Muwaddat – Chapter Forty
by Aysha A Bagudo..dady da mummy sun shiga matsanancin tashin hankali, mutuwar akram ta gigitasu ,gigita mai tsananin, zuciyoyinsu suka nemi daina aiki tsabar rikicewa.
gabad’aya rige rigen shiga office din likinta sukayi ,jikinsu na tsuma tsabar tashin hankali da suke ciki, anan ma dai sake tabbatar masu da rasuwar akram likita yayi kusan zaucewa mumy tayi ta dinga wani irin kuka mai rikitarwa da ta’ba zuciya, tun cikin daren suka soma kiran wayar yan’uwa da abokan arziki, shi kuwa bunayya yana rungume da gawar yaya akram, har asalatu , ya kasa sakinsa duk yadda dady yayi dashi ,kuka kawai yake kamar wani zautacce wannan ne karo na farko da mutuwa ta ratsashi ,ta ta’ba zuciyarsa da komai nashi, mutuwa ce da ba zai ta’ba mantata arayuwarsa …ya rasa yaya ,da’nuwa ,amini, abokin shawara ‘jigo mai mahimananci arayuwarsa , “wa zai samu ya maye gurbinsa a rayuwa ?
**********
washegari aka basu damar d’aukar gawarsa bayan sun saka hannu kasancewar haka dokar asibitin take, koda aka iso gida, da gawar akram gidan ya cika makil da mutane, mak’ota da abokan arziki ummi ma tuni suka biyo jirgin safe, yaran gidan sunata kuka har da burgima ,duk wanda yazo sai ya tambaya ko daman bashi da lafiya ne?
ace “eh yana dai rashin lafiya a tsaye tsaye bai dai kwantar dashi ba, wasu na ta mamaki mutuwarsa, saboda mutane dayawa sun ganshi daren jiya , har karfe goma na dare yana tare da abokansa suna hira a kofar gidan .
Bayan an shirya akram zuwa gidansa na gaskiya, aka kiran iyayensa domin yi masa addua,mumy dai wannan lokacin tayi dauriya sosai sai dai har lokacin ta kasa tsaida kukanta akan mutuwar d’anta , muryarta na tace” Ibrahim na yafe maka duniya da lahira ,ibrahim baka min komai ba a tun tasowar, haka zalika har girmanka, baka ta’ba sa’bawa umarnina ba,”duk abinda nake shi kake min babana na yafe maka , Allah ya jikanka ya sadaka da malaikun rahma ,Allah ya gafarta maka yasa mutuwa Hutu ce gareka ya k’arasa addu’a wasu zafafan hawayen rashi d’anta ya gangaro mata ,yanzu shikenan ta rasashi ya tafi ya barta batare daya bar Mata abinda zata dinga tuna shi ba …?
shima dady haka yayi masa addua , tare da sumbatar gawarsa dukkaninsu babu Wanda bai sumbacesa ba, suna danne hawayensu saboda malamai sun hanasu kukan da suke ,tare da nuna musu illar kuka ga mamaci bashi da wata amfani , mamaci addua yafi bukata ba kuka ba ..
Sannan aka soma k’ok’arin d’aukar gawar ibrahim akram domin kaishi makwancinsa na gsky ….
Ai gama d’aukar gawar ke da wuya muwaddat na mikewa ta saka wata razananniyar k’ara mutane sukayo kanta suka ririketa, amman bata daina ihun kiran sunan yaya akram ba ,cikin kuka faiza tazo inda take ta riketa ” aunty muwaddat ki bar kuka haka, muyi masa addua adduarmu yafi bukata …
,Amman ina sai yunkurin kwacewa take daga hannunsu tana wani irin kuka kafin daga bisani numfashita ya tsaya cak ya daina aiki alamun ta suma,nan aka kwasheta zuwa d’akinta na gidan.
Dan d’akin mumy Makil yake da jama’a, sai alokacin wasu daga cikin dagin mumy suka fahimci abinda ake ciki game cikin muwaddat ,take ummi ta dibo ruwa cikin roba tashiga yayyafa mata, dogon ajiyar zuciya ta sauke hawaye na sake gangaro mata “shikenan sun rasa yaya akram ?
“shikenan ya tafi ya barsu bazai dawo ba ?
Take gefen kanta yayi wani irin mugun Sarawa ,ummi tace “ki kwanta ki huta kinsa bake kad’ai bace ,ta gyara mata kwanciyarta” ni zan koma cikin mutane idan kina bukatar wani abu ki kirani “kai kawai ta iya d’agawa ummi hawaye na bin kuncinta, kana ta lumshe ido , ummi ta fice daga d’akin.
ta barta tashiga cikin mutune amsar gaisuwa har dare muwaddat na d’aki babu Wanda yabi ta kanta ..
