Muwaddat – Chapter Seventeen
by Aysha A BagudoYana jin ta kashe wayar gabad’aya ,ya zame ahankali ya kwanata dafe da marasa dake masa zugin sha’awa ,cikin wani irin shauki yasoma juyi akan katifarsa tare da runtse tsumammun idanunsa da suka gama canza kala tsabar jarabar dake cinsa.
kusan awa daya ya d’auka kwance batare da bacci yayi nasarar d’aukarsa ba, illa juyi daya keta faman yi rike da mara, da kyar yasamu ya yunkura ya sauko daga kan bed yashiga bathroom yayi wanka ya fito ya sake kwantawa yana rawar sanyi ,dan jin yayi tmkr wanka da yayi ma sake k’ara masa wani sabon sha’awa yayi, ranar dai kwana yayi yana watsawa jikinsa ruwa ko zai rage jin abinda yake ji,gbdy yayi week, jikinsa yasoma sakewa, numfashinsa yasoma barazanar d’aukewa dole tasa ya sake mikewa yayiwa kansa allurar kwantar da sha’awa sannan ya d’an ji dama ajikinsa har bacci yayi nasarar d’aukesa .
**********
yau tsawon kwanaki uku kenan ala’meen bai sanya muwaddat acikin kwayar idanunsa ba tunda safe kafin ya tafi aiki ,zai so ganinta amman hakan bata samuwa , idan kuma ya dawo shima baya ganinta saboda wasu lokutan da yamma tana kitchen ,ko a parlour sun daina haduwa ,lokacin da yake zuwa parlour ita kuma tana d’akinta makale da wuyar bunayya, dan haka ko yana son ganinta babu dama ,to idan kuma ya aika kiranta yace daita me ?
shi Gabadaya ma yanayinta firgitashi yake da zarar ya ganta yanxu ne gabansa zai kama faduwa ,sai daya kwashe kwanaki wajen biyar bai sanyata acikin kwayar idanunshi ba, yanzu daya sauko cikin shirin zuwa office yake tambayar eiman “wai me yasa yayarku yanxu bata zaman parlour’n, ko bacci take da wuri?
“Babu wani bacci, kawai dai tana gama cin abinci sai ta shige daki kamar mai yin bacci ,nan kuwa hirarsu suke ita da yaya Auwal a waya ..
Ya d’an zaro idanu kad’an cikin kad’uwa,acikin zuciyarsa yace hirar suke da Auwal ?
“Kwarai kuwa yaya ala’meen, ai sau tare idan kaji tana waya to dashi ne wani lokacin har da dariya zakaji tana yi ,wannan zantuttukan nata yasa ya fahimci ba a zuciyarsa yayi maganar ba azahiri yayita “ai sai ma ka ga yadda suke ji da junansu,, cikinsu duk Wanda bai ji muryar Dan ……
A matukar fusace ya buga mata tsawa “dan Allah malam ban tambayeki duk wad’an nan bazanye surutan ba ,tambaya daya na miki sai wani zuba kikeyi kmr ruwa ,ke kam mijinki nada aiki yana gama fad’ar haka ya juya afusace..
Tabi bayansa da kallo tana ta’be baki “maseefaffen kawai ,ince Kaine ka tambayeni ,ni kuma yazama lazin na fayyace maka komai, idan ma surutu ne ubanwa ya koya min ?
Dubeshi sukai sukai da wuya kamar lagwani ..
ta karasa maganar tana kwashewa da mugun dariya ..
“Yayan kike zagi ,da yiwa dariya haka ?
Taji muryar ihsan daga bayanta “tayi murmushin “ke munafukarsa to ni ba zaginsa nayi ba …
“To me kikayi idan ba zaginsa kikayi ba?
“Nafa ji duk abinda kika fad’a Dubaishi sukai sukai da wuyansa kamar.. ai da sauri eiman ta matso gaban ihsan ta rufe mata baki “haba yar’uwa so kike yaji ya markad’a min duka ?
ihsan ta cire hannuta a saman bakinta “ai wallahi gara ya lallasaki saboda baki da kunya “to kiyi hakuri yar gaban goshin d’anta na daina …
A ranar bayan sallar magariba hisham ya ziyarci ala’meen suna samansa suna tautaunawa hisham yace “ni kuwa ina bakuwar gidanku muwaddat madam fa ta dameni da maganarta ..
