Muwaddat – Chapter Forty-one
by Aysha A Bagudo.Alhamdullahi mu dat na samun kulawa matuka
daga bangaren ummi, duk abinda take so shi take mata
,sannan duk abinda ya dace mai ciki taci ko amfani dashi
shi ummi take bata
Sai da aka samu tsawon wata guda cur da rasuwar yaya
akram ,sannan bunayya ya bayyanawa su dady labarin
halin da Yaya akram ya tsinci kansa a dalilin rashin auren
days so yi suka hana , har ma da labarin yaransa dake
kasar Spain ,wannan dalilin ne yasa ya kamu da ciwon
zuciya , bai tsaya iya nan da ba har sai daya labarta
musu irin nadama da yayi da tuban da yayi kafin
mutuwar ta riskeshi
“dan haka shi ya yanke shawarar cikin satin zai Shiga
kasar ,koda kuwa baza’a bashi yaran ba, amman at
least dai yasan wani abu daya danganci akram ,mu
musan inda ahlinsa suke
Hankalin dady kusan yafi na kowa tashi a lokacin tunda
bunayya ya soma mgn yake kallonsa tamkar hoto ,ya
kasa kwakwarar motsi ,gabadaya so yake yaji
zantuttukan bunayya sun zamo tamkar a mafarki ne
suke Shiga cikin kunnuwansa, Amman yadda bunayya
din ya Shiga fito da hotuna akram da yaransa da polina
yana nuna musu ,daya daga cikin hotunan a bircth
sukayi , wasu a wuraren shakatawa wasu a gida
suna dry
cikin farinciki ,varan masu tsananin kama dashi sosai,
basu d’auko komai na polina ba sai Karin hasken fata.
da kyar dady ya samu ya dinga furta kalmar “inna lillahi
wa inna ilaihi rajiun yayinda tuni parlour’n ya kaure da
kuka ,Kowa kuka yake mumy cikin kuka tace “duk son
zuciyarka ne ya jawo haka….
Kasa na rasa d’ana a dalilin banzar ra’ayinka ,yaro ya
nuna maka aure yake so amman ka kekashe kasa kace
Sam sai ya gama karatu , ai ga irinta nan kasa an haifa
min jikoki ta hanyar zina .
kuma a wata kasa wallahi
Muhamud ka cutar dani ,ka cuceni cutar da har na mutu
bazan manta ba
‘ummi ta Mike daga inda take ta isa inda mumy take
zaune ta rungume akin kuka tace “kiyi hakuri aunty
zuwaira , haka Allah ya kaddaro kowa da irin kaddara da
Allah yake masa
,ki d’auka wannan jarabawarmu ce ,sai fatan Allah ya
bamu ikon cinyeta ,kiyi hakuri gabadayanmu muyi
kuskuren, “,dole nayi kuka mukarama ,saboda nima na
biyewa son zuciyarsa ,na mance ni macece ,yanzu ina
zan samu kmr akram?
“yaushe zan haifi d’a kmr akram ?
“a koda yaushe yana k’ok’arin kyautata min da yi min
biyayya ,Allah dai ya gafarta masa yasa ya huta ,yasa
karshen walahar kenan ,Allah ka hadasshi da malaikun
rahma ,ya Allah kamar yadda kace aljanna yaya maza
suna karkashin tafin kafafun iyayensu to ni Allah
kagani na d’agawa akram tawa kafar , kasa aljannah ce
makomarsa ta k’arasa fad’in hk tana wani irin kuka
“a lokacin da maganganun mumy ke Shiga kunnuwan
dady ,ba iya kunnensa kad’ai maganar ta tsaya ba, har
zuciyarsa yake jin komai, kusan zaucewa yayi, ya dinga
sambatu “shikenan ni na kashe d’ana da kaina, tun
da’akayi mutuwar bai zubda hawaye ba ,sai na zuci
,Amman yanzu hawaye ne kwance a saman kuncinsa
gabad’aya, ya dawo abun tausayi ,wuni ranar babu
Wanda ya sakawa cikinsa komai kowa ka kalli fuskarsa
(3
ta kud’e saboda kuka
Allah sarki mumy kwana tayi ranar da zazzafan zazzabi
ajikinta ,Sam ta kasa runtsawa jin mutuwar akram take
sabuwa agareta
,dana sani kuwa tayi shi sau babu adadi ,tayi nadamar
biyewa son zuciyar mijinta ,shine duk ya janyo komai
yayi tsanani a gareta, tabbas akram yaro ne mai ladabi
da biyayya, ba zai ta’ba bijire umarninta bare na
mahaifinsa ,”danasani na amince masa a lokacin dayazo
da batun yana son yayi aure .
da yanzu ya’yansa zasu zame min sanyi idaniya a gareni
, kallonsu kad’ai zai rage min rad’adin rashinsa, bazan
sakawa ranna soyayyar ya’yansa na wata uwa duniya ba
,domin kuwa da wuya uwarsu ta bari ta gansu shikenan
bazataga jikokinta ba ?
