Maleeka Malik – Chapter Twenty-six
by NadminMASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
“”Wayar Malika yake ta kira,ammh kuma gashi tana Ringing ammh kuma ba”a picking hankalinshi in yayi Dubu ya tashi,haka ya shiga cikin mota yayi zaune yana dafe kai,wayarsa ne ta dau Tsuwa yana dubawa yaga Wata Nombace agaggauce ya daga kiran yana Fadin”Hello…”
Joda dagachan bangaren tace”Hello ya Saleem Joda ce..”Jikinsa na rawa ya Fito daga motan yana Fadin”Joda,kuna ina ne,ina ita malikan? ta haihu ne? ko bata haihuwa ba..? Haka ya Shiga jeramata tambayoyi alokaci daya,cikin damuwa da alhini tace”Muna asibitin da Maman Abba ke aiki,kuma haryanzu Anty malikan bata haihuwa ba,sau biyu ana Saka mata Ruwan Nakuda,ammah haihuwar shuru,wlh Ya Saleem Anty malika tana Shan Wuya,yanzu hakama ana cukun cukun Turamu General hospital gusau ne..”
Dafe kai Saleem yayi yana Fadin”Innalillahi wa’inna Alaihirraju’un,ganin nan zuwa yanzu…”Yafada yana katse kiran ko cikin gida bai koma ba ya Fada mota ya tasheta asukwane,da Sauri ya dinga latsama Megadi hon,wanda ya Rugo da gudu ya Budemai get ya sulala zuwa waje da Gudu.
*
Zahra ko tana zaune kan kujeran Da Saleem ya tureta bata iya tashi ba saboda takaichi da bakinciki,tana jin sanda yayi hon da kuma Ficewarsa lokaci daya,tsaki taja afali kafin tatashi tana tattara kololin daya watsar tana Fadin”Allah sa daga haihuwar ta mutu,basai naga karyan Tsiya ba..
ko Ajikinta bata damu ba,saima gyara zama datayi afalo tana chanje chanjen tasha ko ajikinta,saboda gulma ita ta kira Saleem tana Sanar da ita Abunda ya Faru,da kuma halin da’ake ciki,shewa Saleema tayi kafin tace”Kin min Daidai ta wajena,haka nakeson ki rika yin komai cikin taku,ni Allah yasa ma wajen haihuwar daga ita har Abunda ke cikin nata su Haura chan,sai mu fatan Allah ya kiyaye hanya mu sai munzo..”Dariya suka Sheke dashi atare kafin Zahra tace”Kamar kin Shiga Raina haka nace,….”nan suka cigaba da hiransu suna zagin malika da fatan kada Allah yasa ta haihu lafiya,su Fatan mutuwa suke mata,saboda yadda sukaji jininta arayuwarsu ta Duniya.
Koda Saleem ya isa asibitin har anbasu takardan izinin tafiya da malika Zuwa general hospital gusai so bai tsaya ba,suka sanyata amota Shida Joda da Maman Abba,wacce ta bar motarta anan asibitin BAyan ta kira Baban Abba ta sanar dashi Abunda ke Faruwa,yakuma amince taje har chan general hospital gusau din.
Saleem yayi gudu bisa hanya,sakamakon ganin irin kuka da salatin da Malika keyi tana Fadin ita mutuwa zatayi,duk inda hankalinshi yake toh alokacin atashe yake,gudu kawai yake tsulawa cikin lokaci sai gasu acikin haraban general din,maman Abba ita tafita ta gudu ta sanar Da Nurses su kuma suka zo da Gadon daukan marasa lafiya,ko kafin su kariso sai suka Hadu da Saleem ya daukota ahannunshi nan suka nuna mai dakin da zai Shiga da ita,nan ya Shiga da ita ya kwantar da ita kan wani karamin gado yana kallon Fuskarta yarda halittarta ta chanza Saboda wahala.
Korarshi sukayi waje,ammh da ya zauna kusa da itane ya rikemata hannu yana Lallashinta,Ranar dagashi har maman Abba da Joda babu wanda ya Runtsa saboda tashin hankali,har wajen asuba malika shuru bata haihuwa ba,ga karfinta ya kare,kawai sai likitoci Suka Nemi Saleem daya saka hannu zasu Shiga da ita dakin Tiyata,nan da nan ko ya rattaba hankalinshi tashe,daman ya gaji da wahalar da Malika kesha hakanan..
