Search
You have no alerts.

    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    ……………….”””Rayuwar Farinciki tare da Wata Soyayyah mai tsayawa azuciyar masoya Shi Saleem da Malika Suke gudanarwa gwanin ban Sha’awa ga Wanda ya gani,Yadda take mai ladabi da biyayyah yafi komai burgeshi da ita,uwa uba kuma komai zata gudanar sai da Shawaranshi da kuma izininshi.

    Malika tana da tarin Dukiya wanda batasan iyakarta ba, akallah bankunanta sunfi guda 5 kuma kowanne banki Duk wata riban kudi na miliyoyi suna Shigo mata harma ta rasa wani Tunani zatayi domin Taimakon al’ummah Dashi Domin dai ita bata da muradin kudi ayanzu haka Kudinta shine mijinta da Yarta,yana mata komai na bukatan Rayuwa da cigaba baya duba tana Dashi komai dayasan hakkinshine yana kokarin kare mata shi Har gobe Kudin da malika ta mallaka bai taba Tsole mishi ido ba,Yana kokarin Dorata ahanyar mai kyau tare da kyakyawan Shawara Domin Rabauta daga Duniya har Zuwa gobe kiyama..

    Mganar Filayen datace a bincikamata a malumfashi an samu har Saleem yaje ya gani an kuma yi ciniki da dillallai an biya kudin manyan Filayen Guda biyu wanda aka bashi Duka takardun Filayen mai dauke da Sunanye malika,batayi wasa ba tabama Saleem Duka dama,shi kuma sai ya Umarceta data bama kawun nan Daddy dake nan Malumfashi kwangila kula da ginin makrantan da masallacin Saboda sune ke gari,shi kuma yana Nesa,ammh yamata alqawari lokaci bayan lokaci zai Dunga Zuwa yana Duba aikin.

    Haka ko akayi ta Tura musu Kudin da zasu isa Duka aikin nan da anan aka bama ma’aikatan gini kwangila,suka Fara gininsu cikin Nasara Abunka da Kudi kafin kace kwabo gini yayi Nisa kuma Alhamdulillah Da Saleem zai je Duba aikin Tare da Malika Sukaje,taga komai da idonta ta kuma yaba,awajen ma Sai da tayi kwallah Saboda Tunawa da Daddyta datayi ammh tana mai addu’an Allah jikansa da Rahma.

    Tabiya Family house dinsu sun gaisa Duk da bata zauna ba,tama iske Hajiya ta koma katsina Satin daya gabata so basu hadu ba,Haka Dangin Daddy suka taru suna sakama malika albarka,itakuma sai tace su godema mijinta Domin Shine Silan zamowarta Duk Abunda ta zama ayanzu,Domin da babu Shi acikin Rayuwarta da yanzu batasan awani Hali rayuwarta Zata Shiga Ba.

    Joda da marwan Sati biyu sukayi gidansu Ummi suka tatattara su ka koma lagos wajen aikin mijinta,wanda kafin su tafi sai da ya kaita malumfashi tayi sallama da yan’uwa da abokan arzuka kafin yakaita Zamfara tayi musu kwana daya ya kaita katsina wajen Hajiya nan ta kwana daya,tana Dawowa suka tattara suka tafi suka bar su Ummi Cike da kewa.

    *INA LABARIN ZAHRA*

    Zahra dai tana cikin gararin Rayuwa Domin daga Abba har momi sun Fita batunta bamai Kulata balle ya Shiga Sha’aninta har gwarama Nadira takan xauna ta lallasheta in taga tana kuka,ko ita din ma ba kamar da ba,kowa laifinta yake gani.

    Zahra kishinta yakaita ga aikata Abunda yazo yana damunta,gashi tana Bala’in son Saleem ammh lokaci daya Zuciyarta da Sharrin Shedan suka Taimaka wajen Nesanta ta da Abunda tafi kauna Duk Duniya,bata Fitowa kullum cikin daki tana kwance tana kuka,shiyasa kafin tagama idda duk ta lalace ta kwarzane kamar ba Zahra ba mai iyayi da Rawan kai yanzu Duk bashi,sai ki ganta ta zauna tayi Shuru tana Sharan Hawaye kamar ba ita ba.