Tayiwa kanta tamvayar,
wasu hawaye masu zafi suka zubo mata wannan
zazzabi bai hanata tashi cikin dare tayi alwala ta Shiga
sallah tana nemawa d’anta rahma gurin Allah
Akwana daya dady yayi da wannan labari ,ya dawo abun
tausayi ,Dan idan ka kalleshi sai ka tausaya masa ,Dan
kuwa yayi kuka tamkar k’aramin yaro, har wata doguwar
Rama yayi gabad’aya ya fita haiyacinsa , surutui ya koma
yi ,kallo day’a zaka masa kasan baya cikin natsuwa da
kwanciyar hankali, daman kuma dauriyar mutuwar kawai
yake Amman a yanzu komai ya dawo masa sabo, har sai
da mumy tazo tafi shi dauriya da tawakalli har ma daga
karshe ta dawo bashi baki ,ummi ma tayi iya kokarinta
dan gani ya samu natsuwa tare da bashi tabbacin za’a
zo da yaran ,dady yayi wa kansa alkwarin ba zai sake
takura ya’yansa akan karatun boko ba haka zalika
yaransa mata duk aure zaYi musu ya hutawa
rayuwarsa….
Su ummi basu dawo Lagos ba sai bayan da akram yayi
wata biyu ,lokacin cikin muwaddat ya Shiga wata na
takwas ,tun da suka dawo muwaddat bata sanya
bunayya a idanunta ba, yana can yana fama cikucukun
Shiga kasar Spain , sai data samu tsayin wata daya
sannan ya zo mata da labarin tafiyarsa ,zuwa kasar span
, shi da yaya alameen acikin satin tabbas taji dadin
kwarai da gaske ,sannan taji rashin jin dadin kartazo ta
haihuwa baya nan, sai dai ta nuna bata damu ba sosai ,
saboda gudun kar ya gane ya rusa tafiyar ,yace har sai
byn ta haihu ,ita kuma abinda ba zata so kenan yaya
ba,yaya akram ya wuce komai agurinta ,yafi komai a
rayuwarta ,sanin inda yaransa har uku suke shine
farincikinta
Yau tsawon kwana Goma da tafiyar bunayya amman ko
sau daya basuyi waya dashi ba ,tashiga damuwa sosai
har damuwarta ta fito fili, kullun ummi na kwantar mata
da hankali Wanda hakan ya rage mata tsananin tunanin
rashinsa kusa daita ,hakan ba karamin dadi yakewa
muwaddat ba gani yadda ummi ta sake maidaita yar
gata ,bata aikin komai kayan data Cire sai dai a wanke
Wanda zata sakawa jikinta ma sai dai ta gansu ,komai
ummi ce ,shi yasa kullun take jin ummi ta zarce matsayin
uwa gareta, ta zame mata komai na rayuwarta ,yanzu da
ta gudu tabi uwa duniya a wannan ranar yaya rayuwar
zatayi ?
‘Allah nagode maka da ka arzurta ni da samun uwa kmr
ummi ,allah ka ja da ranta, ka kara Mata Nissan kwana
,samun irin su da wuya a wannan lokacin…
Tana kwance a d’akin ummi saboda gyaran d’akin da
zaayi ,karar wayar dake gefen gadon ummi ce ta tasheta
daga baccin daya soma d’aukarta mai dadi ,cikin tsaki da
yatsina fuska ta d’auki wayar ta manna a kunneta tare da
fad’a “Assalamu alaikum “daga can bangaren aka amsa
mata da waalaikas salam ,tana jin sautin sanyayyiyar
muryar tasan sanyi idaniyanta, burin zuciyarta tsayayen
namiji abun tikaho, nmjin dake shirin tafiyar da rayuwarta
da komai nata, Muhammed Auwal kenan cikin sanyayyiyar
muryarsa yace “na tasheki a bacci ko ?