Duk wannan abun da’ake hankalin bunayya na kanta ,har gurin tara bai ji motsinta ba,ya tambayi ihsan nan take fad’a masa ai bata da lafiya, tun sanda aka fita da gawar yaya akram tana d’akinta ,
Yayi shiru ,can yace “je dubo min jikinta ..
Tace “to ta juya tashiga gidan jim kad’an ta dawo da sauri tace “kamar fa har yanzu, Dan naga sai rike ciki take ..
“Okay kawai yace ya tashi , ya zagayo ta baya wajen window d’akinta, saboda mutane dake parlour’n ,yasan muddin ya ratsasu ya wuce sai ummi taga laifinsa , ,nan ya hangota kwance sai murkususun rike cikinta take ,hankalinsa yayi mugu mugun tashi ,take ya lalubo wayarsa ya kira layin ummi, sai da yayi kira kusan Goma sannan ta d’auka ya sake yi mata gaisuwa sannan ya sanar daita halin da muwaddat take ciki .
Cikin sauri ummi ta Mike jikinta na rawa ko gama jin abinda zai fad’a mata batayi ba ,ta rad’awa mumy abinda ake ciki sannan ta fito ta nufi d’akin muwaddat ta iske ta zaune ta had’a uwar gumi tana rike da cikin tana junjuya kai “ta k’arasa da sauri ta dafa kafadarta “,muwaddat lafiya ?
“Mai ke damunki ?”wani guri ke miki ciwo ?
Tayi mata tambayar a rud’e hankalinta a matukar tashe “ummi cikina ….mutuwa zanyi “inna wa inna ilaihi rajiun “ciki kuma ni yasu ?
Tashiga girgiza mata kai “tashi maza muje asibiti , “a’a ummi bazan iya tashi ba ,”ki d’aure muje kinji , ahankali ta yunkura zata tashi ummi na rike daita Amman sai ta koma ta zauna tana ciza bakinta, ganin haka yasa ummi tasoma duba ta domin gano inda matsalar take , dan dai tasan cikin bai isa haihuwa ba, bare tayi tunanin ko nakuda ce ,saboda har yanzu cikin bai wuce wata shida ba, ummi takira bunayya a waya ..
Haka ya dinga ratsa mutane Dan har lokacin mutane na zaune ,yayinda wasu sunyi bacci ,wasu kuma idanunsu biyu suna dannar zuciyar mumy dake zaune rike da carbi a hannunta.
jam’i yayi gurin yin gaisuwa, suka amsa gabadaya ,wadan da suka San abinda ya faru suka shiga nunawa sauran yan’uwan da basu sanshi ba , “ai shine yayi wa muwaddat ciki ,wata daga cikinsu tace “Dan wannan yaron ya iya dirka mata ciki “?
“Ya wuce wai tunda ga zahiri nan kingani ajikinta daga baya a wayance da an musu aure ….
haka suka bishi da kallo har sanda ya isa bakin kofar ya tsaya yana kwankwasawa, ummi ta bud’e masa,yana Shiga yasoma tambayar ummi ” ummi meke damunta?
” ina tace miki yana mata ?
ya k’arasa kusa daita ya rike hannuta “fad’a min ina ke miki ciwo muwa ?
“,da kyar tace ci..ai ko gama ji bai yi ba ya sureta zaiyi waje daita , ummi ta dakatar dashi “kai ajiye min yarinya ina zaka kai min ita?
Muryarsa a raunane yace “haba ummi kina ji fa tace cikinta ke ciwo ?
“nace ka’ajiye min ita Ka fani sonta ne ?
“ko kuwa kafini bukatarta a raye ne?
Ahankali ya maidaita saman gado ya kwantar yana jin kmr ya saka kuka ,ummi tace “damuwa ce da fargaba tayi mata yawa har ya janyo mata wannan ciwon Wanda idan batayi hankali ba , za’a iya rasa bby .
“Dan Allah ummi ki taimaka kar na rasa baby nah ….yayi mgnr muryarsa na rawa yana k’ok’arin sake rike hannun muwaddat ,ita kuma ta fixge tana zabga masa harara tace “,wallahi da zan rabu dashi da har abada bazan manta wannan lokacin ba, “ni ummi Dan Allah ki rabani da cikina nan na huta na gaji dashi , bana iya baccin kirki bani da kwanciyar hankali duk motsin da zanyi sai ya takura min yanzu bakiji yadda nake ji ba kmr na mutu….
