Maleeka Malik – Chapter Thirty-five
by NadminMASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
…………….”Lokacin da Bikin Saleema da Sadiq ya rage Saura Wata daya Takardan Transfer din Saleem ta Fito an maidashi Headquatersu ta Katsina, *POLICE HEADQUATER AIRPORT ROUNDABOUT KATSINA STATE* Murna wajen Malika ba”a mgana dama Tafison su koma katsina da Zama ta gaji da zaman Zamfara.
Nan da nan suka Fara parking din kayansu na Sawa,Domin komawa katsina,wanda Malika keta murna har Maman Abba na mata Tsiyan zata tafi ta barta,dariya tayi tace haba ai ko Birnin Sin ta koma suna Tare bazasu taba Rabuwa ba,Sati daya da Samun Tranafer din Suka gama duka parking din Abunda zasu dauka sukayi sallama da makota,shima Saleem din already yagama Sallama da Headquater nasu,bayan ya mika Sauran aikin zuwa ga hannu sabon Acp wato Shugaban wajen na yanzu.
Maman Abba ta zama kawar alqawari don da ita suka dumguma Zuwa katsina gidan da Daddy yabama Saleem wanda koda suka isa Hajiya ta tura musu su Dose sun gyara gidan,sun musu abinci,babu Abunda ya samu gidan,domin ana kula dashi Sosai,ga motocinsu guda biyar Nashi Biyu na Malika biyu wanda Daddy ya mallaka musu sunanan a mazauninsu Rufe da Tamfol,dama already makulayan motocin na hannun Saleem..
Malika da Maman Abba sun zaga lungu da Sako na gidan suna yabawa,Tare da jinjinama Daddy irin Kudin daya kashema gidan,komai na Zabinta an saka mata shi,harda Abunda ta Fiso arayuwarta Swimming Fool,Wayyo Dadi kashe Malika Duk da haka sai da tayi kwallar Tunawa Da daddyata ammh bai Hanata Nuna Murnan Tafi jin dadin wannan gidan Fiye da gidansu na Zamfara ba.
Maman Abba kwana daya tayi ta juya Zuwa Zanfara wanda Malika da Saleem suka Mata Sha tara na arziki don Ta nuna musu kara Sosai,Malika bata da Wata damuwa yanzu don Gata ga hajiya,ko banza tana jin kamshinta ba kamar da,da ko kamshin Wani na gida bata ji…
Saleem ya kai Trasafer letter dinshi Zuwa Sabon Headquater su,yayi wasu cike cike kafin Yafara Zuwa office cikin kwanciyar Hankali,dawowar Malika katsina yasa Hajiya ta dawo mata da Dose suna tayata wasu abun don Cikin malika yana da girma Sosai,Dawowarta katsina yasa tafara Zuwa Asibiti Awo asibitin Federal Medical centar katsina, Tunda da suna Zamfara maman Abba ke Zuwa har gida tana mata,Cikinta Watanshi Takwas yanzu ammh sai ka tsaya ka kara kallon yadda yayi Wani girma yana neman Rufe Malika gashi ya Kumburata Sosai Afuska da jiki,tafiya dakyar tashi Dakyar ammh kuma ahaka take Shirin Tafiya Abuja bikin Saleema,wanda Saleem yayi mata bakam Saboda yaga Malika bata da Hankali baisan ina zata da wannan Tulelen cikin ba taje tabama mutane aiki.
Malika batayi Shawara da Saleem ba Ta Turama Ummi Zunzurutun Kudi har Miliyan Talatin,wai gudummuwar bikin Saleema,dana ya marwan Tunda wanchan Lokacin bata bada komai,Sai ga Ummi ta kira Saleem yana office tana tambayanshi Cike da mamaki yake Sanar da ita bai sani ba,yana wajen aiki ammh in ya koma zai tambayi Malikar ita ko koda Ummi ta mata waya tana tambayanta wannan kudin na miye Dariya kadai tayi kafin ta Sanar da Ummi Gudummuwarta,Bakin Ummi bude take Fadin kudin Sunyi yawa,malika tace Allah Ummi basuyi ba,sai dai inda bazaki ki karba ba,Ummi kasa mgana Tayi, illah godiya datayi ta zubama Malika,shikanshi Abbi Dayaji yayi ta mamaki har yayi tama Saleem Fadan yazai bar malika ta dinga Wasa da kudi haka,yakamata ya zauna da ita su Tatauna Abunda ya dace su Dinga yi da Ribar Dukiyarta bawai Shanshanci ba,kaji Abbi😂.