Al’amen yayi murmushin takaici yana yatsina fuska “ai nima da muke gida daya ba ganinta nake yi ba …
“Malam cewa zakayi baka so ganinta ba .”wallahi idan dai har zaka yarda yau kwanana biyar kenan ban sata a idona ba ,nima hakan na damu daita Wanda bansan dalili ba gabadaya tunaninta yaki barin zuciyata ta huta ..
Hisham ya buga masa harara “banason maganar banza so dai kawai kake kace min ka fara sonta cikin murmushi ala’meen yace” kusan haka ne ni ban ta’ba tunanin wata yarinya a zuciyata ba sai wannan karon daren jiya fa har kasa bacci nayi amman duk da haka bakaji yadda nake jin tsoron shiga harkarta ba domin na gane take takenta tana da wulakanci..
hisham ya numfasa had’e da cewa
“Abokina ka cire zance wulakanci ai ko tana yi nasan bazata iya yi maka ba ,abinda nake so dai kai, in dai da gaske kana sonta,to kabita a sannu ku saba daga nan sai ka fara nuna mata soyayya, ka tabbata kafin ta koma garinsu ka dasa soyayyarka a cikin zuciyarta ,ala’meen ya sauke naunayen ajiyar zuciya tare da cewa “shikenan sai dai akwai wata matsala fa “
“Ta me kenan ?
“Akwai yaron gidan da’ake rokonta a can,in takaice maka shakuwar dake tsakaninsu tayi yawa , ni sai nake ganin kamar soyayya suke ,duba da yadda zasu d’auki tsawon lokaci a waya suna hira ,kuma idan kaga dariyata ko maganarta da shine, wannan abun na matukar d’aga min hankali fiyye da tunaninka “
“Zancenka zai iya kasancewa gaskiya zai kuma kasamcewa hasashe ne kawai saboda shakuwa babu abinda baya sawa ,sai dai ai last time danazo ai na gansa, ko bawani yaro fari dogo mara kiba mai doguwar fuska da saje mai shegen miskilanci ba ?
“Shine d’an iskan yaro da bai ganin kowa da mutunci in takaice maka har ya gama kwanakinsa a gidan nan kallo arziki ban ishesa ba balle gaisuwa yaro k’arami ya d’auki girman kan tsiya ya d’aurawa kansa, kodan yaga ubansa wani ne oho ?
“Hakan ma zai iya zama sila amman ni yanzu abinda nake so da kai tunda abun yazo hk, ka samu goggonka ka tuntu’beta, kafin kasoma bayyanawa ita yarinyar soyayyarka, idan akwai wani abu a tsakaninsu sai ka janye ,karka soma bayyana mata soyayyarka ace an rigaka kaga kai babu yadda zakayi tunda wata kusan tafi wata “ala’meen yace ‘shikenan zan yi haka amman ni sai naga yaron kmr zai wa muwaddat kad’an a batu na soyayya, sai dai idan saurin ido zai yi..
“Kai dai ba wannan bace damuwarka domin kasan namiji baya kad’an a soyayya ko aure idan tana son shi sai kaga anyi musu aure, an jisu shiru ,kafin wani lokaci ya tirka mata ciki. ala’meen yayi saurin runtse idanunsa saboda d’acin kalmar yana daga masa hannu “ya isheka malam ka daina hasasho wannan rayuwar tsakaninsu, kwakwaluwarka ta hasko maka ni ne zan aureta har ma na dirka mata ciki hisham yasa dariya yana nunasa “wallahi ala’meen baka da mutunci yanzu dai kiri kiri ka’ajeye latifa a gefe “ai kama sheida ne ban ta’ba sonta ba kawai darajar Goggo hajara ne , bazan iya cewa mahaifiyarta banasonta ba ,saboda amintakan dake tsakaninsu amman ni Sam Sam ban ta’ba jin ina son latifa araina ba, “shikena yanzu yaya kenan za’a yi, ni gashi madam tace na karbar mata number muwaddat..
Cikin rawar jiki ala’meen yace bari na kiraka maka faiza sai ta sada ka da ita ,ya fiddo wayarsa ya kirata tana d’auka yace” ki turo min muwaddat da ihsan yanzu ina son ganinsu …
Hisham ya dubeshi “ni da ka hado da eiman na sha dariya ,tare da cewa abokina ni fa ina son ihsan gara kasani ,tun yanzu ina riko tunda kayi min kwacen babbar to zan koma Kan karamar ..cikin Dariya ala’meen yace “kai tafi can babban banza yar kawar tawa danake ji daita zan d’auka na baka alhalin kafin aureta yazo , zakama mata tsufa, Dan bana jin nan da shekara Goma za’a aurar da ihsan saboda akidar son boko da dady yake da ,idan kaji yadda dady yake zuzuta sai sunyi boko sosai sai kayi mamaki ..
