Search
You have no alerts.

    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    ………………………”Tunda Suka dau hanya bai kara koda kallon inda take ba,Tukinshi kawai yake,sai da sukayi nisa kana ya Saka karatun alqur’ani cikin kira”ar Mallam Abdullahi Abba,cikin Suratul Maryam,cikin kwarewa da zakin murya da hadda mai dorewa yake bin karatun…..

    Tun tana rakube gefe,tana kallonsa Abun na burgeta hardai ta saki jikinta tana morema kallonshi,sai taga kamar zai waigo,sai tayi saurin kauda kai tana Kalle kalle,shiko yana ankare da ita,kawai ya barsane saboda baisan yawan mgana kada yarinya ta rainashi,duk da mawuyacin abune hakan tafaru,duba da yarda ya darsar da Tsoro mai girma azuciyarta.

    Tuntana jin dadin Tafiyar har ya Fita kanta,don wannan Shine karo na Farko datayi tafiyan mota mai tsawo haka,Tun tana kalle kallen hanya,har dai wani Barci mai dadi da Nauyi ya kwasheta,bata farka ba sai dataji yana daka mata tsawa da Fadin

    “Ke…”Firgita tayi tatashi da hanzari tana mutseke idonta daya chanza kala,saboda barci,tsaki yaja ya bude murfin motan ya Fita,sai lokacin ta waiga taga motar su ta tsaya abakin wani masallaci haka,agabansu taga wani Symbol an Rubuta *WELCOME TO ZARIA..*

    Gyara zama Tayi tana bin wajen da kallo yadda yake da Hada hadar mutane,ga masu saide saide,nan kowa nata sha”aninsa waje kamar kasuwa,tabe baki tayi tana ganinshi ya tsallaka titi yaje ya dauki buta ya zuba Ruwa yashige wani lungu,da alamu zai kama Ruwa ne,sai zuwa chan taga ya Fito yaduka yafara alwala,har ya idar tana kallonshi ta kuramai ido ta cikin mota,tana mamakin yadda taga shi alwalanshi dabam dana mutane😂kodai naki ne daban Hajja malika.

    Agaban idonta ya Shiga masallacin ya dau tsawon mintina kafin ya Fito,kai tsaye ya tsallako Titin yazo ya bude mota ya shiga itako Tun lokacin data hangi wani mai doya da kwai yana soyawa taji miyanta ya tsinke taji shi take bukatar ci,har ya tada motar tana ta kallon Doya da kwan,inda take kallo ya kallah kafin yace”Ke lafiyanki kuwa kika kurama bawan Allah ido yana kan sana”arshi..”?

    Hadiye miyau tayi tana kyafta ido,kamar wacce tayi karya,Sake baki yayi yana kallonta yadda takara kafe mai doya da kwai da ido,Girgiza kai yayi yana Fadin”Wai miye haka? ko zaki ci ne..? Da sauri ta gyada mai kai tana kara kallon mai doya da kwan,Sake baki yayi yana kallonta kur kafin yace”Ke kina da hankali kuwa? wanchan doyan da ya wuni awajen tun safe all Diseases sun gama sauka akanshi..?

    Sadda kai tayi tana Share kwallah kamar wata yarinya bai yi mgana ba,illa balle murfin mota dayayi ya Fice da kanshi ya tsallaka wajen mai Doya da kwan ya Siyomata na 1k cikin leda,ya kawo mata,jikinta na rawa ta cafki ledan ta bude har miyanta nabuzowa ta Shiga ci hannu baka hannu kwarya.

    Hannu ya harde kawai akirji yana kallonta yadda take tusa doyan kamar ta samu abinci,aransa yana mamakin kodai yunwa takeji ne? bai samu zarafin mgana ba,saboda ganin ta kusa cinye doya da kwan,haba ya rike kawai yana kallonta cike da mamaki,Haushin kanshi ma yaji da kallonta dayakeyi tsaki yaja ciki ciki ya Kunna motar yatadata suka Fara tafiya cikin slow.