Saleema dataji sai gata har katsina Tazo godiya,Malika bata bi takan Godiyar datake mata ba,sai ma Tambayanta datake wata irin mota take so kuma take Sha”awa Saleema bata kawo komai ba tace Vibe motar tana burgeta,gyada kai kawai Malika tayi aiko ko Sati basu da wannan mganar ba sai ga motar Saleema ta iso daga kwatano,Saleema sai da tayi kukam Dadi Saboda Farinciki Ummi da Abbi da hajiya sun kasa mgana,Shikamshi Saleem bai sanin Malika zatama yan gidansu kyauta sai dai yaji lbri daya yi mata mgana Sai tace Gift din Aure ne tabama Saleema da ya Nuna mata kashe Kudin yayi yawa sai da Malika ta maida Abun Fada,tana Tunanin Yanzu don ta bama Ummi yan kalilan kudade,kuma ta Siyama Saleema mota sai yazama Abun mgana,Bataji dadin haka ba,Dole Saleem ya kwaso Rantsuwa da magiya da lallashi ya Dora kafin Malika ta Hakura.
Saleem ya Fara Hawa daya daga cikin motocin da Daddy ya mallakamai Tun yana Raye prado din,Na Malika ko ya saka Aranshi zata koma hawa motar kanta,ammh sai dai ta koyi Tuki don Shi bazai yarda da Wani Direba don wannan ai Salon iskanci ne,kai kana nam Bude da baki wani gardi na gane maka mata,kowani kwalliya tayi yana ankare ta madubi yana Hadiyan yawu😂,Ammh bai sanar da ita ba ya bari sai Allah ya Sauketa lafiya.
*.
Biki na Saura Sati daya Bakin lagos suka Sauka Ya marwan da Joda,Ashe joda itama da dan matashin Cikinta har ya Fito,inaga Tun Haduwar Farko tayi gamakatar dashi akofar daki😂Malika na jin Joda tazo itama tace zata Tafi,Saleem yace kadama ta sa rai Joda ta Fita lafiya babu inda zata sai ana gobe Daurin Aure zasu Tafi tare,Ranar lahadi su dawo tare,don bazai barta tana yawo da wannan Abun cikin ba,Dole Malika ta Sadadu da,domin Ta tuna karonsu lokacin bikin Joda,shiyasa wannan karon bata Tada Hankalinta ba,in tayi Duba da gaskiya Saleem ya Fada tayi Nauyi da yawa koda Tama je daWurin babu Abunda zata iya,sai ma karama jama”a Nauyi.
Sai Ana gobe biki Malika tazo ita da Saleem wanda Hajiya wannan karon tazo tama Rigasu gaba da kwana Uku kafin suzo,Su merry malika tabari agida Tunda ba Dade zasuyi ba,Koda suka je sun iske ango ya iso Shida tarin tawagansa wadanda ya Saukesu A hotel,shima din ba dadewa zasu yi ba don In anyi biki Ranar asabar lahadi litini zai Wuce da Saleema wajen aikinsa don Bashi da Wani Hutu mai yawa.
Chan su Malika suka iske Ayda an zama yan mata,Ta kusa Shekara biyu,tana Tafiyanta ko”ina Gwanin ban”Sha’awa tana makale da Ummi ko Abbi ko Anty Saleema,ammh saboda wayon data keda shi tana ganin Iyayenta ta makale musu musamman ma Saleem wanda Tunda ya dauketa taki yarda ya Sauketa ko nan da nan chan,Dole yayi Hakuri yana Yawo da ita.
Gida ya cika da yan Kumo mata ammh banda maza dayake achan baban gidansu Daddy na kumon za”a Daura Auren,so su Abbi ne zasu Bisu chan wannan karon basu zasu biyo ba,Ranar daurin Aure Tun Safe Su Abbi suka kama Hanyar kumo tare da Saleem da Ya marwan da ango da tawagan abokansa,Sauran abokan Abbi da Wadansu wadanda aka gayyata Duk chan kumo zasu je,sai dai su Hadu achan.
Karfe 2:30pm Aka Daura Auren Saleema da Angonta Sadiq,Akan sadaki mafi daraja da kima,basu baro kumo ba,sai da suka tsaya sukayi Walima agidansu Abbi kafin su Dauko hanyar komawa Abuja cikin Rantattsun motocinsu.