“Okay a she dai zaku aurar daita din komai dadewar ,ai na d’auka sai dai ku dinga jikata kuna sha ,sukayi dariya a daidai lokacin da ihsan ta shigo parlour’n had’e da sallama tana gama shigowa eiman ma ta kunno kai da sallama ta d’an kalli hisham tana fara’a ,tace “eye yaya hisham dinmu lallai kana jin dadi har wata kiba da kasuba ka fara ajiyewa, abun yabasu dariya gabadaya al’ameen ya had’e rai yana duban ihsan “ke wace kizo min da wannan shirmamma.. “wallahi yaya bansan ta biyoni ba kawai nima yanzu na ganta “
eiman tace “a’a karkaga laifinta yayanmu batasani ba ,na biyota dan kar ayi ban dani Dan tunda naji ka kira aunty faiza nasan tasamu ne ,sannan ta juya ta kalli hisham had’e da shagwa’be fuska tace yaya hisham “wai tambayar danayi maka akwai shirme aciki ?
“Rabu dashi mun fi kusa ni dake kinsa bata baci atsakaninmu, yanzu manta da wannan yayan naki yaushe zan zo in kai ki kiyiwa minal yini ?
Tun kafin ta sake cewa wani abu al’amen ya Mike ya korata waje da gudu ta arta tana dariya har da rike ciki ya kalli ihsan yana huci “,ina muwaddat ?
“Tana d’akinta yayi shiru na wasu sakwani sannan yace me takeyi ?
“Gaskiya ban dai sani ba amman bari na duba, ta juya ta fita da sauri ta sauka kasa d’akin muwaddat ta nufa bata sameta aciki ba sai kawai ta nufi parlour’n dady tana ganinta tace “aunty muwaddat wai inji yaya ala’meen kizo ku gaisa da yaya hisham muwaddat ta d’an bata rai “Anya kuwa ni yace miki “kwarai kuwa ke yake nufi muwaddat tayi shiru kmr bazataje ba sai hjy hajara ta galla mata harara ba shiri ta Mike, ita ba gaisawa da hisham bane bata so kawai d’akin ala’meen din ne bata son shiga d’an tunda tazo bata ta’ba yin hanyar bangarensa ba ,amman yau dayake babu yadda ta iya da ranta haka nan ta nufi hanyar tana yin sallama ta yaye labulen parlour’n tashiga..zazzakar muryarta ta doki kunnen ala’meen yadda muryarta ta ratsa jikinsa ko daga bacci ya tashi muryar bazata bace masa ba ,gabadaya suka had’a baki suka amsa sallamar datayi kafin ta gama shigowa kamshin turarenta duk yagama shige musu hanci gabadaya hatta parlour’n ma ya gauraya da kamshinta ,ala’meen dake kishinged’e ya d’an lumahe idanunsa ahankali kana ya bud’esu akanta suka d’an kalli juna kafin daga baya ta kawar da fuskarta hisham na nuna mata gurin zama ta gaishesa sannan ta zauna cikin fara’a kad’an bazakace itace take zagewa da Auwal su raba dare suna zuba surutu ba ,da kyar ta sake bud’e bakinta tacewa hisham” ya gida da madam ?
“madam tana nan lafiya tace a gaisheku suka d’an yi shiru batare da sake cewa komai ba kusan second biyu hisham yace “malama muwaddat me yasa kika da wuyar gani gashi baki son mutane ?
Yanzu da ba Dan na tura a kiraki ba har na tafi bazamu gaisa ba kenan? Murmushin gefen baki tayi “kaga kuma ganina ba wahala garesa ba amman ga Wanda bai kama kansa ba zai wuya ya gani sannan batun rashin son mutane, ni mutane masu shegen surutu ne banaso..
“Al’amen ya jefa mata wani irin kallon da shi kansa bai San yayi hakan ba ,nan Dana ta tamke fuska tana sake kawar da kanta gefe hisham ya cigaba.
hisham yace “shikenan na fahimceki “minal tace ki d’aure ki sake kawo mata ziyara acikin zuciyarta tace “ita idan ta matsu tana son ganina why not tazo ,amman a zahirance cewa tayi InshaAllahu zanje “Kamar yaushe kike ganin zakije ?
