Maleeka Malik – Chapter Nineteen
by NadminMASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
————————“Har Weeked din tazagayo Saleem bai sakarma Malika ba,Kullum Fuskarshi ba Fara”a,Karatunta kadai yake kokarin yimata shima ba cikin dadin rai ba,kamar yadda ya saba ba,Shiyasa duk karatun ya Fita akanta,Damuwa tayi mata yawa kuma bata da wanda zata Fadamawa,sai Allah shi kadai take kaima kukanta dayayi mata mganin Abunda ke damunta.
Daga wannan Fushin rashin dalilin da Saleem ya hauta dashi Ta fahimci ta fada tarkon sonshi mai tsanani,Domin ta azabtu sosai,ashe koda baya mata mgana sosai,Fuskarshi dayake sakar mata ma kadai Tana sata nishadi,ammh da zarar ya bata rai Shikenan itama zata Shiga damuwa,balle wannan karon da Fushin nashi ya tsauri dayawa ne ta rasa ina zata saka kanta taji dadi….
Yau ta kama Lahadi ne,Tun safe ya Shirya cikin wata dakakkiyar Shadda Navy blue,mai maiko da yarari tana Falo tana gyarawa ya Fito daga dakinshi yana daura agogon hannunshi,da ganin yadda yake komai cikin hanzari zaka Fahimci sauri yake,ganin Fitowarshi yasa ta rankwafa tana gaisheshi akufule ya amsa kafin ya dago kanshi yana kallonta kanta na duke kasa,tana wasa da Kwalliyan hannun Bakar Doguwar rigar dake jikinta.
ido ya samata kawai yana kallonta,cike da mamakin ganin yadda tayimai rama ido,Gyara tsayuwa yayi kafin yadan yi gyaran murya yana Fadin”Armm nace ba..”Dagowa tayi cikin tsoro da mamaki tace”Na”am me kace..? Kur yayi mata da manyan idanuwanshi yana wani shafa gemunsa da hannunsa guda,saurin kauda kai tayi jikinta yakama bari haka kurum,yana lura da ita,kawai sai ya barsa yace”Zan yi Doguwar tafiya yau,bansan ya zamuyi da abincinki ba..”Yafada yana kara gyara zaman rigar jikinsa.
Kanta na kasa tace”Ba damuwa akwai sauran Fura jiya,kuma maman Abba ta kawomin Faten wake jiya,toh banci ba,sai naci shi yau..”Bai damu ba kawai ya tabe baki ya Wuce yana wasa da makullin motar dake hannunshi yana Fadin”Ok sai na dawo..”Mikewa tayi tana bin bayanshi da kallo cike da sha’awa murya chan kasan makoshi ta Furta”Adawo lafiya Allah ya tsare..”Addu”arta tamai dadi sosai har sai da ya waigo yana kallonta,ita kuma tayi saurin Kauda kai,tana cigaba da kakkabe kujera,Mirmishi yayi yana kallon cikinta wanda ya tasa,kafin ya kada kai ya juya yana Fadin”Nagode da adduanki..”Ya furta cikin muryan kulawa da jin dadi,Kafin ya Fice da sassafa yana takunsa na isa da takama mai cike da jarumta.
Sai da ta tabbatar daya Fice kafin ta koma bisa cafet din Falo tayi zaman dirshan hannuwanta dafe da kirji tana dan ware ido kafin ta bude Lebe kamar tana kwakwaiyon mgana ta furta.._Nagode da addu’anki.._……” Tafada tana Wani lumshe ido,kamkame jikinta tayi tana dariyan jin dadi,cikin jikinta tabi da kallo kafin ta kuramai ido tana shafashi take fadin”Boy katayani murna Abbanka ya yafemin laifina,har yayimin mirmishinsa din nan,mai tsada kuma yayimin godiya..”Tafada tana bayyanar da jin dadinta,ganin babu mai bata amsa yasa ta rarrafa tatashi ta cigaba da Abunda takeyi,ammh ranta fes,gefe daya kuma yau Saleem din yafi koyaushe yimata kyau,don ta yaba da wankan sosai,sai kuma ta Fahimci cewa kamar in yasa manya kaya yafimasa kyau sosai,barin ma ya karya hulan nan nasa,wayyo kamar taje ta Rumgumeshi ta lasan mai baki haka takeji.
