Search
You have no alerts.
    The Den of Novels

    … parlour’n ne ya sake d’aukar shiru na tsawon minti goma, gabad’aya ahlin dake zaune a gurin sun tattara hankalinsu da natsuwarsu gurin sauraron bayanan uncle uncle umar,” bunayya zuwa yanzu dai nasan ka tuna abinda na fad’a maka a wannan lokacin, kuma ka fahimce inda maganata ta dosa ?
    Cikin wani irin yanayi mai tsarkakkiya bunayya ya d’aga kanshi still kwayar idanunshi na cikin na uncle dinsa , “dan haka ka kwantar da hankalinka muwaddat tana nan a matsayin matarka ta sunnah ,haka zalika yaran da zata haifa maka suma a matsayin ya’yan sunnah suke ba ya’yan zina ba ….

    Naunayen ajiyar zuciya gabad’aya ahlin suka sauke had’e da yiwa Allah godiya ,ummi kam har da sujjada tayi domin nuna farincikita ga Allah ubangijin talikai da yasa ba zina yaranta suka aikata ba.

    Uncle umar ya numfasa kana ya cigaba da magana kamar haka “a zahirin gasky yan’uwana wannan abinda ya faru akanmu aya ce garemu ,Kuma kuskuren ne babba da aka so aikatawa Allah ya kiyaye ,yanzu da ba dan nayi tunanin aurar dasu ba da me kuke tunanin zai faru?
    ” barin ma ke ummi da kike wa yaro kallon yaro ne ba zai iya raya sunnah ba ,kisani duk qanqatar najimi ya wuce ki d’aukesa a matsayin yaro ,domin namji baya ta’ba kasancewar yaro agurin mace dan ga zahiri nan kin gani .

    ” Sannan ku dinga sauraron uzirin yaranku idan sunzo muku dashi, karatu baya hana aure, haka zalika aure baya hana karatu, kowanne da muhallinsa arayuwa ,”qalu bali gareku iyaye masu ra’ayin son yaransu suyi karatun boko fiyye daraja aure ,shi kansa karatun idan mace ko namiji nada aure sun fi samun natsuwar yin sa , a galla uncle umar sai daya d’auki sama da minti talatin yana bayani akan kuskuren da ummi ta tafka , sannan daga karshe yace Allah ya kiyaye gaba ..

    Gabad’aya suka had’a baki gurin cewa” ameen” Abi da dady suma suka tofa albarkaci bakinsu take parlour’n ya kaure da hayaniya wanda ya jawo hankalin yaran gidan kacukan faiza ta tattara hankalinta zuwa parlour’n dan haka nan ta kasa samun kwanciyar hankali ..

    Ahankali bunayya ya d’auke tsumammun idanunshi cikin na uncle umar da tun sanda ya soma zayyano magana suke kanshi ,ya maida su ga muwaddat dake zaune har lokacin hawaye na gangaro mata,
    wani irin sanyi dadi ne ya shiga ratsashi , daman shi tun da yake saduwa daita bai ta’ba jin cewar zina yake aikatawa daita ba.

    ” ahankali ya mike daga zaunen da yake da niyyar Isa inda take, idanunshi suka sauka akan yaya akram wanda yayi folding din hannuwansa duka a kirji yana kallon yatsun kafafubsa, kallo d’aya bunayya yayi masa ya fahimci halin da yake ciki ,Sam baya cikin hankalinsa da natsuwarsa ,ko bai fad’a masa ba ,yasan tunanin yaransa yake , madadin ya k’arasa ga muwaddat kamar yadda yayi niyya sai ya k’arasa gurin Yaya akram, ya d’aura duka hannuwansa a saman kafad’arsa, murayarsa can kasa ta yadda babu mai jin abinda zai ce ” cool down yayana, karka bari wannan matsalar ta dameka, ka bani dama yayana …”ina neman alfarma agurinka da ka bani damar fahimtar da iyayenmu cewar …..
    “Cewar ke ….?
    “No bunayya this is not the right time da zasu sani ,da sauran lokaci tukuna, yana gama fad’ar haka ya juya ya bar parlour’n hankalinsa a matukar tashe.