Ta yatsina fuska had’e da cewa” babu rana gaskiya amman ina da niyyar zuwa ,sai lokacin ala’meen yayi karfin halin cewa karka yarda da zanceta makaryaciya ce da sauri ta kallesa cike da matsanancin mamakin tare da tsaresa da fararen idanunta “yaushe wannan ya fara atsakaninsu da har zaice mata makaryaciya? kalmar datafi tsana kenan a rayuwarta sai gashi a karon banza a kirata dashi, hisham yayi saurin cewar karyar me tayi maka ?
“Ranar da mukaje gidanka muna dawowa gida sai naji tana bada labarin karya wai taga gidan sarkin garin nan taga gidan gwana kai har gidan zoo tace munje ….
sukayi Dariya hisham yace “ina laifi data kareka.
“ta dai kare kanta dai nasan tayi haka ne Dan kar gaba a sake tursasata fita..
Muwaddat ta d’an Mike tsaye saboda shirmensu ya fara cika mata kunne dole daman tasan hisham zai kasance kmr ala’meen gurin zuba tmkr ruwa ,tunda sai hali yazo daya abota kan zo daya ..hishsm yace “ya kuma kika tashi ana hira ?
“Ni zan koma ciki idan kaje ka mika min gaisuwata gurin madam”
Ala’meen ya fahimci shi take son ta gujewa saboda kallon dayake mata hisham yace “amm madam fa tabani sako a amsar mata number wayarki a she Ranan nan har kuka rabu baku amshi number juna ba muwaddat tace “mantawa muka yi saboda hira ta d’auke mana hankali anan take ta gaya masa number ya shigar dashi cikin wayarsa yace “baki gaya min sauran lambobinki ba dan naji ance layuka uku gareki cikin yatsina fuska tace “ka manta da sauran tunda za’a iya samuna Akan wannan layin ,hisham yace “haba muwaddat ina ganin ko mutun yana rowar number baya yiwa kawarsa ba ,duk yadda yayi muwaddat ta tsare gida ta hanna sauran number’s dinta Wanda tabashi din ma ta karamar wayarta ce datake amsa kira Wanda abi ya tsiya mata ,wai saboda koda cajin babbar wayar ya kare, Dan bayason yakirata bai sameta ba ..
shi kuwa hisham Dan dai yajata da hira sai cewa yayi “ke din da nake son ki zama surukata sai gashi kun kulla kawance da daman ..
Da sauri tace wace irin suruka kuma ?
“Au baki da labarin ina rikon ihsan ko?
Cikin dariya tace “da dai faiza kace me yuwa na Dan tsaya maka tunda ita ihsan ai uban gidanta na hannun damanka ne ..
Hisham ya jiyo ga ala’meen dayazamanto tamkar sauna a zaune yana kallonta “,kai maigidana kaji abinda surukata ta fad’a….
Ala’meen yayi murmushi yace “,ai ina ganin ko ita surukar taka a halin yanzu bata isa aure ba bare aje ga faiza ko ihsan, hisham yace “haba babban yaya karka raina min hankali mana kawai saboda ba’ason bani kanwa sai kuma ace yaya ma bata isa aure ba ,kina jinsa dai big sister ya fad’a tare da kallon muwaddat.
Ta d’an kawar da fuskarta gefe “eh to abinda ya fad’a gaskiya ne, sai kaje kayita jiran lokacin idan kaji zaka iya “kenan idan na fahimci ki kenan kin goya masa baya akan maganar sa na cewa kema baki isa aure ba ballanata kanwarki?
Ta sake had’e rai “wannan ai maganarku ce ni dai na tafi ka gaida gida tana shirin fita daga parlour’n sai ga eiman ta biyota da wayoyinta big sister an damemu da kiran wayarki muna cikin kallo an hanamu jin gari ya Auwal yakira wasu ma duk sun kira ni dai nace musu kina d’akin yaya ……….
Cikin matsanancin jin haushi muwaddat tace “,to d’an me zaki biyoni da waya d’akin mutane ,ko ance miki dadewa zanyi ,Muje gani nan saukowa eiman na shirin fita aka sake bugowa ta juyo da sauri “to ga Auwal nan ya sake kiranki .
Cikin tsawa tace dan rashin da’a kai tsaye kike kiran sunansa bako rusunawa ?
Bata amshi wayar daga hannunta ba har kiran ya sake katsewa “oya maza ki koma da wayar idan na sauko zan kirasa ..
