Maleeka Malik – Chapter Three
by NadminMASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
Acikin jerin mutane na 8 masu Fitowa *MALIKA* tana daya daga ciki bayanta kuma Amintattun Excorts dinta ne joy and peter,sanye cikin bakaken court kowanne ya toshe bakar Fuskarsa da wani makeken bakin gilas,Joy shike rike da Brief case dinta,wanda manyan bayanai game da document na kamfafonin mahaifinta ke ciki,ma”ana kowani Kundin bayanai,Shiko peter dama kullum dan Rike jaka ne da wayoyi dama aikinsa kenan.
Yau din ma tana sanye ne cikin shigarta,buh na yau Suit tasaka na mata riga da sikat,Ash and white,wanda sikat din,da kadan ya wucemata gwiwa,Fararen kafafunta kal,duk suna waje bayan ta kawata kafarta da wani Ash din cover,wanda yake da dan Dudu,Yau anci sa”a bayan ta dane gashinta atsakiyar kanta ta Makaleshi da band,tasaki jelan ta baya,sai ta dora wani ash din vail,ta yaneshi daga tsakiyar kan,Fuskarta sanye da wani glass,mai duhu wanda ko kwayan idonta baka iya hangowa.
Farace Tar sosai,irin Farin ne bamai launin jaja ba,Doguwa ce ammh ba sosai ba,Allah yabata wani Abu waishi tsarin hip,ga kuma madaran shanu suma babu laifi,daga tsayenta tana da Shape din,cocacola ne,Hancinta ba dogo bane sosai,ammh yadace da Doguwar Fuskarta,mai dauke da karamin bakinta,wanda yake Fari tas,shima Gashin idonta zarazara ne kamar yadda idanuwan nata keda girma,Gashin giranta ko baki silif,yana ta Sheke,.
kallo daya zakamata Kazata wannan bata hada komai da Hausa Fulani ba,kai infact ma, zaka zata irin bakin nan,ne dake Shigowa Nageria harkan kasuwanci ,daga yanayin dresssing dinta da yanayin yadda take mgana zaka Shaida tabbas wannan ko Aturawan takai makura.
*MALIKA MALIK..”* Kenan Y’a kwaya daya Tak,ga *ALHAJI ABDULMALIK DAN KASUWA* Wanda saboda kudinsa da tarin kaddarorinsa da kamfafononi,tundaga gida Nageria har zuwa kashashen ketare,yasa ya zamanto cikin jerin masu kudi na hudu A kasarmu ta Nageria.
Tana Saukowa daga kan Step din jirgin Tuni dama motocinta tare da Sauran Excort dinta sun zo daukanta,Duka motocin wannan karan 4matic ne,kuma 12 ne,kowane akwai tambarin *MALIKA MALIK*1 har zuwa 12 akallah excorts dinta masu tsaronta zasu kai su ashirin,kuma babu dan musulmi ko daya kuma babu jinsi mace,duka mazane kuma wasu gardawa konace samudawa,Tunkafin ta kariso suka bude mata Daya daga cikin motocin,ta Fada cikin isa da takama,nan da nan kowa yakoma motarsa suka bata Wuta sukabar Aiport din aguje,babu wanda ya damu domin indai malika malik ne kaf Nageria,yaro da babba babu wanda baisanta a Talabejin ba,in ma Mutum baita ganinta ba,to babu Shakka yasan lbrin sangarta tare da lalacewa ta malik malik,da sunan wayewa ko kuma nace GATA.
*
_KATSINA_
*GRA*..
Cikin Gra ne Tamkamemen gidan mahaifinta yake,mai kama da yanki Guda saboda girmansa da kuma Fadinsa,inda za”ayi Estete,tsab za”a iya yin guda 40 kuma kowanne da girmansa,Hon suka zuba masu gadin dake sanye da Uniform sukazo suka budemata don sunsan hali,minti daya suka kara korace Awajenta.
lokacin da motocin suka Fara sulalawa parking space,kowani Excort ya fito daga motarshi yana bin motarta da gudu bata tsaya ba,sai A babbar kofar da zata sadata da cikin babban Falonsu,Budemata sukayi jikinsu na Rawa masu,gadin kuwa fadi suke”Wlcm back madam…”cikin isa ta zuro kafarta waje kafin ta bayyana waje Fuskarta babu Fara”a ko kadan bata kallesu ba,kawai tafara Tafiya joy da peter suka take mata baya,ajiyar zuciya sauran suka saukesu,suna Fatan yasa anrabu lafiya kenan.
