Maleeka Malik – Chapter Twenty-four
by NadminMASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
“”””Har Dare Zahra bataga Angonta ya leko ba,sai tafara damuwa,Saleema ce tace mata tayi hakuri zasu Shigo Shida da Sadiq kila idon mutane, ne yahansu shigowa tun dazu,Da farko tabar damuwa ammh data ga har pass 9 ai sai ta dau wayarta ta laluboshi sai taji ya sakata a call waiting.,lokacin yana waya da Malika ne,yana gani ya Shareta saboda yasan ko ya katse kiran, ba wata mgana bace mai muhimmanci ba,Shirme ne kawai da Shiririta.
Zahra ko kamar ta Fashe saboda takaichi da bakinciki gefe guda,kuma wani Tarnakakin kishi ke dawainiya da ita gashi taki hakura da kira sai kira take yana sata a call waiting,ranta ko ya kara baci kamar ta Fashe ita kadai,kuma bai kirata ba,sai da yagama waya Da malika kana ya kirata,lokacin har kwalla sun Fara taruwa a idanuwanta.
Tana Dauka Sai ta Fashemai da kuka,Shuru yayi yana Sauraranta cike da mamaki yace”Topha…Lafiyanki kuwa..? Tana Shesshekan kuka tace”Shine..Shine ina ta kiranka kaki dauka kana chan kana waya da wata ko..? Mele baki yayi kafin yace”Da wata kuma..? Ni bada wata nake mgana ba da yayarki ne,kuma bisa adalci duk wunin yau ban kirata ba,Kinga ko takirani ai na dauka na bata hakuri ko..?
Wani bacin rai ya Shiga zahra sai ta danne kafin tace”Ok..Shine najika Shuru baka Shigo waje na ba..”,Mamakin kalamanta yayi kafin yace”Haba don Allah Zahra mena ke ci na baka na zuba,akwai saboda rashin kunya sai na Wuce gaban Ummi da Abbi zuwa inda kike,tsayama su bakin dake dakin in na Shigo ina zasu..? Yafada cike da Dattako,Tura baki tayi kai tsaye tace”Toh su Fita mana..”Baki yakama kafin yace”Toh badani za’ayi haka ba,duk Abunda kikema Rawan kafa in inkinyi hakuri zaki sameshi zuwa gobe,sai kin barmin Abun Fada ba..”
Ko ajikinta sai ma kara narkemai datayi tana Fadin”Toh Tunda kasan Abunda nakema rawan kafa mai zai hana ka min kwatantancen dakin sai nazo kabani ka Huta da Rawan kafan..”,Tafada tana wani shafa Bakinta,Zaro ido yayi bai mata mgana ba kawai ya yanke kiran gabadaya yana kiran Sunan Allah,har Sadiq dake gefenshi yana waya da Saleema ya dago yana kallonsa,bai mai mgana ba,ganin ya dauki wayarsa ya Shige Tiolet,shiko wayar ya dauka saboda kada zahra takara kira,sai ya sanya Nombarta cikin blacklist ya dauro alwala ya Fito..
Jin ya kashe wayarsa,bai sa tagane tabargazan datayi ba,saima kara kokarin kiranshi datake,ammh ta gaza samunshi,tayi tayi taki Shiga kwata kwata,cikin damuwa ta Fito Falo ta Samu Saleema kan kujera tana waya ta daga mata duka tana Fadin”Ke kanwar Miji tashi ki rakani dakin yayanki yanzu..”Ba Saleema kadai hatta Nadira dake gefe tana charting sai da ta dago tana kallon Zahra cikin wani yanayi mai kama da kinyi hauka..
Saleema tayi Saurin yanke kiran tana kallon Zahra tace”Dakin yaya Saleem,lafiya kuwa..? Yamutsa Fuska tayi kafin tace”Kawai ina son ganinshi ne,ko laifi ne don nace kirakani dakinsa,ai naga dai an daura aure yazama mijina..”Tafada tana kallon Nadira,wacce ke kallonta cike da takaichi.