    take shima bunayya ya biyo bayansa a tare suka shiga part dinsa ..
    Sun dade zaune acikin d’akin Yaya akram suna tautaunawa bunayya na fama dashi ,akan ya bari ayi komai a wuce gurin, “kowani bawa da yadda kaddararsa take zuwan masa , haka zasuyi hakuri su d’auki kaddararmu dan Allah yaya ka bari na nasar musu , fur Yaya akram yaki, bunayya yayi rarrashi yayi ban hakuri amman yaya akram yace a’a haka bunayya ya hakura da rarrashinsa yana mai jin tausayin Dan uwansa acikin ransa ….

    Da yammaci ranar kafin abi da uncle umar su wuce , dady yasa aka Kiran masa yaya al’ameen ,
    Yana zaune akan kujerar dake fuskantar dady jikinsa na rawa dan haka nan yake ji ajikinsa akwai abinda ke faruwa ,lokacin da dady yake zayyano masa batun auren muwaddat da bunayya kad’an ya rage zuciyarsa bata buga ba tsabar firgici da tashin hankalin daya tsinci kanshi ,wani Abu mai duhu ne ya gilma cikin idanunshi take ya runtse idanunshi jikinsa na sake d’aukar zafi da rawa , yace ” kenan da matar aure na yita soyayya kenan, har ina muradin mallakarta a matsayin uwar ya’ya na ?

    “Haka ne inji cewar dady shiyasa lokacin da kazo min da zance kana bukatar auren muwaddat kaji nace maka ka bar magana, ga faiza nan ka nemi auranta ,Kai yanzu a tunaninka akwai diyar cikina da zan iya hanaka aurenta ?

    “Babu aminu saboda ina sonka Kuma Ina jinka tamkar d’an cikina ,sai dai lokacin nayi mamakin yadda ka watsa min kasa a ido ,ka nuna min son ranka ,wanda ni a nawa tunanina ko ranar ake d’aura aurenka da muwaddat nace ka barta zaka hakura kabi umarnina ..
    nasiha mai cike da kwantar da hankali dady ya shiga yi masa saboda ganin yadda ya fita ranshi , haka su abi ma, daga karshe dady yace “har yanzu kofar neman auren faiza a bud’e take agurinka , idan kana bukatar , amman kaje ka samu aminika kuyi shawara, ni kuma zan nemi iyayenka da batu ..”

    Kasa sarrafa harshensa yayi duk da maganar yake son yi , ya yunkura da kyar ya tashi yana layi , Kai tsaye d’akinsa ya nufa ya fad’a kan katifarsa tare da runtse idanunshi .
    “anya kuwa zan iya ?

    “Anya zan iya rayuwa da wata ba muwaddat ba ?

    “Hakika wannan yaron ya cuceni ..ya cucueni ya gama dani ..ya dafe kanshi da duka hannuwansa ..

    Daren ranar da labarin auren muwaddat da bunayya har ma da cikin jikinta , ya ziyarci kunen faiza, k’aramin hauka tayi a d’akinta tana d’aukar duk abinda hannunta yaci karo dashi tana bugawa, a bango tazama tamkar wata birkitacciya, ahankali take furta “wayyohllly Allah rayuwata, “wayyohllly zuciyata, shikenan na rasa shi …..
    “, Ina sonka kai ne mutun na farko da zuciyata ke so ,na Sha fama da ciwon rashinka ,ciwon sonka ,zuciyata ciwo wayyohllly….
    cikin haka mumy dake k’ok’arin shiga d’akinta taji sautin ihunta cikin sauri ta fad’a, d’akin hankalinta a tashe a razane tace “ke ..faiza meke damunki ?
    Faiza na gani mumy ta sake rushewa da sabon kuka tare da zubewa kasa bisa gwiwonta mumy ta k’araso “ki fad’a meke damunki ,ko kin fara shaye shaye ne faiza ?
    kalli yadda kikayi da dakinki ?
    Faiza ta girgizawa mumy Kai tana kuka “mumy yaya auwal ne .
    ” Me Yaya auwal din yayi Kuma ?
    Ta kamo hannu mumy ta d’aura daidai saitin zuciyarta “mumy Yaya auwal nake so ,Kuma wallahi shi kansa ya sani ba tun yau ba ina matsanancin kaunarsa ,mumy da son shi na rayu na girma, bazan iya rayuwa babu shi ba ,na sha wuya a dalilin soyayyarsa ,a she mijin yayata ne mumy..
    “Yaya zanyi mumy ki bani shawara yaya zanyi ?

