Search
You have no alerts.
    The Den of Novels

    …..cikin wani irin birgicewa da matsanancin tashin hankalin bunayya ya soma magana cikin sambatu “abi tashi …taimaka ….
    Ka taimakawa rayuwata abi, mu kai ummi hospital ,abi bana son na rasa ummi nah ,wallahi Ina sonta bana son na rasata ,kuskure ne abinda nayi bazan sake ba ,wallahi nayi nadama jikinsa na kyarma yake wannan sambatun “ummi ki tashi dan Allah karki min haka …
    “Karki tafi ki bar muhammed auwal dinki …
    “Idan kika tafi duniya zata masa zafi …..
    “Hakika ummi baki cancacin haka daga garemu ba ..

    Abi dake rike da hannun ummi gam cikin nasa jikinsa ya sake d’aukar wani kyarma yana zubda hawaye masu ciwo da rad’ad’i … …..

    Hawayen da yasan sunfi kowani hawaye ciwo da rad’ad’i arayuwarsa
    ,domin kuwa zuwa lokacin ya rigada ya gama sadaukarwa kansa cewar ummi ta rigasu gidan gasky ,dan haka ahankali bakinsa ke furta kalmar” Inna lillahi wa Ina ilaihi raji’un …
    “Shikenan mukarama kin tafi kin barni …….

    Jin haka yasa hankalin bunayya da muwaddat sake kololuwar tashi, a matukar firgice bunayya ke bin abi da wani irin kallo ‘kwal’kwaluwasa na juyawa ….
    can ya zabura ya mike tsaye ya soma magana cikin d’aga murya “abi me kake cewa haka ?
    “Kana nufin ummin tawa ce ta rasu ko me ?
    “Impostible abi, ka..ka daina furta haka ga ummi nah ” “ta Yaya ummi nah zata mutu yanzu?

    “Ummi ba zata mutu yanzu ba ,lokacin mutuwar ummi nah bai yi ba ,kwata kwata ma babu mutuwa acikin idanuwanta,idan ba zaka taimakamin mu kaita hospital bane kawai nasani ….”Ni..ni sai na kaita ………
    ya k’arashe maganar yana k’ok’arin kwace ummi daga hannun abi ..

    Yayinda muwaddat ta kasa motsi daga inda take ,ta dawo tamkar mutun mutumin a durkushe tana duban gangar jikin ummi da bai motsi ,koda bata san mutuwa ba tasan tabbasss ummi ta tafi……..

    Wani irin fad’uwa gabanta yayi da mugun karfi, take wani Abu ya tsarka mata tun daga kirjinta zuwa kasan mararta ….
    Cike da tashin hankali bunayya yasoma k’ok’arin ciccibar gangar jikin ummi hawayensa na diga bisa fuskarta, abi yayi karfin halin tallafota jikinsa , shima hawaye yake, hakika wannan abu da ciwo yake ,yasan mutuwa tana kan kowani bawa da yayi eimani da Allah ,amman sam bai ta’ba expecting mukaramarsa zata tafi ta barshi a daidai wannan lokacin ba, ban da kalmar Inna lillahi wa Ina ilaihi raji’un babu abinda yake furtawa har suka fito daga bangaren abi ,nan ne fa binta mai aiki ta fahimci akwai damuwar dake faruwa acikin gidan ganin abi da bunayya suna tara tara da ummi .
    Jikinta na rawa ta k’arasa garesu tana tambayarsu “lafiya alhaji meke faruwa da hjy ?
    “Me ke damunta ?
    Daga abi har bunayya babu Wanda yayi k’ok’arin bata amsa, illa k’ok’arin nufar hanyar fita da suke cikin tsananin tashin hankali..

    Ita kuwa muwaddat da kyar ta soma k’ok’arin Mikewa tsaye bisa kafafunta ,ai ko gama Mikewa batayi ba, tayi kasa luuuuuu tare da sakin wata razananniyar k’ara ta fad’i kasa sumammiya wannan k’arar data yi ne yayi sanadiyar da binta ta nufi hanyar parlour’n cikin matsanancin tashin hankalin tana zuwa ta risketa cikin matsanancin hali take jikinta na rawa tana sallalami ta janyo sauran ruwan da aka yiwa ummi amfani dashi tashiga tsiyaya mata tana Kiran sunanta ….