Saleema tayi dariya tana kallon Zahra kafin tace”A”a ko daya,sai dai ni bazan iya wucewa dake zuwa dakin yaya Saleem ba,Su Ummi fa na falo,kuma bama haka ba wlh Yaya Saleem zai iya marina in na rakaki gwara kiyi hakuri ki kirashi ta waya..”Tafada tana sakin hamma,Jagale Zahra tayi kafin tace”Ina ta kiransa ban samesa ba…Tafada kamar zatayi kuka.
Batama bama Saleema damar mgana ba,ta mike tana Fadin”Tunda bazaki rakani ba,ni bari naje da kaina,nasan bazan bata ba..”Tafada ta na kama hanyar Fita daga dakin,Nadira ta mike data ga rashin hankalin na Zahra ba karami bane,itako Saleema Abun ne ya bata mamaki,domin bata zata Zahran takai haka Wauta ba,Nadira ta sha gabanta tana Fadin”Wlh in kika Fita daga dakin nan,sai na kira Momi na sanar da ita,haba kidinga Abu kamar Wata mara Tunani da ilimi,in kin fasa Fita kin zama shegiya…”Tafada cike da masifa.,tana gama Fadin haka ta juya ta koma ta zauna tana sakin huci,
Jin Abunda Nadira tace ne,yasa Zahra takasa Fita,sai ta joyu afusace tajuya koma ciki tana kunkuni,Sauran iyayenta kuwa kanzil ba wanda tace musu,sun so ne sai ta Fita wlh gari na wayewa su tatarra su koma Kano suce amarya ta Hutar dasu takai kanta daki,Saleema tabi zahra da kallo tana wani Tunani aranta na indai zahra ahaka take Tunanin Sace zuciyar Saleem,to da sake domin Yaya Saleem ba irin sauran sakarkarun mazan data sani bane,Mutum ne mai aji da takama,da Wuya su Shirya matukar bata gyara takunta ba,ganin haka yasa ta mike tabi bayanta,koda taje ta isketa ta kumbura kamar ta Fashe,saboda Fushi ita ta zauna tana ta bata hakuri tana kara nuna mata sai fa ta rage wani abu saboda tsaro,ammh suk zahra bataji tana ganin Abunda takeyi Shine Daidai.
Washegari Tun bayan Angabatar musu da Abun kari suka karya sukayi wanka kowa ya Shirya saboda su isa da Wuri don bazasu kwana a zamfara ba dagachan zasu juya kano ne,Itako zahra an cakare cikin wata Shadda Ash colour dinkin Riga da Sikat,kayan Sun fita da ita ba laifi,Ummi ce ta Shigo gaida amarya da baki,Allah ya kyauta lokacin tana Sanye da mayafi da anyi Abun kunya,ammh fa ita kanta Ummi tayi mamaki ganin amarya tana gaisheta zaune kan kujera ta mike kafa idonta kyar akanta babu alamun kunyar nan ta Surukai,Abun ya daure mata kai sai dai batayi mgana ba ta Share,ammh aranta tana Fadin”Wannan wata amaryace Saleem ya kwaso kuma..?
Magana tayi akan Zata tafi da zahra chan wajen Abbi zai hadasu ita da Saleem yayi musu Nasiha ko gama Rufe baki Ummi batayi ba Zahra ta mike zumbur tana gyara mayafi tace”Yauwa Ummi muje..”Tafada tana yin gaba,ba Ummi kadai ba duk mutanen dakin sai da sukaji kunya,Tun ballatana Nadira taji kamar ta dora hannu aka ta yanka ihu,Saleema ko Wani iri taji don bataso ace wacce take goyon baya tana irin wannan Ba,duk zata bata musu Shirinsu Malikar ma ta Fita samun Fada wajensu Ummi.
Ummi ko Yaken Dole tayi tabi bayan Zahra tana kallonta cike da mamakinta,gefe daya kuma tana Tur da wayewa irinta yan matan zamani,don yanzu sai ace wannan ba komai bane wayewar zamani ce,ganin Sun Fita kuma batasan hanyar ba,shiyasa tabama Ummi dama ta Shiga gaba suka hau sama har Falon Abbi inda yake zaune bisa kujera Saleem wanda ke sanye da Farar Shadda dinki Muhammed,Aikin jikinta baki ne hakama hulan kanshi baka ce,yana zaune akasa kusa da kafafuwan Abbi kansa akasa alamun biyayyah da ladabi.