“ummi ki cire min wannan jarababbe ciki wallahi idan na mutu ke kad’ai akayiwa hasara ta k’arasa mgnr tana fixgo numfashi da kyar iya gaskiyar ta fad’a saboda rad’ad’i azabar da take ji a kullun kwanan duniya ..
wani irin kallo bunayya ya bita dashi kmr ya rufeta da duka ,”hakuri zakiyi mamana haka duk wata take ji yayin rainon cikinki wata yazo mata da sauki wata Kuma haka zata yi ta fama har ta haife abinda ke ciki..
“kingani ai shi Wanda yayi cikin ma bata rayuwarki yake ba shi ta abinda ke cikinki yake , kuma ko mutuwa kikayi ni dince ke da hasara shi wata zai samu ya aura ,” yanzu dai kaje ka siyo min allura da wannan magani ,ta fad’a masa idan aka d’auki lokaci zata soma blending idan haka takasance sai dai kayi hakuri da cikin …..
Da sauri ya juya cikin sauri ya fita yashiga mota sai wani pharmacy batare da ‘bata lokaci ba ya siyo maganin ,ya dawo ya kawo mata,yana tsaye ummi tayi mata allura Amman har lokacin wani haushin muwaddat din yake ji saboda tsanar cikinsa da tayi .
babu laifi muwaddat ta Dan samu saukin ciwon da take ji har bacci yayi nasarar d’aukarta ..
karfe uku na dare ta farka a firgice saboda matsanancin ciwon da marata da kugunta ke yi, haka yasa ta dinga laliban abun kunna makunin wuta dake gefen gadon, ta yunkura ahankali tashiga ba bayi,wata firgitar tayi ta mike tsaye da sauri daga zaman fitsari da tayi akan farar tukunyar bature ta fito babu shiri, zaman datayi a gefen gado tayi imani baxai ta’ba yaye mata damuwa da fargaba tattare da tashin hankali datake ciki ba, ta mike ahankali ta samu wani k’aramin towel tayi kuzugu dashi gudun kada jini ya kai ga ‘bata mata jikinta.
ahankali ta samu ta dinga takawa ahankali har ta fito daga d’akinta gabanta na sake fad’uwa da karfin gaske, tasoma tafiya cikin sanda tayi bayan gida ,ko daya bata ji wani ciwo ajikinta ba saboda tsoro da tashin hankali data tsinci kanta ciki alokacin data ga jini ya maye gurbin fitsari, wannan shine sanadiyyar firgita datayi tare da fitowa daga d’akin domin isa ga uban gayya, tun kafin cikin ya gama fita daga jikinta, dan bata manta kamalaman ummi ba , “matukar ta soma belliding komai na iya faruwa ,ciki kuwa har da rasa babyn cikinta , ita kuwa idan ciki ya fita yaya zatayi da jarabar bunayya?
tasan ko kashe zai iya yi akan wannan kadararren cikin ….. …
cikin ikon Allah koda ta karasa d’akin kwance ta sameshi akan doguwar kujera ,ya had’e hannayensa duka yayi pillow dashi idanunsa na kallon celling d’akin, yayi shiru da alamun har lokacin yana cikin jimamin mutuwar yaya akram ne, wanda itama har lokacin bata daina jin rad’adin rasa d’anuwata datayi ba.
tunda tashigo hankalinsa gabadaya ya koma kanta ya kafeta da tsumammun idanunshi yana kallonta cike da tashin hankali dan take zuciyarsa tashiga bugawa tana aiyano masa abubuwa da dama akan shigowarta .
tsayawa tayi tana dubansa kamar yadda yake kallonta, “ya zame mata dole ta karaso garesa tun kafin lokaci ya kure mata ta shiga uku, hakan yasa tacigaba da daga kafafunta ta k’arasa inda yake kwance wanda jin hkn ma bazai ta’ba yaye mata damuwar da fad’uwar gabar da take ciki ba, ahankali taga ya kawar da kansa gefe nan take jikinta ya kama rawa amman duk da hakan da yayi bai hanata isa garesa ba ,tana isa ta tsugunna a gabansa kawai tayi imani yana jin durkusonta amman ko juyowa da kanshi bai yi ya kalleta ba , kara daurewa tayi ta dafa gefen cinyar hannunsa tare da furta “bunayya “meye ki tafi ki kwanta kawai … ya fad’a batare daya juyo ya kalleta ba dan zuwa lokacin zuciyarsa ta gama tabbatar masa da lafiya take wani abun ne daban ya shigo daita, a take a gurin sauran karfin gwiwar dake zuciyarta ya kare sai dai kawai hawaye taji sun tsiyayo akan kuncinta .
cikin karfin hali tace “bunaya jini…. “
“what ?
ya furta da karfi tare da mikewa zaune “me kika ce?
bata iya sake furta komai ba sai dai kife kanta datayi ajikin kujerar tasa masa kuka..
d’agota yayi tare da girgizata da karfi “ki fad’a min mana me naji kin fad’a yanzu?