__________________
Sai da ya Shiga cikin kano kana ya kira Zahra ya fadamata gashi a kano,kinga zahra kamar kanta zai Fado kasa saboda zumudi,dama already Tun jiya da sukayi waya ya sanar da ita yau din yana tafe,so Tun safe gidan ya rikice da hidiman taron bakon Zahra,wacce takejin kamar ta bude ido ta ganta agaban Saleem.
Hajiya saratu wacce suke kira Momi itama Zahra har mamaki take bata ganin barin jikin Datakeyi,har sai da tayimata fadan saura in saurayin yazo karta kama kanta Tunda ta riga tasan halin kayanta,Mirmishi kawai Zahra tayi aranta tana Fadin”Momi bata san so ba..”Koda Saleem ya kira Yace gashi ya shigo kano sun riga sun kamallah komai har zahra ta buga wanka da kwalliya cikin wata dakakkiyar Shadda mai ruwan orange,ammh light dinta dinkin Riga da zani ne,Tayi daurin ta wanda ya Fitar da gashinta wanda ta daureshi da band daga baya,Fuskarta cikin Simple make up,wanda Nadira ta bata lokacinta wajen tsansara mata ita,abinci ko basu san adadin kala nawa suka girkamai ba,balle ababen sha da suma babu kalan wanda ba”ayimai ba,ga kuma surkin irin na kwali ma”ana na bature
Kai tsaye Zahra ta sanar dashi ya tambayi Anguwan GRA,in yazonan ya Tambayi gidan tsohon alkalin alkalai Bukar mada,za”a nuna masa,haka ko akayi dayake gidan ba batattace bane,bai sha wahala ba,sai gashi ya faka motarshi kirar 4matic acikin kayatattacen haraban gidansu zahra,Koda ya Fito daga motan ya hankalce yake bin gidan da kallo yana Dan tabe baki,Megadi ne ya kariso da hanzari ya rankwafa yana gaisheshi ya amsa daidai yana kiran zahra,sanda ta Dauki wayan yake sanar da ita gashi aharaban Gidansu ta Fito.
Tsalle ta buga tana dafe kirji bakinta yaki Rifuwa,zaman mayafin jikinta Nadira ta gyara mata tana kara Fesa mata Turare take Fadin”Oy act very well best,nasanki banda rawan jikin nan,naki da kuma shegen kanki dabaya zama waje daya.”Tafada tana dunguremata kai,dariya tayi tana Ficewa cikin wani taku,kafarta sanye cikin wani ubansu takalmi mai dan Tudu ammh ba sosai..
Afalo ta tarar da Momi zaune cikin yauki da Murna tace”Momi ya iso fa..”,Da kallo ta bita kafin ta mike tana Fadin”Masha Allah,ki mishi sannu da zuwa,Ammh don Allah ki natsu Kinji zahra..”,Tana yar dariya ta Rufe Fuska tana fadin”To momi..”Tafada tana wucewa zuwa kofar da zata sadata da haraban gidan.
Tundaga nesa ta hangeshi yana jingine jikin motarshi yana latsa wayarsa,takowa take gareshi cikin wani taku,kamar wata hawainiya,ammh duka idanuwanta na kanshi harta kariso gabanshi bai sani ba,sai da yaji wani Sihirtattacen kamshi ya dukeshi kana ya dago suka hada ido da ita,Ajiyar zuciya ya sauke ya maida wayarsa aljihu yake Fadin”,Madam sai yanzu,? bayan kingama shanyani awaje..?
