Maleeka Malik – Chapter Twenty-two
by NadminMASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
Malika taga Fitan Joda da sauri Abun sai ya bata dariya,ganin tana dariya ne yasa ya dagota yana kallonta Tunkafin yayi mgana Malika tace”Joda ce ta Fita da sauri..”
Ido ya ware yana kallonta kafin ya kalli kofa yana Fadin”Wai dama ku biyu ne adakin nan..? Yafada kai tsaye yana shafa gemunsa,Dariya yabama malika sai da dan dara,Kumatunta ya shafa yana Fadin”Eh mana,dole na tambayan kinsan ke kadai nagani..”Mirmishi ta sakarmai kafin tace”,”Ai tama Fice Abunta,Sannu da zuwa..”Yana zama gefen gado yace”Yauwa ya hanya? kun dawo lafiya,ya karin hakurinmu..?
Yake Fada yana rikota bai mata mazauni ako’ina ba sai akan cinyarsa,Yana zaunar da ita,Kanta na kasa ta zauna tana Fadin”Mungode Allah..”Kanta ya aza bisa faffadan kirjinsa yana Shafa kanta yake fadin”Allah yajikan Daddy da rahama yasa yana kyakyawan mtsayi..”Da Ameen ta amsa muryanta asanyaye
Sun dade ahaka kafin ya tada ita zaune ledan Takeway din dayazo dashi ya dauko yana riko hannunta yake Fadin”Muje falo,na gaisa da joda,sai kuma naje nayi taking shower ko..?gyada mai kai tayi kafin ta rike hannunshi gam,su Fice daga Dakin yana rike da ita….
Joda na zaune suka Fito mikewa tayi tana dariya take kara gaishe da Saleem,ledojin hannunshi ya mika mata yana Fadin”Yauwa Hajiya Joda,barka da zuwa garin zamfarawa,Kiyi hakuri fa dazu ban ganki ba,kinsan Abunda akace amanace gareka toh dole sai ka kiyaye,kinsan Malika amana take awajena,shiyasa idona ya rufe bana ganin kowa sai ita..”Ba Joda kadai ba hatta malika sai da ta murmusa,karban ledan Joda tayi tana Fadin”Eh lalle naga alama,gaskiya acigaba da kularmana da Amanar Daddynmu muna son haka..”Tafada tana yar dariya
Mirmishin yake yayi yana Fadin”Au kema kin bada goyon baya kenan,? Da hanzari Joda tace”Sosai ma..”Kada kai yayi kafin yace”Toh Allah bani ikon Kula da Amanar taku,ammh itama yar Amanar naku bata jin mgana,tacika taurin kai..”Yafada yana kallon Malika adage,hannu daya kuma yana Sosa dan sajensa,Dariya Joda tayi tana kallon Malika data shagala da kallon Saleem saboda yadda yayi mata kyau cikin Uniform dinsa na kakin yan sanda😂
Taimakama Malika yayi ta zauna bisa kujera kiss ya sakarmata a goshi kafin ya mike yana Fadin”Let me go and take Shower na dawo kinji..? Gyada mai kai tayi kafin tace”Toh…”bai kara mgana ba ya juya cikin takunsa na isa ya nufi dakinsa,daidai sanda wayarsa dake aljihu ta dau Tsuwan Neman agaji,Tana gani ya ciro wayar daga Aljihu yakara akunne daidai sanda yake Tura kofar dakinshi ya Shige tanajin sanda yake Furta”Amin Afuwa Madam..”
Wani Yam taji acikin ranta,Nan da nan Zuciyarta suka raya mata abar sonshi ce Ta kirashi ma”ana amaryanshi,wani takukin abu takeji yana mata wayau bisa kirjinta,har sai da wasu siraran hawaye suka zobomata tayi hanzari sanya hannu ta share tana kokarin daidaita kanta,lokacin dataji sawun tafiyar Joda wacce ta Fito daga kichen dauke da Filet din data Juye musu abincin da Saleem ya taho musu dashi.