Abangaren Gidan Biki kuwa ya cika Dakam da jama”ar kumo data Saleem da Jama”ar Ummi da Abbi Allah Sarki Harda yan malumfashin sunzo ma Ummi biki Mota guda,Wanda harda Matan Baffan joda Wato wanda yabada Auren Ba Ummi kadai ba Hatta Hajiya Taji dadi sosai Suka Dinga ina suka saka dasu saboda karramawa Ummi ko bak’inta kawayenta ne lauyoyi kowacce kagani babbar mace mai ji da ado da Dukiya mai yawa kunnawansu da hannayensu suna Kara kaina Zinare da Azurfa kamar ba kudi ake Sakawa Asiya ba.
Saleema ma taga jama”ar daba ta taba tsammani ba,Domin yawancin yan Sch din su na Buk yan Faculty su na medicine duk sunzo mata harda Wadanda sukayi Housemanship dasu,A Murtala Aminu kano,Abun mamaki Nadira ta cika alqawari wajen karfe 12 na Rana sai ga tazo Direba Dr Hambali ya saka ya kawota Saleema taji dadin Zuwanta haka ta Rumgumeta tana mata sannu da Zuwa dayake ita da yar Dr Hambalin tazo mai Suna Farha.
Takaita har Wajen Ummi sun gaisa ta mata Allah sanya alheri harda 5k dinta kusan Dama Nadira tana da wayau,tasan yadda zata kyautatama Mutum harda wata 5k din tabama Ummi tace inji momi tace ace mata bazata samu Zuwa ba,alhalin Momi da Zahra ma basusan Auren Saleema ya taso ba, Abbi ko hidima tamai yawa Bai kira Bukar Madan ya sanar Dashi ba.
Saleema dakin dasu Malika da Joda suke Dakin Hajiya Babban nan takai Nadira,sunyi mamakin ganinta ammh sai suka Shanye mamakin ganin yadda Ta nufosu da dariyarta da komai,gaisawa sukayi suna Tambayan Juna yaushe gamo,Malika sai kallon Nadira take ganin yadda takara kiba da Cika kamar ba ita ba lalle ta samu kwanciyr Hankali.
Itako Nadira Malika take kallo ganin yadda cikin jikinta yayi kato,sannu ta mata hartana Zolayanta da ko yan Biyu ne,Malika tayi Dariya kawai domin lokacin tana cikin Takaichi ne domin Kayan ankonsu da sukayi ita da Joda da Saleema da Ummi ,sunki Shiganta dalilin haka fa Ummi tace kada ayi mata Riga da Sikat ayi mata Doguwar Riga ne,ammh kwata kwata taki Shiganta,Har karba Ummi tayi ta kira mai dinki ta sake bashi ya dan Buda,ammh koda Malika ta sa,yadai Shigeta ammh kuma ya matse mata ciki Sosai tana Numfashi Sama sama,dole Ummi tace ta cire,Kuka ne kadai Malika batayi saboda takaichi Dole tana ji tana ganin kowa da kayan kwarai ita sai wata Doguwar rigarta ta sanya mai Roba na kamfanin Armani,ganin haka ne yasa Ummi ta bada Wata atamfa tace yanzu take so a dinkama Malika mai yalwa yadda zata samu ta Sanya.
Nadira sai after la’asar tatafi Malika ko da karfin Hali harda tambayan Zahra Nadira tace tana gida,mirmishi kawai Malika tayi tace agaida mata da momi da Zahra Nadira tace zasu ji,har wajen mota suka Rakota ita da Joda kafin suyi sallama su Fada mota bayan an basu kaya biki,har suka bar Haraban gidan Su malika Na daga musu hannu.
Yan Daurin Aure basu dawo ba Sai After sallar mangarib,sai gasu Sun Shigo,Falon gidan suka baje suna Sauke gajiyan Hanya Yan kumo na musu barka da Sauka,shikuma ango da tawagansa a hotel da suka sauka suka yada zango harda Shi Sadiq dinn,Ya marwan Dai matarsa ya nema ta bashi abinci don Yunwa yakeji koda Saleem yaga Uban garan da joda ta Hadoma Ya marwan kwabe Fuska yayi yana Tambayan Shi ina nashi,Ya marwan na mai Dariya yana Fadin”Ka kira matarka mana,nima ai matata ce ta gatantani..”Jin haka yasa Joda ta saki dariya tana Fadin”Ai ko ya kirata bazai jita ba yanzu tana chan tana kumburin Kaya ya ki Shiganta harda wanda Ummi ta bada aka Dinkamata yau din nan..”