Sai bayan an Shiga da ita dakin Tiyata din ne yasamu sukunin kiran Abbi ya sanar dashi Abunda ke Faruwa,wanda yadinga salati yana kiran Sunan Allah,Koda yake sanar dasu Ummi da hajiya,wacce bata dade da dawowa daga kumo ba,don ko bikin Zahra da Saleem da akayi batanan,Suma salatin suka saka suna Fatan Allah ya sauketa lafiya,itako Saleema tanaji ammh sai ta nuna kamar bata sani ba,nan ko cikin ranta addu’a take kada Allah yasa Malikan ma ta rayu.
Joda kuma ta kira Hajiya Binta ta sanar da ita Abunda ke Faruwa,matukar tsausaya Hajiya ta tsausayama Malika,saboda tasani yau zataji Abunda kowacce uwa taji kafin ta haihu,Haka ta dinga mata addu’ar Allah yasa ayi aiki lafiya afito lafiya.
Alhamdulillah Anyi Nasarar Yima Malika aiki kuma an Fito mata da kyakyawan yarinyarta wacce take kama da ubanta sak,sai dai ta debo hasken Fatan mamanta,Tuni har ankaisu dakin hutu malika bata Farfado ba,ammh an gyare bby tas gwanin ban sha’awa,Murna wajen Saleem ba’a mgana sai da yayi Sujjuda ya mika godiyarsa ga Allah (SWA) domin Shine ke badawa kuma Shike Hanawa.
.
Shi yayi ta kiran yan”uwa da abokan arziki yana sanar dasu anfito da malika lafiya kuma ansamu Babby girl,ciki harda Zahra wanda haihuwar kwata kwata bata mata dadi ba,sai ta nunama Saleem din don daya gayamata haka tayi Shuru taki mgana sai da yakara maimaitamata kana tace Allah ya raya ta yanke kiran,ya dade yana kallon wayar yana mamakin zahra yana so ya Fahimci wani abu game da yarinyar,wacce Tun Abunda tayi jiya ya gane ya bar Shiri Tun rani,ammh zai tambayi malika in takoma gida yaji wani irin zama suke gudawar ita da Zahra.
Malika bata Farfado ba sai da yammah,nan ta ci karo da Abunda aka Ciro mata,haka ta dauki yarinyar tana kuka,ba kukan komai take ba,sai kukan Mallam zai rabu da ita,acikin wannan Halin ya Shigo ya sameta nan ya hadasu ita da Bbyn ya Rumgume yana mata godiya,ammh abun mamaki Malika kanzil batace mai ba Tun yana ganin Rudin haihuwace da kuma aikin dake jikinta,ammh har washegari Batamai mgana ba,dayayimata zata kauda kai tana kuka Abun yabashi mamaki matuka,ammh sai ya kyaleta sai sun koma gida yaji meya faru kuma.
Sai Ranar yakoma Zamfara yabar Maman Abba da joda,koda ya koma Zahra kota tambayeshi ya maijego da bby,kuma koda yake chan Asibitin koda kuskure bata taba kiranshi taji ya ake ciki ba,sai dai inshine ya kirata,mamakinta kawai yakeyi,ammh sai bai mata mgana ba ya kyaleta yaga iya gudun Ruwanta,Ranar bai koma asibitin ba,saboda goggo Hadiza aka turo tazo daga Malunfashi don ta zauna da malika tana kula da ita,tunda dai joda yarinyace bazata iya ba,Maman Abba kuma ta dawo gida,washe garin ma kiran Ummi ya samu yana wajen aiki ta sanar dashi gasu asibitin basu ganshi ba,yace yana tafe,daga wajen aiki gusau din yakoma chan ya tarar da Ummi da Hajiya da Abbi sunce sunma dade da zuwa,sai wajen la’asar kana sukayi Shirin Tafiya inda Ummi taja Saleem gefe tana Tambayanshi”Ina abokiyar zaman malika da batazo asibiti ba,kuma joda ta sanar da ita makociyar Malika ce tazo ta taimakamata kwanansu biyu tare,bata tafi ba sai da goggon Malika tazo..?
