Maleeka Malik – Chapter Thirty-two
by NadminMASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
………………Malika Saboda gajiya dakyar ta iya tashi sallar asuba koda ta idar idonta na Rufewa ta koma bisa gado,wani barci mai Nauyi ya sake Daukanta bata tashi ba sai pass 10 lokacin data tashi har Saleema tama Ayda wanka ta goyata,baki ma Tuni sun yi wanka sun karya Wasunsu Duk Sunyi Shirin Tafiya expecillay kawayen Joda da suke Zaria da kaduna Wadanda sukayi mkranta tare.
Yan kumo ma koda tatashi Tuni motarsu ta mika,lalle tasha barci itama wankan tayi ta Shirya cikin Wata Atamfa blue mai kwalliyan pourple ajikinta,Ta daura dankwalinta irin Daurin Zahra buhara,Sai da ta karya kana ta Saka babban Mayafinta ta yane kanta dashi kafin ta Fita tana gaishe da Ummi da Ya marwan Data ga suna mgana,Saleem na Wajen Shida Sadiq gaishesu Tayi Sadiq ne kadai ne ya amsa cikin sakin Fuska,shiko Mallam Fuskarsa ba Annuri ya amsa mata da lafiya lau,daganan ya Dauke kai Duk da yana Satan kallonta ta Gefen ido domin ba karya ta mai kyau sosai a ido kamar yatashi yaje ya Rumgumeta ya fadamata irin missing dinta dayayi ammh bazai iya ba,Tunda ita datayi laifi ta gagara bashi hakuri shiko bazai bata, sai sun koma gida suciga ba daga inda suka Tsaya.
Daganan Shashen Da’a Sauki su Joda Ta nufa taje suka gaiggaisa chan tama tarar da Saleema,sai lokacin taga Ayda wacce ke barcinta lum abayan Saleema,ko da tashiga Duk suna ta haraman Tafiya ne,nan sukace tama ya marwan mgana Kawayen Amarya zasu Wuce,awayar Joda ta kirashi ta Sanarshi yace Su Fito koda suka Fito sukama Ummi sallama ta basu 20k tace su raba kafin Marwan yasa Direba ya kwashesu Zuwa tasha su hau mota su hudu Ne Shima 20k din ya basu yace Suyi na mota suka karba suna Godiya
Koda Azahar tayi gabadaya yan kawo amarya sungama Shirinsu suka taso keyar Amarya Joda Zuwa Falon Ummi suka Damka amanarta gareta tare da yan Nasihu sai manya Robobi guda biyar,Daya na cincin,daya na Dubulan,daya na Alkaki,daya na hikima,daya na Nakiya,sai Buhun shinkafa Biyu dana Tuwo daya sai kwalaye suma Sunfi Ashirin gasunan burjit,ba laifi dangin Uban Joda sun mata kayan gara Sosai kusan katsinawan Dikko akwai kaya da Babban Harka.😂
Ummi tayi ta Fadan meyasa suka Wahalar da kansu,sukuma sukace ai bakomai an zama daya basu zauna ba Suka bar Joda nan suma Direba ya kwashesu Shi zai maidasu Malumfashi,bayan Ummi ta cikasu da kudi da Turaman zannuwa aka Rabu cikin Mutumci da karammawa.
Sai Da daddare kana Abbi ya tarasu gabadayansu yayi musu Nasiha da Fada mai Ratsa jiki,wanda kowa Nasihan Abbi ya Shigeshi musamman Wajen da Abbi ke Nusar dasu hakuri da Mazajensu da kuma girmama Aure wanda Abu ne mai matukar amfani kana ya horesu da yaki da Shedan azamantakewarsu komai ya Shiga tsakaninsu na bacin rai kada su kullaci Juna Su tsaya su Saurari uzurin Junnsu su kuma ba junansu Hakuri wanda indai Sukayi haka Har Abada bamai jin kansu,kana daga karshe ya Horesu da su zama Tsintsiya daya madaurinta daya Domin Dukkansu yanzu sun zama Ahali Guda Daya,koda akabama Ummi damar mgana bata ce komai ba Domin tace Abbi ya gama mgana Albarka tayi ta saka musu,Hajiya ma ta tofa albarkacin bakinta daga karshe ta karke musu da Tsiya da mutunin nata Saleem,wanda yake Wani cin mgani,kamar wanda akama Dole.