Wani mirmishin dariya tayi tana kulle idanuwanta da tafukan hannunta take Fadin”,Am srry,Barka da zuwa jahar kano,koda mai kazo an Fika…”Dan mirmishin yake yayi yana binta da kallo afaikace kafin yace”Au! haba..?Ashema hakane..”Yafada cike da dan barkwanci,dariya tayi mai sauti kafin ta juya tana Fadin”,Yanzu dai duk ba wannan ba,mu shiga Daga ciki..”Bai yi gardama ya fara binta abaya ita ko jin kamar yana kallonta,sai yasa salon tafiyar da Nadira tagama koyamata duk sai ta rude ta fara hardewa kamar zata fadi.
Shiko Saleem idonshi kur akanta cikin mintina ya kare mata kallo,Mele baki yayi aranshi yana ayyana Malika ta Fita komai na cika amace,ammh kuma duk da hakan zai iya maneji,ammh Shegen rawan kanta ne ke bashi haushi,domin ta gwadamai har suka isa falon bakin ta nuna mai daya Daga ciikin kujerun Falon,ya samu waje ya zauna yana binta da kallo,ciki ta koma sai kuma chan ta dawao tazo ta zauna akasa suna kara gaisawa tana tambayanshi ya mutan gidan.
Basu jima ba sai ga Nadira da yar aikinsu sushigo da manyan Farantai shake da kololin abinci,daya kuma shake da jugs na Lemukan da suka hadamai,Nadira ta zauna suka gaisa sosai harda dan barkwaci yayi mata,kusan dai mutumin naku shima in yaso wasa toh babu wanda yakaishi iya barkwanci da Raha.
Fita tayi ta basu waje suka cigaba da hiransu,wanda duk rabin hiran Zahra keyi,shiko sai jefi jefi zaiyi dan dogon mgana,ammh daga gyada kai sai mirmishi in yazama Dole,ada bai yi niyyar cin komai ba,ammh zahra ta nuna bataji dadi ba harda hawayen karya tayimai,shiyasa yace ta sanyamai Sinasir,da miyar ganye,wanda yaji manshanu da naman Rago yaji kuma dayawa saboda Dama sinasir mutuminshi ne,shi da waina yana sonsu sosai.
Lemun kuma kunun ayan yasha sosai,sai zobon shima dai baisha da yawa ba,sun sha Fira har anan yake sanar da Zahra cewa Basu rabu Da malika ba,kamar yadda Duniya ta dauka,so yanzu hakama tana zamfara tare dashi ya sanar da ita hakane saboda yana ganin kila yayi maneji da ita,Sanda ya sanar da ita taji ba dadi ammh soyayyarshi ta Rufemata ido,ta sanar dashi babu komai,ko da’ace Itace ta hudu tana sonshi ahaka kuma zata aureshi yaji dadin mganarta ya sanar da ita da zarar ya koma gida sai Tuntubi mahaifinshi yadda suka yanke zai sanar da ita ta waya,Ai murna kamar Zahra ta Shide,sai kace ance gobe ne bikin.
Sai After 4 kana yayi Shirin tafiya,bai Tafi ba sai da zahra ta shiga dashi babban Falon gidan ya gaisa da momi,wacce ta yaba dashi sosai Fiye da Tunaninta,domin bata zata cewa zaben na zahra ya Wuce tsara ba haka gashi kuma dan manyan gida ne,cikin Fara”a da kunyar Diyar Fari ta amahesu suka gaisa kafin yayi musu sallama Su Zahra da Nadira suka rakosa har wajen mota,suna karayin sallama kenan sukaji hon,megadi ya bude get,sai ga wata bakar motar BUGATTI,Ta sawo kai cikin gidan,kusa da motar Saleem aka faka motar kafin direban ya Fito da gudu ya bude bangaren baya Alkali bukar mada ya Fito yana gyara zaman babban Rigan jikinsa.
Zahra ce tace”La..Shikenan ma Nadira ga Abba nan..”Tafada cike da murna,shiko saleem gabanshi ne yafadi,gaakiya bai so sukayi arba ba,ganinsu tsaye yasa ya kariso yana kallon Saleem cike da mamaki,Tunkafin yayi mgana Saleem ya rankwafa yana gaisheshi,hannu ya bashi suka y musabaha yana kallon su Zahra tun kafin yayi mgana Nadira tayi karaf tace”Yauwa Abba gwara daka dawo,Saurayin Zahra ne yazo ACP SALEEM KABIR KUMO..”