    Itako Malika hankalinta kwance take cin Abunta,sai dai kuma chan sai zuciyarta tafara tashi,dakatawa tayi tana yamutsa Fuska,ta ture ledan tana toshe bakinta sboda yunkurin Amai data Fara,Kallonta yayi rabin hankalinsa naga driving Yana Fadin”Ke wai lafiyan ki kuwa..?

    Hannunta na bakinta tace”Amai nakeji..”Tsaki yaja da karfi yana kokarin samun wajen parking yake Fadin”Ba dole kiji amai ba,kalli fa Abunda kika yabama cikinki,kina ci kuma babu Natsuwa…”Yafada daidai yana parking din motar,kogama tsayawa batayi ba ta balle murfin motan ta Fice da gudu,nan bakin Titin ta gudu ta Shiga kelaya amai gwanin ban tsausayi,Fitowa yayi yana kallonta cike da takaichi yadda ta tara mai jama”a marasa gani su kyale,wani ma cewa yayi haba yallabai kamata mana wai sannu baiwar Allah”Haushin hakane yasa yaki karisawa gareta,sai dai kuma karfinta ya kare,don duk Abunda ke cikinta sai da ya Fito,tun tana yunkurin Aman harta kai tana neman Faduwa daga durkushewan.

    Cikin Zafin Nama ya isa gareta ya Rikota da hanzari yana Fadin”Ke miye haka..? luuu tatafi jikinsa tana neman gadashi,Rikon ya tsaurara yana binta da kallo yadda ta bata gaban Hijabinta da amai da kuma bakinta,Saboda yadda jikinta yayi lakws ko idanuwanta bata iya budewa,Rasa yadda zai yi da ita yayi kawai sai ya zaunar da ita da karfi akasa yana Fadin”Ki zauna Dakyau zani mota na dauko miki Ruwane,in kuma kika saki jiki wlh kisha kasa no my water inside..”Ya fada yana Sakinta da hanzarin ta Daba duka hannyenta akasa ta dafe kada tasha kasa don ta lura Saleem kan babu mutumci A al”amarinsa.

    Cikin motan ya koma ya dauko mata ruwan goranshi,tun da sh ma’aboci shan Ruwa ne,baya rasashi yana zuwa ya bude ya mika mata,jikinta na rawa ta karba sai dai kuma ruwan na neman barewa saboda Bata da karfi jiki,saurin rikewa yayi yana zabgamata harara bai Saurareta ba ya shiga kwararamata Ruwan agaban Hijabinta aman ya Gangara,ammh bai saka hannunshi ba,hannunta yace ta tara ya zuba mata Ruwa,Ta kuskure bakinta ta zubar sau uku kafin ya zubamata ta wanke Fuska,yana shirin zubda Sauran Ruwan ne tace ahankali..”Zan sha ruwa…”Bai kalleta ya mikamata kawai aransa yana jin Haushin kansa,kawai an cuceshi an hanashi kuka.

    Sai da tasha ruwan sosai kafin ta zubda Sauran Tana ajiyar Zuciya Kallonta yayi yana duba agogon Fatan dake hannunsa yana Fadin”Kinga Malama zaki tashi mu tafi ne,ko kuwa ni nayi gaba ne..? yafada yana Wani kallonta a hagunce,Tana jin haka tafara kokarin mikewa,ammh kuma takasa,saboda kanta dataji yayimata Nauyi,dafe kasa tayi tana cije baki ta samu ta mike tana Mustsike ido,ammh kuma kafafunta na rawa,ganin zatayi baya yasa tayi hanzarin mikamai hannu ya kamata,ada yaso yaki mikamata hannun nashi ne,ammh ganin dayayi zata Fadi da gasken shiyasa ya mika mata hannunsa da karfi ya rikota tayo Rimi ta fado jikinsa bata samu masauki ako”ina ba sai Afaffadan kirjinsa.