Kame kame Yafarama Ummi Tundaganan tagane akwai mtsala,kafin yasamu karyar cemata zahran itama tana gida bata da lafiya,Ajiyar zuciya Ummi ta sauke kafin tace”gaskiya Abun baiyi tsari ba ka gyara zamantakewar gidanka,ai yakamata Tunda ba kwance take ba,ta biyoka yau tazo dubata ko? kansa na kasa yace ma Ummi ba daga gida yake ba,ammh insha Allahu gobe zasu zo tare,Ummi bata komai ba,sukayi musu sallama suka koma hanyar Abuja,su suka kawomusu kwando guda na coolers,cike da abinci sai kayan Fruits.
Mganar da Ummi tayima Saleem ta tsayamai arai har yakoma gida yana auna magarta inda yaga tabbas gaskiya ne,kuma Duniya na nan na Zaginshi akan Abunda Zahra tayi,ammh ba komai bari Malikan ta daawo gida zaiji dalili,Tun adaren ya sanar da Zahra cewa gobe zasu je asibiti da ita ta Duba malika,kodaga yanayin yadda tayi ya Fahimci batayi niyyar zuwa ba,aiko hakane gari na wayewa Zahra ta kwanta tana rawan sanyi tace bata da lafiya,mamakinta ya kamashi bai mata mgana ba ya sakai ya Fice,wanda duk Abunda tayi Saleema ce ta kitsa matashi,yana Fita ko ta kirata suna Dariya,nan Saleema ke sanar da ita gobe zata zo,su cigaba daga inda suka tsaya murna ta kama zahra tadinga Jin dadin zuwan Saleeman agobe.
Har Washegarin Ranar da Saleema zatazo Saleem bai sani ba,saboda Tun Safe yatafi gusau saboda yau din za”a sallamosu su dawo gida,koda yaje shiyayi cike cike da kuma biyan kudin wasu magungunar daba’a biya ba,kafin abasu sallama,shida kanshi yazo yana hada musu kayansu bayan su joda sun kwashi wasu kayan zuwa mota,Nan ne Malika ta kalleshi kafin tacemai tana neman wata alfarma ne,koda ya bata dama kawai sai tace don Allah yayimata alfarma barin ayi suna kafin ya saketa..”Mganar tazomai abazata zama yayi kusa da ita yana tambayanta shi bai gane ina ta dosa ba? waye yace mata Shi Saleem zai saketa..? kin amsashi tayi yayi mganar Duniyar taki magana daga bayama sai ta sakamai kuka,dole ya rabu da ita,ammh bawai don ya bar mganar ba,sai da yayi Shuru ne sai sun koma gida ya turketa yaji daga ina aka samo wannan iskancin.
Suna dawowa sukaci karo da Saleema ta iso,Saleem har ga Allah yayi mamakin ganinta,daya tambayeta meya kawota kuma yaushe tazo..? Sai tace bata dade ba,kuma tazo ganin mejego ne da kuma bby,Cikin mamaki yake tambayanta meyasa bata zo asibitin ba,sai tayi missing step tace wai Zahra tace mata yau zasu dawo gida,Yayi mamakin jin haka sabida ko zahra batasan yau za”a sallamo Malika daga asibiti ba? toh waya gaya mata..?bai maida mganar Serious ba,ya share kawai bai zauna ba yakoma wajen Aikinsa,itakuma goggo Hadiza ta saka Ruwan zafi tatara malika bayi tamata wanka ta gasata sosai duk ko achan asibitin tana gasata,ita kuma maman Abba ita tama bby wanka aka sanyata cikin kayan sanyi masu kyau da ban Sha”awa..”
Zahra ko Da Saleema wannan Haihuwa dai bata yi musu dadi ba,Har yammah basu shigo sun duba Maijego ba,kuma anajin dariyansu afalo,ammh kuma basu shiga ba,sai dare kana suka Shiga suka dauki yarinyar awulakance har zahra na Fadin tabiyo jar Fatan kakaninta Arna,Tafada tana dariya Saleema ko Fadi take,sai dai amata fatan Shiriya kinsan ana tsotson Iskanci da rashin tarbiya ajikin Nonon uwa..”haka sukayita fadar maganganu son ransu,Joda taso tayi mgana Ammh goggo Hadiza ta hanasu tace su kyalesu komai zasuyi kada su tankansu saboda su neman wanda zai tankasu ne suyi fada dashi,Haka akayi ba wanda ke bi takansu aiki ko ko changal basayi acikin gidan alhalin Saleema cewa tayi zatazo ta taimakama zahra da aiki,Joda ce da Maman Abba ke ta dawainiya da Malika suyi girki su gyara gida,su sakama malika Ruwan wanka,aikin goggo Hadiza kawai Yima Malika wanka da kula da ita ita da Bby,wacce ta samu Ruwan Nono sosai wanda yake taimaka jaririyar wajen samun Abinci sosai.