Bari na kashe kar NASA ki Haifa min yaro mai mannen
ido tunda NASA shima baby bacci zai yi, ya fad’a cikin
farinciki “Kamar kasani har ma da yankakken kunne tayi
maganar cikin muryar shagwa’ba “sorry love banyi zaton
kina bacci ba, ganin rana ce a fuwa zuciyata, ya baby nah
ki fad’a baby kar yayi fushi yanzu ummansa zata koma
bacci yayi hakuri inzo inganshi da kunnuwansa da
idanuwansa ,suka sa dariya ,”kai bunayya bakagajiya da
soyayya wallahi ,ya bakunta da fatar kunyi nasara?
Baki ai sun kusan dawo wa ,to dai da dan nasara zance
,domin dai an sanar mata da komai tayi kukanta ta
hakura, batun zuwa da yaran ne kam babu sauki, wannan
sai dai zuwa wani lokaci idan sun girma kenan..
Ni dai zanyi k’ok’arin ziyartasu akoda yaushe, saboda su
sani su shaku dani, shine kawai hanya mafi sauki da
zanyi domin sadasu da sauran yan’uwa dan bakiga
macen ba muwaddat wallahi kmr kece kika haifeta ,sak
kamarku day’a sauran mazan kuma yaya akram Allah dai
ya jikansa “ameen tayi mgnr tana goge hawayenta “ba
kuka zakiyi ba muwaddat mu godewa Allah ,dayasa ta
fahimcemu, bata takaryata cewar ba yaransa bane da
me zamuyi ?
Muna nan dawowa cikin satin nan, nafi son ki Haifa min
baby nah ina nan ,ina son ganin haihuwarki ,naji ihun
first nit dinki zanso naji na haihuwa, shi Kuma kowa za’a
Kira?
Suka sa dariya gabad’aya “bunayya kenan har kasa na
harareka a waya “kai kai to ina dawo kuwa sai na biya
kudin harara da kudin da bazasu kirgu ba tasan irin
kudin da yake nufi ,dan haka ta’ajiye wayar kawai
Yau ta kama ranar dawowarsa tun asuba ummi tasoma
shirya masa abinda zasu ci idan sun sauka ,ita kuwa
muwa at tayi wan ata gyara ji inta ta awo turarru a
tabi jikinta dashi domin shirin tarbo mijin abun har yaso
yabawa ummi mamaki ashe datayi k’ok’arin aurar da
muwaddat ga wani , tabbas da tayi kuskure ,maganar
abi daya ce da zasu bi junansu ,yanxu ma da basu tare
ba, suke bare bare, ina ga sun koma gidansu , kusan
tafisu matsuwa tana gama shiryawa tashige cikin
Bargon ummi tare da kashe fitila d’akin ta kwanta wani
bacci mai dadi ne ya d’auketa
Karfe takwas da rabi na safe taji tashin sautin muryarsa
a daf da shigowa d’akin ummi tayi saurin juyawa kofar
baya a dole bacci takeyi .
Tana jin shigowarsa har da mayar da kofar ya rufe da key
a zuciyarta tayi dariya shi kuwa har wani sanda yake wai
kar motsinsa ya tadata ahankali ya haye gadon ya zauna
daidai inda ta mayar da fuskarta .
Take zuciyarta tashiga dokawa ta dinga kokuwa da
numfashinsa, lokacin dataji ya sumbaci lips dinta ,ya
gangaro zuwa cikinta shima yayi masa kiss tare da Dan
shafawa alamun ko yana cikin koshin lfy ,sai lokacin ta
bud’e idanunta Dan kar ya zarce daga hkn, dan tasan
hali, ita dai kam sai dai tabawa wani labarinsa ,ahankali
ta tashi zaune tana yatsina fuska ,ya matso kusa daita
sosai ‘Sannu na tasheki ko ?
Kafin tace wani abu ya rungumeta ajikinsa yana murnar
ganinta da kyar ta samu tarabata da jikinsa ya kamo
yatsun hannuta “,ya baby nah ?
Ni na isa, ayi min afuwa ya kike kin tashi lfy?
Lafiya lau ya kuka baro min yarana fatan duk suna cikin
koshin lfy?
“Alhamdullahi duk suna lafiya kmr mu barosu har
airport suka rakomu su da mamansu abun tausayi .
