Maleeka Malik – Chapter Thirty-one
by NadminMASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
…………”Hajiya Binta tayi matukar Murna da ganinsu sosai haka ta Shiga Dawainiya dasu Ayda ko Ram ta goyeta bisa bayanta tana jijjigata saboda yau tatashi da Rigima ne.
Koda suka iso katsina Malika ta nemi Saleem awaya ammh bai Daga kiranta ba,sai tamai Uzuri ko yana Wani Abu ne,ammh Abunda ya bata mamaki har Washegari bata ga kiransa ba,kuma harda zasu Wuce malumfashi da Hajiya ,ta kirashi taji yayi hanging din kiranta A Number Busy kuma daya gama bai kirata ba,Abun sai ya bata mata rai Taga toh metamai Ammh ya Dau Wannan Fushin da ita,Tunda ga lokacin itama Tayi alqawarin Fita batunshi.
Duka gidan suka Tafi,sai aka bar Dose da Wata yar aiki da Hajiya ta Dauka sai sauran ma’aikatan Haraban gidan da megadi,Koda suka isa malumfashi a family House din Su Daddy Su ka yada zango wanda dama Tun Daddy na Raye ya gyarashi Sosai Adakin Hajiya Innaro suke sauka in sukazo wanda Shima yake gyare tsaf Duk da Wacce ta Haifi Hajiya Binta tana nan da Ranta acikin gidan.
Malika bata Tafi gidan Baffan Joda ba sai da yamma Direba ya karisa da ita,koda tajema joda batanan tana makotansu inda ake mata Dilka da Halawa,sai da taje chan suka hadu,nan Suka Rumgume juna suna murna ganin juna cike da doki kafin su Zauna suna bayan sun gama gaisawa da Sauran yanmtan Wasu suna ta kallonta cike da mamakin anya wanna ce malika malik din da Suka sani..? Lalle Rayuwa juyi juyi na gaba yakoma baya Inda ada ne ko da kudi suka saka baza suga malika ido da ido ba balle har Su ganta akusa dasu haka.
Malika nan ta tare Wajen Joda suna cigaba da Shiryen Shiryen,Ayda kuma tana Wajen Hajiya ita da Merry,sai inda ta Fara Rigima ne zata kawota ta bata nono Tunda babu Nisa da Family House din Su Daddy,An tsara komai cikin Tsari sai wanda ya gani bangaren ango ma ba karya domin Duka iyayan nasa sun baza Kudi sosai bayan Tarin gayyatan dasukayi Hardashi Marwan ya gayyaci abokan aikinsa Sosai.
Saleema ma ta iso ana gobe Daurin Aure tazo ta tarar da gida cike da yan’uwa anata harkan arziki da Murnan Auren ya marwan,sai dare ne ta tambayan Ummi ashe Auren Zahra da Ya Saleem ya kare..? Nan Ummi ke Warwaremata Abunda ya Faru Tabe baki Saleema tayi tana Shaidama Ummi Nadira ce ke Sanar da ita Abunda Ke Faruwa tace Zahra ta zama Abun Tsausayi kuma tayi Nadama,Jinjina kai Ummi tayi kafin tace’Ko tayi Nadama bashi da amfani Saleema,dama ko addini ba’a son irin wannan Nadamar Saboda kana yinta ne,sanda Ruwa ya karema Dan gada,Kinga ko,ko kayita bata da Wani amfani agareka,shiyasa Amfison ka Tuba Tun kana da Sauran Damarka yanzu kuma babu Abunda mukayi iya Don Aure ya kare atsakaninsu..”Gyada kai Saleema tayi kafin tace”Wlh hakane Ummi,Allah ka tsarkakemana Zuciyarmu da imani..”Ummi ta amsa da”Ameen Ameen Saleema.
Sai da yamma chan Sai ga Sadiq ya iso bai dade da isowa ba Sai ga Uban gayyan ya iso cikin motarsa 4 matic ya kara kiba da Fari kamar bashi ba,daka ganshi zaka Fahimci ya samu kwanciya hankali da Natsuwar Zuciya,shiko ya marwan sai chan dare ya dawo yana chan Tare da Wasu abokansa wadanda ya Saukesu a hotel,sai kalilan ne ya Saukesu agida suna tare dasu Saleem da Sadiq suna hira kamar ansan juna,Duk da Shi Saleem bamai yawan mgana bane,kuma yawancin abokan ya marwan din ba baki bane agaresa so Duk yasansu sosai.