    Dukkansu sai da jikinsu ya amsa,shi harda sakin ajiyar zuciya ammh Siririya,ganin suna bisa Titi ne,kuma mutane na Wucewa suna ganinsu,shiyasa ya sassauta rikon dayayi mata yana Fadin”Ke miye haka,baki da kunya ko? yafada yana kallonta cikon ido,bata kulashi ba Tunda ta samu ta iya tsayuwa da kafarta sai kawai ta sakeshi ta Wuce ta Shiga mota tana sauke Numfashi.

    Tabe baki yayi Ya shige bangaren Direba yana kokarin tashin motan ne yaji muryanta tana Fadin”Ban yi sallah ba..”Bai ko kalleta ba sai da ya tashi motan ya daidaita bisa Kwalta kafin ya kalleta yana Fadin”Ke wai don Allah hala ni bawanki ne? karki ka ga nayi Shuru na kyaleki kina Abunda kika dama,Tun dazu daga kice wannan sai kice wannan,kamar kin samu wani sakarai ko bawa,Toh bari kiji kada ki dauka don Mahaifinki yabani amanarki,zan lalace agindi ina miki bauta ba,u bettee stand up yarinya,don Wlh ni ba bawanki bane,uselless girl kawai…”Yafada yana Huci.

    Hawaye suka wanke mata Fuska ta sadda kai tana Sharbewa wani wawan tsaki yaja yana Fadin”Ji bakinta don Allah,wai banyi sallah ba..? Ke dama kina sallah ne,kin ma san wani Abu waishi addini ,tsayama don Allah plz ke musulma ce..? Yafada yana kallonta kai tsaye duka hannunsa na kan Sitiyari yana murzawa,dagowa tayi ta kallesa Idanuwanta cike da mamaki bata samu zarafin mgna ba ya katseta da cewa”Eh nace ke Musulma ce? Koda ke musulma ce,ina tamtama da addininki don ban yarda da Kalmar shahadanki ba,sai na kara fada miki kin tabbatarmin tukunnah..”

    Jagale Tayi tana kallonsa cike da mamaki,gefe daya kuma Zuciyarta cike da tsoro na,hallayar Saleem wadanda suke Fitowa daki daki,ganin yadda take kallonsa tana tsiyayan hawaye yasa ya watsamata harara yana Fadin”Stop looking at me,in ba haka ba yanzu na chanza ma Fuskarki kammani,Bush girl..”

    Tana jin haka ta maida kanta gefe,tana tsiyayan hawaye,kukan tsausayin kanta na kamata,tanayi tana saka gefen hijabinta tana Sharewa hawaye dagan motar ta dau Shuru,tuni ya taka motar yana Gudu son Ranshi kamar zai tashi sama.Itako Tun tana kuka har ta hakura wani barci ya sake kwasheta ta sulale bisa kujeran motan tana barcinta,sau daya ya kalleta bai kara,ammh Ransa in yayi dubu ya baci gabadaya an kashemai Rayuwa,tsakani ga Allah.

    Yana shiga gidansu Ana kira kiran sallah mangariba,har yasa motar nashi aparking space Malika bata Farka ba,shikuma bai tasheta ba,sai da ya Fito ya bude booth din motar Megadi ya cida akwatunanta zuwa cikin gida yana masa barka da zuwa,Bude motar yayi inda take ya duka ya fara marin kumatunta yana Fadin”Ke..Ke..Tashi mana..”Dakyar Ta bude ido tana binshi da kallo idanuwanta suna budewa dakyar.

    Gaba yayi yana kokarin ciro wayarsa Daga aljihu wacce ke neman Dauki,sunan Abbi yagani,bai daga ba illah waigowa da yayi yana kallonta ta Fito daga motar tana tafiya dakyar,Wani kallo yake mata na lalle yarinyarnan,ganinshi tsaye yana jiranta yasa ta daga kafa ta cimmai,bai mata mgana ba,yayi gaba tana binshi abaya tana kallonsa yadda yake komai cikin izza da jarumta,Aranta tana Fadin ga Namiji har Namiji ammh ya bata kanshi da mugunta da mugun Hali.