Suna Shiga Falon Tunda zahra ta hangi Masoyinta ta fara washe baki,sai kawai tatafi kusa dashi zata zauna,kanshi na kasa ya dago yana hararanta cike da takaichi,ganin haka yasa Abbi fadin”Kyaleshi diyata dawo nan..”Ya fada yana nuna mata dayan gefen,Ranta baiso ba takoma nan ta zauna tana kallon Saleem cikin so da kauna kamar ta jawoshi ta Rumgume haka takeji,balle yadda yayi mata kyau yau sosai..
Ummi dake tsaye gefe ta rike haba tana Fadin Cikin ranta”Allah mai zamani…”Zahra saboda shagala da kallon Saleem bata iya gaida Abbi ba,sai Shine yake gaisheta yana tambayanta ya kwanan bakunta,sai lokacin ta danji kunya ta sunkuyar dakai tana ansawa,ammh kuma ta gefen ido tana kallon Saleem,shiko kunyar Duniyace ta isheshi gaban Ummi da Abbi,kan Abunda zahra tayi gabadaya sai yaji auren ma ya Fitarmai aka yarinya kamar mai tabuwar junnu.
Nasiha sosai Abbi yayi musu,Yayima Saleem nasihan adalci a tsakanin matansa,Tunda Nauyi ya hau kanshi sai ya dage,banda nuna bambamci kowani wariya ga daya daga cikinsu duka matanshi ne,daga karshe yajamasa kunnen sai ya jajirce dole yazama na Namiji don zama da mata biyu babu sauki,don ko Shi da yake ubanshi daya gareshi,Yayima zahra Fadan tabi mijinta tamai biyayyah Shine Ribanta da Tsiranta aduniyama Har zuwa ranar Gobe kiyama.
Kuma yayi mata nasihan ta zauna da abokiyar zamanta Lafiya ta kuma bata girmanta,wanda ko Ummi ma da Abbi yabata damar mgana Abunda tayi ta jadaddamata kenan,Sakale tayi kawai tana jinsu ammh azahirin batu hankalinta baya tare dasu yana chan tana Tunanin yarda zata ci uban Malika ne hankali kwance,Duk Nasihan da suke mata bata jiba,Domin tace duk suyi su gama miji dai natane ita take da ikon Sarrafashi yadda taga dama basai wasu sun tsara mata ba.
Bayan su Abbi su sallamesu Saleem ya Dukar dakai yana godiya kafin su tashi su Fita,suna Fita zahra tayi zaraf ta riko hannunshi tana sakin mai mirmishi cike da salon makirci,Fizge hannunshi yayi yana kallonta kai tsaye yace”Zahra..Wai mike kanki ne? nan fa gidan iyayena,haba kidinga Abu kamar wata kilakin karuwa,dubi abunda kikayi dazu agaban su Abbi,yanzu Fisabillahi haka h amare masu kunya keyi tsakani fa ga Allah..”Ya fada cikin bacinrai.
Tura baki tayi kafin tace”To menayi kuma? ai ba Rashin kunya bane,suma su ummi murna zasuyi Ina son dansu sosai..”Kuramata ido yayi kafin yajamata wani dogon tsaki ya Kama hanya yana saukowa daga Steps da hanzari ta biyoshi har suka sauko hanyar dakinshi ya nufa,tako biyoshi jin tana biye dashi ne yasa ya waigo yana kallonta ganin ya tsaya ne,yasa itama ta tsaya tana kallonshi,Fuskarshi ba fara”a yace”Lafiya ina zaki naga kina bina ne…?
Rausayar dakai tayi kafin tace”Ina kuwa..? inda zaka mana..”Turbene Fuska yayi kafin ya nuna mata hannu yana Fadin”Kinga malama Wuce ki koma daki yanzu zamu tafi gidanmu sai kije chan kiyi ta rashin kunyarki,ammh wlh bazan bari ki barmin Abun Fada gaban dangi da iyaye na ba,karki sake ki Biyoni wlh..”Yafada yana Jadadda bayaninsa,Kafin ya juya ya Shige dakinsa ya banko kofa yana Ma kanshi jajen ya auro ma kansa jaraba da kudinsa.