*
Karfe 2:30 na Ranar Asabar Aka Daura Auren *MARWAN KABIR KUMO* Da amaryansa *JODA MUHAMUD MALUMFASHI* Wanda aka Daura shi kan Sadaki Dubu dari biyu lakadan ba ajalan ba,Daurin Auren daya samu Hallartan manyan baki daga kowani bangare kama daga barayin shi kanshi Uban gayyah,sai Saleem danashi Harta Sadiq Ba’a barshi abaya ba Uwa uba kuma Abbi da nashi Tawangan ga tawangan Sauran Daurin Aure guda uku Wanda suma ta kowani bangare sun Hallarcin Wannan Daurin Auren daya Tara Dimbim Jama’a.
Maman Abba ta cika alqawari ta biyo Baban Abba sunzo Tare Wanda Sai dai Malika ta ganta kwatsam haka Suka Rumgume Juna Suna murnan ganin Juna,haka amarya Joda Wacce aka tsarama kwalliya ta Nuna tsara tana Sanye da Wani leshi mai kalan Blue black da Ratsin kwalliyar pick,sai mayafinta ma pick da jakarta da takalmin kafanta,sosai taji dadin Zuwan maman Abba,haka ta Rumgumeta tana mata maraba da Zuwa,Ita kuma Tana mata Tsiyan Amarya tasha kamshi .
Ana gama Daura Aure da Awa daya bayan sungama sallaman bakin da zasu Tafi sai kuma suka koma Shirin komawa Abuja da amarya,wacce aka Dauketa daga nan gidan data ke party Zuwa Family House din Su Daddy Inda Hajiya ke taronta ita da Danginta domin suyi Bankwana,lokacin ita kuma Malika suna Tare da Maman Abba ta rakota kofar gida Baban Abba yace ta Fito su Wuce,shine ta roki alfarman ya dan mata lamani taje tama Hajiya Allah Sanya Alheri Tunda babu Nisa,dakyar ya yarda Ammh da Sharadin bazata Dade ba.
Malika na Sanye da Leshi ne mai maroun colour wanda keda kwalliyan Ja ajikinsa,Riga da Sikat wanda ya Fito da ita Sosai itama an mata kwalliyan Duk da ba cika mata akayi ba,ammh kam kallo daya zaka mata ka fahimci dama chan tana da Sirrin kyanta,mayafin data yane kanta Dashi Ja ne,mai wasu Ratsin Duwatsu masu daukan ido,hakama takalmin kafanta baki ne mai daurin igoyoyin ja ajikinsa kunsa mutuniyar akwai son Takalma masu Tsini da Tudu.
Ayda ce ahannunta Wacce itama taji adonta cikin Riga da wando,Rigar Pick ce,wando ko na Jeans ne baki sai wani takalminta mai kyau da Tsari pick colour kanta ko yasha kitso wanda aka sanya band din kanana aka kama mata Daki daki,Sun Fito da Maman Abba zasu koma Family House din su Hajiya,duk akwai maza sosai akofar gidan da kuma Tarin hadaddun motoci,.
Saleem ko da suke jingine jikin motarshi Shida Sadiq da wani abokin ya marwan mai Suna Hamza,sai Baban Abba,dukkansu sunci Dayan Shaddodi Farare dinki Muhammed ne wanda ya dace dasu Samarin zamani,Lokacin da su malika Suka Fito hankalinsa na bisa waya bai gansu ba,Sai da Sadiq ya tabosa kana ya Dago ya Sauke ganinshi kan malika tana tafe sabe da Ayda suna hira da Maman Abba tana sakin mata kayatattacen mirmishin din,Wani yam Saleem yaji lokaci daya yaji Ranshi ya baci ballema Daya ga da Sadiq din har dabHamza sun kura mata ido,yana ji Sadiq na gayama Hamza mai jan gyalen nan matar Acp ne.