“ina magana kinyi min shiru “jini da gaske kike kuwa?
“da gaske jini aiko ya saketa a gigice ,yayi shiru tareda dafe kanshi da hannayensa biyu…
tashi yayi ya fice daga d’akin hakan ba k’araminn tayar mata da hankali yayi ba, ta mike da niyyar binsa amman sai marata ta d’auka, dole tasa ta koma ta durkushe agurin saboda wani azababben ciwo da take ji, sai dai ta damu sosai da rashin ko in kula daya nuna mata , kusan minti goma sannan ta iya dan daddafawa ta mike tsaye amman duk da hk sai taji ta kasa d’aga kafafunta.
dole tasa ta koma ta zauna, zaman ma gagarata yayi sai gata ta zame kasa ta kwanta ita kanta bata san tsayin lokacin data d’auka tana birgima ciwon da tayi wa lakabi da ciwon mutuwa ba,acikin wannan halin taji shigowarsa ya d’auketa.
sam batayi tunanin bud’e idanunata ba saboda ita kanta ba zata iya d’aukar nauyin bud’esu ba, babu abinda bunayya bai yi mata ba, yaga ciwon ya daina haka jinin ya tsaya amman ko saukin ciwon bata daina ji ba..
dole ya d’auke zuwa wani hospital, ita dai tun daga nam bata sake jin komai ba ,sai kara motocin da suke wuce duk da idanuwanta arufe suke hkn bai hanata jiyo hayaniyar tashin muryayin mutane daban daban ba , bata tabbatar da inda take ba sai da taji tsinin allura ya rasa fatar hannunta sannan ta tabbatarwa kanta asibiti ya kawota kwana likitoci sukayi akanta da kyar aka samu jinin ya tsaya ..
********
tana bud’e idanunta babu abinda ya gane sai wani madaidaicin agogon bango dake tsaitin gadonta karfe uku daidai na rana ta gani batasan iya awani ko kwanakin datayi a kwance ba tasan dai tajima a hospital.
babu wanda yazo daga cikin dangi mumy sai ummi dake tare daita,Dan har lokacin haushin abinda aka yiwa al’ameen suke ji ,ganinsu duk yaudararsa akayi , Allah sarki ummi da ita ya zame mata dole itace ke faman zariya akanta , dady shima da abi duk sunzo,sai dai kallon fuskokinsu kadai zai sa ka fahimci suna cikin rad’adin rashin Yaya akram ..
kowa yazo sannu yake mata ita kuwa wani irin kunya ne yake dawainiya daita, shi kuwa uban cikin batasan yaushe rabonta dashi ba dan tun da farka bata sanya shi a cikin idanunta ba har bisa ga wannan lokacin, nan take ta fara tunani ina yake?
“koda fushi yake daita akan laifin da ba nata ba?
sai zuwa yamma can sai gashi yashigo hannunsa rike da lododi ya matso kusa daita sosai yayi mata sannu muryarsa can kasa kasa kmr mai tsoron yin magana .
cikin sanyi murya ta amsa masa “da sauki shiru ne ya biyo baya can ta katse shiru ta hanyar cewa “bunayya kayi hakuri dan Allah da furucina, bai ce mata komai ba ya d’aga kanta ya d’aura saman cinyoyinsa sannan ya sunkuyo ya sun baci kumatunta.
“ki daina bani hakuri dan Allah ,abinda nake so dake kiyi hkr mu rungume cikinmu , ba fa shege bane kamar yadda mukayi tunani tun farko ,a gabanki komai ya faru baa bayan idanunki ba ,ke din mamata ce ta sunnah ,yau ko cikin shege ne ai Kya rungumi kaddaramana dole,bare babu ko daya ..
“Ke da ya kamata ki zaki kara godewa allah lokacin da cikin ya bayyana , na tsaya tsayin daka akan lallai cikina ne , na jajirce akan nawa ne, ida nace bani nayi cikin ba fa yaya zakiji a lokacin ?