Waina ce da miya sai Ferfesun kayan ciki,wanda shi din nema malika taci ba laifi tasha ruwa takoma tana maida Numfashi,itako Joda wainarta taci takoshi tanayi tana kallon katon talabijin dake Falon inda ake haska Shirin akushi da rufi daga Tashar Arewa24,tuwon Shinkafa ake koyawa nan da nan Joda tace”Anty malika gaskiya yakamata bayan kin haihu ki zage ki koyi girki ba dadi ace kullum ya Saleem na bisa hanyar Restaurant zuwa Siyo abinci alhalin kowa yasan yana da mata..”
Tafada tana kallon Malika,wacce tayi zuru ta kurama Talabijin ido,Abunda Joda ta fada gaskiya itama tayi wannan Tunanin ammh rashin wanda zata fadamawa ne yasata tayi Shuru da bakinta,ammh Tunda har Joda tayi mgana bari tace wani abu,Cikin sanyinta na kullum tace”Tabbas hakane Joda na dade da wannan Tunanin araina,arayuwata na rasa abubuwa dadama daza”ace mace ta gari ta mallakesu,shiyasa Mallam zai kara aure..”Tafada tana Sharan kwallah,Ido waje Joda ke kallonta kafin tace”Wani mallam din..? Malika na kallonta tace”Saleem…”da hanzari Joda ta tsame hannunta daga Filet din wainar datakeci tace cikin tashin hankali..”Ki bari don Allah,? Wlh bansani ba yaushe zai yi auren? kuma wata yarinya ce..?
Malika na Yamutsa fuskar takaichi tace”Karki ga laifinshi Joda wlh yayi kokarin sosai,samun Namijin da zai zauna dani Awannan zamanin wlh irinsu sunyi karanci,Bansan yaushe bane bikin ammh kamar Ummi tacemin wata uku akasa yanzu kuma da gayamin za’a kai wata Tunkafin rasuwar Daddy..”Tafada cikin rauni,Cak joda ta Dauki Filet din wainarta ta maida kichen taje ta wanko hannayenta tadawo falon kusa da Malika ta zauna tana Fadin”Anty Don Allah kidaina damuwa,Kinga Fa halin dakike ciki,kada kibari wannan mganar tasaki cikin damuwa..”Mirmishin yake Malika tayi kafin tace”Kinga na damu ne Joda? ni tsorona Daya yadda rayuwata zata dawo acikin gidan da zarar mallam ya samu nasarar auren wacce yakeso..”Zuru Joda tayi mata da ido kafin ta sanya hannu ta dafa kafadanta tana Fadin.
“”Wlh bazaki Wulakanta ba Anty malika,haba aiko yadda yaya Saleem ke miki dagani yana cikin mayen sonki ne..”Idon Malika na maiko tace”uhmm haka kike gani dai,ammh babu soyayyata acikin ranshi sai dai tsausayi da kuma girmama girman Amanar da Daddy ya barmai..”Wani Shu’umin Mirmishi Joda tayi kafin tace”Haba Anty malika Kifa daina gaddama akan wai yaya saleem baya sonki…? Ai tsausayi shine ginshikin Soyayyaha,Tunda dai yana tsausayinki toh ina mai tabbatar miki da cewa yana Sonki har cikin ransa..”Tabe baki Malika tayi batayi mgana ba,sai ma ta yunkura ta mike tana mikama Joda Filet din Ferfesun kayan cikin data ke ci tana Fadin”Sakamin shi A fridge gobe da safe zanci..”Mikewa joda tayi tana Fadin”Toh Allah ya kaimu,ammh yakamata kima yaya Saleem mgana ayo cefene sai na dinga girkawa ni,ya huta yawon siyo abinci..”.
Malika na tafiya zuwa hanyar dakinta tace”Ki mai mgana mana..”Tafada cikin Kufula saboda harta Saleem din saboda kishi haushinsa takeji yanzu,Da kallon tsausayi Joda ta bita kafin ta kada kai zuwa kichen tana Fadin”Insha Allahu Anty malika zaki Farinciki arayuwarki,domin nima sai inda karfina ya kare na ganin kinyima sauran mata zarra agidan mazajensu.