Abbah yace”Masha Allah,..”Yana mirmishi yana kuma kallon Saleem,Zahra ko Fuska ta Rufe tana juyar dakai,Yar dariya Abbah yayi yana Fadin”Hakane..? to ku koma gida zan yi mgana dashi..”Nadira ce tace”To Abba ashigo lafiya..”tafada tana jan hannun Zahra wacce ke dagama Saleem hannu afakaice,sai da suka shige kana Abbah ya dawo da kallonsa kan Saleem yana Fadin”Sannu da zuwa..”Kan Saleem na kasa yace”Yauwa Abba,mun sameku lafiya..”Ya karba da lafiya lau.,daga ina kake,ma”ana waye mahaifinka..”
Bai yi gardama ba ya Sanar dashi sunan mahaifinshi,cikin jin dadi Abba yace”Masha Allah,tafiya tazo da sauki,ai Mahaifinka ba boyayye Bane,ikon Allah,munsan juna chan abaya gaskiya,kodai mene zan tabosa ta waya insha Allahu..”Yafada yana bayyana murnansa Afili,Saleem yayi kasake yana jin Bukar mada na Shirin ballo masa ruwa,Abbi da baisan da wata mgana ba,yanzu in ya samu lbrin mai zai ce mai..? Shiyasa har sukayi sallama ba cikin dalin rai ba,Wani karin fargaban ma,shi da kanshi ya umarceshi daya bashi nombar Abbi,kuma ya sakamai yana jin cewa yagama yawo,Abunda yafi bashi tsoro shine har yana sanar dashi ya kwantar da hankalinsa kamar ya samu zahra yagama.
Har yakai zamfara yana Tunanin irin matakin da Abbi zai dauka akanshi in yaji lbrin yana neman wani auren batare da saninshi ba,bai shiga gida ba sai da ya biya yyima Malika takeway,koda ya koma gidan bayan sallar mangari ne,Ta idar da sallah kenan ya Shigo,bai jira ma tayi mgana ba,bayan amsa sallaman datayi ya ijiyemata lodojin daya Shigo dasu ya Fice zuwa dakinsa yana jin jikinsa agajiye kamar wanda akayima mugun Duka,yana shiga dakinsa ya Tube ya Fada wanka yana jin Barci yana Lumshe mai Ido.
Abunda Saleem yake gudu shi ya Faru,don bayan dawowarshi gidansu Zahra da kwana biyu yana office da rana tsaka ya samu kiran Abbi,wanda sai da gabanshi ya Fadi,ya daga yana mai sallama Abbi sai ya karba sallaman kafin ya zarce da Fadin”Ashe kuma aure kake nema bamu da lbri…?”Wani yam yaji,kunya da tsoro duk sun kamashi,Sosa kai yafarayi kafin yace”Injiwa Abbi..”? Ya dakatar dashi da Fadin”Inji uban yarinya,jiya da yammah Tsohon Alkalin Alkalai ya kirani Bukar mada,ya sanar dani cewa kun ma daidaita kanku kaida yar wajensa,daga karshe ya jadaddamain ya baka Auren yarshi Duniya da lahira..”
Wani zufane ke ketomai ko tako”ina Dakyar ya samu zarafin Cewa”Tsaya kaji Abbi,wlh sau daya na…”Yimin Shuru mallam ba wannan na Tambayeka tunda kanunama Duniya bamu da daraja awajenka Saleem ai Shikenan,da ka boyemana ni ko Aisha akwai wanda ya isa ya hana ka kara aure ne? wlh babu saboda haka na kira ne na sanar dakai Sati mai kamaawa zan kira kumo,Baffa zai zo mu tafi kano ane ma maka aurenta…”Daga haka ya yanke kiran.