    “Kai jama’a wannan wani irin tashin hankali ne Kuma ?
    Ganin yadda ta birkice sai kuka take tana furta kalmar tana son auwal yasa mumy rungume faiza akirjinta tana shafa bayanta ” kukan ya Isa haka ,hakuri zakiyi kinji faiza, ki d’auka haka kaddararki take ,zan taya ki addu’a, inshallahu Allah zai sausauta miki abinda kike ji acikin zuciyarki akansa ,matukar kika bi umarnina a matsayina na mahaifiyarki , kika min biyyaya zaki ga abinda zai biyo baya ,sai kinyi mamakin irin mijin da zaki samu ….
    ” daga yau ki sawa ranki tamkar baki ta’ba son wani mai suna auwal ba a rayuwarki…

    Ahankali muwaddat take ta kowa zuwa hanyar d’akin faiza tana son ta d’an kwanta ta huta ,tasan idan ta kwanta a d’akinta bunayya ba zai barta ta huta ba ,dan ta kula da rawar jikin da yake ,sai dai zuwan nata babu abinda ya janyo mata sai shiga tashin hankali da firgici ,domin kuwa duk wannana tautaunawa da suke a cikin kunnen muwaddat sukayi shi, wasu zafafan hawaye ne suka shiga gangaro mata da sauri ta juya ta bar gurin ,saboda jin motsin fitowar mumy ..

    *********

    Kwance take a d’akinta akan gado, duk tunani duniya ya isheta , gabad’aya tausayin faiza take ji ,da zata iya da tasa auwal ya sawwake mata, ya aure faiza “to cikin jikinki kuma kiyi yaya dashi zuciyarta ta tambayeta ?

    Mirginawa tayi ta mike cike da sanyi jiki ta sauko daga kan gadon, ta koma jikin window ta tsaya had’e da rike labulen window tana mai ciza lip’s dinta still tunani take .

    Tun sanda ta sauko daga kan gadon yana tsaye a bakin kofar ,ya hard’e hannuwansa duka a saman kirjinsa kawai Yana kallonta .
    hankalinsa yayi
    matukar d’agawa saboda hango tashin hankali da yayi a tattare daita.

    Ahankali ya taka zuwa inda take ,ji kawai tayi an dafa kafad’arta ta baya, da sauri ta juyo a matukar tsorace ,suka had’a idanu ,fuskarsa babu walwala sannan babu wata
    damuwa ,girasa d’aya ya dage mata yana Sanya kwayar idanunsa cikin nata ,sunkiyar da kanta kasa tayi ,yayinda shi kuma ya janyo hannunta zuwa kan gado, ya zaunar daita ,shima ya janyo karamar kujerar mirror ya zauna suna fuskarta juna ahankali muryarsa a kasalance ya Kira sunanta “muwa ……
    Taji wani irin zirrrrrrrrr a gabad’aya ilahirin jikinta ,tana jinsa taki amsawa har sai daya sake kiranta, ta d’ago kyawawan idanunta dake cike da ruwan hawaye “me ne ne damuwarki muwa ?
    “I thought wannan cikin shine damuwarki ,yanzu Kuma komai ya daidaita, to meye abun dogon tunani saboda Allah idan dai ba so kike ki illatamin d’a ko ya ba ?

