Search
You have no alerts.

    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    “”A daren Ranar Dr Abbas,ya kawo sakamakon gwajin Malika inda sakamakon ya nuna Malika tana dauke da ciki har na tsawon Sati goma,wato wata biyu da sati biyu kenan, malika ta karbi takardan ta Tsurama ido,sai taji kwallah na zuraromta,lokaci daya dawani takwalli da kuma natsuwar zuciya Tun bayan data dinga maimaita Innalillahi wa”inna Alaihirraju’un,kawai don kuka ya zama dole ne gareta,ammh lokaci daya tana jin tana bukatar itama abokin da zai kasance shi kadai ne zaiji kanta Aduniya,shiyasa ta daura kudirin kullah kawance da Abunda ke cikinta,kila watarana shi zai zama gatanta.

    Hankalin Daddy ya bala”in kwanciya lokacin daya ga Malika ta kwantar da hankali,bata kara nuna damuwarta kan cikin ba,Dr Abbas da kanshi ya kawo mata magungunar karin jini,da kuma na sa cin abinci,yawan tarun miyau kuma datakeyi,ya umarce ta data rika yawan shan sweet hakan zai taimaka ya rage tsinka mata yawu.

    Mganar Amai kuma yace sai zuwa cikinta in yayi kwari,ammh yace taguji Abunda bataso,saboda shima yawan aman yana sakarma damai ciki jiki,duk sai tazama ba kuzari atare da ita,wani lokacin ma sai anyi mata taimako da drip ko zata samu karfi,ta karbi duka dokokin likita da hannu biyu kuma ta shiga kokarin kiyayewa,Sai dai Abun da bata gane ba Hajiya binta ta taimakamata.

    Sai washegari kana Daddy ya kira Abbi ya sanar dashi Abunda ke Faruwa,
    Abbi na zaune bisa kujera afalonsa Ummi na gefensa alokacin,Mikewa yayi Tsaye yana Fadin”Allahu Akbar..!Allahu Akbar..!Allahu akbar…”!Har sau uku yana nanatawa kafin yace”Kaji ikon Allah ko Abdulmalik,Wlh rabon dake tsakaninsu ne yasa akayi auren nan cikin gaggawa,da”ace munyi tsaiko ko munyi gaddama toh da Allah ya nuna mana karfin rabo,ko wani cikinmu ya bar Duniya,ko asamu cikin ta wata hanya,wanda dukkanmu bazai mana dadi ba,Kai Allahamdulillahi Allah Abun godiya,ina malikar tana lafiya ko? Yafada yana bayyana Farincikinsa Amganarsa.

    Daddy yana mirmishi yake Fadin”Hakane wlh Abokina,sai mu godema Allah,Malika na nan lafiya,sai dai Abunda ba”a rasa ba,kasan masu shigar sabon ciki sai ahankali,wuni take amai komai taci sai ta dawo dashi,abincin ma ba sosai take ci ba…”Jinjina kai Abbi yayi kafin yace”Allah sarki hakane Abun sai ahankali agaisheta kafin muzo,kuma insha Allahu mijinta nadawo zai zo ya dauki matarsa ya kuma baku hakuri insha Allahu.

    Daddy yace”Ayyah bakomai kumo,Allah dai ya Rufamana Asiri kawai..”Nan suka Cigaba da tattaunawa kafin su yanke kiran,Ummi dake gefe ta zaku ya gama wayar taji wani Abun Farinciki ne ya samu haka,yake ta faman washe baki yana kabbara.

    Nan yake sanar da ita Abunda Daddy ya sanar dashi,Washe baki tayi tana hamdala ga ubangiji take Fadin”Masha Allahu da samun Surikar Farko,kuma Alhamdulillah da samun karuwar jika agidanan akaron Farko…”Take Fada duka hakoranta waje,Mikewa tayi tana Fadin”Bazan ji wannan Abun Farincikin ni kadai ba,dole sai Hajiya taji itama..”Ta fice yana mata tsiyan ko kunya,itako tana Fadin”Ba marwan bane,saleem ne ba Dan Fari bane balle yace wani Abu..”