Tare Sukayi Dinner dukkansu Harda amarya da ango wanda ya zaku abashi dama ya kebe da amaryansa,Aiko suna gama cin abincin Abbi da Ummi suka Haura sama,shima yaja matarsa suka Fada dakinsa suka yi lum dasu,Sadiq ko afalo suka yada zango Shida Saleema Suna Hira,Saleem ko Dakinsa ya Shigo yana Dauke da Ayda ganin haka yasa Malika komawa dakin Saleema ta kwanta tana Tunanin mafita,Aranta taji komai ya sauka Duk Fushinta itama ta Saukeshi Takuma kudiri niyyar bama mallam Hakuri da Zarar sun koma gida
Barci yafara kwasanta taji Bude kofa da Shigor mutum kamshin Turarensa kadai ya tabbatarmata da Shine,sai ta kara lafewa jikin katifa kamar mai barci gabanta yazo ya Tsaya yana Dauke da Ayda Wacce take ta Sharar barcinta cikin Aminci,Dukawa yayi ya Kwantar da ita gefen Malika yana yafa mata blanket din da malika ta Rufe rabin jikinta dashi…
Hannayensa Duka ya Tura acikin aljihun Wandon barcinsa na pjm,Yana kallon Fuskar malika cike da so da kauna Hade da Wata kewa,Rankwafa yayi yana kallon karamin bakinta da kirjinta wanda ya kara cika,Kamar zai kai hannu ya Shafa mata Fuska sai kuma ya Fasa,yana tsuramata ido saboda yaga kamar tana motsi kenan ba barci take ba,Asirinta ne ya Tonu da mirmishi ya Subucemata bata Shirya ba,Agaggauce ya dago yana Kara Tamke Fuska yayi Saurin Juyawa zai Tafi ta damko hannushi da Hanzari,bai waigo ba yace cikin muryan Dakewa
“Meye haka kuma..? plz leave my Hand..”Yafada yana jin Wani iri kawai yadda ta kamkame hannun nashi,Jin Haka yasa sai ta kara narkewa cike da Shagwaba take Fadin”Haba mallam..,Ni..Ni ko nice fa Yar Amanarka kadaina sona ne yanzu..? Muryanta ta narkar dashi ya dago yana kallonta yadda take wani lumshe ido Baki ya tabe kafin yace”Keba Amanata bace,don da kin dauki kanki ahaka da bazan hanaki Abu ba,ki mtsama sai da kikayi,Mganar ko na Daina Sonki ne Eh na daina Sonki ko da mgana ne..”Yafada yana Tara gashin Giransa waje Daya.
Mirmishi ta sakarmai tana kokarin mikewa kenan Sai ga Saleema ta Shigo,ganin hannunsu sarke cikin na juna yasa ta koma da baya tana Fadin”Oh!Srry…”Tafada tana kunshe dariyanta ganin yadda ya Saleem yake maka mata Harara,Ganin haka yasa malika ta sakeshi tana kallonshi bai kara bi ta kanta ba ya Fice daga dakin Duka hannuwansa suna cikin Aljihun wandon barcinsa kamar wani basarake.
Girgiza kai tayi ta mike daga Kan gadon Tiolet ta Shiga ta Dauro alwala tazo ta yi Shafa’i da Wuturi kafin tayi Shirin barci ta kwanta tana Tunanin mallam dinta wanda tayi Kudiri Niyyar sai sun koma Zamfara zata Shiga Fagen lallashi Ta lura bazai sauko da Wuri ba,har tayi barci Saleema bata Shigo ba itako Saleema dakin Hajiya taje tayi kwanciyarta Azatonta ya Saleem zai kwana wajen Malika ne,Tunda ya Sadiq na dakinshi.
*
Washegari Tun 7 Saleem yakai Sadiq airport inda ya Shiga jirgi yakoma wajen aikinsa,itama Saleema koda karfe 9 tayi ita da Direba sunyi nisa ahanyar komawa kano,dama Weekend ne tazo,suna da aiki sosai a asibiti ,Shima Saleem wajen 12 din Rana ya Fito cikin Shirn sa na Tafiya yacema Ummi zai Wuce da Ummi tamai mganar ba tare zasu Tafi da malika ba,sai ya tamke Fuska yace gobe Direba yazo da ita,shi yanzu sai ya bi Wani waje ba zamfara zashi kai Tsaye ba,kanzil Ummi batace mai ammh Tana Lura da Saleem da malika wannan Zuwan ba wata jituwa atsakaninsu,bata yi Shisshigi ba balle tazo taji kunya Fatan isa lafiya tamai Domin tasan ko tace ya tsaya Su Tafi tare da Malika sai ya bata mata rai Don Shigen Taurin kai gareshi.