    Ummi na zaune Afalo ita da Hajiya suna hira,suka ga megadi na Shigo da akwatuna,cike da mamaki suke binsa da kallo har ya dire Akwatun a tsakiyar Falon yana haki,Hajiya tace”Kai daga ina kuma wadanan kayan? Bakinsa awashe yake Fadin”Magajin yallabai ne,ya iso yanzu..”Kowa yasan haka yake cemai Basu samu zarafin mgana ba,sukaji sallamar Saleem ya Shigo Falon bayanshi kuma Malika ce tana Tafe tana kalle kalle.

    Da hanzari Ummi da hajiya suka mike,Hajiya ce ke Fadin”Lale..Lale marhababiki..”Take Fada bakinta washe,lokaci daya da”a tarihin rayuwar malika datataba dukawa tana gaida wani,har kasa ta zube saman cafet tana Fadin”Ina yini..”Bakinta na rawa,Hawaye na tarowa a idanuwanta,tarota hajiya tayi tana Fadin”A’a tashi ya’nan nan ma ai gidanku ne..”Saleem dake gefe yaji kamar ya make Hajiya saboda shisshiginta,Tsaki yaja aciki yana kallon Ummi yace”Ummi na Fita yanzu ko? Hararansa tayi tana Fadin”Bansani ba…”Kwabe Fuska yayi kamar zaiyi kuka yake Fadin”Nidai wlh An tsaneni agidan nan,daga dawowata ba wanda yayi kewata,Abbi ya koroni ke kuma yanzu kina hararata..”

    Malika dake zaune kan kujera kusa da Hajiya take binshi da kallon mamaki,ashe dama ya iya mgana cikin Dadin rai,Bata gama mamaki ba taga Ummi taja kunni da karfi kafin ta Mangareshi a keya tana Fadin”Eh din an tsaneka ka gyara halinka in kaji haushi..”Kara yasa yana yarfe hannu yana kuma rike kunnashi Dariya hajiya tayi tana Fadin”Ke Aisha,wannan ai ba duka bane tabashi kikeyi,ki gaframai mari mai zafi kigani in zai kara mgana..”

    Wani bad look yabama Hajiya kafin ya Daga hannu yana Fadin”Eh sannu fa,toh bata gafrin ba ko ke zaki Gafra min ne,Uwata…”Mikewa tayi tana Fadin”Sosaima kuwa yaro..”Ganin Ta nufoshi gadan gadan yasa ya arce da gudu,sai suka ci karo da Abbi wanda saukowanshi kenan jin hayaniya,Rikesa yayi yana bin Ummi da kallo wacce ke gefen malika suna gaisawa,Yana ganin Abbi sai ya kame hannunshi A gefen kunnenshi yana Fadin.

    “Sir…”Mirmishi yayi mai kafin shima kawai ya kamemai,dariya su Ummi suka saka ita da Hajiya itako Malika mamaki Saleem ke bata,ashe ya iya mu”amala da mutane haka? Rikosa Abbi yayi har zuwa wajen dasu Malika suke,wanda tayi saurin mikewa tana gaishesa da Abbi,saboda kunya mutumin ba tun yau ba,tun yana zuwa duba Daddynta.

    Amsa mata yayi yana tambayanta ya Daddnyta da jiki asanyaye take karbamai,Ummi ya kallah yana Fadin”Kamata Aisha ki rakata dakin Saleem din,ki saki jikin yata,nan ma kamar gidan ku ne kinji..? Gyada kai tayi,ammh gefe na zuciyarta na rawa da Fargaba hade da tsoro,na jin ance a kaita dakin Saleem.