Saleem baida masaniyar Abunda ke Faruwa,don baya zama agidan in yafita Tun safe sai dare yake dawowa,kuma babu wanda ya Sanar dashi ga Abunda ke Faruwa,wanda Wuni suke suna zaune afalo suna Hiransu suna dariya,ko ajikinsu kuma adafa abasu suci suna wulakanci,Malika ko tana cikin damuwa bata cikin natsuwarta saboda ita harga Allah Ta yarda da mganar Zahra tana cikin Fargaban in Mallam ya saketa ya zata kare da rayuwarta,ammh ta gagara fadama kowa ta bar Abun acikin ranta.
*
Ranar bakwai din na zagayowa Ranar akayi suna jaririya taci sunan Ummi Aisha suna kiranta AYDA,Anyi sha’anin cikin Farinciki da murna,yan malumfashi sunzo harda yan Kumo ma sunzo ansha suna,wanda Su joda sukayi abinci kala kala agidan maman Abba,sun dafa white rice da Miyar nama,sai friede rice da Kuma jallof mai Cosslow,sai Soyayyan Naman kaji dana rago,Sunyi kunun aya,Sai alale na leda,wanda yaji kwai,kuma bayan lemukan da Saleem yasa aka sauke musu domin baki,Kuma su kadai sukayi duka aikinsu agidan Maman Abba,sai dai suka kwaso su cikin manyan kololi suka dawo dashi nan gidan
Malika ta Shiga ta Fita cikin kayan alfarma ita da Ayda,musamman maman Abba ta sake kiran Ummi mai lalle da kitso ta sake cakareta,bayan nan mai kwalliya tazo itama ta tsantsaramata kwalliya Abun sai wanda yagani,dayake simple make up ne tayi mata,sai ta Fito ras da ita,Abunka ga farar fata,dama gata da kyau ai sai kawai tashiga kyalli,Zahra ko da Saleema kamar su mutu saboda bakinciki domin ko sun sani wlh karfin hali kawai suke,ammh Malika tafi karfinsu dukkansu,domin ta Wuce da saninsu ta bangarori dama,Ranar sai ga Hajiya saratu momi da Nadira sun diro sunan wanda suka zo suna ta ma zahra Fadan bata sanar dasu malika ta haihu ba,nan tayi ta borin kunya tana Fadin wai ta kira wayarsu bata samesu ba,Nadira ce tace sunyi waya da Saleem yake sanar da ita jiya,yace kuma yau ne Suna,shine ta Fadama momi suka taho,duk da basu wani dade ba,ammh ko malika da basa shiri da zahra taji dadin zuwansu da zasu tafi momi ta bata 10k da kuma Atamfa guda biyu da kayan babys,ko Saleem basu gani ba,don Tun safe ya Fice sakon gaisuwa kadai sukabari agaya mishi.
Taron sunan baiyi wasu jama’a sosai ba,daga yan malumfashi ne sai yan kumo,wadanda suma suna gama cin suna suka koma,dama sunzo da motar gidane,sai yan group din *MALIKA MALIK PAID* Da yan *HAFNAN AND JANAF PAID GROUP* Da sukayi mata kara mota guda suka zo ma malika sunan Ayda wanda ta dinga mamakin daga ina suka samu lbrinta,nan Dotata Ladingo tayi dariya kafin tace”Karki damu da sanin ina muka samu lbrinki,domin mommyna Janafty ita take sanar damu lbrinki,kuma dukkanmu nan masoyanki ne,duk dabamu taba ganinki ba,muna kaunarki..”Jin haka yasa malika tayi murna sosai da Farinciki nan aka zubo musu abinci suka baje suna ci suna hira,su Sisina Aisha alto da Sahiba sai ci ake hannu baka hannu kwarya😂su mommyn Abdul me,su Rafi’atu,Fati sadi,mommyna khadija tame gari,momyna khadija bashir,Dijah Abdul,Dija muhd,Zuwaira Andijat,My besty halima,Fatima zahra,haleema,Ummi imran, Mmn useey,Ummi bilal,Fatima garba,mom sadiq,Suwaiba,shafa yola,Murja bagudu,Deejart,Mmn baraka,Mmn Amira,mm siyama,Ummu bilal2,Rouky niger,Azeeza,hadiza,Durling Rukayyah, Masoyiya takwarar malika,khadija Aliyu,khadee Noor,mmn Haneef,Mmn mama,yar Fulani,Nazeeha Ahmed,Saleema Hamza,Ayshert usman,Maman khairat,Bbyj,Asma’u Shehu,Ummah sabo,Zainab jega,Hafsart Umar,Fatima musa mamn Nabila,Mmn ummulos,Nafeesa Fee,jikar hajiya,Mrs Umar Faruk,Sardiya,Suna da dayawa wanda bakina bazai ya ambatonsu duka ba.