    Hannuwanta ya kamo cikin nasa yana. Massaging ahankali “ki taimaki rayuwata ki daina wannan tunanin ,murna yakamata kiyi ba wannan tunanin ba …
    Hannuwanta ta zare cikin nasa ta kwanta tana runtse idanunta ,tashi yayi ya daga inda yake ya kwanto samanta ya Kai bakinsa daidai kirjinta ,kissing din saman nonuwanta ya shiga yi ,take gabad’aya yanayinsu ya soma canzawa ,babu abinda yake bukata kamar yaji shi cikin jikinta ,yayi missing dinta har bai san yadda zai misalta ba ,baya taja kad’an daga kwance da take tana sauke naunayen ajiyar zuciya,matsota yayi ,ya kamo fuskarta da hannuwansa ya had’e bakinsu guri d’aya ya shiga tsotsa duk yadda taso taki yarda hakan ya cutura dan bak’aramin damka yayiwa bakinta ba , ahankali ya samu narasa cafko laulausar harshenta yashiga tsotsa yana tsiyaya mata miyon bakinsa …..
    Ta soma k’ok’arin fixge bakinta duk yadda taso ya barta yaki sai daya tsotsa son ranshi sannan ya mike ya barta yana kallon tsakiyar idanunta “wannan ya zamo karo na karshe saboda bana Jin sonka araina yanzu duk da matsayin ka gareni ,”ni din ma yanzu na daina sonki a Raina, kawai dai cikina dake jikinki nake so,dan haka sai ki adana makaman yakinki yana gama fad’ar haka ya bar d’akin ..
    daren rayuka uku basu samu damar runtsawa ba, faiza al’ameen da muwaddat ..

    ********

    Washegari suka d’auki hanyar komawa Lagos, jirgin safe suka bi ,12:00 dot a Lagos tayi musu ,bello direban ummi ne yazo d’aukarsu ,tun cikin jirgi yake manne mata ajiki ,ita kuma tana sharesa ,acikin motar ma saita glass din bangarensa yayi saitin da take zaune duk wani motsinta akan idanun shi ,suna Isa gida ummi tasoma fita ,suna gaisawa da baba mai gadi ,sannan muwaddat ta fito .
    Shima fitowa yayi yana mika kana ya k’araso kusa daita kamar zai shige jikinta ,ta kalleshi taja tsaki sannan ta juya …

    cikin sarsarfa tashiga d’aga kafafunta ,shima ya biyota cikin sauri sauri “malama kiyi tafiya ahankali mana kinsan fa bake kad’ai bace, gabad’aya shi a wannan lokacin tsakin da tayi bai tsaya masa a rai ba , duk da yaji zafi sosai .

    a halin yanzu duk abinda zatayi bai damesa ba,shi dai karta salwantar masa da cikin jikinta, wannan ne bazai yarda ba , jin abinda yace yasa ta kwasa da d’an guda kawai dan ta Kara hassalashi , hannuwansa duka yasa ya dafe kirjinshi yana furta “ya salam tare da k’ara sauri bai fi sauran taku biyu ya cafko ta ba ,tayi saurin shigewa d’akinta ta rufo kofar da sauri had’e da murd’a key ta jinkina bynta da kofar tana kuka tana sauke ajiyar zuciya.

    jikin kofar ya k’arasa yashiga bugawa da iyakacin karfinsa yana kiran sunanta amman taki bud’ewa ,ummi cikin sauri hankalinta a matukar tashe ta k’araso garesa tace “Kai lafiyarka zaka cika mana gida da hanayi ?

    ya juyo ahankali ya dubi ummi kamar zaiyi kuka yace “ummi muwadda ke kokarin min hasarar baby nah …..