    Da Hajiya Babba Taji rike Ummi tayi tana Fadin”Don girman Allah Da gaske kike Aisha…? Tafada tana zaro ido,Rantse mata tayi tana sanar da ita shi mahafin malikan da kanshi ya kira waya ya sanar da Abbi,ai Hajiya Sakin Kabbara tayi itama kafin tace”Kai Salihu Dan albarka ne,da haushinsa nakeji game da ta”asar da yayi ammh yanzu ya wankemun zuciyata kal,kai ni wlh duk gidan nan ko Kabiru yanzu bai kai Saleem Farantamin ba,shi yafara yin aure agidan nan,gashi kuma shi zai Fara haifamin tattaba kunnina ina raye…”Tafada tana sharan kwallah Farinciki,lbri fa ya zaga ko”ina hatta Saleema dake mkranta tasamu lbrin nan,wanda Sadiq yake sanar da ita,shima Ummi ta gayamai shiko Marwan yana chan ya samu lbri jinjina kai kawai yayi yana Kiyasta dama ana samun ciki daga zuwa daya😝🤔,lalle ko in hakane ya jinjinama Karfin mazankutan kanin nasa.

    *

    Jirgin daya kwaso al’ummah Dabam Dabam daga birnin na ikko wato lagos shine ya yada zango A babban Filin jirgin Mallam Aminu kano international Airport.

    Acikin wanda jirgin ya sauke harda Acp Saleem kabir kumo,wanda ya sauka jiya da daddare,daga kasar ta chicago,to dama dayake jirgin daya shigo wanda zai yada zango a lagos ne,shiyasa ya kwana a hotel da safe kuma ya biyo jirgi zuwa kano.

    Tafe yake wayarsa makale akunnasa yana sanar da Inspector sale,gayinnan karisowa,sanye da riga da wando black and White,na kamfanin armani,sai wata jaket daya dora asaman farar rigarsa,jakar brief case dinsa ne makale ne kafadansa,sai kafarsa dake sanye da Rufaffen Takalmi na Fatan damisa.

    Hankalinsa na kan wayar da yake yi sai ji yayi gam!an ban gaje shi yayi baya har sai da wayar hannunsa ta subuce masa ta fadi kasa ta tawartse, dagowa yayi cikin zafin nama yaga wani banzan ne,wanda ke Tafiya baya kallon gabansa.

    Ita kuma ta taho tana sauri hankalinta yana ga Best dinta tada hango,hannu ta dagamata jikin ta na rawa ta nufeta,ashe shi kuma saleem ya taho,kawai sai ta bangajeshi batare dama ta lura ba,sai da mai afkuwa ta Faru.

    Durkushewa tayi tana tararra mai wayar tana Fadin”Oh! my god…Na bani ni Zahra…”Take Fada tana kwaso mai part part din wayarsa data baje akasa,Dagowa tayi daga tsugunnan ta mikamai wayar tana Fadin”Am so srry I don”t know dat u ar coming kayi hakuri…”Ta fada lokacin data sanya idanuwanta akansa bata san sadda ta Furta “Wow…!!!…”Saboda yadda gayen ya Tafi da duka imaninta.

    Shiko sagale yayi yana binta da kallo,kyakyawan Budurwace,doguwa mai kyan tsari da jiki dana Fuska,fara tas,ammh daga kallon Farko zaka Fahimci tana da rawan kai da kaudi,Sanye take da riga da sikat na wani leshi mai adon duwatsu,ta sanya babban mayafi ta Rufe jikinta,cikin Abunda baifi sakan goma ba,ya kare mata kallo,itako bakinta sake tana binshi da kallon kurillah zuciyarta na bugawa.

    Yaken baki yayi mata kafin ya mika hannu yana fadin”Is ok…”Ya fada yana mikamata hannu da nufin ta bashi wayarshi,gani yayi hankalinta baya jikinta ta saki gabadaya hankalinta akanshi tana kallonshi,wani takaichi ya cikashi,da dan karfi ya Furta”Hy…”

    Sai gashi tayi Firgigit ta dawo hayyacinta,bai mata mgana ba,illah hannun daya mika mata,kunya duk ta kamata tana sosa keya ta mikamata tana fadin”Tanque sir…”Kanzil bai ce mata ya ratsa ta gefenta zai Wuce ganin da gaske yake tafiyan zai yi yasa da azama tace”plz Nace ba…?.

