Search
You have no alerts.

    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
    “Da wannan bakin lbrin su Abbi suka koma ma su Ummi,wanda suma Abun yadakesu sosai,Abbi kuwa daki ya shige,ya kwanta yayi Shuru cike dadamuwa domin Tundaga wayewar gari zuwa yanzu baisan adadin mutanen da suka kirasa ba,suna tambayansa,game da al”marin ba,Toh mezaice musu banda eh,Domin bashi da ikon boyee Abunda ya Fito Fili,gabadaya kunyar Alhaji Abdulmalik da Duniya gabadaya ta kamashi,yarasa ina zai saka kanshi,saboda yana Tunanin koda zai kwana yana rantsuwan baisan gudurin Saleem akan Malika ba,wlh karyatashi za”ayi,Tunda da kafarshi ya taka yaje nema masa auren nan,ammh wlh ko alama baida sani game da mugun kudirin Saleem.

    Abunda yafimai Ciwo shine yadda Saleem ya ci mutumci Malika,kuma ya tozartata mafi munin Tozarci kamar wani dabba,wanda baije mkranta ba,ko wanda bai taba sanin Addinin ba,ai duk mai cin zarafin mace dan akuya ne,kuma duk mai Ramuwa kan mace tayimai Abu bai cika jarumi,macen da”aka halliceta da hakarkarinka,kafita daraja ta ko’ina kana gaba ita akowani fanni,kai Shugaba kake gareta,ammh saboda sakarci kakoma bayanta kana wani kunfar baki,Haba ai aiko anyi asara ba kadan ba,Shi ji yake kamar Saleem ba jininsa bane,Tunda har zai iya tozarta mace,wanda Shi Tunda yake baitaba kwatanta ynkuri tozarta mahaifiyarsu ba,balle yace gado yayi ko kuma Abunda yaga anayi ne ya kwaikwaiya,Toh ba daya kanwar Biyu kawai Duniyace tare da Shedan suka kulla Abota dashi yaci zarafinta,daga karshe ni kuma ya batamin suna,ammh bakomai Duniyace ta ishi wanda baizo bama,ballatana wanda ke cikinta,Haka Abbi yayi ta sake sake aransa,Abun yaki barinsa ko kadan.

    Sai da Ummi tazo tayi ta lallashinsa,tana bashi baki kana ya dan sausauta damuwarshi,yana kada kawai,domin Shi kadai yasan Abunda ke ranshi,na bakinciki da takaichi,haka mutanen kumo suka koma suma da lbri mara dadin ji,Itako Hajiya Babba baki ta rike tana Fadin”Anya ni kabiru shigan Salihu aikin yan sandan ba shaye shaye yaje yafara ba..?

    Ya marwan ne yace”Ba wani shaye shaye Hajiya,dan iska ne kawai,kuma ba komai yakeso yaga ya cimma ba,sai bata sunan Abbi aduniya,kuma ya aikata hakan shikenan aie..”,Yafada yana huci Girgiza kai Hajiya tayi kafin tace”Anya ni ina tamtama kila dai yafara shan Wiwi ne aboye ba”a sani ba,ammh cikakken mutum mai hankali bazai aikata Abunda ya aikataba gaskiya..”Tafada tana jadadda Bayaninta,ba wanda ya sake kulata,domin kowa yasan Saleem ko taba bayashi tsabar Wulakanci ne da tozarci kawai,Shi kanshi marwan Saboda halin da”ake ciki ya sa yakara kwana biyu kafin yakoma,rana daya Suka wuce da Sadiq.

    Itako Saleem dataji lbrin Abun yayi mata dadi,domin tace Abunda ya saleem yayi Shine daidai,domin ita haka kurum ta tsani Malikar wlh,taji yadda aka koyamata Hankali,tayi kokarin kiran Layin ya saleem,din ammh bata tafiya,sai da sukayi waya da Sadiq ne yake sanar da ita ai Saleem baya kasarma,shi ya sanar da ita Abunda ya faru da Malikar da mahaifinta,wanda ko alama bata tsausaya musu ba,sai ma Allah kara datakeyi acikin zuciyarta,gefe daya kuma tana sakama Saleem Albarka.

    *

    Kwana uku kenan da Faruwar al”amarin Inda Malika ta farka,tunda ta farfado,ta kuma dawo daga hayyacinta ta tuna dukkan Abunda ya faru da ita batayi mgana ba,illah kuka datake tayi,wanda baya da Sauti sai dai kaga hawaye nabin gefen idonta yana gangarowa,komai sai an mata bata iya zama saboda Dinkin da akayi mata akasanta,wadanda dai ada ta raina su ke dawainiya da ita,Hajiya binta da joda,wadanda tsausayin Malikar yakasa barinsu sutuna Abunda tayi musu abaya,Bata iya mgana sai dai kallo da ido,bini bini kuma sai kuka.

    Ayayinda Alhaji Abdulmalik kam jiki sai godiyar Allah,domin bakinsa ya karkace baka iyama jin Abunda Yake fadi saboda baknsa babu Dadi,ammh kowa ya Fahimci Malika yake tambaya,wacce kuma anki sanar da ita Halin dayake ciki ne kada takara shiga wani hali.

    Yan Malumfashi Sun koma,illah Kawu Shitu da”aka bari sai yadan kara kwana biyu,saboda ya taimakama Hajiya binta da jinya,Tunda Masu laluran guda biyu ne,kuma ita kadai bazata iyaba,Don ma Joda na tayata kula da Malika,shiyasa Abun yazo mata da sauki.

    Sai dai Malika tayi sati kana tafara koyon zama da dubara,kuma aranar ne tayima Hajiya mgana tana tambayan Daddynta,Dafa kafadanta tayi tana Fadin”Ina so ki saurareni dakyau Malika,ki kuma yi hakuri da Abunda zan sanar dake,bisa faruwar Abunda ya Faru dake,shiya yi sanadiyar Faduwar Mahaifinki har Dalilin haka yasa ya kamu da ciwon barin jiki,yanzu haka shima yana kwance acikin asibitin nan..”

    Zaro ido tayi kafin ta fashe da kuka tana kokarin tashi,ta riketa Tana lallashinta,ammh ko sauraranta batayi kukatake Wurjanjan tana kiran Sunan Daddyta nan Hajiya binta ta kalleta tana Fadin”Kidaina kuka bari likita yazo indai da yuyuwar zuwa ki ganshi sai na kai ki ki ganshi,ammh tabbas Alhaji yaga jarbta asakarma ka y’a adaren Aurenta,kuma bayan angama cin zarafinta…,”Tafada tana jin kunar Abun.

    Cak Malika ta tsaya da kukan datakeyi kafin ta Dago tana kallon Hajiya Binta tana Fadin”Saki kuma..? Ta ambata tana jin wani iri acikin jikinta,gyada mata kai tayi kafin tace”Kwarai da gaske,bai barki ba,sai da ya Rubutu miki takardan sakinki Malika,bayan ya dawo ma mahaifinki dukkan kyautan dayayi zuwa gareshi,kuma ya sanar dashi cewa bai aureki don yana Sonki ba,sai don ya rama Abunda kijayimai….”Kuka yakara kwacema Malika,tanayi har takoma Daga kwance tana Tuna kalaman Saleem inda yake Fadin _Zan Lalata miki Rayuwa adare Daya,kamar yadda kika lalatamin nawa a Shekaru biyar da suka Wuce.._

    Shi kawai take tunawa tana tsiyayan kwalla,Tana kuma jinjina kai,bata gama Tunani ba,Hajiya binta ta katseta da cewa”Kuma yanxu amganar dani ke miki,baya kasarnan akace Tun ranar daya aikata gudurinsa yasa kafa ya bar kasar gabadaya,Abun takaichi da haushi kamar yadda Aurenku ya game Duniya haka lbrin sakin Aurenki yagama zaga Duniya,saboda rashin adalcima muna Asibtin nan,Yan jarida sun zo har nan,suna kokarin jinta bakinmu akan gaskiyan Abunda ake yawo dashi Aduniya…”Ai sai Malika taji kamar zata Shide,yanzu kamar ita Malika malik,itace wannan Abun ya faru da ita kamar amafarki,yanzu duk jin kanta da yansda maza ke tsoronta,ammh an samu mai Wulakanta rayuwata haka bayan ya tozartani..? take tambayan kanta tana kuka harda rike kai.

    Kallonta Hajiya binta tayi cikin tsausaya take Fadin”Kuka yazama dole Malika,ammh kuma bazan gaji da Furta muku wannan kalmar ba keda Alhaji,wlh ko kaffara ba zanyi ba,Allah ne,ya turo saleem ne cikin rayuwarku keda Mahaifinki domin ya koya muku Hankali,kuma ya nuna muku Akwai Abunda kudi da takama bazasu taba baka ba,yanzu Duk kudin Abbanki bai isa yadawo miki da budurcinki ba,kuma bai isa ya dawo dake Daga Malika bazawara,zuwa Malika budurwa wacce batataba aure ba,Bai isa ya kankare ikon rabbi ba,Domin bakin Alkami ya rigaya daya bushe,Da ace ke dashi kun dauki Nasihata,da kuma mganata akan ki gyara rayuwarki,da duk haka bata Faru ba,ammh kuka kekesa kasa kuka jina,kuna ganin kamar ina Takura miki ne,gashi yanzu komai ya kwabe Zakuyi Nadama sanda bata da amfani . “Tafada tana Share kwallah.

    Hannuwanta ta sanya ta toshe kunnata,tana kuka harda jijjiga,kamar wata mahaukaciya,bata son mganar,ji take kamar ace yanzu ta mutu kwata kwata bata Aduniya,da wannan Abun kunyar dake rayuwarta,Ranar dai Wuni tayi kuka kamar wacce ta zauce,sai da akayi mata allurar barci kana aka samu sauki.

    *BAYAN KWANA BIYU*

    An samu cigaba sosai abangaren Daddy,wanda har ana iya Fahimtar mganarsa,kuma hakan ya samo asali ne,daga Ganin dayayima Malika taji sauki,haka ta Rumgumeshi tana kuka tana Fadin”Am srry Daddy it my Fuilt…”Take fada,shiko hawaye yake yana Fadin”A”a babby,ba kuskurenki bane nawa ne,da”ace Tun farko na doraki kan Turban da Addininmu ya koyar ban barki kara zube ba, na tabbata da baki hadu da saleem ba,balle har ki cimai zarafi ya biyo yaba yayi ramuwa gareki,na dora laifin duka akaina babby,…”Yake yana tsiyayan hawaye,kawu Shitu ne yasa baki yace in bai bar kuka toh Malika bazata kara zuwa wajensa,ba shine yasa ya daina kuka,ammh ya kafe ta da ido,yana hango tsabar rama da kuma yadda komai na Babby ya chanza,tana zaune Shuru tayi tagumi bini bini kuma ta hau sharan kwallah.

    Kwananshi hudu da fara Fitar mganarshi Su Abbi suka zo gaishesu Shida Ummi da hajiya babba,Wanda Abbi ya rike hannun Alhaji Abdulmalik gam yana ji kamar yayi kwallah,yake Fadin”Wlh Tallahi,Na rantse maka harga Allah Abdulmakalik da zuciya Daya nazo neman ma Saleem Auren Malika,bani da masaniyar Komai game da Shirinsa,Don Allah kayimin aikin gafara hakika da inada sani kan komai,wlh da ban bada goyin bayan ya aureta ba,ballantana har ya cimata zarafi…”,Yafada cike da kunar zuciya.

    Mirmishin yake Daddy yayi kafin yace”,Haba Kabir,har sai ka Rantsemin ?yau kake tare dani,Wlh na sani karka damu kanka babu komai,ni ne silan Faruwan komai,domin na bada dukkan guduMuwata Wajen lalacewar Tarbiyan Malika kamar yadda Saleem ya Fada….”

    Ya dakata yana runtse ido wasu kwallah suka zuraromai kafin ya cigaba da Fadin”Sai dai Abu Dayane yamin Yamin ciwo sakin dayayimata kabir,karka manta ko abaya na sanar dakai nayi kwadayin hada zuru”a dakai ne,saboda na samu wanda zai taimakeni ya Tarbiyartar Da malika kan hanya madaidaiciya,Tunda ni na gaza,ya koyar da ita Addinin Allah,wanda zai sa ta rabauta Ranar gobe kiyama,ammh kash saboda Kuskurena yasa Burina bai cika ba…”Yafada yana sakin kuka muryansa ta shake,yana daga kwance.

    Duk wanda ke dakin sai da yayi kwallah hatta da Ummi da Hajiya babba,sun tsausayama Daddy sosai,Hannu Abbi ya sanya yana Sharema Daddy hawaye yake Fadin”Insha Allahu burinka zai cika kada kadamu Na tabbata yanzu Malika tana matsyin matar Saleem ce,saboda na Turamai sako ta E-mail dinshi na sanar dashi matukar bai Janye sakin dayayima matarsa ba,toh babu shi babu ni har abada,kuma nasan cewa indai yaga sakona zai janye sakin dake tsakaninsu…”yafada yana kallonsa,Saboda Farinciki sai ga Daddy na Hawaye yana mirmishi.

    Sunjima cikin asibitin sai da zasu tafi suka shiga inda Malika take,lokacin da Hajiya binta ta sanar da ita Iyayen Saleem ne,Sunanshi kawai da”a ambata sai da gabanta ya fadi,lokacin data dago ido ta kalLi Abbi,kawai sai taga yana rikidemata zuwa Fuskar Saleem wacce babu digon tsausayi ko kadan,bayan taja tana makyarkyata,babu inda jikinta baya bari,hawaye kuwa sun Fara wankemata Fuska,Da suka Fahimci hakane yasa basu dade ba,suka musu sallama suka tafi,bayan su ijiye musu Katan katan din lemukan da suka kawo musu,domin dai irinsu Alhaji Abdulmalik baka burgesu don ka basu kudi har gwanda ka basu Abunda kudin ya siya.

    ___________________

    *CHICAGO*

    “””Kwance yake akan wata kujera,mai kama da goduwa,ammh ba chan ba,ya zuro kafarsa daya kasa,daya kuma ya dorata bisa wani karamin Center table din glass,wanda ke tsakiyar kayatattacen Falon konace tsararre.

    Sanye yake da wani karamin wando baki 3quater,jikinsa babu riga sai wata farar vest,wacce ta dan kamashi,ammh ba sosai ba,idanuwansa suna lumshe ne,yayin da sanyin gari tare da Dakin yake Fitar da wani Ni”ima na dabam,Duka hannunsa,suna kan kirjina,ya zagaye shi dasu,ammh kana kallon Fuskarsa zaka Fahimci koda barcin yake toh yana matukar jin dadin barcin dayake saboda yadda lokaci bayan lokaci yake sakin mirmishi shi kadai.

    Ya dade ahakan kafin naga ya bude lumsassaun idanuwansa,kamar wanda akayima duka,ayanayin yadda ya yunkura ya mike zaune,sauke duka kafafunsa yayi bisa lallausan cafet din daya malale Falon,kanshi ya jingina jikin cussion din kujerar,yana shafa sumar kanshi har zuwa fuskarsa kafin ya gangaro zuwa sajensa,da kuma gemunsa,wanda yafara barinshi yana taruwa

    Shi kadai indan ya Tuna Abun sai yaji tsikar jikinsa ya tashi,yaji gabadaya jikinsa ya saki,kuma kasala ta rufeshi,bayan Faruwar Ramuwar yaji dukkan Nauyi tare da bacin ran daya kunsa shekaru biyar sun Washe daga zuciyarsa,yaji yasamu salama da sa”ida,ammh Abun da bai sani ba shine yau kimanin kwananshi goma da zuwarshi kasar ta Chicago,duk da bai samu zama ba,akwanakin da isa,saboda zirga zirga kammallah sauran abubuwa,da kuma samun muhallin zama,wanda ayanzu yake cikin tsarin wasu apartment,masu kyau da tsari,inda yake sama hawa na biyar.

    Abunda ke bashi mamaki Shine ko da zai Wuni bai Tuna Abun ba,ammh da zarar yazo kwanciya barci,daya Runtse ido sai Abun yazomai,babu inda ke kashe mai jiki,sai Ni”mar daya kwaasa ajikin Malika,tare da wata Natsuwar da Tunda yake baita samu ba,duk da bai taba sassan jikinta ba,buh he know her body is so softy sexy and Ronantic,wani lokacin in baiyi wasa ba har mafarkin ya kara saduwa da ita yakeyi in ya tashi da safe yayi ta jin haushin kansa,dayayimata zuwa daya cizon yatsa yake aransa yana daya sani yakara Mata koda Second around ne,da Duk haka bai Faru dashi ba

    Tunani yake yana ayyana ashe haka ma”aurata ke Dibam gara bai sani ba,tsakani ga Allah Tunda kaddara tasa ya dandana,toh fa dole yazo yayima Rayuwarshi Fada,da zarar ya koma gida zai nemi mata yayi aure don tsakani ga Allah Tunda yagane Dadin wajen mawuyacin Abu ne yakara juriyan dayayi Ada,kafin yasan Dadin Abun…

    Wannan Tunanin ma dayake gabadaya tsigar jikinsa ya tashi,yanayinsa Tuni ya chanza,hannu ya sanya yana Dafe Sandar girmanshi,wacce Ta mike sambal,tana barazanar fasa wando🙈😜Dafeta yayi da karfi yana sakin Nishi sama sama,yadade cikin wannan Halin kafin ya bude idanuwansa da suka chanza kala suka koma jawur.

    Akasalance ya dago kanshi ya zura hannu ya dauko Syetem dinshi dake gefe ya she ,kan Center table din dake gabanshi ya dorata bayan ya jawo Abun zuwa gabanshi,Budeta yayi yafara latse latsenshi yafi minti talatin kafin ya fara gajiya har zai Rufeta sai kuma ya fasa, Aransa yace bari ya Shiga E-Mail dinshi ya gani ko ambarmai sakonni.

    Yana shiga ya tarar da sakonnin ba adadi,ammh sako biyu ne sukafi daukan Hankalinshi sakon ya marwan dana Sadiq kamar bazai bude ba,sai ya fara Shiga na Sadiq inda yaga uban ashariyan zagi da tsinuwan da Sadiq ya dinga jeramai,yana fadamai Halin daya jefa mutane,aciki harda halin da Malika da mahaifinta ke ciki,ko ajikinsa yana karantawa yana dariyar jin dadi,domin Tuni sunyi waya da Inspector Sale ya sanar dashi komai,duk da Tun zuwanshi garin sau daya yayi amfani da wayarsa.

    Bai maidamai da amsa ba ya Fita ya bashi waje yana yar dariya,sakon ya marwan Shi yayi Nadamar Budewa, Da kakkausan kalamai cikin Manyan haruffa yaga sakon Abbi zuwa gareshi,Zufa yaji Ta ko”ina ta zuraromai,hankalinsa in yayi Dubu ya tashi,jikinsa narawa ya fara tafamai da amsa kamar haka.

    _Don Allah Ya marwan kabama Abbi da Ummi Hakuri,wlh nayi kokarin samun wata hanyar da zanyi Ramuwana,batare da hakan ya shafesu ba,ammh na gaza na samo wata hanya,sai nayi duba naga wannan Shine hanya maafi sauki,don Allah suyi hakuri su Yafemin bazan kara ba,Kuma Wlh na janye sakin danayi mata yanxunan,Ammh don Allah kada kabari Abbi ya cireni daga cikin Sawun ya”yansa,da zarar nagama Abunda yakaini nan da wata 2month da wasu kwanaki zan dawo gida_

    Yana gama Rubutamai ya Turamai yana kashe System din gabadaya ransa amatukar bace,wlh inda yasan Abun zai gani kenan bazai taba duba sakon ba,koda yakoma gida sai ya Fake da bai bude sakon Ya marwan Din ba,Tagumi ya zuba yana ayyana irin cutar da akamai,wai ya maida shegiyar yarinyarnan dayafi tsana dakowacce mace,tsaki yaja kafin ya mike yana tafiya kafarsa na nitsewa cikin Cafet din dakin ya nufi wani koridi,jim kadan sai gashi ya Fito dauke da Ruwa ahannunsa yana sha gefe daya kuma yana duba agogon Fatan dake Daure ahannunshi,tsuke bakinshi yayi yana Fadi asarari.

    “Tunda yarinyarnan ta Shigo gonata ban huta ba,na Rama ammh kuma Kaikayi na neman yakoma kaina…Yazama dole na ninka ramuwa na akanta na ci ubanta dakyau yadda yakamata..”

    Yake Fada yana dan mirmishi kafin ya Cigaba da kurban Ruwanshi,yana wani Yamutsa Fuska kamar an sashi dole.

    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    Note
    error: Content is protected !!