Ganin ya Shige ya barta yasa taja kafafunta takoma cikin dakin tana wani bata rai,ba wanda ya kalleta sai Saleema,wacce ke mata kirari cike da Iya Shege,nan da nan ta Shiga washe baki kamar wata sakarya,Yadda suka zo haka suka dauki hanyar Zamfara,ammh wannan karon babu Saleema,wacce har ta Shiga mota Saleem yamata jan ido yace ta Fito,Tana tura baki ta Fita yayi mata kaca kaca,lokacin da Tajema Ummi tana kukan yahanata zuwa gidanshi,Shiko yace sai dai ta mutu Tunda ba uwar wani Zatamai ba intaje,dole ta hakura tanaji tana gani suka Fice daga haraban gidansu.
Sadiq shi ya sake daukan amarya sai motar gidansu Abbi da direba guda daya,Sai motar haya guda daya,wacce Saleem yayi tashanta,daganan Zamfara Kano zata Wuce dasu,Sun riga Saleem yin gaba,don shi kadai yataho amorarshi ammh bayan ya kira Malika ya sanar da ita suna bisa hanya,Ummi ko bata barsu haka ba,ta basu Turamen zani guda goma,da Turaren Wuta,dana daki,sai kudi ta ba masu kawo amayar aka rabu cikin girma da arziki.
Lokacin da Saleem ya kira Malika Tuni har an gama mata kunshinta ja da baki da kitsonta 2Steps😂,wanda yayi mata kyau over sai wanda yagani kunsan Farin fata yana karban Jan abu da baki atare,sai kitsonta wanda ya kasance yiri yiri ne,dama akwai gashi sai ta fito ras da ita,Abu daya yayimata cika katon Tulalen cikinta,wanda tayi wanka ta Shirya cikin leshinta riga da zani ta kashe daure bakace Malika malik din nan bace mai sanya kananun kaya masu Fitar da tsiraici.
Tun jiya su goggo hadiza suka iso ita Zulai tare da suka taru dasu Maman Abba suka sha bikinsu ajiya,suna kuma kokarin Debemata kewa sosai,wanda yayi nasaran ragemata damuwa,da kuma kishi,duk da taji abun,mussaman da lokacin daura aure ya kusanto har yazo ya Wuce,taji Abun aranta,ammh basu barta Tashiga halin damuwa ba,Hatta Hajiya binta dake gida tana takaba sai da ta kira Malika tana kara tausanta,Mirmushi kawai malika take aranta tana Fadin”To in batayi hakuri ba, ina zata da wannan cikin,ko tabar gidan Saleem bamai kwasanta ya zauna da ita don Allah,saboda haka hakuri yazama dole gareta.
Yana sanar da ita tasowarsu ta sanar dasu Joda,suka fara shiryen Shiryen taransu,duk da dama chan ashirye suke,gidan suka kara gyarashi sosai kafin su shiga kichen su dukufa wajen shiryama yan kawo amarya delious mai dadi cikin mutumci da kima.
Basu iso ba sai wajen 2 na rana suka iso,wanda Malika najin Sautin hon dinsu da kuma karar bude get,gabanta ya amsa ta tashi da Sauri Ta shige daki tana kokarin danne Abunda ya tasomata,Su joda da Maman Abba ne da Su zulai suka Fita suka tarbesu,Zahra dake cikin mayafi hankalinta na kan karema gidan da kallo,Haka take bin ko’ina da kallo har suka Shiga falon gidan suka zazzauna ana gaisawa ana tambayan gajiyan hanya,Joda ce kan gaba ta nuna musu dakin Zahra wanda ke kusa dana Malikan suka tashi suka Shiga da Zahra ciki,wacce dama ta kagu akaita dakinta taga wani iri ne.