Tuni Ran maza ya baci,idanuwansa har sun kada saboda kishi wayarsa ya Cigaba da dannawa kamar babu Abunda ya Dameshi Sako ya Turama malika kamar haka _Ki tsaya a inda kike ganin zuwa,ban Amince ki kara ko taku daya ba._ Tana jin Shigowar sako Dama wayar na hannunta tana Danna Sreen din Sunanshi yana Wayo ta saman Wayanta Dauke da Sunan data Sanya mai * ABBU AYDA* Mirmiahi tayi kafin ta Shiga sakon da ya Rubuta ne ya Daure mata kai ta Dakata da Tafiya tana waige waige ganin Haka yasa maman Abba tsayawa tana Fadin”Matar Acp lafiya kuwa…? Kowani kike nema..?
Miyau ta Hadiye kafin tace”Kinga mallam ne yamin Sako yanzu yace na jirashi gashinan Zuwa,kuma inata waigo banga ta inda zai bullo ba..”Tafada tana Raba ido,mirmishi Maman Abba tayi kafin tace”Baki lura dashi ba gashi ta bayanmu yana Tahowa aie…”Da hanzari Malika ta juya sai ko ta hango Saleem yana takowa wajensu cikin takunsa na isa yadda taga yanayin Fuskarshine Sai da Firgita,cikin jin kai ya kariso garesu maman Abba na gaisheshi ya amsa cikin sakin Fuska kafin ta danyi gaba,Malika ta kalleshi taga ya Hade rai duk sai ta Daburce cikin sanyinta tace”Mallam ina yini..”
Bai amsa ba ya mika hannu yana Fadin”Bani ita Kirjin biki…”Yafada kai tsaye yana kallonta batayi gardama ba Tamikamai Ayda ya karbeta itako tana ta wangalemai baki dama Tunkafin ya karbeta bai kalli malika ba ya Juya yana Fadin”ki koma ciki malama ban amince kije ko’ina ba,yanzu zamu Wuce Abuja in kuma baki gama bikin bane,in ngama ganin Ayda zan aiko miki da ita ciki..”Daga haka ya juya ya Fara Tafiya,Kunya da Haushi suka kama Malika tayi jagale tana kallon Bayan Saleem kafin ta saki ajiyar Zuciya ta karisa kusa da maman Abba tana Sanar da ita Yadda suka yi da Saleem,dariya tayi mata tana Fadin”Kishi ne ya taso karki damu bari naje kila in yagama dama ya biya dani ko Sharp sharp ne mu gaisa..”Jin haka yasa sukayi sallama dama Tun aciki malika ta bata kayan biki musabaha sukayi kafin su Rabu malika takoma cikin gida itakuma maman Abba ta Nufi Baban Abba wanda har ya Shiga mota Shida Abba ita kawai suke jira.
Malika ko data Shiga cikin Abun sai yaki barin Ranta sai da tayi kuka aboye,Kafin ta dauro alwala bayan ta Wanke Fuskarta tana cikin sallah ne kawayen amarya suKa Dinga zuwa daukansu suna Fadin gashi chan za”a tafi bata damu ba,don ko da ta idar sallar bata Fita zaman ta tayi tana mamakin mallam,shifa yake koyar da ita hakuri ammh yau gashi laifi kadan ya Riketa dashi yakasa yimata Afuwa.
Tanan zaune sai ga kiranshi kamar bazata Dauka ba sai dai ta daga kiran cikin Gadara yace”Kina ina..? Ranta acunkushe tace”Ina cikin gida..”Kifito ki karbi Ayda mu zamu Wuce ne..”Daga haka ya yanke kiran,Wayar tabi da kallo kafin tatashi ta Tafi,Abunda ya kara mata mamaki mikomata Ayda Yayi ya juya zai Shiga mota sai itacene tace”Mallam ni wata mota zan Shiga..? A karkarce ya kalleta kafin yace”Zuwa ina..? Kwallar har sun Fara cikamata ido tana kallonshi tace”Zuwa Abuja..”Tana Fada cikin Sanyinta,Ganin yadda tayi ne yasa ya sauke ajiyar Zuciya yana kallonta akarkace kafin yace”Au yau zaki koma kenan..? Ni zatona sai kin sake Wani satin kinga ko sallaman Jama’a kya taya Hajiya..”Jin Abunda yace ne yasa taji Zuciyarta ta tsinke batamai mgana ba ta juya,ganin haka yasa ya Sha gabanta yana Fadin”Ki Shiryo kayanki mutafi don Tun dazu su ya marwan da tawagar amarya Suka mika..”