    ” amman na rantse da Allah ummi idan wani abu ya samu cikin nah zan aikata abinda gabad’aya kowa zai yi dayasani.. “

    “yi min shiru a nan kafin na tarwatsaka ,mara kunya kawai da bai san ta ido ba, ” daga dawowar mu zaka soma nuna hali .

    wani irin kallo ya dinga bin ummi dashi kafin daga baya yace “haba ummi karki fad’a haka mana ,yanzu idan na bari tayi gangancin da muka rasa cikin nan ummi baki sani ba ko shi kad’ai ne jikanki a duniya, ni dai ki fad’a mata duk iskanci da zatayi ta bari ta haifa min d’ana ko ‘yata dake cikinta ,duk ma abinda zai biyo baya wannan ba matsalata bace bare ya dameni ni dai cikina kawai nafi ji….

    wasu zafafan hawaye ne masu zafi da ciwo taji suna sauko mata akan kyakkyawa fuskarta ,cikin sauri tasanya hannuta ta sharesu tare da jan numfashi da kyar ta fesar “shi kenan bunayya ya daina sonta, daman tasan yaudarata yayi da daddan kalamai masu tsuma zuciya ,a she duk yaudara ce, ba ainihin soyayyar bace, tunda gashi ta cikinsa yake yi bai damu da daita ba…. wani sabon tsanar cikin taji, tana jin dama arasa shi a halin yanzu taga abinda zai yi tun da dai tasan duk wulakacinsa da iskancinsa bai isa ya aikata lahira saboda cikinsa , sautin muryar ummi ce tasa saisaita kukanta “wai bunayya mai yasa baka da ta ido ne?
    “ni kake fad’awa duk abinda ya fito daga bakinka saboda kai idanunka a tsakar kai suke?

    hannusa ya kai ya shafa sumar kanshi zuwa keyarsa tare da tsosawa ala’mun jin kunya, kana muryarsa can kasa yace “ummi kiyi hkr idan ranki ya ‘baci amman dan girman allah ki fad’a….. juyawa tayi a fusace ta bar gurin tana takaicin hali irin na bunayya ace mutun, shi sam bai san kunya ba, wannan wace irin rayuwa ce?

    bayanta yabi da kallo yana mamakin mai yasa ummi take masa irin haka tare da d’aukarsa tantirin mara kunya, “shikenan shi sai ya tsaya yana kallo ayi masa hasarar cikinsa?

    “idan su basason cikin shi dai yana son abinsa kuma akan cikin babu abinda ba zai iya yi ba, sai dai ayi masa uziri a qalla ya kusa minti talatin a tsaye a bakin kofar muwaddat , karo na biyar kenan yana jan tsaki mai tattare da bakinciki “bai san abinda ummi take nufi dashi ba ?
    haka yagama tsayuwarsa ya kama hanyar part dinsa .

    tun daga lokacin ya sanya ido sosai akan lamarinta saboda take takenta da yake gani, so take ta rabu da cikin shi, kuma yayi biyu babu, bashi ga tsuntsu bashi ga tarko, dan haka duk inda tayi a cikin gidan idanunsa na kanta, sai dai idan bata fito ba, haka zai yi balance a parlour’n ummi wanda ke had’e da bedroom din muwaddat , yayita satar kallonta, idan yaga al’amun zata juyo sai yayi saurin d’auke idanunsa ya waske ya kama kallon wani guri, babu abinda ke sake daga masa hankali da motsa masa sha’awarta kmr yadda take karya kugunta kmr ba mai ciki ba, wannan abu na maseefar tsuma shi har ma yaji tamkar ya fixgota zuwa jikinsa, bangarenta kuwa duk abinda yake akan cikin haushi yake bata sai ta dinga jin kmr ta shake masa wuya ya mutu kowa ya huta,tun tana jan tsaki ,da gaya masa bakaken magana har tazo gabad’aya ta daina kulashi asalima sai ta shiga boye kanta a d’aki saboda bata son ya ganta bare har ya tuna mata cikinsa da take dauke dashi ,ta rigada ta Yankewa kanta halakar komai dashi tunda har yace ya daina sonta cikinsa yake so ,yadda take nuna rashin kulawarta akansa abun na damunsa matuka yana jin tamkar yayi kuka amman saboda tsabar miskilanci irin nasa ,ko a fuskarsa baya nuna damuwarsa ,yayinda ummi gabadaya tagama dagosa , ita kanta abun na bata mamaki saboda tsabar miskilancinsa bazaka ta’ba cewar shi yayi cikin ba ,kwata kwata baya shiga sabgar muwaddat yanzu ,sai dai idan yaga zata yi missbihave akan cikinsa, yanzu ne hankalinsa zai tashi sannan zai nuna kulawarsa ,har ma yayi kasa da muryarsa yace “ki dinga kula da kanki mana ,ya kike abu haka ,ko kin manta bake kad’ai bace banason kina careless da kanki irin haka fa.. ….