Dakinta yana da girma,Shimfide da wani cafet mai taushi,wanda ya mamaye dakin gabadaya sai makeken rolay bed dinta da kuma Wardrope mai girma da Fadi,sai dressing mirror,sai kofar Tiolet,zahra a wulakance take bin dakin da kallo,Bawai dakin bai mata bane a”a so take taga na ita malikan ya yake? don ita zatonta Saleem ya raina mata wayau Ne Shiyasata ya sanya awannan dakin wanda da kadan yafi na gidansu inda take kwana.
Joda da Maman Abba da Zulai su suka dinga kwaso musu kololin abinci zuwa cikin dakin Zahra inda suka ga Abun mamaki amarya ta zaune kan tsakiyar gado ta cire dankwali shigen gashinta mai kama da Hammatan dan iska awaje,duk ya mike Kallo kowa daya daya take tana wani girgiza kafa,Maman Abba da joda suka kalli juna suna mamakin wannan al’amarin daga zuwa har za”a nuna hali,sai da suka Fita zahra ta kalli Nadira take cemata”Wai yan biki kenan,? hala bata da wasu dangi ne ita Malikar,koda yake sai dai in taron arna..,”
Tafada tana yar karamar dariya,Tsaki Nadira taja tana Fadin”kedai kike kidanki da rawanki,in banda Shiga Abunda bai shafi mutum ba,ina Ruwanki da danginta,kedai tafi wajen Shigen rawan kanki da Shisshiginki miji ya ram miiki,kinga ko kya ga karshen Rawan kai..”Goggo Shatu tace”Kwarai da ma gaske,ai tama baras,Nadira tunda ta yada hali gaban Uwar miji,mai ya rage kuma,ai babu Shi Nadira,Allah dai kawai ya sauwake…”
Zahra ta tura baki ta kauda kai tana dauko wayarta tacigaba da Laluban Nombar, Saleem ammh har yanzu bata Shiga kuma,sadiq yace batare suka taho ba shi yana baya gajiya tayi da kira ta hakura takoma gefe tana kallonsu Nadira na cin abinci,Farar Shinkafa,da miyan nama,sai Fride rice,sai kunun aya mai sanyi,da ferfesun Naman kaji,kallonsu take don ita babu abinci agabanta so take ma suyi su tafi abarta daga ita sai angonta.
Sadiq kuwa Joda tayi ta dawainiya dashi,bayan tabashi na Direban da zai maida Su Nadira ya kaimai,ya dawo yazauna falo yana cin abinci yana ma Joda hira har yana tambayanta Shi bai santa ba? tace mai ita kanwar Malika ce gidansu daya,Sai alokacin Malika ta Fito tana taku dakyar suka gaisa Da Sadiq yana kara kallonta kamar ba ita, ba kamar wata zara acikin wata,shi baima san cikinta ya tsufa ba haka don Saleem baya yarda yayi mganan Malika dashi,koshi ya jawo hirar Kauceta yake,ya basar.
Suna cikin gaisawa da Sadiq din sai ga Saleem ya Shigo gidan yana waya,yana sagale da yar jakan kayansa,Sai da ya katse wayar ya kariso garesu yana bama Sadiq hannu suka tafa yana Fadin”Kai mutumina kayi Wuta ahanya fa..”Yar dariya Saleem yayi kafin yace”Ah to mezan jira,ai ban saka lerna ba,balle na dinga na lallaba Titi..”Yafada yana kallon Malika dake tsaye tana gyara zaman mayafin kanta,Kwabemata Fuska yayi kafin yace”Ba sannu da zuwa Yar Amanata..”Batayi mgana ba,illah karisawa datayi gareshi tana saka hannu ta karbi jakan hannunsa tana Fadin”Yanzu fa ka shigo..”Sannu da zuwa..”Kin sakin mata jakan yayi saima Rumgumota dayayi ta gefe yana Shafa fuskarta yace”Bar jakanan kawai kinyi Nauyi dayawa kada na zama mara tsausayi..”