Bata kalleshi ba ta mikamai Ayda ita kuma takoma cikin ta dauko karamar jakarta bayan tama matar gidan Sallama Tunda anan suka zauna Tsawon kwana uku,Koda ta Fito Shida Sadiq ta gani yanzu,ba don Sauran kayanta na gidan Su Daddy ba,da Saleem baida niyyar biyawa,Allah dai ya Dorata akanta ta Biyama tama Hajiya sallama suka kwashi kayansu ita da merry,shi kuma ya bude musu booth suka saka kafin su Fada mota su dau hanyar Abuja.
Ko amotar kanzil bai cemata ba,itama bata tankashi ba,shida Sadiq suke ta hiransu sai wani lokacin ne Sadiq ke sakota ciki itako sai da ta murmusa,shiko Saleem da Sadiq ya sako malika zai dauke baki ya hade rai,Tun Sadiq bai Fahimta Ba har yagane ma’auranta sun Samu mtsala,baiyi mgana ba kawai yayi musu Fatan Allah Daidaitasu domin yasan koyayima Saleem mgana ba Kulashi zai yi ba.
Su ya marwan sun isa ba Dadewa sai ga su malika,Ummi ta Rumgumeta tana murna Abun mamaki Saleema tazo tana gaishe da malika ta kuma yi Saurin karban Ayda tana mata Wasa,sai ga Saleema ta dauki akwatunan Malika tace dakinta zata sauka,Ummi na mata tsiyan yau kuma Anty malika akayi Uwar daki da ita,tace eh yau Ummi ba bakuwar ki bace tawace.
Dakinta ta kaita ta Hadamata Ruwan wanka da kanta Ta Shiga tayi kafin tazo ta rama sallar mangariban data samesu ahanya,tana zaune kan Dardumar aka kira Issha’i ta mike ta gabatar kafin ta Fice Zuwa Shashen baki inda aka Sauke su Joda,ko da joda da kawayenta da yan’uwanta suka ganta sai suka Fara mamakin wace mota ta Shiga joda ce ke dariya tana Fadin”Lalle masu abu da abunsu mallam ne ya taso Abunshi..”Dariya malika tayi tana ma Jodan dakuwa,ta iskesu ankawo musu abinci kala kala da Abunsa suna yaba kirkin Dangin Marwan da mahaifiyarshi,Dariya kawai malika tayi tana kara gayamusu haka suke kowa nasu ne musamman Ummi da Abbi.
.
Batabaro dakin ba sai wajen goma na Dare Saboda ta karajin barci ga gajiyan zirga zirgan biki inda Allah ya taimaketa ma Ayda na Wajen Saleema kilama tayi barci,Falon babu kowa sa yan kumo suna hira,gaishesu tayi suka amsa cikin sakin Fuska suna tambayan Ayda tace tana Wajen saleema,daki ta Wuce koda ta Shiga ba kowa Saleema bata ciki,kila tana sama wajen Ummi,yadda barci yaci idonta ne yasa bata tsaya komai ba Ta kwanta tana jan blanket ta Rufe kafafunta dashi,cikinta kuma acike yake shiyasa bata nemi abinci,ba ko minti goma batayi barci ya kwasheta Saboda gajiya ko addu’an barci batayi ba.
Saleema ko tana Falon Abba,suna hira dukkansu iyalan wadanda sukan Dade basu hadu ba,ya marwan da ya saleem da ummi da Abbi da Sadiq sai Wajen 12 kana suka sauko bayan Ummi ta koresu tace zasu kwanta suma barci suke,Koda Saleema ta Shigo dakin dauke da Ayda Wacce itama ta dade dayin barci ahannun Abbi,ganin Malika na barci sai bata tasheta ba,ta kwantar da Ayda gefe itama ta Shirya cikin kayan barcinta kafin ta hayo gadon bayan Ta Rufe musu kofa kuma ta rage Wutan Dakin Kusa da Ayda ta kwanta tana kamkameta kamar wani zai Rabasu,dama ko banza Saleema irin Abbi suna da Son yara kanana.
MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