Shiko Saleem yana Shiga daki yafada gado suna cigaba da waya da zahra,wacce ke mai kukan Shagwaban Tun jiya ya manta da ita,shi dariya ma ta bashi,tana wani sangarta duk don ta burgeshi,shiko acikin ranshi yana Fadin”Duk sangartanki naga Malikata😂,ammh azahiri sai ya biyemata yana lallashinta da bata bakin tarinka hakuri dashi tasan yanayin aikinshi ko yayarta ta gidama hakuri take dashi Tunda tasan yanayin aikinshi,Zahra batasan dalili ba daya ambaci Malika sai taji ranta ya baci,ta alura akomai akace sai yace Malika kaza,abun na bata haushi Duk da ta riga tasan yadda badakalan aurensu ya faru,wanda abaya taso ta taso mai da mganar tana tambayanshi,Daure mata Fuska yayi yace kada ta sake tafara Shiga hurumin da ba nata ba,bayason rainin hankali sam,kuma a yarda ya nuna mata,bazai dauki ta raina mai malika,don zata samu matsala babba ma kuwa itako Zahra arawan kanta tagananin Malika bata da wani anfani wajen Saleem Tunda ya aureta ya saketa adaren Farko,sai daga baya ne ya dawo da ita,akwai ko ahaka tayi mata zarra😂🤔
Dakyar ta bari yashiga yayi wanka ya Fito bayan ya dauro alwala yazo yayi sallar issha’in data Subucemai,Shafa’i da Wuturin daya sabayi yau baiyi ba saboda nacin Zahra kawai biyemata yayi saboda sun kwana biyu basu wayar dare ba,koda Ranar ma sama sama suke mganar,Hira suke tasha tana bashi lbrin irin tanada tanadan datayima bikinsu wanda takejin kamar tajawo ranar biki zuwa gobe saboda Zumudi,Shi ko zumudin bayayi ammh ita datake budurwa rawan kafanta yayi yawa Shi har mamakinta yakeyi,tunda yake baitaba ganin Amarya mai Shigen rawan kafa ba irin Zahra,wanda halittace domin da zata bari data bari Tunda Momi na mata Fada,hakama Nadira wani lokacin kamar ta maketa takeji in tayi wani abun,shiyasa basa shiri da Yaya Nadir,saboda yadda bata komai cikin natsuwa..’lalle zahra kin samu mtsala😂
Bata barshi ba sai wajen 12 koda ya Fito Falo Tun har sun kashe komai na kayan Wuta sun Shige daki sun kwanta,bai shiga dakin ba ya dawo dakin yayi Shirin barci ya kwanta cike da Tunanin yadda zai Tunkari Malika da zencen kara aurenshi,bayaso yakara tadamata da hankali kan wanda take ciki,bata gama warwarewa,ammh ya yanke shawaran zai sanar da ita,ammh zuwa gaba kan lokaci ta dan saki ranta.
*
Washegari Da Saleem zai Fita office,Joda tayi mai mganar Cefane,hakika Saleem yaji dadi ko bakomai yanzu Duniya andaina kiwon Dabba kamar da,yanzu duniya cike take da masu saka ido,yanzu haka Allah kadai yasan mutanen da sukayi zundenshi na Siyan abincin dayake Tafe yi kullum ba ranar banza,Musamman yan wajen aikinsu yasan baza”a rasa masu dogon baki ba😂.
Har afuska ya Nuna ma Joda jin dadinsa akwai yana Fita ba dadewa sai ga Sargent musa ya Kawo kayan Cefena niki niki,Joda ta karba ta kai kichen ta sanya komai cikin muhallinshi,da ta bude store din kichen din wanda ke shake da kayan abinci kala kala Nau’i Nau’i,nan da nan Joda ta zage damtse tana hada hadar Dora,girki ita kuma Malika tana daki yau ko Falo bata Fito yan mulkin sun motsa,shiyasa ko Saleem daya Shigo dubata da safe barci karya tayimai,har ya fice basu gaisa ba sai da ya Fita kana ta bude ido,tana bin bayanshi da kallo cike da Soyayyarsa mai Cike da muradi da sadaukarwa.