Tana Shiga Falon wanda ya kawatu dawasu royal chairs hadaddu masu kyau da tsari sai wani tamkamemen plasma,daya kusa cinye rabin bangon dakin,ko sallama batayi kamar ba,don ba dabi”arta bace, *HAJIYA BINTA* ,Dake zaune tana kallon Atashar Arewa24 ta dago tana kallon Malika wacce ko kallonta batayi ba,saima zuwa datayi ta gabanta zata Wuce,tasa Tudun takalminta ta murje mata kafa,Azaban da Hajiya binta taji ne yasa ta saka ihu,wanda ya Fito da Alhaji maleek da hanzari wanda ke kayatattacen Falonsa na sama yana hutawa,Dattijone don zai iya kai shekara 67 aduniya Abun mamaki baki ne silif,ammh kuma yana da kyau da hanci,Fuskarsa tacika da Farin gemu ammh kana kallonsa zaka Fahimci Farin gemun na halitta ne ba wai na Tsufa bane,domin duk inda jin dadi da Hutu yake toh Alhaji Malek na tare dashi,don Shida iyalansa basayin wata Daya A nageria sai Sun Fita waje sun Huta.
Ihun Hajiyane yafito dashi yaga ko lafiya,ammh sai ya ci karo da Malika tana kokarin karisowa gareshi da hanzari ya tafi gareta yana Fadin”Wlcm back my Sweetbbby….”Yake Fada yana Rumgumeta matseshi tayi tana Fadin”Dddylove i really miss u…”Kiss yayimata agoshi yana Fadin”Miss u more Sweetbby,yanzu mrs Suzan takirani tace komai yayi daidai..”
Wani mirmishi tayimai Tana Fadin”U know me Daddy,bazan taba baka kunya.”Wata Dariya yasa yana Fadin”Hhhh..Datz my Sweetbby,maza ki wuce daki kiyi wanka ki Shirya ki sauko muyi lunch..”Tabe baki tayi kafin ta cire glass din idonta tana Fadin”No not now, Daddy naci abinci a cikin jirgi,but now zan Shiga in huta sai na Fito we tok later..”Shafa kanta yayi yana Fadin”ok maza my Sweetbby ahuta lafiya karki sake kitashi sai around 6 haka kinji..?”Kai tadagamai tana bashi kiss a kumatu tace”Daz why i love u,my Daddylove much wlh..”dariya yayi kafin Shima ya maidamata da kiss din,da hanzari Ta nufi wani Daki dake kusa da Inda Abbanta ya Fito tana Shiga dakin su peter suka rufamata baya.
Alhaji Malik ya kalli Hajiya binta yana Fadin”Lafiyanki kuwa naji ihunki daga sama…? dagowa tayi daga murza kafarta, datakeyi Yar matashiyar matace wacce ashekaru bazata gaza 36 aduniya ba,farace tas,ammh tana dan jiki,idonta cike da kwallah tace.
“Haba Alhaji,malika ce fa tashigo babu ko sallama kamar ba yar musulma ba,kuma don rashin kunya tabiyo tagabana zata wuce hakan bai isheta ba,sai da ta takani da Katon takalminta mai Tsini..”Tafada cikin takaichi.
Tsaki Yaja yana Fadin”Gaskiya Binta fitinarki da tseguminki yafara isata fa,Haba kin sakama yarinyarnan ido,ita da gidan Ubanta in bataji dadi anan ba,waje kikeso taje taji dadi ehe..”?Yafada yana tsareta da ido.
Kallonsa tayi baki bude tana Fadin”Ammh tsakani ga Allah Alhaji Abunda Malika tayi yanzu ya kyautu..?”Hannu ya dagamata yana Fadin”Kinga Binta kifita daga idona indai akan Malika ne,banda Abunki nawa malika take,haryanzu fa yarinyace wani Abun sai ana nusar da ita,kuma kibar wannan mganar kada ki kuskura ki tankamata,yanzu nan sai takama Fushi,kuma kinfi kowa sanin yadda Fushin malika yake awajena Atoh.”Yafada irin Abun ya isheshi haka,ya sa kai yakoma cikin kayatattacen Falonsa bayan ya saki Siririn tsaki.
Hajiya Binta ta bishi da kallo tana kada kai,idonta ya ciko da hawayen takaichi da kuma haushin iyayenta da suka biyema Rudin Duniya da kuma tarin Dukiya suka kawota inda ba”a san mutumcinta ba,daga Uban har yar duk basu da mutumci babu wanda ke ragamata.
Dauke hawayenta tayi tana mirmishin karfin hali,Tuna duk mutuwa ce taja mata wannan Tonon Sililin,da”ace Abban *JODA* na raye ta tabbata da bata auri Alhaji Malik ba,balle har tazama Abun wulakantawa awajensu.