kwalalo ido Saleem yayi yana Boye dariyarsa yake Fadin”Ke Da gaske..? Kice yau akwai danja kenan,ai ko bari na noke ya marwan yiman alfarma ci wajen wanda matarka ta kawo ma,Wlh yau In Malika ta ganni na zama Nama..”Dariya suka sakamai Shida Joda,sai ga Ayda ta Shigo da kuka Hawaye Shaba Shaba da majina,Joda ce tayi Saurin Daukanta tana Fadin”A”a Aydan Abbi waya tabaki..”Tana murje ido tace”Annie…”Dan ware ido Saleem yayi kafin yace”Tab yasin sai dai kiyi Hakuri Ayda ta,nima in naje Rama miki ai nakai kaina,Srry kinji zo nan kyale Annie..”Yafada yana mika hannu ya amsaheta Hawayenta yake Share mata yana Fadin”Ke ne Ayda kin cika Rigima kina ganin Annie naki ta zama sai a lallaba ammh sai ki dinga Zuwa kina damunta,Bakije wajen Abbi bane,ko baki ganshi bane..”Kai ta gyada kamar wata Babba kafin ta Washe baki ta tashi daga jikin Saleem ta koma ta Dane Bayan Ya marwan tana Kiran”Dadddi…”Rikota yayi yana Dariya yana Fadin”Aydata,ai na dauka yau ba’a ga Daddin bane..”Rikota yayi yana mata Wasan daya saba yana Cafata sama Tun tana jaririyarta yake mata Haka,harta girma data ganshi zata Nufeshi ya dauketa yana mata Wasa yanzuma Dariya take kyalkyalawa cike da Sha”awa Joda ko wayarta ta Fitar tana musu video tana aika musu da mirmishi Shiko Saleem bai biye musu ya jawo kulan Sinasir din da Joda ta kawoma Ya marwan ya loda uku A filet ya zuba miyar da akayita da Naman rago,ya ja gefe yana lodama cikinsa don Zahirin Batu yau din nan yasha Yunwa don ko a kumo bai wani tsaya yaci abinci sosai ba Saboda Shi haka yake bai cika Cin abinci agida ba.
Suna cikin haka Sai ga Malika ta shigo da tsinin Cikinta agaba hannunta Rike da Doguwar Rigar da Ummi ta kara badawa aka Dinka mata ammh Still taki Shiganta,Tana Shigowa Fuskarnan ba Annuri ta Nufi Saleem yana cin abinci sai ji yayi ta ta tsayamai bisa kai tana Tura baki dagowa yayi yana kallonta ganin haka yasa ya danne Dariyan dake neman kwacemai yace”Uwar biyu meya faru ne..? Na ganki kuma da Riga ahannu lafiya ke baki sa kayan bane,kiman kwalliyan dashi..?.”.Yafada yana kallonta mganar daya Fada kamar ya Tunzurata ne,kawai sai ta Fashe da kuka tana Fadin”Yaushe zan yi wata kwalliya da wannan cikin,Kowa ya saka kayanshi mai kyau ammh banda ni,shine kuma kai kana nan zaune ko ajikin ka..”
yana Danne Dariyanshi yace”Ashh,duka sunki Shiganki ne,Kai Abu baiyi dadi ba gaskiya,…”Tana Share ido tace”Wannan ma fa Ummi ta kara badawa akamin Dinkin Sauri itama bata Shigeni ba..”Ido ya zaro yana danne dariyarsa yake Fadin”Kai don Allah..? Kuma sai kace wata giwa ace Abu har an sake dinkawa ammh kuma yaki Shiganki..”Ya Fada yana Dan Ware ido kamar gaske.
Dariya ce takama Joda da Ya marwan wanda suke ta Danne ta kada ta Fito Tun Shigowar malika,Wani kallo ta Watsama joda kafin tace”Ke kuma wa kike ma Dariya..”Tafada cike da Haushi Ya marwan yayi Saurin tashi yana Rike Ayda yake Fadin”A”a fa kada ki Wuce kan matata,ga mijinki chan Shiya fara dariyan fa..”Yafada yana nuna Saleem da baki,wanda ke kokarin Rike dariyansa ammh kuma taki rikuwa sai da ta Fito Waje,Malika ta tsaya tana kallonsa cike da takaichi ,mikewa yayi yana Dariya ya Daga hannu yana Fadin”Allah ban miki dariya ba,Srry afuwan haba Malika ta,Haba yar Amanata,Kinfan san Nidake bata baci kada ki bari Ya marwan ya Hadamu fa..”Ya fada yana Dariya wacce takasa tsayawa.