Malika bata da masaniya sai dai Fitowa tayi ta iske Saleem ya Tafi,tana duba wayarta kuma taga ya Turo mata sakon _Ummi tace mu Taho tare nayi mata karyan Ba Zamfara zani Direct ba,Ban yi ra’ayin Taho dake bane,so wanda ya kawoki sai kimai mgana ya maidoki.._ Sakon nashima Dariya ya bata sai Da ta kyakyata ita kadai tana kaunar Halin Mallam Shifa akomai na *MALIKA MALIK..”!* _Sai na rama ne_ Bata damu ba illa itama ta Hau Shirin tahowa don batason daga gobe takara kwana kada ta kara wani laifin.
Joda ko da ya marwan basu Fito ba sai bayan Azahar Amare kenan Akwana a Hantse inji Hajiya Babba,Dukkansu sai Shekin amarci suke suna walwali kamar Zara da Wata,daga gani Ya marwan baiyi Wasa ba,don Joda idonta ya tona mata asiri saboda yadda ya kode saboda kuka,koda suka kebe da malika adakin Saleema kuka ta sakama ta Ita kuma tana mata Dariya,aranta tana Fadin!Uhmm joda aike bakiji komai Tunda har kika iya Tafiya da kanki,nice Wacce tafi kowa jin maza Tunda harda su Dinki da jinyar Sati biyu,ammh afili sai ta Shiga lallashinta da bata wasu Shawarwari Wadanda zasu amafeta,tare suka Wuni Ranar hatta Dinner ma tare suka taya Ummi Shiryaawa sunayi suna Hiransu Cike da Kaunar juna da Soyayyar,wanda kaunar Ummi ya cika ransu ayayinda itama kaunar Surukan nata ya ki Boyewa acikin Ranta tayi ta godiya ga Allah daya Hada Zaratan ya’yanta da mataye na gari tare da Fatan zaman lafiya a tsakaninsu har Abada…
Malika Tun Safe tagama Shirinta ita da Ayda da Merry,Direba ya kwashesu sai Zamfara,sukansu su Ummi da Abbi Sunji kewar Tafiyar malika mussaman ma Ayda Wacce ta Shiga Ran kowa.
Da Wuri suka isa Wajen Azahar Direba Ruwa kawai yasha ya juya ita kuma suka zage suka gyara gidan Abunda ya bata mamaki wlh Saleem bai taba abinci datamai ba,harda miyan data hadamai,dama ya Fada,ta zata Wasa ne ashe da gaske yake miyar dai batai komai ba,da soyayyen Nama,wanda saboda ya Soyu sosai,sai ta zubar da Shinkafa kawai ta gyara kicin din kafin ta Dora girki Duk da Uban gayyah baison da Dawowarta ba,so take yau ta wanke laifinta kaf.
Sai Bayan la”asar ta Dora girkin Megadi tabama kudi yayi mata cefanan miyar ganye Ta yimai Tuwon Semo,don ta san mutumin nata yana Son Tuwo kowani iri ne yana Son Shi da miyar ganye,bata gama ba sai gabda mangariba,lokacin ta Mulmulashi a leda ta zubasu cikin kololinta masu kyau da tsari,Ta gyara kichen din kafin ta Fito tA karbi Ayda ita kuma saka merry tace takara gyara mata Falon ta sakamata Socket din Turaren Wuta.
Wanka ta Shiga tayi ,tayima Ayda suka chakare,bayan tayi sallar Mangariba,Wani material less dinta ta saka Doguwar riga wacce ta Fito da Tsarinta tsab dayake Rigar Ashape ce,ta ci daurinta wanda ya zubomata da gashinta bayan ta saka band ta matseshi ta baya,Ayda taci wata Doguwar rigar bulawus mai bulewa itama harda Jan baki Malika ta saka mata domin Taran Abbanta…
Bayan issha’i motar Saleem ta sawo kai gidan Bayan ya Zuba hon megadi ya wangalemai get ya Sulala ciki,Malika na jin tsayuwar motarshi yasa ta Fada daki da Sauri ta Fara mata kanta Feshin Turare,sai da tabbata da kowani lungu Ya samu mazaunin kamshi kafin ta Fito Falo tana takun isa,Shiko Tunda ya doso kofar Shigowa Falon,yaji wani kamshi ya dakeshi Lumshe ido yayi yana Shafa kanshi afili ya Furta”Lalle na yarda mata ne Ni’imar cikin gida..”Yake Fada yana Mirmishi Shi kadai kafin ya saka kanshi cikin Falon da sallama hannunsa na kada key din motarsa sai wayarsa dake Rike A hannunsa.