    Kai tsaye inda aka faka motar data dawo dasu daga hospital d’azu suka nufa daita , direba na hangosu ,ya zabura ya mike ya nufo inda suke cikin sauri ,dan ko ba’a fad’a masa ba ,yasan babu lafiya ,domin fuskokinsu da gangar jikinsu kad’ai ya nuna masa haka ,cikin sauri ya bud’e musu gidan baya , bunayya yayi saurin shiga yana rungumo ummi jikinsa ,abi yasanya gangar Jikinta cikin motar ya rufe,kana ya nufi gidan gaba , gabad’aya jikinsa a sanyaye yake ,cike yake da fargaba da tashin hankali ,ya sani ya rasa mukaramarsa har abada , ya kasa kamanta halin dayake ciki , duk yadda ake jin mutuwa Yana jinta fiyye da haka a gangar jikinsa ,zai kaita hospital ne domin bunayya ya tabbatar da bata raye ko ta fawwalawa Allah komai ……..

    Shi kuwa bunayya jikinsa Banda rawa babu abinda yake ,ya sake birkicewa ,sai faman zuba sambatu yake rike da hannu ummi ,yana jin babu wata bakar rana arayuwarsa kmr wannan ranar ,tun da yake arayuwarsa bai ta’ba jin makamancin bugun zuciya da tashin hankali irin wannan ba ..
    ya d’auka tashin hakalin rabuwa da muwaddat wani bangare ne na rayuwarshi ,a she rabuwa da umminsa yafi komai tashin hankali da ciwo …
    ” hakika bai san yadda rayuwarsa zata kasance nan gaba ,”shin me yasa mutuwa zatayi masa haka ?
    “Karya ne wallahi umminah bazata mutu ba ya fad’a da karfi Wanda yasa direba taka motar da karfi ,shi Kuma abi yashiga goge hawaye yana sake maimaita “Inna lillahi wa Ina ilaihi raji’un…..

    Cike da tashin hankali Abi yaciro wanshi yasoma neman layin d’aya daga cikin likitocin asibitin Ummi ,yana shaida musu halin da Ummi ke ciki, ikon Allah ne kawai yakai su asibitin, domin wani irin shararan gudu da driver yake tsulawa akan titi.

    wani irin mahaukacin burki me k’ara direba ya taka dai dai lokacin daya shigo haraban asibiti ,da isowarsu asibiti,sun iske bakin k’ofan emergency cike da manyan likitoci, take likitocin suka soma k’ok’arin k’arasawa inda motar take , yayinda wasu daga cikinsu ke turo gadon d’aukar mara lafiya ,cikin gaggawa gaba d’aya likitocin hankalinsu a tashe yake sanadiyar ganin Ummi cikin mawuyacin hali.

    cike da tashin hankali aka ciccibi Ummi aka dorata akan gadon asibiti aka fara turata Bunayya yafito a guje , kallo d’aya zaka masa kasan yana cikin matukar tashin hankali, hannu Ummi ya rike cikin nasa yana binsu gudu gudu sauri sauri ,yana gunjin kuka yana Kiran “Ummi nah karki min haka…..
    ” Ummi na na tuba bazan k’arawa ba..”
    ” Ummi nah ki tashi karki tafi kibarni please Ummi, yayinda ruwan hawayensa ke d’iga a saman fatar hannun ummi , kai tsaye d’akin likita akayi da ita, nan take likitoci suka rufa a kanta ,suna bata taimakon gaggawa..

    Likitocin sunyi iya kokarinsu amman abun tafi karfinsu ,shi kansa bunayya ya kasa aiwatar da komai, dan kuwa kusan shi yafi su rud’ewa ,nadama dana sani babu wanda bai yi ba ,jikin likitocin yayi sanyi, suka shiga kallon juna , gabad’aya an rasa wanda zai iya fahimtar da wad’an bayin Allah rasuwar ummi, saboda ganin halin tashin hankali da suke ciki, ba d’an ba,ba uban ba ,kowanensu ka kalli fuskarsa kasan yana cikin tsananin tashin hankali …