Sai da Maman Abba ta Shigo kana Malika ta Fito da katon cikinta suka gaisa tana mata sannu,Joda ma dake kichen ta Fito suka gaisa kafin takoma ta cigaba da aikinta don Malika tace tayi mata Tuwon Shinkafa miyar Ganye,Maman Abba taji dadin ganin yadda Malika ta chanza ta cire damuwar komai acikin ranta,har ta nuna mata ta hanyar Furta mata,daga karshe tabata Shawaran ta rinka zuwa kichen din duk da haka tana kallon Abunda Joda keyi tana koya da haka zata sha mamakin abunda zata Tsinta kafin Allah ya sauketa lafiya,Malika taji dadin haka tace daman zaman kadaichi ya isheta in Joda ta Shige kichen ta barta ita kadai,gashi ita kallo bai dameta ba.
Sai da Joda tagama Tuwon nan Maman Abba taci kuma tatafi dashi saboda yadda Tuwon yayi mata dadi,Malika ko taci taci takara kamar cikinta zai Fashe,wanda ya ragu Joda ta ijema Saleem,malika ta dauke tace shi zataci da daddare,dole Joda ta girkama Saleem farar Shinkafa da miyat kaji,Koda ya dawo Joda ta gabatar da abinci bakinshi ya kasa rufuwa nan Falon ya zauna dirshan yana cin abinci,ammh sai yaga Malika nacin Tuwo daya tambayi Joda ina Amanarshi ta samu Tuwo,nan take sanar dashi ita tayi dazu kuma yar Rigimar nasa ta dauke tace shi zata ci kafin ta kwanta.
Kura ma malika ido yayi yana kallonta tana cin Tuwonta cike da Sanyinta yadda ta saba,mirmishi kawai yayi yana Fadin’,Tunda itace zataci toh nayi mata afuwa,ammh da wani ne yau Allah bazan barmai ba..”Yafada yana Hade giransa waje daya Dariya joda ta dinga musu tana Fadin”Kunfi kusa aie..In ma zaka karbi kayanka ne babu Ruwan Joda aciki..”Yana cin abinsa bai sake mgana ba,saboda yaga yau din Mulkin Malikar ya motsa ne,ganin haka yasa joda ta Shige daki ta barsu anan.
Shima yana kammallah jin abincin da kanshi ya kwashe kololin zuwa kichen ya wanke hannayenshi ya dawo Falon yana kallon Malika tana wani yamutsa baki,gabanta ya karisa yana kallonta kafin yace”Ya..? kin koshi ne..? Kai ta gyada mai akarkace,Filet din Tuwon ya dauke ya nufi kichen dashi da sauri tace”Don Allah asamin a fridge gobe zan karya dashi..”bai juyo ba,kuma bai yi mgana ba ya Shiga kichen din yasanya mata shi cikin Fridge din ya Fito.
Yana zuwa gabanta baiyi wata wata taji ya daga cak,ya sakata cikin kirjinsa da ita,kuri tayi mai da ido tana binshi da kallo ganin hanyar dakinshi ya dosa da ita,shiyasa tace”Ban wanke hannu ba Mallam..”Bai mata mgana ba sai da ya direta bisa gadonshi kafin ya durkusa kusa da ita ya Dauki hannun damanta wanda taci tuwon dashi ya saka abakinshi yara lasheshi daya bayan daya,sai da ya sule hannun tas,yana yi yana kallon kwayan idanuwanta,Lumshe ido take tana jin wani yanayi yana Shiga jikinta.