Da Malika ya ci karo Wacce take kasheshi da murmishinta Tundaga Nesa,wani sanyi ya ratsashi tsaye yayi yana kallonta ita kuma tana wani Taku Zuwa gareshi kamar Wata Wahainiya tana Zuwa ta Fada jikinsa daga ita har Ayda tana wani Narkemai ganin Sunyi baya ne kamar zasu Fada yasaka Duka hannunsa ya tarbesu dashi ya Rumgumesu tsam ya matsesu yana sakin Wasu tawagayen ajiyar Zuciya,Ayda ko tana ta taba Sajensa tana gwarancinsu na yara,tana wangale baki bata gane iyayen nata Sun Shiga wani yanayi ba..”
Kiss ta sakarmai awuya tana Fadin”Nayi kewar malamin mijina..”Tafada tana,Kara lafemai kamar wata mage,Ajiyar Zuciya ya saki kafin yace”Nima nayi kewar marajin matata Sosai,Malika kece Farincikina..”Yafada yana Sumbatar Tsakiyar kanta,Shuru tayi kafin tace”Baka na Fushi dani ba,kai akomai na Malika sai ka rama ko..? Yar Dariya yayi kafin ya Rabata da jikinsa yana kara Rike Ayda yace”Ashe kingane,Ammh Kadan nake Ramawa saboda in na Rama da yawa yana Zurmawa dani..”Yafada yana Dagamata gira,Hannunsa ta riko tana Dariya tana Fadin”Tuba malika take,Mallam yayi mata Afuwa bazata kara nuna damuwa ko Bacin rai game da Hukuncin ka ba..”
Suna tafiya Zuwa hanyar dakinsa yace”Gud matar Aljannah,Allah miki albarka ammh na dade da Hucewa kawai Ramawa nima nakeyi..”Yafada suna Shiga dakinsa kan gado ya kwantar da Ayda kafin ya kamo Malika ya Rumgemu yana Faman Shinshinar Wuyanta,hannayensa kuma yana karakaina ajikinta,itama matseshi tayi tana Sauke ajiyar Zuciya kafin ya lalubi bakinta yana bata wani irin kiss mai tsaya a zuciyar wanda aka yimawa.
Da malika taga Saleem ya Rikice mata,Dakyar ta yakice jikinta ta Dauki Ayda ta mikama Merry ta dawo Mallam ya Dasa sabon karatunsa,domin yayi kewar Dalibarsa tasa sosai,Susuce mata yayi yana zayyanamata yadda yayi kewarta itama zagewa tayi tana mai salo salo mai Tafiya da Zuciyar masoyi,sai da suka dawo natsuwarsu kafin ya Kwasheta Zuwa Tiolet ko awajen wankam ma Rabi da rabi Duk Romance ne da tsotse tsotse,Shikanshi wanka dakyar sukayi bayan kowanne yayi wankan Tsarki,Suka Fito suka Shafama juna mai cike da Soyayyah ko abinci ma Ranar cikin Bedroom ta kawomai nan suka ci,tana kan cinyarsa tana cinyar dashi,shima yana cinyar da ita cike da Soyayyah da kauna,Ranar dai an gantale suka kare😂😂,don kololin kadai ta tattara Zuwa kichen,kafin ta Dawo suka Cigaba daga inda suka tsaya Ranar dai Ko Ayda Wajen merry ta kwana Tunda taga iyayen nata Tunda suka Shige daki ko lekowa basuyi ba,Shiyasa itama tayima Ayda Shirin barci suka kwanta.
Ko Washegari basu Fito da Wuri Ba,sai da Merry ta buga musu kofa Ayda na Rigima kana malika tazo ta amsheta,Ranar Saleem ko aiki baije ba yana Nanike da Matarsa da yarsa Abun Alfaharinsa wanda ko Kuda bayaso ya tabasu saboda yadda yake Kafa kafa dasu,itama malika haka take,Duk Abunda tasan Saleem bayaso tana Gudunshi,shiyasa yanzu karatun nasu ya Dau Nisa,don Malamin nata ya Rike mata wuta,Rabi karatu ne Rabi kuma Karatun Samun lada ne,Wanda dukkansu yanzu sun zama cimgam din juna ko gajiya basuyi,kowanne baya gajiya da Rabar jikin Dan’uwanshi.
MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