    Ganin haka yasa sai momi ta Fara jawota ajiki ganin tana neman kashe kanta da Tunani,ammh Duk da haka zahra bata dawo da karkashinta na baya ba,Duk da ko Daga momin har Abba yanzu Sun Yafeta sun koma mata addu”an Allah ya Cire mata wannan mugun kishin kuma ya bata Wani mijin na gari.

    Satin daya wuce suka Sha Bikin ya Nadir inda ya Auri Wata Scientics Aisha bala,Itama anan Asibitin Aminu kano,anan Suka Hadu suka Fara Soyayyah har ta kaisu ga Aure.Auren da akasha Shagali sosai Duk da Zahra ta dan Warware ammh ba kamar da chan ba,suna zaune awajen Asibtin Aminu kanon nan ya Nadir ke da gidanshi mai kyau da tsari.

    Awajen bikin ne Nadira ta Hadu da Wani DR HAMBALI, wanda ya kasance Shima likita ne Anan Mallam Aminun kanon,kuma Senior Ya Nadir ne don ba yaro bane zai kai Shekara 45 aduniya yana mtsayin Constlant ne yanzu,matansa Biyu, ya’yansa Biyar,Bakano ne gaba da baya,yazoma Nadir Daurin Aure Anan yaga Nadira kuma yaji ta Shiga Ranshi har kuma ya gabatar da kanshi kuma nan da nan Nadira tayi accepting dinshi,bayan ya Sanarma Nadir din shima yayi Na’am da mganar,har kuma ya Sanar ma da Abba kuma ga duk alamu Nadira tana son Dr Hambali.

    Nadira tana kwance Suna waya Da Dr Hambali,Zahra na gefenta tana buga game awayarta taji Nadira na gaisawa da Ya”yan Dr Hambali Abun yabama Zahra mamaki har sai da ta dago tana binta da kallo,ganin yadda take Wani Lallaba yaran kamar Wasu ya’yanta na cikinta tana ji baban ya karbi wayar Nadira ta chanza murya tana mai Shagwaba,Galala Zahra tayi tana bin Nadira da kallon mamaki,wacce Tun lokacin da Zahra ta Fara mata kallon Tuhuma bata bi ta kanta ba sai da Sukayi irin Rabuwar da suka sabayi Cike da kaunar juna,kana ta dago tana kallon Zahra bayan tatashi Zaune tana kallonta kai tsaye tace”Best lafiya..? irin wannan kallon ai sai kisa na kware..”

    Zahra ta Tabe baki tana Fadin”Wai keda waye kike wannan uwar Kashe muryan..? Ba dai da Tsohon Likitan ba,.? Wani Mirmishin Takaichi Nadira tayi kafin tace”Eh dashi ne,kuma ke kika ga tsoho nidai bangani ba kuma,kinsan Allah best ina Son Dr Hambali sosai kuma da izinin Allah Shi zan Aura..”

    Kwalalo ido Zahra tayi tana Fadin”Kutumar ubanchan,best kina da hankali kuwa..?tsohon zaki Aura mai mata har biyu da ya”ya..”.?.”Wani Dirty look Nadira ta sakarma Zahra kafin tace”Eh Shi fa,ko yana da wani Aibu ne,ok sai yanzu nagane ina kika dosa,Saboda yana da mata harda ya’ya ko? Toh ni ba Ruwana da matansa balle ya”yansa Ni da Zuciya daya nakeson Dr Hambali,kuma da Zuciya daya zan Shiga gidanshi matanshi kuma zan basu girmansu a matsayinsu na wadanda ke gaba dani ba Ruwana da kishin Hauka,kishina kenan shine na koyi yadda zan tsaya azuciyar mijina ta hanyar mishi biyayyah da yin Duk Abunda yake so,ya’yansa kuma Suma ya”ya ne Tunda Shine Ubansu kuma soyayyar gaskiya Shine kaso Uba kaso ya”yanshi Shine maganar Gaskiya…”