Ya fada yana shafa cikinta lokaci daya yake Fadin”Kai cikin nan yayi kasa sosai,koda yau zai Fito Duniya..? Sadiq ne yace”hhh karma kayi Fatan haka don zaka tashi daga angon amarya ka koma angon karni,wlh baka ba kwanan dakin Amarya sai dai kwanan Asibiti..”Dariya joda ta saka,shiko murmusaa kawai yayi Malika bata hakura ba jakar ta sake karba ya sakarmata yana kallonta Mirmishi tayimai tana Fadin”Kada kahanani samun lada awajen Allah…”Hannunsa ya daga yana Fadin”Wane ni? ai ban isa ba,Allah yabamu ladan dukkanmu..”
Batayi mgana ba. ta Wuce zuwa dakinshi,shi kuma ya tsaya suna gaisawa da joda da maman Abba data Fito yanzu sai Zulai wanda dama Malika ta sanar dashi zuwansu,har dakin Malika ya shiga suka gaisa da Goggo hadiza yana mata godiya,Yana Fitowa dakinsa na yawuce yabar Sadiq zaune yana mai tsiya,koda ya Shiga dakinsa nasa,ya tarar da har Malika ta hadamai Ruwan wanka,Mamaki ta bashi yadda yaga cikinta ya tsufa dayayi mata mgana sai tace zai hanata neman lada,sai ya kyaleta bai samu lokacin yaba lalliinta da kitson ta ba,sai da yayi wanka yayi sallah yaci abinci kana,haka yadinga Sumbatar hannu yana Shafa kanta,nan take ya bata 5k yace tabama wacce tamata lalli da kitso,domin zahirin batu yagani kuma ya yaba.
Sai wajen biyar na yammah yan kano sukayi Shirin tafiya,bayan sun gama jerama Zahra akwatunta sun mata yan nasihu duk da sun san baji zatayi ba,Nadira tayi kwaba tayi kwaban kamar bakinta zai Cire,ammh Zahra sai ta nuna taji,ammh kuma nan ko bata jin zata dauki mganarta,da zasu tafi sukace Zahra ta Fito su mika amanarta ga Malika,ammh sai zahra tace Allah ya kyauta tabi kishiya,sai dai in Malikar ta matsu ta shigo dakinta ayi mganar,ganin haka yasa babu wanda yakara bi ta kanta,da zasu tafi har dakin malika suka shiga don su gaisa lokacin tana dakin Saleem,sai da joda ta Fita taje ta kwankwansa musu ta kirata tazo suka gaisa cikin mutumci,daga karshe sukace ga Zahra nan kanwata take gareta,don Allah tayi hakuri da ita,su zauna lafiya da juna,don su samar ma mijinsu zaman da kwanciyar Hankali,sunji dadin yadda Malika ta karbesu sai sukaji ta burgesu sosai,domin ba haka suka samu lbrinta ba,domin ance bata da dabi”a sam,sai suka ga sabanin Tunaninsa,dazasu tafi haka sukayi ta sakamata Albarka da fatan Allah ya sauwaketa lafiya.
Sai da suka Fita haraban gidan kana Saleem ya Fito sukayi sallama ya basu kudi 3k sukuma Su joda suka Fito da Musu da kaji da meatpie da donout,din da sukayi musu wanda sukayi raping dinsu,suka basu suna ta godiya,Nadira dai mamakin ganin Malika take da ciki,don batajin ko Zahra tasan da cikin nan,don data sani da ta sanar da ita,Abun mamaki sai ga amarya acikin yan rakiya tana Rumgumesu tana daga musu hannu ammh Fuskarta babu alamun Rashin jin dadi ko Kuka ko damuwa,a’a fuskarta cike da Annuri.
Suna tsaye motarsu tatashi suka Fice daga haraban gidan Zahra na daga musu hannu,sai alokacin taga Malika wacce datake bayan Saleem,sai yanzu ta Fito ta gefenshi gabanta ne ya Fadi ganinta da turtsetsen ciki,wani karin Abun takaichin ma hannayensu sarke dana juna suna mgana kasa,kasa malika ke sakin mirmishi Daga ganin Wata mgana mai dadi yake gayamata.
Duk da ahoto tataba ganin Malika bata zata afili tafi kyau ba,koda ita da datake amarya bazata Nuna ma malika kyau ba,duk da ko cikin jikinta wanda yake hanata kwalliya,Babu karya kyanta ya daki zahra sosai balle ma cikin dake jikinta wanda ko Saleem bata sanar da ita ba.