    **********
    Suna zaune a parlour’ gabadaya ummi abi bunayya, muwaddat ta fito daga bedroom dinta sanye cikin shigarta ta koda yaushe wato bakar abaya da hijabi madadin ta yafa mayafinta kmr yadda tasa ba, sai dai tunda cikin jikinta ya bayyana take jin kunyar sanya kayan da mayafi kayan datasa , sai ta koma d’aura hijab akai Wanda hakan bai ragewa bunayya komai daga cikin tarin kaunar dayake mata ba ,sai ma wani zallar soyayyarta dake dawainiyya dashi tun da ta fito idanunsa ke kan cikinta ya kasa d’auke idanunsa, ita kuwa ko kallon inda yake bata yi ba, kai tsaye hanyar kitchen ta nufa tana tafiya a natse kmr batason taka kasa, shi kuwa ya cigaba da kallonta ,a koda yaushe ya d’aura idanunsa akanta har bai son d’auke su, komai nata na burgeshi ,a duniya bai ga abinda zatayi da zai ji kaunarta ya bar gangar jikinsa ba ,barin ma halin yanzu da yasan tana d’auke da gudan jininsa, wani irin mahaukacin kaunarta ne ke sake ninkuwa acikin zuciyarsa dama gangar jikinsa …

    tana daf da shiga kitchen suka ci karo da zahra yar binta mai aiki ruwan dake hannuta ya zube a kasan tayis ,garin muwaddat tayi baya, aiko sansi ya ja ta ,ta tafi suuuuuuuuuu zata fad’i wani irin k’ara ta saki mai razanarwa had’e da tsoro..

    Shima bunayya Kara ya saki cikin wani irin zafin nama ya ruga a guje tana jiran ta jita tayi zubewar ‘yan bori a kasa sai jinta yi ta fad’a jikin mutun “ke baki da hankali ne ?
    “naga alamun fa bakisan ciwon kanki ba muwaddat, balle kinsa abinda kike yi , kina k’ok’arin yi min ganganci fa saboda bakisan zafin abinda kike d’auke dashi ba, na rantse da Allah muwaddah kika min hasaran d’ana ko ‘yata zanyi mummunar sa’ba miki acikin gidan nan …

    ahankali ya mike tsaye tare daita ajikinsa ,yana lalla’bata, su ummi kam mutuwar zaune sukayi suna kallon sarautar Allah.

    Muwaddat na gama tsayuwa bisa kafafunta ta fixge a jikinsa, zuciyarta tmkr zata tarwatse ,tana jin kmr ta rufeshi da duka amman babu hali ,idan da halin yin haka ma zata iya ne ? ta tambayi kanta cike da sanyi jiki ta juya tana jan tsaki shi kuma yashiga kitchen din “binta …………..”
    ya kwallawa binta mai aikin kira cikin zafin nama yana huci “wace .. wace wannan dake shirin min ganganci ?

    ” wallahi zan dagawa kowa hankali a gidan nan fa, idan ba’a yi hattara ba binta wacce jikinta ya d’auki rawa ta soma bashi hakuri “kayi hakuri ranka ya dadi yarinta ce tazo kama mun aiki, ni kaina bansan yadda akayi ruwan ya zube a hannunta ba ,yanzu haka ka gani ga mopa na d’auko zan goge da kaina..

    “bai sake cewa komai ba ya juya ya bar parlour’n batare daya kalli inda iyayensa suke zaune suna binsa da kallon ba .