    Tafada tana mikewa Zahra data daskare tana bin Nadira da kallon Mamaki,kafin Ta Hadiye miyau mai daci tace”Yanzu ke Nadira sai ki Shiga cikin kishiyoyi har biyu..? Tabe baki Nadira tayi kafin tace”Toh Shine me..? Naga dai kowa ya iya allonshi ya wanke,balle ma dukkansu matan nasu muna waya dasu Anty Umaima da Anty Bilkisu basu da Wata mtsala,kinga Zahra keda zaman gida ke Burgeki gaki gashi ammh nikam kinganni nan nakusa tashi,kuma mganar Auren mai mata da kike mgana in ka tsarkake zuciyarka ka Shiga da Zuciya daya wlh ko mutum nada Mugun Nufi akanka sai ya koma mai..”Daga Haka ta kada kai Ta Fice daga dakin tana wake wakenta ko ajikinta..

    Da kallon mamaki da al’ajabi tare Da Nadama Zahra ta Bita,domin ta Fahimci mgana ne Nadira ta sakamata Awasa wandada suka Zafeta sosai,Tagumi ta lafta tana Nazarin Rayuwarta ta baya Sai kawai taji Hawaye suna zubomata,Tasani cewa malika bata taba kulla tanta ba kuma ta sani macece mai kirki sosai ammh son Zuciyarta da mugun kishinta ya Rufemata ido,harta kaita ga Aikata Abunda yazo ya Rabata da mijinta mai sonta da kaunarta,Kuka yazoma Zahra ta Fada kan gado,tana kuka abayyane mai cin Rai Tana juya mganganun Nadira acikin aranta,duk da Nadira bata taba bata Shawaran banza game da zamanta da Malika ba,aamh bata tsammaci zata iya murje ido ta Fadamata wadanan bakake mganuganun ba,Abun ya mata ciwo sosai Wuni tayi kuka tana karajin Nadamar Abunda ta aikata ta kuma dama ace Ana Dawo da hannun agogo baya data Ruga da Gudu ta gyara kuskuran datayi abaya,da yanzu tana gidan Mijinta cikin kwanciyar Hankali Nadira bama zata ganta ba balle harta gayamata wadanan Bakaken mganungun.

    _Anan zan dan yi jan hankali garemu mu yan mata Wadanda muke Waje bamu Shiga daga ciki, ba babban burinmu Shine in mai mata yazo yace yana sonmu,Abu na Farko Shine bazamu Tsarkake Zuciyarmu ba,balle mu barta ta sakama na alheri A”a sai mu bari Shedan ya Shiga Zuciyarmu yana zugamu kan in mun shiga gidan kokarin mu,Mu Fitar da wacce muka samu aciki,bama Tunanin ita ya taji lokacin da mijinta ya auro ki ya kawoki cikin gidan..? Bata kishin Mijinta..? wlh yan mata muna Kuskure Shiyasa Auren zamanin nan kwata kwata baya karko saboda Zuciyarmu ba alheri muke Shiga gidan Aure,shi kuma Allah sai ya barmu da Dubaranmu,daga karshe inta ciki ta tsarkake Zuciyarta Daga karshe ke baki Nasarar Fita da ba, ke ki kori kanki da kanki,wlh mata mu Farka mu chanja munanan Hallayyarmu na zafin kishi wanda bazai kaimu ko”ina ba sai ga Halaka,mune fa da munji wata kawarmu zata auri mai mata ko za”a kara mata Kishiya jikinmu na raawa mu wanke kafa muje mu sameta,in munga ta kwantar da Hankalita Zunciyarta mai kyau ne,sai mu hau cewa koke kina Zaune haka kishiyafa za”a miki ko kuma ke ko yanzu wance me ya’aike ki Shiga Gidan Kishiya kuma kike Zaune baki mike Tsaye ba..? Kuji fa wani zence ..? Toh Ta mike tsaye da me? Wlh da kin yarda da Shawaranta kingama wayo don Maza yanzu Sunfara tsada kuma na garin yanzu Sunyi karanci iskanci kadan zakiyi ya taraki gida wlh da anyi mgana yace Ga mata nan Sunyi Arha kamar ledan pure water,zai maida gomanki wlh,Toh ki natsu keda kika samu Shiga ki sadda kai Ki kuma tsarkake Zuciyarki da Tsoron Allah,ladabi ,da biyayyah ga mijinki kada ki daina,ko aure yace zai kara kada ki zama ballagaza yi kishin musulunci Kina nuna kinfi Shi so ma ya Raya Sunar ma’aiki sai kiga ya Saki jiki,in kina da Rabo ma sai ki tashi da makullin motan Uwargida ta bada Halin kai😂ke kuma ta Waje ko Kinshgo wlh bazai bari ki Raina matarshi Saboda Abunda tayi Darajanta ya karu ko kin Shigo da mugun Nufi sai kiga daga karshe yakoma kanki,Toh Shawarata gareku Shine keda kike Ciki kada kiyi Wasa Damke Abunki don duk yadda kika kai ga Raina mijinki in Wata zata sameshi Sarki zata maidashi saboda gata da so😂 So Tun Wuri ku sauya taku,Domin nima ina kafa kafa danawa kada wata tazo Wuf tamin pdp ta Ture gwannatina na Shiga uku😂,ammh bayan fa na Tsarkake Zuciyata,ALLAH YAYI MANA JAGORA YA KUMA TSARKAKEMANA ZUKATANMU AMEEN SUMMA AMEEN_