Mikewa tayi rike da wayarta tashige wani korido tana kwalama Atika mai aikinsu kira,domin ta umarceta ta shirya lunch bisa Dinning area.
Katon Falo ne,wanda yaji kayan alfarma,Tunda tashiga tafara yadda kayanta,Tacire vail ta Wurga ta cire band din kanta,ta warware gashin kanta bayan ta Fara cire botir din Rigarta gabadaya halittun kirjinta dake jikin beriziya suka bayyana,Peter ko da joy suna tsaye kyam,don madam bata basu daman Tafiya ba,Indai Tsiraicin Madam ne,Su Tuni sun dade da haddace kamminshi don bata da kunyan idon maza,Hatta Swining pool in zata wanka tare dasu take zuwa tayi Tsirara daga ita sai pant agabansu ko gefen gyalenta.
Murya ta saka tana Fadin”Merry…Dose…”Take Fada cike da Fushi sai gasu sun Bude wata kofa sun Fito da gudu agabanta suka zube suna Fadin”Srry madam…SrrrY…”Wani Wulakantattacen kallo take binsu dashi kafin ta sanya kafa ta shuri merry sai da ta kifa,lokaci daya ta gaurama Dose mari tana Fadin”U too u are Animal,..”Take Fada tana huci Baya sukayi suna kuka suna bata hakuri da hannu ta dakatar dasu kafin tace”,last chance…”Bata gama Rufe baki suka mike daya tafara kokarin ciremata takalmi daya kuma tafara kokarin karisa balle mata botir din Rigarta bayan ta ciremata Coat da hannu tayi musu peter alamu, sai kawai naga sun nufi wani kofar glass,wanda sai da ta dauki hoton Fuskokinsu ashe Na”urace awajen kafin ta bude musu su Shiga,sun Shiga ba dadewa sai gasu,sun Fito wanda kafin Su Fito sai da Na”uran tagama cajesu tsab ta tabbatar da basu tare da komai kana ta barsu suka Fito,suna Fitowa tayi directing dinsu da hannu alamar su Fita,kai tsaye suka bude kofa suka Fita,bayan su merry sungama cire mata duka kayanta,harda bra da pant tsiraranta haihuwar uwarta suka dagata tsab,sai cikin katon bedroom dinta inda katon Tiolet dinta yake,wanda yaji kayan alfarma kyace baza”a mutu ba,cikin jazucci suka sakata bayan suncikashi da wani Ruwan kumfa,Dose ce ta Fice ita kuma merry ta fara Yimata wanka tana kwance ta lumshe ido ko agefen gyalenta..
Niko nace *KUTUMAR UBAN CHAN*😿
Dose na Fitowa takoma kayattacen Falon ta kwashe duka kayanta,kafin takoma Toilet din ta watsasu cikin wani dogon kwando na tara kayan wanki,Fitowa tayi kafin ta isa wani makeken Abu wanda ke dauke da glass,ashe Na”urace Sai da Ta tantance Fuskar Dose kafin wata yar kofa ta bude,Kayane jere cikin tsari iya kallonka mallam,dogayen Riguna,riga da wando ne,suit ne mini sikat da mini wando,Duk sagale cikin hanger,kai kace ka shiga bouitque ne,Wata yaloliyar Doguwar Riga ta daukomata wacce marabanta da Tsirara kadan ne,saboda tasan yanzu barci zatayi kuma iyakarta gwiwa,ta Fito mata dashi kafin kuma wajen ya Rufe kansa,Sun dauki tsawon minti talatin atiolet din kafin Dose ta kuma suka daukota wacce suka nannade da wani katon Towel,suka zo suka ijyeta kan wani dogon Stool,ban gama mamaki ba,sai da naga tana ta Shafemata da mayuka masu tsada itako tana zaune idonta na lumshe,har tagama ta fesheta da body sray,Dose ta matso kusa tana gyaramata zaman gashinta wanda yadan jike kadan da Ruwa,tana kokarin kunna Hand drayer,ta dakatar da ita,da hanzari ta dauko yar Rigar data dauko ta ziramata wacce ta Fito mata asalin tsarin kirjinta,tunda babu bra babu pant,Dose ita kadai ta dagata bata sauketa ako”ina ba sai akan wani gado,mai kama da alkaki saboda yadda yake amulmule,wani karamin Filo fari dake gefe ta Rumgume tana lumshe ido,Katon blanket ta dauka ta Rufamata shi har zuwa Kanta
Gefe suka koma ko motsi basuyi suma dana kallesu suna sanye da Riga fara,sai bakar biri da wando,sai Hula akansu kace wasu ma”aikatan hotel,sai da tasha iska kafin tadaga musu hannu,da hanzari suka kada kai suka Fice suka jawomata kofar,nan kowaccensu ta maida hannuwanta abaya,domin akidar madam in tana barci babu mai tashinta sai ta tashi da kanta,kuma zata iya bukatan wani Abu,kuma in tamaka kira daya baka zo ba,korace sudinma tana daga musu kafa ne don tana jin dadin zama dasu.
