Kura a Rumbu – Chapter Twenty-two
by Maryam Farouk (Ummu Maheer)"Dagaske ne Anty, masu ƙwacen mashin ne suka bige shi; waɗan da suka kai shi asibitin ma na san ɗaya daga cikin su tare muka fara Maitama Sule" Mu'azzam ya faɗa jin Anty Labiba ta dage akan ƙarya kawai Bilal ya shirga ba wani abu daya same shi. Zuwan ta kenan ta tarar suna jimamin abun, Na kira Abba na gaya masa an masa takwara sannan na ƙara da faɗa masa dalilin da ya saka Bilal be duba mu ba har na bawa Bilal ɗin waya suka gaisa da Abban ya sake bashi haƙuri. Bayan. . .