“Ni gaskiya ki amshi wayar a hannu , ni yanzu meye laifina bayan agabansa bazan kira sunansa kai tsaye ba “ki ma yi kiga yadda zai yi kaca kaca da namanki Dan kinsan shi baya d’aukar shirme ..
eiman ta marairace” murya big sister Dan girman Allah ki taimaki rayuwata ki amsa kinga na rigada na d’auka da farko ,kinsan Halinsa zai d’auka ban kawo miki bane …
Gabad’aya daga muwaddat din har eiman a tsorace suke ita eiman najin tsoron kar idan yazo yaci ubanta, Dan bai mantuwa, sannan bai yafiya duk dadewar Abu zai hukuntaka akansa, sai dai idan yagadamar Kyaleka, ita kuma muwaddat rashin sanin abinda zata fad’a masa idan ta ashi wayar take, cikin haka ya sake kira “kin gani ko big sister ya sake Kira Dan girman Allah ki rabani da wayar nan .
Ala’meen kasa d’aurewa yayi yace “shi din waye da baza iya amsa wayarsa anan ba ?
“Batare data juyo ba cikin tausashiyar murya kmr zatayi kuka tace “auwal kanina ne fa, sannan ta amshi wayaoyinta ta bar d’akin cikin ‘bacin rai , itama eiman sai lokacin ta saki ranta ,tana sakawar a’lameen murnushin Wanda za’a iya kiransa,Dana mugunta …
Hisham ya juyo ya dubi ala’meen “ina ganin fa yarinyar nan ta gane kana son yayarsu “kai haba bana ji wannan shirmammiyar yarinyar zata fahimci wani abu ,ita kanta uwar gayyar batasani ba .
“Kana son kace min ita makauniya ce shiyasa bata lura da irin mayataccen kallon da kake yi mata ba ko? Sannan me ka fahimta a yanzu da aka kawo mata wayoyinta ?
“Na fahimci kmr tashiga firgice gabadaya dai ta tsorata “shine abinda na gani gaskiya ka tashi tsaye kar hasashenka yazamo gaskiya,kar yaron yazo yayi kuli kulin kubura da kai akasa..
hisham ya k’arasa mgnr yana dariya ala’meen yace “Allah ma bazai sa ba InshaAllahu rabona ce …
Hisham ya Mike ” to Allah yasa, nima bari tafi Dan na fara tunanin madam Dina nasan tana can tana jirana ala’meen ya hararesa nima dai zanyi madam Dina kodan rashin mutuncin da kake min babu ikon ayi cikakkiyar hira da kai sai ka tsiri cewa madam na Jira .
“to ai gara ni da matar tawa ma ina fitowa kai fa tunda bakuwar gidanku tazo aka daina ganinka ,ai ina jin duk ranar daka mallaki yarinyar nan ,an daina ganinka gabadaya suka kwashe da dariya har da tafa hannu sannan suka Mike tare suka sauko zuwa kasa al’amen yayi masa rakiya ya shiga mota ta tafi shi kuma ya dawo gidan har zai hau samansa sai yaji hayaniyar kannensa acan bangaren dady , sai ya tsinci kansa da nufar bangaren ba Dan komai ba sai Dan ya kalli muwaddat yana shiga ciki ya iske gabadaya yaran gidan suna ciki hjy hajara tacel kardai abokin naka ya tafi tun ba’a kai muku abinci ba yace mumy “ai kinsa halin hisham in da yana son ci da kansa zai tambaya..
Idanuwa yashiga budewa yaga ta inda zai ganta ,babu ita babu alamarta a parlour’n Dan haka ya juya ya wuce ya koma samansa hankalinsa a matukar tashe saboda yasan watakilla tana can tare da Auwal a waya
Ilai kuwa abinda zuciyarsa ta kissima masa ne ke faruwa acikin d’akin muwaddat, domin kuwa fad’a ne sosai yashiga tsakanin Auwal da muwaddat ta inda yake shiga bata nan yake fita ba “Dan wulakanci da iskancin banza me ya kaiki d’akinsa ?
Kika bar ni ina kiran wayarki how many hours “wato kin fi damuwa dashi akaina, ke wai ma meye atsakaninki da shi ,?
“waye shi da bazaki d’auki wayata agabansa ba?
“Ni ina nan an tsareni ganina,gani wawa bansan abinda nakeyi ba ke kuma kina can kina shirme da katon banza , Dan haka gobe goben ki shirya zan zo na d’aukoki ki dawo gida zuciyata baza iya d’aukar nauyi nan ba, gara kina kusa dani daman nasan saiko ake son yiwa rayuwata shiyasa aka tsiro da zuwanki wannan hutun ..