Itako Malika Tana kallon Zahra ne cikin ilimi da wayewa,daga sama har kasa,tabe baki kawai tayi cikin ranta batace komai ba,Ganin yadda ta kura musu ido ne yasa Malika tayi kokarin Fizge hannunta tana nuna mai Zahra da baki,dagowa yayi yana kallon Zahra wacce ta harde hannu akirji tana kallonsu Fuskarta babu Fara’a ko kadan.
Da Sauri Malika ta isa ga Zahra tana mata Fara’a tace”Sannu da zuwa amaryarmu…”Tafada tana bata hannu su gaisa,baya zahra tayi da hannunta tana ma malika wani kaskastancen kallo na Wucin gadi kafin ta mele baki tana Fadin”,Yauwa sannu dai buh found of correction Hajiya malika amarya Saleem kabir kumo kidaina saka min jaye..”
Tafada tana wani yamutsa Fuska kamar taga kashi,wani nauyi da kunya suka kama Malika ta sauke hannunta asanyaye tana mirmishin yake kafin ta kada kai kawai ta Wuce cikin tanajin yau fa kenan,? lalle akwai aiki ja agabanta game da amaryan mallam,Shiko Saleem waya ya tsaya yanayi wanda Sadiq ne ya kirashi yana sanar dashi har ya kusa isa garin Abuja motarshi ta samu mtsala,ammh zaiyi ma bakanikensa waya,shiko yanzu zai bi motar haya zuwa Abuja,so duk Abunda yafaru baida masaniya,yana kokarin yanke kiran ne yaga Malika ta wuce cikin gida,itakuma ta zahra ta matso inda yake tana mai wani kallo kamar ta lasheshi danye bai gasu ba
Tana karisowa kusa dashi ya yanke wayar yana binta da kallo,riko gefen hannunshi takama Tana Fadin”,Haba Honey Shikenan kuma tun jiya bankara ganinka ba…”Tafada tana saka kanta bisa kafadanshi,ganin megadi awajen karya dizgata yasa yadan riketa suna tafiya zuwa cikin gida yace”Ai yanzu ina tsammanin korafi ya kare ko? Tunda gaki gani,naga Yar Amanata taje kun gaisa,hop kin gaisheta da kyau Antynki kenan Malika Abdulmalik dankasuwa matata ta farko kuma uwar ya’yana..’
mganar ta zafeta Shiyasa ta tabe baki batace komai,shima ganin haka sai yaja bakinshi yayi Shuru,suna shiga falon suka iske Joda da Maman Abba,sunsaka hijabai zasu Fita da alama zataje gidan Maman Abba gabadayansu ganin Zahra rike da angonta Abun yabasu matukar mamaki sudai a al’adan bahaushe amarya tana kunshe adaki tana fargaban zuwan angonta,wasu ma saboda kunya ko siyan bakin akayi basu iya budeshi suyi mgana,ammh yau agidan Saleem suke ganin wani sabon salo,ai Tusa da lasifika😂
Irin kallon da suke binsu dashi ne,yasa Saleem dan jin kunya yana kokarin raba rikon da Zahra tamai ammh taki sakinshi saima kara kwantar da kanta take bisa kafadanta,Girgiza kai kawai yayi yana basarwa nan sukayi sallama da Maman Abba,wai ashe Zulai da joda ta dauke zasuje gidanta su tayata kwana Abba da babanshi suna zaria wajen maman mijinta,Goggo Hadiza kadai aka bari,wacce duk kunya saleem ya takuramata tana cikin dakin Malika bata ko Fitowa falo,takuma gayama malika gobe da Safe zasu koma malumfashi insha Allah.
