa yana tausaya mata daga ita har muwaddat din…
Dammmmmm kmr saukar aradu yaji zuciyarsa tayi wani irin mahaukaci buguwa da karfin gaske ,har sai daya dafe daidai saitin zuciyarsa , take bugun zuciyarsa ya tsaya sakamakon jin dagon sharhin da abi ke wa uncle umar ,kusan second biyu numfashinsa ya dawo gangar jikinsa ,zuciyarsa tashiga bugawa da sauri ,nan da nan gumi ya shiga keto masa a dukkanin ilahirin jikinsa .
“ko ina na jikin shi kad’uwa yake kamar mazari “dan Allah abi karka ce haka, ina matukar bukatar muwaddah arayuwata “Kai ne fa kace min nan gaba zanji dadi har ma nayi farinciki da abinda zai faru , sai yanzu na fahimci manufar maganarka ,dan Allah ,dan girman Allah abi idan wani laifi nayi yasa zaka kawo wannan dagon sharhin ,ka yiwa Allah kayi hakuri, karka haramta mana aurenmu daya inganta , sambatun yake har sanda ya k’araso gurin da muwaddat ke zaune sunkuye da kanta tana zubar da ruwan hawaye , while zuciyarta na bugawa.
“abi ni dai koma meye ina sonta haka, idan da aure ko babu ina sonta, kuma zan rayu daita muddin rai, cikin sa’a ya cafki tafin hannunta cikin nasa yana massaging dinsu hankalinsa a matukar tashe ..
wani k’ara ta saki da karfi ta fixge hannunta cikin nasa ,wani irin duba yayi mata yana jin tamkar ya rufeta da dukan abinda tayi ..
muryarsa a harzuke yace ” ke malama ki fito ki fad’a musu kema kina Sona mana , kamar yadda nake sonki, kuma zamu sake sabon aure da zarar kin … kin ..
saurin katse harshensa yayi saboda ganin irin kallon da ummi ke jifansa dashi ….
Ita kuwa muwaddah hawaye ne ya gangaro daga idanunta yayinda bakinta ya kasa furta komai sai kallonsa data cigaba da yi ..
jikinta a sanyaye ta yunkura zata tashi da niyyar barin gurin dan bata jin zata iya cigaba da zama agurin ..
Saurin riko laulausar tafin hannunta yayi sannan yace “where the hell are you going?
Bai jira mai zata ce ba ya maida ita mazaunin da take k’ok’arin tashi “you are not going anywhere sai kin fad’a musu ni dake duk muna son juna kuma… .
wata uwar razananniyar tsawa abi ya buga masa had’e da furta “live her alone ,ko kana hauka ne ?
Bunayya ya marairaice fuska yana girgizawa abi kai “maza tashi ka koma can “plz abi karka min haka ……
Allah sarki ita kam ummi zuba masa ido tayi kawai ta kasa ce masa komai , tana jin wani irin zallar ‘bacin rai na ratsata ,gefe d’aya Kuma hawaye na bin kuncinta ,ji take a duniya bunayya ya gama tozarta ta ,ya gama wulakantata ,ya bada damar da duniya zatayi Allah wadai daita.
“shin ita din uwa ce kuwa ,ko kuwa iyaye mata ta rako duniya ?
“Shin ta cancaci ta zama cikakkiyar uwa kuwa acikin alumma?
“Wace irin tarbiyya ta bawa d’anta?
” ta sani bai taso a gabanta ba, amman dukkanin rayuwarsa tana hannun Allah da ita, da Allah ya damkawa lamuransa ,ko da yake bai kamata ta ga laifinsa ba ,dukkanin laifi yana kanta da mahaifinsa ne …..
Uncle umar dake zaune a gefen abi ya kallesu daya bayan d’aya yaga duk sun shiga rud’anin da tashin hankali , ya d’an yi murmushi wanda ya bayyana zatin fuskarsa kana yace “kamar yadda akram yace “zina suka aikata ,haka din ne zina ce sai dai ta wani bangaren ba zina suka aikata ba bisa tawa hujjar da zan zayyano a yanzu …..
Bari nayi muku bayani dalla dalla , wato ba kowace aya bane ake samun ayar datayi magana akan irin wannan auren ,ita aya tana zuwa tayi magana a dunkule kun ga ne ?
” Kamar yanzu misali duk cikin alqur’an babu inda Allah yace wannan auren ya haramta , hadith’s annabi s.a.w ne da akin annabi suka zo suka bayyana hakan ,akwai abubuwan da suke zuwa a dungule ba kowani abune suke zuwa a rarrabe ba …
Ahankali uncle umar ya dube bunayya da yayi tsura masa ido yana kallonsa a firgice yace “zo nan babana ka zauna a kusa dani …
Ba dan yaso tashi daga kusa da muwaddat ba, ya mike da kyar ya k’araso kujerar da uncle umar yake, ya zauna jikinsa na tsuma zuciyarsa na bugawa da karfin gaske, hannu uncle umar ya Kai ya kamo hannun bunayya…..
“Muhammud auwal ka tuna wata rana bayan dawowarka kasar nan da wata biyu ,alokacin kana tare da muwaddat na kiraka a waya muna waya da Kai har ka had’ani daita ,har kake min wasa kana son muwaddat amman iyayenka sunki su amince ,kullun suna maka kallon yaro da sauransu , “alokacin ko zaka iya tuna abinda na fad’a maka ?
Bunayya yayi shiru yashiga tention din tunani ,kusan minti goma yana tunanin maganar da uncle umar ya fad’a masa a lokacin amman bai tuno abinda uncle umar ya fad’a masa ba ….