Sunsha Ankonsu cikin red din materila sunyi head da blue,abun sai wanda ya gani,malika tayi Farinciki ganinsu sosai haka sukayi ta daukan Hotuna suda malika da bby Ayda,Fatima zahra ko ana riketa tana abarta ta Shiga dakin Zahra taci ubanta😂🤔Dakyar Su Nazeeha da Ummi imran suka rirriketa suna bata baki kana ta hakura,Har sukayima Malika sallama bayan sun bata sha tara na arzikin da suka kawomata ,basu saka Zahra da Saleema a ido ba,ammh d Yawansu sun so su gansu koda tsaraban Harara ne su basu koda bazasu dake su ba,Saboda murna da godiya har bakin mota joda da Malika suka rakosu suna musu godiya suna dagama musu hannu har suka Fice daga gidan.😂
Anyi taro lafiya an watse taro,Ayda da mamanta sunyi goshi matuka domin Abbi 50k ya aikomata dashi Ummi ko akwati tayi Sir da kayan Babby da mamanta balle dataji ita akama takwara,Ya marwan ko Shima kayan yara ya turo dashi daga lagos,da kudi 30k akabama malika,haka shima Sadiq kudi yabata 20k Malika saboda Farinciki sai da tayi kwallah ta kira Abbi da Ummi tana musu godiya tana kuka,harta da Sadiq din da Marwan Saleem ya kirasu yabata tayi musu godiya sukace ai babu komai suma yarsu ce,Su Zahra da Saleema ba karamin mamaki sukayi ba da sukaji uban Dukiya da kayan da malika tatara,nan da nan hassada da haushi ya kamasu,nan Zahra taji itama tana son ta samu ciki itama ta haihu ataramata kudi,Niko nace banza abanza,ke keta Dukiya indai kudi ne Malika ta mallakeshi da wanda zai siyeki keda Mai zugakin gabadaya.
Shiko Uban gayyar bai siyan mata komai ba,illah wata sarkan gold mai kyau Sarka da Dankunne,Ranar daya kirata ya damkamata sarkan adakinshi ne,yana rike da Ayda ita kuma malika na Faman gwada sarkan gaban madubi tana washe baki murna ta cikata Fadi take”Wayyo Mallam wht a special gift,gaskiya am so hppy wlh Allah ya saka da alheri ya kuma rayamana Ayda cikin tafarkin islama..”Da Ameen ya amsa yana mata dariya Abun yayimai dadi yadda ta nuna murnanta afili,domin yasan cewa Malika ta mallki dubunsu kafin yanzu kuma ko ayanzu tana da Dubunsu ammh kalli yadda take murna akan kyautan da yayimata wacce bata Wuce yarwa abola ba indai awajentane..
Kwantar da Ayda yayi bisa gado ya taso yazo ta bayanta ya Rumgumeta duka kyakyaawan Fuskokinsu suka bayyana acikin madubi,mirmishi take sakin mai bayan ta dora hannuwanta kan nashi,cikin wani salo yayi mata Rada akunne yana Fadin”Ummi Ayda..”yafada yana Shinshinar Wuyanta Cikin kasalar daya saukarmata tace”Umhmm Abbu Ayda..”Mirmishi yayi har Hakoransa farare suka bayyana,Cikinta ya mtsana tayi yar ihu tana Fadin”Kai mallam wajen operation din nefa ka tabamin..”Tafada cike da Shagwaba Saurin juyo da ita yayi yana Fadin”Ayyh am srry..”Ya fada yana shafa kumatunta,Kafin yace”Tambayarki zanyi,kuma ina so ki sanar dani gaskiyan al’amarin..”