Har su joda suka Fice bata sakeshi ba bai sake mata mgana ba,illah hanyar dakinta daya nufa,sai da yabari sun Shiga kana ya Saketa yana kallonta kafin yace'”Wai miye haka…? Sakarni alwala zanje nayi na samu jam’i kema ki gagggauta yin naki sallar..”Tura baki tayi tace”Toh ina zaka? baga tiolet anan ba,ka shiga muyi alwalan tare..”Tafada tana kokarin kwantomai bisa kirji,ganin haka yasa yayi Saurin Fadawa tiolet ta biyo bayanshi sukayi alwala yana Fitowa yayi hanyar Fita tayi zaraf zata biyoshi ya waigo cikin haushi yana Fadin”Ina kuma zaki bini..Ehe..?
Diddira kafa tahauyi kafin tace”Inda zaka mana,don naga baka da niyyar sauken alqawarin dakama iyayena wajen kula dani da rike amanata…”,Tafada harda matso kwallar Karya,kansa ya dafe kafin ya karisa gareta ya riko hannunta yana Fadin”Injiwa… ? wayaga miki bazan kula dake,kinga ana kiran sallar mangariba,sauri nake naje na samu sallar cikin jam’i ko baki son ace mijinki yana kokarin yin sallar cikin jam’i..”Kallonsa tayi kafin tace”Ina so mana..”Da hanzari yace”Toh kibarni naje nayi na dawo,saurin mekike,yau ba tare zamu kwana ba..”,Da hanzari ta gyadamai tana Mai wani kallo,Sakin hannunta yayi yana gyara hulan dake kanshi yake Fadin”To kingani,oya Kema kiyi sallah asakemin wata sabuwar kwalliyan wannan ban Amince inci amarci da ita ba.,Sai na dawo..”Ya fada yana karisa Ficewa daga dakin,Sufa tayi ta haye kan gado tana Rumgume Filo cike da murna,cikin rawan jiki tatashi tayi sallar ta Tube kaya ta Fada tiolet tayo wanka akazo aka shafama lotion kafin abi kowani lungu da sako na jikinta da Turare,Wai saboda rashin hankalin zahra wai Tunda Saleem yace ta sake kwalliya to kwalliyan kayan barci yake Nufi batayi sanya ba ta bude akwatunta na inners ta zabo wata arniyar riga wacce tsawonta bazai gaza cinyarta ba,gata da budadden gaba,gata kuma raga raga,pant kawai ta sanya babu bara,sai ko gabadaya halittan kirjinta suka bayyana waje,tana kallon kanta amadubi tana jujjuyawa take fadin”Haba dole ya raina kansa in yaga wannan kayan,yasan nawa ba irin nata bane…”
*
Shiko Saleem bai dawo gida ba,sai da yayi sallar issha’i kana ya dawo,kuma koda ya dawo bai Shiga dakin kowa ba sai yawuce dakinsa yayi wanka ya sanya jallabiyansa Mai Ruwan toka kafin ya dauki wayarsa ya kira Malika yace tazo dakinsa ta sameshi yanzu,bayan ita sai ya kira Zahra yace itama tazo dakinshi ta sameshi yanzu,Jin kiran dayake mata sai bata kawo cewa harda Malika ya kira ba,ita atunaninta kila chan ne zasu first nigt dinsu😂ai bata tsaya sauyawa kaya ba sai ta kara gyara fuskarta gyalen kawai ta yafama kanta,bata kuma Fito ba,sai da ta kada wani garin mgani tasha da madara kana tafito tana rarraba ido,ganin dakin daya ke hari dazu sai ta sa aranta nan ne dakin saleem din.
Da confident dinta ta Shiga,Cikin Siririyar Sallamarta,Turus tayi ganin Malika zaune akasa ta mike kafafunta,Shikuma Saleem yana rawan jikin jeramata Filulluka,bayan yagama yakoma mtsamata kafa,yana mata mgana kasa kasa,cikin ran zahra tace durun uwa Salatin Arna😂😹ita za”a torzata,tsaye kawai tayi hannunta bisa kugunta tana jifansu Da wani mugun kallo,Malika ce ta ankare da ita sai ta tabo Saleem ta nunamai Zahra,ganinta ahaka kafafu duk awaje yasa ya zaro ido😳😳Lokaci daya yana Fadin”,Zahra lafiyanki kalau kuwa..? Kinga yadda kika Fito marabanki da tsirara kadan ne..”
MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