    Da kyar Dr najib ya juyo Yana dubansu cike da tausayawa “alhj sai dai muyi hakuri ,dan zuciyar madam ta daina bugawa , ta rigamu gidan gas…….
    maganarsa ce ta tsaya cak sakamakon wata uwar cakuma da bunayya yayi masa, yana sakin wata irin k’ara kana jikinsa na rawa yace “you are very stupid Dr najib……..
    ” ummin tawa kake cewa haka?
    “idan ka sake furta wannan kalmar ga umminah sai na kasheka da hannuna …
    ” mamarka ce zata mutu amma ba umminah ba, ya k’arasa fad’ar haka yana matse wuyansa da rigar jikinsa da , likitocin sukayi caaaaa akasu suna k’ok’arin kwatar wuyar Dr najib a hannu bunayya ..
    Da kyar abi yasa ya sakar masa wuyar riga ta hanyar buga masa tsawa,”kana hauka ne bunayya ?
    “hawaye na bin kuncisa yace “abi bakaji abinda yake cewa akan umminah ba?
    ” wai ummina ce ta rigamu gidan gasky ,ummi nah fa …..
    Mamana…. mahaifiyata ce fa……. ..
    ya juyo cikin rawar jiki ya kalli likitocin dake tsaye akanta, yace “dukkaninku baku San aikin da kuke yi ba kawai dai kuna nan ne just for nothing ,ku bar min d’akin ni zan duba mahaifiyata amman sam ummina bata mutu ba …..
    Abi ya rigada yasan d’ansa baya cikin natsuwarsa da hankalinsa, mutuwar uwarsa tazo masa a bazata da kuma shekarunsa na kuruciya .

    Jiki a sanyaye ya kamo hannunsa “muje waje bunayya “
    “a’a abi babu inda zani sai nasan halin da ummina take ciki , akwai jijiya d’aya dake jikin kowani d’an adam ,abarni abani damar na dubata da kaina matukar na dubata zan……zan………
    Sai Kuma kuka yaci karfinsa ya kasa k’arasa maganarsa ya durkushe gaban abin “shikenan nayi sanadiyyar mutuwar mahaifiyata da kaina ? Abi ya kamo shi shima kukan yake son yi
    “Kayi hakuri bunayya haka Allah yaso muje dai waje likitoci su samu suyi aikinsu,”abi ummina ce fa kwamce bata motsi ?
    “Ka furta kalmar Inna lillahi wa Inna lillahi raji’un da kyar dai abi ya janyo shi sukayo waje sam idan kaga bunayya bazakace shine mai shegen girman kan nan da dagawa ba abi ya rungumeta shi ajikinsa yana furta kalmar Inna lillahi wa Inna ilaihi raji’un ,wanda sai lokacin Allah ya raimakeshi ya rika yayita yi yana zubar da hawaye …

    Awa uku cur likitoci suka sake d’auka akan Ummi ,cikin hukuncin Allah sai gashi ta farfad’o tare da sauke naunayen ajiyar zuciya ,godiya suka shiga yiwa Allah , suna murna, sun yi farincikinki sosai domin ummi mutun ce ,akwai kirki da sanin yakamata, uwa uba sanin darajar dan adam , sam ita bata da wulakacin ,da talaka da mai kudi duk matsayi guda garesu a wajenta , rasa irinsu ba karamin hasara bane, amman idan Kiran babban sarki ne babu yadda za’a yi dole ta amsa Kira Kuma dole zuciya tayi hakuri .. . …

    Farkawa kawai ummi tayi ta ganta akan gadon asibiti, ta fahimci hkn ne sakamakon ganin mutun biyar daga cikin likitocin dake aiki akarkashinta ne tsaye bisa kanta suna Kara Mata ruwa tayi hanzarin mikewa zaune tana raba idanu tare da tuna abinda ya haddasa Mata zuwa asibitin ,Dr saratu dake bayanta ta k’araso jikinta a matukar sanyaye sai dai kallo daya Tayi mata abinda ya faru yashiga dawowa cikin ‘kwalwaluwarta idanunta kamar gauta alamar tana cikin tashin hankali Kuma har lokacin idanunta Basu daina zubar hawaye ba, ta fasa ta razananniyar k’ara tare da fizge hannuta daga rikon da Dr Salim yayi Mata ta kamkame saratu ajikinta tana kuka magana take son yi amman ganin likitocin yasa ta kasa furta komai sai kuka ” to me ma zata ce ?
    “Duk abinda zata fad’a a yanzu tamkar ta tonawa kanta asiri ne, dan hk ta cigaba da kukanta Dr saratu na shafa bayanta , Dr saratu ta kamkameta tana rarrashinta alamar tayi shiru ..
    .
    ” ki kwantar da hankalinki mukarama inshallahu komai zai daidaita ganin kamar akwai wani sirri na musamman dake bakin ummi yasa likitocin suka fice daya bayan d’aya suka bar d’akin Dr saratu ta kwantar daita “ki kwantar da hankali koma meye ki damunki ki fallawa Allah …..
    Ki yawaita furta Inna lillahi wa Inna ilaihi raji’un ,zuciyarki na matukar bukata hutu a halin yanzu ummi ta runtse idanunta gam ..