    Haka Zahra ta Wuni kukanta bamai lallashinta don ko Nadira ta dawo dakin Ta ganta tana kuka,ammh sai ta bata tanka ba kuma harga Allah ta gayamata hakane ta kara ankarar da ita kuskurenta bawai don gori ko Cin Zarafi ba.

    Karamar mgana Fa ta zama babba Domin Mganar Auren Nadira da Dr Hambali ta Tabbata domin har iyaye sun Shiga ciki Dr Hambali ya Turo magabatansa wajen Abba sun Nemi Auren Nadira kuma yabasu kama daga yadda yayi binciken Shi Dr Hambalin Mutumin kirki ne,An sanya Rana Wata biyar masu Zuwa murna wajen Nadira ba’a mgana Zumudi take Abunda tare da kara Fito da Salo Salo na Soyayya ga Angon nata Dr Hambali.

    An saka ranar da Sati daya sai ga Jerin matan na Dr Hambali da ya”yansu sunzo gaida momi su kuma ga amaryar tasu Nadira,ku kanku Abun sai ya burgeku yadda suka zo suna wasa da Dariya momi haka suke cemata momi sama momi kasa,Dama Nadira tunkan suzo ta yi musu kayatattacen Tarba,bayan ta tsala wankanta,haka ya”yansu suka zagayeta suna Kiran Anty Nadira kaza,Anty Nadira kaza,haka suma iyayen nasu Duk dukkansu sun Girmema Nadira Nesa ba kusa ba,ammh suna Darajata,musamman ma yaddaa Nadira take basu girmansu Daidai gwargwado Tunkan ta Shigo kuma hakan ya samo Asali ne da adalcin miji da suka samu kuma Dukkansu Zuciyarsu mai kyau ce…

    Nan suka Wuninma Nadira sai yammah kana Dr Hambali yazo ya Daukesu harda momi da Zahra amasu rakiya, wacce Abun ya tabata,taji dama itama Tun Farko ta kwantar da Hankalinta ta tabbata Malika sai ta mata Abunda Matan Dr Hambali basu ma Nadira ba,momi Dubi biyar tabama yaran suka ki karba sai da iyayansu suka saka baki,itakuma Nadira tabama matan nashi kyautan Turaruka,suma dai dakyar suka amsa sai da Dr Hambali ya saka baki,haka suka rabu cikin farinciki kowani bangare Sun Tafi cike da Kewa da Farinciki,suna Tafiya momi na ganin Zahra da zata shiga daki tana Dauke Hawayenta itako Nadira Kichen ta Nufa domin ta Zubo abinci hayaniya yahana ta ci,Da kallon Tsausayi ta bita kafin ta kada kai Aranta tana Fadin Dama Allah ya kadarra baki da dogon Zama achan Zahra Allah ya baki wani mijin,yakuma sa wannan Abun daya Faru ya zama darasi agarki,agaremu,agareni ni mai Rubutun,da kuma agareku masu karatu Ameen ya Allah.