Sai da yagama lashe hannun kafin ya mike yana kallonta yace”Daga yau kinga makwancinki nan,ke ko kunyar Joda bakiyi ga dakin mijinki ammh kina kwana da wata katuwar mace..”Yafada yana Shafa gemunsa daya Tsirowa na rashin kunya😂,Ware ido tayi tana kallonshi kafin ma ta samu zarafin mgana ya Fada tiolet yayi wanka ya wanke baki kafin ya dauro alwala koda ya Fito jikinsa babu riga,sai dogon wandonshi Jikinsa gabadaya yana digan Ruwa,jallabiyansa ya sanya ya shimfida sallaya ya tada sallar Shafa’i da Wututri yayi kafin ya rufe a addu’o,insa,Koda ya idar da Sallan Malika ta dade da yi barci,shiyasa yana tashi ya dauketa yakaita tsakiyar gadon ya gyara mata kwanciya,shima cire jallabiyan yayi da dogon wandon jikinsa,Ya bar kanshi daga shi sai gajeron wando ya Kwanta kusa da Malika ya Rumgumota kam,yana sakin ajiyar Zuciya,itama cikin barci ta zagaye hannayenta bisa cikinsa ta rikeshi gam,Blanket ya Rufa musu yana shafa maran Malika zuwa saman Tulelen cikinsa haka kurum yakejin Nishadi na Shigansa,yana jin wayarsa na Dukan neman agaji ammh ya share don yasan zahra ce,shi haushin datake bashi ta manta yana da mata ne? ammh sai ta dinga kiranshi duk sanda taga dama,Tsaki yaja aransa yana Fadin dole ya tashi tsaye don ya lura sam zahra bata da adalci.
*
Kwanaki suna ta gangarawa ayayinda muketa cinye kwanakinmu Aduniya,Ahaka ne har gashi auren Zahra da Saleem yana ta matsowa har yarage saura 4weeks ta kowani bangare anata Shirye shirye musamman ma bangaren uwar gayyah zahra,tun akwanakin da suka rage tafara banke banken mganugunar mata kamar hauka,wannan kuma shawarar Nadira ce itace kan gaba wajen amsomata tana duramata ammh basu bar momi tagani ba don susan zasu ci ubansu.
Ta bangaren Saleem ko baya wani Shirye Shirye domin ayanzu yafi jin dadin rayuwarsa Fiye data kullum,Domin shakuwa mai cike da salon soyayya ta shiga tsakanin Malika da Saleem,wanda shi Saleem din bai Fahimci haka ba,Sakamakon zuwan Joda shi yakara musu kusanci da juna,shine sanadin kwanansu waje daya wanda yayi sanadiyar kara musu Shakuwa da kusantan Juna.
Duk da halin da malika ke ciki da zarar Saleem ya nemeta bata iya mai gaddama zata bashi dukkan Hadin kai da zai samu natsuwa,shikuma yana son binta ahankali saboda cikin jikinta ammh kuma zumarta ne ke janshi wanda indai zata kwana cikin jikinsa bai ya kauda ido akanta sai ya lalubeta ko kadan ne,ita kuma bata iyamai gaddama,domin yakoya mata jarabanshi bata iya hakuri dashi indai yana nan tana kakume dashi.
Daga bangarenshi babu Shirye shiryen dayake gudanarwa ko kudin kayan aure ma Ummi ya tura kudi a banki ta bada oder kayan akwatuna,tsarin Shirye shiryen bangaren amarya kuwa sai da ya bude musu Wuta ita da Nadira,Abun takaichi aure kamar wani auren Mawaki,Evets wajen goma suka lissafomai baki ya sake yana kallonsu daga karshe ya Rufe bakinsu da Fadin Shidai banda daurin aure babu Abunda zai hallata,so in ma sun Shirya bidi’o’insu toh shi dai bandashi ayi lafiya 3hundered thausand ya tura musu yace suyi Abunda ya zama dole,sai kuma yahadasu da Sadiq tunda yaga yamatsamai Shiyasa ya hadasu don yaga shima dan Rawan kan ne kamar su.
Baita yarda yayi ma malika mganar ba,itama batayimai ba,sai ranar Suna kwance bayan sungama Samun Natsuwa tana kwance bisa kirjinsa,wayar Saleem tayi ta daukan daukin kira,wanda lokacin after 11 na dare ne,yana ji ammh sai ya dauki wayar ya kashe,ganin haka yasa Malika cewa”Ka daga kiran ka Mallaam..”Tafada cikin karfin hali.
Yana jinta yayi mata Shuru ammh kuma yana Rumgume da ita yana Shafa gashin kanta zuwa bayanta,Cikin kasalattaciyar murya yace”In dauka fa kikace?kinsan waye ke kiran ne..?Kai tsaye tace”Na sani ba amaryanka bane..”Abazata yaji mganar nata,duk ya ji wani iri ammh sai ya dake cikin karfi hali yace”Waya fadamiki zan kara aure..”Kai tsaye tace”Ummi ta sanar dani tun lokacin da aka sanya ranar..”