    Likitoci na k’ok’arin fitowa abi ya fad’a d’akin shi kuwa bunayya da sauri ya bi bayan d’aya daga cikin likitocin yana tambayarsa ,yanayin jikin umminsa ,suna tafiya doctor na yi Masa bayani ,har suka shiga cikin office dinsa, ya dan juyo yana dafa kafadar bunayya “ka kwantar da hankalinka inshallahu zata samu sauki, ka dinga had’awa da addua zamuyi mata allurar yanzu dan ta samu relief, bunayya yayi jugun hawaye na kwarara akan kuncinsa , da kyar yayi karfin halin juyawa batare da ya cewa likitan komai ba, ya bar office din kai tsaye d’akin d’a’a kwantar da ummi ya nufa ,yana shiga ta bud’e idanunta tana ganin shine, ta d’auke kanta zuwa wani bangare tare da cewa “kace masa kar ya k’araso gareni banason ganinsa ,ya bar d’akin nan bana son ganina acikin idanuna , karaf maganarta ta shiga cikin kunnuwanshi .
    tun kafin Wanda aka bawa sakon ya fad’a masa , ya tsaya daga inda yake yana duban ummi da har lokacin kuka take ..
    “Ummi ….
    Ba..bana son jin komai daga bakinka ta k’arasa maganar tana sauke numfashi da kyar “
    Hannu abi ya d’aga masa al’amun ya tafi kawa ..

    Ahankali ya juya jikinsa a matukar sanyaye ya fice ya nufi harabar hospital din yana jin wani irin kuna acikin zuciyarsa , kai tsaye bayan mota ya bud’e ya shiga ya zauna yana jin wani irin bakinciki ,batare da bata lokacin ba direba ya yiwa motar key ,suka bar hospital, zaune kawai yake a bayan motar amman shi kad’ai yasan abinda yake ji ,shi kad’ai zai iya misalta halin tashin hankali da yake ciki.

    da fari baiyi tunani zai damu a dalilin cikin jikin muwaddat ba domin ganinsa haka shine sakamakon masu hali irin na iyayensa ,sai yanzu ya fahimci abun ba haka bane, suna shigowa gidan ,ya nufi part din umm domin ganin halin da muwaddah take ciki ,can karshen gadon ummi ya iske kwance tana jujjuya Kai had’e da rike kasan mararta ,ya k’arasa gareta da sauri yana k’ok’arin kamota jikinsa ta goce “karka ta ‘bani … kana ta yunkura ta mike tsaye ta soma tafiya.

    Da kyar take takawa ta fito tana layi hakan yasa ya biyo bayanta da sauri yana Kiran sunanta “muwaddat Ina zaki cikin wannan hali ?
    Ta juya ahankali domin fad’a Masa bakar magana jiri ya kwasheta tayi kasa zata fad’i cikin rud’ewa ya kamota jikinsa ya d’auke cak dan ganin jini a bin kafafunta , part dinsa yayi daita , da kyar ya samu jinin daya soma bin cinyoyinta ya tsaya amman ya Sha wuya sosai, yanzu wani irin son cikin ne ya dawo masa sabo fil ….
    Allurar bacci yayi mata domin tasamu natsuwar zuciya, amman ta burkice masa tana zuba masa ruwan bala’i ..