“kiyayyaki da cikin nan ko rashin son shi bashi zai sa idan allah yasa rayayye bane yaki zuwa duniya ba. nida muhammed auwal ina sonki da cikina, kuma a shirye nake da cin uban duk Wanda ya shegenta min shi da cewar bamu da aure …….
idan kuma har yanzu baki bukatar rayuwa dani ne idan kin haifa min cikina ki bani abinda kika haifa kowa yakama gabansa dan banga amfani tarayyata dake ba…
akwai mata dayawa da suke bukatata ,nace sai ke ,kinga sai nasamu daidai dani na aura na huta da salo, nayi nisa da rayuwaki dana d’ana watakilla ma bazaki sake sanya mu cikin duniyarki ba..
hawaye suka gangaro mata haka nan yau din nan take jin kaunar abinda ke cikinta ,wannan cikin shi zau kara ninkin soyayyarta a zuciyarta bunnayya, ta sani yana sonta soyaya mai tsanani da wuyar samuwa a wannan lokacin, zuwa yanxu yakamata ta rungume mijinta tinda iyayensu sun tabbatar mata da auren nasu..
cikin sanyi murya tace “shikenan na yarda na amince nima ina son abinda zan haifarmaka, yayi yar dariya tare da lakace mata hanci”abinda zaki haimana dai ni da ke ta d’an rufe idanunwanta alamun kunya, shigowar ummi yasa bunayya ya d’aga kanta dake kan cinyarsa ya d’aura akan pillow ,ya mike yana sosa gefen wuyansa wai shi kunya, wanda ita ya barwa kunya tunda gbdy ta kasa bud’e idanunta, sharewa ummi tayi ta nuna bata ga komai ba , ita dai Allah Allah take ta haife cikin tana jikinta ,ko suna baza’a yi ba ,zata aunasu gidansu suje can su karata , dan ba zata sake barin a sake auno mata wani cikin agidanta ba gara su tafi gidansu suje su karata..
kwanata uku aka sallamota suka dawo gida aka cigaba da karbar gaisuwa …
******
Mutuwar akram ta doki kowa acikin dangi ,hankalin bunayya yaki kwanciya har lokacin ,zuciyarsa taki sabawa da mutuwa da rashin akram, tausayin rayuwar yaransa yake ji, ko yaya Polina zataji idan labarin mutuwarsa ta risketa?
“shi ba ma wannan ba, yaya zaiyi ya sanarwa iyayensu wannan labarin ?
“sannan yaya zai gano inda polina take ?
Yasan dai ko yaganta da wuya ta basu yaran ,Amman at least dai yasan inda jini yaya akram suke rayuwa …
D’akin yashiga zagaye daga baya ya soma binciken kayan yaya akram ko zai ci karo da wani abu daya danganci Addresse din polina, Amman bai ga komai ba ahankali idanunsa ya sauka akan wayarsa dake yashe can gefe ya k’arasa ya d’auka yana dudubawa anan yaci karo da numbobinta har guda biyu ,yasoma kira number Kira daya ta d’auka kmr zatayi kuka cikin harshen tsadadden turancinta tace “hello my everything I have been calling your phone for five days, I hope you are doing fine?
runtse idanunsa bunayya yayi sosai, cike da tausayawa sannan yace mata “yana lafiya yayi wata yar karamar tafiya ne ,Amman shi dan’uwansa ne zaizo Spain kwanan nan ,a ina take ya bada sako akawo mata ita da yaranta ?
“tayi shiru da kmr bazata sake yin magana ba ,sai dai taga bai dace ba, tunda gashi da number’sa ya kirata idan bai da halaka dashi akram ba zai bar masa wayarsa ba ,muryarta a sanyaye tace “ya sunanta acikin ‘yan’nuwansa ?
Kundinbala yayi yace “Muhammed Auwal aiko ta sauke naunayen ajiyar zuciya tace “bunyaya …?
Da acikin faricikin yake tabbas da sai ya dara saboda yadda ta kira sunansa Amman sai ya ciza lips dinsa kawai yace “right that’s my second name ,Dan haka tayi murmushin ta bashi full details dinta, ajiyar zuciya ya sauke sannan yashiga tambayarta yaranta da ainihin sunan da mahaifinsu yake kiransu dashi, nan ta sake sakankace tare da amincewa da lallai d’anuwan akram ne kuma na jini ..
*Sauran page 2 labarin muwa ya kare , muwaddat zai yi ending a 46 ,so kuyi min hakuri da page 44 , banason ganin complete muwaddat a waje yana yawo ,dan girman Allah kumin hakuri saboda nasan wasu daga cikinku zasuji babu Dadi aransu,Nima ba haka naso ba,sai dai Ina da dalilina nayin haka*
Mmn sudais ce