Yana maganar yana shafa fuskarta zuwa cikinta cikin
minti ashirin tasoma jin bakon alamari na maganarsa da
ta canza salo zuwa wasanin daita, ta soma
Biye masa sukayi Amman acikin minti talatin taji
bunayya na neman canja akalar wasa ,hakan yasa ta
nuna masa alamar ba’a wasa biyu alokaci daya a kare
lafiya ,amman take ya nuna mata shi mai iya wasa kala
hudu ne a lokaci day’a, amman wannann wasan shima
bazai iya ba adaidai wannan lokacin burinsa bai wuce ta
haihu su tare a gidansu ba, ta tsura masa ido tana jin
yadda soyayyarsa ta dawo mata sabuwa fil ta kai bakinta
ta sumbaci fuskarsa,” ina sonka mijina, kmr ta tsira
masa allura yayi wani firgigib ya cakumota ya kwantar
ajikinsa ‘bunayya wai meye hk ?
Sone aunty nah
Bai barta haka ba sai daya auratayya daita ,iya murzuwa
ta murzu a hannunsa .
Wuraren misalin karfe tara na safe taji jikinta yana mata
ciwo iri iri’ Amman hakan bai hanata hirarta da ummi ba’
da binta mai aiki ba’ hkn kuma bata sanarwa da kowa ba
har ta Mike tashige dakin ummi ta kwanta Cikin baccin
Clwon mara a, al sa onu u a uguntaya ama ara
da wani juyi ,baccin da bata koma ba kenan
Cikin minti Goma sai gata a tsaye ciwo yayi tsanani
wauta irintata, sai ta kwanta Amman ciwo ya gagara
zama bare kwanciya
cikin haka marata tayi wani irin Murd’awa ta saki wata
razananniyar kara sai ga ummi tashigo a guje kmr zata
fad’i tana ganinta tasan abun yazo.
ta fita da sauri tsawon minti biyar suka shigo tare da
bunayya, lokacin har faya ta fashe Sam ummi batasan ya
biyota ba “,me haka bunayya ?
Ko kulata baiyi ba ya ykarasa da sauri gurin da
muwaddat take durkushe tana ciza lebe babu kunya
bunayya ya kamota yana shafa gashin kanta zuwa
bayanta ” sannu kuwa yayi mata yafi sau Goma sha
gabadaya amatsayinsa na likita kasa aiwatar da komai
yayi ,ummi tace tashi ka fita waje kabarta taji da Abu
daya
da kyar ya bar d’akin ya Shiga kai kawo atsakanin d’akin
da parlour’n Amman har lokacin shiru babu labari aiko
ya sake shigowa yayi zaman Durshan agabanta, ita kuwa
tuni ta manta da sha’aninsa ,har ma da ummi sai kiran
sunan Allah take ,da yan adduo,i ummi ta fita cikin sauri
ta sake dawowa da sauri tana bashi umarni ya fita ,shi
kuma sai magiya yake mata kada a barta ta mutu ,ummi
ki taimaka mata mana , mata dayawa gurin haihuwa
suke mutuwa .
“dan Allah ki taimaka karta mutu kalle yadda take shan
wahala muje hospital “ko hospital din mukaje iya abinda
zan iya mata kennan, yanxu ta soma nakudar fa sai zuwa
nan da awa biyu zata haihuwa “inna lillahi wa inna ilaihi
rajiun ya furta awa biyu ummi ?
‘Ta Dan daga masa kai kawai ,ai awa biyu tazo ta wuce
shiru da tafiya tayi tafiya ta Dan bud’e idanunta sai
ganin bunayya tayi zaune a gefen gado yanata faman
goge hawaye
Muwaddat bata haihu ba ai data gama shan wahala,
zuwa lokacin hatta ummi hankalinta ya tashi ,shinkuwa
bunayya ma ya daina kuka ya zuba mata ido yana jiran
yaji ance ta mutu domin ya sadaukar da mutuwa zatayi .
Wuni zirrrr tayi durkushe tana abu daya Sai karfe Goman
dare ta haifo yaronta nmj , acikin jinin da take tsugunne
bunayya ya rarrafo ya rungumeta ajikinsa, yana mata
sannu ,ya dinga furta sannu har sai da ummi ta rufe
masa baki saboda yawon sannun dayake mata sannan
ta d’auki yaron tayi bayi dashi.