Da Haushi ya kama malika sai ta bishi zata makamai Rigar hannunta tana Fadin”Zaka sani ne,wato ma Dariya kake,Tunda ni kamin ciki kabarni da aiki ko,ai akanka zan Wuce yasin kuwa..”Ganin tayo kanshi yasa ya haye gadon yana Dariya sanin dayayi bazata iya hayowa ba,itako ganin haka yasa tayi tsaye kafin ta saki kukan Shagwaba,Ganin haka yasa ya sauko daga kan gadon ya Rumgumeta ta baya yana Fadin.
“”Srry bari kuka kinji,nine ko..? Bazan karaba insha Allahu na bar dariyan.”Yafada yana Kamkameta ta gefe daya kuma ya zuro duka hannayensa biyu yana Shafa tsinin Cikinta,ya marwan da joda ko Tun Shagwaban Farko suka Fice dauke da Ayda suna Dariyansu Saleem,shiko dakyar ya lallashi yar rigimar nashi tayi Shuru,abinci ma sai abaki ya bata,yayi mata wanka ya Shafamata mai,Ranar dai bata sanya kaya ba ammh Washe gari Dole Saleem ya Fice Zuwa neman ma Malika wanda zai Dinkamata kayan da zai Shigeta kada Ta Cinyeshi danya da Masifarta.😂
Washegari ko Sai da Malika ta Sanya Wani leshi wanda Saleem yasa aka Dinkamata Riga da zani,rigar sai aka Budeta sosai har Zuwa gwiwanta,Dalilin daya sanya ta barshi ya Fita kenan ammh da tace wlh sai dai su zauna tare agida Tunda dai Shi yayi mata Abunda kaya suka Daina Shiganta,😂Saleem yaso su koma katsina Aranar ammh Ummi ta hana Dole suka bari sai monday,yan kumo da abokan Sadiq dai Aranar suka koma.
*
Ranar monday Tun Safe da karfe 10 am na Safe iyalan IG kabir kumo,suka Raka amarya Saleema da angonta Sadiq suka hau jirgi zuwa garin Abia inda Sadiq din yake aiki acikin masu rakiyan Harda Abbi da Ummi da Hajiya babba da Hajiya binta da malika da Saleem,da Ayda da joda da ya marwan,dukkansu suka rakasu har Filin jirgin Nnmadi azikiwe internationl Airport,suka rabu cike da kunci Saleema dakyar ta saki Abbi da Ummi wanda ta Rumgumesu tana kuka,hakama tama Saleem da Ya marwan Wadanda suma sunji ba dadi musamman ma Saleem domin Shine yafi kowa Shakuwa da Saleema,haka ta Rumgume joda da Malika tana kuka,wani karfin Hali ta rike Ayda wai sai tatafi da ita😂Malika ko tace ta bata Halas malak ta tafi da ita har Saleema ta fara murna Saleem yace Bazai yuyu ba ta bari ta kara girma lokacin,Sunzo ganin gida,sai ta tafi da ita,Dole murnan Saleema ya koma ciki Dakyar Sadiq yajata suka Shiga jirgin Tunda ana ta kiran Sunanyensu,Haka suka dawo gida jikinsu Duk yayi Sanyi musamman Ummi,Motar Saleema kuma Sadiq yace zai aiko Direba yazo ya dauka ya kaimata chan,Tunda achan zatayi Service dinta,kusa da mijinta.
Suna dawowa Daga raka Saleema,Su malika sukayi Shirin Tafiya,Ummi taso su tsaya ammh Saleem yaki,wai saboda wajen aikinsa,kuma bashi da alamun barin Malika dole Ummi ta bisu da Allah kiyaye hanya,Wannan karon Saleem yacema Ummi zasu tafi da Ayda bata hanasu ba Tunda yarsu ce,ammh sai Ayda ta watsa musu kasa a ido ta makale Ummi tana kuka Dole Saleem ya kyaleta,da Abbi yaji lbri dariya yayi yana Fadin”Su Saleem masu ya”Toh rigimar me yakeyi ga matarsa chan da wani cikin,ko kuwa Rashin kunya yaran zamani..”Dariya kawai Ummi da ya marwan sukayi tayi Sanin Halin Saleem din da Shi kanshi Abbi.
Tare da Hajiya Binta suka Wuto katsina sai aka bar gida Daga Joda sai ya marwan wanda sai Wani Sati zasu koma Lagos din,Su malika sun isa gida lafiya,hajiya kuma har gida suka kaita,koda suka koma su Merry sun gyara ko”ina na gidan,Saleem baima Zauna ba office ya wuce saboda an kirasa yana da baki itako Malika Suna dawowa Ta fada gado tana barci don ta gaji ga bayanta ya Rike kafarta kuma ta haye Saboda Zaman mota.
MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