    Cak ya tsaya kafin ya waiwayo yana Fadin”U say what…? Mirmishi ta sakamai kafin ta mikamai farin hannunta tana fadin”Am *ZAHRA BUKAR MADA* by Name, inko…? Wani kallo ya watsa mata kafin ya dan ciza gefen bakinshi yace” Am *ACP SALEEM FREEKING KABIR KUMO*…”Da hanzari ta katseshi tana Fadin”Wow Fabulos,ashe ina tare da ACP ne,kai Nice to meet u Sir…”

    Mirmishi yayi mata,ganin yadda take wani rawan kafa,yana shirin barin wajen takara cewa”Plz sir can i hv ur digit…? Zaro ido yayi yana fadin”Whta…? Langwaba kai tayi tana Fadin”Plz Sir…,? Bata rai yayi saboda tsakani ga Allah ta isheshi agogon hannunsa ya duba kafin yace”Ok 080…….'”😝Haka ya rattabamata tana kwashewa bisa wata faskekiyar wayarta kafin ta gama tana Fadin”Tanque Sir…”

    Juyawa yayi yana Fadin”U ar wlcom…”Da kallon sha”awa ta bishi ganin yadda yake takunsa cikin isa da takama,tana kallonsa har suka hadu da inspector sale,suka yi musabaha suka gaisa,kafin su danyi wani mgana,suka kara musabaha,kafin ya bashi key din motarshi sukayi Sallama daganan shikuma ya Fada motarsa kirar 4matic ya Fice daga Airport din da hanzari.

    Hankalinta na wajensa sam bataji karosowar mutum akusa da ita ba sai ji tayi an daka mata duka abaya,Zabura tayi zata saka ihu sai ganin *BEST NADIRA* Dinta wacce ke tsaye jaye da Trolly dinta tana zabgamata harara,da hanzari ta Fada jikinta tana Fadin”Wlcm home my best,kefa nake ta jira tun dazu..”.

    Wacce aka kira da best ta bamberata daga jikinta tana Fadin”Toh tsarani,kika dai tsaya tsinannan rawan kanki,keda wa nake hango ki tsaye tun saukowata daga jirgi..? wani Fari ta mata kafin ta ja hannunta da hannu daya dayan kuma taja trolly dinta tana Fadin”Kedai bari my best today i meet my mr Right wlh…”Da kallon mamaki Best din ta bita kafin tace”Topha wanene shi..?

    Suna tafiya ta bata amsa da cewa” * ACP SALEEM KABIR KUMO*….”Baya taja tana maimata sunan da sigan tambaya”Acp saleem kabir kumo fa kika ce? tsayawa tayi itama tana kallonta kafin tace”eh kinsan shi ne…? Mirmishi ta saki kafin tayi gaba tana Fadin”Eh mana waye baisan shi ba yaron IGP ne fa nakasa gabadaya…”Ido Zahra ta zaro tana Fadin”Wow!Kice Abba ma zai sanshi…?

    Tsaki taja tana Fadin”Kina da mtsala,toh bama Abbah ba,kowa dake kasar nan yasanshi,ko kin manta shine fa kwanaki ya auri diyar dan kasuwan nan mai kudin bala”in nan Malika malik,kuma ya saketa adaren Auren..”Kwalalo mata ido tayi daidai lokacin da suka iso bakin motar da zahra tazo da ita kirar 306 tana Fadin”Kai don Allah ya”akayi ni ban sani ba..?

    Tsaki taja tana zagayawa bangaren mai zaman banza,sai da ta bude motar ta shiga kafin itama zahra ta bude baya ta jefa Torolly din ta bude bangaren Direba ta shigo daidai lokacin da Nadira take Fadin”Dallah wake ta sha”aninki keda sai kiyi sati baki hau social media ba,mu gani kamar last 3 month ne Abun ya faru,wlh kwanakin kowata jarida Abunda tayi ta bugawa kenan haka Social media anyi ta yama didi da zencen..”

    Shuru zahra tayi bayan tayi Tagumi take Fadin”Toh kuma wai da gaske ne..”?Hararanta tayi tana Fadin” Bansani ba,Tunda zan miki krya ne,Kinga zaki tukamu zuwa gida ne,ko kuwa zaki tsaya jin gaskiyan ne..? Tafada cike da kosawa,tabe baki tayi tana fadin”Oho miki dai,badai ya saketa ba,niko naji na gani inaso,don ganin farko naji yamin wlh best ya sace zuciyata inaji kamar i can’t do Withount him…”Galala Nadira ke kallonta kafin ta kada kai tana Fadin”Eh naga alama..”Ta fada tana binta da kallon mamaki,yadda take driving tana mirmishi ita kadai.