Tsaye saleem ya mike yana Goya hannunshi abaya,gashi da Abunda ke ranshi ne,kuma wanda yake bukata Abbi ya sanar dashi,ammh yaki farinciki baisan dalili ba,baya Farinciki da Auren Zahra kwata kwata arayuwarshi ga kuma Abbi ya dau Fushi dashi,ganin bashi da mafita ne ya kwashi rawan jikin kira ya marwan yana sanar dashi Abunda ke Faruwa,baki ya rike yana Mamakin me Saleem zai zama age dinshi yaron da ko 30 bai gama cikawa ba,Har zai ijiye mata biyu da ya jefamai tambayan ina zai kai mata biyu..? Kasa bashi amsa yayi don bazai iya sanar dashi rataye Malika yayi ba Shiyasa yake son kara aure,shidai rokon shi daya Ya kira Abbi da Ummi yabasu hakuri ya sanar dasu abunda yafaru,ganin ya damu ne shiyasa ya lallasheshi da cewa yanzu zai kira Abbin suyi mgana.
Koda Marwan ya kira Abbi,bayan sun gaisa yake sanar dashi Abunda Saleem ya gayamai,Mirmishinsu na manya Abbi yayi kafin yace”Rabu dashi Marwan,Yarinta da Shirme na damun kaninka,Nayi alqawarin bayan na shiga mganar auren nan daya dauko zan zare hannuna a sha”anin Rayuwar Saleem,saboda naga kamar ni na zama mai Takura gareshi..”Jin haka yasa Ya Marwan ya dinga ba Abbi baki,ammh yace shifa ya riga ya rantse so kawai yama barma mganar,dole ya hakura domin yafi kowa sanin Abbi kaifi daya ne.
Mganar da Abbi ya sanar dashi ya tabbata domin Ranar sati,da daddare bayan sungama karatu da malika sai ga wayar Zahra,nan take sanar dashi dazu su Abbinshi suka bar gidansu,kuma ma wani karin albishir an sanya musu ranar aure wata biyu masu zuwa,mganar tazomai abazata,haka yayi tagumi rike da waya yana jin zahra kamar ya fashe da kuka,Zuciyarsa bata karkata da Abbi ko Ummi, ba tafi karkata ga Malika tana tambayanshi anya ko yayi mata adalci Abunda yake Shirin aikatawa,duba da Halin data ke ciki,cikinta ya Fito sosai dayake tana da girman ciki,yanzu kawai ya sanar da ita zai kara aure ya zataji..”? Kawai zuciyarsa takasa natsuwa waje daya,duk sai yaji Danasanin biyema Zahra ma dayayi balle har yaje gidansu.
Zuciyarsa taki bashi karfin gwiwan sanar da Malika Abunda ke Faruwa,sai kawai ya share zuwa gaba ya sanar da ita,Sati daya da saka Ranar Ummi ta kirata da yammah,ranar ko ta koma awo,tadawo agajiya tana kwance kan kujera tana maida Numfashi,Bayan sun gaisa Ta tambayeta jikinta ne,tace mata da sauki yanzu tadawo daga asibiti,sai Ummi ta fara mata Nasiha da zaman hakuri kafin ta gangaro tana sanar da ita sai ta kauda ido game da Saleem da sabuwar amaryanshi duk da batasan ina zai ijeta ba..”
Tana kwance ne sai da ta zabura ta mike zaune tana Dafe kirji cikin Fitan hayyaci,Tama kasa cema Ummi komai kawai idanuwantane suka ciko da kwallah tana girmama girman tsanar da Saleem yayimata,ashe duk hasashen datakeyi gaskiya ne ya rataye tane saboda amanar mahaifinta bawai don shi yana Ra”ayin zama da ita ba,gashi zai auro wacce yakeso su zauna tare,ita kuma ko oho,Bayan sungama waya da Ummi takasa zama waje daya,zuciyarta na mata zafi,dan cikinta sai motsi yake,nan ta zube bisa Cafet din Falo tana ta kukan tsausayin kanta,batason haka take mugun son Saleem ba sai yau da akace zai yi aure,ji take kamar ta kashe kanta saboda bakinciki,ta riga tasani ita tazama bora shara,dama yaya lafiyar kura balle tayi zawo.