Shuru yayi bai kara mgana ba,itama sai taja bakinta ta tsuke,still kuma Zahran bata hakura ta daina kira ba,afusace ya dauki wayar ya kasheta gabadaya yana tsaki cikin ranshi,har ta Fidda rai da zai mata mgana taji yace”Ammh meyasa baki taba Nuna min Ummi ta sanar dake ba..”Tana kwance bisa kirjinsa bata dago ba tace”Saboda baka bani damar haka ba,bansani ba ko kana Tunanin cewa zan hanaka kara aure ne,nikuma ko daya babu yarda zan ce ka zauna dani ni daya mallam,Allah yabada zaman lafiya yasa ayi sha’ani lafiya agama..”takarishe Fada tana Sharan kwallah.
Tsausayinta ya kamashi,Fuskarta ya dago yana Share mata hawaye yake Fadin”will tok later,juz sleep now kinji..”,Gyada mai kai kawai tayi takoma bisa kirjinsa ta lafe,shikuma yana ta lallashinta ta hanyar Shafa bayanta zuwa kugunta cike da salon lallashi,har barci ya kwasheta shiko idanuwansa biyu yana Tunanin yadda yanayin zamansu zai kasance irin zahra ta Shigo rayuwarsu.
*
Bai kara tada mata da mganar ba,shiyasa itama tayi mai Shuru,bata karamai mganar ba sai da taga yafara gyaran gidan,gabadaya dakunansu zuwa falon duk an chanza komai da komai anyi sabon Fenti,kuma daga yammah daga Falon ya Fitar da dakinsa,aka gyara aka zuba komai da Malika taga haka sai tamai mganan cewa badai anan zai saka amarya ba,sai ya bata amsa da cewa eh anan gidan zata zauna,ammh adakinsa,shi kuma Zai koma sabon dakin daya gyara,sai Malika tace Me zai hana su koma gidan da Daddy ya bashi su zauna dukkansu,sai ya dinga zuwa musu Weeked.
Ya dade yana kallonta cike da mamaki kafin ya girgiza yace mata”Bazai yuyu ba,bai zauna da ita acikin gidan da akabashi saboda ita ba,cin Fuska ne wannan kawai ta barshi tazo nan su zauna,kuma Shi baya ra”ayin zama shi kadai yafison ya hadashi matanshi waje daya ta bari in tana so ta zauna agidan ta bari sai ta haihu sai su rinka zuwa suna hutunsu achan,data mtsamai sai ya bata Fuska yace tadaina ma Damunshi Dole Abunda ya tsara shi za”ayi.
*
Biki saura Sati biyu Aka kai akwatunan aure kano,wanda Ummi da ita da wata kawarta da wasu goggonin Saleem yan kumo suka kai kayan,akwati takwas,shake da kayan arziki wanda aka karbesu hannun bibbiyu Abunda sai wanda yagani,Suma achan din anyi musu kara sosai sunci sun sha,kuma sunyi guzurin Abun soye soyen da’akayi musu basu ci ba,Takwaichin Turaman atamfafi ashirin Hajiya Saratu momi ta basu da kudi 50k,Daga kano zamfara suka Wuce suka kaima Malika kayanta wanda aka hadamata dana Haihuwa,Dayake tayi scanning ance mace zata haifa,akwati hudu nata uku kuma kayan bbys ne Abun sai wanda yagani,Malika taji dadin zuwansu ba kadan,ita da ada take jin haushin baki suzo gidansu,ammh sai gashi yau Malika tana neman ma bako yazo wajenta koda daga kauye ne..
Ba Aranar suka koma ba,sai washegari suka koma Abuja,wanda kafin tafiyarsu sai da suka tara Saleem da Malika suka yi musu nasihan da fatan su xauna lafiya da junansu,Amarya kuma Ummi tace ranar da za’a dauko ta daga kano Abuja za”a kawota sai ta kwana kana washegari su wuto zamfara da ita.
MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