_________________
*ABUJA*
“”Duka iyalan gidan sun hallara bisa babban Dinning area,mai kama da Fili guda,ajiyane da daddare suka kara samun Zuwan wani dan gidan,bayan Saleem,wato Ya marwan wanda yake aiki alagos,Zaune suke dukkansu suna breakfasrt suna dariyan hajiya wacce ta sanya kujeranta kusa data saleem,Ummi na kokarin saving dinta,tayi Saurin Tsoma hannu a filet din gaban Saleem,wanda yake cike da Soyayyan dankali da kwai,bata Fuska yayi kamar yayi kuka,itako hajiya ta cika baki hartana maida Saura a Farantin,Ummi tana Dariya tace”Hajiya ki barmishi kayanshi bari na zuba miki naki..”..
Hajiya ta gyara zama tana Tsungulin Saleem tace”Barni Aisha yau tare da Ja”irin nan zan karya..”Tafada tana kara saka hannu ta cika baki,har miyau dana baki suna biyowa,Kauda Fuska Saleem yayi yana Fadin”Na Shiga uku Ummi,kalli harda miyan bakinta take sakamin..”Dunguremai kai tayi tana Fadin”An saka din,don kaniyarka,Wlh in kaja tsiya zan maka kaki yanzu nan,kuma wlh na matseka saika hadiye,..”Tashi yayi da Sauri yana kakaro amai,tako damke hannunsa gam,taki sakinsa,Ya marwan dashi da Saleema suna ta tsintsiran dariya Abbi na zaune yana kallonsu,don yasan koyayima Hajiya mgana baji zatayi ba,Ummi ko bata saka baki ba,sanin halin hajiya in Tafara Abu bata iya bari,Saleem din ne kadai mganinta.
Gani yayi tasaka karfinta tana Rikeshi tana neman ta maidashi inda yatashi,Ganin haka yasa ya rike mata hannu yana Fadin”Sakarni kiji wata mgana..”Hararansa tayi tana gyara daurin dankwalinta tace”Anki din,ni zakama wayau,ai wlh yau in har ba lbrin kasamu matar aure zakamin ba,ko ubanka kabiru bai isa ya kwaceka ba,sai kasha majina na..”Tafada tana kebe Fuska,Ummi ce ta rike baki tana bin Fuska Saleem da kallo…
Shuru yayi yana bin Hajiya da kallo kafin yace”Really,,? kina son nayi aure kenan hajiyata..,?”Jin haka yasa ta washe baki cike da goro tace”Sosaima Haba Salihu,kunfa girma kungama balagewa asannin haihuwarku a kumo harda masu mata biyu,bama daya ba..”Rausayar dakai yayi yana Fadi cikin Ransa” Dis iz d right Time….”Yafada kafin yakalli hajiya yana Fadin'”,kamar ko kinsani Hajiya mganar auren ce tadawo dani wannan weeked din..”
Kowa dake wajen yadauka yanamata wasa ne don ta sakeshi,shiyasa harda Ummi amasu dariyan,kura masa ido tayi kafin tace”Da gaske kake Salihu..? Gyada mata kai yayi kafin yace”Eh da gaske nake Hajiya ina son kisa baki Abban yaje nema min auren yarinyar danike so..”
Jin yadda yayi mganar babu alamun wasa yasa kowa yadaina dariyan dayakeyi hatta Abbi dake ta cin abinsa sai da yadago yana kallon Saleem,wanda ya kurama waje daya ido,Jansa kan kujeran daya tashi Hajiya tayi bakinta yaki Rufuwa tana Fadin”Alhamdulillah Allah yakarbi Addu”a ta,to maza ga kabirun nan,sanar dashi wata yarinyace,Allah sa dai yar gidan Mutumci ne..?Bai wani Damu ba kai tsaye yace””Ba wata bace illah Diyar shahararran Dan kasuwan nan wato *ALHAJI ABDULMALEEK DANKASUWA*…”
Gabadayansu suka razana da jin zencensa saleema data tura chips abaki sai da ta Furzoshi waje,Shiko Ya marwan,yakafa kai yana kurban coffoe,sai da ya kware yafara Tari sama sama,Ummi dake zaune sai da ta mike hannunta dafe da kirji shiko Abbi kasake yayi yana Bin Saleem da kallo,wanda yayi saurin boye razanar daya ga sunyi Afuskarsa.