Haka yazo ya sameta cikin wannan Halin,daya tambayeta meke damunta,kawai sai tace cikinta ke ciwo,ya damu ya duka kusa da ita yana kallon cikin yake tambayanta ko su tafi asibiti ne? Kai ta girgizamai kafin tacemai ita ta sha mgani zai bari,Ganin yadda take kallonshi asace tana sharan kwallah ne zuciyarsa ta fara zargin wani abu,Daga karshe ma rarrafawa tayi ta mike ta shige dakinta tana Sharbe hawaye,da kallon mamaki ya bita,domin ranar ma ko takeawy din dayayimata ma bata kallah ba,balle har yasa ran zata ci,Dayakoma daki yayi ta tunanin kodai wani ya sanar da ita Abunda ke Faruwa ne,ammh kuma baya Tunanin haka,Saleema ce mai bakin rariya kuma basa shiri,ko shi din ma ya rage sakarmata Fuska don ya gane tana da raini ne,ganin bashi da amsa tambayoyinshi yasa ya watsar da batun ya cigaba da harkokinshi ammh bawai don bai damu ba,A”a sai don yana wofantar da Abun karya bashi muhimmanci.
Ko washegari da zai Fita sai da ya lekata tana kwance cikin bargo idanuwanta sun kumbura saboda kuka,Domin kwana tayu tana kukan tsausayin kanta da kishin Saleem daya hanata Runtswa,sai ajiya takara sanin cewa soyayyar Saleem yayi mata mugun kamu sosai,domin kishinshi ya kusa illata jiya,ga yunwa taki cin abinci.ganinta cikin wannan halin ya bashu tsoro har Saida ya zauna gefen gadon,yana yaye bargon data Rufa dashi,hannunta ya riko yaji zafi sosai,har saida ya dago yana kallonta kanta na bisa Filo tana kallonshi itama cikin wani yanayi.
Kuri yayi mata da ido,yana kallonta kafin yace”ke wai meyasa kin cika Taurin kai ne *MALIKA..*..”Yafada cikin wani yanayi yadda yakira sunan nata,sai da tajishi har tsakiyar kanta,Lumshe ido tayi tana jin wani yarr,balle ma yadda yaketa murza tafib hannunta,Cigaba da cewa yayi”Tun jiya nace miki ko zamu tafi asibiti ne kika ki yarda wai kinsha mgani,don Allah kalli idanuwanki yadda suka kumbura suka chanza kala?ko haka kikeso na barki daga baya wani abu yafaru Abbi da Ummi ko Daddynki suce da gangan naci amanarki ko..?
Dakyar ta iya bude idanuwanta cike da kwallah tace”Bafa wani abu bane,nama ji sauki..”Tafada tana kauda kai,Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya mike bayan ya saki hannunta,wanda shi kanshi Taushin hannun nata yafara dibamshi zuwa wani yanayi na dabam,A kaikace yace”Toh naji kin samu sauki,yanzu dai kya bari ko Maman Abba nama mgana tashigo ta dubaki kafin tatafi asibiti..”,Jin ya ambaci Maman Abba da hanzari ta dagamai kai,tana share kwallah,Ido ya sakamata har ya kada kai zai Fita ya dawo da baya yana Fadin”,Wai don Allah na tambayeki mana? wannan Koke koken duk miye silanshi,da nayi miki mgana daga jiya zuwa yau sai ki kama min kuka kina Share min kwallah,Nayi miki wani abu ne Daya bata miki rai..?”Yafada yana mai kureta da ido,duka hannunsa Sarke cikin aljihun wandonsa,na american Suit dinsa.