    Shima yana jin haka ya gimtse Fuska yana Fadin”Dakina kuma Abbi? ina laifin Saleema,tunda yar’uwantace mace..”Karo na Farko Da Daddy ya mangareshi akai yana Fadin”kaga naka nan, don yar”uwantace mace,ko saleeman na nan ai kafita kusanci da ita,ba matarka bace ok baka tuba ba ko,dama tuban na karya ne..”?Da sauri ya rike hannun Abbi yana Fadin”No Abbi wlh Tuban gaskiya ne,nakuma yi niyyah bazan kara aikata makamancin haka ba..”Gyada mai kai yayi yana Fadin”Gud..Maza dauki kayanta ka shigar mata dashi,ke kuma Ummin Marwan,ki sama mata Abunda zataci Tunda sunsha tafiya…”

    Hajiya tace”Gaskiya kam,gashi kuma kusan mace mai shigan karamin ciki yanzu duk jikinta yayi mata Nauyi. “Afakaice ya zabgama Hajiya harara yana kunkuni aranshi,yana gani Ummi ta rike malika suka nufi dakinshi kamar ya kurma ihu ba dama.

    Kan daya daga cikin Kujerun Falon Abbi ya zauna yana Fadin”Yanzu mukayi waya da Alhaji Abdulmalik yana tambayana ko kun kariso nace haryanzu baku zo ba,yace yana ta kiran wayoyinku duka bai samu ba,kakirasa ka shaidamai kun iso..”Da Tom ya amsa yana latsa wayarsa bai sanar da Abbi tun wanchan lokacin ya sagale Nombar Daddy ba,sai ya lallaba ya ciresa daga blacklist,kafin ya kirasa Yadaga suka gaisa kafin ya sanar dashi sun iso,gama Abbi zai mai mgana,cike da fara”a Abbi ya karba suka gaisa kafin su cigaba da tattaunawa,daga karshe Abbi ya tabbatarmai da cewa kada ya damu insha Allahu zai kula da rayuwar malika tamkar yadda zai kula da Da’nsa Saleem,Daddy yaji dadin haka sosai,sukayi sallama cike da Farinciki.

    Mikamsa wayarsa Abbi yayi yana Fadin”Dauki kayanta ka shiga mata dashi ciki..”Jiki asanyaye ya mike aransa yana Fadin”Karyata takusa karewa,daga ramuwa na koma dan dakon kaya…”Yake fada yana daukan manyan akwatun guda biyu ya nufi dakinshi yana Ayyana yadda zai Fita daga wannan gadar zaren daya Fada.

    Yana Shiga dakin nasa,ya tarar da Ummi zaune gefen gadonshi ita da Malika,da alama mgana take mata,ita kuma malika tana gyada kai,wani haushi ya kamashi kai tsaye ya wuce wajen makeken wardrope dinshi yana ijiye akwatunan,ya juya zai Fita kenan Ummi ta mike tana Fadin”ina zaka,dawo ka hadamata ruwan wanka,tayi sallah,ni kuma bari naje na hado muku Abincinku ko..”

    bai waigo ba yaji ya daskare atsaye saboda wani kololin Abu dayazomai Wuya,Ummi bata Fahimci halin dayake ciki ba ta Fice tana jawo musu kofa,Juyowa yayi yana kallon Malika wacce kanta ke duke tana wasa da zabban hannunta.

    Kugunshi ya kama da hannu Biyu yana Fadin”Kuturin bala”i kenan ruwan wanka?lalle ya kamata nazo nayi gaba Tunkafin na tashi daga *SAI NA RAMA* na koma _SALEEM BAWAN MALIKA_………”

    Yafada yana jin Tukukin Abun har cikin ransa,Itako tana zaune,sai da mganar ta kusa sata dariya,tayi saurin Rufe baki tana rawan jiki,Ganin ya Tsuramata ido yana kallonta cikin ni ki kema dariya? lalle zaki ci ubanki yanzu kuwa..”

    Bai kara kallonta ba,ya shige tailet din da karfi ya bango kofar kamar zai ballah,ajiyar zuciya ta sauke kafin ta fara bin dakin da kallo,komai neat,kamar ba dakin Namiji ba,koda yake ta lura mugun baida kazanta yanaji da kansa.

    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    Note
    error: Content is protected !!