    *
    *ZAMFARA*

    Cikin Wannan Halin kara’in Soyewar Da Saleem da malika ke tsakar kwasa laulayin ciki yayi ma Malika salamu alaikum,wanda Ranar data Fahimci tana da shigar ciki Wuni tayi amai da zazzabi mai zafi,koda Saleem ya Dawo daga office yaga Halin datake ciki bai jira cewar datakeyi ya kyaleta basai sunje asibiti ba,ya Tada ita Zaune ya saka mata hijabi,ya kama hannunta Zuwa mota.

    Private hopital ya kaita nan da nan aka Dibi jinita aka gwada sai ga sakamakon ya Fito Malika na Dauke da 2 month preganant,Murna wajen Saleem ba’a mgana bakin nan har kunne,ko kafin su koma gida sai da ya biya yayi musu takeaway Tunda bata da lafiya bata yi girki ba.

    Malika dai wannan karon Cikin yafi Wahalar da ita Fiye da Cikin Ayda Wacce keda Shekara daya kenan,tafara Tatatan Tafiya Tuni,har mikewa tanayi ita kadai,Kullum cikin laulayi take,ga amai komai taci baya zama,ga Zazzabi dashi take Wuni ta kwana,har asibiti ta kwanta har sau biyu Ammh Abunda sai Addu”a,Duk sai ta rame kamar ba Malika ba,yadda cikin ke Wahalar da ita yasa Ummi tasata Ta yaye Ayda ita kuma tatafi da ita Abuja saboda Wahalan na Malika ya ragu Tunda yanzu Ayda Tunda tayi yawo kuma sai Shigen Rigima ba.

    Cikin yasa Malika tayi muni duk tayi baki,ga Wasu manyan Pimples da suka Fitomata bula bula afuska,gashi yasata kazanta don in ba Saleem bane ya matsamata ya Shiga da ita tiolet yamata wanka ba,sai Malika tayi kwana Uku batayi wanka ba😂gashi kuma ya saka mata wata irin Masifa Abu kadan sai tataso tana jijiyar Wuya gashi yanzu Duk yadda take Bashi kulawa abangaren Shimfida yanzu ko kusa da ita ya matso,yanzu zata bata rai,balle yace zai Shiga majalisar dinkin Duniya,yanzu zata hau kuka,,Saleem yanzu lallaba malika yake,Saboda ta zama alallaba Auren zamani,saboda yadda take Wahala harta da Abbi yazo Dubata Saleema tazo daga kano tamusu kwana biyu takoma Tunda sun kusa gamawa ana ma mganar Aurenta da Ya Sadiq ne,Su joda dai sai dai suka kira ta waya suka mata sannu,ko fa awayar ne Malika in Masifarta tatashi yi take,merry kam na Hakuri don da ita da Saleem sun Fi kowa ganin Masifar Hajiya malika,mai Cikin yan gayu,shi Acp dayayi mgana tafara Zumbura baki tana kunkuni Duk shi yajamata wahala,😂Toh ya zaiyi Tunda Shi ya kumsa Abunda ke saka bala’in ai ya lallabata arabu lafiya,ko abinci bata ci daga Shasshaka sai awara take iyaci,sai daga baya kuma tafara cin kwaden garin kwaki ,ai Dole Acp Saleem ya jingine buhun gari,😂Shasshaka kuwa maman Abba keyowa tana kawomata,domin ita ke kula da Malika jamgwanm,,in kuma batanan Tasaka merry ta mata wata Rana ma sai an gama ta kawo mata Tature tace bataci😂Shiyasa ACP saleem fa ya ijiye kiyuwa ya zage yana Taimakon Malika don in ya Zauna harta Wajen kwanansu sai yazama bolan Juji saboda Rashin gyara,gashi ta hana Merry Shiga dakinnsu guda biyu,iyakar gyaran nata daga dakinta sai Falo,da kichen…..

    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    Note
    error: Content is protected !!