Da bunayya duk akayi aikin jini, sai da aka gama gyarata
tsab ya ganta lafiya sannan yake tambayar ummi abinda
aka Haifa ummi ta d’auko masa yaron ta mika masa .
“Gsky Muhammed Auwal bashi da kunya ,lokacin da ya
d’auki yaron sai ya soma murmushi yana cewa “aunty
muwa kalleshi kiga da wa yayi kama dani ne ko?
Ummi tace “oho ni yasu wannan yaron na rasa ina
kasamo wannan rashin kunyar ,oya tashi maza ka bar
d’akin nan, ‘haba ummi karki min haka mana Dan Allah
,ke daya kamata ki tayani dubawa da wa yayi kama
shine zaki koreni “,ungo nan jairin mara kunya kawai ,da
ubanka yayi kama ,maza tashi ka fitar min a d’aki
bunayya ya saki murmushi sannan ya tashi ya fita
Yana fita yashiga sheidawa abokansa zance haihuwar
da’akayi masa, yana murna, sannan ya d’aura a duniya,
saboda jin haihuwar yake tamkar amasa albishiri da
gidan aljanna.
,cikin awa daya kira suka dinga shigowa wayoyinsa da
sakonni ,duk Wanda ya kira yayi masa barka sai kaji
yana masawa da ameen ameen ,abunsa har ya daina
ba wa ummi mamaki
Da daddare ummi da mai binta mai aiki ,suna zaune a
parlour’n suna hirarsu ,ita kuwa muwaddat tana d’akinta
ta tasa jaririnta gaba ta tsura masa idanu tana kallon
kyautar da Allah yayi mata Wanda ko da wasa bata ta’ba
tunanin zata iya samun ba
soyayyar yaron ne ke fixgarta ,ta sauke ajiyar zuciya, ta
Dan gyara zaman domin kara gyarawa yaronta kwanciya
ahankali yashigo d’akin ya zauna akan kujera ya kura
mata ido yana kallonta ‘ke ma kina son baby ko ….?
Tayi murmushi kawai sannan tace “Ni fa ban iya abinda
ka iya ba
Ya matsota sosai yana aika mata da wani tsumammen
kallo “wani na iya dake baki iya ba?
‘ ,duk abinda na iya ,kin iya fiyye dani , dukkanin mu
muna son baby nan but ki tattara soyayyarki ki ajiye gefe
saboda nawa yafi naki “tunda Kai ka min na kudar ba ?
‘Ko ban Miki nakudar ba ,na tayaki rabi suka dariya .
Ranar safiyar suna yaro aci suna Ibrahim wanda
bunayya ne ya zabi sunan,ba’ayi wani abu daya
danganci bidia ba bunayya ya bukaci a bashi matarsa su
tare agidan da abi ya gina masa ,amman ummi tace ya
bari tayi koda kwana arbain ne
“A daidai wannan lokacin akayi biki al’ameen da faiza
,inda amarya ta tare a gidan da dady ya mallakawa
al’ameen ,faiza dai ta rungumi kaddarar auren a’lameen
ne kawai ba dan ranta yaso ba,amman asalin soyayyarta
naga bunayya ,daman kuma haka duniya take ,ba komai
kake so, kake mallaka ba ,sai abinda Allah ya ga damar
baka ,Wanda hakan shine mafi alkhari
Byn shekara biyu
Ibrahim Wanda ake kira da akram yayi girman ban
mamaki saboda kulawa da gatan da yake samu agurin
iyayensa da kakaninsa ,domin wata irin soyayya suke
nuna masa na fitar hankali inda ummi taso kwarai su bar
mata shi ,Amman kememe bunayya yaki yarda ,kullun sai
saka ranar kawo shi yake, Amman yaki har ummi ta
fahimci bai son basu yaron ne , ta hakura sai dai duk
weekend din duniya a gidan ummi yakeyinsa…shima Dan
ya samu damar sakewa da muwaddat ne
Sosai muwaddat take bawa yaronta kulawa tare da taka
tsansar aikata wani abu akan idanunsa ,duk da
kasancewarsa yaro karami bata yarda su aikata wani
abu akan idanunsa, koda kuwa kiss ne sai bayan
idanunsa, idan yana gidan ummi kuwa cin karensu suke
babu babbaka iskanci iri iri bunayya na biye mata
Mmn sudais ce
MUWADDAT