    Bayan fitarsa ummi ta dubi abi shima daman kallonta yake yace “kina ganin ikon Allah ko?
    “uhmm Kai dai bari lamarin bunayya ya daina bani mamaki ya dawo bani tsoro, yaro Sam bashi da kunya ,bai San ta ido ba ,abubuwa yake tamkar bai San da zamanmu acikin gidan ba.

    “A haka ma kenan da munyi ganganci hanashi aurenta da me kike tunanin zai faru ?
    “Uhmm abubuwa dayawa kam barin ni da nace sai alameen, suka sa dariya “ai wannan take taken nasa inda ta aure al’ameen din ma ba zai barta tayi rayuwar aure mai dadi ba …

    “Oh Allah da mu biyewa son zuciya da mun shiga uku ,gashi hausawa sunce son zuciya ‘bacin zuciya, “da dai kin shiga ni dai ban da ni ,sai dai nayo tsaliliyar amaryata , “Kai hubby hannuwana duka a sama ta daga hannunta “na daina musu shishigi wallahi ,na cire hannuna acikin lamarinsu , Allah Allah ma nake ta haihuwa su tarkata su koma gidansu ..

    Abi ya numfasa “nima tuni nasoma wannan tunanin akansu , InshaAllahu abinda za’ayi kenan kowa ya huta ,saboda ni kaina al’amarin bunayya yasoma bani tsoro ,ahankali suka cigaba da tautauna yadda zasu tsara musu gidan da zasu zauna ,har kusan la’asar suna zaune ,abi ya tashi yace zashi masallaci ..

    *********
    tana kwance ruf da ciki a dakinta d’aure da towel fitowarta kenan daga bayi tayi shiru tana tunani, on expecting taji saukar yatsan hannu tun daga tsakiyar kanta har zuwa bayan wuyanta wani irin zirrrrrr taji agabadaya ilahirin jikinta take zuciyarta ta bugu saboda ko bata juyo ba, tasan dan kasadar da zai aikata mata hk, karamin tsaki taja saboda tunowar datayi bata rufe kofar ba, ta yunkura zata mike yayi saurin kamota jikinsa ita kuma ta kama towel din dake daure ajikinta, jin tumin jikinta yasa take joystic dinsa ta mike tashiga har bawa ta juyo ahankali tana dubansa ,ya lumshe mata ido “tunanin me kikeyi?
    “idan kina da damuwa ko wani guri ke miki ciwo ki fad’a dan banason rasa cikin jikinki kmr yadda zan rasaki yayi mata tambayar yana rungumeta ajikinsa shiru tayi batare da tace masa komai ,sai dai ar anta tace “ai kai ne damuwata muhammed auwal ina zaka daina damuna da batun cikin nan?
    “ni nafi cancatar ka damu dani ba wani cikinka ba..
    ta yatsina fuska “me ye haka kuma nifa banason kebewa d kai ,dan Allah kabarni na rigada na cireka a duniyata kamar yadda ka cireni , ta yunkura zata tashi ya kamota ya zaunar daita “kinsan Allah karya ne kice kin cireni a duniyarki, wallahi idan aman alquarni zaki dinga min ba zan yarda saboda da son muhammed auwal ki rayu duk tsawon shekarun nan yadda nake ji jikina akanki kema nasan haka kike ji “ni dai dan girman allah koma meye ni dai ka bar rayuwata banason wata halaka da kai…. “
    ta mike ta shige bayi da sauri tana k’ok’arin danno kofar, ya Kai hannunsa Yana lumshe tsumammun idanunsa shi kad’ai yasan yadda yake ji alokacin , kusa Kai yayi cikin bayi . ……

    mmn sudais

    MUWADDAT

    ~NA~

    *AYSHA A BAGUDO*
    ~DEDICATED TO~
    _AUNTY SALAMATU AYYUBA_
    _(UMMIN KADUNA )_

    warning!!!

    don’t read this novel if you know you are not married… ❌❌❌coz this book contains only for mature people , if you read it, is for your own risk ……

    WATTPAD @HAUESH

    bismillahirrahmanirrahim

    Note
    error: Content is protected !!