“Kema dayake kinsa mugun nufin dake ranki shiyasa kika yi zamanki, bakya ko tunanin dawowa maza daman tun da wuri idan ma sonki yake kice masa kina da miji Dan wallahi babu mai auren ki matukar ina raye ya karasa mgnr yana furzar da iska ..
shiru tayi har yagama balainsa batace masa komai ba …
Gashi kuma dai suna rike da wayar ,yadda bai yi yunkurin cewa daita komai ba haka zalika Itama bata ce masa komai ba, illa Kunar zuciyar da take, hakika Auwal yayi bala’in rainata wannan wulakanci ko iyayen da sukayi silar zuwanta duniya a yanzu basa mata fad’a irin haka ballanatana shi datake masa kallon kani gareta amman babu Wanda ya janyo wannan tozarcin kamar ita itace silar faruwar haka ta bashi abinda bai cancaci yagani ba ,banci haka tasan babu yadda zai dinga yi mata irin wannan matsefar kamar wani ubanta ..
Ganin tayi shiru taki cewa komai ta barshi shi kadai sai balai yake yi yasa yaja dogon tsaki har sai data yi saurin cire wayar a kunnenta ya fillingin da wayar akan gado batare daya kasheta ba ya sauko daga Kan gadon ya fito kai tsaye part din ummi ya wuce yana shiga ya isketa zaune ita kad’ai tana kallon labarai sallama yayi aciki sannan ya haye sama inda d’akin mahaifinsa yake ,tabi shi da kallo duk yadda akayi ransa a bace yake “,to waye ya bata masa rai ?
Ta tambayi kanta tana runtse ido ,kamar ta Mike ta bi bayansa sai kuma ta fasa tasan da matsalar data shafeta ce dole zai tsaya gareta Amman tunda ya nufi gurin mahaifinsa a sauka lafiya …
A bakin kofar abi ya tsaya yana kwankwasa kofar abi dake cikin d’akin yana duba wasu mahimman takardun kasuwancinsa yace” waye ?
Muryarsa can cikin makoshi tamkar bai so ta fito tace “.ni ne “abi najin haka yasan kowaye Dan haka ya bashi umarnin shigowa ya tura kofar d’akin yashigo da sallama aciki ,abi ya d’ago ya dubesa yana nazarinsa kallo daya yayi masa yasan yana tattare da damuwa kuma duk abinda ya kawoshi a daidai wannan lokacin mai mahimmanci ne, Dan haka ya tattara takardun dake zube agabansa gefe ya nuna masa gurin zama “ka zauna fatan dai kana lafiya ?
Muryarsa tamkar Wanda zaiyi kuka Dan ma dai nmj duniya ne, kawai ya waske yace “,abi kana son nayi yawanci rai a duniya ?
Da sauri abi ya gyara zama yana girgiza masa kai “,kwarai kuwa Auwal meyasa zaka fadi irin maganar da tasanya gabana faduwa?
“Akan muwaddat ne abi ina sonta kuma da aure, wannan shine karo na karshe da zan furta hakan gareka ka aura min ita ka daina duba kankantar shekaruna, ni aure nake so a halin yanzu “abi ya numfasa yana cigabada dubansa yana nazarinsa tabbas yana hango gaskiyar abinda ya fad’a Amman ta yaya kamar Auwal zaa ace zaa aura masa muwaddat ?
Amman saboda ya kwantar da hankalin yaron yace “shikenan zan duba lamarin sai asan abun yi “zuwa yaushe kenan zaka nemeni kan mgnr, saboda ina son muce tare da ita ne?
“abi yabi shi da wani kallon mamaki kafin daga baya ya kira sunansa “bunayya kasamu natsuwa nace zanyi wani abu akai “bunyya ya ciza gefen lips dinsa kad’an yace “abi to kace ta dawo gida hakan nan nasan kun tura can ne saboda ni ,to wallahi idan bata dawo ba komai zai iya faruwa dani .
ya kamo hannunsa ya d’aura daidai saitin zuciyarsa “abi kaji bugun da zuciyata take ?
“Abi ya runtse ido saboda yaji yadda zuciyarsa ke bugu fastly “shikena zansa ta dawo gobe InshaAllahu zanyi waya da alhji Muhammud yanzu kaje ka kwanta kasamu natsuwa ..auwal ya Mike tsaye yana layi tamkar wani mashayi ya nufi hanyar fita..
Muwaddat page 20
October 23, 2020 Muwaddat Complete
bismillahirrahmanirrahim