Runtse ido tayi tana Kyabe baki tace”Allah ba komai..”Ta fada tana juya baya,kada yaga hawayenta,Ya dade yana kallonta kafin ya kada kai yafice Abun na mishi ciwo,ace yarinya bata da aiki sai kuka,haba ai abun yayi sosai,gashi kukanta damunshi yake,in yana kaunar mutuwarshi toh yana kaunar kukan Malika,ita kuma bata ganewa
Yayi sa”a yana Fita yacikaro da Baban Abbah zai Tafi kai danshi mkranta Daga chan ya Wuce wajen aiki,wajensa ya karisa suka gaisa kafin ya tambayeshi ko Maman Abba na nan,don Allah yana so ta shiga ciki ta duba mai dakinsa ce,batajin dadi,Baban Abba da kanshi yakoma cikin gida ya sanar da Maman Abba sakon Saleem batayi jinkiri ba ta sanyi hijabinta suka Fito tare,nan suka gaisa da Saleem din yace zai Wuce in akwai wata mtsalane su nemasa awaya,Adawo lafiya tayi mai kafin ta Shiga gidan Aranta tana Fadin”Insha Allahu ma ba mtsala”Sukuma magidanta kowanne ya Shige motarshi zuwa wajen aiki.
Halin Da Maman Abba taga Malika ya bata tsoro,da hanzari ta dagota daga kwancen tana Fadin”Madam meya sameki haka? jikinki ya dau zafi,Allah yasa ba maleria bace ke son kamaki ba..,? Rau rau Malika tayi da ido kafin tace”Bansani ba,kilama itace…”Tafada wasu hawaye masu zafi na zubomata,Kuri Maman Abba tayi mata da ido kafin tace”Kinga idonki kuwa? kuka kisha haka,alhalin kisan irinku ba”a son suna shiga damuwa ko zama da ciwo haka..”Jin haka yasa kuka ya ciyo Malika batasan sadda ta fada jikin maman Abba tana Fadin”Toh ya zanyi..? Maman Abba ki Fadamin ya zanyi? Aure zai fa zai kara..”Tafada cikin gunjin kuka tana Rumgume maman Abbah.
Maman Abba datayi mutuwar zaune jin Statement din Malika na karshe da azama ta dagota hannuwanta dafe bisa kirjinta tace”Ki!…Me?Kishiya fa kikace? wai da gaske kike Madam..?Malika na kuka tace”Wlh da gaske nake,kuma bai sanar dani ba mahaifiyarshi ne, ta kirani take gayamin..”Zaro ido Maman Abba tayi kafin tace”Ke don Allah..? Kina nufin shi bai sanar dake ba? kan durun jar uba ni Samiha,Yo Allah na tuba ni kishiya ko tashiga motar hayace ai bana bukata,balle ta raba miji..”Tafada tana jinjina Abun.
Kan kafadarta Malika ta yada kai tana kuka,Rumgumota Maman Abba tayi kafin tace”Ammh ko bai kyauta ba,ai ko bakomai kyaci darajan cikin dake jikinki da kuma soyayyar data hadaku zuwa ga aure..”Dagowa malika tayi tana kallon Maman Abba kafin tayi mata mirmishin yake tace”Bazan ci wannan darajan ba Maman Abba,ba auren soyayyah mukayi ba,hasalima auren mu ba kan Turban zama bane,an kulla shine kan Turban _SAI NA RAMA_………”
Jagale Maman Abba tayi tana kallonta kafin tace”Ban fahimceki ba…”Tafada cike da mamaki,gyara zama Malika tayi tana kallonta kafin tace”Nasan bazaki gane ba,sai kinji lbrinmu daga Farko har karshe…”Nan Malika ta Shiga bama Maman Abba tarihin rayuwarta Tundaga farko har zuwa aurenta da Saleem,da komai da komai bata iya boyemata ba,ta karishe tana Fadin”Na sanar dake lbrina ne,Maman Abbah domin kila kina da hanyar da zaki Taimakamin,wlh inason Saleem so mai tsanani,ammh naga alaman ni bana gabanshi ya tsaneni,Tun kuskuren dana aikata abaya,ya zanyi..? Wani mataki zan dauka nima yasoni kamar yadda mazaje keson sauran matansu..?
Tafada tana tsananta kukanta,Sai gashi Maman Abba ma kuka take,kukan tsausayi Malika da kuma rayuwar datake ciki,Riko tayi ta mikar da ita tsaye tana Share mata kwallah tace”Hakika lbrin rayuwarki Abun tsausayi ne Malika,ki kwantar da hankalinki insha Allahu sai inda na gaza,zan taimaka miki wajen samun soyayyar mijinki ahannunki,wanda nake da tabbatacin cewa shima yana Sonki..”Malika ta girgiza kai tana Fadin”Bar gayamin haka saboda naji dadi ni nasan cewa Saleem bayasona ya tsaneni..”