    Duk yadda yayi k’ok’arin ya shawo kanta ta fahimceshi amman abin yafi karfinsa, sai faman had’ashi da Allah take ya rabata da ciki ,gabad’aya ya sake shiga rudu ..

    yana kallonta ta fice daga bangarensa shima ya biyo bayanta anan suka ci karo da idanun baba mai gadi kallo daya yayi masu ya kawar da kansa yana Allah wadai da masu hali irin su “da al’amun uwarsu bata da lafiya, amman hakan bai saka sun hakura da juna ba, wannan wace irin maseefa ce haka?
    yayi maganar a kasan ransa ” ko yake zuwa yanzu ya daina ganin laifin su sakacin iyayensu ne ..

    Binta bunayya ya shiga yi har ya karaso inda take bai tsaya wata wata ba ya d’auketa ya sabata a kafad’arsa yayi d’akinta daita ,ya kwantar yana mata sannu , sannan ya koma cikin part dinsa, har kusan magariba yana d’akinsa kwance bai tashi ba tunani Kashi da Kashi ke dawainiyya dashi, jifa jifa ya kan Kiran abi ya tambayi yanayin jikin ummi ,sannan haka ya dinga zariya tsakanin part dinsa zuwa na ummi domin duba lafiyar muwaddat..

    Karfe biyun dare muwaddat ta farka daga baccin daya d’auke ta ,yana zaune akusa daita ya zuba mata ido, hannushi cikin nata jin motsin datayi ne yasa ya gane ta farka da sauri ya mike yana Kiran sunanta muwaddat, sai ma ta rufe idanunta wasu zafafa hawaye na zubo Mata babu irin maganar da bai mata ba amman ta shareshi band’aki ya shiga ya had’a mata ruwan mai d’an dumi zuwa yayi zai d’auketa duk da Jikinta babu kwari sai data fixge tana zabga masa uwar harara “bana son jin hannunka ajikina na tsaneka ka rabu dani ..
    Kuka ne yaci karfinta, jin kukan nan yake har cikin zuciyarsa ya kasa ce mata komai “

    Can kusan minti goma yace “plz muwaddat kina bukatar kulawa da taimakona a daidai wannan lokacin ..

    “Banason ko wani iri taimako ne daga gareka ka barni na mutu na huta da wannan bakinci ,” komawa tayi tayi kwanciyarta, har kusan asuba yana fama daita tana jin Fitarsa matsalaci ….

    Koda ya dawo ma kusa daita ya tsaya ,ban da hawaye babu abinda idanuwanta ke zubarwa cikin sanyayyiyar muryarsa yace “Dan Allah muwaddat na rokeki ki bar kukan nan haka kada yayi miki illa “
    “Yaya kuke son nayi, gaki tashin hankali gurinki ,ga matsalar ummi ,Ina bukatar kowane daga ciknku arayuwata ,bana son ba rasaki “kiyi hakuri muwaddat ki d’auka kaddararmu ce tazo haka …
    Gefe ta juyar da kanta “ka rabani cikin Nan ni banaso …….

    Shiru yayi kawai had’e da kafeta da tsumammun idanunsa ,yau tazo Masa da abubuwa dayawa tashin hankali da rudani , gabad’aya duniya ta cakud’e mashi waje d’aya ba ta bangarenta ba, bata bangaren umminsa ba ,bai ta’ba sanin haka tashin hankali irin wannan daya ke ciki yake da ciwo ba , “ya zai yi da kaddara data afka masa?
    ” d’an da zai fara samu a duniya shine yazo ta wannan hanyar ….”

    Cike da muryar kuka tace “dan Allah ka rabani da cikin tun kafin ummi ta dawo ,na had’aka da Allah ka ci ….

    “Dan Allah dan annabi malama ya isheki “

    “enough muwadda “
    ” Wai ma me kika d’auke ni ne ?
    “Mahaukaci ko me ?

    “Nasan na aikata zina dake na tsawon lokaci har ga sakamakon nan ajikinki ,amman wallahil azim bazan iya zubar da wannan ciki ba ….
    “Bazan iya d’aukar wannan zunubin ba …
    “bazan iya kashe kiyashi ba ,bare gudan jini …… I can’t muwaddat Yana gama fad’ar haka ya juya fuuuuuuuuuu cikin tashin hankali…

    Mmn sudais
    MUWADDAT PAGE 39

    Note
    error: Content is protected !!