Hannayenta ta harde bisa kirji tana Fadin”yes ina jinka,Allah yasa na sani..”Gyara Tsayuwa yayi yana kallon cikin kwayan idanunta Yace”Mganar dakikamin a asibiti kince kada na sakeki sai mun dawo gida? waya sanar dake cewa nace zan sake ki bayan kin haihu..? Shuru tayi tana dukar dakai taki mgana,Ganin tayi Shuru taki mgana yasa yace”Kinga ki sanar dani waya gaya miki wannan mganar da bata da Tushe ballatana makama,in baki gayamin ba,zan kira goggo Hadiza yanzu,kila ita in ta tambayeki ki sanar da ita..”
Jin haka yasa ta riko hannunshi da Sauri wanda yake Shirin Fita,bisa gefen gado suka zauna kafin tace”Basai ka sanar da kowa ba,Bani son Tun bayan daidaitan al’amarinmu babu wanda ya sakejin kanmu kai baka alfahari da hakan..? kai ya gyada mata bai yi mgana ba,Sai tacigaba da cewa”Toh meyasa zaka kai karata? dama zan sanar dakai Wacce ta Fadamin ammh sai kamin alqawarin bazaka dau wani mataki ba,kowani hukunci ba..”zuru yayi mata da ido yana kallonta kafin yace’Banyi alqawarin ba,ammh ki fara sanar dani Abunda ya Faru..”,
Hannunshi ta riko ta matse cikin nata kafin ta fara bashi lbrin Abunda yafaru da ita da Zahra ranar,bata rage komai ba ta karishe cikin kuka tana Fadin”,Na shiga tashin hankali Mallam,wlh in ka barni banson ya rayuwata zata kare ba,ga Shi Daddy ya tafi ya barni bani da kowa sai kai,kai ne gatana,don Allah kada ka barni ka zauna dani koda bazaka kyautatamin ba,kazama bango Abun jingina gareni..”Tafada tana Fadawa bisa kirjinsa tana kuka.
Riketa yayi yana buga bayanta,idanuwansa sun kala sunyi jawur,Sai yanzu yake kara Fahimtar Abubuwan da Zahra ta aikata Tun haihuwar malikan,Ashe munafukace Mai Fuska biyu,kuma gulman nata harda mijinta aciki,lalle yazama Dole yayi gaggawan daukan mataki akan Zahra kuma sai ta sanar dashi wajen wa taji wannan mganr,Cikin sauri ya raba Malika da jikinsa ya mike yana Wuce ya Fice daga dakin atamanin,cikin Tsoro Malika tabishi tana Fadin”Mallam,tsaya kaji..Ka tsaya…”Tafada tana kokarin Fita sai kukan Ayda ya dakatar da ita ta koma da hanzari ta daukota ta sabata,ta bi bayan Saleem da Sauri.
Tundaga Falo ya ke kiran Sunan Zahra murya a kaukaushe..”Zahra!.Zahra..!
Zahra…Zahra…”!Yake Fada yana Bude murya cikin bacin rai,Zahra da Saleema dake kan gadon Zahra suna hira sukaji muryan Saleem yana kiran zahra cikin muryan bacin rai,atare suka diro daga kan gadon suna Rigen Rigen Fitowa daga dakin,Ba su kadai ba hatta joda dake cikin daki ita da goggo Hadiza suka Fito hankalinsu tashe,saboda jin kiran bana lafiya bane.
Zai Shiga dakin Zahran kenan sai gata tafito agaba Saleema na biye da ita,Tana Fadin”Lafiya hone….”Ji kake Tas!Tas!Tas!….”Saleem ya kwashe Zahra da maruka Zafafa guda uku atare,saboda gigita da zafin mari sai da Zahra ta wuntsila tayi baya zata Fadi Saleema ta tarota ta Fado jikinta,cike da mamaki suke binshi da kallo yadda yake nuna Zahra da yatsa yana Sakin Huci,daidai lokacin da Malika ta kariso idanuwanta duka awaje saboda karan marukan dataji zahra tasha….
MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