    *WACECE ZAHRA BUKAR MADA*

    Diyace ga Tsohon Alkalin Alkalai na kasa gabadaya *BUKAR MADA* Asalinshi dan Maiduguri ne,dagashi har matarshi *HAJIYA SAHURA* Kafin zuwanshi wannan mtsayin ya rike alkalai akotuna dadama kafin yazama Alkalin Alkalai.

    Sun dade da aure kafin Allah ya basu Haihuwa Mace *ZAHRA* Kuma Tunda ga ita bai kara samun haihuwa ba,gashi da son ya”ya wannan Dalilin ne bayan rasuwar dan”uwanshi Shehu dake lagos da zama shida matarshi da yaranshi,ya dauko Biyu daga ciki, *NADIRA* da *NADIR* wanda ya rikesu tun suna yara awajensa sukayi karatu,har zuwa girmansu….

    Ita kuma Nadira da Zahra kusan sa”annin ne tare suka tashi sun Shaku da juna matuka,komai nasu tare sukeyi kamar wasu yan biyu,shiyasa suke kiran juna *BEST*,tare sukayi karatunsu a jami”ar Base dake Abuja,Nadira ta karanta Microbiology,sai Zahra data karanta *Mass com* Dukkansu sun kammallah harta master dinsu kowacce ta gama,ammh basa aiki saboda Abbansu bayi da sha’awan haka sai dai yafi sha’awar kowacce taje dakinta in mijinta ya yarjemata ta yi aikinta,in kuma ya hana ta dai samu ilimin,shiko Nadir likita ne ajami”ar Malesiya yayi karatun likitansa,abangaren mata,ayanzu haka yana Asibitin Mallam Aminu kano yana aiki a matsayin babban likita.

    Ko atasowar Nadira da Zahra akwai bambamci hallaya atare dasu,domin Nadira tafi zahra wayau da sanin kan Duniya sosai,sakamakon ita Zahra bata son komai sai tabara da sangarta,ga rawan kai da Feleke barta da son asani da kuma Shigen Shisshigi ammh fa sakaryace,sai dai akwai daukan wanka bata shigar banza,saboda Bukar mada bai barsu haka ba,Shida Hajiya sahura basu yi musu Rikon wasa ba,

    Zahra sha”anin Shigen shigen Yanar gizo bai dameta,ko waya ma ba damunta yayi ba ita dai barta da kallon India Series kamar wata mayyah,to anan tafi Auki,ta Wuni tana kallo bata gaji ba,in ko ka ganta da waya toh ba chart take ba,sai dai game don anan Tafi auki,sakamakon Nadira mace ce mai son Nuna ita wayayyiyace,Tana son Shiga yanar gizo,babu Kalan Social media Da batayi sai dai wanda bai Fito ba,kuma babu Wanda indai ubanshi kusa ne agwannati da bata sanshi ba,shiyasa tasan lbrin Saleem da Malika,domin Malikar ma tana Following dinta a intergram dinta,ada suna zaune Abuja ne,ammh bayan saukan Bukar mada daga Kujerar Alkalin Alkalai,sai suka koma kano da zama.

    Haduwarta da Saleem A Airport ma taje dauko Best Nadira ne,wacce taje lagos wajen mamanta Hutu,shine suka hadu da Saleem kuma lokaci daya taji ya sace mata Zuciya da gangar jiki gabadaya.

    Wannan kenan.

    _____________________

    Shiko Saleem daganan Kano Zamfara ya Wuce kai tsaye,bai fara isa gidansa ba,sai da ya biya headquater su yayi Report ya gaisa da abokan aiyukansa,kafin ya isa gida,yayi wanka yaci abinci dama already ya tsaya wani restaurant ya yi ma kanshi take away,yana gamawa ya fadi bisa gado yana barcin gajiya wanda bai tashi ba sai gab da kiran sallar mangariba.

    Washegari Tun karfe 7:30am na safe yasaka hancin motarsa bisa hanyar Abuja,domin ya kosa yaje ayi wacce za”ayi domin yasan Abbi da Ummi suna jiracesa dashi ne.

    A yau din yana sanye ne da Riga da wando,Wandon Nevy blue ne,sai Rigar Ash ce tana da ratsin layin blue ajikinta,kuma dogon hannu gareta,mai dauke da botura ta kasan hannun,kafarsa ko Yau Budadden Takalminsa ne mai kalan blue shima mai kyau da tsari.

    Kusan mutumin naku da gudu bisa hanya kamar zai tashi sama,sai gashi koda karfe 11:00am na safe tayi mai kofar Tamkamemen gidansu yana Zuba hon,megadi yana lekowa ya ganshi,jikinsa na rawa ya wangalemai get yana mai sannu da zuwa,Shiyama budemai kofar motar sanda ya gama daidaita zamanta a parking space….

    Bayan ya Fito sun gaisa kai tsaye ya nufi cikin babban Falon gidan,ammh wani sashe na zuciyarsa na bugawa da tsoro baisan da wani tarba Abbi zai karbeshi ba,da siririyar sallama ya kutsa kai Falon,babu kowa sai karan tashin Talabijin daya keyi Shi kadai,tsaye yayi atsakiyar Falon yana karema ko”ina kallo,ganin babu motsin kowa shiyasa ya kara daga murya yana sallama cikin fargaba…..

    Ummi na kichen tana hadama Abbi breafsat dinshi yau ya tashi bayajin dadin jikinsa,.taji sallama daga farko,ammh jin Shuru ba”a karayi ba yasa tabasar,ammh sai takaraji an sakeyi bata dauki murya ba ,ta Fito da hanzari tana amsawa sai ta ci karo da Saleem tsaye yana kallonta,

    Daure Fuska tayi kamar bata taba saninshi ba ballantama ganinshi tace”Lafiya mallam daga ina..? Gwiwanshi ne yaji yayi sanyi yana neman dukawa ya gaisheta yaji Muryan Abbi da kakkausan murya yana Fadin”Kai…Kul!…Kada ka sake ka dukamin Agidana…”

    Abbi ya Fada yana saukowa daga saman Step sanye da bakar jallabiya,Jin haka yasa Saleem bai dukaba ya mike yana marairaicewa Abbi yana gama saukowa ya kalli saleem yace cikin kakkausan murya

    “Yi baya nace…!Ya fada da tsawa,sororo Saleem yayi kafin ya bude baki yace”Ab….!Yi baya nace Saleem..!Abbi ya kateshi yana sake maimata mganarsa,mganar Abbi cikin fada ne yasa Hajiya Fitowa tana Fadin lafiya,sai kuma ta ci karo da Saleem baki ta kama tana Fadin”Kai kuma Salihu daga ina haka? sai kace wanda yayi sata aka biyoshi kana wani rarraba ido kamar wani maye…”Tafada fuskarta ba Fara”a

    Yana ganinta yafara taku zuwa gareta yana Fadin”Yauwa hajiya don…”Saleem zanci mutumcika nace kayi baya kaficemin daga gida ko?

    Cak ya tsaya yana kallon Abbi shiko kara tamke Fuska yayi yana Fadin”Ficemin daga gidana,ai kaji sakona wlh tallahi indai ni kabiru ni na haifeka bazan yadda kacigaba da amsa sunana amtsayin sunan mahaifinka ba,sai ka juya daganan katafi katsina ,kaje kabama Mahaifin Malika hakura ka kuma dauko matarka ku dawo cikin gidan nan tare,na ganka ka Shigo kafarka kafarta,sannan zan yarda ka sake shigomin gida har ka rabi suna na amtsayina na mahaifinka,in kuma ba haka ba,Wlh tallahi bani ba ka Saleem har Abada kuwa kajima na rantse….

    Yana gama fadar haka ya juya yana Fadin”Aisha kawomin Ruwan zafin..”Daga haka ya haura sama ransa bace,toh Ummi tace bata ko kara kallon Saleem ba ta koma kichen ta dauko Fulas din ruwan zafi da kofi tayi hayewarta sama,Hajiya babba ma kallonsa tayi kafin ma tayi mgana taga ya juya Fuu..!ya Fice kamar zai tashi sama baki ta rike tana fadi afili…

    “Anya wai yaron nan kalau yake…? kai ban yarda ba kila dai ya fara shan kwayoyin zamani…”Tafada tana kara rike Haba, kafin ta juya ta koma dakinta tana sababi ita kadai.
    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    Note
    error: Content is protected !!