Saleema ce cikin Rudani tace”Ya saleem Wai wakake Nufi..? Kai tsaye yace mata..” *MALIKA MALIK..”*…Da ita da Ya marwan sai gasu tsaye suna zaro ido atare suka Furta..”,Bura uban chan…”
Suka Fada suna kallon Saleem kamar wani tababbe,Hajiya datake nazartansu tace”Kai wai miye haka daga Fadar suna,kun shiga Rudi lafiya meyake Faruwa ne..? Ya marwan ne yace”Komai ma yafaru Hajiya bakiji sunan daya Fada bane..?Tabe baki Hajiya tayi tana Fadin”Wannan bai dameni ba,indai yar gidan mutumci ne,Amemasa aurenta Tunda yana Sonta..”
Wani kallo Ya marwan,ya ke Wurgama Saleem,wanda yaki bada damar Ya kalleshi balle ya Fahimci wani Abu,To waima yaushe Saleem yataba haduwa da Malika,yarinya da Da Namiji ma baya gabanta? Bai gama mamaki ba yaji saleem na Fadin”Nidai hajiya gashi na kawo wacce nake so don Allah ki matsawa Abbi yaje gun mahaifinta ya neman min Aurenta,kuma one anoder thing,don Allah Abbi karka sanar dasu Aikina,ka sanar dasu ina aiki da hukumar costome ne,in komai ya daidaita zan sanar da ita dakaina plz Abbi..”Yafada yana hada hannuwansa kafin ya Ture hannu Hajiya dake Rike dashi ya Nufi hanyar dakinsa da sassarfa Saleema da ya marwan suka bishi da kallo baki sake.
Hajiya ce ta kalli Abbi,wanda yacigaba da karya wasan tana Fadin”Kabiru maza ka hanzarta,Tunda daga jima kasan mahaifinta Tunda kaima babba ne agwannatin,Tunda har ya nuna yanaso to gwara agaggauta yimai kaji ni ko bakaji ni ba..?”Batare dawani Tunani ba Abbi yace”Insha Allahu hajiya zan kira mahaifinta awaya mufara mgana dashi abokina ne,tare mukayi Dan Fodiyo dashi ammh bayan mungama Zumunci yayi Rauni..”
washe baki Hajiya tayi tana Fadin”Kajima ko,to maza kabar zencen kira zuwa zakayi don wannan mganar bata waya bace..”Gyada kai yayi yana Fadin”karki damu hajiya komai zai daidaita..”Hajiya na murna tana ta sakama Abbi albarka,Ta mike tana kallon Ya marwan tace”Andai ji kunya babban banza,har kaninka yafika sanin ciwon kansa,kadai je,kayita yawo a iska haka zaka zo ka koma,wlh in ka mutu,ana sadakan uku zan saka asallami kowa,daganan kowa ya manta dakai,Tunda ba wani mgaji gareka ba,balle akalleka Atuna ka”Tafada tana Wucewa rai bace.
Ummi dake zaune takalli Abbi tace”Yallabai kako gane wata yarinya Saleem yake mgana..? Hannu yadagamata yana Fadin”mubar wannan mganar Aisha zamu tattaunata letter..”yafada hankalinsa kwance.
Ajiyar zuciya Ummi ta sauke kafin ta mike tahaye sama ranta bace,Saleema tabi bayanta aranta tana Fadin”Lallema ya saleem,ya daukoma kansa dala ba gammo,inma ta yarda zata aureshi don ita ko Qur”ani aka bata zata dafa ta karyata Cewa Ya saleem da malika malik suna soyayyah macen da bata san Darajan kanta bama balle hartasan da wani..”Saleema tace afili”kilama ta girmeshi wlh, yarinya kamar arniya wacce bataga Ruwan musulunci ba”Tafada tana bin bayan Ummi da Sauri taje tasanar da ita kamar ta wahalar da kanta bazai samu damar Auren wannan yarinyar ba,.
Shiko ya marwan bayan Saleem yabi koda yazo dakinsa sai ya tarar da ya rufe da key,jinjina kai yayi yana fadi Cikin Ransa”Ka Rufe kan ka mana,Tunda karasa wacce zaka Furta zaka aura ko wasa ne,sai wannan watsatsiyar yarinyar..”Yafada yanajan tsaki ya wuce dakinsa,yana ayyana tabbas akwai yarinya haryanzu Atare da saleem….
MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