Maman Abba tace injiwa? wlh dabaya sonki babu wanda zai tilasta mishi zama dake Malika,yana sonki buh Shikanshi baisan yana sonki ba,kece ya kamata kitafiyar dashi ta hanyar da zai bayyanar da son nashi batare daya sani ba..”Zuru malika tayi mata kafin tace”Ta yaya kenan..?
Mirmishi Maman Abba Tayi kafin tace”matso da kunnanki kusa kiji..”Da hanzari malika ta matso da kunnanta Maman Abba tayi mata rada,wanda ya sata sakin mirmish,gira maman Abba ta dagamata tana Fadin”To ya..? Mirmishi ta saki kafin ta bata hannu suka Tafa tana Fadin”Mu wayewar banza ai muna da ita Maman Abba,barikin ce kadai bamu kware akai ba..”Dariya suka sheke dashi kamar basu bane dazu suke kuka ba.
Maman Abba bata tafi ba,sai Da rana ta kana ta koma gidanta tayi aiki ta dora girki,Tunda yau Dutynt dare take dashi,Malika taji dadin shawarwarin Maman Abba,ko banza ta samu mai bata shawara da kuma wanda zata kallah yau amtsayin wacce suke da kyakyawan alaqa da ita,Shikenan jiki ya warware dama kishi ne da rashin abokin shawara,koda Saleem yadawo da rana ya kawo mata abinci ya ganta ta samu sauki,har Fuskarshi taga jin dadinshi ba kamar yadda ya fita da safe ba
Ita da kanta ta kira Hajiya binta take sanar da ita auren da Saleem zai yi,Hajiya tayi Shuru aranta tana salallamin Malika da kishiya ai sai Allah,toh meta sani banda gata da sangarta,Hakuri dai tayi ta bata da kuma kara jadaddamata data kula da kanta da Abunda ke cikinta,daga karshe tasanar da ita da zarar Joda ta kamallah Semester ta karshe zata turo mata ita ta taimakamata har ta haihu,Malika taji dadi sosai har sai da Ta nunama Hajiya murnanta tana ta mata godiya.
Hajiya binta batayi karambanin sanar da Daddyn Malika Ba,saboda gudun tashin hankalinshi balle akwanakin nan Ciwon nashi yatashi har suna Tunanin komawa ma asibiti asake dubashi,ko tashin jikin nasa ma Shi yace kar asanar da Malika saboda kar hankalinta yatashi har yataba lafiyan Abunda ke cikinta..
—————————-
Bayan kwana biyu da yin haka Kawai yana zaune a cikin office dinshi misalin karfe Uku na rana sai ga wayar Abbi,gabanshi har yafadi daya ga kiran,cikin sanyi jiki ya daga kiran,Yana ma Abbi sallama bai amsa mai ba yace cikin wata murya mara Dadi..”Saleem don Allah komai kake yanzu ka bari kataho katsina,asibitin da”aka kwantar da Mahaifin malika zaka zo,domin nima da safe matarshi tamin waya akan nazo jikinsa ya tashi Tub jiya da daddare,basu kwana agida ba sai asibiti,kuma yana ta kiran sunanyeku kaida Malika..”
.
Zumbur ya mike yana Fadin”Innalillahi…Ganin nan zuwa yanzu insha Allahu..”Yafada yana goge zufan dake kwararo mai ta saman kanshi,bai dauki komai ba,sai makullin motarshi ya Fice da hanzari yana addu”an Allah ya tashi kafadan Daddy ko gida bai koma ba,daganan ya dauki hanyar katsina bai ma Tuna daya biya ya sanar Da malika ga inda zashi ba,jin yanayin muryar Abbi dayaji shi ya tabbatarmai da Jikin Daddyn ba dadi…
MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