“Ka kasa tunawa ko ?
Bunayya ya girgiza masa kai yana mai zuba masa tsumammun idanunsa da suka burkice suka canza kala zuwa ja…..
Uncle umar ya sake girgiza kansa yana murmushi ……
“To ba wani Abu na fad’a maka ba ,a wannan lokacin, sai tabbatar maka da auren muwaddat ,domin alokaci ,ce maka nayi” bunayya karka damu da maganar umminka da abi muwaddah matarka ce halak malak kayi komai daita,matarka ce ,nasan alokacin ka d’auki maganar da wasa nake maka, Wanda ni har ga Allah da gaske nake saboda sanin abinda zai je yazo ….
“Nasan kana son muwaddat sosai fiyye da tunanin kowa ,tun daga lokacin da nayi k’ok’arin rabaku ,sosai na fahimci damuwar da kashiga a karancin shekarunka .
“Ni Kuma a niyyata nayi k’ok’arin rabaku ne saboda tseratardaku daga aikata zina ,domin bisa abinda naga kuna aikata a wannan lokaci idan aka barku guri d’aya komai zai iya faruwa da yanzu ba wannan labarin akeyi ba …
Sannan ni da kaina na taso daga London nazo nema maka auren muwaddat, duba dana ga ka gama karatunka har kana dokin zuwa gareta ..
Kasani duk abinda kuke aikatawa Ina sane ,koda bana ganin abinda take turo maka dashi ,to Kai Ina ganin abinda kake yi a d’akinka ta hanyar CCTV camera yadda kake jadda mata soyayyarka da furuncinka gareta ,shiyasa a matsayina na kanin mahaifinka na d’auki alhakin wannan bangaren daya shafeni .
“dan a neman aure shi namiji bashi da wakili domin namji idan zai yi aure shine alwakilin kansa ,namiji zai iya zuwa ya nemawa kansa aure shi kad’ai ,amman maimakon yaje din zai iya tura waninsa babansa ko wani dan’uwansa ,wannan shi ake Kira da wakili ,ita Kuma mace bata iya zamewa kanta alwaliyya dole ita tana da waliyyi ,mace duk runtsi bata iya bada kanta dole ne wani nmj ne zai bada ita , yanzu muwaddah duk duniya bata da alwaliyyi da wuce mahaifinta, Kuma daman alwaliyya manya agurin mace guda biyu ne d’a da uba, da’ace mace bata da uba,amnan tana da d’a , tana da yaya uwa daya uba daya ,tana da kani uwa daya uba daya ,to babu wanda ya camcanta ya zama alwaliyyinta kmar d’anta haka addini ya tsara saboda d’a yafi sonta d’anta bazai kaita inda zata cutu ba ,haka zalika uba bazai kai yarsa inda zata cutu ba ….
“Sai wakilinka wato ni kenan naje na samu alwaliy na muwaddat na tambayar masa aurenta agurinsa, saboda idan ka d’auki d’anka, misali ka bawa wani d’aunwaka amatsayin ya rike maka , to tamkar ka damka jagoranci yaron ne gabad’aya a hannunsa, zai iya masa wakilci aure zai iya masa komai koda kuwa shi mahaifin yaron bai fad’a maka hakan ba, inda yabaka d’ansa ka rike masa shi, to ya baka wannan ragamar a hannunka, to kamar yadda mahaifinka ya bani kai auwal ,tkmr ya bani ragamarka ne,
amman ita ummi bazata iya bada auren muwaddat ba, saboda ita macece shiyasa dana tashi sai na nemi shi mahaifinta da batun , tare da neman shawaran d’anuwana mukazo tare Kuma akwai sheidu alokacin da aka d’aura aure a wannan lokacin, kwarai ya haramta ma’aurata suje su aikata wani Abu ,domin idan suka aikata hakan niyyarsu niyyar zina ce sai dai ko da wasa idan aka fad’a musu ,su din ma’aurata ne ,Koda zasu d’auki abun amatsayin wasa sukaje suka sadu da junansu ,sunan abinda sukaje sukayi ba zina bane aure ne ,koina suje Koda kuwa gaban alkali ne suka ce ba zina suka aikata ba, za’a iya kafa hujja, da wane bance maka wance matarka bace , sai yace “eh na tuna ka fad’a min domin akwai hadisin da yake magana akan haka “manzon Allah s.a.w yace ” salasun jidduhunnajid rahzulnajid abubuwa guda uku , gaskiyarsu gaskiya ne ,haka zalika wasansu wasane .attalaqu ,
wanniqa’u, wal ukutu , na farko saki na biyu Kuma bada aure na uku shine ka yanta bawa ,a wata ruwayar manzon Allah s.a.w yace “ko kuma ka maida mace misali idan namji ya saki matarsa saki d’aya ko Kuma ya saketa saki biyu, ko da wasa yace ya maida ita ta maidu .
Ta bangaren ka bawa mutun aure , lafazin, na baka aure kad’ai akwai abubuwa dake tattare dashi …..
Daga cikin abubuwan dake tattare dashi ace wa mutun ai wancen matarka ce kuma matar mutun din ce da gaske, sai mutun ya d’auka da wasa ko kuma mutun ya d’auka ba’a wasa ba ,to duka wannan yashiga ciki …………
Mmn sudais
warning!!!
don’t read this novel if you know you are not married… ❌❌❌coz this book contains only for mature people , if you read it, is for your own risk ……
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim