Search
You have no alerts.
    The Den of Novels
    Chapter Index

    *MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE*
    Washe gari daƙyar na yakice bacci nayi shirin makaranta, ina gama karatu Bilal ya kirani har gurin ƙarfe ɗaya muna hira kafin ya barni na kwanta dama ga gajiyar dana kwaso a makaranta jiyan na ɗora data girki sannan dana dawo gidan ma ban zauna ba na tarar anyi fenti a ɗakina gaba ɗaya an hargitsamun kaya seda na gyara su sannan na kwanta. Shaf na manta da munyi faɗa da Hansa’u jiya na zauna jiran zuwanta har ƙarfe tara seda na kirata sau biyu bata amsa ba wanda nasan ba halin ta bane da wuya na kirata a waya bata amsa ba sedai irin haka idan munyi faɗa. A fili nace
    “Lallai, wai ita ta ɗauki abun har zuci ashe. Ni da ya kamata nayi fushi ta zagar mun Habibi banyi ba se ita? To ai shikenan” na ɗauki jakata da Lab coat na fito falo na tarar da Mama tana ware atamfofi. Sau biyu ina ce mata zan tafi tana mun Allah ya tsare hanya. Ɗari biyar ce a jakata, zata kaini ta dawo dani amma bani da canjin da zanci wani abu kuma yau ɗin wuni zamuyi se ƙarfe huɗu zuwa biyar zamu taso. Ganin na tsaya yasa ta tambayeni lafiya? Na shiga sosa kai, tsaki kawai Mama tayi ta buɗe POS ɗin ta dake gefe ta zaro dubu ɗaya ta miƙa mun tana cewa
    “Banda shegen iyayinki me yasa baki zo kin masa abincin a nan ba?” Karɓa nayi tareda mata godiya na fita. Ina son Mama, bata zafafawa a lamuranta. Nasan ba wani son zancen aure na da Bilal take ba musamman yanda duk yan uwanta suke sukar abun amma tunda nida Abba muna son ita ma ta karɓa tana mana addu’a.

    Seda muka fito break kafin muka tsaya da Hansa’u nace mata “wai saboda maganar jiya yasa baki biyo mun ba yau kuma na kiraki baki amsa ba?”
    “In biyo miki kuma? Ina ce kikayi kowa tasa ta fishsheki babu kr babu ni akan Bilal iyayenki ne kawai na zaki bari ba. To tunda ni ba iyayenki bace ai gara na tattara tsumman rayuwata na baki guri tunda baki na baze iya shiru ba har idan naga abinda ba daidai ba se nayi magana” Hansa’u ta bani amsa, sena rungumeta ina cewa
    “Haba ƙawata ki barni in kama wa? Ai kin san dai tsakani na dake ya wuce ƙawance kema yar uwata ce kina cikin waɗanda bazan rabu dasu ba ai” ta mun banza, dake nasan nice da laifi dukda naji haushin abinda ta faɗa akan Bilal amma kuma nima abinda na mata ya shallake wanda tamun hakan tasa na ringa bata haƙuri harta sakko muka tafi siyo fanke da lemo. Bayan mun zauna nace mata
    “Amma tsakani da Hansy dole a ringa jin kanmu har idan zaki ringa taɓa mun Yarima. Ya kamata ki ringa mun kara, ko baki son Bilal darajar ƙaunar dake tsakani na dashi ai yaci ki mun kara. Bana so ki dena zaginsa a gabana idan ma zaki zage shi kiyi can a inda bazanji ba dan nima bazan miki kara ba sena rama masa”

    “Ai shikenan, ni dai bazan zauna tare dake ina kallo kina ƙoƙarin jefa kanki a halaka kuma nayi shiru na barki ba dole in faɗa miki gaskiya ko ki ɗauka ko karki ɗauka ruwanki” ta bani amsa, a hasale nace
    “Auren Bilal ɗin ne kike kira da halaka Hansa’u? Wai me kike nufi da Bilal ne? Ki gaya mun me yake aikatawa da har kike kiran aurensa da jefa kai a halaka wane mugun hali yake dashi da ban sani ba?” Na ƙarasa ina miƙewa tsaye. Watsa hannu tayi tace
    “Kin fini sanin halakar da nake nufi sedai idan kin so ne zakiwa maganata mummunar fassara. Akwai halakar duniya data wuce mace tayi rashin dacen mijin aure? Bilal be dace dake ba, kiso ko karki so sena faɗa ke kike sonsa amma shi ba sonki yake ba idan ma kuma yana sonki to akwai dalilinsa na hakan amma ba zaki fahimci abinda nake faɗa miki yanzu ba ba kuma na miki fatan kiyi nadamar kin jij maganar masu sonki a sanda komai ya lalace miki. Tun wuri ga maza fululu masu ƙaunar ki dagaske ki nemi mijin aure a cikinsu ina mai tabbatar miki har ba Allah ya ƙaddara ba Bilal ya samu wadda ta fiki sedai kiji wani zancen wlh” ta ƙarasa tana bari na a gurin. A maimakon sulhu se gashi mun sake tafka wani faɗan dan da aka tashi ban tafi ba seda na sameta na sake zazzaga mata rashin mutunchi na faɗa mata nasan baƙin ciki take mun ba wani abu da saboda na samu me so na zamuyi auren soyayya da ƙuruciyarmu ba irinta ba da zata auri tsoho sa’an Babanta shine take mun baƙin ciki. Kwaɗayin daya kaita ta amsa zata auri tsoho shi zesa ta haɗiyi baƙin cikinta ta kalle mu ni da Habibi na musha soyayya. A bakin titi na cimmata suna jiran Adaidaita da ƙawayenmu biyu Zainab da Hussaina duk yan unguwar mu ne tare muke tafiya dama. Hansa’u ta ringa kuka ko a jikina su biyun ma da suka shigar mata nayi musu tatas nayi tafiyata na barsu raina fes domin ba wanda ya isa ya taɓa Bilal na barshi, dama ta kama kanta ta fita a sabgata dashi se mu cigaba da lallaɓa zumunchin mu amma ta soka kanta a inda ba’a gayyaceta ba.

    Dana koma gida tsaf na kwashe labari na bawa Bilal daya kirani, ga mamakina se yace wai ban kyauta ba me yasa zan mata haka ai kamata yayi naji uzurinta domin yanda muke da ita kowa yasan ba zata cutar dani ba
    “Kenan ka yarda kana da mugun halin da har zata ringa faɗar irin Maganganun nan akanka?” Na tambayeshi, se yace
    “No Halims ba haka bane. Abinda nake nufi da se ki mata uzuri ki bita a hankali kiji menene hujjojinta amma yanzu abinda kika mata gaskiya baki kyauta ba ai tsakaninku ya zarce haka gaskiya banji daɗi ba” ya ringa mun faɗa har naji haushi ma na kashe wayar.

    Kwana biyu da suka biyo baya banje makaranta ba mun samu interval kafin mu fara theory parts na jarabawa. Tun a washe gari da Mama taga har yamma bance zanje gidansu Hansa’u ba ita kuma bata ga tazo ba ta tambayeni ko lafiya se kawai nace mata jiya da muka taho gadon ƙaya ta wuce gidan yayarsu. A washe garin ranar da rana Abba ya dawo daga Enugu sunje wani aiki da magriba bayan ya dawo daga masallaci ina ɗakina na idar da sallah na jiyo yana ƙwala mun kira, Abba bashi da faɗa daga sautin muryarsa na san akwai wani abu abinda ya fara zuwar mun ko zancen Bilal ze mun tunda yace kafin ya dawo musan abinda muke ciki.

    Ina fita naga Hansa’u a zaune, a raina nace lallai ma, ƙarata ta kawo ko me? Haka na samu guri na zauna nan kuwa Abba ya haɗa mu duk mu biyun ya mana kaca kaca kowa ya bata laifinta. A yanda yace tun da la’asar daya fita aka bashi labarin wai munyi faɗa a makaranta a raina na ringa tsinewa munafukai nasan kuma baze wuce Nasir ko Musan gidan inji ba sune yan unguwar mu kuma a gabansu mukayi faɗan shine ashe sunzo unguwa suna yawo damu, Abba ya mana kaca kaca yace kuma mu bawa juna haƙuri kuma idan ya sake jin irin haka ba faɗa ba seya haɗa mana harda duka mun san kuma ze aikata. Yana da sanyi da wasa da dariya amma fa kaifi ɗaya ne muddin yace zeyi abu zeyi dan haka muka masa alƙawarin haka ba zata sake faruwa ba. Washe gari kuwa da mukaje makaranta komai ya wuce, dukda dai Hansa’u na lura bata gama hucewa ba amma ni na sake gaba ɗaya ina ta janta har daga ƙarshe ta huce muka cigaba da sabgoginmu.

    Ranar Asabar Bilal yace ze zo, tun haɗuwar mu a gidan Anty Labiba be samu ya dawo ba se waya mukeyi, sun sake komawa Abuja ance wannan watan in sha Allah albashinsu ze fara shiga harma za’a biya su na baya da basu samu ba. Naji daɗi sosai ko ba komai maganar aurenmu zata taso masu ganin ba aure na zeyi ba zasuji kunya. Allah ya sani ina son Bilal tamkar rai, yanayinsa da halayyar sa sun min a irin mijin da nake fatan aure na kuma faɗa na ƙara ciki wuya ko daɗi zan zauna dashi domin shi nake so ba wani abu ba duk wanda suke zuwa masu abin hannun da ake ganin sunfi dacewa dani ni basu gaba na shi ɗin shi nake so kuma ina ji a jikina gaba se mun zama abinda ba’ayi zato ba duk masu gulma se sunji kunya.

    Kamar ko yaushe nayi masa snacks samosa da cake se dambun nama da Anty Hasiya ƙanwar Abbanmu ta kawo masa na ɗibar masa. Tsayin fara soyayyar mu Allah keda kullum amma duk sanda Bilal ze zo sena masa abinci ko wani abun taɓawa da zan bashi. Tun Mama na biye mun harta fita sabgata a cewarta abin nawa bana ƙare bane, harta kai shi ze faɗa mun abinda yake so ko in tambaye shi babu ko sisinsa haka zanyi yazo ya cinye har ya tafi da saura balle kuma da azumi gidanmu yake shan ruwa idan be zoba zan aika masa dashi haka in sallah tayi zan haɗa sha tara ta arziƙi a kaiwa Hajja mahaifiyarsa sannan in haɗa masa wanda zasu zo da abokanansa suci se an samu me mutunchin gaske ne cikinsu ze iya ɗaukar wani abu yace mun ga tukuici amma hakan ni sam baya damuna domin dan Allah nake masa kuma arziƙin so da ƙauna.

    Seda a gama jere masa snacks ɗin da kunun aya me sanyi kafin na zauna muka gaisa muna kashe juna da murmushin ƙauna. Na cika masa kofi da kunun ayar yasha ya gode Allah yana kallona yace
    “Wato Halims, bansan kalar murnar da zanyi ba ranar da aka ƙwala shelar ɗaurin aure na dake, ina ga se na hau kan hasumiyar masallaci tsabar murna” na ƙyalƙyale da dariya nace
    “Ka dai rufa mana asiri kar ace ango ya karye a garin murnar aurensa” yace
    “Allah Halims baki san yanda nake jinki a raina bane kedai kawai Allah ya kaimu ranar da zan nuna miki komai a aikace ba surutun da kike ɗauka wasa ba”.

    Na sadda kai ƙasa ina murmushi kawai ba tareda na ce masa komai ba, ya fara cin samosa yana mun hira can yace “Albishirinki Halims” na ɗago na kalle shi tareda cewa
    “Goro” ya karɓi kunun aya kafin yace
    “Albashin mu ya fara shiga, an turo mana na wata uku jiya”. Sosai naji farin cikin albishirin ɗin nada na gyara zama ina cewa “kai alhamdulillah naji daɗi sosai Allah yasa albarka” ya amsa da
    “Amin” yana cigaba da cin kayan gabansa. Hira muka cigaba ina jira naji ya sako zancen aiko sa rana tunda salary ya fara shiga amma shiru hakan yasa nace masa
    “Dama ko jiya Abba yake sake mun magana nace in sha Allah idan kazo zan gaya maka, to ashe ma jira ya ƙare tunda abinda muke tsammani ya iso”.

    Seya shafa kansa yace
    “Eh wlh, ai Baba Malam ma yace kawunku na Galadanci ya masa magana akan akwai bikin da za’ayi acan gidan kakanninku so samu suna so a haɗa”
    “Lah bikinsu Salina ya taso kenan” na katse shi se yace
    “Ina ga su ɗin ne, yace wai wata shida suke so a saka wancan ɗin”. Ɓata fuska nayi nace “har wata shida?” Seya kalleni yana cewa
    “Yayi kaɗan ko?”
    “Kaɗan ko dai yawa?” Na faɗa ina ɓoye fuskata. Na zata ze tsokaneni akan abinda na faɗa se naji yayi shiru dana ɗaga kai na kalleshi se naga yayi shiru yana kallon center table ɗin dake aje. Da yar damuwa nace
    “Lafiya dai naji kayi shiru?” Ɗan murmushi yayi yace
    “Babu komai, kawai ina tunanin yanda al’amura zasu kasance ne. Idan son samu ne ma ni nan da wata uku ma a kawoki gida na sedai uzururrukan da suke gabana bana tunanin a shekara ɗaya ma zan iya kammala su” ya faɗa kamar zeyi mun kuka.

    Da sauri na kalleshi jin abinda ya faɗa, ya marairaice fuska yace
    “Kin san nauyin da suke kaina Halims. Yanzu fa ba tareda anyi shawara dani ba aka saka bikinsu Fauziyyah yanzu haka a yanda akayi sa ranar saura wata biyu da sati uku bikin. Daƙyar fa na lallaɓa Baba Malam ɗin aka maida sa ranar wata shida a lissafi na idan akayi nata kinga na sallameta sannan na koma kan ginina na ƙarasa se azo ayi sa ranar mu idan na samu yanda nake so ma wata ɗaya ko biyu za’a saka shikenan”.

    Kallonsa kawai na ringayi na kasa cewa komai, ban ma gane kan lissafin da yake ba. An saka auren ƙanwar sa wata shida se anyi nata sannan azo a fara maganar namu a ƙalla dai shekara ɗaya zuwa da rabi yake sake nemowa akan shekara biyar ɗin da muka kwashe. Karo na farko da Bilal yayi wani abu da naji haushinsa har raina amma bance komai ba na sunkuyar da kai kawai ina jinsa yana cewa
    “Kin san na gaya miki harda gadonta na haɗa nayi sponsoring karatu na in ba dan haka ba waye ze ɗora mun wahalar aurenta ace se na mata kayan ɗaki dole?”
    “Zaka mata mana tunda ai bata da wani yayan da ze mata bayan kai. Kaine makwafin mahaifinta a yanzu” na faɗa murya a ciki, se yace
    “Haka ne idan ina dashi zan mata amma a halin da nake ciki yanzu nima ai ban tsaya da ƙafata ba ga kuma tawa wahalar a gabana. Se yanzu nake dana sani lokacin da Alhaji Lawan yace muyi musanye na bashi kango na ya bani wani gida complete dana karɓa canjin nayi wani abu dasu ƙila da tuni yanzu mun haifi Nur da Nurain ko?” Ya ƙarasa da sigar tambaya. Ɗan murmushi kawai nayi yaci gaba da surutan da duk uzururrukan sa da basa ƙarewa ne kullum yana so yayi kaza da kaza kafin ayi waye da waye jin yanda nake amsa masa maganganun yasa yace mun
    “Ko kin fara jin bacci ne naji kina amsawa daƙyar?” Se kawai nace masa eh”. Yayi murmushi yace
    “Karki damu Halims, in sha Allahu komi ya kusa zuwa ƙarshe kinji jinkirin kuma ze zama alkhairi”.

    Murmushi kawai nayi na miƙe ganin shima ya miƙe tsaye, muna tafe yana cigaba da surutansa ina binsa da toh har muka je get. Seya juya ya kalleni yana murmushi yace
    “Halims menene?” Na buɗe ido na kalle shi nace “me ka gani?”
    “Duk yanayinki ya canza mana ko akwai wani abu da baki gaya mun ba?” Ya ƙarasa yana jingina da ƙofa tareda langwaɓe kai yayi kalar dake sake wujijji gani cikin soyayyarsa. Sena sauke kaina ƙasa dan ma karya yaudare ni. Ya cigaba da cewa
    “Kici gaba da yi mun addu’a kinji in sha Allah zan baki mamaki”
    “Toh, Allah yasa” Na bashi amsa. Yaso ya sake jan hirar amma na bashi uzurin kaina namun ciwo ya tafi. Seda na tattare sauran snacks ɗin na kai kitchen kafin na samu Mama a falo suna kallo dasu Imam. Gefe na samu na zauna ina ɓata fuska sau ɗaya Mama ta tambayeni meya faru nace babu bata sake cemun komai ba.

    Wayata dana saka caji ta shiga ƙara daga ringing tone ɗin na gane shine hakan yasa na zareta na wuce ɗaki. Sama sama na ringa amsa masa maganganun da duk kame kame yake can yace mun
    “Seda naje aje mashin na shafa naji babu komai nace yau Halims tayi mantuwa”
    “Mantuwar me?” Na tambayeshi se yayi yar dariya yace
    “Baki packaging mun sauran snacks ɗina ba, sannan abincin ma an manta dashi”. Dariya da mamaki ya bani lokaci ɗaya amma se kawai na bishi da cewa
    “Kash aiko na manta”
    “Ko na aiko a karɓa dan kin san da zan fita ma cewa Hajja nayi kar a ajiye mun abinci” ya sake faɗa, ban san lokacin da nace masa
    “Ai kana tafiya su Imam suka cinye”
    “Kai, harda girkin da kika mun?” ya faɗa se kawai nace masa
    “Ni dama banyi maka girki ba ai iya snacks ɗin nayi” ga mamaki se ji nayi yace
    “Toh shikenan Allah ya tashe mu lafiya” daga nan ya kashe wayar.
    Mamaki sosai ya kamani, wato dama abinci ya biyo baya lallaima Bilal.

    Mun saba a ƙalla koda yazo zance idan ya tafi kafin kwanciya bacci se munyi doguwar waya har se na fara bacci haka da Asuba shi ze tashe ni amma yau har na gama shirin tafiya makaranta banji wayarsa ba. Dake ban saba ba duk se abin ya dame ni na manta ma da fushin da na farayi hankali na ya sake tashi dana kira layinsa naji a kashe. Gaba ɗaya wunin ranar sururu nayi shi kowa ya ganni seya tambayi ko bani da lafiya ne haka dana dawo ƙarshe kawai nacewa Mama kaina ke ciwo na shige ɗaki naci gaba da kiran wayar Bilal amma har sannan ƙarfe biyar a kashe. Hansa’u na kira dan dama bata shiga makaranta ba ita bayan mun gaisa nace mata tazo dan Allah idan bata komai,
    “Wlh lalle aka samun na ɗauka kema zaki zo ai ko kin fasa” ta bani amsa. Shaf na manta gobe za’a fara bikin Zainab dake tunda mukayi faɗa da Hansa’u ta ara ta yafa ni kuma da muka shirya banma bi takanta ba tunda tun asali dama ai shishshigi yasa ta shigarwa ƙawata faɗa bayan munfi kusa. Ko ankon dan dai mun rigada mun siya ne amma da bazan ba.

    “Kina ina?” Na tambayeta ta bani amsa da tana gidansu Ummi me lalle se kawai na zura hijabi na Mama na mitar lallen se yamma sakaliya zan tafi me yasa bazan bari se da safe ba tunda bazani makaranta ba nace mata ai baƙi za’a mun ba ja ba. Naji daɗi da na samu Hansa’un ita kaɗai sauran duk an cire musu sun tafi kangon da za’ayi Hennah party, tas na kwashe yanda mukayi dashi jiya na gaya mata ta gama saurarona tayi shiru nace
    “Baki ce komai ba”
    “To me zance Halima? Ni da kika ce in cire baki na daga sabgarki da Bilal yanzu kuma in ce wani abu ki canza mun ma’ana?” Ta bani amsa. Se nayi tsaki nace
    “Ke matsalarki ruƙo wlh ba komai ya rigada ya wuce ba kuma? Dan Allah ki bani shawara me ya kamata nayi? Wlh ji nake kamar nayi ta kurma ihu wlh ko abinci wlh daƙyar na iya shan tea ji nake komai ya tsaya mun”

    “Lallai kinyi nisa to Allah ya taro ki” ta faɗa tana cire lallen hannunta. Zanyi magana wayata tayi ƙara, seda na sauke wawiyar ajiyar zuciya kafin na tashi daga kusa da ita inaji tana cewa
    “Ai dama kin ƙarasa zubar da ajin ya taka wlh, ai dai Halima kin bada mata Allah ya yafe miki kawai”.

    Gefe can na koma na amsa, shiru nayi ina jinsa yayi sallama seda ya maimaita sau biyu kafin na amsa.
    “Ina kika tafi?” Ya tambayeni kamar wani Babana. Na tura baki nace
    “Gidan lalle”
    “Ya miki kyau, to gani a ƙofar gida ya za’ayi yunwa nakeji na taso daga aiki naje gida kawai naga wai tuwo Hajja tayi da miyar kuka fa” ya faɗa. Sena rasa me zance masa ma, wato saboda anyi abinda baya ci a gidansu shiyasa ma ya kirani da haka nan ne baze kira ba yake nufi ko me?
    “Hello” ya faɗa jin nayi shiru sena sauke ajiyar zuciya nace
    “Ina zuwa toh” na miƙe ban ko cewa Hansa’u na tafi ba na wuce gida. Yana jingine jikin lifan ɗin sa kamar kullum cikin gayu irin na yan birni idan ka ganshi da yanayin shigarsa zaka ce ɗan wani hamshaƙin mai kuɗi ne. Wuce shi nayi na gida, ta ƙofar kitchen ta baya na shiga. Muma tuwon mukayi amma da lafiyayyar miyar ɗanyar kuɓewa data ji naman rago. Seda na ɗumama miyar kafin na zuba a flask na ƙulla manshanu a leda da yajin daddawa sannan na shirya komai cikin basket me murfi na haɗa masa da kwalin exotic ɗaya da robar ruwa. Ina zuge basket ɗin Mama ta shigo kitchen ɗin, kallo ɗaya tamun ta girgiza kai kawai ta fita nima sum sum na fice kamar wadda aka kama tayi sata, koda yake satar ma nayi ai.

    Tabbacin abinda ya kawo sa kenan ina miƙa masa basket ɗin ya ɗora a gaban mashin ɗin ya hau ba tareda yace mun komai ba ya amsa key ya bar gurin, tsabar mamaki da al’ajabi kawai na bishi da kallo se naji zuciyata ta karye banma sani ba ashe hawaye sun ɓalle mun seda na fara ganin dishi dishi kafin na ankara.
    *MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE*

    Note
    error: Content is protected !!